Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsargu a cikin zuciyarta ganin irin kallon DA suke Mata tare DA nufota Tafara ja baya dariya suka kece DA ita tare DA nuna ta sukace "Ke har kina Da Hanyar tsarewa a wajen nan Ai Babu Mai iya Cetonki Y'ar budurwa gwarama ki bamu had'inkai ba Wani Abu zayi Miki ba Muna gamawa zamu barki kitafi.

"innalillahi wa Inna ilahiraji un Tafad'a tana runtse idonta tace auzubillahi Zata iya cewa a iya rayuwarta Bata tab'a Shiga tashin hankalin data tsinta kanta cikinshi ba Bude idanunta tayi DA suka ciko DA kwalla tace "don't touch me please karkumun komai Niba Y'ar iska bace Dan Allah "Dariya suka Kara kacewa Daya ya damki hannunta Yace "Haba y'an Mata Ina ganinki wayayya Yazakina mana maganar gidadawa Iya karfinta ta fusge hannunta tare DA cewa.



"Tunda Na Biku DA laluma kunkiya to Bari kuji wallahi Wani yayi gigin tab'ani saina kasheshi banzaye y'an iskanbanza Ta ida fad'a Ranta a matukar b'ace "Maimakon Suji haushi Dariya suka Kara kecewa D'aya ya damketa Zai d'auketa Aiko Iya karfinta ta fusge tare Da rugawa a guje Binta sukayi Suma a guje gudu kawai take batare DA tasan inda ta nufa ba Suma Binta suke kasancewar gudun mace Da Namiji ba Daya Ba Aiko batayi Nisa ba suka chafkota Ihu NAJMAT tasa Aiko nan suka rirriketa Daga ya sungumeta wutsil wutsiltu take tana ihu tana neman dauki suko dariya suke Suna cewa "keda kike DA karfin guduwa yanzunma Sai karfinki ya kwaceki.



Sai wajen 6 ya fito daga lectures Yana Shiga Mota zaitada motarshi yaji wayarshi Na ringing d'agawa yayi yaga murza ne Ke Kiran Bayan sun gaisa nan murza Ke fadamai Allah yayiwa mahaifinshi rasuwa kwana biyu Da suka wuce "Subhanallahi Najib yafad'a tare DA cewa ,"Shine baka sanar Daniba dawuri sannu brother Allah ubangiji yajikanshi yasa ya huta Gani nan zuwa yanzu nayi muku ta Aziya ".




Daga nan kai tsaye ma unguwar SU murza ya nufa Dan ya rik'e unguwar tun zuwanshi Na farko kasancewar hanyarshi ce ta komawa.




Yana zuwa yayi musu ta Aziya baijimaba ya fito a lokacin ana Kiran magriba murxa yabukaci DA yayi Sallah saiya wuce Hakan akayi Saida yayi Sallah tukwana sukayi bankwana Tafiya Yake cikin Mota bakajin komai Sai k'aran AC tuk'i yake cikin nutsuwa yayi Nisa nan yafara jiyo Kukan mace Da ihunta Kamar tana neman d'auki Nan yafara waige waige Chan ya hango wasu Maza biyu D'aya sungume Da wata budurwa dake wutsil wutsiltu DA neman d'auki Da ihu Harzai wuce Saboda Yana tsoron taimako a zamaninnan Amma yaji zuciyarshi ta kãsa koba komai Saboda Allah zaiyi Kuma ya lura yarinyar Na bukatar taimakonshi Parking yayi tare DA nufar wajensu cike DA b'acin Rai sunzo daidai zasu Shiga Wani gida DA ita ga alamun gidansune Yayi saurin Shan gabansu tare DA wanke d'aya Da Mari D'agowa yayi tare DA shak'arshi ganin Hakan yasa d'aya sakinta Tsabar rud'u Nan tafad'i wajen sumammiya Dan Tariga ta sadak'as Da rayuwa Najib baimabi ta kan yarinyar ba dasu ya Fara Aiko nan yahau Naushinsu ba k'akkautawa Duk ya lakata SU ganin Dai mutumin nan yafi k',arfinsu ya sasu rugawa gidansu tare Da Saka key .




