Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

malama," Aneesah ta dake tace "bbu abinda bana yi Hajiya, tun daga kan shara, wanke wanke, goge goge, girke girke, da duk aikin da kika sani Hajiya," Hajiyar ta tabe baki tace "yyi, duk wata dubu goma sha biyu nace xan dinga badawa kuma idan washing machine ya wanke ma babies dina kaya yau to gobe ita xata wanke masu, snn tun karfe bakwae xata xo aiki ta bar min gidana karfe shidda na yamma, ina fatan ku ba fulanin daji bne kun fahimce ni," Ammi tayi murmushi tace "mun fahimce ki Hajiya mun gode, amma karfe shiddan da kika ce Hajiya yyi dare don gidanmu da nisa sosai, ki rage kudin aikin in yaso sae ta dinga barin nn ko xuwa karfe biyar ne," hajiyar tayi masu wani kallo ta tabe baki tace "karfe biyar da rabi xata dinga barin nn period, idan hkn yyi maku to ta fara aiki daga dis vry moment, idan kuma bai maku ba ku ja tsumman rayuwarku ku fice min daga gida don ni bna kai wa wnn lkcn ina surutu da yan aiki talakawa irin ku," tana kaiwa nn ta juya ta shiga takunta cikin isa har ta hau balcony ta shige falo...
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: 8...... Sumy ta mike da mamaki tana kallon yayarta Meenah don ita tsakani da Allah tayi maganarta ba wae don su yi fada ba, pretty tace "sumy ke kika fara neman tsokan gskya meye xaki hadata da wata banxa can kuma ma 'yar aiki, wae ta fita kyau" Meenah tace "ki kyaleni da 'yar walakanci kawae na faffasa mata baki ynxun nn....." ganin abun nasu na son ya xama fada sosai don sumy har ta fara kkrin cakumo yayartata tana cewa "to ki fasa min bakin kiga idan ban cire maki hkora ba ynxun nn nima," yasa Hajiya ta shige tsakaninsu da sauri tana basu hkuri, "haba bbies dina meye abun fada a nn iyye, kema sumy baki kyauta ba don me xaki ce wata tsinanniya can ta fi yayarki kyau idan ba tsokana ba," ta juyo tana kallon meenar tace "manta da ita meenah xolayarki take kinji, kuma ku kwantar da hankalinki indae mayyar 'yar nn ce wllh watan nn na kai wa karshe xan sallameta, ita wacece da xata dinga gasar kyau da daughters dina, ku kyaleni da shegiyar kawae kuje kuyi shirin birthday din da xaku kar lkci ya wuce," a hka ta lallaba 'ya yan nata suka hkura suka haye sama pretty na cewa "Allah ma yasa ba yau bne karshen xuwa partynmu" sumy tayi dariya tace "kuma fa hka ne wllh," hajiya tayi jigum tana tunani bayan tafiyar 'ya yan nata, ita kanta kyan Aneesah mamaki yake bata wani lkcn, yarinya hka sae kace aljana don kyau, anya ba plan aka yi mata da yarinyar nn ba kmr yanda su pretty suka ce ba, amma ta kusa kawo karshen komai idan Allah ya yarda wnn watan ne watanta na karshe a gidan taje can ta samu wani gidan tayi masu aikin ita kam ta yafe duk da ta san yarinyar ta iya aiki sosai uwa uba ga iya girki da tsafta, ta tabe baki a xuciyarta tace na sa a kawo mani wata balagaggiyar mummuna hankalina a kwance na 'ya yana a kwance, ta sake kwado ma Aneesahn dake tsaye a kitchen ta gama dukka aikinta na ranar amma tana tsoran tunkarata tace xata wuce, ta fito da sauri har tana tuntube ta durkushe gabanta tace "gani Hajiya," Hajiyar ta tabe baki tana hararta kmr xata makureta don tsana tace "idan kin ga dama gobe ki taho da Asuba don xaki hada ma son dina da xae dawo daga holland goben girki lafiyayyu, xakiyi masa fried rice da plantain kadan, sae farfesun kayan ciki da kaxa, snn ki hada masa cream salad, sae kuma kiyi masa cous-cous da miyar kwae, snn finally ki hada masa ginger drink mai kyau, daughters dina kuma kiyi masu jollof din taliya da naman rago da dan farfesun fish don sun fi son shi, ina fatan dae yhu re nt daft duk kin fahimce ni," Aneesah tace "nafahimta Hajiya," Hajiyar tace "tashi ki bani waje to, idan kinga dama karki xo da wuri ki ga rashin mutunci," Aneesah ta mike a sanyaye tayi mata sae da safe ta bar gidan
