Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

khady tace ''shegiya love Baki da wasa kin damk'i Yaya najib da yawa wallahi ba k'aramun dacewa sukayi ba Yaya yayi Babban kamu wallahi"Dariya Khairat tayi tare da wak'ar "soyayya ruwan Zuma "haka sukayi da Mai shak'iyanci.



Kai tsaye gidansu najib suka nufa Horn yayi get man yafito ya Bud'e suka shiga bayan Sunfito sai hira suke suna Murmushi a lokacin har amfara kiraye kirayen magriba.



Hakan yayi daidai da fitowar sa'adatu zata fita Yawon banxanta data Saba tayi wannan mugun ganin Yaya najib da wata.ta fad'a a Fili cike da mamaki Harsuka kusa zuwa inda take tana Kallonsu zuciyarta na matuk'ar tafasa ganin kyakyawar budurwar dasuka fito tare tasan bama zata iya had'a kanta da yarinyar ba tafita komai batasan lokacin da wasu zafaffun hawaye suka zubo mata ba a guje ta Koma part d'in Umma ta rufe bakin ta da hannunta Dan rik'e kukan Daya taho Mata Amma ya gagara sosai ta fàshe da kuka kamar wacce akace uwarta da ubanta sunmutu lokaci Daya .



Tab'e Baki najib yayi a zuciyarshi yace "'sakarai y'ar wahala "Tambayar shi Najmat tayi tace "wacece ko kanwarkace ?



girgixa Mata Kai yayi yace "y'ar aiki ce'' Dan sosai yakejin haushin a Kira banzar yarinyar chan da k'anwarshi shikadai yasan bakin cikin dayakeji Dan sosai ya tsani Sa'adatu bakomai yasanya hakanba sai lalacewarta a rayuwarshi ya tsani Yaga y'ar iska ko d'an iska sosai yake k,'yamatarsu Babban abunda ya K'ara sawa ya tsaneta labarin daya samu cewa Sa'adatu y'ar mad'igoce Babu abunda ya tsana a rayuwarshi sama da wannan abun Hakan yakara ninka tsanar ta a cikin zuciyarshi ga kuma k'yamatarta da yake Dan zai iya rantsewa Koda Kud'i bazai îya cin abun hannunta ba Kuma bawai Bata da tsafta bane kawai shi haka yake da kyamatar Dan Iska .




Hakan ya sashi cewa Najmat"y'ar Aikinsu ce"Gyad'a Kai NAJMAT kawai tayi part aunty Amarya suka nufa yace Mata "Bari na kaiki b'angaren auntyna kugaisa sainaje nayi sallah kema kiyi .



to tace sannan suka nufi part d,'in door belt ya danna aunty Amarya tafito ta Bud'e musu turus tayi ganin Najmat gabanta cike da mamaki tace "pretty"Itama Najmat cike da mamakin ganin matar data jima tana burin sake ganinta tace "Aunty tare da nufarta cike da farincikin sake ganinta tayi hugging d'inta itama hugging d'inta Aunty Amarya tayi cike da mamaki najib ya tsaya Yana Kallonsu a zuciyarshi yace "Sun San juna daman''.



Sunjuma rungume da juna sannan suka shiga Kowannensu fuskarshi d'auke da tambayoyi najib ne ya kasa daurewa bayan sun zauna yace "Aunty Daman kin Santa ne daman........✍🏿





*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*






_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment