Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saida xobo sallama snn ta
dauki bokitin gyadar ta ta bar dandalin don
abokinta mudatheer ma bae xo ba, tana isa gida
taga wata tsohuwar mota da ta gama shan
wahalar duniya tana neman freedom a fake a
kofar gida, ta bi ta gefen motar ta shiga gidan,
shatu ta gani xaune kan 'yar kujera, kan tabarma
kuwa wani tsoho ne dake ta washe baki, gaban
Aneesah yyi mugun faduwa ta dake ta karaso
dan tsakar gidan da sallamarta snn ta shige
bukkarsu, shatu na wagale baki tace "sannu da
dawowa lu'u lu'u, in kin ajiye bokin ki fito ga
malam tanko ku gaisa," Aneesah tayi kmr bata ji
ta ba ta sulale kasa a hankali cike da tausayin
kanta taji kmr ta fasa ihu, shatu ce ta shigo
dakin da kanta tana ganin Aneesah a wnn hali ta
hade rai, tace "ke ni fa ban son iskanci da rainin
hankali, kina ji ina kiranki xaki yi bnxa dani ga
bawan Allah can ya xo tun daxu yana jiranki, an
gaya maki yana xuwa gun 'yan mata ne da sunan
xance, wllh sae dae su suje gidansa su same shi,
don mun samu ya tuko santaleliyar motarsa har
nn shine xaki masa walakanci, maxa shafa jan
baki da hoda ki fito yana jiranki," Aneesah ta
mike tsaye da kyar tana kkrin mayar da hawayen
da ya cika idonta, shatu na kallonta tayi duk
yanda ta ce mata, snn ta sa ta yafa wani dan
guntun mayafi, xata fita shatu ta jawo ta da
sauri, ta marairaice fuska kmr xata yi kuka tace
"ki tausaya min Aneesah idan muka rasa wnn
daman mun shiga uku hka xamu ta tsaya wa a
talauce har mu mutu, don Allah ki ba sa hadin
kai, duk me yace maki kiyi, kinga ko sati biyu
baxa a yi ba xa a daura auren ku, idan ma baki
son xama wnn kauyen ne sbda 'yan sa ido kawae
sae ki koma kauyen dake gaba da wnn yana da
gida a can aka ce wae, ki rufa min asiri kar ki sa
a mana dariya don ixuwa ynxu lbri ya gama
baxuwa wae malam tanko na birni xae aure
Aneesah, kar ki bani kunya don Allah," tunda
shatu ta fara xancen ta kan Aneesah a kasa
yake tana kukan xuci, har shatu ta sallameta
tace maxa taje yana jiranta, ta fita jikinta a
sanyaye ashe har ya fita kofar gida yana jiranta,
tana karaso wa kuwa ya washe hakora yana
murmushi yace "yauwa 'yan mata sannu da
fitowa," ita dae bata ce kmai ba ta tsaya kanta a
kasa, yace "to mu shiga cikin mota muyi hiran
mana amaryata," ta dago cike da tsana tana
kallonsa tace "A'a nn ma ya isa," yace "haba
amaryata ae yawa ne a gan mu tsaye kmr yara a
nn, ke dae shiga kawae,"ya bude motar yana
kallonta, Aneesah tayi murmushin takaice tace
"ni fa baxan shiga wnn motar ba malam," ya
tsaya kallonta na kusan minti biyar snn ya bude
motarsa ya shige ya ja ta yyi gaba, ta tabe baki
a xuciyarta tace Alhmdllh ta shiga gida abinta,
shatu na tsaye a bukkarta sae kai komo take ta
kasa xaune ta kasa tsaye, Aneesah na shigowa
ta riko hannayenta da sauri har wani bari jikinta
yake tace "har ya tafi, nawa ya baki," Aneesah ta
dan koma baya tace "wae fa mama sae na shiga
motar da kila ko fitila ma bbu, ni ko nace masa
baxan shiga ba shine ya wuce," shatu ta xaro
kwala kwalan idonta ta daura hannu a ka ta
kwala ihu tace "shiknn ta ja mana, Na shiga uku
ni shatu don ubanki koransa kika yi sbda kin
isa?? Na banu na lalace," Aneesah ta tsorata
sosae da yanayin da shatu ta shiga, ta dinga
komawa baya, cikin tsawa shatu tace "xo nn don
ubanki shegiya mugu,"
