Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rigar, shima a lokacin ya sake watsa ruwa yasa trouser 3 quarter da singlet ya fito dukkanmu mirmishi muka sakarwa junanmu na zuba mai sakwaran leda biyu yace in k'ara d'aya na k'ara sannan na zuba miyan a d'an bowl na miya wanda tasha ganda da kifi ,na tsiyayo mai lemon kwakwa wanda yasha Madara da flavor, Bayan na zuba mai ya kalleni yana cewa " maza sa spoon muci tare "
D'an dubansa nai amma ban tanka ba na d'auki spoon d'in na fara ci, leda d'aya naci na k'oshi shi kuwa saida yaci leda uku da rabi yasha lemon kofi uku,kallonsa nai muka had'a ido da sauri na kauda kaina ina d'an mirmishi " kallona kikeyi ko Kinga inada ci sosai , kin san ni bana wasa da cikina fa "
"Hhhhhmmmm niba haka nake nufi ba fa"

Mik'ewa yai yana fad'in "kyama fad'i gaskiya".
Nidai mirmishi kawai nakeyi.


Misalin k'arfe bakwai motocin gidan suka jeru tare da mutan gidan harda Aunty ummu sulaim don yimai rakiya wanda mota guda tana d'aukene da kayansa kuma ita zamu shiga Nidashi, ina sanye da doguwar riga bak'a me adon Brown mayafinta ne nad'e a kaina takalmina ma brown ne sau ciki, ina tsaye bakin k'ofa rik'e da wayoyinsa sanda yake gyara igiyan takalminsa, ya d'ago muka had'a ido wasu hawaye danaketa k'ok'arin b'oyewa ne suka silalo hannuna ya rik'e d'aya hannun yana rufe k'ofan part d'in namu,saida muka shiga bayan motan muka zauna driver yaja yabi bayan motocin su Abbah ya rik'o hannuna cikin nasa yana magana a hankali " Kar kiyi kuka kinji Khadeejah ki kwantar da hankalinki kamar yaune zanje na dawo shekara d'aya da y'an watanni ba yawa garesu ba kuma kinaji Abbah yace kina samun hutu zakuzo min sannan Nima zanzo in mun sami time ko yaya ne , karki damu kinji ,ki maida hankali sosai kan karatunki,Kinga lokacin ma da zan dawo gaba d'aya kin kammala duk karatun nak ko"?
Gyad'a kai nai ina shashshek'a, wani tausayi ne ya lullub'eshi besan meyasa yakejin wani bak'on yanayi tare dashi ba kwana biyu tausayin ta keji maimakon da da yake bala'in jin haushinta, jin kukan ya tsananta yasa ya kamo fuskata daf da tashi "ki fad'amin meye matsalar in dai akwai wata damuwa ki sanar dani ,ni wannan kukan ne banso ki daina plss" unexpected naji harshensa kan fuskata yana lashe hawayen dake fita a idona, limshe idon nai da sauri inajin gabana na wani fad'uwa ,hannuna na damk'e sosai cikin nasa yake lasan fuskan nawa wanda lokaci guda hawayen ya tsaya sai fad'uwar gaba , jawoni yai jikinsa sosai ya Sani cikin k'irjinsa ina shanshanar k'amshin sa, wata nutsuwa naji tana saukar min don wannan shine karon farko a rayuwata dana tsinci kaina kwance jikin namiji haka,pitting bayana yake alaman rarrashi yana fad'amin magana me sanyi "kiyi shiru ki fad'amin meye matsalan meke saki kuka haka ki sanar dani kinji"
Tsintar kaina nai da fad'in "kayimin alk'awarin zaka rik'e amanar aurena,zaka rink'a tunani a kowace rana,sannan zaka kauda idonka daga kowace mace". Duka cikin miryan kuka da shagwab'a nake wannan maganar,
Mamakin magana ta yake yanajin salon danai maganar har cikin k'wak'walwarsa, cikin kunnena ya zura bakinsa yana cewa " I'm promise promise. . . . .
Dai dai lokacin motar ta tsaya da sauri na tashi a jikinsa ina gyara rigata mirmishi yai yana kallona sannan ya bud'e mirfin muka fita.
Bamu dad'e a airport d'inba aka fara kiran fasinjoji nan naji gabana ya k'ara fad'uwa yana lura dani don haka ya gyad'a min kai alamar k'arfafa gwiwa, sallama ya farayi da kowa ya tsugunna gaban Abba yana mai sallama ya shafa kansa yana samai albarka, haka ma Aunty murja tai mai sannan ya rik'o hannuna Aunty sulaim da Sweety yai musu sallama ya rik'o su salis ma ya rungumesu jikinsa,a sannan ya k'araso gabana ya rik'e dukkan hannuwana yana kallon cikin idona wanda suka k'ara cika da hawaye duk yanda naso maidasu sunk'i tsayawa rungumoni yai jikinsa ya matseni sosai yana pitting bayana muna a haka tsawon lokaci muka k'arajin kiran da akewa fasinjoji a hankali ya zameni a jikinsa yana kissing d'ina ya juya yana jan y'ar k'araman jakansa,ina tsaye ina binsa da kallo naji an rik'o hannuna a hankali na juya sweety ce ta gyad'a min kai tare da rik'o hannuna muka tafi gun motocinmu wanda tuni su Abban har sun wuce.







