Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin ankonsu kamar yanda suka Saba khady da Sarat so suke su tambayi Ummy wacece Najmat Dan Suma sunga Kamar ta b'aci Saida suka gama cin abinci tukwana Hajiya tasa su Khairat su Rakasu d'akinsu haka ko akayi Najmat da Amira Daman a mugun gajiye suke ba b'ata lokaci bacci yayi awon gaba dasu.




"Palour yarage daga Ummy sai Hajiya sai su Khairat da Sarat da khady Sai najib dake Shirin tafiya gidansu Dan ya k'agara ya gansu ba k'aramun kewansu yayi ba.



Hajiyace ta kalli Ummy tace "Habiba wannan yarinyar fa "Sauke ajiyar zuciya Ummy tayi Nan tabasu labarin had'uwarsu dasu har zuwa Auren Aunty Nafisa da babanta da Kuma shak'uwar su da Amira da tak'aitacce tarinsu kamar yanda ABIY yafad'a musu".



Ba Hajiya ba hatta su Khairat yara Saida sukayi mamaki Babu dangantakar komai tsakaninsu Amma wannan tsananin kama haka aita b'aci "Hajiya ce tace "Allah Mai iko tunda nazo duniya bantab'a ganin tsananin.kama haka ba Kuma kuji ikon allah ba dangin iya bana baba"Murmushi Ummy tayi tace."wallahi ko Hajiya Ai danma bakiga uban nata ba Ai sak kamarshice Tayo Shima sak kamarshi d'aya da Jidda saidai.kice anfi ganin Kamannin nata Dan ita macece.





Gaban Hajiya ne ya Bada Daram tace "Habiba kina nufin itama uban nata Kamarshi d'aya da Jidda"wallahi ko Hajiya Konima Saida kamar tabani tsoro najib yafad'a "Hajiya ce tace "Dan Allah ku nunamun hotonshi?Najib ne yace ''nidai bani da hotonshi Sannan Ummy ma tace Nima banida hotonshi".




Tagumi Hajiya tayi kamar Mai tunanin wani Abu saikuma chan tace "Habiba kardai ace d'ana adamune baban yarinyar Nan Daman Nasha mafarkinshi Bai mutuba"Tab'e Baki najib yayi yace "Hajiya yanzu Zaki fara sambatun ko taya za ayi babanta yaxama Adamunki bayan shi sunanshima Muhammad Kuma ma Adamunki Daya jima da rasuwa zakice wai Adamunki har yanzu bazakibar Sambatu akanshib"



Kuka Hajiya tafara Tace "Nidai kawai hakanan jikina yake bani adamu na na raye Allah ya isa tsakani na da Wanda sukayi sanadiyar rabuwata da d'ana wallahi inbanda zargi haramun da sainace da SA hannun Haule a sace adamu na wallahi harna koma.ga mahaliccina bazan tab'a yafe musu ba".duk cikin kuka take maganar Nan tana shaftar majina.




Tashi najib yayi.don yasan Hajiya tafara zancen adamun Nan nata Sai Allah Ummy ce tayi ta lallsshin Hajiya harta samu tayi shiru.





Najib yasamu tarba ta musamman daga family d'in nashi Babban farincikinshi Kuma yanda ya Samu Umma da Abba sunkoma rayuwarsu kamar da wannan abun yafi Mai dad'i Umma ta tarbi d'an nata sosai Tashiryamai kayan ciye ciye harsaida ya ture hirar uwa da d'a sukayi tayi har yamma yanason.lek'awa b'angaren Aunty Amarya Yana tsoron Umma sai da akayi Sallar magriba ne bayan ya dawo daga masallaci ya Samu yashiga b'angaren nata batare da ya bari kowa ya ganshiba.




