Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rago muka rabashi gida uku muka shigar da kaso d'aya gida, sannan kaso d'aya muka rarraba kyauta zuwa gidan abokan yaya da dangin Aunty Hafsa, kaso d'aya mukai sadaka ga marasa k'arfi kamar yanda addini ya tanadar.





Duk yanda sweety take son inje gidansu nak'i, tsakanina da ita sai waya wayarma wani sa'in kashewa nake don karta dameni, in tazo gidanmu kuma zai amshe da fara'a kamar da, wani lokacin kuma in tace zata zo sai ince bana gidan duk don dai janyewa daga gareta.




Bayan sati d'aya da sallah su yaya suka dawo gida Nigeria, mukai murna kamar me da dawowarsa,kamar yanda shima yai farin ciki da ganinmu cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali.


kwana uku da dawowar yaya ba tare daya huta gajiya ba muka shirya muka d'au hanyar garinmu sakkoto sabida yawon kiran da suke mai da masu cewa zasu zo mai sannu da zuwa, ganin zai wahalar da yan uwansa ciki harda iyayensa mata yasa yaga k'ara shi yaje musu,don yasan zumunci irin na family d'insu kowa k'ok'ari zaiyi yaga yazo, don haka k'ara shi yaje su ganshi.


Mota guda aka d'aukar mana daga tasha sabida yaya bazai iya dogon tuk'i ba sabida akwai gajiya tare dashi, ta d'ebemu da kayanmu da tarin tsarabar da yaya yaiwa dangi, don saida ma yaje kasuwar haji camp ya k'aro kaya da tarin yawa don tsarabar saudiya bazata ishi arabawa danginmu ba don yawonsu.




Mun isa sakkoto yamma lis cike da gajiyan mota, y'an uwa da abokan arzik'i aka taremu cikin farin ciki da murnar ganinmu, bayan mun gama gaggaisawa da kowa muka nufi b'angaran umma na inda nanne masaukinmu da Aunty Hafsa shi kuma yaya ya nufi b'angaran samarin gidan don yai wanka ya huta, muma wankan mukai sannan mukai sallah aka kawo mana abinci da fura mukayi k'at.


Bayan sallar isha'i yaya ya shigo parlour ya samemu d'an zama yai cike da gajiya yana cewa "Umma zuwa zanyi in kwanta don jikina ba k'wari wlh".

Cikin nuna kulawa ummana tace " Ayya sannu Haruna ai kayi k'ok'ari daga dawowa ka d'auko hanya haka, Mu munata shirin zuwa maka barka".


" ai umma in nace zan barku Ku taho wahalar zatai yawa,amma yanzu da nazo duk saimu gaisa da kowa, in mukai sati guda sai mu koma kinga hakan yafi ai".


"Haka ne kam sannu kaji, tashi kaje ka kwanta ka huta, Allah ya tashemu lafiya".

Mik'ewa yai yana mana sallama ya fita zuwa sashin mahaifiyarshi umma Babba itama yai mata sallama sannan ya wuce shashinsu.




Washe gari da safe bayan mun karya kumallo munyi wanka . yaya ya fito da tsarabarsu ya warewa iyayenmu mata nasu sannan y'an uwanshi maza da mata sannan ya ware na sauran family duk Wanda yazo sai abashi abinda ya samu.


Ranar gidan yini akai bak'i na zuwa yiwa yaya sannu da zuwa har dare.


Tsawon kwanakin da mukai babu inda mukaje ,sai mu da ake zuwarwa, haka har muka cinye sati guda mukayo kano.






Taku ce
Y'ar mutan Ja'ojiπŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com






0⃣1⃣1⃣





Tun bayan dawowar yaya Haroon daga saudiya sai alak'arsu ta k'ara k'arfi da Alh.Usman domin Alh, ya bud'awa yaya sosai a harkar kasuwancinsu, a da kaya yaya ke ansa agunsa ya ringa rabawa ma'aikatan wajan aikinsu, in anyi salary su bada,Yanzu kam abin yafi gaban nan domin yanzu ya bashi damar sa han nunshi sosai harkarn kasuwancinsa, duk wasu kaya in sun shigo mai sai ya bawa yaya jagorancin rarrabasu zuwa store store, don haka ya zama yaya shima yanzu baya samun zama, daya tashi gurun aiki zai shiga sabgogin kasuwancinsa, don haka yanzu sai bayan sallar isha yake shigowa, wata rana ma sai wajan goma, sosai muka k'ara samun ci gaba aharkar rayuwa, har mota yaya ya siya sabuwa ya aje mana tsohuwar tashi a gida tare da driver duk inda zamu ya kaimu.