Taku ce
Layuza kabir Adam πŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣4⃣




Ban Sani ba ashe haka kewa Ke damun zuciyar d'an Adam, cikin kwana uku kacal da tafiyarsa amma duk kewanshi ta addabi rayuwata ko ina na gidan ji nake yamin fad'i musamman in lokacin cin abincinsa yai wanda daman nan ne muke duk wata hurd'a me tsayi wai ashe zama kawai waje d'aya koba jituwa a tsakani yana sanya kewa in an rabu? Tabbas ban san da hakan ba sai yanzu, nidai nasan ba wani abu me girma bane tsakanina da shi wata rana ma saimu kwana mu yini magana sau biyar bata shiga tsakaninmu ba banda cikin kwanakin yafiyarsa da suka gabato, amma duk da haka duk inda wani abu ke had'amu in na zauna gun banjin dad'in raina,ko d'akinsa in na shiga sai Inji k'walla ta taru a idona, uwa uba da zan tafi school na saba ya kaini ya d'aukoni koda wata kalma bazata shiga tsakaninmu ba amma zamana kawai kusa dashi muna tafiya a haka ma dad'i kemin, gashi yau din Abba yace min in fara anfani da motata zuwa school d'in tunda daman hannuna ya fad'a,


Fargaba da tunani suka dameni amma haka na daure na naita addu'oi kafin shigata motar har na shiga na tada inata addu'oin neman tsari daga sharrin k'arfe, tafiya nake a nutse cikin yanayi na y'an koyo har Allah ya sadani da school d'in, da Hafsah Aminiya na had'u tana ganina nai parking ta k'araso tana dariya tare da rik'e baki "ah lalle Har hannu ya fad'a kenan masha Allah, Allah ya tsare dukkan sharri"
Fitowa nai bayan na rufe motan muka jera ina bata labarin fargabar danakeji harna k'araso, dariya take tana fad'in 'aima kinyi k'ok'ari Allah ya tsare Sharrin k'arfe"
"Ameen Ameen tawan"
Muna hira a haka muka k'arasa ga hall d'in bamu.

Koda aka tashi duk way'anda suke y'an hanyarmu tare muka tafi dasu nace Duk su shiga in rage musu hanya,ai kuwa nan sukaita godiya kunsan d'an makaranta komai girmansa yana son rage hanya πŸ˜ƒ


****
Duka sweety ta tarkato ta dawo part d'ina da zama komai tare muke koda batada da lecture in zan tafi school zata tashi miyi break tare mu gyara ko ina sannan in tafi in barta, gashi tana matuk'ar k'ok'ari wajan kyautata mu'amala tsakaninmu duk da muna rayuwa ne Irin ta k'awaye amma hakan bai hana tana bani girmana.


