Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi har kasa ya gaisheta ta amsa cikin fara'arta motarta ta shiga ta wuce Shima motar ya shiga a bakin gate ya tambayi security d'in akan Saida yaushe su Sa'adatu suka dawo d'an Jim bala yayi yace "Gaskiya inaga lokacin 12 ta kusa"bai bashi Amsa ba ya wuce Yana Jinjina sakacin da umma ta tarka har 12 yara na waje ko a kanta.





katafaren clinic Ne Mai matuk'ar tsaruwa da girma Yana Daya daga cikin manyan asibitocin da ake ji dasu a jijar KADUNA. Saboda akwai k'wararrun likitoci cikinshi *N.A.N.SPECIAL HOSPITAL KADUNA* tun daga shigowar motarshi tun kafin ya fito ake mik'omai gaisuwa d'aga musu hannu kawai yake Har ya shiga office d'inshi gaisheshi ake.




Zaune yake.yana wani bincike a laptop Habib ya shigo d'ago kanshi kawai yayi yamaida ga Aikin da yake tsaki NAJIB yaja yace ,"mutum sai d'an banzan miskilanci dariya ma mutum bayayi Dan mugun Hali sai Jan aci kamar mace "ko kallonshi najib baiyiba Dan yasan dashi yake Saida yace "Akwai patient da za ayiwa aiki yanzu sai sannan Yad'ago yace "okay kuje kushirya ganin Nan zuwa "NAJIB ne yace "Okay Amma abokina Kamar yau da abunda ke damuka"



"Me ka gani inji NAJIB"kawai naga kamar ranka a b'ace "Bakomai Cewar NAJIB sannan ya tashi Dan yayi Shirin Shiga aikin.




4pm ya dawo gida Kasancewar yau ba ba ayi aiki da yawa ba Yana dawowa bayan ya watsa ruwa Kai tsaye b,'angaren Umma ya nufa Yana shiga palour yadanyi Murmushi yace ,"Ummana sannu da hutawa"itama Dan Murmushi tayi Dan bazata iya fushi da first born din nata ba "tace yawwa har andawo ya Aikin alhmdllh Umma to Allah ya tsare ya Kara karkun Kai amen ya fad'a dan yaji dad'i saukowar tata da wuri dukda sun Saba irin haka Kuma ta sauko.





Sa'adatu ke gaisheshi ko kallon inda take baiba bare ta sa ran ansawa Hakan ba k'aramun ciwo yake Mata ba tarasa me tayiwa Yaya NAJIB ya tsaneta haka gashi ita.kuma.har kullun wutar sonshi k'ara ruwawa take a cikin zuciyarshi Umma ce tace "Uban bakin Hali bakaji Yar uwar ka na gaidaka ba shi haushi ma yaji da Umma ta kirata da Yar uwar shi Bai amsa Mata ba sai cewa yayi"Ina khairat yafad'a Yana kallon Sa'adatu Babu alamun wasa a fuskarshi "Ta na d,'aki ta fad'a Dan taji dad'in Tambayar tata ma da yayi a zuciyarta tana tsoron kome zaiwa khairat yake tambayarta Dan tasan Daya tambayi mutum tofa laifi ne.





Tashi yayi ya nufi bedroom d'in su khairat A kwance ya sameta tana waya Daman ya nad'e belt d'inshi Aiko ya zaro batayi aune ba tafara Jin saukar belt ihu take baimasan tanayiba zuba Mata kawai yake tako ina.




Nan su umma sukayo dakin Jin ihun da khairat dasukajiyo "salati Umma Tayi tace "uban Me ta maka Dan ubanka zaka haumun d'iya da duka "baimasan Umma nayiba laftar khairat kawai yake rikeshi Umma ta fara tana karka kashemun y'a NAJIB Amma baima saurareta ba Dan yau saiya koyawa khairat hankali kuka.umma ta fàshe dashi tace "NAJIB ka hada Dani ni zaka daka ba itaba Saida khairat ta Suma Nan Umma ta buga K'ara Nan ne NAJIB ya k'yaleta sai huci yake Bugunshi da hannu Umma ta fara tace ka kasheta hankalinka ya kwanta da gudu sa adatu taje ta d'auko ruwa ta yayyafa Mata dandanan ta kawo ajiyar zuciya tana daga Ido tafara kuka tana "Yaya Dan Allah kayi hak'uri ta fad'a tana boyewa bayan sa,'adatu.





