Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

stones ne rigar tayi iya haduwa Sannan ta d'auko belt din rigar ta nadashi nadin larabawa sak Najma tafito balarabiya ita ba balarabiya ba ita ba bafullatana ba ita ba baturiya ba haka ba bahaushiyaba nama kasa gane da wata kala tayi kama Dan iya haduwa ta zubu.



"wow tafad'a data Duba kanta a madubi ''gaskiya nayi kyau ta fad'a tana Murmushin Daya lotsarda dimple d'inta turarruka Kala-kala ta feshewa jikinta masu sanyi k'amshi Kasancewar Najma mace ce Mai son k'amshi Nan ta d'auko takalmin ta Mai Dan tudu ta sanya.



Palour ta fito Dan Amira tarigata fita cikin takunta na k'asaita kamar batason ta taka k'asa "Wow daughter Ammafa kin had'u Aunty Nafisa tafad'a tare da tasowa tayi hug d'inta Murmushi Najma tayi tace thanks my mom Abiy ne ya fito Shima ya Yaba kwalliyarta Sannan suka jera ita da Abiy suka nufi hanyar dazai sadasu da inda driver yake jiransu bayan sunyiwa Aunty Nafisa bye bye.





Suna Isa Abiy ya shiga Front sit Najma da Amira suka shiga back seat driver ya jasu ''jiyowa Amira tayi tace ''wow Dusti kinyi kyau"Murmushi Najma tayi tace ''thnks Dusti like you kema kinyi kyau"Murmushi Amira tayi tace "Ai bankaikiba haka sukaci gaba da hirarsu jefi jefi har Abiy Har suka isa makarantar.




Saida Abiy ya tsaye aka gama musu komai da cike cike Sannan kowa yayi department d'insu Kasancewar ba course d'aya zasu karanta ba Najmat zata karanci permancy itakuma Amira Economic zata karanta.




Tunda suka shiga school din kallo ya Koma wajensu musamman Najma wasu har tuntub'e suke Dan kallonta Tatafi da imanin su musamman samarin school din Hatta Yan Matan Saida ta burgesu.



Mutane suna son tunkaranta hatta Mata suna son suyi friendship da ita Amma ganin yanda take Jiji dakai da daddaurewa Dan sun lura yarinyar tana ji da class bama kad'anba Basu tunkareta ba.



Koda 2pm tayi tagama lectures d'inta bayan tafito Amira takira ring biyu tayi picking"Dusti Kun tashi kuwa tafad'a cikin cool vooice d'inta "eh Dusti ai tun 1 muka tashi harna Kira driver inama cikin mota "okay to ganinan tafad'a Dan tagane inda driver yayi parking kai tsaye chan ta nufa tana shiga driver yaja suka tafi.




Haka rayuwa taci gaba Najma da Amira sun maida hankalinsu sosai akan karantunsu ba wasa musamman Najma Dan yanzu kullun cikin karatu take da bincike da course d'insu akwai wahala Harkar gabanta kawai take a school din samari da Dama sun kwata suna sonta masu kasada harsu tunkareta Amma ko kallo Bata ishesuba Dan kwata kwata soyayya Bata gabanta ita dai burinta taga ta kammala karatunta ta zama kwararriya Likita Kawa d'aya tayi tunda tashiga Mai suna Raliya Yar Ghana ce itama Dan taga tana da hankali da nutsuwa ga kuma itama karatu yakaita Hakan yasa suke friendship da Najmat Najmat Kam ba abunda zatace sai Alhamdulillah Dan tana ganewa sosai da sosai Dan kaf department d'insu yanzu haka ba Mai k'ok'arinta Dan ko tambaya akayi kowa sai kasa Bada amsa Amma Najma zata tashi ta bada Hakan yasa ko a class din suke ji da ita Dan tana mugun burgesu wasu har haka suke cewa ga kyau ga ilimi ga gayu komai ta had'a.



Hakan yasa kowa yake jida ita tun Bata sakewa mutane fuska harta dawo tana sake musu saboda ganin yanda suke Nuna mata kauna Amma Bata sake musu irin dai wasan wannan da maza da mata suke tsakanin dalibai dadai sauran su a a a mu'amula suke Mai cike da tsafta yawaicima duk akan harkan karatunsu ce.