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By khaleesah Haiydar 7.... Ammi ta girgixa kai a hankali tace "baxa ki iya ba Aneesah muje kawae," Aneesah ta xame hannunta a hankali daga rikon da Amminta tayi mata tace "xan iya Ammi, ki tafi gida kawae sae na dawo," bata jira abinda Ammi xata ce ba tayi saurin barin wajen ta bi kofar da Hajiyar ta bi ta shige cikin gidan tana karanto Addu'o'i cikin xuciyarta, ta ga kanta a wani makeken falon gske mai cike da kayan alatu da kayan more rayuwa " ya salam! Aljannar duniya knn," ta dinga bin falon da kallo a hankali gabanta na faduwa sae kace ba Nigeria ba, wnn wani irin aiki suke yi hka, gskya wasu kam sun more duniya, ta rasa inda xata bi don falon ba kowa sae karar Ac da wani ni'imantattcen kamshi dake tashi, ta kai minti kusan goma a tsaye tana naxarin komai na falon duk da wasu tana ganinsu falon baffanta, taji ana taka matakalan bene a hankali ana saukowa ta tsura ma stairs din ido tana jiran taga ko Hajiyar ce ke sauko wa, wata kakkyawar yarinya da baxa ta wuce ta ba ce ta sauko tana sanye da kayan bacci, yarinyar ta mitsike ido tana kallonta da mamaki, Aneesah ta kauda kanta, yarinyar cikin gadara tace "who re yhu," Aneesah tayi shiru bata ce mata komai ba sae wani irin kallo ma da take ma yarinya, yarinyar ta juya da sauri ta koma sama, sae ga ta ta dawo da momynta, Hajiyar tace "ohh House Maid dinmu ce pretty," Hajiya ta karaso kasa a walakance tace "bbyna xata xaga dake ko ina na gidan ta nuna maki duk aikin da xaki dinga yi, sae ki fara daga ynxu," ta kira prettyn tace "sauko bby ki nuna mata House chores din gaba daya," yarinyar ta sauko tana yatsine fuska tace "momy ni kayana xata fara wanke min kafin ta fara komai, don ni ynxu na daina gane wankin washin machine din nn, shi kuma iliya baya wanke min da kyau gugan ma na Hauka yake min," Hajiya tace "to maxa ki fito mata da kayayyakin taje bakin tap a kusa da garden ta wanke, ki hado mata da na sumy don naga kmr tana da kayan wanki ita ma," prettyn tace "na meenah fa," Hajiyar tace "A'a kinsan halinta tana iya cewa bata samu ba, kwaso mata naku dae kawae," prettyn ta juya da sauri ta haye sama, Aneesah dae binsu da kallo kawae take. Hajiya ma ta juya ta haye sama, bayan kmr minti goma sae ga prettyn da tulin kayan wanki ta watsa mata su a gabanta, Aneesah ta dinga bin kayan da kallo, cikin gadara prettyn tace "kuma yarinya ki tabbatar kin wanke mana kayanmu da kyau, suna bushewa kuma ki goge mana su, snn karki kuskura ki hada min fararen kayana da wasu kayan don idan suka dafe wllh sae kin siya min sabo," ta juya tana tana karkade jiki ta haye sama. Aneesah tace "hmm, ikon Allah," ta girgixa kai ta kwasa kayan da sabulae da omon da ta watsar mata ta fita daga falon ta shiga neman garden da kyar ta samo sbda girman gidan, ta ga bokitae da manyan robobin wanki a wajen ta tara famfo ba