Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'and'ana kud'arki,waima in rasa wa zan aura sai y'ar Arabic, jibi wani tafkeken hijabi da kika saka waike ustaziyya, ni wlh an gama dani,kuma ina so ki karkad'e kunnuwanki da kyau ki jini, domin in kika kuskure koda da wasa kika watsani cikin friends d'ina wlh kin k'arawa kanki bala'i,Kinga dai yanda aka shirya bikin nasan wai ina son bikinba sai don in fita kunyar abokaina,don haka in akazo gaban jama'a kika nuna wa duniya Ke gidahuma ce wlh zaki shiga hannuna, don haka ki bud'e kunne kiji ki k'ara ji friends d'ina zasu zo daga k'asashe daban daban in kika nuna gaban su Ke y'ar Arabic ce ustaziyya hhhhmmmm".

Wani takaicine ya mamaye zuciyar Nahna amma saita rink'a kiran "innalillahi wa inna ilaihi ra'jiun" cikin ranta nan nutsuwa ta sauka a zuciyar ta,takalleshi karo na farko ta kauda kanta tana wani mirmishi na gefen baki tace "duka naji zancen ka,inka gama zan wuce ciki".

Baice mata komai ba ya zuge glass d'in sa yana bawa motar key,
Ganin haka tai wucewarta gida, tana shiga sweety tai musu sallama ta fita,Sam bata bari Aunty Amrah ta fahimci wani b'acin rai tare da itaba, bayan kusan 10 minutes itama ta wuce gida,tana danne duk b'acin ranta.




Taku ce
Y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​



0⃣2⃣4⃣



Saura kwana hud'u a fara biki y'an sakkwato suka fara zuwa mota biyu, washe garin zuwansu akaje akayi Jere(kafi),tunda suka dawo kowa tofa albarka cin bakin sa yake kan tsaruwar gidan Duk da gidan a cikin gidan su yake,kamar yanda mahaifinsa ya fad'a sai ya dawo daga India zamu tare a gidanmu, an k'ara tsara part d'in sosai gashi kayan sun amshi gun,duk zancen da suke ina jinsu araina ina addu'ar Allah yasa in riski farin ciki a cikin gidan ba wai had'uwar gidan ba.


Shirye shirye fa sun kankama don yau laraba gobe Alhamis za'ayi kamu da lecture, yau tun safe bamu zauna ba,k'awayena da y'an uwana duk muna tare gidan me k'unshi wanda muka fita tun bakwai na safe amma har ya zuwa yanzu k'arfe biyar ba'a gamawa mutum uku cikin mu ba wai duk da hakan ma masu kunshin su uku ne a gidan, duk y'an uwana wanda suke sa'annina da k'awayena ban bar kowa ba,sabida ina jin yanda ake k'orafi duk sanda biki ya taso cikin k'awaye ko y'an uwa in amarya ta x
Zab'e wasu ta bar wasu cikin duk hidimarta shi yasa na d'auki aniyar yin iya bakin k'ok'ari na wajan ganin ban b'atawa kowa ba,


Waya ta dake kan cinyata ta d'auki ringing na kalla fuskana d'auke da mirmishi na d'aga wayan" Hello Amarya kin dawo gida ne?"

"Um um sweety wlh har yanzu muna can".

" kai Ku nawa ne haka?"

"Hhhmmm mun kai mu ashirinfa ko ma munfi,amma da yawa an gama don kusan mutum goma sun koma gida saimu sha d'aya yanzu anan".

" ok Kinga muma yanzu muka dawo daka gun k'unshin Kinga duk y'an uwanmu na katsina sunzo, yanzu kan maganar kayan da za'a bada gift ne gobe gun lecture, yanzu masu aikin suka kirani sun gama komai shine nace ina za'a kai a ajiye miki tunda bakya gida".

Shiru nai can nace " Gaskiya gidanmu ba wajan ajiyar kaya Sweety don cike yake da mutane,kuma gidan yaya usman ma cike yake,ina ganin kawai ki ajiye a gidanku sweety goben sai ku wuce dasu gun".

"OK to ba damuwa Aunty nah,ya maganar gyaran kan goben fa da wuri zamuje kar mu shiga lokacin kamu".

