Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun duniya na kwance Baffa yake fitar da yayansa mata qasashen waje suyi karatu, idan ma kuma kina karatun kika fitar da miji dukka ze miki auranki.

Nice ya ta Ashirin da bakwai a gidan mu, Ma’u kwalisa shine laqabin da akeyi mun a makaranta saboda yanda Allah yayi ni dason gayu abin ya hade mun da irin qirar halittar da nake da ita dan haka nake bawa gayu haqqinsa yanda ya kamata.

Tun muna SS1 na qudurce a raina nifa dana gama secondary aure zanyi duk kuwa da yanda nake da qoqari sosai a makaranta nidai kawai aure nake so abinda ze baku dariya shine ko saurayin bani dashi dan bana kulasu, ni a lokacin ma duk wanda yace yana sona tofa ya zama abokin gaba ta har tsokanata yan gidan mu sukeyi indai kana so muyi rigima dakai to ka nuna wani kace saurayi nane.

Ranar da muka fara haduwa da Bashir wata rana ce mun taso daga islamiyya da yamma, muna hanya wani da Ake kira Ibbah saurayine dan layin mu daya nace shi ala dole sona yake yi mun taho a hanya kawai ya tare mu.

Ibbah girman Ingila ne acan aka haife su dan basufi shekara biyar da dawowa Nigeria ba dan haka gaba daya dabi’unsa na turawa ne abinda yasa nake qara tsanarsa kenan muna tafe muna hirar mu se ganin sa kawai mukayi a gaban mu ya kalleni yana murmushi yace “Hey pretty yau na kamaki bazaki gudu ba, tsaki nayi masa na murguda baki kafin na kauce ina cewa

“Aikin banza mutum kamar maye yayi ta bin mutane, se kayi tayi ai dan wahala” nayi gaba abina se ji nayi caraf ya riqomun hannu banyi wata wata ba kuwa na kwashe shi da mari kafin na hau zazzaga masa tsiwa ina zaginsa.

Tahowar da Yaya Abubakar din gidan mu da Abokanan sa uku yasa na dakata ina hararar Ibbah dayayi mutuwar tsaye yana kallona, Yayan ne ya tambayi meya faru Alawiyya tayi caraf tace masa “Ma’uce ta Mari Ibbah saurayinta” tun kafin ta gama na juya kanta da masifa ina cewa

“Ta ina ya zama saurayina wallahi karki sake hadani dashi niba saurayina bane” kawai na saka kuka kawai se suka samun dariya dan yanda nayi abun seka rantse wani mugun abu aka jinginani dashi.

Daya daga cikin Abokan Yaya Abubakar wanda ban sanshi ba, cikin taushin murya yace mun “waya gaya miki mekyau tana yin kuka rabu dasu ba saurayin ki bane ki share hawayenki”.

Haka kawai naji ya burgeni, na saka hannuna na goge fuskata tsaf kuwa fuu nayi gaba na barsu suna ci gaba da yi mun dariyar ina jin Yaya Abubakar na bawa Ibban haquri kafin ya taso su Alawiyya a gaba suka biyo bayana.

“Ma’u danja Ma’u rigima daga ance mutum saurayinki kawai ki kama kuka ke wai baki san kin girma ba” Bala daya daga cikin Abokan nasu ya shiga taokana tun kafin ma na bude baki Yaya Aliyu da duk yafi sauran abokan su kirki ya tareshi da cewa

“Zaka fara ko Bala, Ma’u kyaleshi yi shigewar ki gida” seda n harari Bala na murguda masa baki kafin na shige dan sam bana son Balan nan saboda yana shan Taba nasha ganinsa yanayi ni ban ma san me yasa su Yaya suke kula shi ba.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa muna hira yanda muka saba nake bashi labarin abun da ya faru
“Wani sabon abokin Yaya Abubakar ne yace na dena kuka amma su da duk se dariya ma sukeyi mun” na fada cikin shagwabar da idan ina gaban Baffana jina nakeyi kamar wata yar jaririya zuba tabara nake son raina idan akayi sa’a Goggo na kusa ta make ni.

“Banda dai tsiwa irin ta Mamana ya zaki mari mutum kawai dan yace yana sonki, ki kiyaye kar a sake kuma gobe kuje har gida dasu Alawiyya ki bawa Ibrahim din haquri kinji ko” Baffan ya fada. Sena marairai ce nace “toh Baffa bazan kuma ba.