******
Can k'asar india kuwa Uk ya shiga rubibi kasancewar yai jinkirin dawowa yasa duk abubuwa sunyi nisa bashi don haka yaita k'ok'arin daidaita komai har tsawon kwana biyar sannan ya sami nutsuwa, kuma sai a ranar ya sami sukunin saka layinsa nacan cikin wayanshi, da dare bayan yai sallar magriba ya d'auko wayan ya kira Abba,cikin farin ciki suka gaisa Abban yake tambayarsa meyasa baisa layinsa ba har wannan kwanakin yanata nemansa ,fad'a mai uzurinsa yai amma dukda hakan dai Abban yai mai fad'an yasan yanzu yanada mata kuma tana buk'atar kulawarsa kuma zataso taji kiranshi tun tuni don haka ya hanzarta ya kirata, amsawa yai dato sukai sallama, bin wayar yai da kallo yana nazarin maganganun Abban nashi, gaskiya bai kyautaba a yanda ya tafi yabar yarinyar tana cikin damuwa ya dace ya nemeta da wuri dukda yana yawon tunata koda yana busy lokaci lokaci tana fad'omai a rai amma baiyi yunk'urin nemanta ba,kodake ba laifinsa bane busy ya shige da yawa.

Duba lokaci yai yasan yanzu a Nigeria yamma ce bari ya bari sai can bayan yai sallar isha'i kamar k'arfe sha d'aya ma gomansu lokacin anyi magriba a Nigeria d'in don haka ya jawo laptop d'in sa yaci gaba da gudanar da sak'k'onin cikin ta.




*****
Bayan sallar magriba muna zaune parlor da sweety muna kallo dukda rabin hankali na baga kallon yake ba,wani Irin yanayi nakeji Mara dad'i cikin zuciyata, yau kwana biyar da tafiyarsa amma yaci ace ko yaya ya kirani amma shine harya manta dani kodake daman nasan wannan kulawan da yaita bani ba har zuci bane kawai don zaiyi nisa ne,nasani banda gurbi a zuciyar sa tun tuni, nima gajeran tunani ne yasa na fara wannan hasashshen yanzu gashi can ya koma inda ya saba ganin wayayyan mata taya ma zai tuna dani,naso inji labarinsa ko gun sweety ne amma bazan iya tambayarta ba tunda itama batamin maganar shi ba ko kad'an, inaga kotai tunanin ya kirani ne shiyasa batamin batun ba. . . .
Mik'o min wayata tai da taketa ringing a d'aki banjiba sai ita tajiyo shine taje ta d'auko min, bani tai tana d'an dariya tace "Aunty nah ga Broth na kira tabbatas wannan number d'insa ce "

Karb'an wayan nai wanda zuwa lokacin har wayan ta tsinke nabi number d'in da kallo a zahiri ta k'asar wajace kuma nasan shi kad'ai nake dashi a waje k'ara kira akai na d'aga jikina a mace tare kuma dajin wata Irin fad'uwar gaba,daga can naji muryanshi na fad'in "hello"
Saida ya sake mainaitawa sannan na tattaro nutsuwa da k'warin gwiwa nasawa kaina na masa da fad'in " Assalamu Alaika"

"Wslm " yace yana d'an mirmishi daga d'aya b'angaren
K'ara tausasa muryata nai nace "Barka da dare ka wuni lfy,ya aiki ya karatu"?

"Duka Alhamdulillah,ya kk ya school"

"Alhamdulillah"

" Kin jini shiru kwana biyar ko ina busy ne sosai sai yau na sami nutsuwa "
"Um hmm Allah ya taimaka ya bada abunda akaje Neman"

Har cikin ransa yaji dad'in addu'ar ya amsa da "amin na gode"

"Um hmmmm"

Shiru mukai na D'an lokaci sannan yace "Akwai wata matsala "?

" a'a ba komai "

"OK sai anjima ko "
"Allah ya tashemu lafiya"

Daga can ya katse kiran nabi wayan da kallo ina d'an mirmishi, maganar Sweety naji wanda nama manta da ita a gun "Tom Aunty na tunani ya k'are anji lafiyar miji ko"
Dariya nai kawai na kauda kai,zama tai gefena tana fad'in "ai ina kula dake kwana biyu yanda kike shiga tunani kuma nasan dan bai kiraki bane don haka ma ban miki maganar ba karki samin kuka"

"Hhhhhmmmm kin ma maidani wata kala daga magana sai kuka "
Kiran salla ne ya tashemu muka shiga d'aki donyin sallan,

Yau kam nayi baccin farin cikin wanda Har naso makara,haka na yini ranar ba wata damuwa Har mamakin kaina nake yanda zuciyata take k'ara fad'awa tarkon k'aunar wanda banko son kallonsa ada mutum na farko daya takura rayuwata kuma na tsani d'abi'unsa amma gashi k'addarar aure ta gifta tsakanin mu har gashi na fad'a k'aunarsa ikon Allah kenan wanda yafi gaban komai.