" hhhmmm zamu b'ata fa in kina cemin Aunty kawai kicemin Nahna na yafimin dad'i".

" ni dai bazan ceba,ki dai shirya da wuri goben".

Mirmishi nai kawai na kashe wayan.



Bamu muka tafi gidaba sai bayan sallar magriba, a gajiye muke matuk'a ga yunwa damuka tara tun Karin safe sai lemo da biscuit kawai da mukasha, gidan namu babu masakar tsinke don jama'a ana tai mana sannu na sami gefen kujera na zauna ina fad'in "Wash Allah".

Gwaggo na dake zaune kan kujerar tace " sannu Khadijah tun safe sai yanzu dole Ku gaji ai".

D'an mirmishi nai nakai dubana fa Aunty Amrah data shigo parlourn d'auke da abinci tana ajiyewa mutanan d'akin a gaban su, nace "maman biyu bamu key d'in gidanki mu tafi yanzu don Duk a gajiye muke wlh".

D'auko min key d'in tayi tana rad'amin Abu a kunne ".

Girgiza kai na fara ina fad'in " wlh ba ruwa na nifa na fice daga parlourn da sauri ina dariya".

Babbar kula aka cika mana da abinci duka wanda zamu kwana dasu gidan yaya usman suka taso muka wuce.


Kusan raba dare mukai hira da y'an uwana da Aminiyata Hafsah wadda ta had'o kayanta ta dawo gidanmu har agama biki,


Da safe bayan munci abinci mun gyara gidan me gyaran jikin nan sarkin naci tazo wai tunda yau jiya ba'ayiba yau ba inda zanje sai anyi,badan naso ba na zauna aka fara min,
Wayata aka kawo min da take ta k'ara nasan sweety ce koda ban gani ba,ina d'agawa tace "Amarya gamu k'ofar gidan yaya usman ".

" Ku shigo mana".

Bayan sun gaggaisa da jama'a ta lek'o da kanta d'akin da ake min gyaran tana d'an mirmishi tace "y'ar Sudan a gyaramin ita da kyau yanda d'an uwana zai gigice inya ganta".

Hararanta nayi ina mirmishi nace " jirani 10 minutes za'a gama"


Bayan kusan minti a shirin na fito inata zuba k'amshin turaren da ake turaramin jiki wanda ya gama kama fata ta, duban y'an matan nayi ina fad'in " dawa dawa ne basuyi gyaran Kai ba?".

Da yawansu ko wacce da gyaran kanta tazo k'alilanne zasuyi

"To kunsan yanda za'ayi munyi magana da maman Amira me saloon ta cikin layinmu zan kawo mata costumers kuma kunga ni sweety taje ta biya kud'i a sabon gari tayi bucking, don haka Kar maman Amira taga rashin kyautawarmu taga mun gujeta don haka Ku kuje gunta tai muku in na dawo zan bata kud'in ita Hafsah sai muje da ita can karna barta nan cikinku bata san kowa ba zata takura koya kuka gani".

" eh hakan yayi saikun dawo ".

Bayan mun shiga shiga mota Sweety na driving sai Ramla cousin sister d'inta na zaune gefenta nida Hafsah muna zaune baya, ta cikin madubi ta kalleni tana mirmishi tace " Amarya gaskiya kina birgeni wlh yanda kike ji da family naki,komai baki son b'ata musu rai family dinku sunada zumunci matuk'a wlh".

Y'ar dariya nai ina fad'in " kinga kuwa tun jiya su Aziza suke tambayarki kina ina yanzu kuma da kika zo suna can gidan mu buku had'u ba sai zuwa jimawa ".

Dariya tai sosai tace " kai Aziza y'ar is ce wlh harna tuno bidirinmu a sakkwato in muna chart inna tuna mata ces din gidan lalle muyita dariya,inaji da Aziza Duk cikin y'an matan family d'inku nafi ji da ita don Kuna matuk'ar kama wlh dukda kamanninku duk d'aya ne amma kamarku da Aziza ta b'aci shiyasa nakeji da ita".

Hira mukaci gaba dayi har muka k'arasa cikin kasuwar sabon gari, gefen shagon saloon d'in mukai parking bayan ta rufe ko ina na motar muka shige shagon, mutum biyu ne ciki me shagon da yarinyar ta ba b'ata lokaci aka fara min yarinyar kuma ta fara yiwa Ramla.