Umma ce tace ficemun daga da'ki NAJIB ficemun da ganin ko Kuma Nima dukan nawa zakayi dakayimun tsaye "kiyi hak'uri Umma zan fita sannan ya Koma kallonshi gurin khairat yace "Wallahi kad'an na Miki mudddin bazaki chanza haliba nafara jibgarki kenan kamar jaka.a gidannan sannan ya gallawa Sa'adatu harara yace "ke Kuma wallahi daga yau na k'ara ganin kin fita keda khairat ko wani a gidannan saina Miki abunda yafi nata daga yau na rabaki da ita Babu ita Babu ke ko d'aki na raba muku kuma wallahi na Kuma Ganin Wata mu'amula ta shiga tsakanin ku ni kadai nasan irin. Hukuncin da zan yanke muku ke Kuma khairat bakin get ma na samu labarin kin lek'a hmmm kinsan sauran.




"Salati Umma tayi tace "shikenan Shima an raba ni dashi To wallahi baka isaba baka isa ka rabata da Yar uwata ba ,tunda kai baka da kirki bakada mutunci, shege Mai irin halin ubanshi da mugun Hali to ya tsaya iya kanka Amma baka Isa ka hana sauran y'ay'a na zumunci da Yan uwansu ba tunda kai bazakayi zumunci dasuba tofa baka Isa ka hana sauran suyi da Yan uwansu ba Karyarka shege salamamme waccen y',ar iskar tsinanniyar juyar mayyar ta cinye Maka kurwa kaida salammamn ubanka yanda ta gama da ubanka shine kaima yanzu ta had'a dakai.




sannan ta fàshe da kuka tace "Allah ya isa tsakani na.dake Amina kin rabani da mijina da d'ana jaraba kawai Umma take Inda tashiga ba tanan take fitaba NAJIB ko ranshi yayi matuk'ar b'aci Yana son gyarawa kannanshi tarbiya umma tana daure musu gindi ita kawai kishi ya rufe Mata Ido komai saita daura wa aunty Amarya itada ba ruwanta ranshi a matuk'ar bace kamar zai tashi sama ya nufi part d'inshi zuciyarshi na mashi radad'in sauyawar halin Nan na Mahaifiyar shi Kuma yasan Babu Mai zuga Umma irin Aunty asiya (Maman sa'datu) Babban takaicinshi yanda aunty asiya ke juya Umma itace kanwarta Amma sai abunda tace Mata Kuma yasan ba son tsakani da Allah sukewa Umma ba ta ciki na ciki gashi Umma tak'i ta fahimta zurmiyata kawai suke tak'i ta fahimta Hakan yasa ya tsani aunty asiya da diyanta saboda juya mai da hankalin uwa da sukayi.





Nan Umma da SA adatu dukda sa adatu ta tsorata Dan tasan halin Yaya NAJIB ya Kama mutum Jibgashi yake kamar Dabba gashi tasan baida wasa haka yasa duk ta tsorata Umma ce tace "kyaleshi Bai Isa ya raba ki da yar uwarkiba sannan tace taimaka mata Ki gaggasa Mata jikinta zanje nadawo kuka kawai khairat take Dan ta jibgu ba kad'an ba Umma ko fuuu da d'auki makullin mota Kai tsaye gidan Asiya ta nufa.





Tana kuka tace "Asiya kina gani Shima NAJIB din ta raba ni dashi Nan tana kuka ta kwashe komai ta fadawa kanwar tata.