Najib Ko Allah wadarai yayi DA halinsu tare Da Maida Kallonshi ga yarinyar dake kwance a sume Gashin kanta ya rufe Mata fuska Rasa yanda zaiyi DA ita yayi Gashi Babu halin Ya Barta a wajen hakan yasashi kawai d'auksrta tare DA nufa DA ita Mota front seat ya ajeta Tare Da d'auko ruwa Ya yayyafa Mata Firgit ta Tashi tare da sakin Kuka tace "Dan Allah karkumin.komai wallahi niba Yar iska bace Karku illatani Idanunta a rufe take maganar nan Dan Bata son ta d'aga su ma.



"mamaki yakama Najib Dan bazai tab'a manta muryar marar kunyar yarinyar nan ba Kamar yanda Shima yasa Mata Suna mamaki ya kamashi Meya kawo ta nan wajen a wannan lokacin Yana haka yaji ta Bude idanunta tare DA saukesu akanshi DA Shima ita yake kallo DA mamakinta tace "Najib "Karo Na farko Data tab'a Kiran sunanshi Kenan''Shima.kallonta yayi yace "why are you here ''Goge hawayenta tayi tace ''Mota tace ta lalace a hanya "shine wasu suka Biyoni ''ta Ida fad'a tana hawaye.



"Allah kiyaye gaba yafad'a tare DA cewa Ina motar taki "Kasancewar a tsorace Take sosai yasata cewa "Gatachan Dan Allah mu Barta ka maidani gida Dan Girman Allah kada ka barni a wajen nan nasan Idan ka tuno DA abinda nayi Maka a baya zaisa Ka barni SU b'atamun rayuwa Dan Allah ka taimakamun "ta ida fad'a tana sakin Kuka.



"Girgiza kai kawai Najib yayi Dan ya lura sha'anin yarinyar akwai tsantsar yarinta Dan son kwantar Mata DA hankali.ya sashi cewa ,''kinga kiyi shiru bazan barki anan wajenba Koda ace bansankiba zantaimakeki Allah kiyaye gaba Dai kidinga kiyayewa yafad'a Yana kokarin tada motarshi.




Mamaki yacika Najmat Jin kalamanshi Dan a zatonta Irin Cin fuskar DA tamai a baya bazai Bari ya taimake taba Sai yanzu take nadamar irin abunda tamai Ashe mutum Amfaninshi yawa gareshi bantab'a tunanin mutumin nan Zai taimakeni DA komai ba Ashe ba haka bane mutum Babbar daraja ce dashi Dan ba a wulakantashi ita Duk kunya ma ta cikata a sanyayae tace "Nagode bansan Da Wasu Kalamai zanyi amfani wajen gode Maka ba ka taimakeni a daidai lokacin DA nafi bukatar taimako ka tseratarmun DA mutuncina Dan Allah Kayi Hak'urin Duk irin abunda nayi Maka a baya kayafemun Sharrin shai'dan ne ".





"Karo Na farko Kenan DA mace tayi Abu ya burge Shi Yana son mutum Mai saurin Bada Hak'uri Akan laifin DA yayi batare da Girman kai ba burgewa na biyu kuma DA yanda tayi kokarin Kare mutunci ta Kenan akwai sauran kamulallun Mata a zamanin nan danshi Duk kud'in Goro yake musu yalura yarinyar Rashin kunyace kawai DA ita Amma tana Da tsananin kamun kai Da tarbiya Dan ya lura DA mu'amularta DA mutane Ko a makaranta DA yanda mutane Ke respected d'inta Saiyaji d'abi'unta sun burgeshi Batare Daya d'ago Ido ya kalleta ba yace "Kidainayimun godiya Allah zakiyiwa godiya danshi Yakawoni harna taimakeki maganar abunda yafaru a baya Kuma ya wuce ".




Harsuka Isa gida ba Mai magana Kowa DA tunanin DA yake Suna Isa Najib yafara fita sannan Najmat ta fita Haryayi gaba ta Ruga DA gudu tare DA Shan gabanshi ta Hada hannayenta biyu tace " don't tell Abba please if the shaulder of the knower will tell my Abiy" "Kallonta yayi yace "Why? Saboda me bakyason abin naki ya sani''


"Cike DA muryarta Da ta saba DA shagwab'a tace "Hankalinshi Zai Tashi Nikuma banason abunda Zai tada Mai hankali Kuma Zai iya cewa ya sauyamun school Koya hadani DA bodyguards nikuma banaso''.




