Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na tabbatar nafisa zata rik'e NAJMAT da amana haka Kuma Najma yanda ta d'auki nafisa tamkar uwar da ta haifeta Ina ganin Hakan zai yiwa NAJMAT dad'i Kuma zatayi farincikin zama da nafisa Ina ganin hakan itace kad'ai mafitar da Najmat zata dawo da walwalarta kamar da Koma Fiye da da.




Tun da Abba ya fara maganganun Nan Wata uwar zufa ta jika ABIY a zuciyarshi yace ,"ya zakayi mun haka Abban amira Kodan bakasan halin da na shiga a rayuwata ta baya bakasan Azabtuwar danayi ba ta dalilin mace baka san illar da mace ta aikata mun ba Da bazaka bani shawarar K'ara kallon Wata mace ba bare har Takai ga aure banajin zan iya K'ara rayuwar aure da wata mace a duniya Illar da Mahaifiyar NAJMAT ma kad'ai tayimun a rayuwa ta isheni".





Kasancewar kwarjinin da Abba yayi mishi da Kuma Ganin kimar Abba dayakeyi bazai îya Musa Mai Kai tsaye ba da k'yal ya iya daidaita nutsuwar shi yace "To shikenan Alhaji Insha Allahu zanyi shawara sannan sukayi musabaha Abba yayi gida da niyyar kirawowa ABIY NAJMAT.



Duk maganar Nan da su Abba sukayi akan kunnan Amera da Najmat Sunfito wasa kenan suka lab'e sunajin su Wara idanu Najma da Amera sukayi a tare saikuma suka saki Murmushi Najma tace "da zanfi kowa farinciki idan ABIY ya Auri aunty Nafisa lokaci guda Kuma ta had'e Rai tace To idan Kuma Aunty Nafisa tace batason ABIY na fa ,"Amira ce tace "Ai Dole ma musanya ta soshi tab'awa sukayi tare da kashewa juna Ido ganin Abba yataso ya Sanya su Rugawa da gudu suna dariya Kai tsaye bedroom din Aunty nafesa sukayi.





Kwance suka tadda ita tana charting hayewa kanta sukayi Murmushin kawai tayi Dan ta Saba da hayewar yaran nata Nan ta biyesu sukayi ta shiririta.





Abba ne ya Kira Aunty Nafisa a palour ta fita ta iskeshi Najma da Amera suna jin Kiran suka lab'e Dan suji Wata amsa aunty Nafisa zata ba Abba Najma addu'a kawai take Allah yasa Aunty Nafisa tayi accepted.




Shiru sukayi na d'an wani lokaci Ummy Abba sai Aunty nafesa Nan Abba ya korawa Aunty Nafisa buk'atar dake tafe dashi.



Dan danan Aunty Nafisa ta tada hankalinta Wata uwar zufa ta keto Mata Dan Bata da burin Auren Wanda ya manyanta a tsarinta dukda ABIY baiyi wani girma ba dan Bai wuce 40years.



Abba ne ya lura yace "karki k'wari kanki Nafisa ba umarni nake Baki ba shawara ce idan kinsan bakiso kifad'a mun kawai ba wata damuwa .




Dan Jim Aunty Nafisa tayi har zuciyarta Bata son ABIY Hakan kawai yasata fito da gaskiyarta a Fili ta ce ''gaskiya Abba ban sonshi".........✍🏻



*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*





*GOD WE REPENT*🤲🏼



_*Miss hajo ce*_ 🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss Hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafin Nan sadaukarwane gareku NAJMAT ABIY Fans Ina Jin dad'in comment dinku da sharhi fiye da yanda kuke zato Ina alfari daku my sweethearts Love you wujiga wujiga wallahi Shafin Nan nakune kuyi yanda kukeso dashi Ina alfahari daku*

*FREE BOOK*📒
__________________________________

*PAGE 9 & 10*
__________________________________


"Oh my GOD" NAJMAT ta fad'a tana dafe goshi kamar wata babba k'wallace ta fara kwaranya daga idanunta Amera ta maza ta goge Mata tace "Banason kina kuka fa Dusti you forgot we are claver ? Don't mind Dusti now our game will begin".



ta fad'a tana kashewa Najma Ido dariya k'asa k'asa Najma tayi tace "it's true Dusti" .


