Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya
xaga ya shiga motar ta karasa daya bangaren
jikinta a sanyaye ta bude ta shiga, Allah sarki
yayanta da shi ne da da kansa xae bude mata
motar, har suka bar anguwar Hydar bae ce mata
komai ba, Mujaheed ya dinga kiranta a waya ta
kasa dagawa, daga karshe ma sae ta kashe
wayar gaba daya. Suna isa cafen ta bi bayan
Hydar suka shiga ciki, ita dae ta ga yanda xa ayi
ya duba result dinta tunda dae bata da
informations dinta a tare da ita ynxu, amma ga
mamakinta, taga yyi komai bayan ya siya scratch
card, snn yasa aka yi print out din result din, sae
a lkcn ta lura da takardar dake hannunsa da ya
taba karba da ddewa bayan sun gama exams,
nmbers ne a jikin takardar da ya sa ta rubuta
masa, tun daga na exam, xuwa na exam centre
da sauransu. Ya bada kudi suka fita daga cafen,
yana rike da result dinta, sae da suka shiga mota
snn ya mika mata result din ta karba amma ta
kasa budewa, shi dae bae ce mata komai ba har
suka isa gida snn yace "gobe xamu je kiyi
register na jamb," ta gyada masa kai yace "sae
anjima," bata yi masa musu ba ta bude motar ta
fita a sanyaye tace "ngd," bae ce komai ba ya ja
motarsa yyi gaba. Wa shegari Mujaheed da Abdul
suka samu shiga gidan Alhaji sulaiman, ya tarbe
su da kyau ganin Abdul dan Honourable shehu,
da Abdul ya lura da cewa Alhajin bae san abinda
ya faru da dad dinsa ba yasa yace "dad ne yace
ya kawo maka wata mata tana maku aiki nn da
ddewa," Alhaji sulaiman yace "ehh hka ne, har
ynxu tana nn gidan kuwa," Abdul ya juya yana
kallon Mujaheed da ya ji ddin jin hkn yace "eh
dama ca yyi mu xo mu taho da ita ne," Alhaji
suleman yace "ohh har ya shawo kan komai knn
ynxu?" Abdul yace "eh" ba tare da ya gane mai
Alhajin yake nufi ba. Alhajin yace "to shknn
amma ae ya ci ace ya kirani ya fara sanar min
da xuwanku, ga shi duk kwanan nn bna samun
layinkansa" Abdul yace "ehh ya dan fita waje ne,
ynxu hka ma yana can kila gobe xae dawo gida,"
Alhaji suleman yace "to shknn," kmr yaushe xa
ku tafi da matar? Abdul ya juya yana kallon
Mujaheed da ya dan masa sign alamar yace yau,
yace "aa ynxu xa mu koma tun shekaranjiya
muke garin nn, aka ce baka nn, kuma sae kana
nn ake shigowa gidan," ya gyada kai cikin
gamsuwa yace "shknn bari na kira su hajiya na
sanar masu," ya ciro waya ya kira matan nasa da
daddaya da daddaya suka su dinga shigowa
falon, ya sanar da su abinda ke tafe da su Abdul,
1st wife din tace "to amma ai da Hajiya zuwaira
xata kira ni tayi min magana in hka ne," Abdul
yace "dad bae ma sanar mata ba," 2nd wife din
tace "to ynxu ta ina xa a fara neman wata mai
aikin, gashi muna jin ddin aikinta a gidan nn," last
wife din tace "to ai akwae masu aiki dayawa a
gidan naga," 1st wife din ta watsa mata harara
tace "amma ai duk ta fi su kwarewa," last wife
din ta tabe baki tace "sae yau ku ka san da hka
knn, duk da da kuke walakantata baku san tana
aiki ba sae yau da ake shirin tafiya da ita ," Abdul
ya mike hka ma Mujaheed kamr sun hada baki,
yana kallon Alhajin yace "dad, xamu koma lkci na
kurewa tana ina ne," yyi hakan ne don baya son
asirinsu ya tonu su yi saurin barin katsina don
matan na iya kiran mum dinsa. Alhajin ya kalli
matan nasa, da yake shima dan duniya ne cikin
tsawa ya ce "ku kira min ita mana kun min hake
hake a falo kmr an dasa ku," suka mike kowa na
fadin abinda ke xuciyarsa suka bar falon.