*NIGERIA*🇳🇬
*KADUNA*


Kamar yanda mahaifiyarta ta umarceta Haka sa adatu tayi hankali kwance batare da wani zargiba Dan tana da freedom a gidan Nan ko Ina shiga take bangaren Yaya najib ne kawai bama ta tarki tinkaraba dan Babu wasa.



Yau Friday Abba yadawo daga china Babban danshi mafi soyuwa a wajenshi yakira ya d'aukeshi haka har suka isa suna hira gwanin Sha''awa Kasancewar Umma take.dashi ya sashi Fara nufar b'angaren Aunty Amarya.



Yasamu tarba ta musamman daga wajen Amaryar tashi Dan Amina badai biyayya ba Hakan yasa Abba yake matuk'ar sonta Sai bayan magriba ya nufi b'angaren Umma .





Khairat ce ta Fara mashi sannu da zuwa Tare rungumarshi Tana Mai sannu Nan ma sa adatu tayi Mai sannu da zuwa ya amsa Mata cikin sakin fuska Umma ko ko kallonshi batayi ba dan taga lokacin Daya shiga b'angaren Amina.




"Uwar gida sarautargida" Abba yafad'a Yana zama kusa da ita bayan su khairat sun Basu waje murtukewa Umma tayi tace "Ba wani dad'in baki saika koma inda kafito''murnushi kawai Abba yayi Dan yasan halin mutumniyar Tashi indai akan Amina ne Nan dai ya basar yayi ta lallashinta har ya samu ta sauko Bayan sun Tab'a hira a palour Nan Abba yace yagaji baccci zaiyi daki Umma ta rakashi tare da jera Mai sannu Yana Sanya Mata albarka toilet ta shiga ta had'a Mai ruwa wanka shikuma yazauna kan gado Yana zauniya yaji kanshi yayi wani mugun sarawa dafe goshinshi yayi Dan wani juyamai yake Umma tana fitowa salati tayi tace Abban NAJIB lafiya ".



Tsaki yaja Dan Yana ganinta yaji yayi wani mugun tsanarta tashi yayi yayi hanyar Kofa binshi Umma tayi tace Ina zaka Abban NAJIB ya Muna Zaune lafiya lokaci guda ka sauya"Tsaki yaja yace Karki sake ki biyoni jidda kawai ji nayi bazan iya kwana a D'akin Nan nakiba Ina ganinki naji kawai na tsaneki "ya fad'a Yana nufar Kofa kuka Umma ta Fasa tace ",nashiga ukku Amina Allah ya isa tsakani na dake nasan ke kad'aice macen da zata rabani da mijina Amina sakayyata dake sai Allah tsinewa Amina Umma kawai take.




Abba Kai tsaye b'angaren Aunty Amarya ya nufa ita kanta tayi Mamakin ganin nashi Ganin Harya kwanta ya sanyata Mai magana akan wajen Umma yake ba yanda batayi dashiba ya koma yakiya karshe tsawa ma ya daka Mata ba arziki taja bakinta tayi shiru tare da komawa bedroom d'inta ta kwanta cike da tunannika.




Tun daga ranar Nan Abba Bai Kara shiga b'angaren Umma ba Aunty Amarya Tasha wa azin da nasiha Amma a banzan Wata Rana kuka ta Sanya Mai tace Dan Allah ya taimaketa wannan abun da yake Yana k'ara ruruwar rashin jituwar dake tsakanin ta da Umma Karshe Chayai ta Kara Mai maganar Umma zai mugun Sab'a Mata saijan bakinta tayi shiru amma tana addu'a komene ya shiga tsakaninsu Allah ya daidaitasu.



A haka har sati biyu b'angaren Umma duk ta rame abun na mugun damunta kullun cikin addu'a take Allah karkato Mata hankalin mijinta a zuciyarta kuwa tsanar Amina ce kawai Dan ita take da tabbacin tashiga ta fita ta rabata da mijinta da abundai ya dameta.