Ummy bataji dad'in abunda Nafisa tace ba koba Komai kodan saboda Najma yaci ta amince Aiko Nan ta hau ta fad'a Saida Abba yayiwa Ummy magana yace ta k'yaleta ai ba tilastata za a yiba.





Tun daga ranar Najma da Amera suka Mayar da hankalinsu akan yanda zasuyi su had'a soyayya tsakanin. Abiy da Aunty Nafisa Duk sun shiga busy cikin kwanakin nan tunanin su kawai yatafine akan game d',in da suke shiryawa.



B,'angaren ABIY Kasancewar Bai Bawa Abun mahimmanci ba Hakan yasa Yama mance da zance ya shiga harkar gabanshi




Da misalin 8pm kwance take ta d'ora kanta cinyar ABIY tana buga game a Tab d'in ta suna hira da ABIY d'inta.



Cikin hirar ne tace "ABIY gobe inason ka kaini shopping Teddie's d'ina sun lalace Kuma Coculate d"Ina ma sun kusa,k'arewa"




"To daughtern ABIY d'inta zan kaiki duk inda kikeson zuwa Amma zakimun Alk'awari d'aya"wani Alk'awari ABIY "Zaki dage a makaranta kamar yanda kike da Ina son ma kifi da k'ok'ari Kede kike so ki zama doctor in saya Miki k'atoton hospital kema kidinga yiwa mutane allura ko bakiso.




"washe Baki NAJMAT tayi tana dariya tace Ina so ABIY Kuma Na maka Alk'awari ABIY na Zan dage inzama doctor Nima nadingayiwa mutane allura Kuma saina rama allurar da doctor Kharena tayi mun dariya ABIY yayi yace "yawwa My lovely daughter na.





"NAJMAT tun tana yarinya take son ta zama doctor tun lokacin tana shekaru hud'u tayi zazzab'i aka kâita asibiti doctor Kharena tayi Mata allura tayi ta kuka tun daga lokacin tad'au Alk'awarin itama saita zama doctor tana yiwa mutane allura Kuma saita rama allurar da doctor Kharena tayi Mata har yanzu ta kasa mancewa ".




"Abiy nima inason zakayimun wani Alk'awari "Shafa kanta yayi yace Alk'awarin me dear "d'an Murmushi tayi tace kaidai ABIY kawai kayimun Alk'awarin duk abunda na rok'eka zaka amince Kai tsaye "




Murmushi yayi ya na lakutar kumatun ta Dan yasan Najma da iyayi kamar wata babba k'ilama wani iyayin nata ne hakan yasashi cewa "nayi Miki Alk'awarin"Murmushi tayi tace "Promise ABIY nasan kasan dai girman Alk'awari da illar k"in cika Alk'awari".



Dariya ABIY yayi yace "oh Najma badai iyayi ba Sannan yace eh. Naji na yarda shikenan dariya itama tayi tare da wara hannu tace "shikenan ABIY na"lakutar kumatun ta yayi yace "iyayi babe "dariya tayi a zuciyarta tana murnar burinta ya kusa cika .




Washegari kamar yanda Najma ta buk'ata wajejen 4pm suka shirya ita da ABIY sanye take cikin gajeriyar y'ar kanti d'inta pink anmata parking gashin ta sai shek'i da walkiya yake Tasha kyau sosai kamar ka sace ka ruga.




Har sun shiga Mota ABIY ya tuk'a Dan Najma tace shi zai tuk'a ba driver ba harsun fito get d'insu tace Yakaita gidan su Amera tare zasu tafi ba musu ya karkata motar shi ya kâita chan tana shiga ta iske Aunty nafesa tace .




"ta taho ABIY yace zata rakasu shopping ita da Amira har ta Musa Ummy ta harareta ba musu ta tashi ta shirya cikin Doguwar riga abaya Tasha kyau Kasancewar ta black beauty' ce Amira da Najma suka fara yin gaba da gudu suka shige back sit tare da SA lock ba yanda aunty nafesa ta iya sai front sit ta shiga tana Hararar su Najma Yar dariya sukayi Mata.