tare da bata lkci ba ta fara wankin, ba ita ta gama wankin nn ba sae kusan karfe daya, don kayan mugun yawa ne dasu, abun mamaki ma wasu bata ga alaman an sa su ba, ta juya bayan ta gama shanyan kayan tana kallon kudaden da ta dinga gani a wandunayensu da english wear tana ajiyewa gefe daya, ta kirga gaba daya kudin taga dubu biyar da dari biyar ce, tayi murmushi, rayuwa knn, ta dauki kudin da sauran sabulansu da omo sae jik, ta shiga cikin gidan, ta kusan cin karo da prettyn da ta ci kwalliya ta hade cikin riga da wando english wear ta sa spec da dan guntun mayafi xata fita, tayi ma Aneesahn wani irin kallon raina, ta bi gefenta xata fita Aneesah tace "ga wnn cikin kayanku na gani," ta juya tana kallon kudin da Aneesah ke mika mata ta mata wani irin kallo tana yatsine fuska tace "uwar me xan maki da shi, don me baxa ki xuba su cikin waste bin ba," tayi tsaki ta fice daga gidan. Aneesah ta bi ta da kallo da mamaki, ta yi hanyar dinning ta ajiye masu kudinsu a nn. Ta rasa me kuma xata yi gashi prettyn bata nuna mata ko ina na gidan ba, a hankali ta hau sama ta tsaya daga corridr din ta shiga sallama a hankali tana kare ma jerin dakunan kallo, ta kai minti biyar tsaye a wajen snn aka bude kofar da ke kallonta, hajiya ce ta fito cikin tsawa tace "wat! Kina da hankali kuwa, an ce maki 'yan aiki na hayo wa nn," a dan tsorace Aneesah tace "A'a hajiya na gama wankin ne ban san kuma me xanyi ba," cikin tsawa hajiyar tace "ko ma meye baki ga bell daga kasa da xaki danna ba" ta juya a sanyaye xata sauka, hajiyar tace "ko karamin kwakwalwarki bae baki cewa girkin rana xaki daura ba ynxu,"
Like · 4 · Report · 49 minutes ago
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 7...... A wahale Aneesah ta dawo gida ranar daga aiki don yini tayi tana aiki kmr machine, Ammi dake tsakar gida a xaune tana shirin alwala don maghrib tayi ta mike tsaye da sauri tana kallonta tace "duk hankalina ya tashi Aneesa ina ta tunanin inda kika shiga, ba karfe biyar da rabi tace xaki dinga barin gidan ba, ya akayi kika kai har maghriba, ko takowa kika yi da kafa," Aneesah ta kirkiro murmushin dole tace " ban sami mota bane Ammi, amma tun karfe biyar da rabi na bar gidan," Ammi tace "Ayya, naga ma na manta ban baki kudin mota ba, sun baki can ne," Aneesah ta gyada kai kawae duk da ko naira ba a bata ba, kuma dama bata sa rai ba, ammi tace "ta maki mutunci Allah ya biyata, gobe sae na baki kudi idan xaki tafi, daxu mamarsu jamila ta ba ma yusuf dari biyar," Aneesah tace "Allah sarki, mun gode Allah ya saka da khairan," "to ya kika ga aikin Aneesah, ba wahala dae ko, kar fa ki cuceni ki cuce kanki, ki gaya min gskya bata tsauwala maki dae koh?" Ammi ta tambayeta damuwa bayyane a fuskarta, Aneesah tayi murmushin dole don duk jikinta ma ciwo suke mata sbda tsabar aiki tace "Nace maki Ammi matar na da kirki idan ka iya xama da ita, aiki kuma ba wahala Ammi " ammi tace "to shiknn Aneesah, Allah ya taimaka, yyi maki albarka," Aneesa tace "Ameen Ammina," snn ta mike ta shige cikin daki ta cire kayan jikinta. Washegari da sassafe Aneesah ta bar gida don ta isa gurin aikinta da wuri, duk da hka sae da Hajiyar ta dinga mata masifa kmr xata rufeta da duka wae tun daxu su sumy da pretty ke jiranta ta xo ta hada masu breakfst, tana yi su sumyn na taya ta har da ce mata matsiyaciya 'yar talakawa , Aneesah