Washe Gari Alhamis kuwa bayan mun taso boko da yamma babu Islamiyya mukaje har gidan su Ibbah na bashi haquri, da yake yana da sauqin kai yace shi harya manta ma Maman sa se nan nan take dani wai yarinya me kyau da hausarta wata iri ta hado mana kayan dadi muka tafi muna gulmarta wai su a dole turawa.

Muna zuwa qofar gidan mu muka ci karo dasu Yaya Abubakar yau ma su na zaune, gaishe mukayi ina ta satar kallon na jiyan nan daya maida hankali yana danna waya so nake naga ko zeyi mun magana amma har muka shige gida be ko dago ya kalle mu ba.

Baki na tunzura nayi wucewata dakinmu, inajin su Alawa suna cewa nazo mu raba kayan da Maman au Ibbah ta bamu nace bana ci nayi kwanciyata ina jin haushin da ban san koma mene ne ba.

Da daddare Yaya Abu yace na dafa musu Indomie, ina gamawa na juye a flask na bawa Khadija ta kai musu ina zaune a palour Hajia Umma se gata wai naje inji Yayan yana kirana.

Suna zaune a tsakar gida daga gefen inda akayi kujeru na sumunti da tebura, su hudun dai kamar kullum ga kular Indomin a tsakiya an cinye tas Yaya Aliyu ya kalleni yana cewa “wai Bashir ne yace ne yadda ke kikayi girkin nan ba shine muka kiraki ki gaya masa da kanki”

“Wai daman Yaya Bashir kaine” na fada da mamaki ina kallon wanda aka kira da Bashir din. Se yanzu kuma nagane fuskarsa Bashir din gidan Baba me Mota ne, rabon dana ganshi har na manta tunda su ka fara zuwa Jami’a shi aka ce A Zaria ban sake ganinsa ba kusan shekara shida yanzu.

“Daman Fainusa tace Yayansu ya zama dan gayu ashe dagaske take “na fada ina zama a gefen Yaya Abubakar, se Bashir ya dago ya kalle ni yana murmushi yace “dagaske? Har nakai ki gayu?”

Rufe fuska nayi da mayafina irin naji kunyar nan, sosai na ringayi masa tambayoyi meyasa na dena ganinsa yace makaranta ce tasa saboda nisa baya zuwa gida se qarshen shekara, duk sanda yake zuwa mu kuma bama nan munyi tafiya. Haka na shantake seda Goggo ta aiko kirana sannan na tafi.

Tundaga wannan ranar kullum da daddare idan na dafa musu indomi zanje na zauna ina taya su hira kuma duk saboda Bashir dan haka kawai nake jin ina son yin magana dashi, haka ko a cikin gida banida labari se na Bashir yayi Bashir yace kaza ana haka muka fara shirin qualifying exam daga ita zamu shiga SS3.

Bashir ne yake tayani karatu yana ganar dani inda ya shige mun duhu, wannan kusancin da muka qara samu ya saka Shaquwa sosai ta shiga tsakaninmu dan idan na wuni ban ganshi ha har ji nakeyi kamar bani da lafiya gashi lokacin sun fara Service dan ma anan Gombe yakeyin nasa.

Banfarga cewa nayi nisa a soyayyar Bashir ba saboda ban ma san menene so ba, abu daya dana yarda Ya zama wani bangare na jikina haka ina bala’in jin haushin na ganshi yana magana da wata mace ranar haka zan wuni ina qunci.

Yaya Bilkisu ce ta fara haska mun cewa son Bashir nakeyi, nayi futu futu nace qaryane ni ba wani so kawai dai Allah ne ya hada jinin mu amma a qasan raina ina jin dama hakan ta kasance yace yana sona dana ji dadina kuwa.

Mun shiga SS3 kamar anyiwa Samari bushara da zuwa gurina sukayi mun caaa saboda yanda kyau da surata suka sake bayyana sosai, ban kuma canza hali ba ina nan ina tatawa duk wanda yace yana sona rashin mutunchi a qasan raina kuma ina cike da damuwa da takaicin me yasa shi Yaya Bashir baze ce yana sona ba se wannan banzan Balan ne ranar ya wani ce wai yana so na se kace nayi masa kalar budurwar yan shaye shaye.

Muna second term aka fara Registration na Jamb, duk su Alawiyya sunyi ni kuwa ranar da za’a kaisu siyi qin zuwa nayi nace banida lafiya, washe gari da yamma Su Yaya sun shigo gida ake hirar, Ina ji Bashir na tambayar kowa course din daya cike nayi banza dasu sanda yazo kaina har seda Junaidiyya ta tabo ni sena tura baki nace
“Ni ba zanyi ba”.

Kafe ni yayi da idanunsa masu sakani a wani irin yanayi da bansan na menene ba yace
“Me yasa bazakiyi ba?”
“Haka kawai” na fada ba tareda na kalleshi ba, se ya miqe yace na biyo shi muka fita can tsakar gida inda muke zama muna hira.

Idonsa akaina na sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna yace mun “me yasa bazakiyi Jamb ba”
“Ni babu komai kawai bana so nayi” na fada ba tareda na kalle shi ba.
“Toh aure kike so kenan?”

Sena dago da sauri na kalleshi, ganin ni yake kallo se na sauke idona ina tura baki nace
“Ni ban ce haka ba”.

“Toh idan ba aure kike so ba me yasa bazaki ci gaba da karatu ba bayan ma ko saurayin baki dashi wa zaki aura ma”.

Harara qasan ido nayi masa kafin nace “Allah ze kawo ne Idan lokacin yayi”

“Idan kuma yanzu ya kawo fa” ya fada cikin qasa da murya, se na daga kai na kalleshi.
“Allah kasa yace yana sona” na fada a raina tamkar kuwa Bashir yaji ni se ji nayi yace

“Idan kuma ni ne mijin naki fa Ma’una zaki aure ni?”

Abunku da ba kwaila tsabar murna se kawai na tashi nabar gurin da gudu ina dariya ina jinsa shima yana mun dariya abinda ba kasafai ya fiya yi ba.

Kan gado na na hau na ringa tsalle ina ihun murna, Yaya Fati Dake kwance akan Nata gadon ban sani ba ta tashi ta rufeni da fadan wane irin shirme ne zanzo ina wa mutane tsalle a gado kamar wata yarinya. Sena fada kanta ina cewa
“Tsallen murna ne Yah Fati ki barni nayi”.

“Murnar me kikeyi” ta tambayeni bayan data daga ni daga jikinta.

“Bazaki gane ba Yah Fati kawai kedai se lokaci yayi” tashi nayi na shige Toilet nayo alwala, inajinta tana cewa Allah ya shirye ni nidai na tayar na ringa jero sallolin godiya ga Allah daya sa Bashir yace yana sona.

Washe gari dakansa ya tasani a gaba mukaje nayi register Jamb, Law na ciki muka gama komai muka koma gida.

A hankali soyayyar mu ta bayyan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina da Bashir. Da yawa gani sukeyi kawai shirme nane haka shima a bangaren Bashir lokacin daya gayawa Aliyu halin da muke ciki se yace masa

“Anya Bashir kana ganin abin nan me yuwuwane?”

“Me yasa kace haka Aliyu” Bashir din ya tambaye shi, se ya ci gaba da cewa

“Kawai gani nayi kamar akwai tazara me yawa tsakanin mu dasu, ka ture abotar mu da Abubakar wannan ba wani abu bane amma ka fahimceni da wuya kaga mace ta fito daga gidan Attajiri ta auri na qasa da ita sedai shi namiji me kudi ya auri diyar talaka, sannan idan ka dubi irin mazajen da yaran gidan su suke auri babu qaramin mutum a ciki ita kanta Ma’u a kalar da Allah yayi mata Bashir ko a gidan talauci ta fito ba matar qaramin mutum me fafutukar neman abinda ze rufawa kansa asiri irin mu bace ba”.

Shiru Bashir yayi dan tabbas Aliyun yayi gaskiya. Shidin ba dan kowa bane Babansa me rufin asiri ne kawai Ma’aikacin gwamnati me da yake dab dayin ritaya kuma ba wani babbaba kusan yanzu shi ake saka ran ya zama jigo a cikin gidan su tunda shine Namiji Babba yayar sa daya da qanne biyar,

a yanzu ne ma ya gama makaranta yake bautar qasa kafin ya fara fafutukar neman aikin yi kuma.

Amma tabbas yana son Asma’u kuma itama ya yarda tana sonsa ba kuma ya fatan ace ya rasa ta.

“Haka ne Aliyu, ka taya ni da Addu’a Allah ya zaba mana abinda yafi Alkahiri toh”

“In sha Allahu, Allah ya sadamu da akhairan mu” Aliyun ya fada.

Wannan maganar da sukayi da Aliyu seta sa ya dan fara ja baya da Ma’u musamman yanda a yanzu kullum yaje gidan ze tarar da zaratan samari yayan masu qunbar susa a manyan motoci sunzo gurin Ma’un duk da bata fitowa amma hakan se yake ganin kamar wata rana zata iya chanza ra’ayi ta zabi wani daya fishi dan haka se yayi baya da zuwa gidan.