A gajarce tace wa ABIY "Ina yini"ba tare da ya kalleta ba yace Lafiya qalau ygd "Alhmdllh ta fad'a haka sukaje sukayi shipping, sosai su Aunty Nafisa ma ABIY yasa suyi Amma ita batayiba Amera kad'ai tayi ganin Hakan yasa yayi Mata da kanshi sosai ya saya Mata Kayayyaki Dan ko ba komai yanajin dad'in yanda take Nuna kulawa ga y'arshi.da soyayyar da take Nuna ma Najma (kunsan me d'a).






Hakan kuwa yayiwa Aunty Nafisa dad'i saitaji kunyar kin amincewa da soyayyar shi da tayi (Abba ya ce Mata ne ABIY ya ce yana sonta Dan karta k'i saurin amincewa).





Najma ko Amira cikin sauri suka gama daidaita plane d'insu cikin wayau Najma ta kwafe number Aunty Nafisa tayi save a wayar ABIY.




Bayan sun Koma An sauke su Amira da aunty Nafisa Saida Anty Nafisa tayi hug d'in Najma tare da ce Mata "Good bye My Dear ki kulamun da kanki "sannan tayiwa ABIY godiya ta wuce.





Suna komawa gida bayan sun huta after isha'i Nan Najma tace ABIY ya ara Mata wayarshi ba musu ya ara Mata Dan duk abunda Najma takeso tofa saiya Mata.




Whats app ta shiga ta yi sauri tayi search d'in aunty Nafisa da tayi save dazu Salam tayi Mata cikin sa a ta sameta Online tayi wslm Murmushin da ya fito Mata da fararen hak'oranta Najma tayi a Zuciyar ta tace "plane d'inmu Yana tafiya a daidai''


Nan suka Fara chat da Najmat kamar da ABIY take chatting Aunty Nafisa kanta Saida tayi Mamakin Abu Najma d'in da ko magana bayayi shine suke surutun Nan dashi a chat daga k'arshe ne Najma tace "Auntyn Najma Ina fatan sak'o na ya iso gareki fatan Zaki karb,'eni hannu bibbiyu"




Daram gaban Aunty nafesa ya fad'i ta d'an turamai da sticker dariya Mayar Mata Najma tayi da sticker Harara tare da cewa "Haba auntyn Najma ko ba Dan niba kodan soyayyar da kike yiwa najma yaci ace kin sammani ko kad'an ce daga cikin tata badon saboda ni ba please saboda Najma zakiyi jahadin Nan kinsan Najma tana buk'atar kulawarki a matsayin ki da uwa Gareta"





Karo da wannan sakon ya Sanya Aunty nafesa Murmushi lokaci guda taji Kuma tana son Auren ABIY ko Dan saboda Najma d'in Daya ambata ga wani dad'i da taji jin ya kirata mahaifiyar Najma hakan ya sata maida refly da ''uhm ba komai ABIY NAJMAT zanyi tunani insha Allahu.




"Zuwa yaushe kenan kinsan bana son a d'au nisa"Dan Murmushi tayi tatura Mai da "Gobe kamar haka insha Allahu "farinciki gurin Najma kamar ta kwala ihu a zuciyarta tace "NAGAMA dake Kuma aunty nafesa saura ABIY nasan bani da matsala da ABIY Saida ta goge chat din gaba d'aya sannan ta samu ABIY a d'akinshi ta mik'a Mai wayar Murmushi yayi yace angama game d"in kenan"






Gyda'a mashi kai tayi tace "ABIY promise d'in da kamun gobe ne fa zan fad'a Maka please ABIY karkace mun a a a komai zance kace mun ka amunce jawota jikinshi yayi yace "insha Allahu iyayi babe d'ina na amince Murmushi tayi tare da lafewa jikinshi ita kad'ai tasan farincikin da take ciki.