Wata Rana ta shirya ta tafi gidan kanwarta Asiya Tana kuka ta kwashe komai ta fad'a mata asiya ko a Zuciyarta kamar ta tsala guda Dan farinciki Amma a Fili hada k'wallarta tace "wallahi Aunty Jidda Babu Mai rabaki da Alhaji sai Amina yanda Alhaji yake mugun sonki tunda kike dashi Bai tab'a Koda fushi dake ba Amma kiga wai har sati biyu Yana gida baixo inda kike ba,ai na fad'a Miki Amina muguwar Yar bin bokayece. "Nan dai Asiya tayi ta zagin Amina daga k'arshe tace ''yanzu mafita daya ce kawai tashi zakiyi muje wajen malam barau indai mukaje wajenshi magana takare "ta Ida fad'a azuciyarta tana adduar Allah sa ta amince.



Jim Umma tayi sannan tace ""Gsky asiya kisamo Wata mafitar Amma wannan baxanyiba nayi Alk'awarin bazan tab'a shirkaba harna Koma ga mahaliccina,"a Zuciyar asiya ji take kamar ta shake Umma da haushi Amma a Fili tace to Shikenan Aunty Allah kawo Mana Mafitar amen Umma tafad'a sannan ta Koma gida asiya ko tana fita taja tsaki tace watau duk mugun cin Dana Baki har yanzu bakiyi lakwas ba Harkina da bakin yimun gaddama sannan tace ,"tunda Babban aikin yaci ai alhhmdlhh Sannan Tayi shewa tace shegiya kwanannan Zaki fara zawarci kinkusa fitowa Daga daularnan kina ganin ke ga matar Mai Kud'i Muna zuwa kina bamu dubu Dari dubu hamsin ai Wallahi saimun daidaice Koma mu fiki ai karyane ki fimu wlh......✍🏿



*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*





*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[10/6, 7:22 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴

*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*Shafin Nan sadaukarwa ne gareki sis quen pherdaus kiyi yanda kikeso dashi inajin dad'in sharhinki over love u wujiga wujiga*😅

_________________________________
*PAGE 21 & 22*
_________________________________


Najib ne zaune a palourn Aunty Amarya suna fira jefi jefi Amma ya lura kamar da abunda ke damunta Koda ya tambayeta Murmushi kawai tayi tace ,,"bakomai son".



Najib ne yace "Aunty Dan Allah wani taimako zakiyimun game da khairat,inajinka son "Saida ya Dan numfasa sannan yace ''Aunty bazan boye maki ba wannan sa'adatun da take tare da khairat ban yarda da tarbiyarta ba dukda tana Yar uwata Amma bazan bari ta lalatamun. K'anwa ba saboda Wata kusar tafi Wata Aunty yanzu na lura Khairat Kamar ba lokacin dawowa daga school take dawowa ba Kuma na lura Time d'in da take school Sa'adatu yawaici Bata gida Aunty Dan Allah kutaimaka mun muyi yak'in Nan tare Ina hango babbar matsala game da mu'amular su.




Shiru Aunty tayi Dan a gaskiya bazaiyu ta b'oye Mai wani Abu ba Hakan yasata fito da gaskiyarta tace "Gaskiya zan fad'a Maka najib Amma Dan Allah karka dake ta akwai shawarar dazan baka tafi duka mahimmanci.


"sannan ta d'ora da cewa"cikin satuttukan Nan biyu gaskiya yarinyar Nan Sa'adatu tana zuwa school a mota tana d'aukarta Kuma lokacin da zan dawo gida bana ganin dawowarsu Nima ban yarda da tarbiyarta ba Amma Aikin Nan Mai sauk'i ne khairat batayi gaurin da za a kasa lank'wasata ba Dan gaskiya Ina yimusu lectures sosai bantabajin ance ga matsalarta ba Amma ayi sauri a rabata da wannan yarinyar Dan zata iya gurb,'ata Mata tarbiya".




"Innalillahi kawai najib ke ambata Dan Kanshi yagama daurewa Lallashinshi aunty Amarya tafara tace karka damu son Zan taimaka matuka Ai khairat y'ace a wajena zanbaka gudummawa sosai "yawwa Aunty inajinki Dan kaina yagama kullewa wallahi da khairat harararta nayi tabar Abu Amma zuwan yarinyar Nan nema take ta rikitamana family wallahi.