"to ai laifin kine aunty Jidda nace Miki ga inda zamuje a fitar Miki da wannan annobar Amma kin'iki to ai ga abunda nake fad'a Maki Nan kinaji kina gani Suma sauran khairat da Khadijar zata mallake mikisu"Gaskiya asiya yanda kikeso din bazanyu ba ko bakinciki zai kasheni bazan sabawa mahallicinna ba Kede kawai ki kawo Wata shawarar ni wallahi fena ma nakeson karb'owa tsorona kawai Kar Alhaji ya samu labari Dan wancen Karin Kinga irin wulak'anci da yamun".



Tsaki asiya taja a Zuciyar ta tanajin haushin yanda har yanzu Umma tak'i amincewa da zuwa wajen malamin ji take kamar ta mangareta Dan haushi saboda tana ruguza Mata Shirin da take ''to tsaya ta k'wace gidan ita Bata Haihuwa ke ki Mata Haihuwa Nan asiya tayi ta zuga Umma akan ta amso Fena Shikuma NAJIB ta rabu dashi akwai tunanin datake nashi Mai saukine Saida Asiya ta zuzzuga Umma sannan Umma tabaro gidan da niyyar kome zai faru ya faru Amma saita amso Fena Kuma tasan matakin da zata d'auka akan NAJIB.




*INDIA*🇮🇳
*NEW DELHI*



Najma ce kwance ta d'ora kanta Kan cinyar aunty Nafisa tana gyara Mata gashinta Amira.kuma tana kitchen tana girki Dan Aunty Nafisa yau ta tashi batajin dad'i ABIY ne ya shigo "sannu da zuwa my ABIY" yawwa *NAJMAT ABIY* D'ina sannan aunty Nafisa tace "sannu da zuwa Dear"yawwa Momyn Najma ya jikin dasauki tafad'a "ko zamuje asibiti dai""Murmushi tayi tace ". a a a dear dasauki fa"to Allah Kara sauki Sweetheart"ameeen inji Aunty Nafisa.




"ABIY ne yace wa Najma Albishirinki daughter"goro Amira tafara tana fitowa Dariya ABIY yayi yace "yawwa daughter kezan farawa Albishirin ma Cikin shagwab'a Najma tace "ABIY nid'infa "Amira ce tace "yawwa "ABIY ni Zaka fara bawa"to shikenan bari nabaku a tare ya fad'a Yana mik'a musu admissions.

Suna dagawa sukaga admissions ne ihu suka buga a tare da da rungume juna da daka wani uban tsalle A tare ganin sunan makarantar da ABIY zaikaisu bakinsu game sukace *GOLGOTIAS UNIVERSITY GREATER NOIDA* Ba k'aramun surprised d'insu ABIY yayi ba Basu taba tunanin zai sama musu admissions a wannan katafariyar makarantar Mai mugun tsada wadda ta d'iya shuwagabannin k'asashshece rungume ABIY sukayi Tare da fara sambada Mai albarka.




Duk sun rude Dan murna Aunty Nafisa dariya kawai take musu tace,"Gaskiya yau sai an had'a walima a gidannan"aunty ai dole yau ayi walima agidannan inji Najma Tafada tare da da Kara rungume ABIY tace I Love you so much my I ABIY I love you more my ABIY Allah Saka ka a ALJANNA Allah Kara Maka ARZIK'I Ameeen daughtern ABIY ya fada Yana Shafa kanta ranar haka suka yini cikin farinciki Dan Najma a iya rayuwarta ita da Amira Basu taba shiga farinciki irin na yau ba........✍🏻






*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*








*_Miss Hajo ce_* 🤙🏿
[10/2, 1:37 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
____________________________
*PAGE 17 & 18*
____________________________


*NIGERIA*🇳🇬
*KADUNA*

Washegari kamar yanda Umma ta Innata amso fena haka taje b'angaren Aunty Amarya ba ko Sallama ta banka k'ofar dakin cike da. Masifa da bala'i tace "Ina kike Yar gidan matsiyata "fitowa tayi daga bedroom d'inta tare da yin fara a tace "Aunty lafiya".