[12/8, 21:12] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 97..... Hajiya salamatu matar Alhajin ta uku ta shigo falon Ammi na biye da ita a baya, tace "ga ta nn Alhaji," Ammi ta ja tunga daga bakin kofa ta tsaya kallon Abdul da mamaki, shi din ma kallonta yake, Alhaji suleman yana kallon Abdul yace "gata nn, kace ma Shehu ina expectn kiransa, shi hka ake yi" Abdul yace "ok xan gaya masa dad" Abdul ya kalle Mujaheed da ya kasa daina kallon Ammi don mugun kamar da suke da Aneesah kamr an tsaga kara, baka taba cewa ita ta haifi Aneesah don she look 2 young a ido, Abdul yace "mu tafi," Ammi ta dake ta hade rae tana kallonsa tace "mu tafi ina," Abdul ya kauda kansa yana dan murmushi ya juya yana kallon Mujaheed, Mujaheed ya dan fara kame kame kar Alhaji suleman ya gano su, yace "em, dama mumy, Aneesah ce bata da lafiya shine baffa yace mu xo mu taho da ke," nn da nn tashin hankali ya bayyana a fuskarta a sanyaye tace "Aneesah, me ya sameta, ita din ma kashe min ita xae yi ne," tana kai wa nn ta fara hawaye, Abdul yace "ke take son gani shi yasa aka ce mu xo mu taho da ke," yana fadin hka yyi gaba Mujaheed ya bi bayansa, Ammi ta bi bayansu har lkcn tana hawaye tana tunanin halin da 'yar ta ta ke ciki, kullum da Aneesah take kwana take tashi a ranta, barin in ta tuna bata gama mallakan hankalin kanta ba, kuma bata nuna mata abubuwa da dama na rayuwa ba. Tunda Ammi ta shigo gidan ranar ce rana ta farko da ta fito, har ta manta yanda anguwar yake ma, Mujaheed ya bude mata bayan mota, xata shiga taji an kirata da Anty, ta juya sanin me kiran nata, Faruuq ne dan Alhaji suleman din, shima baxae wuce su Abdul din ba, ya karaso yana kallonta yace "ina xaki Anty, su waye wnn," tayi murmushi tace "xan koma can Abuja ne faruuq," yace "me kuma xaki je yi a can Anty, ba gwara ki wuce gombe ba," tace "A'a Aneesah ce bata da lafiya wae," yace "ya salam, me ya sameta, tun yaushe take rashin lafiyar, ix it dat critical," Mujaheed yyi masa wani mugun kallo yace "kana bata mana lkci malam," ya juya yana kallon Mujaheed din yace "fuck yhu, nayi da kai ne" Ammi tace "kar ka damu faruuq sae naje na gani, nima ban sani ba," yace "to bari na bi ku Anty sae na dubata, quack doctors sunyi yawa a Abuja ynxu" a fusace Abdul yace "ah'ah!! Da'alla get out malam kana bata mana lkci, kai kama san hanyar Abujan ne" Ammi tace "kasan halin hajiyarka Faruuq kawae kar ka damu kayi xamanka kai da xaka koma aiki gobe," ya ciro wayarsa daya, ya mika mata yace "to shkkn Anty, ga waya ma dinga gaisawa kafin na shigo Abujan, don ina ga na daga tafiyar tawa, ki gaida min da Aneesar ssae, xanyi missn dinki mum " ta karbi wayar tai masa gdya da fara'arta, snn ta shiga motar, Abdul ya ja motar kmr mai shirin buge faruuq din, suka bar anguwar, Ammi tana kallonsa tace "ka kai ni tasha kawae na hau mota," Mujaheed yace "A'a momy ki bari mu tafi kawae," kiri kiri Ammi taki yarda ta bi su tace su kaita ta hau motar haya kawae, Mujaheed ya kalli Abdul yace "muje park kawae," Abdul bae yi musu ba suka tafi gun shiga mota, suka biya mata ticket, suka tsaya har motar ta tashi, snn suma suka shiga motarsu su ka kama hanya. Karfe shidda na yamma suka shigo Abuja, daga park din