Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________
*Writing by*✍🏻

*Hajara L Sadeq*
*Miss hajo*🖤

~marubuciyar~
*KOMAI MUKADDARI NE*
*K'ADDARAR SOYAYYA TA*
~And now~
*NAJMAT ABIY*
_____________________________________
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_


*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

~*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*~



*Da sunan ALLAh Mai Rahama Mai jin k'ai Ina godiya ga ALLAH SWA da ya bani ikon fara rubuta littafin nan Mai suna NAJMAT ABIY K'irk'irarren labari ne da yazo da nashi salon na musamman Wanda na tabbatar zai nishada'antar da Mai karatu ban yarda wata ko wani su juyamun labari ba LITTAFINE Mai d'auke da darussa da Dama a cikinshi Wanda inkuna biye Dani zakuji sak'on da littafin ke tafe dashi Ina rokon ALLAH yanda na fara shi lafiya Allah yasa na gamashi lafiya ALLAH tsari alkalami na da rubuta abunda yake ba ALKHAIRI ba Free book ne comment dinku da sharhi kawai nake buk'ata kamar yanda kuka karb'i KOMAI MUKADDARI NE ina fatan Shima zaku karb'eshi hannu bibbiyu har kullun burina baiwuce naga na faranta muku my sweethearts*
*I LOVE YOU ALL MY FANS K'AUNAR KU A JINI TAKE SWEETHEARTS*


Sakon gaisuwa da godiya da jinjina gareku y'an uwa kuma masoya k'aunar ku a jini take.

👇🏿
*Ummu maheer*

*Momyn shukura*

*Nearnah M sha'aban*

*Hafsat Zubair (Muhsat)*



*FREE BOOK*📒
___________________________________
*PAGE 01 & 02*
____________________________________



*INDIA*🇮🇳
*NEW DELHI*



*HIGH GARDEN REAL ESTATE*



Naga an rubuta a jikin katafaren get din da shi kanshi abun kallo ne.




Tun daga shigar ka estate d'in zaka tabbatar ba ta k'ananun mutane bace duba da yanayin tsaruwar gine_ginen dake cikinta.



Gidajene na alfarma dukkaninsu iri Daya girman estate din ya wuce misali Dan Bakama iya k'irga yawan gidajen dake cikin ta ba gari gudace Fadar tsaruwar ta B'ata Baki ne kowane gida da get d'inshi da komai a ciki na more rayuwa.



Akwai pack a cikinta inda yara suke wasansu Babu abunda Babu cikin pack din tundaga kan swimming pool da sauran kayan more rayuwa sannan akwai makaranta tun daga primary har secondry duka y'ay'an dake cikin estate din a nan suke karatunsu hankali kwance ga kuma kwararrun ma aikata haka zalika akwai hospital cikin Estate din Shima Mai d'auke da k'wararrun ma aikatan kiwon lafiya.




indai takaice muku Mai karatu duk inda za Akira waje Aljannar duniya tofa estate d,innan takai a kirata Aljannar duniya Dan tunda nake bantab'a ganin estate Mai kyan taba.




D'aya daga cikin gidajen wannan katafariyar estate d'in na kutsa kaina ciki Wanda bakin get d'inta ma shak'e yake da security.




Zaune suke a katafaren palour na alfarma wanda shak'e yake da kayan more rayuwa Babu abunda Babu najin dad'in rayuwa.



"please ABIY don't say no I wan't see her I love her so much ABIY or only once have see it" ta Ida fad'a idanunta na cikowa da ruwa kamar zatayi kuka *NAJMAT* kenan y'ar shekaru takwas da haihuwa kyakyawar yarinya NAJMAT fara ce sosai farinta irin na yaran turawa Mai kyau d'in nan round face d'inta.



