Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun Ina yarinya Idan nayi mashi maganarta Saiyadinga lallashina yace zaikaini wajenta Harnafara wayau ganin Na takura mashi Da zancenta Wani time din yakan cemun kada Na k'aramai maganarta bazai had'ani DA itaba kozan Mutu Nasan lokacin DA yacewa su Abba ta rasu Amma wallahi Bata Mutu ba tafad'a tana rushewa DA Kuka.



"Najib jikinshi ne Duk yayi sanyi Jin labarin ya lura DA Kamar akwai abunda Abiy Ke boyewa Wani tunani.yayi yace to Ko ba y'arshi bace wata zuciyar Kuma tace "Kamanninsu tafi karfin Wasa Tabbas mahaifinta ne Amma Kuma meyasa yake b'oye asalinshi.



Jin kukan nata yayi yawa ya sashi Had'e Rai yace "Wallahi Idan bakiyi shiruba Zan fasa taimaka Maki ki had'u Da mahaifiyartaki''Lokaci guda ta had'iye kukan tare Da cewa "Dan Allah Kayi Hak'uri nayi shiru to".handkerchief ya mik',a Mata yace "goge hawayen "ba musu ta amsa Ta goge Tana shak'ar dad,'ad'an k'amshin dake jikin.handkerchiep d'in "Tashi yayi yace "Muje Na Rakaki''Murmushi tayi tace to tare DA Tashi suka jera suka Tafi.




Daidai gate d'insu ya tsaya yace "zanwuce Bani Handkerchie d'ina "mak'e kafad'a tayi tare DA rugawa tayi bakin get d'insu ta juyo tana dariya tace "goodbye handkerchief Dai ya Zama Nawa "ta ida fad'a tana shigewa gida tana dariya.




murmushi kawai yayi Yana jinjina k'uruciya irin ta Najmat Kamar ba itace ta gama Shan Kuka ba juyawa yayi Yana murmushi Shi kad'ai.




Washegari wajen 6:Pm zaune suke a garden d'in d'in gidan su Amira ,"Najmat ce tace ''Yaya Bani labarin Nigeria"Yana Danna waya Batare Da ya d'agoba yace "Bazan bayarba baki tab'a zuwa bane"B'ata Rai tayi tace "Uhm Dan Allah Yaya Bani bantab'a zuwa ba Kuma Ina son zuwa"ban iya Bada labari ba yafad'a Yana Mai kallonta "Itama kallonshi tayi cikin shagwab'a tace "To fad'amun Sunan state d'in dake Nigeria da sunan garuruwan'' Tsayawa yayi kallon ta baitab'a ganin wacce shagwab'a keyiwa kyauba Kamar Najmat shagala yayi DA kallonta Yana K'ara ganin tsantsar Kamarta DA Ummanshi 'hure Mai Idon DA tayi ne ya fargar dashi fusgewa yayi ''yace kinfasa shopping d'in dakikace zakije.


"Lah ,Na manta Duk kai katsaidani tafad'a tana Tashi tace Bari naje nashirya ka Rakani Bata jira amsarshiba ta fice tayi part d'insu cikin minti baifi Goma ba ta shirya ta fito cikin Arabian gown black tayi nadin labarawa tunda Ta tunkaro wajen Najib Ke kallonta bako kiftawa baitab'a ganin macen DA Duk shigar DA tayi kyau take Kamar Najmat ba yashagala sosai DA kallonta Saida yaga tazo gab dashi tukwana ya fusge Yana kallon Wani wuri Dan Kar yarinya ma ta rainashi.



Shike driving tana front seat tana Mai dariya Wai shikenan Daga yanzu yazama driver d'inta Murtukewa yayi yace "Allah zakija Na koma''hade hannu biyu tayi tace "Sorry my friend bazan sake ba"Murmushi yayi yaci gaba DA tuk'i yace "Amirar fa "murmushin DA ya lotsar DA dimple d'inta tayi tace "Ai yanzu fushi take damu Wai kayi Mata k'wacen k'awa yanzu dakai nake Abota "Murmushi kawai yayi baice komai ba harsuka Isa.