Zokuga farinciki wajen aunty Amarya dayake Daman tasan da zuwan nashi Nan tashiga jeramai Kayayyaki"Dariya najib yayi yace "Aunty duk Ina zankaisu"Murmushi kawai take Dan Baki yak'i rifuwa tace "Aiko saika cinye su tas"wara idanu yayi yace "duka"Ehmana ko sunyi kad'an a k'aro''Marairace fuska yayi kamar k'aramun yaro yace "Haba my big mom karkuma cikin ya fàshe"Dariya tayi tace "Sai a d'inke ai "Murmushi kawai yayi da fruit salad ya fara Nan har bayan isha'i Yana sashen aunty Amarya suna hirar yaushe Gamo.




Cikin kwana biyu Najmat da Amira suka Saba da mutanen gidan sosai Najmat tashiga ran y'an gidan musamman Hajiya Dan jinta take har cikin ranta haka su Khairat dasu sarat.




Najib tunda ya tafi baidawo gidan Hajiya ba Sai a kwana na ukku yazo shida ummanshi "Sosai Umma tayi Mamakin ganin Najmat Dan ita kanta kamannin sun Bata tsoro Itama Najmat b'angaren ta hakane sosai ta tsorata da ganin Kamannin su.




Bayan Umma tazauna kallon ummy tayi ta kauda Kai batare da ta Mata magana ba abun ya daurewa kowa Kai yanda Umma da Ummy ke shiri insuka had'u kamar Sunfito ciki d'aya Hajiyace tace ''ke wai bakiga su Habiba bane"Turo Baki gaba tayi kamar wata yarinya batare da ta kalletaba tace "Sannu"Yawwa ya muka sameku"lafiya''umma ta Bata amsa a tak'aice"Madallah "Ummy tafad'a tare da tashi tabar ma palourn.



NAJMAT ce tace "Ina yini"lafiya kalau y'an Mata"Sannan Amira ta gaisheta ta amsa tashi NAJMAT sukayi da Amira suka koma d'aki suna shiga Najmat ta kalli amira tace "Dusti wacece wannan bantab'a ganin Mai kama Dani hakaba ke ko Abiy bama kama kamar wannan matar''Iwallahi ko Dusti Nima bantab'a ganin Mai kama dake haka ba Sannan ta tab'a Baki tace "mamar wancen mutumin ne"Wani mutumin Cewar Najmat tana hayewa Gado"Yaya najib Mana "Tab'e Baki Najma tayi tace "unhum,Dan ta lura matar batada mutunci ganin yanda take amsawa Ummy magana a wulakance Amira kanta batajin dad'in hakan ba.



sannan taja bargo tayi kwanciyarta baccin Rana itama Amira gado ta haye dansu Khairat suna makaranta saura su biyu ba jimawa bacci yayi awon gaba dasu.




"Haba Jidda banji dad'in yanda kika gaishe da matar yayanki ba meye laifin Habiba a iya tunani na da ba haka kukeba Kuna mutunci sosai Amma ko bakisantaba yau kika ganta ai bakya Mata magana haka ba haba Jidda waike wani irin hali gareki ne kamar me aljannu tukunnama me habibar tayi Miki?.




Umma ce tace "Haba hajiya me Kuma nayi Dan girman Allah"dak'uwa Hajiya tayi Mata tace ''ungo gidanku Dan iskanci ina.miki.magana kina me kikayi Nace Meya had'aku da Habiba ".



"Hajiya ni ba abunda ya had'ani da ita kawai narabu da ita saboda munafuka ce !"Munafurcin me ta Miki?,Kamar zatayi kuka tace "haba hajiya wai bakya ganine y'ar uwartace fa Alhaji ya Aura Tunda nake da mijina baitab'amun kishiyaba shekara da shekaru sai akan Amina wadda taso ta rabani da mijina k'arfin addu'a ya maido da hankalin Alhaji kaina kinmanta y'ar uwar habibace da baban Amina da Maman Habiba uwarsu d'aya ubansu d'aya a fa gidan Hadiza babbar yayar su Habiba Alhaji yaganta ya aurota afa gidan akayi bikin Dan tsabar Munafurcin Dan haka yasa na rabu da ita saboda bazanyi tare da Y'ar uwar mak'iyata ba",




