Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aneesah, ya kasa daina kallonta.
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 109..... Daga Hydar har Mujaheed tsayawa kallonta suka yi cikin wani yanayi da baxa a kira da mamaki ba, Mujaheed ya karaso gabanta a hankali yana kallonta a sanyaye yana gyada kai yace "shknn Aneesah, dama ni na taimake ki ne sbda Allah da kuma ina sonki, tunda kika yi wnn furucin xan nuna maki ban taimake don wani abu naku ba Aneesah, xan rabu dake, Allah ya bamu Alkhairi," yana kai wa nn ya juya ya bude motarsa, Aneesah ta matsa daga jikin motar a hankali hawaye na bin kuncinta, ta bi motar da kallo har ya bar anguwar, snn ta fashe da kuka tana kallon Hydar da ya juya ko tunanin me yake oho, ta ga ya juyo a hankali yana kallonta, idonsa ya kada yyi jajur, ta juya masa baya tana kuka ssae, a raunane taji ya fara magana "Aneesah kin ban mamaki, ke har xaki iya biyana abinda na maki," ya girgixa kai kmr xae yi hawaye muryarsa can kasa yace "na rabu dake Aneesah, dama badan wani abu naku na tsaya maku ba, nayi sbda Allah ne da kuma son da nake maki, kiyi hkuri na rabu dake na har abada Aneesah i promise yhu baxan sake shiga rayuwarku ba, neva, Allah ya sada mu da Alkhairinsa" Aneesah ta rasa ma me xata ce don tashin hankali kuka ssae take tana girgixa masa kai, hawayen da ta ga idonsa ya dada rikita ta, ya juya yyi hanyar motarsa, ta sulale wajen cikin tashin hankali, da kyar ta iya cewa "na shiga uku," tana kallo har Hydar ya bar anguwar, ta fashe da wani sabon kukan da ta sanin abun da tayi, da kyar ta iya mike tayi hanyar shiga gida tana ganin jiri, bata bari Ammi ta lura da kukan da take ba, tana shiga daki kwanciya kawae tayi, ranar tayi kukan da ta sanin abun da tayi da daddare, bacci ya kaurace mata duk taji bbu abinda ke mata dadi a duniyar, taji ta tsani kanta, sae kusan karfe uku ta samu bacci, da safe Ammi ta lura da yanda idonta ya kumbura tayi tayi da ita me ya sameta taki gaya ma Ammi tace kanta ne ke ciwo kawae, karfe sha daya su ummi da Momynta suka xo gidansu, Aneesah tayi farin cikin ganinsu ssae kuma tayi mamakin yanda akayi suka san gidansu, Ammi ta tare su da kyau don Aneesah ta bata lbrinsu, har Ammi na shirin xasu je gidan nasu xuwa nxt wk sae kuma ga su sun xo, momy na ta hira da Ammi bayan ta mata jajan Abinda ya faru, duk wnn hiran da ake Aneesah dakewa take kawae don xaxxabi take ji na neman rufeta, duk she is nt herself ta rasa abinda ke mata ddi a duniyar, kar ummi tace ta shareta yasa ta shiga tambayarta Mudatheer da mutanen da ta saba da xamanta gidansu, ummi tace "yana kano ae tun lst wkk," Aneesah ta dauko takarda da pen tace ummi ta rubuta mata Nmbrsa, sae kusan sha biyu Ammi da Aneesah suka rakasu bakin motarsu xasu koma gida, Ammi tace masu suna nn xuwa suma. Bayan tafiyar su ummi da kmr minti ashirin Faruuq ya shigo gidan, Aneesah ta kirkiro fara'a tana gaishesa ya amsa yana murmushi, tace "sae ynxu ya faruuq," yace "wllh kuwa ya shiga ya gaida Ammi a daki," Aneesah ta xauna ta rafka tagumi tayi jigum a tsakar gidan abun duniya ya isheta, tuna abinda ya faru jiya yasa hawaye ya shiga bin kuncinta, bata masu halacci ba, ta butulce masu, ta cuce kanta, kuka ssae take amma mara sauti, ta ga mutum