A Mota ya jirata Dan bayason fita " Saida tagama shopping d'inta Tazo wajen biyan kud'i ta d'aga Jakarta ta d'auko A T M d'inta tana mik'a musu Taji ance "Anbiya "Tambayarsu tayi waya biya Mata nuna Mata Wani matashin saurayi sukayi ''Kallonshi tayi cikin harshen Hindi tace ''Wayace ka biyamun Zan biya DA kaina"Murmushi yayi Mata yace "I am sorry""Tab'e baki tayi tare DA.maida a t m d'inta tace "Thnks "sannan ta nufi Hanyar fita Binta yayi Yana Mata magiya akan ta bashi number wayarta Amma ta hanashi Ba irin rokon DA Bai mataba Amma fir tace Bata DA waya ganin Zai janyo hankalin mutane wajensu yasata tsayawa tare DA bashi whorng number godiya yayi Mata Yana murnar Jin Dadi Dan ba k'aramun tafiya DA Imaninshi babe d'in tayi ba



Najib dake Mota tunda yaga fitowarta yaga saurayin dake Binta a Baya Yana Mata magana Har zuwa lokacin data bashi number hakanan kawai yaji ranshi ya b',aci Dan ya tsani yaga namiji Nabin.mace tsaki yaja a ranshi yace "itama Ina ganinta Mai hankali harta tsaya Bawa Wani sakarai number" cigaba Da Danna wayarshi kawai yayi.



Tunda tashigo taga ya sauya tayi Mai magana yace bakomai Har suka Isa gida baimata Magana ba Saida zata fita tace "Dan Allah me namaka "Murmushi ya k'irkiro yace bakomai kiyi Maza ki Shiga gida Kar Abiy yayi Maki fad'a '', murmushi kawai tayi tace "Goodnight"Have a nice dream yafad'a Shima Yana barin wajen.





Shak,'uwace sosai ta k,'ara Shiga tsakanin Najib Da Najmat Wanda ba Wanda baisani ba cikin Gidan nan hatta Abiy Dan su d'aukarsu ma soyayya ce suke Amma su bangarensu kawai Abota ce suke yanzu yarage saura y'an satittika Najib ya gama Masters dinshi Wanda su Najmat Kuma Suna level 3 zasu Shiga 4.




Da misalin karfe ,8pm
Kwance take cinyar Ummy Najmat ce tace "Ummy Wai yaushe Zaku Nigeria "Shafa kanta ummy tayi tace "nan Da 1 months kinsan bikin Sarat Da khairat saura Shati shidda "Tashi Najmat tayi tana kallon ummy tace "Lah ummy Kuma Lokacin Muna hutu Wanda damun Koma zamu Shiga level 4"DA Fara arta ummy tace "Kai Masha Allah Kinga DA Abiy zaiyarda saimu tafi tare tunda Kinga DA Dustinki zamu tafi''Najmat Kamar zatayi Kuka tace "Ummy Dan Allah kiyimai Magana yabarni mutafi tare inason zuwa k'asar "Amirace ta fito daga kitchen tace ''Eh wallahi Dusti Ni Idan bazai barki Bama Nima Na fasa zuwan saimu zauna kawai "Ummy ce tace Ku kwantar DA hankalinku insha Allahu Zai yarda mutafi taren Amma Najmat kifara mashi maganar kiji Idan Zai Bari kafin muyi Mai maganar.



Murmushi Najmat tayi tace to ummy yanzu ma zanje nafada Mai tafad'a tana Tashi "Dariya ummy tace kajimun sarkin zumud'i "Dariya Najmat tayi tace "Ai ummy kinsan komai DA zafi_zafi yafi "Amirace tace "Allah sa ya yarda Dai "ameeen Najmat tafada tana ficewa.




