Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigayi tsakanin Suwaiba da Sadiya, still Sadiyar ce ta sake magana dan tafi sauran baki tace “ban gane ba Anty wanka fa mukace miki zamuyi anan kine zancen wani gidan wanka kuma ko bamu da damar da zamuyi wanka a gidan dan uwan mu ne?”

“Allah sarki masu Dan uwa dama kuma babu ita kuna iya juyawa kuje wani Gurin tunda bani kadai bace a gidan ko? Ina ga ai kamar a kwai yar uwarku ma kuna iya zuwa gurinta”.

Ba qaramin mamaki ne ya kama su ba da jin kalaman ta, Antyn da ada a dakinta suke duk wata dabdalarsu qarewar wanka har kayan sawa ta kama basu take idan ana wani taro ka zo da kayan da basu kamata ba seta dakko na fita taro ta baka ko yanzu ita Sadiya bata zo da mayafin da zata hada kayan da zata saka ba dan a safiyar nan suka samu labarin taron sunan suka kuma qudiri niyyar se sunzo duk kuwa da gargadin da Dada tayi musu amma sunce baza’ayi babu su ba wallahi.

Sabon Leshinta ta dakko zata saka bata rigada ta siya masa mayafi ba dan ta tamawa bikin Qanwar mijinta ne zata saka saura sati biyu yanzu se kuma ga wannan taron ya taso shiyasa ta dakko tasan bazata rasa mayafi gurin Anty Asma’u ba tunda tana gari qila harda jaka ta samu amma shine take gaya musu wadannan magananganu haka.

“Ku nake jira zan rufe qofata lokacin sallah ya kwace mun” suka ji muryarta ta dawo dasu daga suman mamakin da sukayi, har Suwaiba ta budi baki zatayi magana Afiya da tun farko bata ce komai ba ta dakatar dasu da cewa

“Sadiya ku muje mana ko bakiji me tace bane”
Dukyanda suka so su sake magana kuwa ta hanasu haka suka tattaru kayansu sukayi waje Sadiya da Suwaiba na kumfar bakin bazasu yarda ba su zata wulaqanta suda gidan dan uwansu ai se sun kira yayan suji idan shi ya bata sabon lasisin wulaqanta su.

Oho bata ma san sunayi ba dan suna fita Jafar ya tura qofar ya rufe dan bata buduwa ta waje dole seta ciki suka ci gaba da kallonsu ita kuma ta shiga daki ta tada sallah. Tana dakin Jafar ya shiga da sallama

“Mami ga Umman su Jawad tazo”(Zahra qawarta)
“toh gani nan zuwa” ta fada ya juy ya fita. Daurin ta ta gyara da fuskar ta ta fito fuska a washe suka rungune juna ita da Zahran da murnar yaushe gamo dan an dade ba’a hadu ba kafin suka zube akan Two sitter ta shiga yiwa Zahra tsiyar qiba.

“Kai matar nan gaskiya wayo kikewa Yah Sayyadi ji yanda kike narka qibar kamar wata Aisha Buhari 😂😂🤐”
“To ya za’ayi barni nayi qibata kowa ya ganni yasan ina jin dadi tunda jikin yaqi zama irin naku jikin models” Zahra ta fada da sigar shaqiyanci suka kwashe da dariya tareda kashe wa, Sallamar da akayi ta katsew Ma’u maganar da tasoyi.

Rahma ce matar Amiru qanin Bashir bayanta kuma Kamila ce itama qanwar su Bashir dince da me aikinta dauke da danta dagaje dagaje dashi ga ledar kaya a hannun Kamilan. Da sauri Kamilan ta shigo dan seda Rahma ta matsa gefe ta bata hanya ta dire ledar a kan centre Table ta na cewa Me aikinta “maza Usaina ki gyara masa jikinsa ga kaya nan ki saka masa nima yanzu zan zo na yi wanka na shirya” ta juya ta fice ita kuwa Usaina ta qaraso ciki tana gaishe su da niyyar ajiye yaron Asma’u tayi saurin dakatar da ita.

“Dauki kayan maza ki bita” ta fada tana nuna mata hanya, ba musu kuwa Usaina ta kinkimi leda da yaron tayi waje harda ja musu qofa se sannan Rahma ta sama ma kanta gurin zama.

“Keda mutanen naki kuma yau Maman Aliyu” Rahma ta fada tana dariya.
“Da kenan Maman Nasir ai sun shani na warke kuma yanzu, kunga ku tashi kuje sama ina zuwa”. Zahra da Rahma suka miqe zuwa sama qaramin palour Ma’u da take sauke manyan baqinta.

