Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina barwa Amna sallahun abinda zata girka ya fito muka kalli juna se cewa yayi

“Kiyi mun tuwo da miyar Kubewa da rana za’a zo a karba”

“Naman rago zaki sakawa Miyar Akwai soyayye ma a Freezer seki diba” na fada ina zuge jaka ta dan duk a zatona da Amna yake seda naji yace

“Dake nake ba ita ba, daga yau ma karta sake yimun girki kuma kullum za’a ringa kaimun lunch office” yana gama fada yasa kai ya fita na bishi da saurin. Sanda na fito yana tsaye a jikin motarsa.

“Ban fahimci abinda kake nufi da nayi maka lunch ba ka manta zanje aiki ne” na fada ina kallonsa, idan ya amsa ni to motar sa ma tayi magana, ya kunna mota ya bata wuta, harya taka ya leqo ta window yace
“Banyarda ki dara qofar gidan nan ba” ya qarawa motarsa wuta ya barni a tsaye.

Kamar mara laka haka naja qafafuna na koma cikin gidan, akan kujera na zube ina sauke numfashi, dagaske dai Bashir yake ya na so ya rabani da aikina kenan. Badan ina tsoron Allah da fita zanyi sedai duk abinda ze faru ya faru amma yau zan haqura idan yaso ya dawo naji me yake nufi dani tukunna.

Anty Suhaima na kira ina kuka na shaida mata komai tunda daman da ita muka fara maganar ai, haquri ta bani tace yanzu zata kira Alhaji qarami ta gaya masa duk yanda mukayi zanji ba’a rufa awa guda ba kuwa sega kiran Alhaji Qaramin.

Shima din nasiha yayi mun akan na kwantar da hankali na shedan ne kar mu bashi qofar da ze farraqamu ya tabbatar mun kuma ze kira Bashir din yayi masa magana.

Ban san yaya sukayi ba dan daya dawo be kulani ba fuskar nan dai kamar ta shanu haka muka kwana kamar abokan gaba. Washe gari dan na gwada Sa’a ta na shirya kuma akayi dace tafi kuma mutu be ce dani ba hakan yayi mun dadi alamu sun nuna sunyi magana da Alhaji Qarami kenan kuma ya barni naci gaba da zuwa aiki.

Haka muka cinye sati biyu cir ana wannan yanayin duk iyakar qoqari inayi gurin kyautata masa dayi masa duk abinda nasan yana so amma kallon banza ban ishi Bashir ba bare na arziqi haka idan zan kwana ina masa magana baze daga kai ya kalleni ba ko wani abin yake so sedai ya kira daya daga cikin yaran yayi masa.

Abinda na lura dashi shine harda zugar mutane a cikin abun nasa kuma daman na san Bashir halinsa ne daukar shawarar wasu indai ka gaya masa abinda yayi daidai da ra’ayinsa tofa shikenan.

Haka dai nake lallabawa ina taka tsantsan da duk abinda ze qara mun laifi a gurinsa ga zazzabin da yake damuna kullum qaruwa yake ga kuma sabuwar damuwar Bashir gaba daya na susuce har wata rama nayi,

A bakin Aliyu naji cewar Monday zuwa Laraba su Bashir bazasu yi aiki ba an basu hutu, nan da nan nima na rubuta letter akan bani da lafiya naci sa’a akayi mun approving da wuri dan daman duk wanda ya ganni yaga mara lafiya.

Nan da nan na shiga shirye shiryen yanda zamu gyarota da Bashir dan wannan zaman doya da manjan da mukeyi bayamun dadi kuma a zahiri na fishi cutuwa sedai nima qudurce a raina indai yana tunanin abinda yakeyi ne zesa na sakko na bi ra’ayin sa na ajiye aiki na na koma Gombe ya dakko wata Mata ya kawo nan to kuwa bazan chanza ba.