Kasancewar su k'wararru a harkar gyaran kai yasa ba'a d'au wani lokaci ba aka kammala mana dukanmu muka taho gida.


K'arfe uku aka fara tafiya wajan kamu da lecture wanda za'ayi a sani Abacha an shirya gun sosai son lecturer d'inmu ce zatayi lecture d'in akan zaman aure yanda nake son malamar yasa muka saba da ita sosai babba ce a hukumar hisbah, ina jin lecture's d'inta a gidan radio don haka na k'udurta a raina ita zata min lecture d'in aure na.
Sosai nayi kyau cikin wata rantsattsiyar lifaya y'ar asalin na nad'ata ta zauna das a jikina fuskata d'auke da k'ayatacciyar kwalliya ta amare,kasancewar malama zarah bata son b'ata lokaci a duk lamuranta yasa ta gargad'emu da kada mu b'ata lokaci gun zuwa ai kuwa k'arfe hud'u hole d'in ya cika damk'am da jama'a, hud'u da y'an mintuna ta iso wajan ita da malama khadijah me tafsiri,
Kamu aka fara yi, wanda yake bisa ala'da dangina suka min kamu da turare me k'amshi daga nan fa Mlm Zarah ta fara suburbud'a lecture akan abunda ya taramu a gun, Allah yaiwa Mlm Zarah kaifin harshe da iya jan ra'ayin wanda takewa magana don ya maida hankali ya saurareta da kyau hakan yasa dukkan hole d'in baka jin maganar kowa sai girgiza kai kawai da akeyi (wa'azi ya fara ratsa mata,😜)

Tofa zance fa Mlm Zarah take saki kasancewar Duk hole d'in ba namiji duk mata ne yasa ta k'ara k'aimi wajan sanar da mata sirrikan rik'e miji gam a tafin hannu, wani abin ma inta fad'a kunya saita rufeni Allah yasa naja lifaya ta na rufe fuskata, tofa nan ta fara kwararo batu kan azabar da Allah ya tanadarwa matan da suke muzguna ran mazajensu,zo kuga jikin mata yayi qlau Duk jiki ya mutu, tana fad'in girman aure da matsayinsa cikin musulunci da yanda ya dace mace ta girmama mijinta, ban k'ara karaya ba saida naji ta waiwayo kan batun biyayya kan macen data auri mijin da bata so, dole ne ayiwa miji biyayya koda kuwa ba'a sonshi, haba Duk sai jikina ya k'ara mutuwa,
Lecture na awa d'aya da rabi tayi tai dagargaza sannan Mlm Khadijah me tafsiri ta tashi ita kuma,ta fara bada wasu sirrika da kissosi nan fa tafi da kabbara suka b'arke a gun, har Irin tafiyar daya dace mace tayi a gaban mijinta saida ta nuna haba wa nanfa na k'ara tsumuwa inaji araina anya duk zan iya wannan abubuwan da suke fad'i kuwa.
Minti talatin Mlm Khadijah me tafsiri tayi, sukai sallama tare da addu'a suka rufe taro, kayan rabo kuwa daman kowa an bashi nashi tun mutum zai shigo ake dank'a mai jakarsa a hannunsa ya shigo hole d'in da ita maganin mutum yace bai samu ba.

Su kuwa malaman gift na alfarma aka shirya musu sosai farantai manya aka shishshirya musu kayan snacks dasu naman kaji aciki lemo da ruwa ma katan biyu biyu aka sa musu tare dasa musu kud'i dubun ashirin matsayin su zuba mai a mota wanda Ummu sulaim ce yayar sweety ta basu kud'in aka rakasu har mota anata musu godiya tare da amsar number wayoyinsu kowa na cewa zata gayyacesu lecture.



Haka ma tunda muka dawo gida labarin wannan lecture ake musamman y'an matan da iya shege zasu tuno wani abun su kwashe da dariya suna fad'in " Nahna da fatan dai lecture d'in nan ta shiga kanki kije ki girgiza Umar".