"Allah kyauta kawai tace sannan tadora da cewa"zan kawo Maka time table d'insu Lokacin zuwa da lokacin dawowa kaga kasan lokacin 2zuwan ta da dawowa saika bawa driver Time table din kaima ka rik'e ">




"Gaskiya Aunty kin kawo shawara Mai kyau Dan wlh da niyar aurar da ita nake Dan nagaji karatunma da barinshi zatayi wallahi" Murmushi Aunty tayi tace ,"sorry babban Yaya"sannan yace "Amma aunty shawarar Dana yanke zan maida ita gidan Hajiya da zama.



""Shikenan Magana ta kare abunda nake Shirin cewa kenan kamaida ita haka yafi dadai Nan dai suka cigaba da tattaunawarsu gwanin sha'awa kamar d'a da uwa.




Kamar yanda sukayi shawara da Aunty Amarya haka ko akai yasa khairat ta had'a kayanta sannan yayi mata kashedin wlh tasake tafadawa sa'adatu ga inda zai kâita zaiya mugun Sab'a mata Umma da Abba Kawai yafadawa Abba ma yayi na am Umma kam cewa tayi Allah kiyaye Dan Bata da matsala da gidan hajiyarta.





Sai da yasa ta had'o kayanta gabak'i d'aya Dazasu wuce Saida ya biya b'angaren Aunty Amarya Nan ta bashi turaren wuta da Turarruka masu tsada tace ya kaiwa Hajiya sannan ya gaishe Mata ita.






A palour suka tarar da Hajiya akan carpet khady na Mata dannar k'afa da fara arta Hajiya ta tarbesu tace "yau inada manyan Bak'i kenan Masu bakin Hali biyu a gidana".




Murtukewa najib yayi yace "ai Shiyasa na daina zuwa gidanki yanzuma sai na Koma ai"haba Mai gidan wasa ne fa Nina Isa sannunku da zuwa khairat ko sai murtukewa take tanajin haushin maidota gidan Hajiya da yaya najib yayi tadawo kurkuku kawai Dan Hajiya badai tsaro ba" harira bak'in halin ne Zaki fara ko Hajiya tafad'a tana kallon khairat,".




Duk inda Khairat takai shak'uwa ta shak'u Dan ba sunan data tsana a kirata dashi irin real name d'inta a zuciyarta tace Nidai an cuceni da akasamun sunan Nan sunan Mahaifiyar babansu ce Aiko ta shaku tace "Kinga dalilin dayasa banason zuwa gidanki Nafad'a Miki bansson sunan Nan inbanda ke Babu Mai fadamun tafada tana tashi tanufi bedroom d'insu Nan tahadu da Yar uwarta kawarta Kuma sarat Aiko kankace me sun rungume juna suna hirar yaushe Gamo.




Hajiya ko tab'e Baki tayi tace " kinji dashi Malalaciya sannan tace "Kai yanzu Najib haka zakayi ta zama ba Mata duba fa kaga sa'anninka wasu hada y'ay'a,najib yaushe zakayi hankali wai,Ace duk fad'in Matan k'asarnan kace ba wadda tayi Maka haba Najib kayiwa kanka fad'a kafin duniya tayi maka ni gaskiyace nake fad'a muku saikuji haushi ku tafi Kuna cewa ni fad'a a yau mai Maka fad'a masoyinka ne NAJIB wani Neman Mai mashi ma yake Amma ya rasa Dan Allah najib Kar nabar duniya Banga auranka ba ka haba Najib kamar Kai ace ko budurwa baka da ita ".




Shiru najib yayi Yana sauraran Hajiya Saida tagama fadan ta hak'uri kawai Yabata yace "insha Allahu Hajiya Zanyi komai lokaci ne"sannan ya d'auko sakon Aunty Amarya Yabata Kuma yace tace tana gaisheki.