Idan da ace wani uzuri can na daban yasa ya yanke hakan zan iya karba amma wallahi indai akan Amirah ne a wannan gabar na shirya karbar komai.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_MrsAM

TALLAH TALLAH TALLAH

"ASMA'U Baban Ali ya kirayeni da ainihin suna na wanda ko a lokacin Auransa da AMIRA da muke kan ganiyar zuba rashin Mutunchi ba haka yake kirana ba "MA'UNA" shine sunana a bakinsa kuma a gaban kowa duk kuwa da baqin miskilanci irin nasa, a gaban wanda yake matuqar kunya ne yake kirana da "HUSNA".

"ASMA'U ASMA'U ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki".. tun be kai ga qarasa ba nace "Sau uku ENGINEER BASHIR AHMAD" dan nidin fa ba baya bace a fagen iya fitsara kawai dai shekaru suka sa na farayin sanyi amma a wannan gabar dole na fito masa a ainihin MA'U ta wadda ya sani shekaru goma sha shida da suka gabata bawai ASMA'U uwar Aliyu, Jafar, Farida, Abdallah, Ahmad da Muhammmad ba.

Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana tabbatar na zallar mamaki ne jin sunansa a bakina Gatsal bako Sakayawa, lallai ya manta dawa yake magana, a zatonsa nayi tibis be san haryau da saurana ba sedai baa tabo ni ba. Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da zuciyarsa take ayyana masa, wani sashe na ingizashi akan  yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa zafa ta iya kwabewa amma idan ya ja da baya ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so kenan.

Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatarwa duniya be isa da ASMA'U ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa tareda qara tsuke fuskarsa da dama can bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda wannan kangararriyar Matar. Cikin kaushin murya yace

"For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara yara ku koma Gombe d....."

"Na gaya maka bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo Matarka Lagos" nayi saurin katse shi.

"Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna zallar bacin ransa.
Qara jinjina qarfin hali da rainin wayonsa nayi a raina, yau na shirya ganin qarshen rainin hankalin Bashir dan haka nace

"Idan har saboda matar ka kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR"
"Haka kika ce"
"Eh"
"Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki".
Wani irin dum naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi muni ji a rayuwata gaba daya, wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir dagaske kake" na fada cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba

"Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA badan babu kyau ba ma sena cike miki ukun ki kinga se kiji dadin yin aikin ki dakyau" ya fada daidai sanda yake shirin ficewa daga dakin.

Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan gadon dake bayana, Allah ne ya rufa min asiri, a yanda nake na tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze hana barin jikina shanyewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan minha" cikin ikon Allah kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan. Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa tamkar kan saka super glue an liqeta haka naji nanda nan kaina yai dum kafin kace meye numfashina ya fara sama sama ba shiri na fara laluben inda Inhaler ta take wadda sabuwa ce na shigo daukowa dan ta cikin jakata ta qare.

Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na nan a toshe. Kai ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin me ma zeyi mun?
Ni Ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan shedan ne amma gashi kamar a zahiri hakan ta faru. Ina cikin wannan yanayin naji an turo qofar dakin, nasan yarana dukka suna makarnata kuma lokacin tashinsu beyi ba.

Nima rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya wai dan na huta na zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan tsakanin nan ashe ashe....

"Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa AMIRAH sabon kaya Zuwa Weekend zata dawo dan haka na baki grace of today ki hada ya naki ya naki kinga yanzu komawa Gombe dole" kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juya yabarni ni bame rai ba ni ba sumammiya ba.

Dakyar na miqe na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin qarewar yau nida yayana. To tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi. Kofar gidan na fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya fada, idan ban manta ba Abokin aikin Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan tunda dama Office ne suke basu dan haka yanzu babu kowa a ciki.

Gidan dake kallon namu na nufa nan kuma Ogan Bashir ne a ciki da nake kira da Baba saboda sunan Mahaifina ne dashi dukda be haifeni ba amma kadan ya rage, nasan yana gida kaman yanda Bashir yake nan yau suna hutune company su dan haka na shiga danna door bell ba saurarawa. Banyi zaton nayi sallama ba lokacin da Anty Matar sa ta biyu ta budemun qofa haka na nausa kai dan fa bazan iya cewa wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa Baba na zaune a palour yana Kallon News na isa gabansa na durqusa.