ma bbu yanda ba su yi da ita ta shiga mota su kai ta gida ba ta ki, duk da a lkcn basu ma san inda xa su kai ta ba, Ammi na kallon Mujaheed da yafi takura mata a kan ta shiga su kai ta gidan tace "kar ka damu samari, gida xan wuce daga nn, xuwa Anjima sae naje gidan baffan." hkn yasa suka bar ta ta hau tricycle, ta wuce gida, su kuma suka shiga cikin gari, Mujaheed yana kallon Abdul yace "ina xan ajiye ka guy" Abdul yyi masa mugun kallo yace "hw dare yhu? dat's nt our deal, ina Aneesar da kace xaka nuna min," Mujaheed ya dan yi shiru snn yace "ae sae ka bari mu fara hutawa ko yallabai" tare suka isa gidansu Mujaheed da Abdul din, a falo suka tar da Hajiya da autarta Amira, Amira ta rungume yayanta tayi masa oyoyo snn ta gaida Abdul dake kare ma gidan kallo kmr sabon shiga gun ganin hadadden gida, ya kalleta ya gyada mata kai kawae, snn ya gaishe da Hajiyar ta amsa da fara'arta, Amira tace yaya dady ya dawo fa, Mujaheed yace "da gske?" tace "Allah amma a lagos ya sauka gobe xo iso nn," Mujaheed ya kalli Abdul yace "mu tafi sama," Bae yi musu ba ya bi bayan Mujaheed din suka haura sama.
[12/8, 21:12] ‪+234 803 751 8717‬: Khaleesat Haiydar
~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 99.....
Mujaheed yyi shiru yana kallon Abdul, Abdul yace
"yes, ae ba xuwan kanka xa kayi ba, rakani xaka
yi," Mujaheed yyi murmushi ya ciro wayarsa, yyi
dailn nmbr Hydar, ya shiga kiransa, tun bayan
abinda ya faru tsakaninsu har yau basu yi
cmmncate ba, har ya fidda ran Hydar xae daga
ya ga ya daga, ba tare da bata lkci ba yace
"dama na kiraka na gaya maka ne, mum din
Aneesah na gida ynxu, ko xaka je ka dauketa
daga inda take ka kai ta gida," Abdul ya fixge
wayar daga hannun Mujaheed din ya katse kiran
yace "ni ka bani Address din gidan naje na
dauketa na kai ta gida, kila hkn xae sa ta daina
min abinda take min, ta dinga ganin mutunci na,"
Mujaheed ya tsaya kallonsa yana doubt dinsa a
xuciya, can dae yace bari kawae muje, xan ma
mum bayani nasan xata yafe min, ko minti biyar
ba ayi ba Hydar ya kira Mujaheed, mujaheed ya
daga hydar yace "ban gane xancenka ba,"
Mujaheed yace "no barshi ma kawae," yana
gama fadin hka ya katse kiran, suna isa gidansu
Mudatheer, Mujaheed ya kirasa yace "ga su nn a
kofar gida Mudatheer yace su shiga daga ciki
don shi baya gida, Mujaheed bae lura da motar
Hydar dake parke a waje ba ya shiga gidan,
Hydar dake xaune kan kujera karkashen wata 'yar
bishiya yana jiran Aneesah don shima shigowarsa
knn gidan ya bi su da kallon mamaki, su kam
basu lura da shi ba ma, Aneesah da tunda mai
gadi yace ana nemanta taji gabanta na faduwa
don tasan Hydar ne ita kuma tsoransa take ji
ynxu ta fito a sanyaye bayan ta nemi ixini gun
Momy, tana fitowa daga falo suka yi ido huda da
Mujaheed a tsakar compound yana taho wa,
Abdul kuma na bayansa, ko lura da Abdul din ma
bata yi ba, ta yo waje da ido cikin wani mugun
farin ciki tace "yayana," Mujaheed ya wara mata
ido shima da farin cikin yace "kanwata," ta taho
da gudu, ya buda hannunsa ta fada jikinsa ta
kankamesa, ya daura bakinsa kan goshinta, kmr
xata yi kuka tace "yayana, ina ka tafi ka barni,"
cikin rada yace mata "abubuwa ne suka min
yawa kanwata," sae a lkcn ta lura da Abdul ya
