Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mallakeshe ta gama dashi sai abunda tace Mai Dan Tama rabashi da danginshi tunda Allah yasa aka maidoshi kaduna da aiki tsawon shekaru goma Sha hudu Amma baitaba waiwayen iyayenshiba Dan Yama manta dasu ita kuwa Hakan yamata dad'i saboda ta dawo mahaifarta.



Sa'adatu ce babbar diyarsu Sa'adatu tun tana secondry ta lalace Dan shekararsu ta karshe akayi Mata ciki gudun asirinsu karya Tonu Tadaina zuwa makaranta inda Dak'yal suka samu suka subar da cikin daga Nan Bata Koma makaranta ba Dan ko jarabawa batayi ba nanko ta cigaba da Yawon bin mazan ta da Yan mata Dan Sa'adatu ba iya maza ta tsaya harta Mata suna lesbian dasu kwararriyar Yar iskace.



Tunda ta tashi take mugun son Yaya NAJIB b'angaren shiko Babu wacce ya tsana sama da ita Irin son da take Maine yasanyata komawa gidansu da zama duk Dan taja hankalinshi amma a banza Dan ko kallo Bata ishe shiba hakan ko ba k'aramun bakanta Mata Rai yake ba haka dai take har hak'uri har lokacin Da burinta zai cika na auranshi.


Kasancewar khairat age mate d'inta ce Hakan yasa tunda ta dawo suka kulla kawance duk yanda Sa'adatu zatayi taja Ra'ayin Khairat tayi Amma abun ya gagara tana son Khairat ne itama ta lalace kamar yanda ta lalace Amma ba yanda batayiba Khairat tak'i lalacewa taso Tasanyata a harkansu ta y'an lesbian Shima Hakan ya gagara Hakan yasa ta sauya dabara take yawo da ita wajajan kawayenta na banza Koda haka zaija ra'ayinta cikin ikon Allah Najib ya shiga lamarin inda ya tarwatsa Mata shirinta hakanko ba k'aramun ciwo yayi Mata ba yanda take murnar Khairat takusa zowa hannu Gashi ya ruguza Mata shirinta Hakan yasa ta aje makaman aikinta akan Khairat kafin tasan abunyi.


Asiya burinsu baiwuce suga Umma ta wulak'anta ba Ita da y'ay'anta Hakan yasa suke banka Mata mugun asiri tanaci yanda duk abunda suka Sanya ta bazata bijire musu ba gashi duk kud'in da asiya ke so da ta tambayi Umma tana sauri zata mik'a mata a tak'aice dai Asiya ita ke juya Umma kamar waina.a tanda Wanda itake Kara chusa Mata k'iyayyar Amina a cikin zuciyarta Wanda har yanzu tsawon shekaru bakwai da Auro.amina tunda Asiya taga.amina ranar da aka kawota cikin gidan Kasancewar basuyi ido hud'u ba Aiko tundaga ranar asiya Bata bari su had'u Dan kosun.hadu saitasan yanda tayi basuyi ido hud'u ba Wanda abun tun yanabawa Umma mamaki harta dawo Tadaina mamakin.



*DAWOWA LABARI*


Sanye yake Cikin k'ananun kaya yayi bala'in kyau sajen Nan nashi yasha gyara k'amshin turarenshine kawai ke tashi a palourn Dan Najib ma'abucin son turare ne Yana mugun son k',amshi Hakan yasa ko Dan yaushe baya rabuwa fa kamshi Duk inda kamshi yake Yana son wajen Hakan yasa yake yawan shiga bangaren Aunty amarya Dan itama ma,'abuciyar son k'amshin ce.



zaune yake a Palournshi dayaji kayan alatu Gyare Yake tsaf Kasancewar kullun sai masu aiki sun gyara k'aramun bowl ne hannunshi Yana Shan fruit salad d'in da aunty Amarya tahada Mai sai wani lumshe Ido yake Dan ba k'aramun dad'in shi yake jiba.




Fena ce ta shigo tafad'a Mai Umma na kiranshi yana gamawa tare suka tafi da Fena sai Surutu take zubamai suna shiga a palour suka tarar da Umma bayan ya gaishe ta da fara'arta ta amsa Najib kanshi yayi mamakin fara'ar Mahaifiyar tashi Dan rabon da Yaga tana fara'a har ya manta.