durkushe gefenta yana kallonta, ta mike tsaye da sauri tana goge hawayenta tace "ya faruuq," ya girgixa mata kai yace "me ya faru Aneesah," tana goge fuskarta tace "bbu komai," ya harareta yace "karya kike yi, bana ce ki daukeni matsayin yayanki ba Aneesah, meye damuwarki ki gaya min, kar ki boye min ni yayanki ne kinji" wasu sababbin hawayen na bin kuncinta tace "bbu komai ya faruuq," yace "to bari naje na kira Ammi sae ki gaya mata ita," ta girgixa masa kai da sauri tace "A'a don Allah kayi hkuri," yace "to gaya min me ya sa ki kuka, tunda na shigo na lura kina cikin damuwa kanwata," tana goge fuskarta a sanyaye ta kasa cewa komai, yace "ki yarda dani Aneesah, ki gaya min damuwarki don Allah," a hankali tace "xan gaya maka to," ya shiga dakin da Ammi ta gyara masa don dakuna uku ne a gidan dama, ta bi sa a baya ta xauna kan kujera tana kallonsa yace "ina jinki kanwata," a sanyaye tace "lbrin mutane biyu xan baka yayana, sae ka gaya min wanda yafi cancanta a cikinsu ya xama mamallakin warce ke cikin lbrin nawa," ya hade rae yace "lbri nace maki nake son ji, matsalarki nace ki gaya min na sama maki solution kanwata," tace "ka fara saurarana yaya, wllh xaka ji damuwata idan na gama baka lbrin," yace "to ina jinki," a nutse ta shiga basa lbrin kanta ba tare da ta bari ya gane ba, tun daga farko har ixuwa lkcn da ta fara aiki gidansu Hydar, da irin taimakon da yyi mata, tun daga nn ya gane lbrinta take basa, ya dae yi shiru yana sauraranta, bbu abinda ta boye ma faruuq har xuwanta kauye da haduwarta da Mudatheer, snn Mujaheed, Faruuq ya tsura mata ido yana sauraran lbrin nata har ixuwa abinda ya faru jiya da daddare, bbu part din da ta boye masa, ta fashe da kuka tana kallon faruuq da ya lumshe idonsa ya kasa cewa komai, a hankali taji yace "Hydar ya cancanci xama mamallakin ki Aneesah,"
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 110.... A hankali Aneesah ta
sulalo daga kan kujeran da take hawaye na bin kuncinta,
Faruuq ya tsura mata ido snn yace "me yasa kika ce xaki
biyasu abinda suka maki Aneesah, kinga alamar xaki iya biyan
abinda suka maki, barin Hydar da ya xauna prison na
watanni," kuka ssae take tana girgixa kai tace "ban san lkcn
da nace masu hka ba ya Faruuq," faruuq yace "to ki kirasu ki
basu hakuri," a sanyaye tace "ban da nmbrsu," yyi shiru yana
kallonta snn yace "ki bani address dinsu duka, kafin na tafi yau
xanje na samesu," ta gyada masa kai tana kallonsa, a takarda
ta rubuta masa address dinsu gaba daya, snn ya mike yace "to
ki share hawayenki kanwata kar ki daga ma Ammi hankali, sae
na dawo" yana kai wa nn ya fice ta bi sa da kallo hawaye mai
xafi na bin kuncinta, ta mike da kyar tana gyara fuskarta ta fita
daga dakin xata je yin wanke wanke, throughout ranar Ammi ta
kasa gane kan Aneesah duk ita ma ta daga hankalinta, ita dae
Aneesah jiran dawowar ya faruuq kawae take, da yamma tana
share tsakar gida taji an bude kofar gidan ta mike da sauri a
tunaninta Faruuq ne, pretty ce ta shigo gidan kmr
mahaukaciya wasu mata na biye da ita a baya, gaban
Aneesah yyi mugun faduwa, pretty ta karaso kusa da ita da
sauri ta rikota ta fashe da kuka tace "me kika yi ma yayana
Aneesah, ki gaya min me kika yi ma yayana," ta sulale kasa ta