Kallon Jafar da Abdallah dake kallo tareda Jawad Dan Zahra tayi tace “ina su Ahmad?”

Jafar ne ya amsa mata yace “Yaya ya fita, yah Amna da Farida ma sun tafi gidan su Amina Shehu sunce sun gaya miki tareda su Ahmad din”

“Eh na tuna, kana jina duk bugub da za’ayi ko waye karka kuskura ka bude kofar nan”.

“Tam Mami” ya amsa mata yana daukar Handle din Game din da suka kunna.

Kitchen ta shiga ta hado ruwa da lemo da tarkacen kayan motsa baki a Babban Try Jawad ne ya karba dan yafi Jafar din girma ya kai saman ita kuma ta dibar musu Abinci da sauran kayan da zasu buqata duk ta basu suka kai, da kanta ta murzawa kofar key ta kuma sake jan kunnensu akan karsu bude mata qofa kafin ta haye saman suka hade da su Zahra aka shiga hirar duniya da abinda ze amfane su ba tareda sun koda taso da zancen Abinda ke faruwa a cikin gidan ba.

A dakin me jego fa tuni abubuwa sun dauki Harami, tana zaune ta ci Ado da wata danyar shadda data sha aiki su Sadiya suka shiga palour suna kumfar Baki da zage zagen abinda Ma’u tayi musu, anan palour aka maida magana basu dasa Aya ba Me aikin Kamila Ma ta dawo tana miqawa Kamilar ledar kayansu.

“Kan bala’i lallai matar nan au kema koroki tayi?” Kamilan ta fada.
“Ta koromu ma bare wata me aikin ki ai wallahi bari a tashi taron nan bata ci banza ba se mun nuna mata nan gidan dan uwan mune muna da ikon yin yanda muka ga dama a ciki, ke Amirah bamu muqullin dakin Yaya naji kofar a kulle take”. Cewar Sadiya.

“Nan fa daya yaya sadiya key din dakin mijin nawa zan baku kema kin san baze yuwu ba” Amirah ta fada tana yatsina fuska, tab waima ta basu key wallahi bazata bayar ba kuwa.

“Oh kema diban Albarkar zaki mana dakin dan uwan mu fa mukace ki bude mana mu shiga mu shirya tunda kinga dai nan ko ina da mutane” Kamila ta karba se kuwa Amirah ta miqe tana sabar yarta da take ta nan nan da ita ga kuma key din a hannunta dan kayan da zata saka dana rabo duk suna ciki bata kuma yarda ta bawa kowa ba banda Ummi se Anty Aisha su kadai ta yarda suka shiga dakin.

“Bafa zan bayar ba Yaya Kamila idan kun matsu da wankan ku shiga na dakin baqi dan na kulle toilet din dakina ma kar a batamin ko ga wani nan ai a kofar daki kuyi amfani dashi” ta shige dakin ta ta barsu sototo baki a bude tsabar mamaki.


Mura ce take damuna wallahi kuyi manaji da wannan 🙏🙏🙏
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 19

Tunda Bashir ya qulla tsiya ya kuma tabbatar Naziru ya kulle gidan dan sun sake yin waya ya gaya masa ya je dakko su Amna a gidan qawarsu a sannan ce masa yayi ya wuce ya kaisu gidan Bilkisu yayar Asma’u kawai dan idan yace gidan Dada zata zargi wani abu kuma baya so labarin ya isar mata da wuri.

kashe wayarsa yayi dan karma wani dayake ganin mutunchi ya kirashi ya roqeshi. Beko qara minti goma a gidan Musa ba ya tafi yana tuqi a ransa yana wassafa irin hukuncin da ze dauka akan Amirah tunda har ta take dokarsa ta nuna bata jin maganarsa tabbas ze nuna mata shima ba kanwar lasa bane.

Daya isa gida shikadai ya ringa safa da marwa a cikin palour yana kwafa tabbas se ya hukunta yarinyar nan hukunci me tsanani, tunanin halinda Baby Iman take ciki yake yana fatan Allah yasa yarinyar tana lafiya wani abu be sameta ba hakan ze dan rangwanta wa Amirah hukuncin da zeyi mata amma ya rantse tabbas wani abu ya sami yarinyar nan se kansa besan me ze mata ba. Yana so ya kira Ma’u amma bayaso ya kunna wayar wani kiran ya shiga qarshe haka ya haqura ya zauna jiran lokacin daya diba kafin ya sake kiran Naziru.