"D'an wara idanu Najib yayi Yace "Sabida wannan abun zaisa yayi haka "Gyad'a kai tayi tace "Eh nasan Abiy Zai iyama fin haka""Gyad'a kai kawai yayi yace bamaiji "Murmushi tayi tace ,"nagode sannan ta wuce gida Shima Najib ya Shige room dinshi ta k'ofar Baya.



Koda suka tambayeta me ya tsaidata ta fad'a musu ne kawai Motartace ta samu matsala a hanya saita barota ta hayo napep.




DA misalin karfe Tara Na dare kwance take idanunta lumshe Kamar Mai bcci alhalin ba bacci take ba tunanin irin abubuwan datayiwa Najib tayi tayi dadinta Daya DA Allah yasa lokacin DA tadinga cimai fuska batayi DA yaren dazai gane ba hakan yasa taji sanyi a ranta.



Amirace ta Shigo tace "Dusti Wai yau meke damunki tunda kika dawo daga school Naga yanayinki ya chanza Ko Magana bakya sonmu "Batare DA ta Bude idanunta ba tace "nothing Dusti I just don't wan't to talk ne kawai"Hmmm yau Kuma kece bakison Magana kodai Wani abun yafaru ne kike b'oyemun "Gajiya Da maganganun Amira yasanyata juyawa tare DA cewa "good night".




Washe gari Najma Bayan tagama shirinta Na school DA misalin 9 am itada Amira a palour suka Tarar DA Najib Na gaisawa dasu Abba ga alamun Shima makaranta Zai wuce "good morning yaya Najmat tafad'a tana kallonshi " Amira mamaki Duk ya gama cikata Najmat ce yau ta gaishe DA Najib Shima kanshi yayi mamaki Cike DA nuna kulawa yace "morning kintashi lfy"Steady tafad'a ganin Zai fita gashi ta tsorata Dan bazata Kara bin Hanyar ita kad'ai ba yasa ta cewa "Dan Allah Ko zaka saukemu "Murmushi Jin Dadi ummy tayi ganin yanda Najma yau Ke respected din Najib "Okay follow me "Najib yafada tare DA ficewa parking space Suma binshi sukayi Amira Dai ta Zama Kamar gunki kallon Najma kawai take Dan taga yanda tayi mugun sauyawa Hakan yasata cewa "Dusti Wai Ko kinshirya DA Yaya Najib ne"Harararta Najmat tayi tace "Kede kinshiga ukku DA gulma "Dariya Amira tayi tace "eh naji nidai fad'amun ''badai zakijiba Najmat tafad'a tana Shiga back seat Sannan Amira ta Shiga front seat suka tafi .




Wajen dawowama Suna gama lectures suka nufi inda yayi parking Basu jimaba sukaga tahowarshi tare DA Wani course mate d'inshi Suna Hira harsuka iso Inda suke Suna Magana DA yaren Hindi Tsayawa Najma DA Amira sukayi kallon Najib dake ta Magana DA harshen Hindi saika rantse daman yarenshi ne kallon kallo Najma DA Amira suka shigayi kasa daurewa Najmat tayi Kenan Daman yanajin Duk abubuwan DA nake cemai ganin wancen Yatafi ya sata kallonshi tace "Daman kanajin Harshen Hindi ne Murmushinshi Mai tsada ya saki tare Da d'age Mata gira yace "Tun aashcharyachakit ho" (Kina mamaki ne) wara idanunta tayi tace "main ek pankti mein teen hoon Aur jitane shabdeein"(Na Shiga ukku Kenan Duk maganar Dana fad'a Maka kwanaki kanajina kayi shiru)


Dan shafa sajenshi yayi tare DA sakin wani rikitaccen Murmushi ya Dan sake D'age gira yace " Agar nabhee abhee Nahin to ham bhaasha bolate hain (Idan banjiki ba a lokacin yanzu Har zanji abunda kikace)...✍🏿



*Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*





*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[11/3, 11:30 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
_________________________________
*PAGE 41 & 42*
__________________________________

Najmat DA kunya tagama rufeta Kenan Duk yaji irin tijarar DA tamai Kenan sadda kanta tayi tace Dan.....katseta yayi DA cewa banason wata doguwar Magana Kushiga mu wuce D'agowa tayi tana Dan Marairaice fuska tace Amma yakamata Na Baka Hak'.....K'ara katseta yayi ta Hanyar cewa kin manta nace komai ya wuce "Batare Da ta Bari sun sake had'a Ido ba tayi sauri zata Shiga back seat Amira ta Rigata tana Mata dariya Harararta tayi tare DA karkada Mata yatsa sannan ta Shiga front seat Shima ya zagaya yashiga yajasu suka tafi.