Najmat ta Samu Abiy Har dakinshi Yana zaune Yana Aiki DA laptop Bayan tagaisheshi ya amsa cikin so da k'aunar Y'ar Tashi nan Najmat take fadamai tana son Binsu ummy Nigeria Idan zasu tafi.



Ganin irin kallon Da Abiy Ke Mata yasata Shan jinin jikinta tace "Abiy Daman Saifa Idan ka yarda Idan baka yarda ba saina hak'ura"ta ida fad'a Kamar zatayi Kuka " Abiy dake Kan gado laptop Na hannunnshi sake duban Najmat yayi dake durkushe k'asar carpet din gadon yace "To ban yarda ba Babu inda Zaki Karki sake zomun Da maganar wannan kowace irin k'asa kikeson zuwa a fad'in duniyar nan kifad'amun zankaiki Koda kuwa kwana d'aya zakidingayi kina dawowa Amma Banda Nigeria Karki K'ara kawomun shirmen maganar nan hope kinfaminceni''Gyada Mai kai tayi kawai Dan Idan tace zatayi Magana zata iya Kuka ficewa tayi Daga d'akin Saida tafita ta fashe da Kuka tare DA rugawa bedroom d'inta ranar kwana tayi tana Kuka.




Washegari Duk Wanda yaganta yasan Tasha Kuka tana Tashi Bayan tayi wanka tayi Sallah tan a break fast Aunty nafisa Na kallonta tace "Dear Naga idanunki sun kumbura Ko Kuka kikayi"girgiza kai tayi tace "a a kaina Ke ciwo"Subhanallahi Aunty nafisa tafad'a Sannan tace "Kinsha magani kuwa?, Gyad'a Mata kai tayi tace eh nasha "to Allah ya sawwake "Ameen Najmat tafada tana Gama breakfast Wanda lakutar abincin kawai take ta Tashi tace" aunty Bari naje gidansu Amira Gyad'a Mata kai kawai tayi tace "Adawo lafiya.



A compound din gidansu Amira ta Tarar DA Najib Na Shanya Kaya "k'arasawa tayi wajenshi bailura Da itaba ta d',Aiko haki a hankali ta d'osanamai a Bayan wuya SA Yad'an firgita dariya tasanya tace "Namiji DA tsoro"Hararta yayi yace "Kinrainani Ko Najmat ,"Dariya tayi tace "a a a nidai banceba sannan tace wanki kake Kenan "Yana Shanya kayan yace "wallahi Ko Wai Saboda exercise "Gyad'a kai tayi tace ''Maimakon ka kirani na tayaka "tafad'a tana Amsar bucket d'in hannunnshi taci gaba DA Shanya kayan Suna Hira Abba ne ya hangosu yayi murmushi Yana Raya Wani Abu a ranshi.




Saida ta gama shanyawa ya kalleta yace"Yadai Naga idanunki sunyi ja Kuka kikayi ne? kanta sadde tace " a a a "B'ata Rai yayi Yace "Zaki b'oyemun Wani Abu NE GA idonki nan ya kumbura Daga Gani Kuka kikasha ',fad'amun waya tab'aki Ko yayi Miki Wani abun'',



Cikin murya Kamar zatayi Kuka tace "to ba Abiy bane ''saikuma tayi Shiru ta sadda kai ''d'ago Mata kanta yayi yace ''Abiy yayi me "Kuka ta fashe dashi tace "Shine yace Wai bazanbi su Ummy bikin DA zasu Nigeria ba Kuma inason inje"ta ida fad'a tana rushewa DA Kuka.



Ganin irin Kukan DA take Har cikin ranshi yake jinshi baisan lokacin Daya janyota jikinshi ba tare Da Fara bubbuga bayanta cikin sigar lallashi yace "Calm down my friend kibar Kukannan haka yafad'a Yana K'ara daddaba bayanta Kamar yanda Ake lallashin jariri.