Mirmishi kawai nake ban tankawa ko waccen suba na wuce toilet na gasa jikina da ruwa me zafi sannan na d'auro alwala nazo nai sallar magriba na maida isha'i don har an fara kiraye kirayen sallar ishan, yau ban tayasu hiran da suke ba don a gajiye sosai nake don haka gado na haye na lumshe ido bacci nasan d'aukata,amma kafin minti biyu wayata ta fara ringing kamar bazan bud'e idon ba haka na daure na bud'e ina kallon kan wayar bak'uwar number ce banyi tunanin komai ba na danna tare da sata a kunne na sanyin muryata ya had'u da baccin da nakeji ya k'arasa muryar yin sanyi matuk'a, sallama nayi tare da saurarawa don jin waye, shuru naji anyi na y'an dak'ik'u sannan naji anyi magana cikin gadara da isa " ki fito k'ofar gida ina jiranki kuma karki b'ata min lokaci".

UK ne na fad'a cikin raina don har abada muryarsa bazata tab'a b'acemin ba to me zan masa me ya kawo shi guna yanzu kuma?

Banda amsar bawa kaina don haka na mik'e jiki ba k'arfi nasa zumbulelen hijabi kan kayan baccin dake jikina,tambaya ta suka farayi ina zani ban kalli ko waccen su ba nace " ina zuwa kirana ake a waje yanzu zan dawo ". Nasa kai nai waje . . .




Taku ce
y'ar mutan Ja'oji πŸ™‹β€β™€

🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *Y'AN ARABIC* 🌸


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​


ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YAKE DAMUN MU ALLAH KA SHIGA CIKIN LAMARINMUπŸ‘



0⃣2⃣6⃣



Jin Hannun Hafsah a kafad'ata yasa na juya ina dubanta,mirmishi tai min tana fad'in "Angon yazo ko? Kinga ya dace mu wuce yanzu gashi har 8 ta wuce ".

Jin abinda Hafsah tace yasa me kwalliyar yin dariya tana fad'in " Amarya Bari mu kwarara miki turare dukda naji sirrin humrah tare dake gaskiya daga ji me gyaran jikinki tayi amfani da zafafan turaruka wajen gyara ki".

Hafsah ce ta tanka mata ni kuwa ban iya cewa komai ba har zuwa sanda ta d'auko kwalbar turare ta fara min feshi kamar ance ta k'arar dashi a jikina, net ta d'auko me taken one million Stone shima ta feshi shi da turaren sannan ta yafa min akaina wanda hakan ya bawa fuskata damar d'an sakayawa shima net d'in babbane sosai ya zuba ta baya,ta gaba kuma fuskata da k'irjina kawai ya rufe,

A hankali nake takawa kasancewar takalmin yamin tsini da yawa,gefena Hafsah d'aya gefen me kwalliyar ce ta rik'emin hannuna,tun kafin mu k'aroso bakin motar abokinsa dake driving ya dannan pin nan take mirfin motar ya bud'e, fitowa Angon yayi cike da fara'a d'auke da fuskanshi hannayensa biyu yasa ya ruk'o hannayena yana lek'a fuskana ya d'ago yana mirmishi me kwalliyar tace " Angon kasha k'amshi ga amaryarka nan nai Mata bridal makeup don k'ara fito maka da ita".

Alamar jinjina yai mata tare dasa hannunsa a aljihu ya ciro kud'i yana mik'a mata yace "ga tukwicinka nan don wannan kwalliyar ta cancanci tukwici bayan an biya kud'in ta ".

Dariya tai tana mai godiya ta juya ta koma, shi kuma yana rik'e da hannayena ya sakani cikin motar, Hafsah gaba ta zauna bayan ya rufe motar Hafsah ta juyo a hankali tana fad'in " Ango barka da dare ya taro"?.

Cikin d'an sakin fuska ya amsa mata,kafin ta kuma magana Abokin Angon yace cikin tsokana "wato Sabida ni ba ango bane shine baza'a gaisheni ba ko k'awar Amarya".

D'an mirmishi tayi tana fad'in" Ah Afuwan ba haka bane kaima zamu gaisa mana,ya taro ya fama da jama'a".

Nan ya amsa cikin tsokana ya juyo gareni yana fad'in " Amarya ansha k'amshi ya taro".

Kaina a k'asa gabana nata fad'uwa, ina k'ok'arin amsa mai Yai caraf ya amshe " Kai dalla rik'e gaisuwarka bama buk'ata, wayon kaji daddad'ar muryar mata ta ne to na amsa Mata".