"Allah sarki Amina yarinyar arziki wannan yarinyar Samun irinta sai an tona Allah dai ubangiji Yayi Mata albarka Yazaunar da ita gidanta lafiya ai Wallahi Jidda tayi sa'ar kishiya Amma malalaciyar Bata da mak'iyar da ta fita Ai Jidda yanzu nema take tafi k'arfina najib kadufa fa kaga Jidda Bata da Masoyan da sukafi makiyana Wanda basa kaunata basa kaunar Mai kaunata Haule. Da d'iyanta ,(uwar su asiya) Yanda ta d'auki Haule da daraja koni Dana dukursa na haifeta Bata d'aukeni da daraja ba fada kawai Hajiya take hada k'wallarta najib ko hak'uri kawai yake Bata sannan sukayi bankwana yanufi wajen aiki.



Sa'adatu ta nemi Khairat ta rasa takirata tak'i d'agawa Taje school d'insu yafi a k'irga amma Bata Samun ganinta Hakan ba k'aramun dakula Mata lissafi yayi ba ganin dai ba alamun Nasara Akan Khairat yasanyata janye makaman aikinta.





Tana kuka ta samu mamanta tace "Allah mama idan bakiyi maganar aurena da yaya najib ba Zaki nemi ni ki rasa haba mama nagaji wallahi nidai kawai ayi auran Nan kowama ya huta kuka kawai take .




Asiya duk ta rud'e Hakan yasata lallashin Yar tata tare da shaida Mata gobe zataje gidan tayi magana da Umma Kawai Daman yanzu ne lokacin da take jira.




Kamar yanda asiya tafada haka washegari Taje har gida ta samu Umma da maganar hada Auren najib da Sa'adatu Umma tayi na'am sosai da wannan Maganar Kuma taga dacewar Hakan a hadasu Auren zumunci Dan. Itama ta gaji da ganin Najib haka ba Aure Saida suka gama shawarar su sannan suka fito Umma ta rakota .


Asiya ce ta hangi Aunty Amarya na Shirin shiga Mota Aiko da gudu tayi baya tare da boyewa bayan flowers gabanta in. Banda dufduf ba Abu da yake Dan yau da ace sunyi Ido hud'u da Amina Aida tata ta kare Saida taga fitar motar ta sannan ta fito tana huci Umma da abun yagama Bata mamaki ta lura duk tsawon zaman Amina a gidan Asiya Bata tab'a yarda suka haduba data ganta take boyewa.




Tambayarta Umma tayi tace Anya asiya Babu abunda ke tsakaninki da Amina kuwa"basarwa Asiya tayi tace bakomai wallahi aunty kinsan nafad'a Miki mayya ce to tsoro nake karta cinye ni ,"Amma Aida mayyace asiya Dani da diyana zata fara lashewa kafin ku na waje uwa ubama Fena da tsawon shekaru ukku a wajenta ,"Cewar Umma "Aunty bazaki gane bane kinsan ni tsoron mayu gareni tab'e Baki Umma kawai tayi ba don ta yarda da zancen Asiya ba Cewar Amina mayyace Dan idan mayyace ai su zata fara cinyewa kafin na waje asiya ko harta fita gabanta fad'uwa yake Dan yau ta auna rijiya da baibai dan yanda takeji da Amina ta ganta gwara tayi Gamo da rundunar aljannu Ido da Ido......✍🏿




*Tofa meye ke tsakanin Amina da asiya da take tsoron had'uwarsu haka*🤔



*Ya kenan Najib zaiyarda da had'in wannan kuwa tsanar da yayiwa Sa'adatu zata bari ya yarda ya aure ta kuwa*🤔




*Shin wai menene ma asalin Tarihin su najib*


*Amsoshin Nan duka suna next page kudai kuci gaba da bibiyata Dan wasan baima fara ba tukwana ba ayi komai ba*



*Najmat abiy fans zanyi tankad'e da rauraya Dan gaskiya duk Wanda yaga na cireshi baya comment ne idan kasan kana karanta book d'innan baka comment ku gyara please Dan duk Wanda na cire ya fita kenan bazaiyu Ina Bata lokaci wajen typing Kuma ka karanta just comment ya gagara please Cwthearts agyra Dan ina da uzurirrikan danake saki ina muku typing yanzu haka haihuwa aka mana amma dan na faranta muku bandaina typing ba idan naga baku gyara ba Nima zan hutashshe da kaina nadaina typing huta roro*😊