Dogon hancin ta ga kuma k'aramun bakin ta da yayi das da kyakyawar Fuskanta dimple d'inta Wanda yake ko batayi magana ba a lotse yake Y'ar wushiryarta data Kara fito Mata da asalin kyanta NAJMAT yarinya ce kyakyawa duk da karancin shekarunta Bai hana kyanta fitowa ba Bata k'iba kuma bazaka.kirata da Siririya ba y'ar chakwas d'in yaran naj ce




Durk'ushe take gaban mahaifinta tana Mai magiya akan ya taimaka ya kaita taga mahaifiyarta ko da sau d'aya ne ita dai burinta taganta a rayuwar ta ko sau d'aya ne.







Maganganun Nan na tilon d'iyar tashi ba k'aramun sosa mashi zuciya suke ba jawota yayi jikinshi tare da rungumeta tare da Fara lallashin ta saboda a duniya Babu abunda ya tsana sama da b'acin ran NAJMAT.




Ko kad'an bayason Yaga kukan tilon d'iyar tashi ga kuma takaicinshi na Son ganin Mahaifiyarta da ta dameshi dashi kwanannan yasan Babu abunda NAJMAT zata nema a wajenshi ya gaza Mata a rayuwa amma.kuma wannan Karin bazai îya cika Mata burintaba saboda Alk,'awari ne ya d'aukarwa kanshi har abada bazai tab'a had"a ta da mahaifiyarta ba Harya Koma ga mahaliccinshi maganganun Nan nata suna k'ara sosa Mai tsohon raunin da ke cikin zuciyar shi.




Cikin sigar lallashi yace "My Najma" d'ago dara Daran idanun ta tayi da ya cika da k'walla tace yes My ABIY "do you wan't. Upset me?ya fad'a fuskanshi na Nuna alamun damuwa.




Girgiza Kai ta fara cikin Y'ar in Ina tace "No ABIY "Shafa kanta yayi tare da sakar mata Murmushi yace ,"if you don't like my frustrations don't talk to me about your mom as from to day "


Goge k'wallarta tayi tare da sakarmashi Murmushi ta gyad'a Kai alamaun ta fahimta Dan itama Babu abunda ta tsana sama da b'acin ran ABIY.




"Yawwa *NAJMAT ABIY* d'inta GOD bless you dariya NAJMAT tayi jin ABIY ya kirata da sunan da tafi k,'aunar a kirata dashi rungumeshi tayi tare da cewa"Amen my ABIY I love you so much"I love you more my daughter ya fad'a Yana Shafa kanta .





Cikin hausarta da Bata gama Nuna ba tace "ABIY innasin janze gidan su Amera , " "inye my baby tafara iya hausa "dariya tayi tare da lafewa jikin shi D'aukarta yayi Suka fito don ya kâita gidan su Amera Kamar yanda ta b,uk'ata Shima gidan cikin Estate dinne hakan. Yasa suka tafi a k'asa Saida ya kâita har cikin gidan Saida Yaga shigarta sannan ya juya da niyyar bayan magriba yadawo ya d'auke ta.



Tana shiga palour Mamy kad'ai ta iske yatsarta tasanya ta fara tsotsa tana waige waige inda zataga Amera
*NAJMAT* Ba magana cewar Mamy "mak,'ale kafad'a tayi alamun bazatayi magana ba "Murmushi mamy tayi Dan tasan miskilancin NAJMAT Cigaba tayi da waige waigenta chan dai ta gaji ta zauna Tana cigaba da Shan yatsanta Mamy ce tace "Dear bana hanaki tsòtsan yatsa ba"Turo Baki tayi tare da shagwab'a fuska ta cire yatsan Yaudai miskilancin kike ji bazamuyi hira ba kenan? Cewar Mamy gyad'a Mata kai Najmat tayi alamun Eh.




Murmushi Ummy tayi kawai taci gaba da kallon news d'in da take. Amera ce ta fito daga bedroom d'insu tana ganin NAJMAT a palourn da gudu ta ruga tare da rungumeta Nan suka.hau tsalle tsalle da wasansu kamar yanda suka Saba sannan suka fara buga game d'insu a Tab Sunayi Mamy tana gefe tayi Murmushi tana Yaba wannan tsantsar k'aunar dake tsakanin NAJMAT da AMERA kamar Wanda suka fito ciki D'aya.