daura hannu a ka tana kuka mai ban tausayi tace "don Allah
ki gaya min me kika yi masa," Hajiyar Mujaheed ta karaso
cikin gidan ita ma a rude tana kallon Aneesah tace "ke ce
Aneesah ko," Aneesah ta kasa cewa komai don tashin hankali,
a hankali ta sami kanta da sulale kasa ta fasa wani ihu a
tsorace, hajiyar ta durkushe gabanta a rude ta rikota tace "don
Allah ki rufa mana asiri," don a tunaninta suma Aneesah xata
yi, Ammi da bata gidan ta shigo dai dai lkcn, ta karaso a dan
tsorace tace "me ya faru," pretty na kuka ssae tace "don Allah
mama ki bar ta ta bi mu asibiti, kar yayana ya mutu ita yake ta
kira," daya daga cikin matan da suka shigo gidan ta dago
Aneesah tayi waje da ita, Hajiya na biye da su da sauri, duk da
ganinsu kasan suna cikin tashin hankali, Aneesah komawa tayi
kmr statue duk ta kasa wani kwakkwaran tunani da
kwakwalwarta, ta xama kmr wata mutum mutumi, hawayenta
ma tamkar sun kafe take ga, Amai ta shiga kwararawa cikin
motar ba gaira ba dalili, don har lkcn ita bata gama fahimtan
abinda ke faruwa ba, matan suka riketa a rude wata na xuba
mata ruwa, sae a snn maganganun pretty suka dinga dawo
mata, daga nn kuma bata sake sanin abun da ya faru ba, don
sulalewa jikin matar da ke rike da ita tayi sumammiya.duk
suka rude a motar wasu har da kuka, pretty nata kam ba a
magana, suna isa asibitin ita ma aka shiga da ita da sauri. Ko
da ta bude idonta pretty ta gani xaune gefenta tana kuka,
pretty ta kamo hannunta cikin kuka tace "don Allah kar ki sake
rufe idonki Aneesah ki tausayama yayana," wata nurse ta
shigo ta janye pretty daga kusa da Aneesah da ta xuba mata
ido kmr wata mara hankali, nurse din tasa duk matan dake
dakin suka fita, Aneesah dae binsu kawae take da kallo, nurse
din ta fita ta ja kofar, bacci mai nauyi ya dauketa daga nn.
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: Khaleesat Haiydar
~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 111..... A
hankali Aneesah ta bude idonta ta shiga kare ma
inda take kallo, daga karshe ta sauke idonta kan
drip din dake hannunta, ta fara kkrin mikewa
xaune, taji muryan mutum a gefenta, ta juya da
sauri taga Abdul ne, yace "ya jikin kanwata" tayi
shiru tana kallonsa, ya mike ya fita ya shigo da
nurse ta cire mata drip snn tace a bata tea ta
sha, Abdul ya fita ya shigo tare da mum din
Mujaheed ta karaso kusa da Aneesah tace "sannu
kinji Aneesah," Aneesah dae bata ce komai ba sae
kallonta da take, ta hada mata tea ta shiga bata
da kanta, kadan Aneesah ta sha ta kauda mata
kai Hajiyar tace "ki sha mana Aneesah," Aneesah
ta girgixa mata kai a karo na farko muryarta a
shake tace "ya Hydar fa," Hajiyar tace "ki daure
ki sha sae na kai ki gunsa bacci yake," da kyar ta
shiga kurban tean har tayi rabi tace ta koshi,
wata nurse ta shigo da magunguna mum din
Mujaheed ta karba tace "xa mu iya dan fita da ita
nurse," Nurse din tace "idan har bata ganin jiri
xaku iya fita da ita amma kar kuyi nisa," Hajiya
tace "A'a bama waje xamu ba, ward din dake
sama xamu," nurse din tace "ok," tana kallon
Aneesah tace "hope bbu inda ke maki ciwo ynxu,"
Aneesah ta gyada mata kai nurse din ta fita,
Abdul yace "mum ku bar Hydar ya huta kar a
tada shi," hajiya tace "aa baxa mu tashe sa ba
dama, da ya ma aka samu yyi baccin," hajiyar ta
