Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan yace okay muje ya fad'a Wana ware hannu Yana wani Had'e gira.





Daga haka Amira Bata Kuma cewa komai ba Dan talura guy d'in yanaji Da Girman kai DA rainin hankali a zuciyarta tace "daman kyawawan mazan nan haka suke y'an rainin wayau Wai Na gaisheshima ya amsa mun a Raine DA wannan tunanin Amira Har suka Isa inda Najma tayi parking back seat ta nuna Mai ya Shiga tsayawa Amira tayi gyara takalminta.



Tsaki Najma taja tace "hurry up Mana so everyone knows I don't wan't to wait"Tsaki itama amirar taja sannan ta Shiga Dan a k'ule take .




Tab'e baki Najmat tayi batama tsaya Ta Kalli Wanda suka d'auko ba ta fusgi motar DA k'arfin gaske Najib kanshi Saida yad'an firgita Dan a rayuwarshi Babu abunda ya tsana sama DA gudu a Mota so yake.yaga fuskarta a zuciyarshi yace " wannan wace ,irin fitsararriyar yarinya ce Ko gaisuwa Bata iya ba tazo tana Mana kasada DA rai "Tsaki yaja a fili a zuciyarshi yace "kodan yaran turawan nan ba tarbiya ta ishesu ba Ji wasu tsinannun Kaya jikinsu Har Amira Da take bahaushiya mamaki yake yanda uncle Umar Shima ya b'iyewa al'adar turawa Har yabar y',arshi tana yawo DA wannan shaggun Kayan cigaba DA danna wayarshi yayi dan ba damuwarshi bane.



Bangaren Najma ma Tsaki taja DA k'arfi a zuciyarta tace shikuma wannan Ko WANI irin marar tarbiyar ne ya shigowa mutane Mota Ko gaishesu baiyiba (kunsan Najma DA tsagwaron iyayi DA son girma) sannan ta Kuma Jan Tsaki a fili a zuciyarta tace "kodan y'an Nigeria d'innan daman ba tarbiyar kirki ce ta ishesu ba (nikam.nace Najma wlh ki iya bakinki Harkin Isa ki kushe mana k'asa)
Wanda Har lokacin Bata Ganshi ba.




Har suka Isa cikinsu bamai cewa uffan Najma tana Jin haushin Bai gaishe ta Amira tana Jin haushin amsa gaisuwarta DA yayi a wulakance Najib ko Danne Danne wayarshi kawai yake Suna Isa gida Tana parking Amira ta Fara fita Tana kunburi cikin sauri tayi part d'insu Sannan Najma itama tafito Ko rufe k'ofar motar batayi ba Shima Najib fitowa yayi cikin nutsuwa Juyawar DA Najmat tayi zata bar wajen shikuma ya fito daga Mota Ji kake gam sunyi Karo.




Cike DA masifa Najma ta d'ago zata balbaleshi tare DA dafe goshinta DA hannu Dan taji mugun zafin Karon Shima d'agowa yayi cike dajin haushi Idonsu ne ya Sark'e cikin Na juna a tare kallon juna suka tsayayi kallon mamaki kowannensu Ke yiwa d'an uwanshi musamman Najib baiko k'iftaba Kara wara idanunshi yake wajen K'ara kallonta mamakine dank'are a cikin zuciyarshi Dan tunda yake cikin family d'insu Ko cikinsu y'ay'an ummanshi Ko y'ay'an family Bai tab'a ganin Mai kama da umman Shi Rai DA Rai ba sama DA yarinyar nan dake tsaye gabanshi Duk yanda mutane Ke cewa Yana kama da umma ganin wannan yarinyar dake tsaye gabanshi ta Dame kamannin tsakin DA Najmat ta Jane ya MAIDO dashi Daga duniyar tunanin DA ya Lula kallonta ya tsayayi ganin Har yanda ta HAD'E fuska take kunburi Sak umma Har irin yanda umma Ke b'acin ranta ganin yanda ya kafeta DA idanu ne yayi mugun b'atawa Najma Rai gashi taga baida niyyar Matsa Mata ta wuce haka ya Sanyata d'aga baki cike DA tsiwa DA masifa tace ..........✍🏿