Ban garan karatu na kullum k'arewa yake don shirye shiryen final exam muke nan da sati biyu.

A b'angaran Sweety kuwa duk yanda nake k'ok'ari wajan yakice ta ita tak'i barin hakan, kullum tana gidanmu ni kuwa na daina zuwa nasu, tayi Iya k'orafinta harta gaji ta bari.


************
_BAYAN_ _WATA_ _GUDA_

Yaya zaune tare da Alh, usman a katafaran parlourn sa na ganawa da bak'i, gyaran murya yai ya fara magana,

" Haroon dalilin nemanka na yau ya banbanta Dana kullum, domin yau magana ce me tarin mahimmanci zamuyi da Kai, wadda bata shafi kasuwanci ba, ina fatan samun nasara".

Sosai yaya haroon ya maida dukkan hankalinsa ga Alh, Usman don jin abinda yake fad'i.

" haroon kan maganar k'anwarka Khadeejah ne, hak'ik'a tun ranar dana fara ganin khadeejah na tabbatar da ingancinta nasan lalle yarinya ce daban da y'an matan wannan zamanin, nutsuwarta, kamun kanta tare da tarbiyarta duka abin birgewane ga kowane mutum dayasan kansa, tun a lokacin na fara wani tunanin game da ita, na fara sha'awar kasancewarta surukata, haroon don Allah alfarma nake nema a gareka ka taimaka ka bani Khadeejah na had'ata aure da Daddy".

Dammmmm yaya yaji gabansa ya fad'i, don bai san mema zaicewa Alh, usman ba, don haka yai shiru kamar me tunani.

Muryan Alh,usman ce ta ratsa kunnuwansa yana fad'in " Haroon taimako na zakayi alfarma nake nema gareka nasan khadeejah tafi k'arfin auran miji irin Daddy don khadeejah matar kamilallun maza ce amma ka taimka kayi wani abu akai".

Cikin sark'ewar murya Yaya yace " To Alh, zanyi shawara da ita Nanan don a sani na dai nasan Nahna bata kula ko wane saurayi don haka bata soyayya, to Amma wani abu guda akwai alk'awari dana d'aukarwa Mahaifina tun sanda ya bani kyautar Nahnah kan cewa bazan mata dole ba a cikin rayuwarta, don haka Alh,yanzu zanjewa khadeejah da maganar nan a matsayin shawara ba dole ba, zanji ta bakinta abinda tace zanzo maka dashi".

Shiru Alh, yayi zuwa can yaja ajiyar zuciya tare da fad'in " Shikenan Haroon ina sauraranka,Amma don Allah kayimin k'ok'ari kaji".

"Insha Allah zanyi k'ok'ari"
Jiki ba k'wari yaya yai mai sallama ya fito.

Tafiya yake a mota amma duka nutsuwarsa bata tare dashi tunani ne barkatai cikin ransa, yama rasa ta ina zai fara don a zahiri bai son abinda zaiwa Nahna dole a cikinsa, Tun had'uwarsa da Alh, usman baifi sau biyu ya tab'a ganin Daddy ba, amma ganin da yai mai ya tabbatar irin sangartattun y'ay'an masu kud'innan ne, hak'ik'a baya son abinda zaisa Nahna cikin matsala ko kad'an don amanar Mahaifinsa ce,
A haka ya k'arasa gida jiki ba k'wari ko kad'an.

Tun shiganshi gidan Aunty Hafsah ta lura da yanayinsa don haka suna shiga d'aki ta dafa kafad'ansa tana fad'in "Abban Ashraf meke faruwa na ganka haka"?

D'an mirmishi ya k'ak'alo yana Shafa gefan kumatunta yace " me kika gani Hafsa?"

" naga rashin nutsuwa da walwala a tare da kai ?"

"Karki damu zamuyi magana anjima yanzu had'amin ruwan wanka tukun?"

Cikin tsarguwa tace "Allah yasa naji alkairi wlh har gabana ya fara bugawa"

"Karki damu bari zuwa anjima d'in".