Magriba ABIY yazo domin d'aukar NAJMAT Nan suka had'u da Abba Yana Shirin shiga Gida mik'awa juna Hannu sukayi suka gaisa ABIY ne yace "Ina wuni Alhaji an dawo lafiya " "lafiya qalau abu NAJMAT ya harkoki
" Alhamdulillah"Masha Allah"Sannan yace Daman NAJMAT na zo d'auka Murmushi Abba yayi yace Baka barta ta kwana ba "d'an Murmushi ABIY yayi Yana d'an sadda Kai yace "Kar Kuma tayi kuka"Murmushi Abba yayi Dan yasan Daman ABIY bazai îya ba Sannan yace to bari na turo Maka ita har yayi gaba sai Kuma ya juyo yace " gobe idan Allah ya kaimu Ina son magana da Kai Muhammad"To shikenan Alhaji Allah ya kaimu ".




Abba Yana shiga ya iskesu suna wasa suna ganinshi Suka ruga a guje tare da hug d'inshi D'aukarsu yayi d',aya bayan d'aya Sannan yacewa NAJMAT ABIY na waje Yana jiranki.




Da gudu tayi hanyar k'ofa Mamy ce tace "Ba Sallama Najma Dariya Abba yayi yace "Bama mugaisa ba shine Zaki tafi ko Daughter"y'ar dariya NAJMAT tayi sannan tayi musu gwalo tare da d'agawa Amera hannu tace "God bye my friend until tomorrow when we meet at school" tayi waje dukansu Saida suka dara tana fita Rugawa tayi ta fad'a jikinshi d'aukanta Yayi Yana Mata Murmushi.





Suna isa gida bayan yayi Mata wanka Boxes kawai ya Sanya Mata Sannan ya Bata abinci Saida ta k'oshi sannan yakaita ta kwanta Saida ya tabbatar da Tayi bacci sannan ya Koma d'akinshi Shima ya kwanta.......✍🏻






*Sai naji ruwan comment tukwana zanci gaba idan banji comment ba zan dakata* 🙅🏼‍♀️



*Hmm my sweethearts ya kukaji salon labarin*




*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*




*GOD WE REPENT* 🤲🏼





*_Miss Hajo ce_* 🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss Hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*FREE BOOK*📒
_____________________________________
*PAGE 05 & 06*
_____________________________________



"Ma'ana.Tauraruwar mahaifinta Najma tauraruwa ce a gareni Bata da kowa a duniyar nan sama Dani haka Nima a halin yanzu bani da kowa sama da ita itace komai nawa shiysa nake tausaya Mata ranar da babu ni....kasa k"arasa maganar yayi sakamakon zafin da zuciyarshi ke mashi."



Dafa kafadarshi Abba yayi yace"Muhammad a da ne baka da kowa Amma a yanzu kad'auka kana da kowa inajinka Kai da Najma har cikin zuciya ta Ina maka kallon k'ane ne Wanda muka fito ciki d'aya insha Allahu indai Ina raye Najma bazatayi kukan rashin uwa ba "Tausayin NAJMAT ne ya tsargu a Zuciyar Abba Yana tausaya Mata na maraicin da ta tsinta kanta tun k'uruciya.





Shawara Abba yabawa ABIY akan ya kamata yayi aure ko Dan saboda Najma amsa mashi yayi da to Amma ba Dan zai aikata hakan ba Dan yanda yake ji a game da tsanar da yayi wa Mata bayajin zai iya K'ara yin aure har abada a rayuwarshi .






NAJMAT ce da Amera sai k'awarsu Simi zaune a compound d'in school d'insu Kasancewar an tashi gashi har yanzu ba a zo an d'auke su ba.



Kasancewar mazajen Estate d'in duk ma aikata ne hakan yasa iyayen su Mata suke zuwa d'aukansu NAJMAT idonta nakan yaran da ake ta zuwa d'auka kowa saitaga mamanshi tazo ta d'aukesu hakan ba k'aramun Bata sha'awa yake ba jikinta ne duk yayi sanyi ji take inama ita ce.