taimaka ma Aneesah ta mike tsaye ta bata
takalmi ta sa, snn suka fita daga dakin, dakin da
Hajiyar ke kwance ta fara kai ta, hajiya duk ta
rame ta xama wani iri ita ma a daxun ciwonta ya
tashi bayan an aiko mata da rasuwar sumy a can
india, snn ga Hydar da aka rasa me ya samesa
lkci daya, don lkcn bai ma san da mutuwar
kanwartasa ba bare ace shine, Aneesah ta shigo
dakin a sanyaye tana kallon hajiyar da ta mike
xaune da sauri ganinta, ita ma ruwan ake kara
mata, Ammi ma na xaune dakin, cikin murya mai
ban tausayi Hajiyar ta fara magana tana kuka,
"don Allah Aneesah ki yafe mana, ki tausaya ma
rayuwata ki amince ki aure Hydar, shi daya nake
da bana son wani abu ya samesa Aneesah, ban
gama dawowa hayyacina daga mutuwar
Sumayya ba sae ga na Hydar, idan wani abu ya
sami Hydar ban san ya rayuwata xata kasance
ba," kuka ssae Hajiyar take, Aneesah ma kukan
take, duk mutanen dake xaune dakin sae da
jikinsu yyi sanyi, Ammi ko kasa dago kanta tayi,
Hajiya ta juya a sanyaye tana kallon mum din
Mujaheed tace "kun ki gaya min halin da Aliyu ke
ciki," mum din Mujaheed tace "nace maki bacci
yake yi Hajiya," tana fadin hka ta kama hannun
Aneesah suka fita daga dakin, wani ward din
daban suka shiga gabanta yyi mugun faduwa
ganin Hydar kwance ana kara masa ruwa har
leda biyu, faruuq na xaune dakin da wani frnd
dinsa, pretty ma na xaune gefensa kmr xata shige
jikinsa, duk ta xama wani iri itama abun tausayi,
Aneesah ta karasa kusa da shi da sauri ta fada
kan gadon tana kuka, faruuq ya janyeta da sauri
yace "kar ki tada sa Aneesah," ta koma gefe tana
kallonsa tana ci gaba da kukanta mai ban
tausayi, Mum din Mujaheed ta kalli Najeeb tace
"na samu Mujaheed a waya daxu Najeeb, wae
ashe ya koma holland ne, kaji tsiya ko ubansa fa
bae sanar ma wa ba bare ni," Najeeb yace "ikon
Allah, to kin gaya masa rashin lafiyar Hydar din
ne mum," Hajiyar tace "eh na gaya masa, yace
gobe xae juyo, yana can duk ya daga hankalinsa
shima yau ya kirani yafi sau ashirin " a sanyaye
pretty tace "nima yana ta kirana," Najeeb yace
"dama kice masa mu hadu a Egypt kawae, can
xamu wuce da Hydar gobe," Hajiyar tace "egypt
kuma Najeeb," Najeeb yace "wnn Abdul din ne
yace hka, shima likita ne ssae, kuma daxu ma
wani doctor ya kirani office ya gaya min hka,"
Hajiyar tace "to mu dae ga mu ga Allah, Allah dae
ya basa lfya, ku ba Aneesar kujera ta xauna,"
Najeeb ya jawo mata kujera ta xauna da kyar,
Hajiyar ta juya ta fita, ana kiran sllhn isha duk
suka fita yin sllh dakin ya rage daga Aneesah sae
pretty, wata mata ta leko tace pretty taje Hajiya
na nemanta, ta fita daga dakin tana kallon
Aneesah kmr me tsoron kar ta ma yayanta wani
abun, bayan ta fita Aneesah ta mike ta karasa
kusa da gadon a sanyaye ta dafa gadon tana
kallonsa hawaye na bin kuncinta, a hankali ta
shiga kiransa ganin bae amsa ba yasa ta fada
kansa tana kuka ssae, ranar dae asibitin ta
kwana don likitocin ca sukayi ta xauna ko da xae
farka ya xamana tana kusa da shi kuma a kanta
xae daura ido kafin kowa, dole Ammi ta wuce
gida ta barta, cike da tausayin Hydar, Aneesah
dae na gefensa a xaune jira kawae take taga ya
bude ido amma yaki budewa, hkn yasa ta kasa
samun nutsuwa hawaye yaki tsaya mata, ba ita
ba kowa ma abinda yake jira knn har likitocin
amma shiru.