ta shiga kitchen a sanyaye hawaye na bin kuncinta tana tunanin hali irin na mutanen gidan karfe bakwae da minti arbain fa ta shigo gidan suke mata tijara hka, cikin minti talatin ta gama hada masu break din ta jera kan dinnin, suka ci suka yi kat, ta dawo ta kwashi kwanukan snn ta ci gaba da aikace aikacen gidan, da rana ta hada masu lafiyayyar jollof din taliya da kaxa sae coconout drink bisa ga umarninsu, snn ta fita driver ya kaita kasuwa siyo masu ice fish da kayan ciki, don farfesun su xata yi masu da yamma kafin ta tafi, ranar ma dae ba ita ta bar gidan ba sae karfe shidda. Hka Aneesah ta dinga wahala a gidan walakancin yau daban ta gobe daban, kullum cikin kuka take a gidan don har marinta Hajiyar nayi, ga wani muguwar tsana da babbar 'yarta meenah ke mata duk tabi ta sa mata ido a gidan da tayi mistake daya ta dinga yayyafa mata masifa knn tana xagi, ita dae Aneesa sae dae ta sunkuyar da kai don sun hanata hada ido da su, ko kuma ta durkusa, duk irin abubuwan da take fuskanta a gidan kin gaya ma Amminta tayi, kullum cikin pretend take duk da irin muguwar raman da tayi, fatanta ita dae kawae tayi wata biyu tana aiki ta tara kudin waec dinta tayi gaba, amma da ta karbi kudi karshen wata matsalar gida ke karar dashi don wani lkcn ma sae su kwana hka basu ci komai ba, sae dae Ammi ta tura yusuf makwabta yaci abinci, hkn yasa ta ji ta fara hkura da karatun ma kawae, indae ta hka xasu dinga samun abinda xasu kai baki, kuma duk da irin walakancin da taga akeyi da abinci a gidan da take aiki ko sau daya bata taba debowa tace xata kawo gida ba, don itama wani lkcin da yunwa take yini a gidan sae ta dawo gida xata ci tunda ba bata suka yi ba ita kuma bata daukan abinda ba a bata ba, da hajiyar ce ma ta lura da hka duk da walakanci da gadaranta ta kan tambayeta ita ta ci abincin idan sun ci sun yi kat da 'ya yanta, sae tace mata aa don ko dan dana masu abinci bata yi idan ta gama girka masu, hkn yasa Hajiyar ta ware mata wani plate daban wae idan ta xuba ma kowa har maigadi da karen dake bayan gidan ita ma sae ta xuba nata, Aneesah tayi mata godiya ta mike ta bar wajen. Ran da Aneesah ta cika wata biyu da sati daya a gidan tana kitchen tana wanke wanke Hajiyar ta kwado mata kira "Aneesah," idan tana kwala mata kira sae ka rantse kace ita ta rada mata sunan, Aneesah ta taho da sauri ta durkushe gabanta tace "Na'am Hajiya," Hajiyar ta galla mata harara tace "da kina jina mahaukaciya kika yi min bnxa," Aneesah ta girgixa kai tace "kiyi hkuri Hajiya na bude famfo ne shiyasa banji ba," hajiyar ta daka mata tsawa "da yake kunnenki na ciwo ne ko 'yar walakanci," Aneesah tayi shiru bata ce komai ba, hajiyar tace "tashi ki ban waje raina ya daina baci shegiya kawae, anjima kya ji abinda xan gaya maki idan xuciyata ta huce," Aneesah ta mike a sanyaye ta bar wajen hawaye cike idonta, tana barin wajen meenah tace "wllh na tsani yarinyar nn mum, bata fa yi kama da 'yar aiki ba, ni ban ma yarda da ita ba kila wllh aikota gidan nn akayi ko kuma plan aka yi da ita, ji ta fa kyakkyawa gata fara, ni ban ga alamar ta taba aiki ba ma," sumy tace "ke dae bari kawae, kinga fa jiya da nake ta kallonta na kalli naga bbu abinda xaki nuna mata sae hasken bleachn," meenah ta mike a fusace tace "kika ce me, to ke din an ce maki kyau gare ki, wllh 'yar aikin nn tafi ki kyau sau dubu."