Tsaki taja cike da bala I da masifa Tace "lafiya ta Isa ta kawoni wajenki Amina, Y'ata nazo amsa tunda ba uban wani yayimun nak'udar haihuwarta ba ,"Kasancewar Amina ba mace ce Mai son fitana ba kawai cewa tayi "Amma saiki bari Wanda ya bani ita yaZo ya amsheta da kanshi shiyake da alhakin Amsar Fena ba ke ba tunda shiya bani ita da hannunshi ba keba",




"Kutumar ubannan Amina harkin samu bakin da Zaki fad'i mun magana to wallahi bari kiji yau Babu wani mutunci a tattare Dani wallahi gwara tun Muna mu biyu ki fitomun da y'ata tunda bake kikamun nak'udar haihuwarta ba ko ke kika haifamun ita kujimun karfin hali''Umma tafad'a tana huci.




"Aunty Amarya da Abun ya kâita bango daki ta shiga ta tattarowa Umma kayan Fena tana kuka saboda ba k'aramun Shak'uwa sukayi da Fena ba Tana son yarinyar Amma dole ta hak'ura da ita kodan Tijarar uwarta Saida ta gama tattara Mata kayan ta sannan ta sungumeta a kan bed tana ma bacci lokacin A palour ta tarar da Umma rik'e da k'ugu sai jijjiga take Kayan ta mik'a mata tare da Fena tace "ga y'artaki Ina fatan d'aga ita daga ita Babu Kuma wani abun ".



Tsaki taja tare da wartar Fena tace "idan fitsari banzane kaza tayi mugani Mana "fuuu tayi waje da yarta Fena ko sai kuka take Dan ita batason bin Umma tafison zama wajen auntynta Suna fita Nan ta durk'ushe gurin tare da sakin marayan kuka Mai tab'a zuciya.





Sanye yake cikin lapcoat ba k'aramun kyau sukayi mashi ba zaune yake a office d'inshi Yana Tunanin yanda zai bullowa lamarin khairat dangane da mu'amular su da SA adatu Dan idan yayi sake Yana hango babbar marsala Habib ne yashigo saida ya tab'a shi sannan ya dawo cikin hayyacinshi "b'ata Rai yayi yace "zaka fara ko"dariya Habib yayi yace "waini abokina kwana biyu sai tunane tunane kake ko ka fad'a soyayya ne" tsaki najib yaja yace"Matsalata dakai kenan sa Ido wallahi , kana ganin har akwai macen da ta Isa na sota a fad'in duniyar Nan Babu ita wallahi wannan shirman soyayyar sai ku "yafad'a Yana Jan tsaki.




Dariya Habib yay yace "Hmmmmm haka kake fad'a kullun harna k'agara naga lokacin dazaka fad'a soyayya irinku masu cika bakin Nan Kune.masuyiwa Mata kuka"Duk inda k'uluwa take najib ya kulu Jin abinda Habib yafad'a yanda yakejin da kanshi har akwai mace data Isa a fad'in duniyar Nan ya furtawa kalmar Yana sonta Jin haushin maganganun abokin nashi ya sashi tashi dan ya Bata Mai Rai yace "yallab'ai ni zan wuce saika barmun office ''yafada Yana kichin-kichin da fuska".




Dariya Habib yayi ganin yanda ya daure fuska lokaci guda sannan yace "yau Kuma ni kake.kora najib"tsaki yaja sannan Tafita tare da tilla Mai makullin Office din yace idan kagama shirman naka saika rufe mun sannan ya fice dariya Habib yayi Yana Jinjina Hali irin na najib.




Kai tsaye najib gida ya nufa
Kai tsaye b'angaren Umma ya nufa a palour ya tarar da ita sai sa adatu gefenta sai khairat na gefe tana latsa waya suna ganinshi gaban su yafadi musamman Khairat Dan yanzu ta Kara tsorata da Yayan nata .




Bayan ta gaishe da Umma ta amsa mashi cikin sakin fuska Nan khairat da Sa'adatu suka gaishesu ko Kallonsu baiyiba saima.latsa wayarshi da yake.



Khairat ce ta tsorata ta maza ta tashi har tafara hawa stairs yace "dawo ki zauna"Har lokacin Bai d'ago kanshiba kamar bashi yayi maganar ba.