dan koma baya a tsorace tana kallonsa, ta kauda
kanta da sauri tana shirin barin wajen gabanta na
faduwa, cak komai na ta ya tsaya ta dalilin ido
hudun da suka yi da Hydar, tuni jikinta ya dau
rawa, ta fixge hannunta daga rikon da Mujaheed
yyi Mata da karfi ta sulale kasa wajen jin kafarta
ya kasa daukarta, Mujaheed ya durkushe gabanta
da mamaki yace "me ya faru kanwata," ta fashe
da wani matsanancin kuka tana kallon Hydar da
ya mike da kyar daga kan kujerar da yake, yyi
hanyar fita daga gidan, Mujaheed ya bi sa da
kallon mamaki shima, Aneesah ta mike tsaye da
sauri ta bi bayan Hydar din, Mujaheed ya bi ta da
kallo xuciyarsa na tafarfasa, har hydar ya bude
motarsa xae shiga Aneesah ta karaso kusa da
shi ta durkushe gabansa tana kuka ssae tace
"wayyoo ya Hydar wllh ban san....." mari mai rai
da lfya ya watsa mata snn ya fincikota ya jefar
da ita daga gabansa ya shige motarsa ya wuce,
kallon kallo Mujaheed da Abdul suka shiga yi a
tsakar gidan, a nutse Abdul ya karaso kusa da
shi yana masa wani irin kallon yace "dama son
Aneesah kke, kake amfani da ni wajen cimma
burinka," to bari kaji na gaya maka, baka isa ka
aure Aneesah ba, Aneesah tawa ce ba ta kowa
ba, Abdul na fadin hka ya juya xae fita daga
gidan Mujaheed ya riko hannunsa yace "ka cire
Aneesah a ranka, she ix mine" yana fadin hka ya
cika sa yyi hanyar fita daga gidan shima.
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
98.....
Hydar ya juya yana kallon Aneesah bayan ya gama parkin a kofar gidansu Mudatheer, karo na farko yyi mata magana yana kallonta don tun da suka fita xuwa cafe yin registration din jamb a duk inda ya kama sae yyi mata magana baya kallon fuskarta yake maganar, ynxu kam kallonta yake ganin bata ma lura da sun iso gida ba, ko tunanin me take oho, tayi saurin sunkuyar da kanta da ta lura da kallonta yake, a nutse yace "me ke damun ki?" ta dago tana kallonsa hawaye cike a idonta, yyi mugun hade rae yace "ni bance ki min kuka ba, i only asked u a questn" tayi saurin goge idonta da tafin hannunta, yana kallonta a hankali yace "me ke damunki Aneesah," tayi shiru, shi ma hka, bayan kmr minti biyar yace "to fita, sae anjima," ta dago kai da sauri tana kallonsa a sanyaye tace "kayi hakuri," ya tsura mata ido snn yace "to me ya faru?" ta goge hawayen idonta tace "ni ban san me nayi maka ba ya Hydar...." sae kawae ta fashe da kuka, ya kauda kansa da sauri, ya bar ta tayi mai isarta snn yace "ki shiga gida dare yyi," bata yi masa musu ba ta bude motar har lkcn hawaye yaki tsaya mata tace "ngd" ya bi ta da kallo snn ya dafe kansa cike da takaici, haushi Aneesah take basa bae san meyasa ba, ganin xae tada xaxxabinsa ne ya sa ya ja motar ya bar anguwar. Duk jikin Aneesah a mace yake ranar, kawae ji tayi tana mugun son ganin Amminta hka kawae, duk da irin kular da momynsu mudatheer da dad dinsu ke mata, ta kasa bacci cikin dare tunanin Amminta ya isheta, to wae ina Amminta, ina ta shiga ta bar ta, meyasa ta kwantar da hankalinta 4 ol dis while ba Amminta, kuka kam ta yi shi har ta gaji ranar da daddare. Abdul kam a gidansu Mujaheed ya tare bayan dawowarsu daga katsina, don ko awa daya basu yi da isa gida ba Hajiyarsa ta kirasa kmr xata yi hauka bayan ta