washegari Najma da ABIY suna garden Najma ce tace "ABIY nafad'a Maka Dan Allah kace eh "Murmushi yayi yace inajinki daughter"ABIY Dan Allah ka Auri aunty Nafisa please ABIY Ina sonta Ina son ta zama mamana Dan Allah kada kace a a "What ABIY ya fad'a Yace Najma a Ina kikasan wani Aure harkikemun maganar na Auri Wata to bazan aureta ba Kuma nakarajin Kinkuma maganar aure saina Sab'a Miki".




najma Bata tab'a ganin ABIY yayi Mata haka ba Aiko take ta rud'e tasa kuka da gudu ta nufi cikin gida tana kuka "dafe goshi ABIY yayi yace "meyasa nayima daughter tsawa sannan ya nufi hanyar data bi Dan ya Bata hak'uri Koda ya isketa palour ya taddata tana kuka lallashinta ya Fara Amma ta tubure tace Ita baruwanta dashi tunda bazai Auri aunty ta ba "Nan hankalin ABIY ya tashi saboda a rayuwar shi Babu abunda ya tsana sama da kukan Najma ko b'acin ranta Hakan ya sashi cewa .


"idan na amince shikenan kin hak'ura cikin kuka tace eh"Na amince Najma zan auri auntyn ki saboda farincikinki "lokaci guda Najma ta d'àgo tace "da gaske ABIY na"gyad'a Mata kai yayi yace "da gaske Daughter tunda Hakan zai maki dad'i na amince".





da gudu Najma ta fad'a jikin ABIY tare da cewa "I love you my ABIY"I love You More Daughter ABIY ya fad'a Yana D'agata sama Nan ya hau Mata wasa Saida ya sata farinciki sosai.



Najma ce ta bukaci da yataho su Tafi gidan su Amera yafadawa Aunty Nafisa Yana sonta wara idanu ABIY yayi yace "Again Kuma daughter"cikin shagwab'a tace eh Mana ABIY nidai saimunje " ta fad'a tana kamo hannunshi ba yanda ABIY ya iya yabi ta saboda Yana k'aunar farincikin Najmat zai iya Sadaukar da komai Akan farincikin tilon y'ar tashi.


suna isa Najmat ta fara yin gaba Murmushi kawai ABIY yayi Yana mamakin iyayi irin na Najma tana shiga da Amira tafara cin Karo rungume juna sukayi Suna tsalle Najma tace "Albishirinki
Dusti "...✍🏻




*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*




*GOD WE REPENT* 🤲🏼





_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss Hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*FREE BOOK*📒
_____________________________________
*PAGE 11 & 12*
_____________________________________



"Goro"inji Amera "ABIY ya amince"wara idanunta Amira tayi tace da gaske Dusti"eh Mana Dosti yanzu Ina Aunty Nafisa"tana palour inji Amira a palour suka iske Aunty Nafisa da Ummy suna Zaune"fad'awa jikinta NAJMA tayi tace ''i miss you my mom"miss you too daughter" Aunty nafesa tafad'a tana Shafa kanta.



Najma ce tace "Aunty ABIY na waje yace na kiraki"aunty Nafisa tayi mamaki kallon ummy tayi gyad'a Mata kai Ummy tayi tace jeki''.




Tana fita a Baki gate din gidan ta sameshi Bayan sun gaisa Kamar yanda Najma ta fad'a Mai haka yayi badon Yana son Aunty nafesa ba Saidan farincikin Najma Ba B'ata lokaci Aunty Nafisa tayi accepted d'inshi.




Abiy ya samu Abba yafad'a Mai ya amince haka Aunty Nafisa ma tace Mai ta amince Abba shi kad'ai yasan farincikin Daya shiga ba b'ata lokaci cikin Wata biyu Aka gama komai da komai na biki cikin Wata na ukku aka d'aura auran Aunty nafesa da ABIY Wanda Abba ne ya wakilce Aunty Nafisa ABIY kuwa shugaban componyn su Kasancewar musulmi ne ba ayi wani shagali ba ranar juma a aka mik'a aunty nafesa d'akin mijin ta.