Sund'au minti biyar Sanna Umma ta juyo tace "Najib Ina son ka Bud'e kunnenka da kyau ka ji abunda zan Fad'a Maka ka saurareni da kunnen basira ba shawara zanbakaba umarni ne a matsayina na mahaifiyarka wacce tayi nak'udar haihuwarka ta kawoka duniya.




Tunda tafara maganar najib gabanshi yaji yafadi Amma kasancewar mutum.ne Wanda bai fiya nuna damuwarshi a fili ya sashi cewa "inajinki Umma Kuma insha Allahu zanbi umarninki matsayina na d'anki Mai biyayya a gareki".




Murmushi Umma tayi tace "ai daman nasan bazaka bani kunya ba najib Allah yayi Maka albarka,ameeen ya amsa sannan ta d'ora da cewa ,"Daman munyi shawara ce da y',ar uwata Najib nagaji da ganinka haka ba Mata Hakan. Yasa muka Yanke shawara da Asiya akan zamu had'aku Auren zumunci kaida,y',ar uwarka sa',adatu Kuma Alhmdllh munyi magana da sa',adatu ta amince "





Tunda Umma ta fara maganar Najib yayi sakato Yana kallon umman tashi Dan Jin maganganunta yake kamar a mafarki me Umma take nufi wai,sannan ya d'ago runannun idanun shi da sukayi ja tsabar b'acin Rai yace "Umma wai kina nufin zaku had'ani aure da Sa'adatu Koko Kunne na ne ya juyamun ba daidai ba ko mafarki nake .



"Umma ce tace ohh so kake na maimaita Maka ne ba mafarki kake ba gaskiya ne zamu had'aku Auren zumunci da SA'a Kuma ba fashi.



"innalillahi wa inna ilaihiraji un Umma kina nufin zaku had'ani aure da wacce ta gama lalacewa a titi waccce maza suka gama lalatata zaku ce na aura Umma ba sab"awa umarninki zanyi ba Ina Mai Baku hak'uri Amma wallahi bazan yarda da had'in Nan ba Sa'a ba class Dina bace ba itace zab'ina ba Bata da d',Aya daga cikin halayyar kalar matar da nake son aura Umma bazan Auri ballagaza marar kamun Kai ba haba Umma kamarni zan auri mace marar Aji marar ilimin boko Dana addini hasalima Kuma karuwar gida.....Bai k,'arasa maganar ba sakamakon saukar Marin da yaji Umma ce ta wankeshi da Mari sai huci take tace "najib ni kake.fadawa maganganun Nan harka Kai matsayin da zaka musamun har yaushe kayi girman dazaka fad'a mun magana A gaba na kake.cewa y'ar y'ar uwata karuwa agabana kake.fadawa y'ar zumu na.wannan maganganun to wallahi kaji ni dakyau komai zaka fad'a Saidai ka fad'a Amma aure ba fashi inko kaga an Fasa auran Nan tofa Saidai ka biyani nono na da kasha Dan akan maganar nan wallahi zan iya tsine maka Kabi duniya ".






Duk inda tashin hankali yake najib ya shigeshi Dan tunda yake tsawon rayuwarshi baitaba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin gashi Abba jiya yayi tafiya bare ya sanar dashi halin da ake ciki Dan shine zai iyabmagancemai matsalarnan cikin Sauk'i.



Baima tsaya Ida sauraran fad'an Umma ba ya tashi ranshi a matuk'ar b'ace kamar zai tashi sama yayi part d'inshi ji yake kamar ya kurma ihu koya rage rad'ad'in dayakeji a cikin zuciyarshi Dan wallahi Daya auri Sa'adatu gwara ya mutu Babu Mata ga Kuma tashin hankalin umma Wai yau itace har ta d'aga hannu ta mareshi Kuma har take ikirarin zata tsine Mai akan waccen Yar iskan yarinyar Tsanar sa'adatu ce ta K'ara nunkuwa a cikin zuciyarshi ita DA mahaifiyarta ranar haka ya kwana ko rintsawa baisamu yayi ba........✍🏿



*Dan girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*




*_Mhiss Hajo ce_* 🤙🏿
[10/17, 8:22 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
________________________________
*PAGE 25 & 26*
________________________________

Tundaga lokacin nan Najib yashiga damuwa DA tashin hankali ko wajen aiki ya daina zuwa Habib Shima ya Taya abokinnashi bak'in ciki Dan koshi bazai yarda DA had'in nan ba lallashin Najib kawai yake Yana bashi baki Najib ba irin Hak'urin DA bai Bata ba Amma tatubure karshe ma chatai ya K'ara Musa Mata akan auran nan Bata yafe mashi ba zokuga tashin hankalin wajen Najib ranar har wani zazzabi ya kamashi.