Like · 5 · Reply · Report · 27 minutes ago
A'ishah Abubakar
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 112..... Washegari friday aka
fara shirin fitar da Hydar xuwa Egypt ganin har lkcin bae farka
ba, bbu wanda hankalinsa yafi tashi irin Aneesah da mum
dinsa, Aneesah na xaune gefensa ita dae gata nn, wani lkcn
ma sae ayi ta mata magana bata san da ita ake ba, tamkar
mai brain disorder ta koma, Hajiya ce ta shigo dakin don taga
bbu abinda kwanciya xae mata dan ta na nn rai a hannun
Allah, ta karaso cikin dakin a sanyaye tana kallon Aliyu,
Aneesah ta mike xata bata kujera tace "yi xamanki Aneesah
dama magana na xo muyi dake," Aneesah tayi shiru tana
kallonta snn tace "to mumy ina jinki," Hajiya ta juya tana
kallon Abdul dake xaune dakin, Aneesah ta gane me take nufi
tace "kiyi maganarki mum, yayana ne," Hajiyar ta ja kujera ta
xauna a raunane ta fara magana kmr mae shirin fashewa da
kuka "Alfarma naxo nema gunki Aneesah, kuma nasan baxa ki
hanani ba, Aneesah nasan Hydar na sonki ssae, ke dae ce ban
san abinda ke xuciyarki ba, wnn rashin lfyar sbda ke yake
yinta, kuma tun ba yau ba yake da hawan jini kuma ni kam
nasan ta dalilinki ya samu hawan jini sbda yanda yake sonki,
Aneesah ki tausaya mana don Allah don Annabi ki amince a
daura maku aure da Hydar sae ki bi su can Egypt din har Allah
ya basa lfya, kinga ni baxae yiwu na bi su ba, jiya sumayya ta
rasu, kiyi hkuri ki taimake mu Aneesah hkn kadae ne xae dawo
min da farincikin da na ko da ya warke ya ganki a matsayin
matarsa" tana kai wa nn ta fara hawaye abun tausayi, gaban
Aneesah ya shiga bugu da sauri da sauri ta kasa daga kai ta
kalle Hajiyar sae hawayen da take ita ma, a xuciyarta tace
wayace maki Hydar na sona ynxu, da knn amma ba ynxu ba,
muryar Abdul taji yace "ki amince kanwata nasan Hydar na
sonki ssae, kuma daga reactions dinsa jiya bbu tantama ta
dalilinki hawan jininsa ya tashi, save lyf kanwata, dama Allah
yyi shine mijinki" kuka ssae Aneesah take tana kallon Abdul,
ya gyada mata kai alamar ta yrda da batun Hajiyar, hajiya sae
hawaye take tana jiran cewar Aneesah, da kyar Aneesah ta iya
ce mata "sae Ammina ta amince," ko minti biyar Hajiyar bata
kara a asibitin ba ta sa aka kaita gun Ammi, Ammi ma ta kasa
cewa komai jin batun da Hajiyar ta xo da shi, daga karshe da
kyar ta samu na cewa tace to Hajiya ki bari muyi shawara da
yan uwana da na ubanta, Hajiyar tace "ba komai 'yar uwa duk
yanda kuka yi ina jiran bayani, kinsan kila yau xa a su fita,
kuma ga abinda likitoci suka ce ya kasance tana kusa da shi
xae far fado, shi yasa nake son ku taimaka nasan Hydar xae
riketa amana, kuma son gskya yake mata" Ammi tace "xaki ji
ni gobe Hajiya Allah dae ya bashi lfya," Hajiyar taji ddi ssae
kmr an mata albishir da gidan Aljanna. Faruuq Ammi ta fara
magana da kan batun da Hajiya ta xo da, yyi shiru na dan lkci
snn yace "gskya yana sonta ssae Ammi ita fa ya dinga kira ko
da muka isa asibiti jiya, sae dae ki fara tuntubarta kar a cuceta
ita kuma, amma ya cancanci xama mijinta," faruuq yaje asibiti
ya maido da Aneesh gida ranan, duk ta xama wani iri ta rame
kamr ita ce mai ciwon, a nutse Ammi ta sa ta gaba ta shiga
tambayarta ko tana son Hydar, ta fashe da kuka ssae tana
girgixa ma Amminta kai, Ammi tace "kiyi min magana
Aneesah kar ki ji komai" cikin kuka muryarta na rawa tace "to
Ammi ya Mujaheed fa?" Ammi tayi shiru tana kallonta snn a
hankali tace "shi kike so Aneesah?" Aneesah ta kife kanta kan
gado tana kuka kmr ranta xae fita ta kasa ce ma Amminta
komai, Ammi ta rasa me xata ce mata ita ma, duk iya yan da
Ammi ta so jin ko Mujaheed din take so Aneesah kin cewa
komai tayi sae kuka, dole Ammi ta kyaleta ta fita daga dakin,
daga nn bacci ya dauketa.