Salati Hajiya tayi ta Salamce tace "Kai kedai anyi Malalaciya wallhi waida wananne kawai dalili to wai inama ruwan Habiba da Miki kishiya dakike magana ince dai ba Habiba ta had'asu ba yamasan y'ar uwar habibace ba Saida akayi auran bama kokuma Kinga Habiba ne wajen bikin yaushe rabon Habiba da k,'asar nan ma barekice ta Saka anyi Miki kishiya kede wallahi kinshiga ukku da wannan bak'in kishin da kika d'orawa ranki kin d'auki tsanar duniya kin d'orawa baiwar Allah wallahi Jidda Ina rabaki da halin Nan Kar hak'k'in baiwar Allah ya tambayeki ni Banga laifin yarinyar Nan Amina ba yarinyar ARZIK'I y'ar mutunci ba ayi Wata ba Nan tazo gaisheni dubu goma sukutum ta d'auka ta bani ke Dan bak'in Rai bakima raga Mata kodan saboda kyautatawar da takewa mahaifiyarki kodan ai ba Haule tayiwa ba bare kiji dad'i.ta Ida fad'a cikin masifa.



Umma kamar tayi kuka haka takeji Dan ta tsani fad'an da Hajiya ke Mata Kuma batajin kunyar agaban y'ay'ana ta rufeni da fad'a Ga Kuma haushin ta na yanda Umma ke yabon Amina jitake kamar ta kurma ihu Dan takaici Amma tayi shiru harta gama fad'anta batace uffan ba.



Dan son barin zancen ya Sanya Umma cewa "Hajiya wai yarinyar Nan Dana gani d'azu wacece" tare suke dasu Habiba yarinyar mijin nafisarta ne Amma Jidda bakiga yanda kuke kama ba kuwa"Aishiyasa na tambayeki Hajiya naga kamar tayi yawa to Kuma Baku da dangantaka dasu kuwa?"Wallahi ko Jidda kema Kya fad'a ba dangantaka kota kwabo Dan Habiba tacemun.mahaifinta d'an gombe ne haka mahaifiyarta tama rasu tonikuma na duba naga ko dange dange bamu dasu a garin gombe Ko almajirin gidana baitab'a xuwa gombe ba bareni harnasamu dangi a gombe"tab'e Baki Umma tayi tace "To Allah kyauta Hajiya zanwuce"to Allah kiyaye " najib ya maida ita gida Shima kanshi Yana mamakin zafin kishi irin na.ummannashi Dan baiji dad'i abunda tayiwa Ummy ba.




Bayan tafiyar Umma Hajiya takira Ummy tabata hak'uri akan bataji dad'in abunda Jidda tamata ba Nan Hajiya tace "waifa akan Amina ne tamiki wannan abun Dan kina y'ar uwarta oh ni Saratu bantab'a ganin Mai zafin kishin Jidda ba addu'a dai nake Allah yaye Mata.



,''bakomai Hajiya "Cewar Ummy ita kanta mamakin kishin Umma take wai akan Amina zata daina Mata magana aminar da bama wani zumunci suke a da ita ba sosai inbanda dawowarta gidan Aunty Hadiza karatu bama tasan da auran ba sai bayan Nan Ake fad'amata a zuciyarta tace "kenan shiyasa Kona kirata Bata d'agawa tsaki taja a ranta tace ikon Allah iska Yana wahalar damai kayan Kara Niko tunda kika gwadamun haka to yanzu natashi zumuncin da Amina muga ta tsiya.





Washegari su Khairat da Sarat sai khady sungama shirinsu na tafiya makaranta Wanda yanzu khairat na level 4 Sarat da khady na level two bayan tafiyar Najib khairat da Sarat suka Samu mazaje Wanda aka had'e bikin tare zasu cigaba da karatunsu bayan auran.