Farincikin wajen Najma ba amagana Koda Ummy tace ta zauna wajensu k'iyawa tayi ita tana wajen ABIY d'inta da Aunty nafisar ta.




Kulawa ta musamman aunty Nafisa take bawa Najma ga wata shakuwa data Kara shigarsu ABIY tun baya son Nafisa dalilin kulawar da Yaga tana bawa y'arshi yaji ya Fara sonta haka suka ci gaba da rayuwa cikin tsaftattaciyar soyayya Mai birgewa.




B'angaren Najmat karatun ta take hankali kwance cikin nutsuwa Kokarin ta ya dawo kamar da Dan ta Koma d'aukar na d'ayanta.




Kwana a tashi ba wuya a gurin Allah ranaku naja haka watanni shekaru sunja Najmat sun kammala secondary school d'insu inda suka fito da Results Mai kyau yanzu haka Abiy Yana nema musu admissions ne ita da Amira.



Duk wani girma da budurtaka ya fara bayyana jikin Najma ga wani kyau data k'ara fuskarnan tayi fresh hancinta zuwad ga d'an k'aramun bakinta mai matuk'ar d'aukar ido Dara-daran maganan ta da su ne suka k'ara fito Mata da asalin kyawunta kallo d'aya zaka Mata kaga cikakkar. Y'ar Hutu da gayu ga class sanye cikin wasu English wears riga da wando tayi parking gashin ta gwanin sha'awa sai k'yalli yake zaune take a garden ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana kurb'ar drink hankalinta kwance.




Bugun dataji anyi Mata ta baya ya sata cewa "Wayyo Dusti Zaki jimun ciwo fa "dan tasan amira ce kad'ai ke mata haka juyowa gabanta Amira tayi itama taxama matashiyar budurwa kamar Najma Amera tana da kyau itama fara ce Saidai Bata Kai Najma ba jikinsu da tsawonta kamar na Najma shiyasama wasu dasun gansu suke cemusu twins ne ,"harararta Amira tayi tace''Tun d'azu nake nemanki Aunty Nafisa tace mun kina Nan ,"Murmushi Najma tayi tace "Allah sarki dusty sorry na walalar dake".




"Amira ce tace Wai ya Maganar koyon driving d'in da kikace zamuyi kinsan admissions d'inmu Yana gab da fitowa ,"Wallahi Dusti nayima ABIY magana so yace zaiyiwa Wanda zai koya manan magana Kinga yau Friday to Monday yace zaizo ya fara koya Mana kinsan bazaiyu ace kamar mu classic Ladies bamu iya driving ba "Dariya Amira tayi tab'awa sukayi "Najma tace ai harna k'agara mu shiga school d'innan zamu Basu wuta "sosai ma dusti,"inji Amira Nan suka zauna suka cigaba da tattaunawarsu akan Show d'in da zasuyi a university.


Sai yamma likis suka koma cikin gida a kitchen suka tarar da Aunty Nafisa tana abincin dinner"sorry momyna kawo mu k'arasa jeki ki Huta "cewar Najma tana Amsar tray d'in maggi a hannun aunty Nafisa Murmushi aunty tayi tace "ai nama kusa Karasawa daughter kawai barshi jeku ku d'an gyara mun palour"to suka Amsa a tare sannan sukaje suka gyara palour suna gamawa ana Kiran Salla.




suna gama Sallah Aunty Nafisa ma tayi Nan suka zauna Aunty Nafisa ta fara Yi musu k'arin q'ur'anin da take musu kafin malamin su yazo sun iya dayake malami yake zuwa har gida ABIY ya d'aukeshi yake koya musu karatu ita da Amira Dan yanzu Amira tadawo gidan Dan bazata iya zama gidan su ba ba Aunty Nafisa ba Najma Ummy ba yanda ta iya sai hak'ura sukayi Amma kullun suna zuwa gidan rabi suna gidansu Amira rabi suna gidansu najma.