Dariya Abdushshakur yai yana tada motar ya cilla ta kan titi cikin gwanancewa,

K'amshin turarena daya cika motar taf ya shak'a tare da lumshe ido kasancewar sa me matuk'ar son k'amshi, yana bud'e ido suka had'a ido da Abdushshakur ta madubi ya kashe mai ido yana fad'in yadai my friend ko har ka. . . ." da sauri ya rufe baki yana dariya,

Hararansa yai yana cewa "wlh ka lalace dasa iso friend ban sanka da haka ba fa".

K'ara matsowa kusa dani yai sosai jikinmu na gugar juna yake yima Abdushshakur gwalo tare da fad'in ka daina kallon mu fa Malam". Bakinsa yasa dai dai kunnena yana magana cikin rad'a" Ke karfa kiyi wani tunani cikin ranki game ne kawai zamu buga kuma wlh kika bari aka miki game over zamu had'u,k'ara kiyi iya yinki ki fiddani kunya kinji na fad'a miki ".

"Hhhhmmmm daman nasan za'a rina ni nasan ba saduda yayi ba kafiya kuma irinta UK amma ba komai Allah yana tare dani ai".

Music me dad'i Abdushshakur ya kunna cikin motar tare da k'aro Sanyin A.C nan motar ta wani shika da nishad'i,tunda muka shiga banyi k'ok'arin d'ago fuskata ba yanda take a lullub'e haka na saddata k'asa har muka isa MEENA EVENT CENTER nan motar mu tai parking a compound d'in gun duk sauran abokansa suna waje don jiran isowarmu, motar sweety ma tana wajan tana ganin isowaemu ta shiga ciki domin fito da sauran y'an matan da zasu shigar da Amarya da ango,
Duka y'an matan anko ne a jikin su yayin da mazan suke da shiga mabanbanciya, muna zaune cikin mota sweety ta shirya gun ko wace mace da namiji kusa da ita,yayin da gaba aka jera plower's baby's guda shida,
Ana mana izinin fitowa ya danna pin Motar ta bud'e shi ya fara fita sannan ya kamo hannu na ya fito dani muka tako a nutse hannuwanmu suna sak'e cikin na juna, muka shiga tsakiya gabanmu y'an yara bayanmu emmata da samari muna k'arasawa kusa da hall d'in aka saki kid'an police Band cikin taushi dasa jiki ya motsa, nan fa y'an yaran suka fara takawa cikin rausaya Kai haka ma emmatan da samarin , muna shiga ciki fa waje ya rud'e da ihun zuwan amarya da ango, a tsakiyan fili muka fara tsayawa nan aka shiga mana b'arin kud'i waje ya rude da rawa da lik'i, min dad'e tsaye m.c ya buk'aci kowa ya koma ya zauna a mazauninsa abar Amarya da Ango kad'ai a tsakiyan filin,
Nan kowa ya koma mazauninsa muka rage mu kad'ai tsakiyan filin ai kuwa ziciyata taci gaba da bugawa da sauri sauri ganin yanda ya k'ara matsowa kusa dani sosai, m.c ne ya buk'aci Ango daya bud'e fuskar amarya,ai kuwa cikin wani salo yasa hannuwansa biyu ya d'age net d'in dake rufe da fuskata k'asa sosai na k'ara yi da kaina ya d'ago da fuskana fuskanshi d'auke da mirmishi ahankali na lumshe idanuwa,nan wani annuri da asirtaccen kyau ya k'ara bayyana tare dani, yarrrrr yaji a jikinsa yana tunanin anya wannan y'ar Arabic ce kuwa,sosai ya zuba min ido don tabbatarwa a zahiri dai yana hango kamannina a fuskana amma wannan tsananin kyanfa daman haka wannan yarinyar take da kyau kodai makeup d'in nan ce tasa tai wannan tsananin kyan. . .