Ina k'ule kan gadona inata zuba karatu don exam d'inmu tayi nisa yanzu kullum ina kan karatu ko zaman parlour banayi Iya kacina cin abinci nake komawa d'aki, sallah kad'ai ce take shiga tsakanina da littafina, yau kam dake ina hutun sallah ko kad'an ban motsaba, ina jin shigowar yaya amma ban fita ba sai yaje sallar magriba ya dawo zanje masa sannu da zuwa.


Jin shigowarsa shida su Asharaf daga sallah yasa na fito parlourn,
" yaya sannu da zuwa ya aiki"?
"Yawwa sannu Nahnah ya gida ya karatu"?

"Alhmdll karatu yazo k'arshe ai yaya".

"Masha Allah , in angama kuma sai a koma degree ko sai kin huta"?

"A'a yaya k'ara in wuce kai tsaye don wannan tsyawa hutun shi kenan sai abu ya shiririce".

"To Allah ya taimaka Nahna autar Baffah".
Ya k'arashe da D'an mirmishi.

Dariya itama tayi kawai tana tuno Baffanta cikin ranta.

Bayan sunci abinci akai sallar isha nan kowa ya tashi don himmar sallah,

Koda Yaya ya dawo daga masallaci yau bai zauna hira ba a parlourn d'akinsa ya wuce kai tsaye inda Aunty Hafsah ta bishi, ganin ba kowa a parlourn yasa su Ashraf shigowa d'akin suna fad'in Aunty zamu kwanta,

"nace da wuri haka me yasa yau bazakuyi kallo ba "?

"Abba ya shiga d'akinsa momy ma ta kwanta"

"OK to bari a kashe kayan kallon"?

Fita tai taje ta kulle duka k'ofofin gidan ta kashe kayan kallo sannan tazo ta shirya su Asharf d'in suka kwanta kan gadonsu.

Tunda ta koma gadonta ta kwanta take tunani aranta, duk yanda akai yau akwai damuwa tare da Yaya ta lura duka d'an wasan da yakeyi k'arfin hali yake, ko dake jiki da jini k'ila baya jin dadi ne.

Watsar da tunanin tai ta shiga karatunta.



A d'aki kuwa Yaya yake shaidawa Aunty Hafsah duk yanda sukai da Abban sweety, itama shiru tai tana tunani zuwa can tace" Da farko dai ina son karka tunkari Nahna da wannan maganar har zuwa ta kammala exam's d'inta don yanzu babu buk'atar a kawomata rud'ani cikin zuciya, sannan shawara ta gaba inka samu Nahna kan batun nan ka bita da rarrashi, sabida inka bata umarni tabi kai tsaye zata ga rashin adalcinka gareta, shima Abban sweetyn ka bishi a sannu karka nuna mai kai tsaye had'in bai ranka domin zaiga rashin kyautarwa gareshi tunda shi yana iya iyinsa wajan ganin ya kyautata maka, sannan babban muhimmun abu shine muyita addu'a Muna neman alkairin Allah cikin lamarin".

Cike da gamsuwa da maganar Aunty Hafsah yaya ya gyad'a kai yace " Naji dad'in shawararrki Hafsah Allah ya shige mana gaba".

Amsawa tai da ameen zuciyarta cike da sak'e sak'e.


******************
Tsawon sati guda yaya bai Sanar da Nahna halin da ake ciki ba, ya bari sai ranar datai last exam d'inta zai zauna da ita.


Ranar Laraba itace ranar da zasu gama exam, duk sinyi shirye shiryen graduation d'insu,
Ranar suna fitowa a final paper d'insu kowa ka gani bakinsa bai rufuwa wasu na fad'in Alhamdullillah, wasu ko Allahu Akhbar kawai suke fad'i, sab'anin wasu da zakaga suna fitowa zasu hau ihu Mara dalili, Wanda (Y'AN ARABIC) suka sha banban da sauran.