NAJMAT shiru tayi Sai ajiyar zuciyar kawai Take saukewa ajere-ajere K'ara lafewa tayi jikinshi tanajin daddad'an k'amshin turarenshi Mai Wani sihirtaccen k'amshi lokaci guda Taji wata nutsuwa Na ratsata Najib Ko wata kasalace saukar mashi sunkai 5 minutes a haka batare DA Kowa ya sake cewa uffanba........✍🏿



*Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[11/7, 8:13 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴

*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{ *Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa* }_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo


*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
___________________________________
*PAGE 45 & 46*
____________________________________

Gyaran muryar Da sukaji ya fargar dasu Najmat ce tafara zamewa cike DA Jin kunya sannan Shima ya zame Amira suka gani kansu itama tana d'an sadda kai alamun Kamar dariya take Harara Najib ya Galla Mata yace ''ubanme kike anan''d'an marairaicewa tayi tace ''Uhm Yaya Daman dusty nazo Nema"tsaki yaja tare DA Tashi yawuce.



Saida Amira taga yayi Nisa tukwana tasa dariya tace "jibeshi Da Allah waini zaigwadawa borin kunya"Najmat ce ta Tashi tace"kede wallahi Kinshiga ukku DA gulma "Dariya Amira tayi tace "Kai dusty Amma fa kunfad'a DA yæwa"cikin Rashin fahimta Najmat tace "Kamarya"Amira Na dariya tazauna kusa DA ita tace "keda Yaya Najib mana"Lokaci guda Najmat ta Hade Rai tace "me kike nufi" Dan daidaita dariyarta Amira tayi tace''Soyayya kuke kidaina ma Wani b,'oye b'oye najima DA Gano Ku"Lokaci guda Najmat ta had',e Rai tace "dusty bansan iskanci tun ba yau ba nafada Maki kidainacewa Muna soyayya DA Yaya Najib Ni friendship ne kawai muke Amma ba soyayya ba meye wata soyayya shirme kawai tafad'a tana Jan tsuka"Danne dariyarta Amira tayi tare DA tab'e baki tace "Uhm in tayi tsami Maji sannan tace "Wai ya kukayi Da Abiy yabarki kuwa".




Kamar zatayi kuka tace"Ya Hana"Subhanallahi Amira tafad'a tace "kai Amma banji Dadi ba sannan tace muje kifadawa ummy nasan k'ila Idan tayi Mai magana yabari .




A palour suka Tarar DA Ummy tana Breakfast"gaisheta Najmat tayi Ta amsa Mata tare DA cewa "Ya y'an gidan naku''Lafiyansu qalau Najmat tafada tana Zama Kan sofa "madalla ummy yafad'a "Amirace tace ''ummy Wai Abiy yace bazatajeba "Ikon Allah ummy tace sannan tace "to shikenan tunda Bai bariba Najmat kiyi Hak'uri Ai akwai next time.



Kuka Najmat Tasa tace "Ummy Dan Allah kiyimai Magana wallahi inason zuwa "Ajiyar zuciya ummy ta sauke tace "to zanjaraba Karki damu .




Ya rage saura kwana biyu tafiyar su Ummy 9ja Wanda lokacin Najib yagama Masters dinshi Da Sati biyu Wanda tare zasu tafi Duk sunyi parking komai Najmat Duk tayi sanyi , zaune suke a palourn ummy "ummy ce tace "Dear Ko baki Da lafiya Naga Kinyi sanyi tun Jiya"Batare Da ta d'ago kantaba Saboda hawayen dake k'ok'arin zubomata tana kokari maidasu Amma ta kãsa"Ya Allah Najmat Kuka Ko ummy yafad'a tana Zama kusa DA ita tare DA tallabota .