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 11...... Wani gigitattcen mari Hajiya ta kai mata tana ball da ita a fusace, "don uwarki ke dabbar wace gari ce, baki da hankali ne xaki bata masa jiki hka da drink muguwa kawai," shi ko Haiydar mikewa yyi da sauri ya bar wajen ya haye sama, kuka ta dinga yi tana ba hajiyar hakuri tana cewa bata sani ba, amma hkn bae sa matar nn ta kyaleta ba, don marinta ta dinga yi son ranta, har ta gaji snn cikin tsawa tace "bace ki ban waje mahaukaciya kawae," da kyar Aneesah ta bar falon tana ganin jiri, a daddafe ta shiga kitchen ta jingina jikin fridge ta dinga kuka a hankali, ganin tsayuwar baxae mata ba yasa ta bude kofa ta shiga garden ta xauna ta hade kanta da gwiwa tana ci gaba da kukan takaici, wnn wace irin bakar rayuwace ita kam, ta kai minti kusan sha biyar a wajen tana ta aikin kuka, taji an dafa kafadarta a hankali, ta dago a tsorace taga wanene, xuciyarta ya kusan shigewa cikinta ganin ko waye, ya xauna gefenta yana kallonta ta matsa a tsorace tare da kkrin mikewa ta bar wajen ya rikota, a gigice ta tura hannunsa tace "nashiga uku, malam ka rufa min asiri don Allah don annabi ina rokanka," ya ki sakinta a hankali yace "to xauna kiji abinda xan ce," ta shiga waige waige a tsorace tace "kayi hkuri nace don Allah," ya wara mata manyan idanunsa yace "sae kin fara saurarata," ta sulale kasa gefensa don yaki sakinta har lkcin, hawaye na bin kuncinta tace "bka ma Allah knn" ya girgixa mata kai a hankali yace "ina yi masa," snn ya ciro handkercheif ya dafe kanta da hannunsa ya shiga goge mata hawayen fuskarta ta kauda fuskar da sauri xata mike tsaye, yyi saurin matsowa kusa da ita ya sakale hannunsa a wuyanta ya ci gaba da goge mata fuskar, ta tsorata sosai don tunda take ba a taba mata hka ba, ta fara kkrin kwace kanta tana cewa "nashiga uku meye hka malam," muryar Hajiya suka ji a kitchen tana cewa pretty wae ina Haiydar ya shiga ne, tace "momy nima shi nake nema har ynxu yaki bamu tsarabar mu fa, ita kuma wnn yarinyar taki taxo ta ba mutane abinci har worm din cikina sun fara cinye min fatar cikin " Hajiyar ta kwala mata kira da karfi "Aneesah!" Aneesah ta turasa da karfi muryarta na rawa tace "innalillahi, wayyo Allahna ka rufa min asiri don ya rasulillahi," ya saketa ya mike da sauri ya xaga yyi hanyar garage, ita ma ta mike da sauri ta bude kofar kitchen ta shiga suka kusan cin karo da Hajiyar...
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~ANEESAH~ By Khaleesah Haiydar
9......
Aneesah ta gama shiri karfe shidda da rabi xata bar gida, Ammi dake xaune kan darduma har lkcn ta bi ta da kallo da mamaki "kina da hankali kuwa Aneesah, ina xaki da sassafen nn hka," Aneesah ta xauna gaban Amminta tana kallonta tace "ae nayi maki bayani Ammi, xasu yi baki ne yau, xan masu girki da dan yawa shine tace naxo da wuri," Ammi ta harareta tace "shine ko karfe bakwae bai karasa ba xaki fita, ina laifin ki bari karfe bakwan,ko fa karyawa baki yi ba " Aneesah tace "A'a Ammi ynxu xan wuce, da wuri bakin xasu iso ne fa," Ammi tace "to ki sha kokon kafin ki tafi," Aneesah tace "ohh Ammina ni bana jin yunwa idan naje can ma ai suna bani wllh," ba dan ran Ammi ya so ba ta bata kudin mota tayi mata Allah ya kiyaye snn ta bar gidan ta kama hanyar gidan aikinta. Ko da ta isa gidan duk bacci suke basu tashi ba, ta danyi share share da goge gogenta tayi mopping ko ina, snn ta hada masu breakfst kafin su tashi ta jera kan dininn, tukunna ta fara girke-girken da aka lissafa mata jiya da yake akwae kayan cefanen gaba daya a fridge. Ba ita ta gama girkin ba sae kusan karfe sha daya don ma gas biyu ta kunna, da electric cooker, ko da ta gama sae da ta fara gyara dinning