*Congratulations my cwt mommah Ina tayaki murnar kammala littafinki Mai suna Amer Da Amera Allah bawa al'umma damar aiki DA fadakarwar DA littafin Ke tafe dashi Ina tayaki murna Sosai mom nusy uwa ta gari*💃🏽💃🏽



*Ga long page nan Asha karatu lafiya Na kwana ukku ne*😂😊



*Kardai a gaji DA sharing Dan girman Allah Bani DA groups sosai ne shiyasa cwthearhs Kar a gaji damun sharing fisabilillah*😊






*_Mhixx Hajo ce_*🤙🏿
[10/20, 7:36 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

_____________________________

*PAGE 29 & 30*
_____________________________

"Tumpaaree Koee aankh Nahin hai ya aap pooree Tarah Se andhe Hain Mujhe baahar jaane Ke lie de do"

(Kai dalla baka da ido ne Ko kai makaho ne zaka zo kamun Karo maimakon ka Bani hak'uriba a a kawai zakazo ka kafeni Da wannan idanun naka abun tsoro Kamar Na mujiya , jibeshi Da Allah ya wani Tara bak'in Abu a fuska Kamar Zaki (sajenshi) dallah Ni Bani hanya Na wuce )Duk cikin harshen Hindi take maganar nan Dan tayi zaton bayajin yaren Saboda Tasan Abbansu Amira d'an Nigeria ne to Yace d'an k'anwarshine Hakan yasa ta balbaleshi son ranta Harwani watsa hannu take irin masifar nan tayi yawa.




Duk maganar da take Najib Yana jinta Saboda ya iya yaren Hindi tun yana yaro Shi mutum ne Mai kaifin basira Duk abunda yasa Burin iyashi tofa saiya koya ya koyi yaren Hindi ne ta dalilin wani abokin karatunshi murza Course mate dinshine shiya koya mashi harshen Hindi sosai Babu abunda bayaji haka kuma Zai iya mayarwa.




Nuna Mata yayi kamar baisan abunda tace ba Amma a zuciyarshi ba k'aramun ciwo maganganun nata sukayimai ba Tsaki yaja a ranshi yace shiyasa bana Shiga sabgar Mata Duk inda suke matsalace wlh jibi wannan k'ank'anuwar yarinyar DA a auran wuri Na haifeta Amma take fad'amun irin wannan maganar Tsaki yaja tare DA barin wajen a ranshi Yana K'ara Tsanar harka DA Mata Dan ba k'aramun B'ata Mai Rai figigiyar marar tarbiyar yarinyar can tayi ba.




Najmat Ko tana ganin yabar wajen baisan abunda tace ba Dariya ta k'yalk'yale Da ita tace d'an rainin hankali yawani shigowa mutane Mota ba gaisuwa aigashinan Na zazzageka baka San me nace ba Dariya kawai Take sosai a haka ta Shiga palour tana dariya.





Kafad'ar Aunty nafisa ta d'aura kanta tare DA cewa"wash Aunty Na gaji"shafa kanta tayi tace "ayya sorry my dear kije kiyi wanka kifito Kiyi lunch Na tanadar Maki Abu Mai dad'i "d'agowa tayi murmushi dauke DA fuskarta tace "Wow my Aunty thnks u so much my lovely mom Kamar kinsan Na Kwaso yunwa sannan ta Bata Peck a kumatu ta tashi hada gudunta ta Haye stairs.




Zaune suke a palourn Abba Ummy Najib Sai Amira dake zaune tana latsa waya Hirar yaushe gamo Abba DA ummy sukeyiwa Najib Abba ne yace "wato son Har yanzu kana nan DA mugun miskilancin nan naka Na tsiya Ko"murmushin DA inba lura Kayi ba bazakagane murmushi ne yake ba yayi yace"Uncle ba haka bane Kawai gajiya ce "Ummy ce tace "gaskiya kam akwai gajiya kam sannan tace ya su hajiya Da Su Jidda "Lafiyansu Qalau Duk sunce a gaishe ku "sannan ya d'auko musu tsarabar DA umma tabada a kawo musu Wanda yawaici duk kayan bahaushe ne Wanda su Basu dashi sunji dadin tsarabar sosai.