Tana gama musu k'arin ABIY yashigo da gudu Najma kamar yarinya ta ruga ta rungumeshi tace "wellcome my ABIY"Murmushi yayi tare da yayi kamar zai D'agata ya kasa Aiko Nan suka kwashe da dariya duka palourn "ABIY ma dariya yayi yace kinyi nauyi daughter"cikin shagwab'a tace "ABIY ni saika d'agani"dariya yayi yace "Jiya ba yau ba daughtern ABIY bakiga kingirma"hararar wasa Aunty Nafisa tayi Mata tace ",Daga dawowarshi Baki bari ya huta Zaki fara ko''d'an turo Baki Najma tayi tace "to Aunty na barshi ya huta shikenan dai ko''dariya aunty Nafisa da Amira sukayi....✍🏻








*Dan girman Allah idan kun karanta kiuyimun sharing fisabilillah*




*GOD WE REPENT* 🤲🏼





_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss Hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*FREE BOOK*📒
_____________________________________
*PAGE 13 & 14*
_____________________________________



Bayan aunty Nafisa tayiwa ABIY sannu da zuwa rakashi tayi d'akinshi tare da taimaka Mai yayi wanka Sai Sanya Mata albarka yake Nan suka fito sukayi dinner d'insu gabak'i Dayansu gwanin sha'awa.



Saida Najma da Amira suka Kara yima ABIY magana akan koyan driving d'in Nan ya shaida musu Monday su shirya zai kaisu makarantar koyo 2 weeks sun k'ware murna gurin Najma da Amira ba amagana aunty Nafisa ce tace.





''Allah ABIY Kai kake D'aure ma yaran Nan gindi duka nawa suke 16years in Banda iyayi irin nasu zasu fara wani driving"Bata Rai najma da Amira sukayi Najma tace "Aunty kullun saiki dinga Mana kallon yara bayan mu manya ne university fa zamu shiga.




"Hararar wasa Aunty tayi tace "Ina girman yake Wanda har yanzu Shan yatsa kike"dariya Najma tayi tace "ai yanzu nadaina ko my ABIY"Murmushi ABIY yayi Mata yace "gaskiya ne daughter yanzu kungirma kunzama manyan yara "dariya sukayi Najma tana jin dad'in yanda ABIY ke kod'asu.





Ranar Monday kamar yanda ABIY ya fad'a haka yaje yayi musu registration a makarantar koyon driving hankali kwance aka fara koya musu Dan a ranar ma sun iya abubuwa sosai.



*NIGERIA*🇳🇬
*KADUNA*



Farin matashin saurayine Wanda a sheekaru bazai wuce shekaru talatin ba kykkyawane ajin farko farine irin farin Nan Mai kyau ga bakin sajenshi Daya k'ara fito mashi da kyawunshi duk inda karshen kyau yake tofa Yakai akirashi Dashi gashi da murdaddan jiki Ga fad'addan k'irji.



Sanye yake cikin k'ananan kaya sunyi mugun k'arb'arshi tuk'i yake cikin nutsuwa yazo daidai wajen Bada hannu an tsaidashi waigawar da zaiyi ya hango Sa'adatu na driving itama an tsaidasu gefenta ya hango khairat.



"what khairat da Sa'adatu watau duk kashedin da nayiwa yarinyar can na ta rabu da waccen Yar iskar bataji ba kenan dandanan Ranshi yayi mugun b'aci yau shikadai yasan irin rashin mutuncin da zai kirtawa khairat idan suka koma gida Mai rabashi da ita sai Allah saboda a duniya babu abunda ya tsana sama da ya hana mutum abun sannan ya aikata a ganin shi wannan karshen raini ne.




Ana Basu hannu Kai tsaye gidansu dake G R A ya nufa daidai wani katafaren gida Mai matuk'ar girma da tsaruwa Wanda kaf ilahirin manyan manyan gidajen area ya keresu a kyau da tsaruwa horn yayi security d'in bakin k'ofar suka wangale Mai gate Yana shiga katafaren parking space din gidan ya nufa Wanda tamk'e yake da manya manyan motoci na alfarma.




Fitowa yake cikin takun k'asaita kallo d'aya zaka Mai kasan ranshi yayi k'ololuwar b'aci Kai tsaye part d'in aunty Amarya ya nufa Yana danna belt Wata kyakyawar yarinya da Baza wuce shekaru hud'u ba ta fito tana kallonshi tayi Murmushi tace ,"sannu da zuwa Yaya"yawwa sannu fena ya fad'a Yana Kama hannunta suka shiga.