,"kukan DA Najmat Ke rik'ewane ya zubo Mata lallashinta Ummy tafara tace "ya Isa haka meye damuwarki Najma kike.kuka ,"cikin shahshek'ar Kuka Najmat tace "Ummy shikenan tafiya zakuyi Ku barni nikadai ba dusty Dan Allah kiyiwa Abiy Magana nasan zaiji maganarki"Daddaba bayanta ummy tayi tace "toyi shiru Bari Na Samu Abba nafada Mai zaiyi Mai magana kinji "Gyad'a Mata kai Najmat tayi.




Abba Na dawowa ummy ta fad'a Mai Najmat Nason zuwa Amma Abiy ya Hana ''cike DA b'acin Rai Abba Yace "dayake sayar Mai DA Y'ar za ayi Dan tace tanason zuwa zaihana Ai yayima Kara dakanshi yace atafi DA ita Dan Rashin yarda Ai Anriga anzama daya sannan yace zansameshi gobe Idan nadawo. Daga aiki.




Har gida Abba ya samu Abiy yace "Haba Muhammad Yanzu Dan Najmat tace zatabi su Amira 9ja Zaka Hana saikace za'a sayar Maka DA y'a Koko Har yanzu Babu yarda tsakanin mu a Tunani Na Anriga anzama d'aya tunda Har mun Hada zuri'a a Tunani Na Ina DA Iko Akan ka DA y'ay'anka Amma tunda ka gwadamana iyakarmu bakomai.


Abiy ne yace ''Abban Amira bahaka bane wallahi kana DA Ikon komai Akan Najmat Dan Allah Kayi Hak'uri Na yarda SU tafi d'in Allah kiyaye hanya ya kaisu lafiya ya maidosu lfy, " Abba ne yace "yawwa haka nake sonji tunda tana so taje Ko kaifa daganan sukayi musabaha.





Kwance take ta d'ora kanta cinyar Aunty nafisa Abiy ya Shigo Sannu DA zuwa Aunty nafisa tayi Mai Sannn Najmat tace "Abiy sannu DA zuwa "kallonta yayi yace "Ke yanzu Najma Dan nace bazakije 9ja ba shine zakije ki had'ani dasu Abba Ai kin kyauta "NAJMAT Kamar zatayi Kuka tace ''dan Alla Abiy kayi Hak'uri aitunda kace bazanjeba Nama hak'ura Dan Allah Kar ranka ya b'aci Kar Kayi fushi dani "yaso yayi Mata fad'a Amma ya fasa Saboda yanda yasan Najmat Ke kiyaye b'acin ranshi DA Kuma yanda take Mai biyayya Hakan yasashi k'irkirar murmushi yace.



"Taya za ayi. Abiy yayi fushi DA Najmat dinshi "Tashi Najmat tayi tare DA rungume Abiy tace "Thnks you uba Na gari"Shafa kanta yayi yace "Na Bari ki bisu Allah ya kiyaye hanya "Zaro idanu tayi tace "DA gaske Abiy ,"Gyad'a Mata kai yayi Yana. Murmushi K'ara Rungumeshi tayi tace "wow Abiy I am very joyful nagode my Abiy Allah ya barmun kai Allah Saka Maka DA alkhairi"Cike dajin dad'in addu'ar y'artashi yace "Ameeen daughtern Abiy Allah yayi Miki Albarka. Aunty nafisa Dai murmushi kawai tayi tace "To konima nabisu Abiy Najmat"Harararta yayi yace "ohhh wayau zakumun Kenan Duka Ku tafi Ku barni to ban yarda ba "Dariya Najmat tayi tace "Gaskiya aunty ban yarda ba a tafi abar Abiy Na Shi kad'ai a gida "Pillow Aunty nafisa ta tilla Mata tace "Ohhh Ke Zaki tafi Niko oho Ko?Dariya Najmat tayi tare dayiwa aunty nafisa Gwalo tace "Badai inda Zaki bimu Kina gida tafad'a tana rugawa dariya Abiy yayi yace "yawwa shikenan ma Najmat ta Hana Kinga ba inda Zaki "B'ata Rai Aunty nafisa tayi cikin shagwab'atace "To Ai satin bikin ka barni muje plx abban Faruq"murmushi kawai yayi yace "kema rigimarce irin ta Najmat Ko "uhm Dan Allah abu Najmat kasan baikamata ace Banje bikin ba Kuma kaga Nadad'e Banje gida ba " Abiy ne yace "zolayanki nake aidole kije yaza ayi Na hanaki zuwa Allah ya kaimu lokacin.