[12/8, 21:11] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 54..... Aneesah ta fasa ihu ta durkushe wajen ganin shatu ta yo kanta, duka kam ta sha shi ranar don shatu komawa tayi kmr wata mahaukaciya, daga karshe ta saba gyale wae xata bi sa gida ta ba shi hkuri duk a rude take, Aneesah dae na durkushe tsakar dakin tana kuka, har shatu ta fita ta dawo kmr an hankadota cikin fushi tace "kuma maxa ki dauki bokitin gyadata ki koma dandali ki tabbatar kin sayar min gaba daya idan ko ba hka ba kar ki kuskura ki dawo min gida, shegiya kawae mugu 'yar bakin ciki," tana kai wa nn ta fice. Aneesah ta kife kanta a kasa tana kuka mai ban tausayi Amminta kawae take tunawa, da kyar ta lallaba ta mike ta dauki bokitin gyadar ta fita daga gidan, a hanya suka hadu da mudatheer ya kirata da kmr baxa ta je ba, har tayi gaba ta dawo, yace "shatu ta doke ki knn," tayi shiru bata ce komai ba tana goge hawayen fuskarta, ya nuna mata benchi ta xauna, bata yi musu ba ta xauna, yace "dandali xaki" ta gyada masa kai, yace "meyasa tun tuni baki je ba sae ynxu, gashi har kusan ten, ae an kusa tashi ma," bata ce masa kmai ba, yyi murmushi yace "me kika yi ta doke ki?" xata yi magana ta fashe da kuka, yyi shiru yana kallonta har tayi mai isar ta, snn ya sake tambayarta me tayi, ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya masa, yyi dariya xae yi magana, ta mike a fusace xata bar wajen ya riko hannunta da sauri yace "Haba 'yar birni ni malam tanko ne ya ban dariya," tayi tsaki ta dawo ta xauna, yace "to wae baki gaya min hadinki da su shatu ba har ynxu" tayi shiru, yace "yau ma baxa ki gaya min ba knn" tace "sbda me kke son sani?" yace "i just want 2 knw a bit about yhu, kinga i may b leavin in 3dayz tym" ta wara ido tace "wucewa xaka yi?" yace "yes, na gama abinda ya kawo ni," Aneesah tayi shiru duk sai ta ji ba ddi, xata yi magana sae ga Zano da kawayenta sun dawo daga dandali, tana ganinta ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "na shiga uku mudatheer xata gaya ma mama, kuma ban ma gama saida gyadar ba, ya ce nawa ne gaba daya, tace "dari uku ne ina ga," ya ciro dari biyar ya mika mata tace "aa ni ka rike kudin ka kawae," ya harareta yace "xaki koma ki kara shan wani dukan kuwa," ta karba tana kallonsa, tace "to gyadar fa?" ya ce "ki koma gida da shi, sae kice su garba ne suka baki kudin xata ji ddi tunda mayyar kudi ce," Aneesah tace "to bbu canji," yace "eh ki kai mata hka," tayi masa gdya ta mike jikinta a sanyaye ta kama hanyar gida, tana tunanin shawarar da karime ta bata ranan bayan ta bata lbrinta tun daga farko har ixuwa ranar da baffa ya kawota kauyen, karime tace ta gudu kawae amma ta kasa gudu wa daga kauyen kuma ta rasa dalili, kwata kwata bata sha'awar barin kauyen ita kam ta rasa meyasa, don wani lkcn ko tunanin gida bata son yi, a hka ta isa gida gabanta na faduwa a xuciyarta tana cewa "Allah yasa Zano bata gaya ma shatu ta gan ta da mudatheer ba, amma sae ta samu ma bata karaso gida ba, shatu na ganin dari biyar ta rikice ta dinga sa ma Aneesah Albarka ba tare da damu da inda ta samo ba ma. Washegarin ranar sae ga malam tanko ya xo da daddare, shatu ta lallabata ta fita, bata yi masa musu ba ta shiga rubabbiyar motar tasa, sae washe hakora yake yace "amaryata muje gun sule mai suya in dan siya maki nama," ta girgixa kai tace "bana ci," yyi dariya snn yace "to muje in xaga dake kauyen ko ya kika ga," gabanta ya dinga faduwa ga tsoran shatu, ba tare da ta sake wani tunani ba tace "toh," yyi murmushi yace "yauwa Amaryata, snn ya tada motar, ya ja ta," shatu na leke ta katanga, tana ganin hka ta sauke ajiyar xuciya ta daga hannu sama tace Alhmdllh bata tona min asiri ba, 'yar albarka.