Tunda suka d'au hanya ba Mai magana ganin yanda Najmat ta takura Tayi sanyi ya sanyashi Janta Da Hira yace "ya school din Fatan Kuna Maida hankali''murmushi tayi tare DA sadda kai tana Wasa DA zoben yatsarta cikin zazzak'ar muryarta Mai rikita Mai sauraro tace "Alhamdulillahi"Masha Allah kawai yace sannan yace Allah Bada SA ar jarabawar "Ameeen ''ta amsa Har lokacin kanta sadde Dan Wani mugun. Nauyinshi take Ji.





Suna Isa Najma Bata Bari sun Hada idoba tayi sauri ta fita Har tuntube taso tayi Dan sauri girgiza kai kawai Najib yayi.




A palour Amira ta sameta dariya Amira ta Hauyi ba kakkautawa tace "Ashe dusty kinsan Jin kunya Ji yanda kike Wani sassada kai Kamar ta kirki"sannan tace Amma fa bake ba dusty koni Saida Naji kunya "Tab'e baki Najmat tayi tace "Saida kika gamamun dariyar sannan tace hmmmmm kede Bari Wallahi Ji nayi Kamar in. Nutse Dan kunya Duk a takure nadawo "Amirace. Tace "kaico Ashe Yana jinki Gaskiya yanama DA Hak'uri kam Ina ganinshi Kamar Mai mugun Hali Ashe Yana DA saukin kai"hmmm Ai ya koya mana hankali Najmat tafada tana nufar dining Dan DA yunwa ta dawo.




Kasancewar yau weekend Kuma Basu Da exams yasanyasu Sai wajen 1 suka Tashi Daga bacci Bayan Sallar asuba Najmat ce ta Tashi Da Bakar yunwa tana Tashi ta fito daga ita Sai gajeruwar doguwar rigar bacci fitowa tayi Dan samawa kanta abunda zataci Bata Tarar DA Kowa ba a palour dining taje ta duba Babu Abinci Tana turo Baki ta Shiga kitchen Dan Har wani bibbiyu take Gani ba Bata lokaci ta Had'a ruwan tea Da wainar k'wai sannan ta fito ta zauna a dining tafara Ci Tana cikinci taga fitowar Najib Daga bedroom dinshi GA alamun Shima yunwar yakeji Sadda kai tayi Dan Har yanzu kunyar had'a Ido dashi take.




Kan Sopa ya zauna Yana d'an Danna waya Batare Daya Kalle taba yace "Akwai Abinci ne?itama d'agowa tayi tace "A a saidai in nahad'a Maka ruwan tea"Okay thnks "Yafad'a tana gamawa ta Had'a Mai ta mik'amai tazo wucewa yace ,"yadai Naga Kinyi shiru Ko baki DA lafiya"dan murmushi Tayi tace Bakomai kawai dai "kawai dai Me yafad'a Yana kurbar ruwan tea din data hadomai "Uhm Bafa komai tafad'a cikin Y'ar shagwab'a ,''gyada kai kawai yayi.





Tun Daga lokacin nan Shiri ya shiga tsakanin Najmat DA Najib sosai suke zaunawa suyi Hira sometimes DA yamma zasu zauna a Garden suna hirar rayuwa yauma kamar kullum zaune take a harabar gidan ita kad'ai tana tunanin mahaifiyarta Dan cikin kwanakin nan tana yawan mafarkinta Wai tana kuka tana Bude Mata hannayenta tazo gareta Amma Nisan dake tsakaninsu sun kasa had'uwa Lurar DA tayi Duk inda mahaifiyarta take lallai tana buk'atar ganin ta k'walla ce ta zubo Mata batare DA ta saniba.