*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*




*_Mhiss Hajo ce_*🤙🏿
[10/11, 11:06 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
___________________________________

*PAGE 23 & 24*
___________________________________



*INDIA*🇮🇳
*NEW DELHI*

su NAJMAT karatu Ake Babu kama hannun yaro Dan yanzu haka sun shiga level 2 Aunty Nafisa ta haihu inda ta haifo santalelen.baby boy d'inta Wanda yaci suna Umar Faruq sunan Abban.su Amira aka.sanya Mai matuk'ar kama da mamansa zo kuga murna.wajen su Najmat yaron Kam Yana shan.gata da soyayya wajen yayartashi Dan indai tadawo daga school tofa Yana hannunta Yana Shan wasa haka. Rayuwar wannan family taci gaba gwanin sha',awa Aunty Nafisa da Abiy sai yanzu suke Kara fariincikin hada aurannan da Abba yayi suka k'ara jinjina lamarin ubangiji inda aka fayyace musu Najma da Amira suka Ida hadawa Aiko sunsha Shan albarka su Najma agurin Abiy da Aunty Nafisa Abba da Ummy ma sunyi farincki matuk'a Wanda har yanzu Najmat Cikin zuciyarta tana mak'ale da tunanin mahaifiyarta da Bata San wacece ba.



*NIGERIA*🇳🇬
*KADUNA*

*WANENE NAJIB*



Alhaji abubakar najib shine mahaifinshi hamshak'in Mai arzik'ine da yayi suna a ciki da wajen jahar kaduna shahararran d'an kasuwa ne Wanda yawaicin harkokinshi a kasashen waje yakeyinsu mutum Mai tafiye tafiye Wanda tafiye tafiyen nashi akan kasuwancinshi ne NAJIB ne babban danshi Wanda yake matukar ji dashi Hakan yasa ya Sanya mashi sunan mahaifinshi najib tunda ya tashi miskiline Wanda idan kaga maganarshi ko dariyarshi tofa Yana gaban umman shine ko abbanshi yataso Cikin gata da soyayyar iyaye ga farinjinin jama'a yayi saukar alkqur',ani Mai girma har saubiyu yayi karatunshi tundaga kan pri har degree dinshi inda ya Yi karatunshi a America ya karanci medicine Kasancewar tun Yana yaro yake mugun son ya zama doctor.



alhmdllh Kuma burinshi ya cika tunda Yana gama karatunshi mahaifinshi ya gina.mai katafaren asibiti ya kashe mak'udan kud'ad'e Wajen Gina kanshi asibitin inda aka sanyawa asibitin SUNA * N A N SPECIAL HOSPITAL KADUNA* Ma'ana *NAJIB ABUBAKAR NAJIB*.





Najib Koda yayi karatunshi Baitaba budurwa ba saboda yanda Yan Mata ke rud"ewa idan suka ganshi saboda Najib saurayine kyakyawan gaske Dan kyanshi har tsorata mutane yake hakan yasa Yan Mata suke rububinshi Wanda ko kallo basu isheshi ba.




Hakan yasa ya tsani Yan Mata saboda gani yake duka haka suke Basu da class shiko.a tsarinshi bazai Auri mace marar Aji ba yanda yake ji da kanshi bayajin zai Auri ballagaza Wanda yanzu haka shekaru talatin da d'aya garai Amma har yanzu Bai da ko budurwa saboda bayajin akwai macen da ta Isa ya sota a tsarin rayuwarshi ma shi Babu soyayya Habib abokinshine tare sukayi secondry school Shima yakaranci b'angaren lafiya ne Hakan yasa suna gamawa Najib ya d'aukeshi aiki inda suke gudanar da Al"amuransu tare ba a tab'ajin kansuba tunda suka taso Saika rantse ma Yan uwa ne Shima dai Habib har yanzu baiyi aure ba amma Yana da budurwa.