Yauma kamar kullun Habib ne ke gefenshi a palourn Shi Yana bashi baki ,"abokina Dan Allah ka cire damuwar abun nan cikin ranka ka Barwa Allah komai shizai magance maka"cewar Habib.




Murmushin takaici yayi yace "watau Habib bazaka gane bane kafi kowa sanin Hali na Kasan Sa'adatu ba tsara ta bace Kuma kafi kowa sanin Yanda na tsani k'azamar yarinyar nan Kuma shine yanzu za a lak'ama mun ita haba Ni.wallahi kainama ya gama kullewa".




Cike DA tausayin abokin nashi Habib yace "Abokina GA wata shawara Ina tsammanin zata taimaka.mana me zai Hana muje mu sanarwa da hajiya maganar nan Na tabbatar bazata Bada goyon bayan abun nan ba,.



"Cikin sauri Najib ya juyo yace "Kai amma.abokina kaid'in k'warone.wallahi Duk tunanina baizo nanba na tabbatar hajiya bazata yarda maganar nan ba sannan ya.mike.tare DA d'aukar key d'in.mota dariya Habib yayi yace "DA sauri sauri haka "Ehmana Ai kasan DA sammako ake.kamun kifi har suka Isa gidan hajiya Habib namai tsiya.




A palour suka Tarar DA hajiya na Sallah Zaunawa sukayi harsaida tagama suka gaisheta ta amsa cikin sakin fuska sannan ta tambayesu ya y,'an gida lafiya qalau suka amsa nan suka Shiga fira DA Habib Saboda mutumin hajiya ne daman.



Najib ne yayi gyaran murya yace "hajiya daman.magana ce ke.tafe damu Kokuma ince taimakonki.muke.nema nan hajiya tace inajinku nan suka kwashe abunda Ke faruwa suka fad'a Mata tare DA rok'onta Dan Allah karta yarda lamarin nan ya faru.


Salati hajiya tayi ta salamce tace Ni Amina na Shiga ukku me jidda take neman ta zama ne watau abun ya wuce iya kanta ya Fara biyo y'ay',a kenan to bazata sab'uba bazan tab,'a lamunta DA wannan shirmen banzan ba "Allah yayi muku Albarka DA Kuka sanar Dani halin DA AKE ciki tunda ita malalaciyar bankai matsayin dazata sanar Dani ba fad'a hajiya take inda take shiga Bata nan take fita ba.



"Bangaren Najib wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarshi koba komai yasan hajiya bazata yarda DA auran nan ba,



Hajiya ce tace "Maza Maza yanzunnan ka kiramun jidda Saida gaban Najib ya Fadi yasan halin umma Sarai zatace yazo ya had'ata da mahaifiyarta Saida hajiya Tak'ara mik'amai tace ''nace ka kiramun jidda sannan ya amsa ya kirawo umma ring ukku ta d'aga hajiya ta amsa.




Hajiya bama ta tsaya Amsa gaisuwarta ba tace "Ina son ganinki yanzu yanzunnan.kome.kike.ki saki.kizo Idan na.isa dake Dan yanzu lamarin naki yafi k'arfina Idan Kinga Dama kizo minti ashirin na baki "sannan ta katse Kiran.



Habib garin dai Maganace ta family d'insu ya Sanya Shi tafiya tare yimusu bankwana nan hajiya ta had'oshi DA tsintsiyar kamshi ya kaiwa hajiyarshi sannan ta gaishe su godiya yayi ya amsa Kashewa Najib ido yayi tare DA yimai Saida safe Yana b'oye dariyarshi ganin yanda ya rikice lokaci guda.




Cikin minti baiyi ashirin ba kasancewar ba nisa sosai tsakaninsu umma ta iso suna hada ido DA Najib gabanshi yayi mugun fad'uwa ganin irin kallon DA take Mai ya Sanya Shi tsurewa.



Har k'asa ta duk'ursa ta gaishe DA hajiya batare DA hajiya ta amsa ba tace "Ni bana buk'atar gaisuwarki jidda yaushe Har Nakai matsayin DA Zaki gaisheni a a ki Aje gaisuwar taki iya iyayennaki na gaskiya sannan ta d'ora DA cewa,Bari kiji jidda Duk irin abunda kike Ina sane k'yalekine kawai nake Dan karmuba Duniya dariya jidda baki d'aukeni a bakin.komai ba to Bari kiji wallahi kinji na rantse Duk shirmanku da kuke bantab'a Shiga ba KO?to wannan nashiga wallahi muddin baki janye maganar had'a Auren sa'adatu da Yaron nan ba ban yafe Maki hak'k'in haihuwarki DA nayi ba ke ni.wallahi dakike ganin wannan yaron yafiyemunke so dubu Nafi sonshi akanki yanda Aka sukukutaki shine Shima Zaki kaishi a lalatamai rayuwa tun yana k'uruciya to wallahi bazan yarda ba ke jidda fa Bari kiji wallahi Akan maganar auran nan zan iya tsine Miki ki Ida lalacewa na gaji DA bak'in cikin ki sannan ta fashe DA Kuka tace "kasheni kikeso kiyi bakincikinki kawai nake k'unsa Yaudai na gaji jidda keni karki k'arama zomun gida na hak'ura dake wallahi nabarwa su haule ke Dame zanji DA bak'incikin wad'annan mutanen DA suka gama chusamun Wanda Har yanzu bai warke ba zanji Koko DA bak'incikin ki zanji ,"Duk cikin kuka take maganar nan




Ba kan umma kad'ai ba hatta Najib Saida ya firgita d'ajin maganganun hajiya Dan yasan hajiya Idan tana fad'a Komai fad'a take Sai yaji haushin ma fad'a matan DA yayi.



innalillahi wa Inna ilahiraji un kawai yake ambata ummako k'wallace ta zubo Mata juyowa tayi Kallonta wajen Najib tace "watau Najib Ni kazo ka had'a DA mahaifiyata KO akanka kaja ta furtamun Kalmar DA KO a mafarki bantab'a tsammaninta daga wajentaba Najib babu abunda zance Maka Kuma ka kyauta ammafa ka sani daga yau babu ni babu kai na yafe ka a Jerin y'ay'a na.kaje ka Nemi.wata uwar Amma baniba kamar yanda kaja mahaifiyata tayimun baki Nima nayi Maka Babu Ni Babu kai Babu Ni Babu kai ''Umma Dan Girman Allah kiyi Hak'uri ki yafemun Wallahi Bada niyyar had'a ki DA hajiya nazoba Dan Allah kiyafemun umma bazanga daidai ba muddin kina fushi dani ya ida fad'a Yana kama k'afafuwanta idanuwanshi sunyi jajur.




Warce.kafarta umma tayi tare DA Jan Jakarta tayi haryar fita Binta Najib yayi kamar zaiyi Kuka Dan Shi Babu Wanda ya tab'a ganin hawayanshi saidai kukan zuci.



Tsinkayo muryar hajiya sukayi DA cewa "Kika Saka k'afa kika fita daga gidan batare da kinyafewa Yaron DA baiji baiganiba ban yafe maki hak'k'in haihuwarki DA nayiba Kuma saikin.biyani nono na DA kikasha yau d'innan....✍🏿





*Dan Girman Allah idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*







*_Mhiss Hajo ce_*🤙🏿
[10/17, 8:23 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
_____________________________
*PAGE 27 & 28*
_____________________________


A tare Najib Da umma suka juya suka Kalli Hajiya kallo d'aya zakayi musu dukansu kasan suna cikin tashin hankali Kuka umma ta fashe dashi tare DA rugawa ta rungumi hajiya cikin kuka tace "Dan Allah hajiya kiyi Hak'uri ki yafemun Idan ma Ina Maki laifi cikin Rashin Sanine kiyafemun Ko zanyi rayuwa Mai dad'i nasan fushin kine Ke jefani cikin masifa Kala Kala hajiya kiyafemun Dan Girman Allah.