Najib ne ya hangota Wajen yanufa Yajima tsaye Amma batasan DA zuwanshiba Sabida tayi Nisa DA lulawa duniyar tunanin Tab'i ya Mata shiya fargar DA ita ganinshi tsaye ya Hade Rai ya Sanyata K'ik'irar murmushi tace "ka fito Kenan"Harararta yayi yace "tunanin me kike tun dazu nake tsaye bakisan DA zuwa Na ba "Tunani Kuma "Tafad'a Tana nuna alamun bakomai"Zaunawa yayi kusa da ita tare DA cewa "Eh Tunani Na sameki kinayi"Dan son barin. Zancen ya sata cewa "Gobe fa su Abiy zasu dawo karkaga yanda nayi missing d'insu "D'an wara idanu yayi yace "Haba kice gobe Muna DA Manyan bak'i "Murmushi tayi tace "Sosai ma gobe zanga Abiy na ,Nasan Yana Chan Yana missing d'ina"Dan hararanta yayi yace "inye Y'ar Abiy Ai nasan ma ya manta dake ba Wani kewanki Da zaiyi,"Shagwab'a fuska tayi tace "uhm Allah kadaina cewa ya manta Dani Abiy bazai manta Daniba tafad'a tana turo baki''dariya yayi yace "Injiwa Ai zamu Gani goben Idan ya dawo "Didddira k'afa tafara cikin shagwab'a Kamar zatayi Kuka tace "Allah Ni kadainacewa haka inba haka ba zamu b,ata ''Sorrry *NAJMAT ABIY* d'inta Wasa nake Maki yaza ayi Abiy ya manta da Tauraruwarshi."yafad'a Yana d'an murmushi.



Lokaci guda ta saki murmushi Jin yakirata DA. Sunan datafi kauna tace "Waya fad'a Maka sunan Dana fiso *NAJMAT ABIY* d'an mak'ale kafada yayi yace "bazan fad'a ba "Uhm uhm Dan Allah fa nace Badan Halina ba " "hmmm lokacin Dakikayi ta borin bazan Hau Miki Mota ba Lokacin Naji Ankiraki DA sunan kin hak'ura"Dariya tayi tare DA rufe fuska tace "ohhh Na tuna ,"




Shiru yayi Itama daganan Bata sake magana ba Idonta ne ya kai Kan zoben hannunnshi k'ure zoben Tayi ta Kallo bako k'autawa Jin shiru yasanya Najib juyawa ya kalleta yaga zoben hannunnshi take kallo tayi 5 minutes tana kallo batare Da k'ak'ak'autawaba Hakan yasashi gyaran murya yace "Kar a cinyemun zobe fa"Sai sannan hankalinta yadawo tadanyi murmushi tare DA sadda kai tace "Zoben ce ta burgeni Dan Allah Ko zaka Bani Shan Miya"


Cikin zolaya yace "a a a bazan baki ita ba Ko kallanmunma Da kikayi batare DA Izini Na ba ya Isa "d'an shagwab'a fuska tayi tace "Dan Allah to ka sayarmun da ita" batare DA ya kalletaba yace "Ba ta sayar wa bace kintab'a Ganin ansayar DA kyautar DA akayi Maka kyautarma ta zobe Daga waje Mai mahimmanci "Uhm to waya Baka Ko Auntyn mu Tabaka "Tafad'a cike DA zallar k'uruciya "murmushi yayi yace "Auntynku Kuma wa Kenan" nufina girl friend d'inka Ko Wife d'inka ,"girgiza Mata kai yayi yace"A a a Dan yafara gajiya DA Surutunta".



"To waya Baka "tafad'a tana d'an Marairaice fuska "gajiya Da Surutunta ya sashi cewa "Mahaifiyata tace ta Bani ita dazan taho tace Nadinga kallonta Kamar itace gabana Kinga Bai kamata ta fita Daga hannu Naba Kamar Na sab'a Mata alkawari ne Kuma kinsan ba 'a Wasa Da kyautar iyaye koke Idan mamanki tamiki kyauta zakiba Wani ne ".



Tunda ya Fara maganar zuciyarta Ta Karaya Yana k'arasawa ta Gyad'a Mai kai alamun ta fahimta sannan tad'an sadda kanta sakamakon kukan dayaci k'arfinta ganin. Kamar DA gangam ya fad'a Mata maganganunan Gani take gorine yake Mata Tashi tayi tana Kuka tare DA rugawa tayi cikin. Gida Mamaki Duk yagama cika Najib to me akayi. Mata Na Kuka anan Hakan ya Sanya Shi Tashi tare DA Binta Koda ya Shiga palour Bai isketaba Amira ya Tarar.