Ihu da tafin daya cika wajan ne ya dawo dashi tunanin daya shiga ai kuwa yaji wata bala'in kunya ta kamashi amma duniyanci Irin nasa da nuna shi wayayyene yasa kawai ya bud'e babbar rigarsa ya sakani a ciki tare da hugging d'ina yana dariya, nan duk friends d'insa na gida Dana k'etare sukayo kanmu da sabon lik'i suna b'arin manyan kud'i don nuna kara ga abokin nasu, ganin yanda mazan suka kewaye mu naji wani sabon fargaba da ta k'ara lullub'eni ai kuwa ban san sanda na kifa kaina bisa k'irjinsa ba tare da kewaye hannuwana jikinsa,wani k'ara rungumeni yai yana shafa bayana tare da kashe wa abokansa ido cikin shak'iyanci ai kuwa waje ya k'ara rud'ewa da ihu m.c ya samu abinyi fad'a yake yana k'ara fad'a"gaskiya wad'annan ma'aurata sun dace da juna Allah ya kawo zuri'a ta gari Allah yasa wata Tara masu zuwa muzo shagalin suna". Masu video fa hotuna suka shiga aikinsu na d'auke d'auke.

Mun d'au tsawon lokaci sannan m.c ya bamu damar zuwa mu zauna nan ya ruk'o hannu na muka tafi gun zamanmu muka zauna a high table,anan na k'are mai kallo shima kayansa kalan nawa ne light blue shadda d'inkin babbar riga da y'ar ciki babbar rigar irinta samarin Zamani y'ar k'arama dai dai jikinsa, idonsa sanye da farin glass kamar yanda ala'adarsa take,sai wata hula zanna me tsadar gaske da akewa lak'abi da minister kalan kayan nashi, hannunsa sanye da agogon vansar chairman world, sai k'afarsa sanye da bak'in takalmi south, duk a cikin abunda bai kai minti d'aya ba nai mai wannan kallon.

Nan akaci gaba da gudanar da event d'in cikin aji da nishad'i,zuwa d'an lokaci aka fara raba abinci ganin duk hankalin jama'a ya bar Kansu yasa ya sunkoyo sosai yana min magana cikin kune "Hhhhmmmm yarinya taga faffad'an k'irji shine harda wani lafewa a ciki to k'walelanki wannan k'irjin na matar zab'in raina ce ba matar tushe ba ".

Ganin masu Neman abinyi sun fara d'aukanmu a hoto yasa ya janye jikinsa yana wani mirmishi, Wanda nima mirmishin ne d'auke a fuskata wanda ban san name ne ba.

Sai misalin k'arfe sha d'aya aka tashi, yanzuma motar Abdushshakur muka hau Hafsah a gaba kamar yanda muka zo,
Bayan sun ajiye mu k'ofar gida ina shirin fita a motar ya rik'o hannuna yana magana k'asa k'asa " yau kin fidda kanki kunya sai kuma Sunday shima kiyi k'ok'ari kinji ko".

Ganin Abdushshakur na kallonmu yasa na gyd'a mai cike da gajiya wanda zakai tunanin shagwab'a ce.


Koda na shiga cikin gida tsokana ta akai tayi wai mun kasa hak'ura zuwa jibi gaban jama'a muke rungume juna, mirmishi kawai nakeyi ba tare dana tankawa kowa ba.

Washe gari asabar akai culture day tun k'arfe biyu ake gudanar da wasannin gargajiya da al'adu a filin wasa na Ahmad Musa sannan zuwa k'arfe hud'u aka wuce lunch sai bayan sallar magriba aka dawo.

Yau lahadi kuma akeyin Mothers day yau kam mu ba fita zamuyi ba a gida muke yinin mu inda muka yini masu kid'an k'warya suna cashewa, tunda naga anyi sallar la'asar fa jikina ya fara mutuwa naji zuciyata ta narke duk y'ar walwalar dake tare dani ta kau na koma jugum,

Ina jin kiran sweety a waya kuwa tana fad'awa Aziza ta fad'a a cikin gida ana sallar magriba fa za'azo d'aukan amarya nan jikina ya k'ara sanyi hawaye suka fara bin kuncina duk k'awayena ma sai jikin su ya mutu da sauran y'an matan, kayan takaici da rawar kai Irin na abokan UK wai tun kafin akira magriba suka fara zuwa d'aukan amarya ance sunzo da wuri wai sai ca sukai eh duk nuk'u nuk'u da fad'an da za'a yiwa amarya ayi mata kafin suyi salla su fito don

Please Login or Register in order to submit comment