Gidan suna kuwa gagarumin ruguntsumi ne ya sake tashi. Ana tsaka da dambaruwar yanda za’ayi a bude qofa, dangi da qawayen Addah sun taru suna mata tijara sun cika palour Amirah taf kaman an sakko daga Idi daidai da iska me kyau babu ta shaqa se kaya kaya akeyi.

Amirah na durqushe se rasgar kuka take har sannan akan yarinyar da harta gaji da komawa da numfashinta ta kwanta laqwas kamar mara rai ita duk wannan hayaniyar ba ganewa take ba, buqatarta a samu me kai mata ya Asibiti dan ta dade da saddaqarwa yau kashi ta ya gama bushewa.

Addah data gaji da tijara da cin mutunchin da Jama’a suke mata ta zaro Key ta cillawa Hajia Mariya datafi kowa hasala a cikin matan dan ita aka dira daka, so take kawai ta fita ta san nayi dan ko karan hauka ya cijeta bazata doshi gidan mijinta yanzu ba se da wannan mota da bata san uban da ya sace ba dan haka ta yanke shawarar daga nan office din Yan sanda zata ta bada report daga can kuma tayi gidansu dan tasan waye mijinta sarai haka kawai ma yayi bala’i bare yau da aka taboshi da lasisi.

Cafkar key din tayi tana watsawa Addah kallon wulaqanci tace “da karki bayar wallahi da sena tubeki na dauki muqullin nan yau” ta fara kutsawa da niyyar zuwa bude qofa Hajia Hassana ta katseta tana cewa
“Mariya wannan muqulli fa aikin banza ne dan ta waje wani hatsabibin yaro ya kullo mu wallahi. Kuna tsaka da hayaniya dazun nan Uwargidanta ta raka baquwa ta bude kofar tana fita yaron nan ya danno daga waje ya rufe jeki duba ma ki gani babu kwadon nan ta ciki”.

Kafin ma ta qarasa dayawa sun dauki sabon kukan tashin hankalin rashin sanin wane kalar bala’in ne kuma yake tunkaro su, To bala’i mana in ba haka ba ta yaya za’a ce an kullo su ta waje ma bata ciki ba yanzu suyi yaya su fita dan dai wannan katangar gidan basu isa su tsallakata ba.

Ummi ce da tuni itama ido sukayi mici mici saboda kuka ta sunkuci Iman tana ceda Amirah “nidai matsa ki gani wannan hayaniyar da hucin numfashin kadai sun isa su qarasata muje ko a Napep ne mu tare mu kaita Asibiti” ta nadeta a cikin shawl din ta kyau ta juya da niyyar fita kamar ana jiran ta kuwa dif wutar palour ta dauke duhu ya mamaye ko ina bame ganin wani a ciki.

Gaba daya guri ya sake rikicewa da ihu dan kina tsaye sedai kiji an wafce miki jaka nan aka shiga turereniyar fita ana faduwa duk wadda kuwa ta fadi sunanta sorry dan taketa za’ayi ana neman hanyar tsira a garin haka aka dungure mata Tv ta fado qas tim Centre table kuwa daman tuni ya karbi rabonsa se fatan kar wani ya taka kwalba a garin gudu.

Wata qara me kama da rugugin tsawa a ka fasa kafin sukaji faduwar abu tim a qasa, sabon gudu ne ya falle ga duhu ba wanda yasan takamaiman ina yake dosa aka ringa gwabza karo ana faduwa kuwa kafin kace me anyi wada wada da kayan palour Amirah,
Seda aka kwashi a qallah minti goma se ga haske ya dawo ai kan kace kwabo wayam sun fice daga palour an dawo tsakar gida kowa tayi cirko cirko fuskokin mata jagejage da hawaye wannan Suna ko jaraba?

Addah data ja qafa da niyyar gudu itama caraf aka riqeta cikin abinda befi sakan uku ba ta saki fitsarin tsoro ganin sunyi ido hudu da Hajia Mariya dake yashe a qasa da ko ba’a gaya mata ba tasan riqaqqun iskokanta ne suka tashi. Tun da tace an sace motar nan abinda take taraddadi kenan dan indai ranta ya baci se sunzo kuma Al’amarin bazeyiwa kowa kyau ba dan Aljanunta basu da mutunchi yanzu basuqi suyiwa kowa na gidan sunan nan bulala dari dari ba.