Da yake itama suna shirin fara SSCE se bata damu ba dukda indai sun hadu se tayi masa qorafin me yasa yanzu baya zuwa gidan sosai se yace mata aiki ne ya masa yawa dan yanzu ya samu temporary aiki a wani company yana zuwa.

Cikin dan lokaci su Ma’u suka gama Jarabawar su, kamar kuma yanda Alhaji ya saba a shekarar ya kaisu gaba daya suka sauke Farali tafiyar da sukayi kusan rabi da kwatan tsarabar da tayiwo ta Bashir ce harda yan gidansu. Randa suka dawo bata jira yazo ba ta hada akwati guda ta kai masa har gida tayi sa’a ta same su gaba daya yan gidan suna nan harda Alhajinsu dan haka bata zauna ba suna gaisawa ta tafi.

Bayan tafiyarta Su Fainusa suka bude akwatin suna zaro kayan ciki, sosai mamaki ya kama su ganin uban tsarabar se Dada ta kasa haquri tana kallonsa tace “Bashir ni meke tsakanin ka da yarinyar nan haka irin wannan uwar tsaraba data kawo mana?”

Fainusa ce tayi caraf tace “Dada soyayya sukeyi, ina jin a Islamiyya ma Ma’un Bashir ake ce mata”. Se Bashir ya harareta yace “ke waya tambaye ki? Tashi a nan kona mammake ki”.

“Ikon Allah, Anya bata fi qarfinka ba Bashir kaida zaka dauko daidai”

“Daman mace tana fin qarfin namiji ne Nafi?” Alhaji Amadu ya katseta, seta girgiza kai tace

“Gani nayi Alhaji idan ka kallemu ka duba gidan data fito kar ace son zuciya ne yasa ya nemi auranta”.

“To ai Annabi ma yace ana auran mace dan Asali da kuma dukiyarta kinga in hakan yayi ma ba laifi bane ballantana nasan ma ba hakan bane, idan matarsa cea se kiga Allah ya qulla abun, kiyi masa fatan Alkahiri kawai” cewar Alhaji Amadu.

“Hakane Allah ya tabbatar da Alkahiri toh ai Asma’u yarinyar kirki ce”. Daga haka suka ci gana da hirarrakin su.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 35

ASMA’U
Muna cikin wata takwas da aure me kamfanin da Bashir yake aiki ya rasu dan haka akayi rabon gado yayansa suka saka kamfanin a kasuwa abinda ya tilasta wa ma’aikata barin aikinsu.

Wannan dalili yasaka Bashir dawowa zaman gida a koda yaushe saboda har sannan babu wani aiki daya samu ya dai rarraba CV amma babu inda aka kirashi. Da farko abin yazo mana da sauqi saboda Alhamdulillah kusan komai na buqata muna dashi a gida dan abinda ba’a rasa ba muke siya irin su kayan miya ko ganye da dai sauran masarrafi dan haka idan na fita makaranta se nayi amfani da kudaden da suke hannuna na siyo mana komai yanda zamu dan kwana biyu tunda kudi basa yanke mun.

Duk sati Baffa yake bani kudin makaranta dan shi yake dauke da nauyin karatuna ga kuma na man mota da ake hadamun dashi yanzu.

Ta inda matsala ta dan bullo mana rashin lafiyar da Baban su Bashir ya fara, bayan kaishi Asibiti suka tabbatar da cewa yana da Suga da hawan jini ne suka taso masa lokaci daya seda yaci kudi sosai kafin lafiyarsa ta samu sannan aka dorashi akan magani abinda ya turgude dan jarin kasuwancin da yake yi kenan dan da kudin akayi duk hidimar Asibitin sa.

Ganin da nayi rayuwa ta fara yi musu matsi, kuma Baban da yake fita ya nema musu na cefane gashi a gida babu wadatacciyar lafiya. Bashir baya aiki a yanzu Amiru yana shekarar qarshe a Jami’a, Afiya tana Level 1 se Fainusa da Sadiya da suke secondary daga Sa’ad,Samirah har Naziru lokacin a primary suke.

Akwai ranar da mukaje duba Baban da da yamma, abinda ya daga mun hankali muna zuwa na tarar da Dada tana yi musu kwadon garin kwaki harda Baban da yake fama da Siga a sannan shi aka zuba masa yaci. Abun ya bala’in daga mun hankali.