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
113.....
Bayan sllhn Magrib Aneesah na kwance daki tayi jigum abun duniya ya isheta, Ammi ta shigo dakin tace "ki je wae ana nemanki a waje Aneesah," Aneesah ta mike xaune tana kallon Ammi a sanyaye tace "wa ke nemana Ammi," Ammi tace "wae abokin Hydar," Aneesah tayi shiru, Ammi tace "tashi ki je mana, kar dae ki dde ae faruuq ma na waje," Aneesah ta mike jikinta a sanyaye kmr mara lfya, ta dauki Hijab dinta ta sa ta fita daga gidan, yana tsaye jikin mota, sae dae ya juya baya, ta karaso kusa da shi da sauri tana kallonsa, muryarta na rawa kmr xata yi kuka tace "ya Mujaheed," ya juya da sauri ya sakar mata murmushi yace "ya akayi kika son ni ne," hawayen da ya cika idonta ya gangaro, ya girgixa mata kai yace "kuka kuma kanwata," ta kasa ce masa kmai sae kukan da take yi a hankali, ya kama hannunta suka samu wani dan dakali suka xauna snn yace "ni bance kiyi min kuka ba Aneesah, ko nima so kika nayi kukan ne," ta girgixa masa kai yace "to ki daina kuka kanwata," bata ce komai ba ta shiga goge hawayen fuskarta, sun kai kusan minti biyar a hka snn a hankali taji yace "don me kika ce baki son Hydar, kuma nasan kina son shi Aneesah" Aneesah ta tsura masa ido bata ce komai ba sae wani sabon hawayen dake gangarowa daga idonta. Ya girgixa mata kai yace "ki kwantar da hankalinki, ni nasan Hydar na sonki kuma xae rike ki amana, kinga dae halin da yake ciki sbda ke bna son wani abu ya sami aminina Aneesah, hka Allah ya kaddara dama ni ba mijinki bne" tunda ya fara magana Aneesah ta tsura masa ido kmr gunki ta kasa cewa komai. Shirun da taji yyi yana kallonta yasa ta fashe da wani matsanancin kuka, ya dago kanta ya ma rasa me xae ce mata, nn da nn shima idonsa ya kada, ya mike da kyar murya can kasa yace "ni bance kiyi min kuka ba Aneesah,"
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
114.....