Kai tsaye Open theater suka wuce inda zasu gabatar da 'Ψ¨Ψ±Ω†Ψ§Ω…ΩŠΨ¬' wato programs na larabci tare da masrihiyya, wajan ya cika yayi mak'il da alumna inda zakaga duka ( y'an Arabic) mata sanye da ankonso na Atamfa sai mazan sanye da shadda iri d'aya gwanin sha'awa da birgewa,

Nahna sanye da kayan sarakuna an mata ado da alkyabba da takalmi irin na sarakai, kasancewarta matar sarki cikin drama d'in, fadawane keta bin bayanta suna mata kirari irin yanda akewa sarakai, a hankali take takowa yayin da masu video da masu d'aukan pictures sukai Ca a kanta, cikin kunnanta taji muryan Ashraf da Khaleel suna fad'in
" Aunty Nahna Aunty Nahan"

D'ago idanuwanta tai ta dubi sashin da suke tare da sakar musu mirmishi,


Tana zuwa ta fara gabatar da kanta cikin harshe mad'aukaki (Arabic) bayan tai sallama ta mik'a gaisuwa ga prover's ga dikkan malamai tare da dukkan Wanda yake wajan,sannan kai tsaye ta shiga gabatar da shirin, inda hankalin dukkan Wanda yake wajan ya dawo kanta.


Yanda take sarrafa harshen larabci tamkar harshenta shine abinda ya burge kowa gashi sin d'in da aka d'orata a kai ya dace da ita,
Bayan gama drama d'in aka shiga muhawar tsakanin maza da mata inda mata ke kare mahimmancin ilimin y'a mace su kuma maza suke kare rashin muhummancinsa duka cikin harshen Larabci,

Sannan aka fara sako k'asidun da suka yiwa Kansu na rabuwa da juna, da Wanda sukaiwa prover's da malamansu.

Abufa yayi abu inda akaita d'aukan pictures ana video,

Basu tashiba sai bayan la'asar inda kowa ya kama hanyar gida da mutanansa,
Sweety taiwa Nahna hotuna kamar me tare da video don duk motsin datai saita d'auketa har abin ya fara bawa Nahna dariya.

Yau kam cike take da tarin farin ciki wanda fuskarta take bayyana hakan.

Bayan sallar isha'i suna zaune a parlour su Ashraf Aunty Hafsah sunata bawa yaya labarin abubuwan da akai a skl d'in su Nahna shikam ya biye musu yanata fad'in Masha Allah, madallah,
Zuwa can ya kira Nahna cikin murya me cike da kulawa yace " Nahna daman ina son muyi wata magana dake me mahimmanci don haka da safe kafin na wuce office zan ganki kinji. . . . . . . "








Taku ce
Y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation.@gmail.com



Wannan page d'in naki ne (Fauzidadi) na bakishi kyauta kiyi yanda kikaso dashi, sabida kulawarki ga wannan novel, na jinjina miki yanda bakya gajiya da adanaminshi.
πŸ‘πŸΎπŸ‘πŸΎπŸ‘πŸΎπŸ‘πŸΎπŸ‘πŸΎπŸ‘πŸΎπŸ‘πŸΎ




0⃣1⃣2⃣





Damm Nahna taji gabanta ya fad'i, dukda bata San me yaya zai fad'a mata ba amma tasan me muhummanci ne,ga yanayin data gani a fuskar sa, a hankali tace To yaya Allah ya kaimu safiyar, mik'ewa tai cikin sanyi tai musu saida safe ta shige d'akinta .

Haka ta kwanta cike da tunanin cikin ranta har bacci me nauyi ya d'auketa.



Bayan sallar asuba tana zaune kan sallaya tana karanta azkar har k'arfe shida ta shafa addu'a ta mik'e tana k'ok'arin ninke prayer mat d'in taji muryan yaya a k'ofar d'akin yana mata magana, da sauri ta aje tai waje, zaune ta sameshi kan kafet ya mik'e k'afansa yana jan casbaha, a hankali ta k'arasa gareshi ta zauna tare da gaisheshi ya amsa fuskanshi d'auke da fara'a ,

" Nahna ya gajiyan taro kuma "

" Alhamdulilah yaya "

" To masha Allah"

Shiru ne ya biyo baya na D'an lokaci daga bisani ya nisa yace
" Nahna kiban duka hankalinki nan, magana ce me mahimmanci matuk'a zamuyi dake "

Dammmm taji gabanta ya k'ara fad'uwa,

" Nahna nasan kinsan Alh Usman kinsan alak'ar dake tsakaninmu dasu, Nahna kin Sani cewa ina tare da shi ne sabida kasuwanci dake tsakaninmu Wanda zuwa yanzu zumunci ne me k,arfi Tsakaninmu."