Bayan kwana biyu ya k'ara kirana da dare muka gaisa nan ma dai ba wata doguwar hira mukai ba yai min sallama,
Tun daga ranar ya zama duk kwana biyu zai kirani mu gaisa ya tambayeni koda wata matsala nace mai babu, duk yanda Allah ya jarrabeni da masifar k'aunar sa ban bada kaina don koshi ban nuna mai na matuk'ar damuwa da rashinsa balle wanda Ke kusa dani mutum bazai gane inda na nufa ba,kuma hakan bai sani na fasa addu'a da rok'on Allah alkairi cikin rayuwar auranmu ba.



A b'angaren UK kuwa fadlah ta sakoshi gaba da nata makaman yak'in kullum da salon da take zuwar mai, kasancewar har ita aka d'iba cikin masu k'ara yin course d'in kuma gidajan da aka kama musu dukka jere suke cikin wani katafaran estate akayi sa'a kuma gidan sa da nata suna jere da juna don haka ko yaushe tana biye dashi cikin school ko a gida, Fadlah nada girman da bai iya wulak'antata don tana cikin matan dayasa aransa inda zai aure a kusa ita zai aura,amma gashi yanzuma da akai mai auran k'addara ta kasa hak'ura dashi kullum fad'a mai take ita ta amince zata zauna dashi a matsayin matar sa ta biyu, ya nuna mata ta hak'ura da batun aure kawai suci gaba da zumunci da mutunci don shi yanzu inma yai mata alk'awarin aure yai k'arya damanshi tsarin rayuwar sa mace d'aya ce zai aura donshi d'an boko ne to amma tunda gashi anmai auran dole to ya k'arb'i k'addararsa bai jin zai zama cikin maza masu tara iyali wannan wanda Basu wayeba, ganin kullum batada aiki sai mai naci damai kuka yasa ya rarrasheta yace ta bari dai yaga yanda gaba zatai amma yanzu suyi abunda ya kaisu kawai randa suka dawo gida Nigeria sa nemi mafita,amma a ranshi yasan bawai auran ta zaiyi ba gaskiya.




Kwanaki suna ta tafiya har yai wata guda da tafiya kuma a sannan muka fara exam wanda ta d'auke mu wata guda itama duka hutun sati biyu muka samu don haka ma wannan hutun bai cikin wanda zanwa mijina ziyara sai hutun mu na gaba da zamuyi tsawon sati shida a gida shine Abba yace muna yi zan tafi India .



Mun koma school nan naci gaba da karatuna cikin kwanciyar hankali sai dai yanzu abunda ya fara damuna sai UK yai sati guda bai kirani a waya ba, kuma inma ya kira Sama Sama zamu gaisa ya kashe tun ina daurewa har abun ya fara damuna matuk'a . . .




Manège manège





Taku ce
y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑 🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​