Najmat ce tace Gaskiya nagaji da zaman Nan wallahi mutafi tare itama Amira tace eh wallahi Dusti mubisu mu maza mushirya "Yawwa sisters Daman friends d'ina nasan ganinku yanda nake Basu labarinku Cewar khairat.



Cikin k'alilan mintina Suka gama shirinsu cikin k'ana Nan kaya rigar iyakar gwuiwa green sai wandonta red sai hed d'in kayan red simple make up sukayi zokuga yanda sukayi wani masifar kyau musamman Najmat Dan sak Takoma kamar baturiya bayan sun fesa turarruka masu mugun k'amshi.




a Palour suka tarar dasu suna jiransu kowannensu masha Allah sukecewa Dan sunyi musu mugun Kyau.



Hajiyace tace ''ku yanzu a haka zaku fita kamar d'iyar arna "Dariya sukayi Najmat tace ,"Hajiya me.kayan sukayi munfa yafa gyale"khairat ce tace "da Allah ku k'yaleta wannan tsohuwar meta sani tafad'a tana jansu a ,Sukayi waje.




Mota suka shiga driver ya jasu tun shigowarsu makarantar kallo ya Koma wajensu Musamman Najma kowa da abunda yake cewa Dan ba k'aramun burgesu tayi ba ganin Hakan yasanya khairat Janta Tayi class d'insu da ita Dan khairat akwai son y'an gayu shysa tunda Najmat tazo jininsu yayi wani mugun had'uwa Dan taga yarinyar classic Ajebo ce ga maganartama ta Isa ta rikitaka uwa uba tafiyarta yanda take taku kamar wata jinin sarauta uwa uba kyau komai ta had'a.




Suna shiga department d'in duk kallo yakoma wajen Najmat Nan khairat tadinga fad'awa k'awayenta ai cousin sister d'intace dake India sukazo biki Nan k'awayenta suka dinga cewa tafisu kyau dayake Najmat tana da warka ba laifi Nan sukahau fira da friends d'in Khairat Suko hada amsar number ta Dan sosai mutane keson suyi friendship da ita.



Basu jimaba lecturer ta shigo domin Fara musu lectures sadda Kai NAJMAT tayi tana danne _dannen wayarta yayinda duka class d'in suka Bata attention d'insu ga abunda Ake koya musu Dan sosai sukejin dad'in lectures d'in m. Amina ga Bata da tsanani.




Cikin lesson d'ine m. Amina tayi Wata tsatsaurar tambaya kowa class d'in baisaniba Kowa yayi shiru ya kasa Bada amsa Najmat datana danna waya Amma Hankalinta nakan abunda Ake koya musu dukda har lokacin kanta na sadde Jin k'ara maimaita Tambayar yasanyata tunowa ai tun a s s two ankoya musu haka yasata tashi tare da d'aga hannu idontane ya sauka ga kyakyawar Matashiyar matar da bazata wuce shekaru 35 ba sanye take cikin wani had'ad'ad'an lace ubansu anyi Mata Doguwar riga d'inkin ya zauna das a jikinta Tayafa gyale matching color Sannan k'aramin medical glass d'inta dayayi Mata mugun Kyau Tasha d'aurin zarah buhari Bazaka tab'a cewa takai shekarun ba duba da yanda gayu ya zauna Mata uwa uba kyau ga dimple d'inta side biyu Daya lotsa Lokaci guda kawai Najmat taji gabanta yabada Daram.



Hakan takansance wajen Aunty Amina itama Lokacin da idonta ya sauka ga kyakyawar budurwar data mik'e ta d'aga hannu Babu dalili kawai taji gabanta ya fad'i a sanyaye Tabata umarni data fito ta rubuta Mata Amsar Dan calculation ne Mai mugun zafi.