"Hajia Ma'un Bashir" haka suke tsokanata kai kowa na Estate din ma haka yake kirana kadan suka sanni da Maman Aliyu wasu Maman twins.
"Meya faru" ya fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka ba amma kallo daya zakamun ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki se kawai na tsinci kaina da cewa "Baba Flat din Maman Boda zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah".

"Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan tambayoyi da daya kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace masa

"Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kayana a yau nabar masa gida kafin ya dawo" na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa. Kuka nake tamkar raina ze fita inda Baba da Anty keta faman zabga salati suna qarwa.

"Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka??"


Wace ce ASMA'U?
Wanene BASHIR?
Me ASMA'U tayiwa BASHIR da har ta cancanci wannan hukunci haka???

Amsar ku tana cikin Sabon littafi na Me suna WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)

Wannan salon na daban ne na kuma tabbatar muku bazan baku kunya ba kuma ina fatan kar ku bani kunya.

I to tell 10
10 to tell Ozers 🤣🤣
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 32

Tareda Anty muka koma, Bashir na zaune a palour muka wuce dakina. Wayata dana gani ta tunamun da gida, wazan kira na gayawa wannan mummunan labarin??

“Alhaji Qarami” zuciyata ta raya mun, nan da nan na danna masa kira cikin sa’a ringing biyu ya daga yana cewa “wato a kwanakin nan dai Ma’u tana yi dani irin wannan kira akai akai haka”.

Kuka na fashe masa dashi sosai ya shiga tambayata ya akayi, dakyar na iya tsagaitawa na gaya masa cewa Bashir ya sake ni. Seda yayi salati ya sanar da ubangiji kafin yayi shiru na wani lokaci yace

“Ma’u kowa da kalar qaddarar sa a rayuwa kiyi haquri ki dauka jarabawa ce daga ubangiji idan kika jure se ki samu saka mako me kyau. Yanzu kina ina?” Alhaji Qarami ya fada cikin jimami, seda Naja sheshsheqa kafin nace

“Yace ya bani iya yau na kwashe kayana na bar masa gidan sa Yaya yanzu ina gidan kayan nake hadawa”.

“Shike nan, ki hada iya abinda ya samu, bari na kira Abubakar dan yace mun yau ze shigo nan din idan yaso ko hotel ne se ku zauna kafin gobe a duba miki gida zuwa muga yanda hali ze yi, ki dena kuka sannan karki kira kowa a gida ki gaya masa kinji ko”.

“Toh Yaya Nagode Allah ya saka da Alkahiri “ na fada kafin mukayi Sallama naci gaba da taya Anty hada kayan dan tuni ta sauke kayan wardrobe dina tsaf tana ta durasu a akwatuna. Seda muka kwashe komai dan seda muka Hada da manyan Jakunkunan Bakko da muke zubo abubuwa daga Gombe daman in na cire kayan ciki sena ninkesu na ajiye da rabon zasu min rana ashe. Har kayana na dakin Bashir seda ta kwaso komai bayan da tayi masa watsa watsa da nasa a qasa.

Da muka gama da nawa kayan dakin yaran muka koma, lokacin Bashir ya bar gidan suma muka shiga hada musu kaya kowa a akwati kafin wani lokaci mun gama Anty ta fita ta samo samari suka ringa dauka suna kaiwa gidanta.

Mun fito da akwatin qarshe kenan Yaya Abubakar ya tsaya da motarsa a qofar gidan, rabon da yazo tunda Bashir ya auri Amirah suka samu sabani sedai mu hadu dashi a gida idan naje Gombe ko muyi waya.