Bayan mun koma gida washe gari banyi shawara da Bashir ba na dauki Buhun shinkafa biyu, taliya, macaroni, semovita komai biyu ga pastar mai hatta Maggi seda na diba na hada sannan na tsaya a hanya na siyi kayan Shayi da kayan miya na tafi gidan.

Yara na samu a qofar gidan suka shigar da kayan, motar Aliyu dana gani ya tabbatar mun da Bashir yana gidan dan daman tun safe yau ya fita dan haka ban shiga ba kawai na wuce gidan mu. A can na tarar da Junaidiyya wai ta zo gida haihuwa ga Yah Bilki ma tazo da tsohon cikinta haka Yah Fati Alawiyya ce dai nata be isa haihuwa ba ni se a sannan ma tunani na ya tafi ga rashin samun cikin da banyi ba.

Dukda ina son yara amma hakan besa na taba damun kaina da sena samu ciki dole dole ba kuma shima Bashir ko sau daya be taba mun maganar ko nuna wani abu akan hakan ba gaba daya mun barwa Allah shi ke bayarwa idan lokaci yayi nasan zamu samu namu muna.

A gidan na wuni har dare dan ina son naga Baffa, se bayan Isha ya shigo gida ashe Yola yaje daurin auren Yar Baffa Sama’ila.

“Mamana ya akayi ne har yanzu baki tafi gida ba” ya fada bayan dana gaishe shi, sena marairaice fuska nace

“Baffa Kasan Alhajin su Bashir bashida lafiya ko”

“Na sani wallahi ai na dubashi ma sanda yana Asibiti sannan bayan sun dawo ma na sake leqa gidan, ciwo ne babu dadi yanzu kuma abinda ake ta fama dashi kenan wannan Siga Allah ya tsare mu dai”.

“Amin Baffa, daman wata Alfarma nake nema idan babu damuwa” na fada ina gyara zamana. Se ya kalleni yace

“Gidan ku Ma’u ni zaki kalla kice kina neman Alfarma a gurina, idan banyi muku abu ba wa kuke dashi a fadin duniyar nan daya fini?
Kar na sake jin haka, ki tambayeni kai tsaye abinda kike so ko menene shi a duniyar nan zanyi miki dan duk abinda na mallaka domin na inganta rayuwar ku ne” Baffa ya fada cikin dakewa alamar babu wasa a maganar sa. Sena saki murmushi. So da qaunar Baffan nawa tana qara ratsani nace

“Wallahi Baffa gani nayi gaba daya rashin lafiyar nan ta saka sun shiga wani hali, kaga yanzu baya iya fita kasuwa ga Bashir kuma aikin da yakeyi ma an siyar da kamfanin shine nace ban sani ba ko akwai abinda zaka iya yi akai”.

“Ash sha yanzu shi Bashir din baya aiki kenan, kinga ko jiya seda mukayi maganar da Muhammadu (Alhaji Qarami) yace mun yana iyakar qoqarinsa akan maganar aikin, kinsan qasar tamu ne yanzu da lamarin aiki ko kana da hanya fa idan wanda yafi ka yazo se kiga an samu tangarda.

Sannan yace daman su masu kwalin Irin nasa me martaba ta daya (first class) suna wahalar samun aiki a ma’aikatun mu na cikin qasa saboda yawanci manyan gurin suna ganin kamar in suka dauke su zasu fisu sedai a ma’aikatu mallakin qasashen waje su daman sunfi buqatar irinsu din ze ci gaba da bada takaddun in Allah yaso za’a dace.

Shiyasa ni nafi ganewa kasuwanci amma ku yaran yanzu gaba daya kun ta’allaqa akan aikin gwamnatin nan da gaba daya abinda kuke samu a wata se kiga Dan kasuwa ya same shi a sati daya wani ma cikin yini, yanzu dai ki turomun shi, idab yana da sha’awa yazo kasuwa idan Allah yasa yana da nasibi a ciki se ki gani.

Maganar Alhaji Amadu kuma zan duba abinda za’ayi, kama daga kan rashin lafiyar tasa har zuwa matsalar iyalin se muga abinda Allah zeyi”.

Sosai na ringa zubawa Baffa Godiya da Addu’oin fatan Alkahiri, har na tashi zan tafi ya tsaidani da cewa

“Yawwa na tuna kuwa Jiya Manager Bankin da nake ajiya munyi magana naji yace zasu dauki Ma’aikata, shi bangaren nasa ze iya aiki a banki ne?”