samu lbrn yaje ya dauko Ammi, daga matan Alhaji suleman, daga karshe bae bari ta kai aya ba yace mata, "2 hell wif yhu," ya kashe wayarsa ma gaba daya, Mujaheed yace "ya dae, kae da wa," yace "mumcy na ta samu lbrin na dauko mum din Aneesah," Mujaheed yace "to ynxu ya aka yi," Abdul yace "nothin," Mujaheed yace "xan maka bayanin komai Abdul don naga bbu ruwanka, yhu're vry calm," shi dai Abdul kallonsa kawae yake, cikin nutsuwa Mujaheed ya fara ma Abdul bayanin yanda abubuwa suka wakana, tun daga lkcn da ya dauko Aneesah daga kauye har xuwa gidansu mudatheer da ya kai ta, bbu abinda ya boye ma Abdul, Abdul yyi murmushi yana cije lebe yace "ku kuka daure min dad knn," Mujaheed ya daga kafada yana kallonsa, Abdul ya tabe baki yana kallon agogo yace almost tym 4 prayer. bayan sllhn maghrib Mujaheed yace su je can gidansu Aneesah kar Ammi taje gidan baffa, suka tafi kuwa, Mujaheed yyi mata bayani ita ma briefly, amma irin kallon da ta dinga masu yasa suka gane bata yarda da xancensu ba, Hkn yasa Mujaheed ya mike tsaye yace "to momy xa mu koma, goben xamu kawo Aneesar, jibi kuma akwae xama a kotu" bata tanka masu ba suka mata sllma, dama shi Abdul tun shigowarsu bae ce komai ba. washegari da Asuba, Abdul ya tashi Mujaheed sllh ganin yanda ya ke bacci kmr wani matatce alamar gajiya, tare suka tafi masallaci suka dawo, Mujaheed ya koma xae kwanta Abdul yace ya ba shi qur'ani, Mujaheed ya nuna masa inda yake, yyi kwanciyarsa. Karfe bakwae dai-dai Abdul ya da da masa duka, Mujaheed ya mike xaune da sauri yana kallon Abdul din yace "wat's wrong," Abdul yace "ni bana son naga namiji na bacci after 6 o clck, wnn ae ragwanci ne, kaga 2 b a doctor ma is a great thing in lyf, da wuya ka ga likita still on bed after six a.m," yana kai wa nn ya mike ya fada bathroom, Mujaheed ya ja dogon tsaki yace "to ni nayi maka kama da doctor ne, wnn ae wlknci ne," karfe takwas Amira ta kawo masu break sama, ta gaishe da yayanta, snn ta gaida Abdul dake bnta da kallo ya gyada mata kai, ta ajye masu ta fita, Abdul yace "kanwar nn taka bakauyiya ce wllh," Mujaheed na kallonsa ya tabe baki bai ce komai ba ya sauko ya shiga hada tea, Abdul yace "ni fa coffee nake sha, " dole Mujaheed ya sake kiran Amira ta kawo masa coffee. Bayan sun gama karyawa Mujaheed ya fito masa da kayansa ganin yaki mai da kayan jikinsa daga shi sae singlet da nicker, Abdul yace "bana sa kayan mutane, boutique xan tafi ynxu" Mujaheed bae tanka masa ba ya shige bathroom, ko da ya fito ya tarda Abdul sanye da kayan nasa yace "ashe dae kai karamin dan iska ne, ae da ca nake da singlet din xaka boutique," Abdul bae tanka masa ba yana ta kallon hotunan wayar Mujaheed din, ya mike yana nuna ma Mujaheed hotansa da Hydar yace "wnn shine Hydar din da kke fada min ko?" Mujaheed yace "yea," mujaheed na gama shiri suka sauka downstairs a tare, mumy tace ina xa ku, Mujaheed yace xamu dan fita ne, tayi masu Allah ya kiyaye, suka shiga mota Abdul ya ja ta. Sae da suka yi nisa snn Abdul yace "ina xamu?" Mujaheed yce waida inda Aneesah take xamu, amma mum ta hanani xuwa kuma ni bana tsallake umarninta," Abdul yyi tsaki yace "kai fa wani gara ne, ae ba kai xaka je ba kai ni kawae xaka yi, naga kanwata."