0⃣3⃣5⃣


Sosai nasa abun a raina har hakan ta fara bayana kowa ya fara gane halin da nake ciki,yin duniya sweety tayi in fad'a mata matsala ta amma sai dai inyi mirmishi ince ba komai tasan zurfin cikina amma duk da haka ta alak'anta hakan ne ga rayuwar aurena,taso gane matsala ne tsakanina da mijina amma batai shishshiga ba taja bakinta tai tsit, ko a school haka abokan karatuna zasuyita tambayata ko banda lfy amma amsar dai d'aya ce ba komai, a haka wata rana Aunty ummy tace min zata kawomin ziyara kasancewar yanzu muna huld'a da ita sosai fiye da da don yanzu duk inda zaka ganmu da Hafsa Aminiya zaka ganmu da Aunty ummy kasancewar tanada matuk'ar k'ok'ari yasa tamu tazo d'aya don muna k'aruwa da juna matuk'a asalinta babanta balaraben chadi ne mamanta kuma fulanin nijar ne don haka kana kallonta zaka gane ba bahashiya bace amma zama cikin hausawa da auran miji bahaushe yasa ta rikid'e a magana da mu'mala tunda tace min zata kawomin ziyara naketa murna don zama da ita akwai k'aruwa sosai ko a harkar karatu ko a harkar yau da gobe, ran asabar ne zuwan nata don haka ina tashi nai ayyukana tsaf nai wanka na gama komai kasancewar sweety ranar bata nan ana bikin k'awarta tun sassafe ta fita, wajan sha d'aya na kira wayanta nace "Aunty ummy shiru baki zo ba"
Dariya tai tace ina shirya oga ne tare zamu fito ya saukeni amma nan da 30 minutes insha Allah ina gidanki"
Sallama nai mata ina cewa saita k'araso.

Tashi nai na shiga kitchen ina tunanin in fara rage aiki kafin tazo don haka na d'ora tuwo don nasan masoyinta a duniya tuwon shinkafa miyar d'anyan kub'ewa kuma ta fad'a min shi zan mata, inata aikina wajan awa guda har na gama tuwon na kwashe zan d'ora miya naji knocking da sauri na k'arasa ina fad'in " sai yanzu Maman boy gaskiya kin makara " na fad'a tare da bud'e k'ofan dariya tai bayan ta shigo tace bazaki ganeba Kedai Khadeejah, tsayawa nai kallonta ganinta ita kad'ai nace 'ina Farha da my boy na ganki Ke kad'ai"

Sai da ta zauna kan d'aya daga kujerun parlourn sannan tace "Abban su ya wuce dasu gun mamanshi wai tace kwana biyu basuje mata week end ba"

"Haba amma shine harda yarona za'a tafi inata murna yau yarona za'a kawo min ziyara"

"Ke bar wannan yaron naki rigimamme ai nan da 4 days zan yayeshi don bazanyi Ramadan dashi ba tunda daman ba shan nono yake sosai ba "

Wuce wa kitchen nai ina cewa"a'a yarona bai kai yaye ba sai dai in kuma k'ani aka samo mai"

Ruwa da lemo na kawo mata sannan na zauna muka gaisa sosai bayan ta d'an sha ruwan tace "Wane k'ani kuma ai nida wata haihuwa sai nan da shekara uku ko hud'u insha Allah kafin nan boy ya shiga school banda wata matsala amma ai konikan danai tsakanin Farha da boy ta b'aci don haka yanzu nake Neman tsari da konika"

Dariya nai kawai ina mamakin yanda take gudun haihuwa kusa kusa,
Hira muke sosai na saki jiki daga hiran karatu yanayin duniya har muka gangaro kan rayuwar aure, to an tab'o inda kemin k'aik'ayi duk da ban cikin mata masu rashin sirri amma wani abun dole kesa kai magana, tana lura da yanayin da nake kwana biyu wanda shine sanadin zuwan ta ma tunda tayi tayi a school taji damuwata nak'i,yanzu kuwa cikin hikima ta sako zancen yanda zan fad'i mata komai kafin ma ta tambaya, labarin mijinta ta fara bani "wato Khadeejah rayuwar aure sai hak'uri mazan yanzu sun girmi karatun me karatu, shiyasa zan iya kashe ko nawa ne kan namiji zan iya sadaukar da dukkan lokaci na ga namiji matuk'ar hakan zai zaunar dani daram cikin ransa, wato Khadeejah akwai wani lokaci da Abban boy ya tafi canada rimi rimi fa muka rabu tunda ya tafi kullum zamuyi waya muyi chart amma daga baya Duk saina ga canji ya fara bayyana inna kirashi sai ya gama hidimar sa zai nemeni kuma inya kira ba wani k'wakk'waran uzuri tsawon lokaci muke a haka na d'au fishi dashi na daina nemansa nima duk sanda ya kira ma sai naso zan d'aga wayan,ban Sani ba ashe dama na bashi tayin abunda yaso,wata yarinya ce take d'auke mai hankali a can tai kanai kanai cikin rayuwarsa janyewar da nai dashi nai fishi sai ta bashi damar sakewa da ita, sai daga baya nai tunani naiwa kaina fad'a nai na shiga nemansa ba dare ba rana na mak'ale masa koda yaushe naita kiransa a waya in yana aiki ya bani uzuri daga na kintaci ya tashi aiki zan ta kiransa saimu raba dare a waya koda yaushe bashi da lokacin kowa sai nawa duk sauran lokacin shi daba na aiki ba to nawa ne wani sa'in ma ko wanka zai yi sai ince yasamin video call zan rink'a tayashi wankan, a dole yarin yar nan ta fita cikin rayuwar sa don kota zo gunsa muna waya zaice ta tafi zai nemeta in da safe kuma aiki bazai bashi damar neman ta, a haka na shawo kan matsala ta cikin sauk'i,Kinga danaci gaba da d'aukan fishi shikenan na barwa wata banzar mijina tun suna soyayya ta iya baki da baki harta koma ta jiki da jiki shikenan ni an cuceni ko".