Sake yunqurawa tayi da niyyar gudu Mariya ta miqe cikin muryar yara tace mata “Addah fatu muje washan goyo ja’ayi yau kowa seya goya ni in ba haka ba nayi masha buyayay goma ke zaki faya kuma”

“Quuuu” cikin Addah ya bada qara, yo ai badanba gara bulalar akan tace a goyata. Ita kadai ma Hajia Mariya ba kadan bace qaruwar mace ce ta gaske bare idan wannan yar Aljanar tata tazo me son goyo seta Allah in kuma bakayi ba kaci na jaki. Addah naji tana gani ta tasata a gaba suka fito inda Jama’a sukayi cirko cirko ta dane bayanta kuwa.

Zanso kuga idon Addah haka ta goya hajia Mariya tana nishi kamar zata mutu ta kaita ta dawo da ita amma taqi sauka tace se an sake haka ta kuma sahu daya da ita sukaje suka dawo sannan ta sauka. Zaba ta ringayi wanda ze goyata in ka tsaya gardama sedai kaji dundu kamar an buga maka guduma kuma in ta hau marasa qarfi suka fadi nan ma ta hau tamola da mutum aifa gida ya sakw zama kamar gidan Allura se kuka ake wannan jaraba har ina.

Aliyu dake cikin dan dakin da Change over da Solar su ta gidan yake ya kwashe da dariya har yana kaiwa qasa. A kan idonsa komai yake gudana dama jira yake gari ya qara duhu ya kashe haske ya qara musu tension akan wanda suke ciki gashi kuwa yayi ga kuma sabon show an samu kai amma fa abu yayi kyau kuma yaji dadi, fitowa yayi ya wuce part dinsu, knocking biyu Jafar ya bude masa ya shiga yana Dariya.

Asma’u dake zaune akan kujerar Dining suna waya da Yaya Bilkisu ta gayavmata su Farida suna can Naziru ya kaisu ta dago ta kalleshi, tun ma kafin tayi magana yace “Mami kinga yan suna kuwa ga wata can tana Aljanu tace se sun goyata kowa takalminta a hannu lipstick duk ya goge”.

Duk yanda taso dakewa tayi masa fada kasawa tayi ta fashe da dariya dan tana hango harabar gidan dan tarwai yake da hasken fitulun da aka zagaye shi dasu, saboda ma taga komai dakyau yasa ta dage labulaye suka rage hasken fitulun palour duk drama da akeyi akan idonta ne tana ganin haske ya dauke kuwa jikinta ya bata Aliyu ne dan ta san aikinsa ne kashe wutakuma dazu ta ganshi a zaune a qofar power room din magana ce kawai bata masa ba ta wuce.

“Allah ya shiryeka, kar naga ka sake fita in ba haka ba ranka ze baci” ta fada tana miqewa.
“Sunan wani film waishi daga murna” ta fada tana shiga kitchen dariya fal ranta, Yogurt ta dauka da cups biyu ta koma dakinta inda ta bar Rahma tana sallar Isha tunda yaranta sun samu mafaka ai shikenan ita kam.

Abuubuwa sun sake rikicewa Addah ido ya raina fata, data san haka ce zata faru kuma da bata kulle qofar ba gara tabar kowa ta tafi gidan ta idan yaso tayi Allah ya isa amma gashi yanzu an bata goma daya bata gyaru ba. Dakyar ta samu ta zillewa yar zulai Aljanar Hajia Mariya tayi bayan gidan gashi ta Rasa wanda ze kira mata Dada dan ita kadaice kuma madafarta a yanzu idan ma ba’a san wandaya kullo su ba ita zata iya nemo wanda ze zo ya buge kwadon amma wannan garqamewa da akayi musu idan wuta ta tashi fa Allah ya kiyaye subi ina su fita?

To kuma kiran Dadar ma ba hali dan an sace waya kuma tasan babu me bata aron tasa idan ma an bata ita ba haddace Number ta tayi ba, dabara ce ta fado mata arai, bari taje gurin Ma’u ta kira mata Bashir ai shine me gida dukma tsiyar da za’ayi sudai a bude su tukunna jama’ar data tara su tafi wannan bala’in ya ragu dan dai kam taga suna yau ganin idonta bakuma ta fata Allah ya sake maimaita mata irin wannan taron. Sadadawa tayi ta faki ido ta zagaya ta kofar kitchen din Ma’u.