Najmat DA gudu ta nufi gidansu amira DA zumud'inta Dan tayimata albishir "A bakin gate taci Karo DA Najib baya tayi Tana huci tace "Sorry ban Lura DA kai bane,"Yana kallonta yace ''gudun Me kike Kamar wata yarinya"tana huci tace ''Yaya Amira zanyiwa albishir Abiy ya yarda za a tafi Dani 9ja "inye kaji bak'auya zataje 9ja''ciikin shagwab'a tace ''Uhm nidai Allah ba bak'auya bace ,Kuma ma Ai India tafi 9ja komai"wara manyan idanunshi yayi yace "A Ina India tafi Nigeria k',asar da Duk inda kayi saikaci Karo Da gumaka"Dariya Najmat tayi tace "mu Ina ruwanmu Da shaggun gumakansu sannan tace ''Ina Zaka naganka DA key ".



Unguwa zani Ko Zaki Rakani ?Gyad'a kai tayi tace "Eh; muje"tafad'a tana binshi parking space juyowa yayi ya kalletata yaga Daga ita Sai doguwar rigar bacci Harararta yayi yace ",wazakibi a haka"kallon jikinta tayi taga normal take cewa tayi ,"me Kuma nayi,''"A haka DA wannan tsinannun Kayan Zaki bini''kara duba kayan jikinta tayi cikin shagwab'a tace "to me kayan nau sukayi Kuma "Tsaki yaja yace "to bazakibini ba ''turo baki tayi tace ''aidaman Bani nace zanbikaba kai kace Na rakaka "Murtukewa yayi yace ''gidan ubanwa nace ki Rakani "K'ara turo Baki tayi tace "ba asaniba mutum Sai zagi Kamar babaguje(Bamaguje ne takeson tace Dan Taji Wani time din Idan Amira tayi zagi ummy saitacemata wannan zagin saikace maguzawa shine itama take so tace ) "Wara idanu yayi yace Dani kike "Tsaki taja tace "Ehd'in tafad'a tare Da murgud'a baki tabar wajen tayi cikin gidan.



tsaye yayi a wajen tare DA Jan Tsaki yace "Mai Hali Baya fasa halinshi Yana.mamakin yanda kwata_kwata yarinyar Bata tsoronshi Ko kad'an Bata shakkar gayamai Magana sannan yakuma Jan tsakin haushin yanda suke shigar turawa Ko ajikinsu sun d'auki al'adar wasu sunmaidata tasu.




NAJMAT tana Shiga tayiwa Amira DA Ummy albishir Abiy ya Barta zokuga murna wajen Amira Hada Rawa ummy Dai dariya kawai take musu.





Yau ta kama tafiyarsu 9ja Wanda jirgin K'arfe Goma Na safe zasu Hau sungama parking d'insu Na komai Najib ma yagama parking dinshi haka su Najmat Abiy ya zuba Mata kud'i sosai a account d'inta Koda zata buƙata Haka sukayi bankwana dasu Abiy DA Aunty nafisa Ji take Kamar tabisu Najmat Sai murna take yau zataje k'asarta ta Haihuwa Najib ma daka Ganshi kasan Yana cikin farinciki dukda baka fiya ganin fara'arshi ba haka Amira DA rabonta DA ƙasar tun tana yarinya haka ummy ma Abba DA Abiy sukayi musu rakiya Har airport Najmat taso. Tambayar Abiy Koda d'aya Daga cikin danginshi yafad'a Mata ta had'u dasu Amma tana tsoron ɓacin ranshi Hakan yasa tayi Shiru DA bakinta tunda Dai tasamu ya Barta Zatajema alhmdllh .