din da suka yi breakfst ta kwashe duk kwanukan, ta gaisar da yan gidan gaba daya, snn ta fara jera sabon girkin da ta yi a dinning din, ta saka ginger drink din a fridge yyi sanyi, tana goge gogen kitchen taji sun fito gaba daya su ukun sun hade cikin kananan kaya suna ta murna xa su je dauko yayansu a Airport, Hajiyar ta rakasu har bakin mota suka ce da kansu xasuyi driving basa son driver ya jasu, tayi masu Allah ya kiyaye ta shigo gidan tana kwala ma Aneesah kira, Aneesah ta fito da sauri ta durkusa gabanta tace "na'am Hajiya gani," "kiyi maxa kije ki gyara masa bedroom dinsa ki canxa bedsheet,ki tabbatar ko ina yyi fes snn ki shiga nawa bedroom din ki gyara " Aneesah tace "to Hajiya," snn ta mike ta bar wajen ta hau sama ta shiga yin aikin da ta sa ta. Cikin awa daya ta gama komai ta sauko downstairs, Hajiyar na falonta tana waya, tana shiga kitchen taji shigowar motarsu, pretty ta shigo da gudu tana dariya ta dinga kwala ma momynsu kira wae taxo taga yayansu, Hajiyar ta fito da sauri suka hade dae-dae bakin kofa ta rungume dan nata cike da farin ciki da murna tace "waw my son ya hanya," shi ko ya hade rae "don Allah ku bar ni naji da gajiya na mana mum, su kuma wa innan sun tashi sun kwashi jiki sun bi ni Airport kamr wasu mahaukata " meenah ta dan tabe baki tace "dan ma ka samu ana farin cikin dawowarka, wllh momy tun a airport yake ta gwasale mu sai kace dole, ni da nasani ma da baxan je ba," ya juya yana kallonta yace "to uwar waye yace da ki xo din munafuka, kin tashi kin yi shiga kmr mai shirin tsallaka wuta kin bini airport, wae ma ban hana ku sa irin wa in nan kayan ba, har da ke ko Zainab," ya fadi yana kallon pretty, sumy ta tabe baki ta dan yi tsaki ta haye sama hka ma meenah da ta shiga gunguni, pretty tace "kayi hkuri yayana," Hajiyar ta hade rae ita ma "kaga matsalata da kai knn Haiydar ba dawowarka ba takura ma 'ya yana, gskya baxa mu shirya ba wnn karan, kawae bbu ruwanka ka sa masu ido duk me kaga suna yi," yace "Allah ya baku hkuri," snn ya haye sama pretty ta bi shi a baya, Hajiyar ma ta bi sa ganin kmr ransa ne ya bace, duk wnn abunda suke Aneesah na jinsu, sae abun ma ya bata dariya, a xuciyarta tace "Allah ya kyauta da irin wnn familyn, don tun da taxo gidan ita kam bata taba ganin mai sllh cikinsu ba, sae dae Hajiyar ita ma idan lkci ya wuce, ita ko dama bata isa tayi a cikin gidan ba sae dae taje garden.
14 mins · Khaleesat Haiydar...
[9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: Aneesah.... By Khaleesah Haiydar 10.... Bayan minti Ashirin Aneesah na xaune cikin garden, don bbu aikin da xata yi a lkcn sae kuma xuwa anjima, da yake akwae kofa ta kitchen da xae sada ka da garden din tanan ta bi ta fita, Hajiya taji tana kwada mata kira ta shigo gidan da sauri ta durkusa daga bakin kofar kitchen din tace "gani Hajiya," ta galla mata Harara tace "gidan ubanwa kika shiga nke ta faman ihu kmr makogwarona xae fito?" ta sunkuyar da kai tace "kiyi hkuri Hajiya ina daga waje ne," ta daka mata tsawa "da'allah tashi ki ban waje muguwar yarinya kawae nasan kasheni kawae kike son yi abinda na haifa ma basu kasheni ba shegiya kawae," Aneesah ta mike a sanyaye xata bar falon sae a lkcn ta kula gaba dayansu har yayan nasu ma na falon, su sumy da meenah suka tuntsire da dariya suka dinga yi, shi dae hankalinsa na kan laptop, pretty na jikinsa tana kallon abinda yake yi, Hajiyar ta kara da cewa "kuma idan kinga dama ki dauko ma son dina ginger drink a fridge," ta juya ta shige kitchen din da sauri, sae a snn ya dago kai yana yatsine fuska yace "ita ce ta hada drink din mum?" Hajiyar tace "eh ita ce ta hada, ta iya sosae son,

Please Login or Register in order to submit comment