Kamar zata balla qofa haka ta ringa doka musu bugu tanayi tana wai waye gudun kar wani ya ganita Har Jafar ze bude Aliyu ya riqo shi yana cewa “kai baka da hankali ko to jeka bude musu baka san me yake faruwa a gidan nan bane” se Jafar din ya fasa amma be zauna ba ya tafi ya gayawa Ma’u.

Ta yar hudar jikin qofar ta hango Addah fuska tayi qozai qozai abunka da fara daurin da aka dandasa mata dazu yayi ta kansa ga kunnenta daya da dan kunne daya babu ta tabbatar bata ma lura da hakan ba. Bude mata qofar tayi tana shigowa kuwa takai qasa tana rushewa da kuka kamar qaramar yarinya.

Kiyiwa Allah Asama’u ki kira Bashir azo a budewa mutanen nan qofa su fita kafin su kashe ni nidai nayi dana sanin wannan qaddararren taron suna ashe rabon wahala ne yasa muka nace se munyi” ta sake rushewa da kuka harda sheshsheqa.

Ba qaramin dauriya Ma’u tayi ta riqe dariyarta ba amma dukda haka da Addah a hayyacinta take seta gane dariya take mata tace “toh Addah meya faru kuma ni da naji shiru an dena kida ma na zata kun tashi ne.
Wayar Baban Aliyu kuwa a kashe take fa dan na kirashi tun dasu naji amma bari na same kira ko yanzu ya kunnata” ta fada tana danna wayar ta lalubi Number sa ta danna kira, kai kodan ta sake kunno musu shi idan be sani ba ai yasa ta kirashi sedai kamar dazu data kira ce mata akayi a kashe take.

“Wallahi Addah a kashe take” ta fada tana janye wayar a kunnenta
“Kiramun Nafi dan Allah ita ta samo mana wanda ze bude mu” Addah ta katseta seta maida akalar kiranta kan Dada itama seda ta mata kira biyu sannan ta daga ba tareda ta yi magana ba ta miqawa da Addah wayar ta karba tana rushewa da Dadan da kuka.

“Nafi na shiga uku na hada taron masifa da Bala’i yau ki taimake ni yar uwata ki kawomun dauki” Addah ta fada cikin matsanancin kuka. Dada da harta kwanta dan cikin ikon babu wand aya kirata ya gaya mata wannan Al’amari dan yayanta da sukaje suna bayanda Asma’u da Amirah suka gwanya musu rashin M fushi sukayi suka bar gidan, ragowan dangin da suke can kuwa tunanin su kirata be zo musu ba koda yake rabi da kwatan yan suna an kwamushe musu waya wadanda suka tsira kuwa sunyiwa tasu boyo me kyau kafin a sane ta.

“Addah lafiya, meya faru? A ina kuma? Dada ta tambayeta cikin damuwa da jin kukan nata tasan ba lafiya ba amma Number Asma’u data gani yasa hankali be tashi da yawa ba tasan koma mene ne da sauqi.

Addah kukan ta taci gaba dayi, ganin da Asma’u tayi bata da niyyar ansawa Dada ya sakata karbar wayar ta danyi mata bayanin iya abinda ta fuskanta da lamarin.

“Ashsha abu beyi kyau ba, yanzu waye ya kulle gidan? Shi Bashir din ya sani?” Dada ta tambaya se Asma’u tace mata
“Muma bamu sani ba Ai, Baban Ali kuma ban sani ba gaskiya ko yasan maganar dan wayarsa a kashe take tundazu dana kira”.

“Shikenan bari nayiwa Amiru magana gashi can yana cin abinci daman nan gidan naku ze taho ya dauki Rahma in yaso se suzo da Naziru yanzu Allah ya kiyaye gaba” Dadan ta fada zuciyarta sam babu dadi, yanzu wannan wane irin abune ai yanzu Allah kadai yasan inda maganar sunan nan zata tsaya sun jawo musu abun fada a gari. Fitowa tayi daga dakin ta ta tarar da Amirun a tsaye yana niyyar fita dan sunyi sallama ta shiga ciki.

“Amiru ka nemi Naziru ku tafi tare gidan Yayan naku ba lafiya ba”.

Da”Allah ya kyauta” ya amsa mata ya fita yana dannan kiran wayar Naziru dan shi duk a zatonsa be wuce a ce rigima ce tsakanin Ma’u da Amirah ba, a hanya ya dauki Naziru daya maze kamar besan me yake faruwa ba, gama wayarsu da Bashir kenan ya kirashi da wani layi yace masa duk me za’ayi karya kuskura ya bude gidan nan qasa da qarfe goma na dare yanzu kuwa har tara ta gota dan haka ya qara musu awa daya se sha biyu ze bude su kuwa.