Saida su Abba DA Abiy sukaga tashin jirginsu tukwana suka Koma gida sabida Abba Sai ana Fara bikin Shima zaitafi cike DA kewar ƴarshi Abiy ya koma gida.




Tafiyar 24hours takaisu Nigeria NAJMAT Suna sauka Bayan sunfito Daga jirgi Sanye suke cikin Wata mayyar pink din Abaya itada Amira sunyafa k',aramin belt din rigar kallo ɗaya Zaka musu kasan Suna cikin farinciki sunyi kyau dukda gajiyar dake tattare dasu kallon Wurin ta tsayayi tana murmushi Ta furta Alhamdulillahi wata nutsuwace ta saukar Mata lokaci gudaWani farinciki ya mamayeta Annashuwa kawai take tare godewa Allah Daya kawota ƙasar ta Haihuwa .



Kai tsaye gidan Hajiya suka nufa Bayan driver yazo ya d'aukesu Najmat Dai tun a Mota suke ƙarewa garin kallo itada Amira Ummy Dai dariya tayi musu tace "Suna Mata k'auyanci ".



D'aid'aya suka Fara Shiga Palourn Najib ne yafara Shiga hajiya cike DA farinciki ta taryashe tare DA rungumeshi Dan ba ƙaraamun kewanshi tayi ba nan ummy ma tashigo ita DA Amira hajiya Sai sannu DA zuwa takeyimusu itama Dai Daka ganta kasan tana cikin farinciki.



ganin Mai shigowa ta k'arshece ta Sanya hajiya yin saranda kallonta ta tsayayi bako k'iftawa Itama Najmat Kallon ta ta tsayayi Najib. DA Ummy Zama sukayi DAn sunsan anrina "Cikin ƙarfin Hali hajiya.ta Matsa kusa da ita Wanda DA ƙyal take iya ɗaga ƙafafunta dafo ta tayi tare DA shafa fuskarta ta murza idonta taga Ko idonta ne Keyi Mata Gizo Dan Sak jidda take Gani gabanta lokaci Da take budurwa.



Najmat Dai tsaye tayi Don tun shigowarta Ido hud'u DA tsohuwar datayi Taji Kamar ta had'u Da wani gudan jininta ƙara shafa fuskar Najmat hajiya tayi cike DA mamaki tace Jidda....✍🏿




*Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*





_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[11/9, 9:07 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴

*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{ *Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa* }_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*
________________________________
*PAGE 47 & 48*
________________________________

"Jidda Kuma "Najmat ta fad'a a ranta Ummy ce tana Murmushi tace"Hajiya Jidda Kuma tayaya Jidda zata Koma haka "juyowa Hajiya tayi tace "ohhh Ashe fa Jidda nace Allah Mai iko naga kamarne tayi yawa ''itadai Najmat tsaye tayi tana tunanin wace Jidda ce Ake cewa suna kama .



Ummy ce tace "kawai kamar halittar Allah ce sannan tace daughter ku k'araso kuzauna kunyi tsaitsaye sai sannan su Najmat suka Samu suka zauna cike da girmamawa Najmat da Amira suka gaishe da Hajiya ta amsa musu tare da cewa "ya gajiyar Hanya"Alhamdulillah suka fad'a a tare Hajiya dai har lokacin idonta nakan Najmat kallo Ummy tayi tace ''waiko hauwa'u ce ta girma Haka Ta Koma kamannin takwararta.



"Dariya Ummy tayi tace "Hajiya Wannan ba Amira bace sunanta Najmat sannan ta Nuna Mata Amira dake gefen. Najmat tace ,"Kinga Amira nan''Ohh Allah Mai iko Dan Kar ace tafiya magana taja bakinta tayi shiru.