[12/8, 21:13] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 100..... Mujaheed na fitowa kofar gidan ya tarda Aneesah durkushe kasa tana kuka, tana ganinsa ta mike tsaye tana share hawayenta, ya karaso gabanta yana mata wani mugun kallo yace "me yasa baki bi sa ba," ta girgixa masa kai tana kuka tace "yayana....." sae kuma maganar ya makale ta fashe da wani sabon kukan, Mujaheed ya girgixa kai ya daga mata hannu yace "kar ki gaya min komai, hold on 2 yhur crocodile tears, dama munafurta ta kika yi kika ce min Hydar baya son ki, don me kika min karya kikace bbu komai tsakaninki da Hydar, whereas masoyinki ne, why Aneesah?" kuka kawae take tana girgixa masa kai, ya kauda kansa ya hade tafikan hannunsa, can ya juya yana kallonta cikin tsawa yace "don me baki bi sa ba, nace don me baki bi sa ba, ae da kin bisa da kukan da kika tsaya kina ma mutane a nn, munafuka kawae" yana kai wa nn ya juya a fusace ya shige motarsa yyi gaba. Aneesah ta sulale kasa a hankali ta bi motar da kallo tana girgixa kanta, kukan ma wnn karan kasa yi tayi, wnn wace irin rayuwace, a hankali taji Abdul ya dafa kafadarta ta juya da sauri tana kallonsa sae a snn ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, ya dago ta yana kallonta ya shiga share mata idonta yace "it's owkay Aneesah," bata ce masa komai ba ya dauko gyalenta ya mika mata ta karba hawaye na bin kuncinta, ya kama hannunta suka bar wajen, ita bata ma san binsa take ba suna tafiya, duk abun duniya ya isheta, har lkcn bata daina hawayen da take ba, sae da suka bar anguwar snn tayi saurin fixge hannunta ta shiga waige waigen inda suke tace "ina xa ka kaini?" yana kallonta yace "gurin babarki xan kai ki," ta girgixa masa kai tana kuka ssae tace "aa Ammina bata nn, ka barni na koma gida," ya kamo hannunta yace "kar ki damu Amminki na gida," ta juya da sauri tana kallonsa cikin muryar tausayi da rashin hope tace "da gske ya Abdul," ya gyada mata kai yace "eh, xan kai ki ki ganta ai," hkn yasa ta dinga binsa jiki ba kwari, suna ta tafiya a kafa, duk a rikice take don bata san ko Abdul gaskiya ya gaya mata ba, ita dae kawae ta ga Amminta, sunyi tafiya mai nisa, ta dan duka alamar gajiya, ya juya yana kallonta yace "me ya faru?" a sanyaye tana kallonsa tace "ruwa xan sha ya Abdul," yaji tausayinta ssae, ya dago ta yace "ba kudi hannuna Aneesah, bank nake dubawa ko xan samu mu cire kudi a Atm," ta gyada masa kai kawae, ya kama hannunta suka ci gaba da tafiyar, har daga karshe suka samu wani banki, ya ciri kudi a ATM tana gefensa a tsaye, sae da ya fara siya mata table water biyu snn, ya tsayar da taxi ya fadi anguwarsu Aneesar, hkn yasa taji mugun ddi, ta yrda ba cutar da ita Abdul xae yi ba, duk da a xuciyarta tana cewa wahalar bnxa kawae xasu je suyi, amma bata nuna masa sun je da Mujaheed Ammi bata nn ba, ko bakomai xata ga makwabciyarsu ta gaya mata ko suna communicate da Amminta, bayan minti talatin suka iso anguwar tasu, sae taji duk wani bakin cikinta ya yaye, hankalinta ya kwanta, Abdul ya nuna ma mai taxin inda xae tsaya dae dae kofar gidansu Aneesah. Like · Reply · More · 2 minutes ago
[1:05PM, 12/23/2016] Khaleesat: [12/8, 21:07] ‪+234 803 751 8717‬: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
101.....