Numfashi yaja yana k'ara gyara zamansa,

Zuwa lokacin duk Nahna ta matsu taji me zai fad'i,

" Nahna wato wata magana ce Alh Usman yazomin da ita me girma , yana son ya had'a zuri'a damu, yazomin da zancan yana son in kin amince yahad'aki aure da d'ansa, Amma Nahna ba dole za'a miki ba amincewarki nake buk'ata, don Nahna ko k'arshen alak'ata da Alh usman kenan in biki aminceba,wlh bazan aurar dake ga d'ansa ba,kije kiyi shawara Nahna in kinga bakya ra'ayi ki sanar dani kinji, abinda yasa ma nai miki maganar don naga baki kula kowa ne ma'a babu soyayyar wani a zuciyarki ko?"

Ya k'arashe maganar da kallonta.

Cikin kid'ima ta gyad'a kai tare da fad'in "eh yaya zanyi shawara ".

" To jeki ina sauraranki daga yau zuwa kwana biyu,amma fa karkiyi abinda zaki cutu kinji Nahna".


Tashi tai tana tafe tana had'a hanya ko gani batayi sosai don tsananin tashin hankalin daya ziyarceta, tana shiga d'akin ta fad'a kan gado tare da fad'in

"innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun, shin wace Masifa ce ke tunkaro rayuwarta,wane sabon tashin hankali ne wannan ,wai shin dama har yanzu UK bai fita cikin rayuwar taba , don tsananin masifa yanzu baya k'asarma amma har saida yabi k'wak'wk'wafin rayuwarta ya had'a da mahaifinsa da sunan yana son auranta kawai don ya cuzguna rayuwarta,wayyo Allah yanzu ina zatasa ranta ,kai wlh Sam babu abinda zatayi da UK matsayin mijin aure, baya cikin tsarin mazan da zata iya aura harta kai tai rayuwar aure dashi,".

Maganganu kawai taketayi cikin ranta tama rasa me zatai kawai saita fashe da matsanancin kuka Mara sauti.


Tsawon lokaci tana kuka me cin rai har bacci yai gaba da ita ,bacci Mara dad'i me cike da tunane tunane.


Bayan awa guda ta farka idonta yai mata nauyi sosai a hankali ta maidasu ta rufe bayan minti biyu ta k'ara bud'esu tana tunano abinda ya faru da ita ,sai taji gabanta ya fad'i rasss nan da nan idonta ya k'ara Kawo ruwa ,ta mik'e a hankali ta shige toilet tai wanka ta fito sanye da towel tana tafe tana Jan k'afa,k'arasowa tai gaban mirror ta shafa mai tare da d'auko riga doguwa tasa ba tare data tsaya yin wani kwalliyaba, don zuciyarta ba d'adi Sam, maimakon ta fita parlour don karyawa saita koma ta kwanta kan gadon tana dafe kanta dakemata tsananin ciwo.

Tunani take kala kala cikin ranta ta rasa ma ina zata tsaya ne . . .
Muryan Aunty Hafsah ta jiyo tana dafata
" Yadai Nahna tunanin me kike haka inata kiranki biki jiba,ko baki da lfy ne?"

Da k'yar ta tashi zaune tana mutsika ido tace " kaina kemin ciwo wlh Aunty, ban jinki ba sam"

"Ayya sannu tashi muje kici abinci kisha magani"

Badon taso ba ta fita, ba kowa parlour don Yaya ya fita office su Asharaf kuma suna skl, ta Shiga kitchen ta d'ebo abincin kad'an tare da ruwan shayi ta fito, cin abincin kawai take ba tare don tana jin dad'insa ba , Aunty Hafsa na gefe tana kula da duk motsinta.

Bayan ta gama Aunty ta mik'a mata magani tasha tana runtse ido, tace

"Aunty ya naga duk kinyi komai harda wanke wanke biki bari na fito ba "

" ba komai naga kina bacci ne yasa kawai nayi nasan akwai gajiya tare dake sosai , ga bashin baccin karatun exams da kika tarawa idonki".

Lumshe idonta tai kawai bata ce komai ba.

Cikin rashin jin dad'in ganin halin da take ciki Aunty tace " Nahna yayanki yamiki maganar d'an gidan Alh usman ko?"

Gyad'a kai kawai tai, Aunty taci gaba. " Nahna ki tsaida hankalinki kiyi shawara bawai dole za'a miki ba in kinga biki amince ba ki fad'i kawai kinji"

"To Aunty "

Daga haka tai shiru don bata son magana ko kad'an,
Ganin tai shiru yasa Aunty tace kije ki kwanta ki huta Nahna"


Mik'ewa tai ta shige d'aki ta fad'a kan gado zuciyarta ba dad'i .