K,'walla ce ta fara zubowa daga idanun ta Bata da wani buri da yawuce itama ta ganta tare da mahaifiyarta suna rayuwa kamar yanda kowace y'a ke rayuwa da iyayenta.



Maman Simi ce itama tazo d'aukanta Rugawa da gudu Simi tayi tare da rungumeta itama rungume y'ar tata tayi tare da Bata peck a kumatu K'walla NAJMAT ta fara Simi ce cikin harshen Hindu tace "Momy ga friends d'ina Najma and Amera.



"hug d'insu d'aya bayan d'aya Maman simi Tayi gaisheta suka Yi ta amsa tare da tambayarsu ya akayi ba azo aka d'auke su ba "Simi ce Kasancewar ta Mai Surutu ta ce, "Moma NAJMAT ai Bata da moma bantab'aganin. maman ta ba ,ABIY kad'ai Gareta Amera Kuma driver su zaizo ya d'aukesu su"





Kuka NAJMAT ta fàshe dashi jin abinda Simi ta fad'a lallashin ta Amera ta Fara tace "Sorry my dusti Babu ruwanmu da Simi daga yau sannan ta gallawa Simi Harara tace tunda kikasa Dusti ta kuka Babu ruwanmu dake ke yanzu ba friends d'inmu bace, ,"sorry my friends bazan sake ba Amma karkuce ni ba k'awarku bace sannan ta Fara kuka itama" .





Hak'uri Maman Simi tabasu sannan taja hannun y'arta tare da ce Mata karta sake irin wannan maganan.(karku manta duk cikin harshen Hindu suke maganganun Nan) .






ba irin lallashin da Amera batayiwa NAJMAT ba Amma tak'iyin shiru Suna haka Aunty nafesa tazo D'aukarsu da gudu Amera ta ruga wajenta tace "Aunty Dosti tun dazu take kuka tak'iyin shiru please Aunty kice tayi shiru Nima zanyi kukan idan batayi shiruba".



A d'an rud'e aunty nafesa tayi wajen Najma tare da D'agata ta fara lallashin ta kamar k'ara zugata take Aunty nafesa ce tace "amera me akayiwa Najma .




Amera da idanun ta suka ciko da k'walla " tace "Simi ce tace Mata Wai Bata da mama Kuma nace Mata ba ruwanmu da ita yanzu ita ba k'awarmu bace"




Saida jikin Aunty nafesa yayi sanyi jin maganan nan tasan a lokacin nan Najma na buk'atar kulawar uwa tun sanda Abba ya fad'a musu Najma marainiya ce take tausayinta Kuma tayi Alk'awarin saita zamewa Najma uwa bazata tab'a rashin uwa ba inhar tana raye Dan tanajin Najma ne tamkar y'ar da ta Haifa a cikin ta .





dakyal ta samu ta lallashi ta suka koma gida tun daga ranar aunty nafesa ta ninka kulawar da take bawa NAJMAT b'angaren ABIY Yana jin dad'in kulawar da aunty nafesa ke bawa y'arshi b'angaren Najma kuwa Damuwa ce tayi katutu a cikin zuciyarta dukda kulawar da Aunty nafesa ke Bata Kuma itama tasan tana son aunty nafesa Amma a zuciyarta tana son taga yau itama ga mahaifiyarta wacce ta haifeta.




Hakan yasa ta zamto kullun silent ta rage hayaniya da kuzari musamman a makaranta ta rage K'ok'arin Dan tun da Najma tashiga school Bata tab'a zuwa da second position ba Koda yaushe first position take zuwa dashi Najma nada k'ok'ari sosai k'ok'arin ta na baiwane saboda gifted ce ta bugawa a jarida hakan yasa teachers din gaba d'aya suke ji da ita a school d'in Hakan ne yasa ma suka Yi Mata jumping yanzu tana jss one ne.


A tak'aice dai.