Cikin takunta na k'asaita da aji ta fito kowa hankalinsu nakanta wasu na gulma da tab'e Baki suna cewa daga zuwanta bakuwa harzara tinkari wannan caculation d'in da ko me masters albarka .



Tana Isa gaban hall d',in Murmushin Daya fito Mata da wushiryarta da Kuma hak'orin makkarta Daya k'ara Mata kyau aunty Amina tayi Mata tare da mik'a mata maker d'in itama Najmat Murmushin Daya lotsar da dimples d'inta tasaki idonta nakan matar a sanyaye kamar wacce aka zarewa lakka ta Amshi maker d'in tare da zuwa gaban white board d'in tafara calculation d'in.




Cikin minti biyu tagama Tare da mik'a.mata maker har lokacin Amina batabar kallontaba Gabanta na tsananta fad'uwa Tana juyawa ta karanta Abunda ta rubuta taga correctly bako kuskure d'aya Wow tafad'a tana kallon NAJMAT ba k'aramun burgeta Tayiba sabida a rayuwarta tana son Taga intelligent Dan tasan ba k'aramun Mai ilimi bane zai iya ansa tambayarnanba.



Murmushi tayi tare da juyawa ta kalli d'aliban tace "Clamp for her"Duka Hall d'in ya hau tab'i su kansu sunyi mamakin k'ok'arin yarinyar ba k'aramun burgesu tayi ba.



Aunty Amina batasan lokacin data rungume NAJMAT ba itama Najmat rungumeta tayi A tare sukaji Wata nutsuwa ta sauko musu Najma ji tayi tunda take Bata tab'a Jin Dad'in runguma ba irin yanda matar Nan ta rungume ta itama Hakan takansance wajen Aunty Amarya ga wata nustuwa data saukar Mata ga kuma gabanta da ya tsananta fad'uwa NAJMAT ji tayi Kamar su dawwama a haka rungume da juna Jin d'umin da Bata tab'ajin irinshi a rayuwarta ba Sunyi minti biyu a haka Kwata kwata Aunty Amarya Tama mance da Cikin Class suke Jin hayaniya ya sanyata rage rungumar datayiwa Najmat Tare da kallonta itama Najmat d'agowa tayi ta kalleta kafe juna sukayi da Idanu bako k'iftawa Aunty Amarya ce tayi Murmushi tare da Shafa fuskarta tace..✍🏿




*Tofa waiya abun yake ne niduk sun gama rikitani fa*😢



*Idan banji ruwan comment ba Yasin zakujini shiru atoh idan Kuma naji ruwan sharhi tohm zakujini ga long page nan na kwana biyu ne wollah*😉



*Kardai agaji da sharing fisabilillah Masoyan asali bani da grps ne*





_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[11/13, 8:44 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴

*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{ *Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa* }_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

*Ina Mai Baku hak'urin Jina shiru dakukeyi kucigaba da hak'uri ba kullun zansamu Daman muku typing ba idan nasamu Dama zakujini kullum idan Kuma Hakan baisamu ba to duk bayan kwana d'aya zaku dinga jina ma'ana yau idan nayi gobe bazanyiba*😢
_______________________________
*PAGE 49 & 50*
________________________________

What is your name pretty?

Cikin sweet voice d'inta tace " *NAJMAT*

Wow is so sweet name


Murmushi Najmat tayi cikin sanyi tace "Thanks "

"Nan department d'in kike Daman"

Girgiza Mata Kai NAJMAT tayi tace"no "


Tunawa da cikin class suke yasanya aunty Amarya musu bankwana Daman tagama musu lectures d'in kama hannun Najmat tayi sukayi waje Dan sosai takeson yin magana da yarinyar .




b'angaren Najmat ma haka ta kasance batare da tunanin komai ba tabita a wani bench dake gaban department d'insu khairat suka zauna Aunty Amarya ce tace "Amma ba school d'in Nan kike ba,",.