Zaune ya iske Aunty Amarya a kan sofa sanye da glass medical cikin shigarta ta alfarma kallo d'aya zaka Mata kaga chikkar Yar boko da gayu tana duba wasu takaddu Jin sallamarshi yasanyata d'agowa tare da fad'ad'a fara'arta tace.



"Likita bokan turai har andawo kenan"wallahi ko aunty nadawo Nakwaso gajiya Allah sa akwai fruit salad ya fad'a Yana zama kan sofa"




Murmushi aunty Amarya tayi tace "Sannu son daga gani kashawo gajiya ai Aikinku ai ladar ku Allah ne kawai zai iya biyanku sannan tace "Ai fruit salad kodan saboda Kai dole na ajeshi sannan tace "fena jeki kan dining ga Jug chan daukoma yayanku.



"Allah sarki my aunty shiyasa nake sonki Allah barmanake Auntynmu"Murmushi tayi tace "amen son" bayan fena ta d'auko Mashi fruit salad d'in cikin nutsuwa yagama Sha sannan ya tashi yace Naji amfara Kiran magriba bari naje nayi salla na wuce b'angaren umma Murmushi kawai tayi tace Agaishesu.



Yana fita masallacin gidan yaje ana gama Sallah b'angaren Umma ya nufa dubawa yayi ko zaiga motar dasu khairat suka fita da ita kosun dawo Yaga basudawo ba hmmm yafad'a Dan shi kad'ai yasan irin rashin mutuncin da zaiwa khairat danshi Babu ruwanshi da Sa'adatu duk iskancin da zatayi tayi ita kad'ai Amma bazai yarda Ya zuba Ido ta lalata mai k'anwa ba.




A palour ya tarar da Umma tana kallonshi ta kauda Kai tare da Jan tsaki har k,'asa ya tsugunna yace "umma Ina yini"Tsaki ta Kuma ja tare da juyowa tace "da ban wuni ba ka ganni eh *NAJIB* nace Ina buk'atar gaisuwar ka ne Watau har waccen matsiyaciyar juyar mayyar tafini daraja da matsayi a wajenka saika fara zuwa gaisheta tukwana ni to bana buk'atar gaisuwar taka Ka Koma wajen uwar taka Ka had'a Mata da tawa bana buk'atar gaisuwar taka maza Koma wajen uwar taka *NAJIB* kaima na barmata ta zama uwarka .......✍🏻





*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*



*GOD WE REPENT* 🤲🏼



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[9/28, 7:52 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
_____________________________________

*Writing by*✍🏻
*Hajara L Sadeq*
*Miss Hajo*🖤

_____________________________________
https://www.instagram.com/hajara_l_sadeq?r=nametag

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*FREE BOOK*📒
_____________________________________
*PAGE 15 & 16*
_____________________________________



Dukanku na hakura daku fad'a kawai take Inda ta shiga ba tanan take fita ba shidai NAJIB yayi shiru dan Idan da sabo ya Saba da fad'an Umma harta gama fad'an ta baice uffan ba tunda ya bata hak'uri sau d'aya Bai Kuma magana haka tagama ta gaji Dan kanta Murmushi kawai yayi yace "Umma zanwuce Saida safe Bata ko d'ago ta kalleshi ba har ya wuce.



Koda ya dawo daga isha 'i Saida ya hanga ko zaiga motar dasu khairat suka tafi da ita Amma baigantaba duba agogo yayi Yaga har 9 "shikadai yasan irin hukuncin dazai yankewa khairat.





Washegari around 7am ya fito cikin shigar k'ananan kaya da sukayi mugun karb,'arshi yayi bala in kyau bayan yaje ya gaishe da Umma dukda ciki_ciki ta amsa Yana Shirin shiga Mota ya hango Aunty Amarya ta fito da alamar wajen aiki zataje.




Karasawa

Please Login or Register in order to submit comment