Kamar wata boarding school ranar hutu haka suka tarar da qofar gidan cike da motoci, yawanci mazajen wadanda Allah ya taimakesu suka tambaya kafin suka fito ne an kuma san inda suka tafi da sukaji shiru suka biyi sahunsu se wadanda yan uwansu suka kira su dauke su.

“Kai lafiya kuwa gidan meyake faruwa haka” Amiru ya fada se Naziru ya marairaice kamar na Allah yace
“Yanda ka gansu yaya nima haka na gani, mu qarasa mugani Allah yasa dai lafiya. Bakin get suka qarasa inda wasu suke qoqarin yanke kwado amma kamar na tsafi yaqi yankuwa wasu daga gefe kuma suna musu magana akan su bari, ta yaya zasu budewa mutum gida bada izininsa ba duk abinda yake ya dawo su tabbata yana kansu.

“Wai meyake faruwa haka ne” Amiru ya tambayi masu yanke kwado dan shi tunaninsa ya tafi kodai gobara ko wani babban Al’amari ne kuma yake faruwa amma kuma hmga kwado ta waje ga kuma kururuwar mata suna jiyowa daga ciki suna ihun a taimaka musu.

“Kagane Alhaji nima bansan me yake faruwa ba gaskiya Beb dita ce ta kirani tace nazo na dauketa a gidan nan tazo suna daman ni na kawota dazu se kuma tace na taho da me yankan kwado idan zan zo kaji iya abinda na sani nidai” shugaban masu kiciniya da kwado ya fada.
Se Amiru ya kalle shi cikin masifa ce“wannan wane irin rashin hankali ne, meye a cikin gidan da har zaku zo ku budewa mutum ba tareda izininsa kona wanin sa ba idan wani abun nema ai se ku fara neman izinin me gidan tukunna”.

“Megida ka ganmu nan dukka jiran a bude gidannan muke takamaimai babu wanda zeje maka yasan me yake faruwa dayawan mu munji shiru ne matan mu basu dawo ba muka biyo sawu wasu kuma kiransu sukayi a waya suzo su dauke su kaji yanda abin yake” wani mutum ya sake fada, se Amirun ya zaro wayarsa bayan yacewa Me Yankan ya tsaya ya dannawa Bashir kira cikin Sa’a kuwa ta shiga.
Basu ko gaisa ba Bashir da yasan kiran ko na menene yace masa

“Ni na saka Naziru ya kulle gidan kuma wallahi duk wanda ya budemun gida kafin sha biyu na dare se nayi sharia dashi” qit ya kashe wayarsa. Se Amirun ya juya yana kallon Naziru daya sha kunu

“Bani key din Idan yaso se yayi shari’ar dani” ya fada fuska babu wasa.

“Amma yaya kasan dai ni laifina ze gani ai kuma...”

“Zaka bani ko bazaka bani ba, daman kasanabinda yake faruwa muka taho amma baka gayamun ba kayita biye masa kunawa mutane shirme. In ba haka ba matan auran zaku kulle har se sha biyun dare saboda shirme” fada sosai Amiru ya rufe Naziru dashi, wayarsa da ta shiga qara ce ta katse shi ya daga Ummi ce cikin kuka take gaya masa halin da ake ciki dan a zatonta yana Katsina shiyasa tun tuni bata kirashi ba.

“Tundazu ina bakin Get din na rasa ta inda zan fita na kai yarinyar Asibiti Yaya tsoro nakeji karta mutu a hannuna” ta fada cikin kuka. Nan da nan hankali sa ya qara tashi, Naziru da yake kusa dashi duk yaji me take fada tun kafin ma ya masa magana ya zaro key ya bude gidan ba tareda ya saurari Mazan da sukayo masa caaa akan daman shi ya kulle amma ya barsu suna shan sanyi a tsaye.

Yana bude qofar da Ummi yaci karo da azama ya karbi Babyn suka juya shida Amirun tabi bayansu suka shiga mota kafin Mata suka fara tseren fitowa kamar an sako kaji daga keji wata dankwali a hannu wata da takalmi qafa daya babu dai me cikakkiyar nutsuwa a cikinsu kowa tayi ta kanta. Suna dai kam da yawa sunce ko su suka haihu sun yafe bare a sake gayyatarsu suje.

Cikin qasa da minti Goma sha biyar gida ya rage Me jego da Addah da

Please Login or Register in order to submit comment