Allah Sarki kunsan uwa DA D'a itama hajiya rungumeta tayi tace "Nayafe Maki Jidda Kidaina Kuka daman ba fushi nake dake ba kawai chanjawar halinkine lokaci guda yasa bama jituwa "


Goge hawayen ta umma tayi sannan tace "nagode hajiyata insha Allahu Zanyi iya kokarina wajen ganin nadaina B'ata Maki Rai Sannan ta Kalli Najib tace "Na yafe Maka Duniya DA lahira Allah yayi Maka Albarka a cikin Dukkan al'amuranka Maganar aure Kuma Na janye tunda hajiya ta nuna Bata so Allah zab'a abunda yafi alkhairi" wani sanyine ya ziyarci zuciyar Najib a zuciyarshi ya furta Alhamdulillahi sannan yaje ya rungume umma Sai godiya yake zuba Mata Itama tana Sanya Mai Albarka Hajiya taji dadi sosai Murmushi tayi a zuciyarta tace "Allah K'ara karkatomun DA hankalinki y'ata"ranar har magriba su umma Na gidan hajiya Dan rabonta DA gidan takai wata biyu Sai bayan Isha'i tukwana suka Baro gidan hajiya Najib yadauki umma kasancewar driver ya kawo ta Kuma ya koma.





Tunda suka Shiga Mota Najib yaga ta murtuke Takoma ummar ta DA "Hak'uri Najib yakarabawa umma "murmushin takaici tayi tace "aini Na riga Na yafe Maka ammafa ka sani Auren nan ba fashi Na janye ne kawai a gaban hajiya Dan taji dad'i sabida haka kasanma Duk yanda zakayi DA kanka zakaje kacewa hajiya kai kakeson auran "Najib Ji yayi kamar ya k'wala ihu Dan takaici zaiyi magana umma ta katseshi tace "banson Jin komai "ba Wanda ya sake magana harsuka Isa gida tukwana kowa yayi sharanshi.




"Oh my god umma yakuke so nayi ne Wai DA rayuwa ta fad'a Yana buga kanshi DA hannu "
Ranar baisamu yayi bacci ba ya durk'ufa tunanin mafitar DA Zai samawa kanshi Chan wata dabara ta zomai Yes ya fad'a yana k'usha DA hannu.





Bayan sati biyu Abbansu Najib ya dawo daga Lagos din dayaje wani babban metting Nasu Na y'an kasuwa alhmdllh wannan karin kam yasamu Shiga bangaren umma Wanda aunty Amarya ce ta tilastamai Akan saiya Shiga Saidai suna had'a ido ya karajin ya tsaneta dakyal dai ya iya Zama harma ya amsa Mata gaisheshin DA take daga gaisuwar nan ba maganar DA ta Kuma Shiga tsakaninsu Dan umma akwai zuciya ba kad'an ba.



Suna haka Najib ya Shigo Sannu DA zuwa yayiwa abban nashi tare DA Rungumeshi Nan suka Shiga firarraki Wanda Duk Akan aikin Najib ne Abba Ke tambayarshi.



Cikin hirar ne Najib yace "Abba daman inason nayi shawara dakai Ina son zuwa India zank'aro karatu Ina son zanyi masters ne Akan aikina Dan Na K'ara k'warewa.


"Dafashi Abba yayi yace wow son Ai Bama saika nemi shawara ba Na amince Maka son Wannan tunani ne Mai kyau Allah ubangiji ya bada sa'a ya Sanyawa karatun ka albarka "ameeen Abba najib yafad'a Yana kallon Umma yaji ko me zatace Harara Yaga ta gallamai sadda Kai yayi Umma ko a Zuciyarta cewa tayi kenan duk Dan gujewa auran Nan ne ya tarki tafiya to ai kaje ka dawo ka sameni duk inda zakaje.






Cikin Wata biyu Abba yagamawa najib Komai Kasancewar ta online sukayi Komai da registration Yanzu haka tafiyar ta rage saura kwana biyu Duk yaje yayi bankwana dasu Hajiya da su khairat Umma ma tun tana fushin harta sauko tasanya Mai albarka tare da fatan Nasara Akan karatun.