Sim sim ta dawo ta zauna "Saida tayi minti biyar da zama sannan Yad'ago fuskarshi Babu alamun wasa yacw " Ina fatan kina sane da dawowar Abba ranar Friday"Daram gabanta ya fad'i tace "a a Yaya"to ai yanzu kinsani Kuma ki shirya da Shirin zan sanar dashi duk rashin tarbiyarki da lalacewar da kike Neman Yi Kuma kishirya na Baki sati biyu daga Nan zuwa sati biyu ki fito da mijin aure idan ba haka ba zan aura Miki Koma wanene ko Mai gadi ta kama shizan aura Miki *Yana gama fad'in haka ya ta tashi ya fice a palour.





Yana fita kuka khairat ta fàshe dashi wiwi tare da rungume Umma tace.
" nashiga ukku Umma Dan Allah ki hanashi Umma wallahi ni Babu abunda nake na banza wallahi Umma banason aure Dan Allah kibashi hak'uri yafasa Sambatu kawai take Umma tana lallashinta tace "insha Allahu Babu abunda zaimiki karki damu "sa adatu ce ta taso tare da dafa ta tace "sorry sis insha Allahu da wasa yake"bangajeta tayi ta karfi tace "da Allah ni sakarni duk ba ke kika jamun ba ke gakinan hankalinki kwance ni kin barni Da jaraba "Tsaki Sa'adatu taja a Zuciyar ta tace kedai kika sani banxa sannan ta cewa Umma zataje gaishe da mamanta "kigaishemun da ita Kuma kice mata gobe Ina son ganinta Dan Allah "to sa adatu tafad'a sannan tabar gidan Kai tsaye gidansu dake rigasa ta nufa madaidaicin gidane Mai Dan kyau ba laifi Babu get sai k'ofa da Sallama ta shiga .




Babanta ta iske Yana wanke wanke mamanta Kuma tana zaune tana Shan kankana B'ata Rai tayi tace "wai mama har yaushe xaikibar baba ya huta ne yanzu fisabilillah abokananmu suka shigo ai abun kunya ne.wlh.



Sannan ta juya wajen babanta tace baba bar wanken_wanken Nan tazo ta k'arasa Yana karkarwa yace "A a a sa'adatuna ba ita ta Sanya niba nice naga ta gaji na tayata Ai Sunna ce sa 'adena ki bari ta huta ta gaji,''duk Yana karkarwa yake fadar maganar Nan "Girgiza kai kawai Sa'adatu tayi Nan mamanta fuuu taja hannunta sukayi d'aki.




"B'ata Rai sa'adatu tayi tana fuskantar maman tata tace "Mama yanzu fisabilillah haka zakiyi ta juya baba kamar wani d'anki"bansan iskanci Sa'adatu ni sa'arkice wai duk maganar datazo bakinki ki fad'a mun bansan fitsara inbanda na gama da uban naki da kinaji kina gani zakiji ana ayyiri,an yiwa uwarki kishiya,shine hankalinki zaikwanta ko "asiya ta fad'a ajiyar zuciya Sa'adatu ta sauke tace "shikenan mama abar maganar "dadai yafi Cewar Asiya.



"daman mama magana akan Yaya najib ce ta kawoni, mama kince kinsan yanda zakiyi ya aure ni har ya so ni, Amma kin kasa komai, Kuma kinsan duk duniya Babu Wanda nake so sama dashi please mama Dan Allah kiyi abun Yi wlh kullun tsanata k'ara ninkuwa take a cikin zuciyarshi nikuma kullun soyayyarshi k'ara ruruwa take a cikin zuciya" ta Ida da ida fad'a tana kama.hannun Maman tata.





"Haba sa'ade na karki damu aikinsan komai a hankali ake.binshi kisa a ranki kin auri najib kin gama nan da d'an wani lokaci"Sanyi Sa'adatu taji a zuciyarta Dan tasan Mamanta tafad'a magana saita cikata ko ta halin k'ak'a Hakan yasanyata jin sanyi a zuciyarta.