Najma da Amera aminai ne tun da suka shiga school din jininsu ya had'u gashi shekarunsu sukaso d'aya koda akayiwa Najma jumping itama Amera kuka tasa akan itafa sai an hada ta Dusti bayanda aka iya itama Amera aka Mata jumping din dukda itama ba laifi tana da kokari.




Shakuwace sosai tsakanin Najma da Amera hakan yasa Koda yaushe a gida Amera Bata da zance idan ba na Dusti ba Haka Najma Bata da zancen da ya wuce na Amera dukansu a cikin Estate Daya suke Koda NAJMAT ta bukaci ABIY ya kâita gidan su Amera Bai Musa ba tun lokacin da Najma ta fara zuwa gidan su Amera y'an gidan su Amera suka d'auki son duniya d'orawa NAJMAT jinta suke tamkar y'arsu.





Musamman Abba dan tunda yaganta ita da Abiy Kasancewar Najmat kamarta Daya da abiy kàmar an tsaga Kara an karya Yaga suna Mai mugun kama da k'anwarshi hau'wa'u ga kuma yanayi da take Mai da babbar y'arshi data rasu Amina Hakan yasa yakejin najmat a ranshi kamar amina ce ta dawo aunty nafesa k'anwar Ummy ce uwa Daya uba Daya budurwace tagama karatunta na deegree a wajen Ummy take da zama.



Ummy da Abba suna da yara Ukku dukansu Mata ,babbar y'arsu Amina Allah yayi Mata rasuwa sai Sarat ita yanzu tana Nigeria wajen Mahaifiyar Abba take sai autar su hauwa'u suna kiranta da Amera Asalin su y'an Nigeria ne aiki ne.ya kawo Abba India Inda ya saya gida a Estate din yake zaune da iyalanshi.


shak'uwa ce sosai tsakanin Najma da gidan su Amera musamman Aunty nafesa Hakan yasa Koda yaushe tana gidan su Amera da andawo daga school tana chan.




ABIY Yana aiki ne.a Babban Componyn sarrafa manya manyan motoci a new Delhi shine C E O a componyn mutum ne Mai Amana baya tab'a cin Haram halal d'inshi yake ci Hakan yasa shugaban componyn yake ji dashi Kuma yakemai alheri sosai ga albashin shi Mai tsoka sosai yanzu haka Abiy Yana da componyn shaddoji da lessusuka nashi na kanshi guda Biyu ga ya mallaki gidaje da Dama a garin New Delhi ciki harda gidan shi da yake ciki ga manya manyan motoci Kuma duk halal d'inshi ce mutum ne Mai Kirki da Kamala ga îya zama da mutane.



NAJMAT ita kad'ai ce Y'ar da Allah ya mallaka mashi Yana son Najma fiye da komai Baya yarda Najma na shiga damuwa Tun da Najma take Bata san mahaifiyarta ta ba tunda ta tashi a rayuwarta da ABIY ta tashi Bata son meye dad'in uwa ba gashi kuma ABIY yaki hada ta mahaifiyarta gata ,da soyayya ba abunda Najma ta nema ta rasa daga wajen ABIY Amma duk da haka soyayyar mahaifiyarta da Bata San ko wacece ba ta na Nan mak'ale a cikin zuciyar ta shakuwace Mai k'arfi tsakaninta da Abiy suna matuk'ar son junansu dukansu biyun basason suga dayan su Cikin damuwa a ta'kaice dai wannan kenan......✍🏻




*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*







*GOD WE REPENT* 🤲🏼






*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS📚🖊️*
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
_____________________________________

*FREE BOOK*📒
_____________________________________
*PAGE 03 & 04*
_____________________________________


washegari Around 6am ya tada NAJMAT yayi Mata wanka ya Mata Shirin makaranta riga da d'an k'aramun siket d'in bakin k,'ugu sai Doguwar safa ya gyara Mata two babies d"in gashin ta bayan tayi breakfast ya zuba Mata a basket d'inta Shima shiryawa yayi cikin Shirin tafiya wajen aikinshi tare suka fito da NAJMAT a hannunshi mota suka shiga driver ya jasu Saida ya biya ya Fara Kai NAJMAT sannan ya wuce Kai ABIY compony.





2:00pm Aka tashi su NAJMAT daga makaranta kamar kullum driver d'in su Amera yazo ya d'aukesu suna shiga palour Aunty nafesa suka tarar fad'awa jikinta sukayi dukan su wayyo baby's zaku karyani fa k'ara hayewa chinyarta sukayi suna dariya NAJMAT hada k'ara dira wa Saida suka gaji Dan kansu tukwana suka sauka "Wayyo baby's Kun Karyanu"dariya suka hau Mata " Najma ce cikin shagwab'a tace "Aunty yunwa nakeji" Abincinku Yana dining a red cooler d'in chan d'ayan na Su Ummy karku tab'ashi kunji NAJMAT ta fara Rugawa sannan Amera ta bita harsun fara cin abincin Ganin Aunty nafesa tabar palourn Aiko suka d,'ad'aga Wanda ta hanasu d'in suka sa duka hannuwansu biyu suka hau shagwalgwala shi suna watsashi a gurin.






salati aunty Nafisa ta fara fitowarta taga yanda suka wulak'anta abincin "me nake gani Amera Najma sauran. abincin Ummy da Abban ne kuka lalata juyowa sukayi Suna kallonta Amera tace "Sorry Aunty we will not do it again "Turo Baki NAJMAT tayi taci gaba da watsa abincin tana jagolgolashi kamar badasu take ba.



Tafa hannu Aunty nafisa tayi tace "watau NAJMAT inama magana kina cigaba ko ta fad'a a d'an tsawace Dan taji ciwon lalata abincin da sukayi Dan Tasha wahala kafin ta girka.



"Kuka da dira k'afa Najmat ta fara saboda ita Babu abunda ta tsana sama da ace tayi ba daidai ba musamman a Mata fad'a komai take Kar amata magana yanda ABIY d'inta ke Mata baya tab'a hanata b,'arna shiyasa in tanayi tofa ba a isa amata magana ba .



haka Mamy ta shigo ta iskesu dawo warta kenan daga office Kallon NAJMAT tayi tana kuka kallon Aunty Nafisa tayi tace "me akayi Mata nafesa ".





"wallahi Aunty Abincin ne suka lalata ita da Amera shine daga musu d'an fad'a ta hau kuka"NAJMA rigima inji Ummy sannan tace "Keda daughter ki da Bata laifi bazan shiga fad'an da zanji kunya ba ta fad'a tana barin wajen,Dan tasan Inma tashiga kunya zataji dan tskanin NAJMAT da Aunty nafesa ba a shiga.






Hanyar k'ofa NAJMAT tayi zata fita tana kuka da gudu Aunty nafesa ta tare ta tare da d'aukanta wutsil wutsiltun ta fara Aunty nafesa tace "Haba My Habibty fushi zakiyi Dani sorry my baby I will not tell you again
indai kinajin magana ta bazan dinga maki fad'a ba".




Lafewa jikinta NAJMA tayi tana sauke ajiyar zuciya "Daddab'ata taci gaba dayi tana lallashi "Haba my sweet daughter kin tab'a ga inda Daughter tayi fushi da Momynta"haka dai Aunty nafesa tayi ta lallashinta harta samu ta hak'ura bacci ya kwashe ta a cinyarta gyara Mata kwanciyarta tayi kan cinyartata tare da Shafa Mata fuskarta Ita kanta aunty nafesa wani Karin har mamakin son da take yiwa NAJMAT take Nan Ummy tafito ta iskesu Murmushi tayi tace "har an shirya kenan dariya Aunty nafesa tayi tace "Dan dak'yal ai Babyn tawace ba dai rigimaba.