Cikin farin ciki na koma ina cewa “Eh Baffa, shi aikin banki indai ka iya kwanfuta da kana da lissafi a takardun ka zasu dauke ka, kuma duk yana dasu”

“Toh bari na kirashi yanzu naji idan da hali se ya fara wannan din kafin sanda Allah ze kawo wani”.
Ina tsaye ya kira Manager ya kuma amsa tareda cewa ze turowa Baffan Email yanzu a tura da CV din, sannan ranar Litinan yaje Bankin ya same shi da hardcopy na takaddun.

Haka na koma gida raina qal na tarar da Bashir ya rigani komawa yana zaune yana shan Shayi.

“Se yanzu” ya faaa yana kallona, seda na ajiye jaka da mayafina na zauna kusa dashi tareda rungumo shi nace

“Canki”
“Kinsan ban iya cankar abu ba ko” ya fada yana kallon fuskata, sena dakko wata ta na bude inda na rubuta Email din na miqa masa ina cewa “Gashi yanzu kaje Cafe ka tura da Soft copy na CV dinka sannan ranar Monday zaka kai hard copy din”.

Kallona yayi da rashin fahimta, nan da nan na gaya masa yanda mukayi da Baffa na rufe da cewa “Idan kuma kafi son kasuwar yace kaje ka same shi, ni da zaka hada dukka ma kana aikin kana taba kasuwancin se ya fi yanda su Yaya sukeyi.

A zatona zanga farin ciki a fuskar Bashir irin wanda nake ciki amma se naga akasin haka, cikin daure fuska ya kalleni yace

“Yanzu Ma’u har kin fara gajiya ne yasa kika tafi nemar mun taimako a gidan ku, daman dazun ina gida an kai kaya yaran suka ce kece kika kawo yanzu kuma kinzo da wannan”.

Tsabar mamaki ma kasa rufe baki nayi na tsaya ina kallon Bashir, a zatona abun kirki nayi ashe shi a nasa girman kan gani yake baya yaci kenan na nema masa taimako a gidan, se kawai na miqe na kwashi gyalena da jaka na ajiye masa Key din motar ina cewa

“Ban shigo da ita ba tana waje naga ka datse get din da kwado” nayi shigewata daki. Yanzu fisabilillahi da ace na samar masa aiki da kuma na zama ni nake dauke da dawainiyar mu wanne yafi? A zatona tunda ya fadi hakan baze yi ba se gashi washe gari yana ce mun ya tura ranar litinin din kuma yaje ya kai Takaddun cikin ikon Allah ba’a rufa sati ba sega shi sun tura masa da takarda sun daukeshi aikin wani satin ma ze fara zuwa.

Haka muka cigaba da tafiya zuwa yanzu duniya tayi mana daidai, Baffa ya dauke nauyin makarantar Sa’ad, Samirah da Naziru ya saka su cikin foundation din sa da yake biyawa Marayu da wadanda iyayensu basu da qarfi makaranta, shikansa Alhajin ya saka Ahmad Yayan mu da yake likita ne yana aiki da Asibitin Malam Aminu Kano su acan ana samun tallafi daga qungiyoyi dan haka ana daukar nauyin magungunan masu lalurori ansamar wa Alhajin kyauta yanzu ake bashi magani ga ganin likita duk sanda ya tashi har kanon yake zuwa tunda sunfi mu kwararrun likitoci se gashi a dan lokaci ya dawo hayyacin sa ramar da yayi duk ta cike ya koma fita kasuwarsa yanzu sannan ga Kayan Abinci da ake rabawa maqota yanzu suma duk wata se an kai musu Albarkacin surukuta nasu rabon ma daban yake.

Dan haka yanzu dan abinda Bashir zeyi musu be wuce na neman Albarka da duk da yakewa iyayensa ba idan yana da hali ni kaina yanzu se sambarka dan babu abinda Bashir ya rageni dashi ya karbi ragamar gidan sa komai yana yi yanzu har kudin makaranta yake bani daman tuni na bashi mota ta saboda zuwa aiki wanda dakyar ya karba acewarsa Wanda ya siyamun bazeji dadi ba, be karba bama seda na kira Alhaji Yasir din a gabansa na gaya masa Bashir ya samu aiki dan haka na bashi motata saboda sauqin zirga zirga tunda ni ina dab da kammala karatun Jarabawa zamu fara,

“Babu komai ai taki ce kina da damar yin duk yanda kika so, daman saboda bana so naga kina hawa motar haya ne ko

Please Login or Register in order to submit comment