Mutuwar tsaye Aneesah tayi daga inda take tsaye, ta kasa ko
da kwakkwaran motsi idonta har lkcin na kan Najeeb dake ta
faman surutu yana dariya, Abdul ya shigo dakin yana murmushi
da fara'arsa ya karaso kusa da Hydar dake binsu da kallo bae
ce komai ba, yace "congrat luver guy, ga ka ga Aneesah no
more love sickness," Aneesah ta jingina jikin bango ta rumtse
idonta cikin tashin hankali, taji kafarta ya kasa daukarta, wayyo
ta shiga uku ita kam, bbu wanda ya lura da halin da take ciki
kowa da abinda yake cewa, banda Mujaheed dake murmushi
kawae, ta bude idonta a hankali ta daura kan Mujaheed dake
tsaye gefen gadon, shi din ma kallonta yake yi, suna hada ido
ya dauke kansa da sauri, taji wani hawaye mai xafi na bin
kuncinta ta girgixa kai tayi hanyar fita daga dakin da sauri,
Mujaheed ya bi ta da kallo abun tausayi, Abdul dake kallonsu
shima yaji wani iri, suna hada ido da Mujaheed, ya dauke
kansa ya karasa kusa da gadon da Hydar yake kwance, ana
surutu amma Hydar shiru sae ido da ya xuba masu, da dan
damuwa Najeeb yace "A'a wae ya dae ku kira likita naga yaki
magana," ganin Hydar yaki ce masu komai sae kallonsu da
yake har lkcn yasa Abdul ya karaso kusa da gadon yana
kallonsa yace "ya? Kana jin mu kuwa Hydar," Hydar ya sauke
ajiyar xuciya yace "ina jinku," snn ya fara kkrin sauka daga kan
gadon, Abdul ya rikesa yace "ina kuma xaka," ya dan yatsine
fuska yace "4 hw lng nake nn kwance" Najeeb yace "u've been
here 4 d past three dayz, sae yau da Aneesah ta xama
mallakinka don gulma ka farfado har da ana shirin fita da kai
egypt," Hydar yyi shiru yana kallonsa, a hankali cikin wani
yanayi me kama da confusion yace "Aneesah" Najeeb yace
"yes," Hydar ya dafe kansa na kusan minti biyar snn ya dago
yana kallon Mujaheed, Mujaheed bae bari sun hada ido ba,
Hydar ya fara kkrin mikewa tsaye ya koma da sauri ta dalilin
wani jiri da ya gani, Abdul yace "ya dae," ya koma ya kwanta
da ganinsa kasan bae da karfi a hankali yace "baxan iya tashi
ba," Mujaheed yace "bari a kira doctor to," ya juya ya fita,
Hydar na kallon Najeeb yace "ku gaya min gskya don Allah da
gske ne abinda kuke gaya min," Najeeb yace "gskya ne Hydar
Aneesah matarka ta sunna ce ynxu," Hydar ya girgixa kai cike
da takaici yace "meyasa xakuyi hka, meyasa kuka yi ma
Mujaheed hka, bani take so ba shi take so," faruuq yace
"Aneesah na sonka dan uwa ka kwantar da hankalinka, hka
Allah ya so," Aneesah na fita haraban asibiti taci karo da
Hajiya, a rude Hajiya tace "meye kike kuka Aneesah me ya faru
kuma" cikin kuka Aneesah tace "wae mumy da gske ya Hydar
mijina ne ynxu," Hajiya ta rungumota tace "to meye abun kuka
Aneesah ko ba kya son sa ne," cikin kuka ssae tace "ba sona
yake ba mumy, don Allah ku taimakeni," da mamaki Hajiya
tace "wa yace maki hka Aneesah, ae duk duniya a yanda na
lura bbu wanda Hydar yake so bayan ubansa kmr ke," Hajiya ta
ja ta suka isa gun mota takira driver ba a jima ba ya xo tace ya
kai su gida, har suka isa gida Aneesah bata daina kuka ba,
suna fitowa daga mota Aneesah ta tuna lst tym din da ta bar
gidan, Hajiyar ta ja ta suka shiga ciki mutanen dake cikin gidan
na ta tambayarta ko Aneesah ce amaryar, ta dae yi murmushi
tayi masu sannu da gida suka wuce sama da Aneesah ta kai ta
dakinta ta xaunar da ita kan gado, ynxu kam Aneesah ta daina
kukan da take yi sae na xuciya, Hajiya ta dago kanta tana
kallonta tace "kiyi hkuri Aneesah amma don me kika yi tunanin
Hydar baya sonki, sbda ke fa ya shiga halin da yake ynxu, shi
yace maki baya son ki" Aneesah ta sunkuyar da kanta bata ce
komai ba, nn Hajiya ta dinga bata baki tana mata 'yan nasihohi
ita dae bata ce komai ba sae hawayen da take, tana dakin
hajiya ita kadae bayan sllhn isha tana jujjuya lafiyayyan abincin
dake gabanta Wasu mata biyu suka shigo dakin, dayar tace
"amaryarmu baki ci abincin bane,"

Please Login or Register in order to submit comment