Najib ne yace "My Amarya me kika tanadarwa me gidan ne "Murmushinsu na Manya Hajiya tayi tace "Ai komai ma na tanadarwa Mai gida guda ''d'an Murmushinshi na gefen Baki yayi tare da Shafa sajenji yace "Kice yau d'an gata nake sannan yace Wai Ina yaran Nan"Ai idan da abunda yafi d'an gata ma yau Kaine Mai gidan sannan ta tab'e Baki tace "Malalatan yarannan dai zakace suna ciki suna baccin Asarar da suka Saba tunda ka kawomun wannan shegiyar harirar Ta lalatamun sauran Khadijar da saratun Ba tsiyar da suke tsinanamun Saidai su ci suyi bacci Ai Saida ka tafi naga mugun amfanin ka nasan da kana Nan da Kai kad'ai zakayimun maganinsu.




Hajiya Bata rufe Baki ba Khairat ta fito tana hammar yunwa "Nuna ma najib khairat Hajiya tayi tace "kagani dai da idonka ko?Sai sannan khairat ta lura da mutanen palourn fad'ad'a fara'arta tayi tare da cewa "Lah Yaya yaushe kukazo sannunku da zuwa tafad'a tana nufar wajen da Ummy ke zaune "Kallonta yayi ya tab'e Baki yace "Lafiya"Jan bakinta tayi shiru a zuciyarta tanaa mamaki Hali irin na yayannata sai bak'in Ran tsiya tafad'a a zuciyarta sannan ta gaishe da ummy "lafiya qalau Amarya ya muka sameku"Murmushi kawai tayi tace "Lafiya qalau ummy Ina su Amira.,



Amira gatanan "tafad'a tana Nuna Mata Amira datayi lik'is duk ta gaji "Murmushi Khairat tayi tace "Ah yau Muna da manyan Bak'i gidan Nan gaskiya Sannan tace Ummy k'anwar tamu tayi saurin girma fa ''D'agowa Amira tayi ta kalleta tare da Galla Mata Harara tace "Son girma yayi Miki yawa matar Nan nice yarinyar "Lallai Kam rashin kunyar da kikemun a waya ne zakimun a Fil....,muryartace ta sarke sakamakon ganin Mai tsananin kama da ummanta da tayi kamar antsaga Kara an karya kallonta ta tsayayi ta kalli Ummy tace.



"Ummy bayan Amira kinsake Haihuwa Dama "Dariya Ummy tayi tace '"Eh Baki sani ba "B'ata Rai Khairat tayi tace "Kai Ummy Kuma shine Baki fad'amanaba Kinhaifo Mana Mai kama da Umma Sannan ta kalli Najmat tace "Sannu da zuwa sister "Murmushi Najmat tayi Mata tace ''yawwa"Yagida "Alhmdllh sister Mai kama da Umma "Murmushi Najmat tayi Mata Dan ba fahimtar zancensu take ba"najib Ne ya gallawa khairat Harara tare da cewa "yanzu Zaki fara zubar kamar aku mahaukaciya"Simsim taja gefe ta zauna Tana gunguni a zuciyarta tace "mutum sai masifar tsiya daga dawowarshi ko na marmarima Babu "Najmat ko tab'e Baki tayi a zuciyarta tace "Kenan shi jarabar tashi har y',an uwanshi Bai bari ba".



Sarat da khady ne suka fito Wanda kansu d'aya a guje Sarat tayi gun Ummy tare da rungumeta tsam itama Ummy rungumeta tayi Dan ba k'aramun kewar y'ar tata tayiba Nan suka shiga gaisawa cike da kewar juna.



Hajiya ce tace "gaisawar ta Isa haka kuu barsu su huta NAJMAT Daman haka takeso Dan ta gaji Abinciccika kala-kala.aka jejjera musu a dining bayan kowannensu yaje yayi wanka Amira da Najmat sun shirya

Please Login or Register in order to submit comment