"Muhammad yanzu dai a iya zamanmu daku kusan shekaru Biyar anriga an zama d'aya Ina d'aukar ka ne matsayin d'an uwa uwa uba Addini mu d'aya haka zalika k'asar mu d'aya Kuma Allah ya hadamu waje d'aya Saidai kamar har yanzu ,Ina ganin baka gama sakin jiki damu ba kamar yanda muka saki jiki dakai",




Abba ne ke maganarnan suna Zaune a garden d'inshi bayan ya Kira Abu NAJMAT "Nima haka nake d'aukarku Alhaji da Kai da iyalanka bansan da wani irin Baki zan iya gode muku bisa ga yanda kuke hidima damu ni da y'ata Saidai ince kawai Allah ya biyaku da mafificin ALKHAIRI"Babu komai Muhammad Najma ai y'a take.a wajenmu dalilin da yasa na nemu magana dakai illa inason sanin takaitaccen tarihinka da Kuma dalilin da yasa kake zaune Babu Mata da ga Kai Sai y'arka abun Nan yajima Yana daure mun Kai .,




Yanayin Abiy gaba d'aya Saida ya chanza saboda maganar Tarihin shi da yayi mashi ga kuma bak'incikin tado mishi da zancen Mahaifiyar NAJMAT da yayi Wanda baya k'aunar tunowa da ita ko misk'ala zarratin saboda Yana k'ara sosa mai zafin radad'in ciwon dake cikin zuciyar shi Dan ajiyar zuciya ya sauke Dan bayajin zai iya fad'a wa kowa Gaskiya game.da tarihinshi idan ma yace zai fa'da to ta Yama zai fara Dan shi kanshima har yanzu cikin duhu yake hakan ya sashi cewa.




"a takaice suna na Muhammad haifaffen garin gombe Iyaye na sun rasu tun ban girma ba nayi Auren soyayya da Mahaifiyar NAJMAT wajen haihuwar NAJMAT Allah yayi Mata rasuwa Nina cigaba da kula da Najma tun tana jinjira Ina son NAJMAT fiye da yanda nake son Kaina zan iya Sadaukar da komai Akan NAJMAT Najma ita nake kallo naji sanyi a Raina Najma itace tauraruwata Najma ta zame mun. matsayin uwa ,uba,d'an uwa,y'ar uwa,aminiya,hakane ya sanya nake Kiran ta da *NAJMAT ABIY* ..........✍🏻


*idan kun karanta dan girman Allah kuyimun sharing fisabilillah*




~*GOD WE REPENT*~👏






*_Miss hajo ce_* 🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss Hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*FREE BOOK*📒
_____________________________________
*PAGE 7 & 8*
_____________________________________


Yau ta kama end of 3rd term Wanda da sun dawo Hutu su NAJMAT zasu shiga Jss two.





Abun. Mamaki NAJMAT dake zuwa first position itace wannan Karin tazo 3rd potision malaman kansu sunyi mamakin lamarin Nan.




Hakan yasa suka sanar da ABIY ya binciki NAJMAT cikin kwanakin nan sun lura akwai abun da ke damun ta.



Shima ABIY ya lura da hakan dan ta chanza sosai ta rage kazar-kazartu abun Yana damunshi sosai.





Koda ya tambayeta me ke damunta Bata fad'a Mai dalilin ba saboda tun ranar da yace karta Kuma Mai magana game da mamanta Bata sakemai ba saboda a duniya Babu abunda ta tsana sama da b'acin ran ABIY.



Wata Rana da magriba ABIY yaje d'aukar NAJMAT Nan suka had'u da Abba suka fara tattauna wa game da lamarin Najma.




Muhammad akwai wuni hukunci danake son yankewa kokuma ince shawara a matsayi na na d'an uwa Dan yanzu an riga an zama d'aya to bansan b,'angaren ka ya zaka d'auki lamarin ba ".




Saida gaban ABIY ya fad'i amman ya fusge yace ,"inaji Abban Amera insha Allahu zanyi Amfani da shawararka ".




"Wani nazari ne nayi Duba da shak'uwar dake tsakanin nafisa da NAJMAT nake ganin mezai hana ka Auri nafisa

Please Login or Register in order to submit comment