B'angaren Sa'adatu hauka ne kawai batayi ba Jin tafiyar da najib zaiyi mema amfanin zamanta a gidan Hakan yasa ta had'a kayanta ta Koma gidansu kota rage rad'ad'in da takeji Asiya ma bataji dad'in tafiyar da najib zaiyi ba Amma dai Koma meye tasan zaidawo kuma had'in Auren Nan ba fashi.



Yau takama tafiyar Najib India Wanda jirginsu cikin dare zai tashi k'arfe Ukkun dare Hakan yasa da dare yagama had'a kayanshi yasa komai a boot Wajen k'arfe takwas ya shiga b'angaren Aunty Amarya Dan Yi Mata bankwana.



Bai iske kowa a palour ba Hakan yasashi jira Baijimaba saigata ta fito daga kitchen "sannu da fitowa my mum"yafad'a Yana kallon ta "B'ata Rai tayi tace "haba son Ina Nan ina jimamin tafiyarka gaskiya inaga sainafi kowa yin kewa"Shima Bata Rai yayi yace "Nima Aunty zanyi missing naki irin sosai d'innan ji nakema kamar na Fasa tafiyar" a a son Ai Abu Mai mahimmanci ne zaka Allah ubangiji ya taimaka ya bada sa'ar abunda akaje nema "sun d'an jima suna hira Saida zai tafi tukwana ta d'aukomai Turarruka masu mugun k'amshi sannan alkqur'ani da wata had'ad'd'iyar zobanya ta gold sai shek'i take .

Tace "gashi son duk inda zakaje kada ka manta da karatun alkqur'ani Mai girma karkayi sake da addini kamar yanda na sanka mutumin kirki kacigaba da rik'e mutuncinka Karkayi sake da azhkar safe da yamma goge hawayen Daya zubo mata tayi sannan ta mik'a Mai had'ad'd'iyar zoben gold din sai d'aukar ido take Sanya Mai tayi a k'aramar yatsanshi.



kasa tsaida hawayenta tayi tana hawaye tace ,"Najib zoben Nan ka rik'eta da kyau zobe ce da na jima Ina tanadinta akan idan Allah ya azurtani da Samun Haihuwa zansanyawa y'ata ko d'ana Saidai Allah Bai nufa ba Allah baisa zanga k'wai na a duniya ba najib Likita ya tabbatarmun bazan tab,'a haihuwaba Hakan yasa na baka ita kaid'in inajinka ne tamkar d'an Dana Haifa najib nasan kaima ka d'aukeni a matsayin uwa Dan Allah najib ka cigaba da d'aukata a matsayin uwa Allah yayi Maka albarka yasanya albarka akan abunda zakaje nema".




Ba k'aramun tausayin auntyn. Tashi ba ya kamashi "Kama hannunta yayi yace "insha Allahu Aunty zan Rik,'e duk abunda kika fad'amun da mahimmanci nagode my cwt mom kidaina damuwa Aunty banason kinacewa Baki da y'ay'a mud'in fa ,mufa y'ay'ankine banajin dad'in hakan da kikecewa please Aunty kidaina Nid'in d'anki ne Kuma zanci gaba da zama d'anki har karshen rayuwa ,".




Abba Dayana jinsu Saida ya goge k'walla saboda ba k'aramun tausayin Amina yake ba yasan rashin Haihuwa Babu dad'i musamman ita da Aka tabbatarmusu da bazata tab'a haihuwaba Hakan yasa yake mugun tausayinta shiyasa yake kyautata Mata.



Daga b'angaren Aunty Amarya b'angaren Umma ya nufa Chanma ta Sanya Mai albarka Itama hada kukanta Dan ba k'aramun missing d'in Najib zatayiba sabida duk cikin y'a y'anta babu Wanda take yiwa son da takeyiwa NAJIB sannan ta bashi tsarabar dazai tafi Da ita.




K'arfe 2 pm Abba ya raka najib airport Saida yaga tashin jirginsu sannan ya Koma cike da kewar d'an nashi mafi soyuwa a wajenshi.




*INDIA*🇮🇳
*NEW DELHI*

Cikin sauri suka gama breakfast din kasancewar sun makara Goge bakinta tayi DA tissue paper cikin sauri ta tashi Sanye take cikin wasu had',ad'd'un English wears pink din riga me umbrella a gaban rigar an rubuta pretty Wandon jikinta black Sai head data d'aura Shima black ba make up fuskanta Amma sainaga ba make up ma tafi kyau natural beauty face d'intane matsakaicin pink d'in takalmine jikinta Wanda baida tsawo sosai takalmin kanshi abun kallo ne.