Abdul yyi kofar shiga gidan ganin Aneesah ta kasa shiga sae kallon gidan da take kmr bakonta, yana shiga xauren gidan ta bi sa a baya da sauri, yyi sallama ya shiga cikin tsakar gidan, tana biye da shi a baya kmr munafuka, cak ta tsaya ganin Amminta tana wanke tsakar gidan da ruwa, Ammi ta dago tana kallonsu, Aneesah bata san lkcn da ta fasa wani ihu tayi kan Amminta da gudu ta fada kanta ta fashe da kuka, suka xube kasa gaba daya Ammi ta dago kanta tana kallonta, Aneesah ta kankameta tana kuka mai tsuma xuciya, Ammi ta kasa ce mata komai, ita ma hawayen cike a idonta, Abdul dae na tsaye har lkcn kusa da su, sae da Aneesah tayi kukan mai isarta kmr ranta xae fita snn Ammi ta dago ta suka mike tsaye, ta ja ta suka shiga daki, muryarta na rawa tace "wayyo Ammina, ina kika tafi kika barni, meyasa kika tafi kika barni" Ammi ta share mata hawaye tace "gani Aneesah, ki daina kuka baxan sake barin ki ba," Aneesah ta dinga gyada mata kai tana jikinta, tana sauke ajiyar xuciya, can ta xauna da sauri tana kallon Amminta tace "Ammi ya Abdul yana waje," Ammi tayi shiru tana kallonta snn tace "ki ce ya shigo to," ta mike tsaye ta fita bata gansa ba, har kofar gida ta fita amma bata ga Abdul ba, ta dawo tana kallon Amminta da take ji kmr a mafarki take ganinta, ta xauna tace "Ammi ya tafi ban gansa ba," Ammi tace "Aliyu fa Aneesah?" Aneesah ta sunkuyar da kai wani sabon hawayen cike a idonta tace "nima ban sani ba Ammi," Ammi tace "to ina baffan naki," Aneesah tayi shiru tana kallon Amminta. Mujaheed na komawa gida Mudatheer ya kirasa, ya daga ko gaisawa basu yi ba Mudatheer yace "yah Jaheed kai ka dauki Aneesah ne," mujaheed dake kwance kan gado ya mike da sauri yace "ni? A'a ban dauketa ba me ya faru?" Mudatheer yace "tun daxu fa bata gida, momy tace tunda mai gadi yaxo yace ana sallama da ita ta fita bata sake shigowa gidan ba, kuma duk an duba ba aganta ba," Mujaheed ya mike tsaye ya katse kiran yace "innalillahi wa inna'ilaihi raji'un," Abdul, fa di da karfi snn ya figi makullin motarsa ya fita, yana fita titi ya kira nmbr Abdul din cikin tsawa yace "ina a kai Aneesah," Abdul yace "fuck yhu," ya katse kiran, Mujaheed ya kusa sake

Please Login or Register in order to submit comment