Murmushi Najmat tayi tace ,,"Eh rakiya nayi"Dafa ta aunty Amarya tayi tace ,"Nayi mamakin yanda kika ansa question d'innan kinburgeni sosai y'ata Ina son naga yaro da k'ok'ari but wace school kike?,.




Murmushi tayi Mata tace "Thanks you aunty Ina karatu ne GOLGOTIAS UNIVERSITY GREATER NOIDA"


Wara idanu tayi cike da mamaki tace "wow India ko? Murmushi Najma tayi tace "Eh"Masha Allah Allah Miki albarka ya taimaka ya sanyawa karatunki albarka "Wani sanyi Najmat taji har cikin zuciyarta cike da farinciki tace "Ameeen nagode"Murmushi Aunty Amarya tayi Mata Itama a zuciyarta tana ganin tsantsar kamar Yarinyar da kishiyarta.



Dubu biyar da zaro a jakarta ta mik'awa Najmat "k'in amsa tayi tace "a a Aunty nagode"b'ata Rai aunty Amarya tayi tace "Ki amsa bakyau maida hannun kyauta baya idan Baki amsa ba bazanji dad'i ba ko ".




Girgiza kai Najmat tayi tace "Allah aunty ba haka bane idan na amsa banmasan ya zanyi dasu ba ban iya kashe Kud',in 9ja ba Kuma tun Ina yarinya Abiy ya hana ni Amsar kud'in mutane shiyasa bana ansa"




Cike da mamaki Aunty Amarya tace "Daman ba Nan k'asar kike ba ?gyad'a Mata kai tayi tace "Eh India nake wannan ne ma first zuwa na 9ja bantab'a zuwa ba"ga mamakin Aunty Amarya tace "ikon Allah nad'auka karatu ne yakaiki india ya Kuma naji hausa rad'am a bakinki"




. Dariya Najmat tayi sosai ganin yanda ta rik'e Baki ,"b'ata Rai Aunty Amarya tayi tace "Dariya ma kikemun ko"Kama hannunta Najmat tayi tace "Sorry Aunty yanda kikayi.maganan ne yabani dariya''to naji fad'amun ya akayi kika.iya hausa haka".



"Abiy na bayamun ko wani yare idan ba hausa ba shiyasa natashi da yaren "gaban. Aunty Amarya ne yafadi Dan son gaskata abunda zuciyarta ta Innata Mata tun farkon ganin yarinyar tace "Shi mahaifin.naki d'an Ina ne Ma'ana wani gari yake ko wace k'asa yake".




Hartazo zatace Gombe "saita tuna kashedin da Abiy yayi Mata ana gobe zasu tafi na cewa kada ta sake ta fad'awa kowa garin da yake ko ta nunawa wani hotonshi Hakan ya sata saurin cewa "Shima d'an India ne tafad'a tana Dan rawar Baki.




India ? Aunty Amarya ta maimata cikin ranta sannan tace "Kuma kince shiya koya Miki hausa ,"rashin sabo da k'arya ya Sanya Najmat d'an rud'ewa zatayi magana Wanda Batasanma me zatace ba wayar aunty Amarya tayi ringing d'aga Mata hannu tayi tace "Ina zuwa pretty bari na amsa waya nadawo ajiyar zuciya Najmat ta sauke tare da mata Murmushi Jin Dad'in sunan data kirata sosai sunan yayi Mata dad'i tana Murmushi tace to saikin dawo" a zuciyarta ta maimaita pretty Murmushi tayi sosai auntyn ta iya fad'an pretty.



Aunty Amarya na barin wajen Dan amsa waya Najmat ta tashi ta Koma class d'in su khairat Dan tsoron Kar idan tadawo tacigaba da Mata tambaya ta k'ureta Amma badan tagaji da hira da ita ba sosai matar ta kwanta Mata arai.