Bugu a baya Najmat takaiwa Amira datake cigaba DA breakfast d'inta tace"acici dalla ki tashi mutafi time Na tafiya kinsan yau Ina DA lectures D'in safe kin tsaya kina bautawa ciki mutum saici kamar kaza"chabd'i Ni kika cewa Kamar kaza Aiko wallahi saikin San wakika cewa haka kuma saina Rama tuluk'in DA kikamun" Amira tafad'a tana nufar Najmat DA niyyar kaimata duka.



A guje Najma tayi palour Bata tsaya Ko Ina ba Sai bayan Aunty nafisa ta b'oye biyota Amira tayi nan ta kankame Aunty nafisa tace "Sorry my Dusti Dan Allah kibiyoni bashi Nayarda ki Rama Please ba yanzu ba wallahi sanyi fasamun fata zakiyi haba my love amirata haba my sweety Na kiyi Hak'uri bazan sake ba"Dariya Amira tayi tace "Mutum Sai tsoro.amma ya iya Jan fad'a kinci sa'ar Munyi latti amma wlh DA saina Rama tafad'a tana rataye Jakarta ,gwalo Najma tayi wa Amira Aiko DA gudu Amira tayo.kanta DA karfi Najma ta kankame Aunty nafisa tace "wayyyo Aunty Dan Allah ki Bata Hak'uri nifa Bada ita nake ba"Aunty nafisa ce tace "kudai bakwa girma wallahi kullun Abu daya Saida suka gama shiriritarsu tukwana Najma ta d'auki key tare DA hug din Aunty nafisa DA little faruq DA yanzu harya Fara rarrafe tukwana suka tafi School a guje Najmat taja motar suka tafi Dan Najma gudu gareta a Mota Amira tun tana Mata fadan harta hak'ura.



Around 2pm Najma tafito daga lectures a cikin Mota ta Tarar DA Amira Dan tarigata gama lectures "sorry Dia kingaji DA jira lectures d'ince yau tayi zafi kinsan Sai yau nayi submitted din assignment d'innan tafad'a tana zagayawa ta Shiga driver seat ta zauna tare DA tada Mota suka d'auki hanya suna cikin tafiya Kira yashigo wayar Amira ganin Abba ne Mai Kiran yasanyata saurin d'agawa.



"Hello Abba "Dayan bangaren Abba yace "Amira tabawa Najma wayar amsa Najma tayi bayan ta gaishe DA Abba Yace Mata "Dan Allah daughter ku wuce Airport yanzu akwai d'an sister ta daya iso yanzu Yana airport kuje ku d'aukoshi daga nan saiku taho gida kubi a hankali"murmushi Najma tayi tace ,"to my Abba nan Abba yayi musu kwatancen yanda xasu Ganshi DA sunan airport d,,'in,




Kai tsaye *Indira Gandhi international airport* suka nufa Kamar yanda abba yasanar musu Suna Isa Najma taja tayi parking juyawa tayi ta Kalli Amira tace ''dusti jeki ki taho dashi nagaji wallahi "Tsaki Amira taja tace kedai kin Shiga ukku raguwa kawai "eh naji dai Najma tafad'a tana dariya.




Amira tana fita tsaye ta hango Shi Sanye yake cikin wasu Ash colour d'in k'ananan Kaya Wanda sukayi mugun karbarshi sumar gashin. Nan nashi kwance Lufluf sajenshi dayasha mugun gyara Kai tsaye wajenshi Amira ta nufa Dan tabbas tasan shine Dan tatab'a ganin Shi a hoto dukda Basu taba had'uwaba kasancewar zuwanta Nigeria d'aya Shima tun tana yarinya.



"Assalamu alaikum Amira tafad'a lokacin data Isa wajenshi d'ago kanshi yayi daga latsa wayar DA yake yace "wa'alaikumussalam"Ina yini anzo lafiya,mune Wanda Abba ya turo kud'aukeka' "Amira ta fad'a Duk a jere "Alhamdulillahi kawai yace

Please Login or Register in order to submit comment