[12/8, 21:11] ‪+234 803 751 8717‬: Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 55..... Aneesah dae bata tanka ma malam tanko dake ta sharara mata surutu a motar ba, hasalima kauda kanta tayi tana kallon glass din motar, ita duk kyankyamin motar ma ta isheta, yace "Haba amaryata ya hka ina ta magana kin min shiru," nn ma bata tanka sa ba, har suka isa gun sule mai nama, ya siya naman dari da hamsin ya bi ta shagon lado ya siya pure water leda biyu snn ya dawo ya shiga motar rike da naman da ruwan ya mika ma Aneesah yana washe rubabbun hakoransa, tayi kmr bata san yana mika mata ba, ya ajiye gefenta yace "sannu amaryata," ko kallnsa bata yi ba har ya ja motar suka bar wajen, taga yyi parkin wajajen gonannakin mutane, ko ina duhu sae dan hasken wata, ya kamo hannunta yace "amaryata ci nama," ta fixge hannunta gabanta na faduwa tace "meye hka?" ya dan hade rae yace "nama nace kici," a fusace tace "ban ci, ka ci kayanka nace mka yunwa nke ji ne" tana fadin hka ya fixge dan mayafin dake kanta yace "ke kar fa ki kawo min raini, kin san ko ni wanene," ta fara kkrin bude motar xata fita ya fixgota yace "ina xaki," ta hankadesa da sauri tace "to motar ta ubana ne da baxan fita ba," yace "ae baki isa ba yarinya sae kin biya min bukatata yau, cikin kwanaki uku na kashe maku fiye da dubu daya, hakosu nace ina yi a rami" ta yo waje da ido a tsorace ta fara kkrin bude motar ya rikota yana kkrin yaga rigar jikinta tace "nashiga uku, meye hka, malam ka rabu dani ni ba 'yar iska bace," yace "ae nima din ba dan iskan bne, kudina da kuka ci xan amsa ta nn," bae ko damu da haukan da take yi ba ya matse ta yana kiciniyar cire mata kayan jikinta, ta fasa ihu, amma bbu mai jinta dan gurin kmr daji yake, ta wanka masa wani lafiyayyan mari tare da basa wani naushi a ido da karfinta, ba shiri ya saketa bayan ya saki 'yar karar axaba, hannunta na rawa ta shiga bude motar ya budu xata fita ya fixgota ta yakushi fuskarsa ta fice a guje, ko dankwali bbu a kanta, gudu kawae take a tsorace tana bin hanyoyin da ta san xae sada ta da gida, garbebe da lado ta hadu da a wani corner suna ta tuntsirar dariya suna lbrin irin bata wata yarinya hajjo da suka yi jiya da daddare, tana ganinsu ta juya da sauri ta canxa hanya, ji tayi lado na cewa kae garu ga 'yar birnin nn ita ce, suka ko bita a guje, ita ma gudun take kmr xata tashi sama, cikin ciyawa ta labe jikinta na rawa har suka wuce ta da gudu, gabanta ya dinga faduwa ga tsoran kar maciji ya sareta a wajen, ta kai kusan minti goma a cikin ciyawar gudun kar ta yi gaba su hadu kuma, daga karshe wata hanyar ta canxa kuma, ta dinga gudu tana waige waige tana kuka kide kide ta dinga ji daga nesa alamar ta kusa dandali, ta tuna mudatheer yace ta xo dandali xae nuna mata abu, bata bi ta dandalin ma ba don bata san ko sun yi can ba ta sake canxa hanya tana dan tafiya da sauri da sauri tana waige waige, ji tayi ta ci karo da wani katon dutse ta fasa ihu tayi kasa xata fadi taji an yi saurin rikota su ka fadi a tare duk da bata wani buge ba dan kan wanda ya kamota ta fada sae da ta fashe da kuka, taga ya ciro wayarsa da sauri yana kkrin haska fuskarta yace "Goddam Yhu baki kalln gabanki ne kina..." yana haska fuskarta da wayarsa taji ya dan koma baya da sauri yyi tsit, ita ma shirun tayi tana