Kai tsaye na fada jikinsa na fashe da kukan dana samu dakyar ya tsaya mun dazu yana bubbuga baya na yace “kiyi shiru Ma’ulle abinda yake so kenan yaga gazawarki bayan shi yayi asara bake ba”.

Tare dashi muka shiga gidan Antyn muka tarar da Baba ya dawo, cikin mutun taka suka gaisa Baba ya shiga bashi haquri akan abinda ya faru kamar shi yayi laifin sannan ya gaya mana ya samu approval an bani gidan kuma harda 50% discount akan kudin hayar ma suka bayar kuma ya biya yanzu ze kira kamfani masu wankin gida suzo su gyara yanzu se muje mu ga gurin ga Key nan an bashi.

A tare muka fita gaba daya, gidan lafiyar sa qalau dan daman ba’a dade da renovating nasa ba qura kawai yayi se yana saboda babu mutane a ciki, muna tsaye ma sega kamfanin daya kira sunzo da kayan aiki cikin qasa da awa daya suka wanke gidan tas har bangwaye seda suka wanke ko ina ya dauki kyalli.

Bansani ba Ashe tunda muka shiga Yaya Abubakar ya kira Alhaji Qarami ya gaya masa maganar gidan, se ganin motar kayan furnitures nayi sunzo da saitin gado da kujera harda labulaye da carpet kamar wasu kayan Amarya nan da nan suka shiga daurawa.

Muna fito wajen gidan motar makaranta ta sauke su Aliyu, da mamaki suka tsaya suna kallon gidan Farida tace “Mami gida zamu chanza naga ana saka sabon kaya a nan”

Gaba daya kasa kallonsu nayi dan ji nayi wata sabuwar karaya tana zuwar mun, yaya zasu ji idan suka gane mun rabu da mahaifinsu? Fitowar da Yaya Abubakar yayi daga cikin gidan ta ceceni daga tambayoyinsu suka nufeshi da murna nan take na sulale na shige gidan Anty ban san Aliyu yana baya na ba seda naji ya ruqo hannuna yana cewa

“Mami meya faru, kukan me kikeyi?”
Aliyu ya wuce shekarun da zance zanyi masa wayo, kai tsaye ina hawaye nace masa “Aliyu mun rabu da Abbinku, kuje ku duba idan akwai sauran abinda ban dauko muku ba a dakin ku wan can gidan zamu koma”.

Gaba daya se yaron ya kasa magana ya tsaya yana kallona, a sanyaye ya saki hannuna ya juya ya fita daidai sanda Itama Aman ta shigo ina jinsa yace mata suje waje na raka su da ido har suka fice daga gidan.

Rayuwa kenan, dan Adam yana tafe besan abinda ze same shi a mintunan da suke gabansa ba, dazu da safe na tashi da yaqinin gyaruwar Al’amura a tsakanina da Bashir, ga labarin abin farin cikin daya same mu bansan mummunar qaddara na tafe tana shirin shafe duk wani farin ciki da nake shiryawa ba.

Shafa cikina nayi, Allah sarki shi kuma tasa qaddarar kenan baze tashi a tsakanin iyayensa ba.

Da taimakon yaran kafin sallar Magriba mun shirya gidan nan tsaf yayin da muka yiwa gidan Bashir qat dan kaida fata Anty ta kafe sena dauke duk abinda yake nawa ne a cikin gidan nan haka kuwa akayi yara suka ringa jidar kaya qananan se murna suke wai mun chanza gida.

kayan Kitchen dina tsaf Gas da qaramar Freezer da muke zuba nama kadai aka bari dan sune nasa babbar me qofa Biyu Yaya Muslim ne ya bani ita da suka tashi daga gidan su na Lagos ya koma Rivers, haka kayan amfani ko ko cokaci Anty bata bari ba harda su spices seda ta tattare.

Haka palour Kujeru da Da Tv se Dining kadai ya tsira dasu sefa gadon dakinsa dan na dakina ma da kudina na siya, wanda ya saka mun shi na cire na sakawa Farida da Amna a dakinsu dan haka masu daurin Gado na gama hada sabon Anty tasa suka hau kwanto nawa tace ko baze hadu a yau ha su kwance a ajiye gobe su dawo su hada.