Tsawon kwana biyun da yaya ya bata tayi tana sauraran taji ya kirata ya tambayeta meta yanke taji shiru , har kwana hud'u bai kirata ba.


Yau da dare tana kwance kan gado tanata sak'e sak'e aranta wai idan yaya ya kirata me zata ce, kullum dai addu'a take tana neman mafita gun Allah, shin wai dagaske UK sonta yake ko kuwa iskanci ne , ita dai tasan farkon ganinta dashi ya nuna mata samartaka daga baya kuma data nuna mai bata ra'ayi ya shiga gasa mata azaba da wulak'antata gaban mutane kuma yanzu yazo da wani zance kodai wulak'ancin da yai matane bai isheshiba zai aureta yaci gaba dayi mata, koma dai mene ne ai tana fad'awa Allah wani tunani ne ya fad'o mata arai, saita saki wani d'an mirmishi tana jinjina kai.




Kuyi hak'uri da wannan don AllahπŸ‘πŸ‘.






Taku ce
Y'ar mutan ja'ojiπŸ™‹β€β™€
🍑🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸 *YA'N* *ARABIC*🌸


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
​

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š



πŸ’» *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

πŸ“ .
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​​

β€‹πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation.@gmail.com




0⃣1⃣3⃣




Misalin k'arfe sha biyu na rana ina kitchen ina had'a abincin rana naji anata knocking k'ofa a hankali nace

" waye "

" Autar Baffa yayanki ne usman"

Tsalle na buga tare da bud'e k'ofan parlourn ina fad'in
" yaya Usman oyoyo"

Shigowa yai ciki yana dariya yace " wash na d'auko gajiya auta ina mutan gidan ko basa nan?"

" eh Aunty taje Unguwa yaya yana office Yara suna skl saini kad'ai, yaya ya Hanya ".

" Alhamdulillah Nahna kin ganni ba zato ko? Wlh Sakkoto na nufa mun sami Hutu, kuma sai muka biyo ta kano yiwa wani abokin aikinmu ta'aziya ,nace to bari in biyo mu gaisa".

" kai amma yaya naji dad'in zuwanka wlh, nima ina ganin cikin satin sama zanzo sakkoton".

"Um su Nahna graduate an girma sai aure kuma ko?"

Mirmishi kawai tai ta tashi ta shiga kitchen don kawo mai ruwa da lemo.


Bayan ta kawo mai ta zauna sunata hira yaya usman yace
" ki shirya kawai mu wuce tare "

Da sauri ta d'ago tare da fad'in "kai anya yaya zai bari kuwa?"

"Me zai hana ya barki tunda daman kina shirin zuwa"

"To ai kai yau zaka juya kuma ni sai nan da sati zan tafi kaga bai San da tafiyar tawa ba yau "

" OK bari in fad'a mai ma nazo"

Wayansa ya d'auka ya kira number d'in yaya Haroon bugu d'aya ya d'auka

"Hello Usman ya kake "?

" yaya lfy qlau ya gida ya iyali?"

"Duk kowa lafiya , ya wajan aikin naku?"

"Alhamdulilah, gani ma na shigo garin naku,nazo gidan sai Nahna kad'ai"

" ah da gaske usman?"

"Hhhmm Allah da gaske"

"OK ina Office amma zanzo gidan yanzu hafsa kuma tana Unguwa, amma ai ba yau zaka wuceba ko?"

"Eh to da dai naso wucewa yau d'in amma zan bari zuwa gobe."

"OK to ina hanyar dawowa."

"Tom sai kazo Allah ya kawoka lafiya."


Hira sukaci gaba dayi da Nahna yana bata labarin ya samu mata k'anwar friend d'insa a nan kano take don haka insha Allah da wuri za'ayi bai so a wuce 7 month.

Murna sosai Nahna tai tana tambayar sunanta yace " Amrah"

Nan yake k'ara bata labarin yana sa ran zai samu transfer zuwa Kano nan da 2 month don haka zai sai gida a Kano ya zauna kusa dasu.

Haba murna kamar me gun Nahna ta mik'a mai hannu suka kashe cik'e da k'aunar

Please Login or Register in order to submit comment