Aunty Amarya Koda ta dawo Bata iske Najmat ba bataji dad'i ba office d'inta ta Koma tunane tunane tayi tayi ganin kanta ya fara ciwo ya sanyata komawa gida cike da tunanin pretty kamar yanda tasa Mata suna Bata tab'a ganin yarinyar da ta kwanta Mata a Rai lokaci guda ta shiga ranta sama da yarinyar Nan.





Sai bayan azahar su Najmat suka koma gida kafinsu Tafi ba irin Neman da batayiwa Aunty ba kamar yanda itama tasa Mata suna Amma Bata ganta ba sai hak'ura tayi cike da Jin haushin kanta na tahowa d',azu da tayi cike da tunanin matar da batasan sunan tabama suka koma gida.




Sa'adatu tunda ta Samu labarin NAJIB yadawo ji tayi Kamar ta zubda ruwa a k'asa ta Sha Dan dad'i Tattara kayanta tayi ta Koma gidansu najib Ko zata samu ta shawo kanshi ta haka Amma me ko kallonta bayayi ko tamai magana baya amsa gaisuwarta ba k'aramun haushinta najib yake ba.




Rayuwar Najmat gidan Hajiya sosai tamata dad'i Kullum suna waya da Abiy da Aunty Nafisa ana saura kwana ukku a fara biki aunty Nafisa da Abba suka iso 9ja.sosai Najmat taji dad'in zuwan su musamman auntyn tata da Kuma lil bro d'in nata da take matuk'ar ji dashi.




Tunda sukazo 9ja magana Bata sake had'a najib da Najmat ba ko sun had'u zata shareshi Shima haka yake shareta Amma a zuciyarshi bayajin dad'in hakan Saidai Kar yarinya ta rainashi ya Sanya yake shareta Shima.





Da misalin k'arfe Shida na yamma Gajiya da zaman cikin gidan Najmat tayi Hakan ya sanyata fitowa compound d'in Kasancewar Yana da fad'in gaske Daidai k'asar bishiyar mangoro tazauna sosai iskan yayi Mata dad'i sanye take cikin Doguwar riga gown Black ta d'aura belt d'in rigar kanta sosai rigar tayi Mata kyau chatting take da wayarta tana Murmushi ita kad'ai sosai chat d'in ke Mata dad'i itada friends d'inta na school.




Najib ne yashigo da motarshi bayan yayi parking hangota yayi waya na hannunta sai Murmushi take ita kad'ai harzaiwuce saikuma yayi wajenta tare da zama gefenta hakanan ya sauke girman kanshi yace "y'an Matan Abiy iska akesha''juyowa tayi ta kalleshi Saitaga ya K'ara haske da kyau kwana biyun da Bata ganshi ba .



'turo Baki tayi ta juya taci gaba da chat d'inta "maimakon yaji haushi sai Murmushi yayi Dan yanzu komai zatayi saiyaji bayajin haushinta saima dariya da take bashi kokuma Yaga abun ya Mata kyau musamman yanda take shagwab'a.



"Wai me nayiwa y'an Matan Abiy ne take fushi Dani haka har take share best friend d'in nata"k'ara turo Baki tayi cikin shagwab'a tace "Kamanta mun b'ata dakai fushi nake dakai kaida kayimun tsawa Kuma kacemun ubanwa yace na rakaka".



Dariya yayi danshi Harya manta ma "Ohhh wai wannan abun ne yasa kike fushi dani.kenan har bakya mun magana?gyad'a Kai tayi tace "eh Mana aimun b,'ata had'e hannayenshi yayi waje guda Yace ''to kiyi hak'uri bazan sake ba "turo Baki gaba tayi tace "Ni ba ruwana dakai ka fiya fad'a'".




wara idanu yayi yace "Nid'in "gyad'a Mai Kai tayi tace eh Mana "Murmushi yayi yace "to na Baki hak'uri fa ai kin hak'ura ko *NAJMAT ABIY* d'inta Dan yasan sunan dazai kirata kenan Tahak'ura.