Har bayan Isha muna jigilar kaya daga tsohon gida zuwa sabo, mungama tattaro komai wanda ze saku a lokacin muka saka ragowar muka barwa gobe idan Allah ya kaimu se a qarasa.

Na fito raka Yaya Abubakar ze tafi masaukinsa daidai lokacin Bashir ya dawo, tundaga waje ya fahimci aika aikar da akayiwa gidan dan ga winduna nan hanhai babu labule ana hango ciki, a sukwane ya shiga gidan, kai tsaye dakin yaran ya leqa ya kuwa yi sa’a se katakwayen gadajen su ya tarar dan mun kwashe katifun saboda bacci a zuwan gobe suma se a dakko su.

Cikin tsananin Bala’i kamar zeyi aman wuta ya tunkaro inda muke
“Ke kadai nace ki tafi bance ki daukar mun yaro ko daya ba” ya fada yana kallona.

Seda na watsa masa wani banzan kallo kafin nace
“Wannan ne kuma kayi kadan Wallahi Bashir, saki dai na saku kuma kamar yanda kace na barmaka gida kafin gobe gashi nan ka gani Allah be hanani inda zan zauna ba amma maganar yara baka isa in bar maka yarana a hannunka ba”.

Sosai rigima ta barke tsakanin mu shi yana rantsuwar sena bashi yaransa ni ma ina ta bazan bayar ba, Yaya Abubakar ne ya katse mu da cewa “Ya ishe ku haka, wane irin shirme ne zaku zo kuna neman tarawa kanku mutane a titi ga yara duk suna kallon ku akan abinda be wuce ku zauna ku sasanta ba.
Ki shiga Gida Ma’u zamuyi magana”

Sena juya ina cewa “ka gaya masa bazan bayar ba idan ya takura kuma seadi kotu ta raba mu” nayi shige wata gida.

A waje kuwa Asma’u na wuce kafin ma Abubakar ya fara magana Bashir din ya katse shi da cewa “Ka gani cikin lallama ka gaya mata ta bani yarana dan wallahi bazan bar mata su ba ballantana ta koya musu dabi’ar raini da kafiya irin tata”.

Seda Abubakar ya qare masa kallo kafin yaja qwafa, ba qaramin danne zuciyarsa yayi ba yace “Naji, zata baka amma kayi haquri kabarsu yau. Nayi maka Alqawari gobe za’a baka yayan ka”.

Shiru Bashir yayi kamar me tunani se yace “Shikenan, Amma wallahi goben idan ba’a bani ba se anyi tashin hankali”

“Babu da wanda zakayi tashin hankali Bashir dan babu wanda yake da lokacin ka, kuma kayi a hankali idan ba haka ba seka rufta kanka a inda duk ihun ka bazaka iya fitowa ba” yana gama fada masa haka ya shige motarsa ya bar Bashir da cizon yatsa.

BASHIR
Ko kusa beyi nadamar abinda ya aikata ba dan a ganinsa yayi irin abin nan na ya tauna tsakuwa dan Aya taji tsoro. A tunaninsa dole Asma’u zata bishi ta roqe shi ya maida ita dakinta, shi kuma ya qudurce se ya gama wanata son ransa tukunna ta gane muhimmancin sa sannan se ya mayar da ita. A lokacin yasan ta biyu ta yanda ko kara ya ajiye mata bazata tsallake ba.

Be damu da kwashe kayan ma da tayi ba, sema guri daya samu a palour ya dora kafa daya kan daya, a cikin kudin da yayi niyyar biya musu umara shida itan ya yi order sabon gadon da za’a saka a dakin da ta cire nata da kuma labulaye kai kujerun ma chanza su ze kawai idan yaso kayan Kitchen in Amirah tazo se ta siyo da kanta tunda shi be san abinda ake buqata ba.