ta kallon fuskar dake gaban screen din wayar, ganin ya ki daina haska ta ne yasa ta fixge wayar daga hannunsa ta shiga haska fuskarsa ita ma, wani kyakkyawan handsome guy idonta yyi tozali da, ta tsura ma manyan fararen idanunsa nata idon, ta saukar da kallonta kan pink lips dinsa dake ta kyalli, wayyo ya Haydar dinta exactly, fixge wayar yyi daga hannunta ita ma, ya tura ta ya mike tsaye yace "kina tafiya kmr wata mara saiti dubi yanda kika min da jikina," bata ce komae ba ta fara tafiya a sanyaye ya fixgota yace "cnt yhu thank me, da na barki da kin fasa kai yarinya," ta fixge hannunta ya sake fixgota ya ja ta suka xauna kan dakalin da yake a xaune, yace "amma fa ke kyakkyawa ce, wait ko ma dae kece mudatheer yace na xo na gani a wancan gurin haukan naku?" ya fadi hkn yana nuna mata dandali, tace "lah kasan Mudatheer ne?" ya gyada mata kai yace "yea sch son dina ne muna sec sch, nn yake service ae, amma gobe xai gama shine yace na xo naga yanda kauye yake tunda ina garin," ke kuma naga baki yi kalan 'yan kauye ba, hw come kike kauye, ko dae hutu kika xo kema, ya sunanki, me ma yake sa ki gudu da daren nn, baki tsoro baki dauki fitila ba Aneesah tace "kai wnn irin tambaya hka sae kace dan jarida," yyi dariya da ya bayyana dimples dinsa, ta tsura masa ido tana kallo, Haydar kawae take tuna wa, ya daura hannu a kanta ya wara idonsa yace "ya dae" ta buge masa hannu tace "meye hka," yace "ohh sowie bby," ta tabe baki a xuciyarta tace "wnn dae dan iska ne dama yyi kama da su," ta mike xata bar wajen ya fixgota har tana faduwa kansa yace "ke baki gaya min sunanki ba," tace "A'a meye haka malam," yace "sae kin gaya min sunanki xaki bar nn," d[truncated by WhatsApp]
[12/8, 21:11] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
57.....
Kamar daga sama Aneesah taji abu ya buge ta da karfi, daga nn
kuma bata sake sanin abinda ya faru ba, karime da su xulai suka
fasa ihu ganin abinda ya faru suna cewa "wayyo shiknn ya kashe
mana Aneesar mu," mai motar ya fito daga motar da sauri yace
"subhanallahi," ya durkushe gabanta ya dago ta, su karime duk
suka xagaye shi suna koke koken Aneesah ta mutu, ya tura xulai
dake daf da kansa tana rusa ihu a fusace yace "ke da'alla ja can
uban wa yace maki ta mutu," xulai ta koma baya da sauri tana
yarfe hannu tace "wayyo ashe bata mutu ba karime," daukar
Aneesah yyi ya saka cikin motar ya dawo xae shiga driver sit,
karime ta bisa da gudu xulai da yayarta Xano na biye da ita a
baya, karime ta rike motar tace "kai ina xaka kai mana 'yar
uwarmu?" xulai ta fara kkrin bude motar a rude wae xata ciro
Aneesah, ita kuma xano ta yi kauye da gudu neman taimako wae
wani xae sace Aneesah a motarsa, shi ko ya fixge xulai daga jikin
motarsa ya jefar snn ya bude motar ya shige, suka dinga ihu suna
bubbuga motar da karfi, bae ko damu da hka ba ya tada motarsa
ya ja ta ya bar wajen a fusace kuma da gudu don har yana neman
buge karime. Shatu ta saki salati ta fito kofar gida a guje bayan
lbrin abinda ya faru ya risketa tana cewa "wayyo shknn na shiga
uku ni indo, ku ka ce me? Ya tafi da ita ina?" xulai dake ta rusa
kuka tace "a motarsa ya tafi da ita," nn da nn lbri ya baxu kauyen
wani mai mota ya kade Aneesah ya tafi da ita kuma a motarsa,
mutane suka dinga fiffitowa da daddaya da daddaya aka taru