Saida suka Sha Hira tun Najib baya sakin jiki Har yazo ya saki sai wajen 10pm ya koma masaukinshi had'adden bedroom dinshi Mai matukar girma DA tsaruwa komai akwai a ciki na bukata d'akin Shima cikin gidan yake kasancewar gidajen Ko Wani Daki saika b'ulla ta palour Amma akwai k'ofar DA Zai iya Shiga ya fita batare DA yashigo ta palour ba Kuma Zai iya Shiga ya fita ta palourn gidan.




Ruwa ya watsa sannan ya dawo gado ya kwanta Bai jimaba bacci yayi awon gaba dashi Dan ya shawo gajiya ba kad'anba.




Bayan kwana biyu Najib ya saki DA mutanen gidan kasancewar ba wani Sabo sukayi dasu ba Dan basufiya zuwa Nigeria ba saisuyi 5yrs Har Fima Hakan yasa basuyi Sabo Dasu ba.




Zaune yake a garden d'in gidan Yana Shan dad'd'an Iskan wajen ba k'aramun dad'in iskan wajen yake Jiba qur'anin DA Aunty amarya ta bashine hannunnshi yake karantawa cikin zazzak'ar qiri'arshi Mai dadin sauraro.




Kamar kullum Sanye take cikin k'anan kaya faruq Na hannunta tana bashi biscuit Sai dariya yake yiwa Auntyn nashi itama tana mashi murmushi tana mishi fira Shima Yana Mata gwalamgwalamtunsu Na yara Hanyar gidan su Amira ta nufa kai tsaye .




Tana knocking Amira ta fito ta bud'e rungume juna sukayi Najmat tace "Haba Dusti Wai meyasa two days kika Baro gida kika dawo nan kinsan bazan juri missing d'inki ba "harararta Amira tayi tace ''eh mana Nima Na dawo gidanmu tunda Aiba haka muka tsaraba Idan yau munkwana Chan gobe mukwana nan Amma kika watsar kullun saidai muyi ta kwana gidanku shiyasa Nima Na dawo gidanmu "sorry Dusti tohm shikenan Nayarda Amma kiyi Hak'uri daga gobe Sai a Fara "kallon bakida wayau Amira tayi Mata tace "nak'i Wayan Ummy tace two Weeks zamuyi Mata tukwana murmushi Najma tayi tace to Naji nan Amira taji sanyi palour suka nufa hug din ummy Najma tayi tare DA gaisheta.




Nan Amira Da Najma suka Hau shiriritarsu Faruq Yana hannun ummy a palour.




Gajiya sukayi DA Zama cikin gidan haka yasa suka fito Dan su tafi garden Faruq Yana ganin fitowar Najma zasu fita Aiko yasa Kuka tare DA Fara Mika hannu "Lallai Yaron nan watau Kaga yayarka shine zaka rikicemun Ko to Ai zanga Mai d'aukarka Idan Suna makaranta "Dariya Najma tayi tace "karkiga laifinshi ummy Kinsan ance Babbar Yaya uwa Bani abuna muje mu shak'ata tare "Murmushi ummy tayi tace "ummm su uwa Manya ga abunnakine Chan kuje kuyi shiriritartaku tare Dan Shima Naga kin Fara bashi training irin naki tafad'a tana dungurar kan faruq"Uhm uhm ummy kidaina dakarmun boy Kuma ma bazai K'ara zuwa wajenki ba daman ya fad'a mun dukanshi kike shine kikayi a gabana to baxai K'ara zuwaba "tafad'a tana d'aukar kaninta tabi Amira Dan hartayi gaba .


Kai tsaye garden d'in gidan suka nufa Basu ma lura DA Najib dayake gefe ba zaune kan chairs kai tsaye wajen table tennis suka nufa nan Aje faruq tare Da ajemai kayan Wasa suka tafi suka Fara buga wasansu cikin. K'warewa ita DA Amira Kallo d'aya zakayi musu kasan ba abunda Ke damunsu Suna cikin Jin dadin rayuwa.