Sa'adatu ce tace "yawwa mama na manta ban fada maki ba kince idan Abba zaizo na fad'a Miki to jibi Friday zaizo" sannan ta Bata Rai tace "Mama Kuma Wai Yaya najib yace Khairat zaiyiwa aure please mama kisa Umma ta hana kinsan Ina bak'incikin khairat tayi aure batare da tayi cikin shege ba Umma ta goya"Dariya asiya ta kece da ita ta mugunta tare da shewa tace "shegiya kinyo halin uwarki Baki d'auka a k'as ba karki damu sa'adane na duk zansan abunyi Bada jimawa ba "dariya Sa'adatu tayi tace ''sai mama "Asiya ce ta d'auko Mata wasu layu da magunguna tace "tasan yanda zatayi ta tutsa layun k'ark'ashin gadon.umma duk yanda zatayi tayi wannan Aikin tofa tayi sannan tabata wani magani tace ta dinga barbad'awa Umma a shayi kullun Harya k'are"Saida dai suka gama k'ulle_k'ullensu sannan Sa'adatu ta Koma gidan Da niyyar aiwatar da aikin da mamanta ta sanyata.




*INDIA*🇮🇳
*NEW DELHI*

Najma ita da Amira shirye shiryen fara zuwa school kawai suke duk sun shiga busy kullun suna shopping sayayya Dan abiy ya D'aure musu gindi A T M ma ya Basu su saya abunda sukeso sukam mutanen namu kunsan ba wasa Aiko jibgo kaya kawai suke kamar ba gobe Dan sund'au Alk'awarin harsu gama school din bazasu maimaita kayaba.



Aiko kaya kawai suke jibgowa yawaicinsu duk manya manyan dogayen riguna ne sai top sai English wears had'addu na gayu ba mtsatsuba Wanda zasu iya yawo ma dasu hankali kwance Abba har fad'a yakewa Abiy akan ya sake musu Kud'i da yawa"shidai Abiy Saidai yayi Murmushi Dan indai akan farincikin Najma ne zai iya Sadaukar ma da dukiyarshi gabak'i d'aya bare wannan d'an Abun danshi d'an Abu ma ya d'aukeshi.





Yauma kamar kullun sundawo daga shopping Amera na driving d'insu Najma sai sauke ajiyar zuciya take a cewarta ta gaji har suka isa gida bayan sunyi parking a had'ad'd'en parking space din dake gidan Abiy Kai tsaye parlour suka nufa bayan sunsa ma'aikatan gidan su kwaso musu kayansu su shigo musu dashi.





Tun a palour suke jiyo kakarin aman Aunty nafisa ta gudu suka nufi toilet din da suke jiyowa Nan suka iske Aunty Nafisa Duk ta galabaita iya rud'ewa Najma ta rude Dan hada kuka Saida Aunty nafisata lallashe tace dasauki sannan ta samu taji dan sanyi.




Saida suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan Najma ta maza takira ABIY cikin k'ank'anin lokaci Abiy ya iso Kai tsaye asibitin dake Estate din suka nufa gwajin farko ya tabbatar da Aunty Nafisa nadauke da juna biyu.



zo kuga murna wajen Najma kamar ta zubda ruwa a kasa Tasha Aunty Nafisa ma tayi farincikin Samun cikin nata tsawon shekaru takwas da aure ta godewa Allah sosai Abiy ma yayi farinciki sosai Najma ko hada rawa Tundaga ranar da aka Ce aunty Nafisa nada ciki Najma ta d'auki son duniya ta d'orawa cikin ga wani tattalin Aunty Nafisa da take ko kuda Bata barin ya tab'a ta .



Abun har mamaki yake bawa mutane yauma kamar kullun bayan sati biyu aunty Nafisa taji sauki sosai Ganin Najma duk ta hanata aiki Aiko tana ganin sun fita shopping Dan saura kwana biyu su fara attending lectures,




Aiko tana ganin fitarsu tayi Maza ta Afka kitchen hada sauri ABIY har dariya yake Mata tace "aikasan Babyn tawace y'ar rigima gwara na maza nayi sauri nayi kafin su dawo"dariya ABIY yayi yace Aiko kiyi sauri karta ritsaki Dan Babu ruwana".