kofar gidan shatu da ta xama kmr mahaukaciya wae an sace
mata 'ya kuka har da majina faca faca, karime da mamarta ma na
tsaye wajen ana ta jajanta abun sae kuka karime take yi, xano ta
raka samarin kauyen xuwa gun da abun ya faru aka bi bayan
motar amma aka rasa inda mota tayi, sae kusan maghrib kowa
ya watse ya koma gidansa, aka bar shatu da 'ya yanta suna ta
kuka, banda Xano da tace "to wae shatu sae kace uwarki ta bata
ko 'yar da kika haifa a cikinki, tunda ba a ganta ba ba shiknn ba"
tayi tsaki ta jawo kayan kwalliyanta xata yi shirin dandali, shatu ta
sharbe majina tace "don ubanki da kin san abunda muka rasa
ynxu da baxa ki ce komai ba," Malam mati ya shigo gidan da
buhu a hannunsa, rabon sa da gidan yau kwana biyar knn don
bae cika xama kauyen ba, yana shiga Bukkar shatu yace "ke shatu
me nake ji a gari wae yarinyar nn mae mota ya gudu da ita, ina
ya kai ta, kin manta jan kunnen da Alhaji ya mana, masifa kike son
ja mana" shatu tace "to ba aikensu nayi ba malam," yace "to shi
mai motan daga ina yake kuma ina xa sa?" xulai tace "bakaken
kaya ya saka gaba daya har takalmi da tabarau, kuma mu bamu
san inda xa shi ba" Xano tace "kila ma dan yankan kai ne," shatu
tace " lah! kuma fa wllh hka ne ya motar tasa yake?" xulai tace
"katuwa ce motar ita ma bakakirin kmr kayan jikinsa," malam yace
"shknn ae barka ma da ya tsaya a kanta," xano tace "shi dae na
gani malam amma tun tuni shatu ta bi ta cika ma mutane kunne
da kuka da sharban majina, sae kace uwarta aka sace," shatu ta
sauke ajiyar xuciya tace "to idan shehu ya xo kauyen nn me xamu
ce masa malam," mati yyi mata kalln bnxa yace "ba sae mu ce
mun aurar da ita, a can wani kauye ba, kuma ba na ce maki ko
sati biyu ba ayi ba da ya kira ni ta wayar Buba ba, yace idan ta
addabemu mu kasheta kawai mu huta da jaraba, da na kawo
maki xancen ba ca kika yi aa ba kina da babban shiri a kanta,"
shatu tace "hka ne malam to tanko fa, ynxu shknn munyi hasara
knn?" yace "to ya xa ayi, ni dae daga yau bna sn na sake jin
batun yarinyar nn a gidan nn, tunda ta bata ta bata, idan shehu ya
xo iya ka nace masa ma an kasheta kawae," shatu ta mike tsaye
tana gyara tsumman xaninta tace "to shknn, amma ni dae ba hka
na so ba wllh, ga shi ynxu shknn mun rasa tanko, tunda dae bae
ce yana son su xulai ba," A hankali Aneesah ta bude idonta ta
tsura ma agogon dake manne a bangon dakin da take, karfe sha
daya ta gani, ta shiga bin dakin da kallo kmr mai son tunano abu
bbu tantama ta gane asibiti take, ta mike xaune a hankali tana
kallon hannunta dake manne da alluran drip, taji an bude kofa, ta
daga kanta da sauri tana kallon mai shigowa, ya tsakar mata
murmushinsa mai kyau ya karaso gefenta ya xauna yace "bby kin
tashi," kallonsa kawae take yi da mamaki, ya daura hannu kan
goshinta ta cire hannun a hankali tace "ka mayar da ni gidanmu,"
ya harareta yace "kina under treatment xan mayar dake gidan
naku?" tayi kmr xata yi kuka tace "xa ayi ta nemana fa don Allah
ka mai da ni gida, ina mudatheer?" yace "oho! kuma naki mayar
dake gidan karfe sha dayan daren xan mai dake gida," tayi shiru
tana kallon agogo, yace "ynxu dae me xaki ci," ta daure fuska tace
"ba komai," yace "gud, bari na kira maki Dr," yana fadin hka ya
fice daga ward din ta bisa da kallo.
2 mins · Khaleesat Haiydar...