Najib DA tun shigowar su yagansu baiko d'ago ya kallesu ba Saidaga baya ya d'aga idanunshi ya kallesu yanda suke buga wasansu hankali kwance Tsaki yaja Ganin Hada figaggiyar marar kunyar Chan )Dan haka yasawa Najmat )Amma Saida gabanshi ya K'ara fad'uwa Kara ganinta Karo Na biyu har murmushinta Sak irin Na umma dimple ne kawai umma Bata DA Shi itakuma Najmat Har two side shagala yayi DA kallonta Yana K'ara ganin. Tsantsar kamanninta DA umma ta yayinda Dimple d'inta Ke lotsawa tana murmushi Yana tsalle tsalle dimple d'inta ya tsaya kallo Sak Kuma Sai yaga dimple d'inta irin Na aunty amarya yanda ya lotsad'in sosai Tsaki yaja a fili sannan yayi saurin kauda tunanin nan a cikin ranshi ya d'auki Hakan a matsayin kamannin halittar Allah ce kawai daman ance mutum Yana DA Mai kama dashi..




Najmat DA suka gaji DA table tennis din nan suka Hau Tsaren gudu ita DA Amira Suna zagaye garden d'in DA niyyar exercise.




Faruq daya gaji da Zama nan ya Fara Kuka sosai Najma DA Amira Bama Susan yanayi ba Dan nishad'insu kawai suke faruq Ko rarrafe yake kawai Yana Kuka.




Najib ne yajiyo Kukan Yaro bayanshi juyawa yayi yaga Yaro Na rarrafe Yana Kuka ga alamun d'auka yakeso Tashi yayi daga zaman Da yayi tare DA nufar inda Yaron yake DA niyyar d'aukarshi Shima faruq d'in wajenshi yake nufowa DA niyyar ya d'aukeshi.




Durk'usawa yayi DA niyyar d'aukar fine boy d'in Dan Yana ganin Yaron yaji yaburgeshj kasancewar Najib mutum ne Mai son yara nan ya duk'a ya daukeshi ya koma wajen xamanshi DA faruq a hannunnshi Yana daukarshi yaji Yaron yayi shiru Sai kallonshi yake nan yashiga mashi Wasa faruq Ko Sai dariya yake Dan yaro ne Mai yawan dariya nan yashiga Wasa DA sajenshi Yana shafawa Yana dariya....✍🏿




*Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*





*_Miss Hajo ce_* 🤙🏿
[10/22, 7:02 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*This page is for you sis Amina Yusuf bawale Ina Jin dadin comments DA sharhin d'inki over thnks for ur love shafin nan nakine kiyi yanda kike so dashi*💃🏽💃🏽🌹🌹🌹🌹


_________________________________
*PAGE 31 & 32*
_________________________________

Saida suka gama exercise d'insu tukwana suka tsaya Suna gama gumi Nan Najmat tahau waiwayen inda ta ajje faruq bataganshiba kasancewar Garden d'in baida wani girma sosai Hakan yasa tayi saurin hangosu Tsaki taja Ganin faruq hannun wancen mutumin a fili tace "Wai meya kai faruq hannun wancen marar tarbiyar d'an Nigerian sanadin ya lalatamun yaro "Harara Amira ta Galla Mata tace "Banson iskanci Najma dad'in abun kema Dai Y'ar Nigerian ce Kuma wancen DA kike cewa marar tarbiyar d'an k'anwar Abba ne Aunty jidda wacce aka Sanya Mata sunana ki iya bakinki "sannan tace. Kodan ma nalura d'an wulakancine shiyasama Ni tunda yazo Banshiga harkarshi "tab'e baki Najma tayi tace ''uhm kede kika sani Naji me d'an uwa Nikuma DA Bani dasu Ko to yayi Mai d'an k'anwar Abba.