Aiko su Najma Basu jima ba suka dawo tana dawowa taga Abiy a palour yana ganinta yayi Dariya"najmace tace. Abiy Ina Aunty''kitchen ya Nuna Mata wara idanu tayi tace "What ABIY kitchen fa Bana hana ta aiki ba ohh shine Dan mun fita tashiga kenan Daman haka take Mani idan munfita kenan Aiko zan dinga kunnan ctv camera".


Abiy da Amira me zasuyi inbanda Dariya Ummy ma da shigowar ta kenan taga yanda Najma ke iyayi dariya tayi b'ata Rai tayi tayi hanyar kitchen din zama Ummy tayi tana dariya tace ''bari muyi kallon game din uwa da y'a Dan tazo K'ara duba lafiyar k'anwar ta,ta''sai sannan Abiy ya lura da ita gaisheta yayi har kasa ta amsa cikin fara a.





Najma na shiga kitchen amshe Kayan aikin tayi tana Bata Rai "tace "Daman Aunty kenan wayau kikemun idan natafi bayan na hanaki Komai to daga yau bazaki sake mun wayau ba Sannan ta kashe gas d'in tace tunda bakison kuku na Aikin shikenan daga yau ba a Kara shiga kitchen order za a dingayi.



"sorry my daughter baxan sake ba kinji yaudinma naji saukine shysa"haka tayi ta lallashinta tun a kitchen har suka fito suna fitowa Najma ta kulle kitchen din ta zare key d'in mamaki duk yagama.kama Aunty Nafisa tanaso tayi dariya tana tsoro lallashi kawai take har suka fito.




Suna fitowa Aunty Nafisa tacewa Abiy"Abu Najma Dan Allah ka tayani Bata hak'uri tafa rufe kitchen din"dariya ABIY yayi yace ba ruwana kunfi kusa "Dariya Ummy kawai take Najma ko murtukewa tayi tace ,"Abiy daga yau baza a sake girki a gidannan ba sai Aunty haifamun babyna Idan tana shiga kitchen zafin zaidinga Shafanmu k'ani Kuma ma bak'i zaiyi Daga yau order za adinga Yi .


"dariya Ummy tayi tace "su Najma manya daga shiga kitchen sai baby yayi bak'i"Bata Rai tayi cikin shagwab'a tace "Ai Ummy na hanata tak'ijin magana ta shiysa"mezasuyi inbanda Dariya Dan har Aunty Nafisa dariyar take Abiy ko tausaya Najma yayi a zuciyarshi yace ,"Allah sarki my Najma ke Baki Samu kwantar wannan gatan daga mahaifiyaba Amma kina bawa k'anin dako duniya baizoba A zuciyarshi yace "har abada Babu y'ar da zan Haifa namata kwatankwacin soyayyar danake Miki my najma.ranar dai haka aka yini ana dramar aunty Nafisa da Najma yau ta kama Monday su Najma zasu fara attending lectures a School....✍🏿





*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*




*GOD WE REPENT* 🤲🏼







*_Mhiss Hajo ce_*🤙🏿
[10/5, 9:47 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

*Shafin Nan sadaukarwa ne GAREKI Maman nusaiba my momcy kiyi yanda kikeso dashi my lovely mom k'aunarki a jini take Ki huta kiyi shekaru irin na dabinon*😝
________________________
*PAGE 19 & 20*
________________________


Tun Asuba da suka tashi Basu Koma ba suka fara shiri Dan 7 am lectures din bayan sunyi wanka Najma ce zaune gaban mirror Tana tsara kwalliya Kasancewar ita simple make up take Aiko Nan tafara tsarawa Had'addiyar light gira tayi sai had'addiyar hodar datayiwa farar lallausar fatar ta kyau ta shafa sai Dan light jambaki dabai fitowa sosai ta goga wa iya zubilllahi shine abunda na ambata ba k'aramun kyau tayiba ita kanta Saida ta Yaba kanta tasan tayi kyau.




Wata bak'ar Doguwar riga (Abaya) tasanya Mai shegen kyau jikinta duk tsararrun

Please Login or Register in order to submit comment