[12/8, 21:11] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 56..... Ya wara dara daran idonsa yace "waw sweet name Aneesah," Aneesah tace "to ka sake ni ai na gaya maka sunan nawa," ya xaunar da ita yace "No Aneesah tsaya mu dan yi hira, don Allah" xata yi magana ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta yace "shhiii," tayi shiru tana kallonsa yyi murmushi yace "kina da kyau Aneesah," ta kauda kanta nn ma bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "hu2 kika xo yi nn Bby?" ta fixge hannunta tace "wae meye hka kke taba ni ne na sanka ne," ya kashe mata ido yana lasan lebensa yace "ni sunana Mujaheed Yusuf," tace "to naji," amma ka bar ni na koma gida, ya harareta yace "not until u tel me y u were running," ta dan marairaice fuska tace "wllh wasu mutane ne ke bi na," ya mike da sauri yace "su wa? A ina suke, me kika yi masu, xo ki nuna min inda suke," yana fadin hka xae fara tafiya ta riko hannunsa tana dariya tace "to me xaka masu?" yyi mata wani irin kallo yace "nuna min su kawae ki ga abinda xan masu," tana dariya tace "ae bn san inda suka bi ba," ya dawo ya xauna yace "da sun biyo ki har nn wllh da na cire masu hakoran bakunansu gaba daya," Aneesah tace "uhmm naga alama" Nan Mujaheed ya dinga mata surutu kmr da can sun taba sanin juna, ita ko ta biye masa sae dariya take yi, ana fara fitowa daga dandali ta mike da sauri tace "kaga ni xan wuce gida kar yayyina su gan ni a nn," xae yi magana ta hangosu xulai ta juya da sauri ta fara gudu ta bar wajen, yace "shit ban san wacece ita ba," mudatheer ne ya karaso gurin yana kallon Mujaheed yace "kana nn har ynxu ashe big bro, da ka shigo da ka ji ddi, amma sae dae 'yar birnin bata xo ba yau" Mujaheed ya dan daga kafada yace "na ganta, ko ba Aneesah ba," mudatheer yace "waw ita fa, a ina ka ganta?" Mujaheed yace "she's such a beauty, ynxun nn ta bar nn wae kar yayyinta su ganta, da gske nn aka haifeta" Mudatheer yyi dariya yace "A'a ko wata uku bata cika ba a nn," Mujaheed yace "ni kam na xo kauye a sa'a don na samu mata, kaga xuwa nan ya kamani duk sati knn" Mudatheer yyi dariya ssae yace "gskya ne, ka ga ni xan tafi kai kuma ynxu kke xuwa, amma fa sae dae gidan da take a nn ba gidan mutunci bne don mutanen gidan kowa ya san su da halinsu a kauyen nn," Mujaheed yyi tsaki yace "dont tel me dat, ina ruwana da halinsu, as far as ba su suka haifeta ba its none of my bzz," mudatheer yyi dariya suka bar wajen yana cewa "kaga ina ta damunka kaxo kauye kana ja min aji ashe alkhairi xaka xo ka tarar a nn," mujaheed yace "yaushe xaka tafi," "gobe da safe," mudatheer ya ba shi amsa, Mujaheed yace "xan samu ganinta da safe kafin mu tafi don Abuja nake son wucewa direct," Mudatheer yace "yes of course amma idan kaje rafi," Mujaheed yace "ehh sae naje to meye a ciki?" Mudatheer yace "to xaka kwana nn ne ko fita xaka yi," Mujaheed yace muje motata ma tana nan ae, ba karamin tashin Hankali Aneesah ta tarar a gidan ranan ba daga shatu don kasheta ne kadae bata yi ba, kuma wae washegarin ranar a gun tanko xata kwana ko taki ko ta so tunda dae shi xae aureta wae, kuka kam ta yi shi har kusan asuba, Da safe ta je debo ruwa a rafi duk jikinta a mace ga yawan faduwar gaban da take yi ta hadu da su Mudatheer suna jiranta karkashin wata bishiya, tayi mamakin ganinsu a tare amma tayi kmr bata gansu ba tayi gaba mudatheer ya kirata da sauri taki juyowa, ya mike ya bi ta yana cewa "Aneesah yau fa xan tafi shine kike min wlknci?" ta juyo da sauri tace "da gske?" yace "ehh," ta ce "to baxa ka sake dawowa ba," ya juya yana kallon Mujaheed da ya kasa daina kallonta yace "yayana xae dinga kawo maki visit ae," ta kalli Mujaheed ya kashe mata ido, ta galla masa harara tace "bana son visit din," Mudatheer yyi dariya yace "yayana ne fa," bata tanka sa ba tayi gaba duk jikinta a sanyaye ynxu Mudatheer wuce wa xae yi ya bar ta, da rana Mudatheer ya bar kauyen duk da ya so ganin Aneesah amma bae samu ganinta ba, Mujaheed ya kai sa har tashan da xae hau mota a motarsa shi da ya kamata daga can ya kama Hanyar Abuja yace ina ae sae ya dawo yyi sallama da Aneesah. Aneesah dasu xulai da karime na dawowa daga kauyen dake kusa

Please Login or Register in order to submit comment