Sorry Dusti wallahi ba haka bane Dan Allah kiyi Hak'uri bansan zakiji haushi ba kiyi Hak'uri kawai nafada ne Nima. Ba saninsu nayi sosai ba aini kece Y'ar uwata wancen mutumin DA tsawo Kamar poll Ni tsoroma yake Bani jibeshi Da Allah daga gani baida mutunci Ko dariya bayayi "Dariya Najmat tayi tace ,"Kai Dusti Dan uwan naki kikewa ba,'a sannan ta sake dariya tace kumafa hakane nan Najmat tabawa Amira yanda sukayi Jiya me Amira zatayi inbanda dariya tace "dusti wallahi kinyimun daidai Nima kinkoyamun Idan zaimun rainin hankali Nima saina balbaleshi DA yaren DA bayaji dariya Najmat tayi tace "Ai haka zamuyi tamai Har mu bashi tarbiya D'an rainin hankali nan sukayi ta gulmanshi Har suka kusa inda yake.



ja Najmat tayi ta tsaya tace Amira ta amso Faruq su wuce itama amirar tsayawa tayi tace "wlh saidai Ke ki amshoshi aike kika ajeshi Tsaki Najmat taja Dan batasan Jan dogon magana ya sata nufar Shi ja tayi ta tsaye tare Da murtukewa Kamar Bata tab'a dariya ba ta kama k'ugu Dan a tunaninta tasan bazaiji me tace ba yasata cewa cikin harshen hindi (Hey d'an raino na Bani baby Na kazo ka wani d'aukarwa mutane yaro aika Bari muyi ciniki dakai sannan ta k'yalk'yale Da dariya tace "Kodan Naga Kayi kama Da Mai Reno karka damu zaka dinga yimun rainon Shi ,kaji Amma kafin nan saika dinga gaishe Dani Ko dayaushe inba haka ba Na fasa) ta ida fad'a tana wani yatsine fuska Kamar taga Kashi.





Najib Yana jinta ya nuna Kamar baijiba kawai ya Mika Mata Yaron Amma a zuciyarshi yaji haushinta DA tsanarta lokaci guda Dan a rayuwarshi ya tsani Rashin kunya gashi ya lura yarinyar kwata_kwata Bata DA kunya kanta a tsakar ka yake Tsaki yaja yace nalura itama k'awar Tata irintace (Amira Kenan)tab'e baki yayi yace "Ina ruwana ma yafad'a Yana ware hannu sannan yaci gaba DA harkar gabansa a zuciyarshi Yana karajin Tsanar Mata.



Yau Monday Najib Zai Fara attending lectures a school din daya Shiga abun mamaki Kuma Ashe makarantar su Najmat ce Shima yashiga Hakan Ko yayiwa Abba Dadi Dan daman anfadamai yanda yaran Ke sharara Gudu a Mota Hakan yasa yayi shawara DA Abiy Akan Najib Zai dinga tafiya dasu Yana maidosu Sai Suna tafiya tare.




Abiy yaji dadin Hakan sosai inda ya bukaci DA Abba ya hadashi DA Najib su gaisa nan Ko Abba ya hadasu Lokaci guda Abiy yaji tarbiyar Yaron DA nutsuwarshi ta kwanta mashi a Rai Bangaren Najib ma hakane ga Kuma Karin mamakinshi Na ganin tsantsar Mai kama Da ummanshi Sak Ko ba a fad'a Mai ba yasan wannan mahaifin Najma ne.




Nan Abiy yayi Mai magana Akan Shi zaidinga tafiya dasu makaranta Amma kafin kagane Hanyar Najma Ko amira zata dinga tafiya dakai lokacin daka gama gane hanyoyin saika dinga kaisu kawai Idan time d'in lectures d'inku yazo d'aya.



Najib yaji Babu Dadi Saboda ya tsani abunda Zai had'ashi Sabga DA Mata Amma kwarjinin DA Abiy yayimai ya sanyashi amincewa Amma a zuciyarshi Sam baiji Dadi ba musamman had'ashi DA marar tarbiyar yaran can Ga Kuma mamakinshi Na yanda yaji Hausa rad'am a bakin Abiy Kuma yalura mutumin yanada tsakaninin kirki haka yasa yacewa Abiy ba damuwa nan Abiy ya Shiga domin kiramai su Najmat SU tafi.





Sanye suke cikin Wata blue d'in gown iri d'aya fuskarsu Kamar kullun Babu make up Sai d'an yafa k'aramun belt d'in rigar DA sukayi ba k'aramun kyau sukayi ba Kallo d'aya zakayi musu kayi tunanin two wins ne Dan hatta yanayin Girman jikinsu iri d,'aya A waiting palour suka had,'u Da Abiy "morning my twins" Abiy ya fad'a Yana ware musu hannaye Daya bayan d'aya Sukayi hug dinshi Najma Ko Sai shagwab'a take zubamai Kamar jaririya shiko Sai biye ta yake a haka suka fito compound d',in gidan Najmat Na mak'ale jikin Abiy.