Jin jina kai nai ina nazarin kalaman Aunty ummy wanda kai tsaye zuciyata ta ban amsa da cewa lalle Irin halin da UK yake ciki kenan a India ba makawa nan da nan hawaye ya kuncewa idona, ni ban tab'a d'an d'ana zumarshi ba wata banza na can tana k'wak'ubemin miji, lafad'a ta Aunty ummy ta dafo tana fad'in "Khadeejah meya faru kuma naga kina kuka?"

Cikin sheshshek'an kuka nace "Maman boy kusan fa cikin wannan halin nake ciki yanzu Umar bai kirana a waya sai yai sama da sati bai neman ba kuma yana kira bama wata magana daga gaisuwa zai kashe,ina jin tsoron ko dai nima wata mace ki janye mai hankali "

Girgiza kai tayi "a'a Kar kiyi wannan zaton Khadeejah ko nima ban zargi mijina ba sai da na sami k'wakk'waran hujja daga abokin aikinsa, don haka karki fara zargin sa ba kyau kin Sani maybe shi ko aiki ne yasha kansa,ko wani dalili kuma mafa ni ina ganin kamar da sakacinki Khadeejah Ke kike bari ya kashe wayan maybe shiru kawai kikeyi bayan kun gaisa bakya fad'a mishi Irin halin da kike ciki na Ke wansa da buk'atar sa kk?"

D'an zaro ido nai nace" Aunty ummy yanzu sai nace mai ina buk'atar sa koma?"

Wani kallo naga tabini dashi na rashin fahimta sannan ta rik'o hannuna tana fad'in " Khadeejah kina son kicemin baki buk'atar mijinki baki muradin ganinshi kusa dake bakya marmarin sake had'a shin fid'a dashi akoda yaushe? "

Jim nai araina ina tunanin kodai ma in sanarwa Aunty ummy asalin yanda zaman mu da Uk yake ko in shaida mata ma bamu tab'a had'a makwanci ba maybe in samu mafita gareta,kai na sake girgizawa cikin raina nace bana cikin mata masu fad'in sirrin auransu wannan haramun ne matuk'a duk halin da zan shiga bazan tab'a fad'awa wani wannan sirrin ba,

Girgiza kafad'a tai cikin yanayin bani kwarin gwiwa tace "Khadeejah ki tashi tsaye ki damk'i zuciyar mijinki da gangar jikinsa karki bari kawaici da Kunya Susa miki waigi tsakaninki da farin cikin ki lalle ne in har kina son samun mijinki a tafin hannunki sai kin zama karuwa y'ar bariki me zafafan kalamai da zafafan aiki amma na soyayya sannan zaki cimma burinki, ina baki shawara Khadeejah yanda mijinki yai doguwar rayuwa cikin masu bud'ad'd'an ido to ganinki za'a rink'a yi a kulle biki san komai ba musamman keda kike *Y'AR* *ARABIC* da yawa mutane wani kallo sukewa macen da take y'ar Arabic me ilimin addini gani suke bata iya soyayya ba bata iya

Please Login or Register in order to submit comment