Lokaci guda tayi Murmushi tace "Nahak'ura ,''tare da mik'a mai k'aramar yatsanta alamun su shirya "Badan ya so ba ya mik'a mata hannu Dan bayason jikinsu na had'uwa.




Idonta ne ya Kai ga zoben hannunshi da harta manta Murmushin mugunta tayi Dan tayi Alk'awarin kota halin k'ak'a sai zoben Nan yazama nata suka shirya ta sakar Mai fuska sukayi ta hira Tana bashi labarin Wuraren data je a kaduna Yana Murmushi.





Khairat ce da Amira da khady sundawo daga anso anko Dan Najmat tace bazatajeba kewarsuce ma tasata fitowa Ga mamaki khady da ita ta fara hangosu ta tsaya tana kallon NAJMAT da Najib kama hannun Khairat tayi tace "Yaya khairat kalli Yaya najib da Najmat "wara idanu Khairat tayi Dan iya rayuwar tata zatace Bata tab'a ganin fara'ar Yayan nata ba sai yau cike da mamaki suka tsaya kallon ikon Allah Amira ce tayi dariya tace "wai mamakin me kuke"badole muyi mamakiba Amira jibi Yaya yanda yake Murmushi hada rank'wafawa Bantab'a ganin Murmushinshi haka ba "Cewar khairat




Murmushi Amira tayi tace "Ai Baku ga komai ba indai Najmat da najib ne wai Kuma saisu rainawa mutane wayau suce ba soyayya suke ba bayan na riga da ganosu.



Wara idanu Khairat da Khady sukayi tare sukace "Soyayya"dariya Amira tayi tace "kuna mamaki ne"Ba dole muyi mamaki ba Amira Yayan da ko kallo mace Bata isheshiba hasalima haushinsu yakeji bantab'ajin Yaya yayi budurwa ba masu soyayya ma shi haushinsu yakeji zakiji Yana cewa basuda aikinyi kwata_kwata fa ya tsani y'an Mata ko kallo basu isheshi ba bare ya tsaya suna magana karkiga yanda yake takura Mana ko hak'oranshi bama Gani Amma jibi yanda yake Mata Murmushi Kinga Aiko dole muyi mamaki"Cewar Khairat.



Dariya Amira tayi tace "Chab ku yake rainama wayau "Aiko dagayau yadaina cika Mana Baki cewar Khairat tana dariya "Kumafa kinsan me sisters Cewar khady saikin fad'a suka fad'a a tare.



Hhh dariya tayi tace "kinmanta lokacin da yake cewa Hajiya shi ko aure zaiyi bazai Auri yarinya ba wacce a Haihuwa ya haifeta ta rainamai wayau Sai babba waddaa. Ta mallaki hankalinta Koma zaiyi Auren.



"Dariya Sosai khairat da Amira suka shigayi khairat tace "Aiko alhmdllh Allah na gode Maka gashinan y'ar jaririya tayi wuufff dashi Amma fa ba k'aramun matching sukayi ba "sosai suka shiga Mai tsiya tare da lab'ewa suna Kallonsu wai suga k'arshen love.




Najib da Najmat da basusan da wanzuwarsuba hirarsu kawai suke Inda Najmat ke cewa "Ita tagaji tundazu suka tafi suka barta najib ne yace to ko yawo kikeso gyadamai Kai tayi tace "eh wallahi"Murmushi yayi yace "to ko Zaki rakani gida anjima saina maidoki "Murmushi tayi tace "eh muje "Tashi yayi itama ta mike "harararta yayi yace ''to yafa gyalan ''warwareshi tayi ta yafa sannan ta bishi suka tafi parking space ya zagaya ya shiga driver seat.



itama tashiga front seat horn yayi get man yafito ya Bud'e musu suka tafi.



Ihu su Khairat sukasa ganin fitarsu

Please Login or Register in order to submit comment