Najib dake tsaye tunda ya hangosu ya ja Tsaki tare DA kauda kai yanajin haushin had'ashi Da yaran nan daza ayi.




Abiy ne yace "Sannu son GA sunan sun fito Ina tunanin zaku iya tafiya Allah kiyaye "Sannan ya ya Kalli Najmat Yace"My dear GA yayankunan daga yanzu tare zaku dinga tafiya zaku gwada Mai hanya zuwa Konan DA one week ne saiya dinga tafiya daku Allah muku Albarka.



Wara manyan idanun ta Najma tayi tare Da saukesu Akan mutumin data Kira Da marar tarbiyar Nigeria Abiy ta Kalla tare fito Da dara_daran idanun ta didddira k'afa DA kukan shagwab'a ta Sanya cikin zazzak'ar muryarta Mai Hade DA maganar shagwab'ab'b'u tace.....✍🏿




*Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*





_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[10/23, 9:18 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
_______________________________
*PAGE 33 ,& 34*
_______________________________



Nidai wallahi Abiy bazan yarda ba Taya xa ayi ace wannan mutumin Zai dinga tafiya damu school Ni wallahi ban yarda ba saidai na fasa makarantar gaba d'aya ta ida fad'a tana Sanya musu kukan tab'ara ."




"Sorry my dear calm down mana ba abun rigima bane.daugher kinfi Kowa sanin bana son ganin hawayenki my beautiful angel Dina kiyi Hak'uri shid'in yayanku ne zakuji dad'in tafiya tare"Abiy yafad'a Yana bubbuga bayanta alamun rarrashi.




"Uhm uhm uhm Abiy nidai Allah banaso Kowa a bashi motar Shi kawai "shafa kanta Abiy yayi cikin sigar lallashi yace "To shikenan Goge hawayen Na yarda za a bawa Kowa motar Shi Amma Ku Fara nuna Mai hanya tukwana kinji *NAJMAT ABIY* D'inta nasan bakya yiwa Abiy musu Akan komai".



Cikin sauri ta goge hawayenta tare DA sakin murmushi lokaci guda Jin dad'in Abiy ya kirata DA sunan DA tafi k'aunar a kirata tace "to my Abiy Na yarda tafad'a tana rik'e hannunnshi "Yawwa my daughter Ko kefa Kinga kin goge kwalliyar Taki Ko Na d'auko Maki Hoda ki shafa "Ba Najma ba hatta Amira dariya ta Sanya tana dariya tace "a a my Abiy ba saina shafa ba.



Najib Ko sank'arewa a wajen yayi Yana kallon ikon Allah a zaton Shi tsawatar Mata zaiyi Amma saiyaga Yana lallashinta Kamar wata baby Yana Dai tsaye Yana kallon tsantsar soyayyar dake tsakanin uba da y'a Dan wannan kad'ai ya tabbatar Mai DA akwai soyayya DA shak'uwa Mai tsanani tsakaninsu tab'e baki yayi a ranshi yace "ah lallai wannan Dole kiyi Rashin kunya Babanki ya sangartaki DA yawa ga Kuma mamakinshi Na yanda yaji Hausa rad'am a bakinta Dan Duk daukanshi batajin Hausa ".