Kallonta yayi yace "Najmat ta wuce nan "Kallonshi tayi tace "eh Yanzu ta wuce tana Kuka bansan me aka Mata ba Na bita Kuma ta Sanya key ,"Tsaki yaja tare DA Zama Kan sofa "Amirace tace Yaya Ko Wani yayi Mata Wani abun "Tsaki ya kumaja yace "Daga Muna Hira shine tahau Kuka ta rugo DA gudu" d'an Tunani Amira tayi tace ''to Daga Hira me zaisanyata kuka sannan ta cija yatsa alamun Tunani Kamar ta tuno.wani .Abu tace "To Ko cikin hirar kayi Mata zancen mahaifiyarka Ko tayi Maka zancen"d'agowa yayi yace "Tabbas anyi haka akwai damuwanei'?"


Amirace tace "Ayya dole tayi Kuka ,ba ayi Mata zancen uwa Saitaga Kamar Gori ne Ake Mata "DA mamaki Najib yace Gori Kuma ,?,to ita Ina mahaifiyar Tata .



Cike DA tausayin aminiyar Tata tace "Mamanta ta rasu tun wajen haihuwarta Amma Har yanzu Wai Bata yarda DA tarasu ba shiyasa "lokaci guda Najib yaji ta bashi tausayi Saboda Yana mugun tausayin maraya musamman Wanda ya rasa uwa Saiyaji ta bashi tausayi cike DA tausayawa yace "Allahsarki Allah yājikanta sannan yace Dan Allah jeki ki lallasheta ''murmushi Amira tayi tace "to "Sannan ta Tashi Shima yabar d'akin cike DA tausayin halin maraicin data tsinci kanta tun. K'uruciya Saiyaji baiji dadin maganar DA ya Mata ba.



Dakyal Amira ta samu Najmat ta Bude k'ofar dakyal ta samu ta lallasheta Har tayi shiru Amma a zuciyar Najma ta innata Babu ruwanta DA Najib tunda yayi Mata wannan cin fuskar Dan a tunaninta DA gangam yayi Mata.



Yau SU Abiy suka dawo sun samu tarba ta musamman Daga wajensu ummy Najmat Ko Dadi Kamar Sallah tana mak'ale DA Abiy tana.mai shagwab'a Yana biyemata "Tace Abiy Dina nayi.missing d'inka sosaifa ''shafa kanta yayi yace "Nima.nayi kewanki soosai daughtern Abiy Saida natafi Naji Daman Na Bari Kingama jarabawar mutafi tare Dan kullun DA tunanin Ko daughtern Abiy ya take nake "murmushin Jin dad'i tayi tace "Nima haka kullun tunanin ya Abiy Na yake Sannan tace "Me Abiy ya rokamun ne"murmushinsu Na manya yayi yace "Miji Na gari Na rok'ama *NAJMAT ABIY* D'inta sannan yace Har yanzu Dai kink'i kawomun sirikina ''yafada DA sigar zolaya.



Rufe fuska tayi tare DA sinne kai a kafadarshi "Dariya yayi yace ''yau Kuma Abiy akejin Kunya "Kara rufe fuska tayi tace "uhm uhm uhm Abiy Nifa yarinyace Har yanzu "Jaririyama kuwa Aunty nafisa tafad'a tana saukawo Daga Kan stairs"Dariya Najma tayi tace ''yawwa auntyna fad'a masa Dai"Hararta Aunty nafisa tayi tace ''Ai Maganace Na fad'a Maki Nimadai Nakagara Naga bikin daughter''Uhm uhm Aunty kema haka zakice Ko Ko tokuma daina tunanin wannan Dan Babu inda zani Na barku ."Aunty nafisa ce tace "Aiko saimu Gani kina Gama makaranta zan aurar dake "dariya Najmat tayi tace ,"to saimu Gani Ai knocking din DA akayi yakatse musu hirarsu NAJMAT ce ta Tashi taje ta Bude ''Najib ne tagani tsaye Sanye cikin farar suit Bata Rai tayi tare DA matsamai Shima batare Da ya bi ta kantaba ya wuce Daman Abiy yazoyiwa sannu DA zuwa Shima Saida Abba ya tilastamai Najmat Ko dakinta ta wuce Dan batason abunda Zai sake had'ata dashi tunda yayi Mata Gori .



NAJIB Bayan sun gaisa dasu Abiy yayi musu sannu Da zuwa suka Ansamai cikin sakin fuska DA Fara a "Abiy yace ya karatu Fatan ana Maida hankali"Kanshi. Sadde yace alhmdllh''To madalla Allah yataimaka "Ameen Najib yafada yace ,"Allah huta gajiya Saida safe yafad'a Yana Tashi nan Aunty nafisa ta tsaidashi ta d'aukomai tsarabar dabino DA zamzam godiya yayi Mata sannan yawuce .