Najib k'annanshi ukku
Khairat sunanta harira sunan Mahaifiyar babansu ce tana da shekaru 19 a yanzu sai khadija Mai shekaru 16 wacce take zaune ne a gidan kakarta ta wajen uwa sannan autarsu da har an cire rai Allah yabasu Mai suna Nafisa suna ce Mata Fena Ganin Aunty Amarya tunda aka aurota Bata tab'a Haihuwa ba gashi tana mugun son yara Hakan yasa Abba ana yaye Fena yabawa Aunty Amarya ita halak malak ansha ko bala I wajen Umma ba irin ruwan masifar da batayiba Amma Abba yaki sauraranta Haka Fena taci gaba da rayuwa b'angaren Aunty Amarya sun shaku kamar ita. Ta haifeta Tana Bata kulawa sosai da sosai Hakan ko ba k'aramun dad'i yakewa Abba ba danko Umma bazatabawa Fena kulawar da Amina ke Bata ba b'angaren Fena ma tana mugun son Aunty Amarya Dan Umma ta tab'a kwata Amsar Fena inda ba irin ruwan tijarar da batayiwa Amina.ba Ashe Abba Yana jinta har sanda take ce Mata juya maganar Tayi mugun tab'a Mai zuciya.



Aiko Tasha wulak'anci wajen Abba Dan har marinta yayi Aiko tundaga lokacin ta K'ara tsanar Amina tanace Mata ita tayi asiri ta rabata da mijinta .



Yaran gidan sun tasone cikin had'in Kai da k'aunar juna suna mugun tsoron Yaya NAJIB Dan baya musu wasa Ko kad'an Mahaifiyar su Hawwa'u Jidda Macece Mai bala'in kishi Dan Bata tab'a zaton Alhaji zai k'ara aure ba kwatsam saigashi ya k'aro aure fadar tashin hankalin da Umma ta shiga Bata bakine tunda aka Auro Amina gidannan Bata da kwanciyar hankali ta tsani Amina Bata k'aunarta Amina kwata kwata Amina ko daidai gwargwado tanayiwa Umma biyayya ummako kullun kiyayyarta Kara ninkuwa take a cikin zuciyarta.



Amina lecturer ce a KASU kaduna macece Mai tsananin kyau ,ilimi ladabi ,biyayya uwa uba tarbiya ga son yara jininsu yazo Daya da najib saikace uwa da d'a idan suna fira duk miskilancin najib Amma bayayiwa aunty Amarya Kasancewar haka yaran gidan suke ce Mata.



Khairat da ta tarki yiwa Aunty Amarya rashin kunya tunda NAJIB ya taka Mata burki Bata sakeba itama khairat a kasu take karatu yanzu haka tana level 2.



Asiya kanwar Umma ce ubansu Daya Umma batajin maganar kowa idan Bata asiya ba da uwarta Asiya da Mahaifiyar ta da Yan uwanta basa kaunar Umma DA mahaifiyarta saboda basuyi zaman dadiba musamman umma sun tsaneta saboda tafisu rufin asiri tafisu dacen Miji dukansu


Amma a Fili basa Nuna Mata yanda suke Nuna.mata sunfi kowa k'aunarta amma a zuciyarsu ji suke kamar su cinna Mata wuta itako Umma ta d'auka duka kenan Dan ita da zuciya d'aya take zaune dasu.



Asiya bayanda batayi da Umma ba akan tarakata wajen Boka a fitar Mata da Amina Amma Umma ta k'iya sabida macece Mai tsananin tsoron Allah tana da fad'a sosai Amma Kuma fad'an ta iya Baki ya tsaya Dan kome zai sameta tofa tana fallamawa Allah komai.



Asiya muguwar makira ce ta bugawa a jarida ta kware wajen hada makirci kashe aure kuwa a wajen ta kamar kashe tururuwa ne gashi Bata da godiyar ubangiji Dan mijinta D'ansanda ne sunyi zaman garuruwa sosai inda Duk garin DA suka zauna saita ha'da makirci.daidai gwargwado Bata nemi komai ta rasaba Amma Bata hangen nata na wani take hange ta Raina rufin asirinta Mijinta malam Sani ta

Please Login or Register in order to submit comment