DA lallab'o Dai Abiy ya samu Najma ta Shiga Mota Amira ta Shiga front seat Najmat tana driver seat Cike da Jin haushi Najib ya Shiga Back seat Sannan ta jasu suka tafi Tunda suka Shiga ba Mai cewa uffan a haka Har suka Isa school d'in kasancewar makarantar Nada girma sosai Hakan ya sata tsaida motar tare DA juyowa baya Shima d'ago wa yayi Dan tunda suka taho baima d'ago ba Saida yaji alamun tsaida Mota idanunsu ne suka sartse cikin Na juna Sai yanzu Najma ta k'are Mai kallo ganinshi tayi Fari kyakyawan gaske ga bak'in sajenshi Daya K'ara fito da hasken fuskanshi Sexy eyes d'inshi dashi yake Kara rikita Mai kallonshi Kwantaccen sumarshi Da Tasha gyara ta kwanta lufff Kamar ana Sanya Mata Mai nan Ko tsabar tsaftace DA gayu Sanye yake cikin wasu had'addun Kaya shirt din rigarshi pink Sai bak'in Wando Duk cikin second baifi biyu ba ta k'are Mai kallo saitaga lokaci guda yayi Mata kwarjini tayi niyyar Mai Rashin kunya Amma kawai saitaji ta kãsa Saboda four eyes din DA sukayi cikin sweet voice d'inta tace "Ina ne department d'in naku".




Najib Yi yayi Kamar badashi take ba Hakan Ko ba. K'aramun ciwo yayi Mata ba Tsaki taja ba tare DA ta sani ba ta juya Amira ce tace ''Yaya Najib DA kai take ina ne department d'inku"Ba tare DA ya d'ago ya Kalli Daya daga cikin su ba yace "ya Isa nan zank'arasa ya fad'a Yana Bude motar tare DA fita .




Najmat tanajin fitarshi Tsaki ta Kuma ja k'asa_k'asa tace "Aikin banza kak'i cewa da kanka zakazo tun a gida ba Saida muka kawo ka ba "Najib ya jita sarai danshi koya kayi magana saiya jika "wucewarshi yayi ba tare da ya Kula ta ba Dan ya lura kwata_kwata yarinyar ta rainashi mamaki yake a rayuwarshi Babu macen DA zata iya hararanshi Bare Har akai GA fadin magana Hasalima tsoronshi Ake DA shakkarshi Duk inda yaje Amma yalura kwata_kwata yarinyar Bata tsoronshi Ko shakkarshi Tsaki yaja tare DA aniyar koya mata hankali Dan bazai iya d'aukar raini Daga wajen Ko Wani irin mutum ba musamman ma mace Da Bata isheshi Kallo ba.





Jin abunda Najmat tace dariya Amira taja tace "kai Dusti wallahi bakyajin magana Kin raina Yaya Najib "tab'e bak'i Najma tayi tare DA kwaikwayar Amira waiwani "Yaya Najib"Su Yaya manya sannan taja Tsaki "dariya Amira tayi kamar ta tuno DA Wani Abu Mai mahimmanci tace lah Dusti kinsanme "A a Dusti saikin fad'a Najmat tafad'a tana zumudin Jin Sabon labari "Wallahi Sunanku yayi matching *NAJIB* And *NAJMAT* Wow Dusti Kuma wallahi a fuska ma kunyi matching Har wani kama Kuke gaskiya ba k'aramun dacewa kukayi DA soyayya ba tundaga sunayenku Har Fuskokinku.





Duk inda kololuwar b'acin Rai Yakai Najma ranta ya baci batasan lokaci DA ta tik'awa Amira k'ulli a baya ba cike DA masifa tace " ba a tab'a cimun mutunci irin Na yau ba yanda kika cimun Dusti wallahi Kinyi mugun gamawa Dani ki rasa Wanda Zaki had'ani dashi Sai wannan sunduk'in kinmayi mugun rainamin wayau "Ta ida fad'a tana Shirin kai Mata Wani tuluk'in Amira tayi Maza tabude Kofa tana dariya tayi waje tare DA cewa "Sorry babyn sunduk'i Bye Sai anjima tafad'a tana cigaba da dariya tare DA barin wajen Najmat cike da haushi ta fito tana cewa "Ai zamu Hade kinsan bashi kikaci wallahi.




A ranar Najib ya ida cike_cikenshi yafara attending lectures Around 3:00pm ya gama lectures dinshi kai tsaye capteria ya nufa Dan yad'an Sanyawa cikinshi Wani Abu.




Tun Daga shigarshi wajen y'an matan dake wajen suke kallonshi Suna Yaba kyawun halitta irin Tashi Tsaki yaja a ranshi Dan ya tsani irin.kallon DA mutane Ke mashi Zaunawa yayi nan ma'aikatan

Please Login or Register in order to submit comment