Najmat wasan buya take DA Najib Dan batason abunda Zai had'ata dashi Daman Abba yasama musu driver yanzu shike kaisu school Ko taganshi a hanya zata sauya hanya yauma kamar Kullum gidansu Amira ta nufa Dan tarage zuwa ma Saboda karta had'u dashi yaumad'in Dan Kar Amira tayi fushi yasata Shiga tana Shiga ta iske bakowa a palourn Nan Mai aikinsu Ke shaida Mata Sunfita unguwa juyawa tayi DA niyyar komawa gida tunda basanan ta zo fitowa Najib nashirin shigowa Kadan ya Hana suyi Karo saurin matsawa tayi batare DA tamai Magana ba Alamun ya wuce shigowa yayi tare Da jingina jikin k'ofar ''Kallonshi tayi tace "Zan wuce "Kallonta Shima yayi Babu Wasa a fuskarshi. Kamar Dai tsohon Najib din dabaya dariya yace "Jeki zauna Magana nakeson muyi''sakamakon kwarjinin DA yayi. Mata yasata. Kasa. Musamai Samun guri tayi a one seater ta zauna Shima zaunawa yayi kusa DA kujerarta Saida yadauki kusan two minutes ba tare DA yayi Magana ba Najma haushi Duk ya cikata a zuciyarta tace jifa rainin hankali juyowa yayi tare DA kallonta yace .....✍🏿




*Dan Girman Allah Idan kun karanta kuyimun sharing fisabilillah*






*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[11/5, 5:13 PM] 🪴Mhixx Hajo ✍🏿: 🪴
🪴
🪴
*NAJMAT ABIY*
🪴
🪴
🪴
*Story and writing*
*By*
*Hajara L Sadeq*
( *Mhiss Hajo*🖤)


💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*SAK'ON GAISUWA DA JINJINA GAREKU MASOYAN ASALI NAJMAT ABIY FANS INA JIN DAD'IN COMMENT,D'INKU DA SHARHI INA GODIYA DA ADDUO'INKU GARENI INAYINKU OVER Y'AN WAJENA*😎

________________________________

*PAGE 43 & 44*
________________________________

I am sorry Akan maganar Dana fad'a Maki bansan mamanki ta rasu ba Kiyi Hak'uri kidinga Yi Mata addu'a Allah ya jikanta.



Najmat Ranta a b'ace tace "wayace. Maka mamana ta rasu ne kai ka kasheta Ne,Ni mamana Bata Mutu ba Kuma insha Allahu saina ganta "ta ida fad'a tana fashewa Da Kuka.




Tausayinta ne ya K'ara nunkuwa a cikin zuciyarshi Hakan yasashi cewa "To kiyi Hak'uri kibar Kukan nan indai kinason ganinta Zan kaiki wajenta "yafad'a Dan son kwantar Mata DA hankali.




Lokaci guda ta d'ago idanunta DA sukayi ja tace "DA gaske zaka kaini wajenta"D'aga Mata kai yayi yace "Sure "Goge hawayenta tayi tace "To tayaya Zaka kaini wajenta Bayan Nima bansan inda take ba "Ga mamakinshi ya kalleta yace "Kinsan inda danginta suke'' girgizamai kai tayi tace "Babu Kowa Nawa Dana Sani DA Abiy kad'ai Na Tashi bansan Kowa Nawaba tundaga Kan dangin uwa Da uba Kuma nasha tambayar Abiy yasanar Dani Amma yak,'i fad'amun Hasalima ranshi baci yake Kuma yace Karna k'aramai maganar.




Mamaki ne ya cika Najib Dan son Jin labarinta Dan ya lura Kamar akwai wani b'oyayyan al'amari cikin labarin yace "To ya fad'a Maki k'asarsu Da garinsu ma'ana inda aka haifeshi "Gyad'a mishi kai tayi tace "Eh Shi d'an Nigeria ne a Gombe state Amma Daga haka baik'ara Bani labarin komaiba Baifadamun garin Ko k'asar Da mamana take ba ".




Nauyayyan ajiyar zuciya Najib ya sauke tukwana yace "To ya akayi yace mahaifiyarki ta rasu Kuma"Cikin shahshek'ar Kuka tace "Wallahi mamana Bata rasu ba Saboda bazan manta ba

Please Login or Register in order to submit comment