Koda ya shiga dakinsa ma yaga kaya a watse be wani damu ba yasan duk cikin haushin sakin ne yasa tayi haka, se kawai ya tattare ya watsa su kan gado yayi shigewarsa Toilet yayi wanka kafin yayi shirin bacci ya zauna akan kujera da wayarsa a hannu.

Cikin sa da yayi qara ne ya tuna masa da yau fa be ci komai ba, se ya miqe ya fito palour kai tsaye ya wuce gurin Dining sedai kafin ma ya qarasa ya hango shi wayam daga teburi se kujeru, yar Show gilas din kwanukan da ta qawata gurin ma an dauke bare yasa ran samun wani guntun abinci.

Dolensa ya sake fita ya siyo abincin a waje a ransa yana cewa “Dole yarinyar nan ta dawo a satin nan dan bazan iya sintirin zuwa siyen abinci ba, yana gama ci ya ahige daki yayi kwanciyarsa abinsa.

ASMA’U
Qarfe 11 na dare ina zaune akan abin sallah tun bayan da nayi sallar Isha ban tashi ba, gaba daya hankali na yayi nisa da inda nake na yi nutso a cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru dani tun daga haduwata da Bashir har zuwa yau daya yanke alaqar da take tsakanin mu.

Tiryen tiryen komai ya ringa dawo mun lokutan da suka kasan ce masu dadi a cikin rayuwar mu da wadanda suke aka sin haka, haduwar mu ta farko da Bashir wadda har muka qulla soyayya a tsakanin mu nake tunawa.

ASMA’U ABDULLAHI TUKUR shine cikakken sunana. Baffan mu Alhaji Abdullahi haifaffen Kumo ne ta Jahar Gombe.

Yana da matan aure guda hudu Hajia Babba da Hajia Umma rana daya aka saka musu lalle se Hajia Anjim kafin ya auro Goggon mu Maryam daga qarshe.

Ita Goggon mu yar Asalin Numan ce kuma Babanta shine limamin garin a lokacin. A yanda aka gaya mana asali ba Baffan mu Goggon zata aura ba, Baffa Sama’ila Amininsa ne saurayinta wanda har an saka musu rana cikin tsautsayi a ranar da za’a daura auran ya gamu da mummunan hatsari akan hanyar su ta zuwa Numan daga Yola wanda yayi sanadiyyar tabuwar lakar bayansa dalilin da yake kwance kenan har yau yana jinya.

A lokacin su Baffan mu sun riga su isa garin, bayan da aka samu wannan mummunan labari hankalin kowa ya tashi har aka watse daga taron daurin aure seda Baffa Sama’ila ya bar wasiyyar akan Baffan mu ya auri Maryam dan beyi zaton ze tashi ba, haka kuwa akayi se kawai gani sauran matansa sukayi yazo da Maryam da suka je bikin Amininsa a matsayin kishiyarsu babu kuma wata jayayya ko tashin hankali suka karbeta tamkar yar uwa.

Zaman gidan mu zama ne me tsafta tsakanin matan guda hudu wanda suke kishi gurin kyautatawa mijinsu da qoqarin ganin ko wacce ta zama ta gaban go shi bata hanyar cutar da yar uwarta ko tashin hankali ba.

Allah ya azurta Alhaji Abdullahi ta kowanne bangare domin ya masa arziqin Dukiya, mata da kuma Yaya saboda seda ya haifi Yara 42 inda biyu suka mutu tun kafin a haife ni yanzu haka mu 40 cif muna raye Maza 24 mata 16.
Mu 8 ne a dakin mu, maza uku mata biyar.

Zan iya cewa kusan nice mafi soyuwar ya a gurin mahaifina kodan ina da sunan mahaifiyar sane amma dai kowa ya shaida nidin yar gata ce ta gaske, Baffan mu yayi matuqar qoqari gurin bamu tarbiyya tareda hada kanmu dan bamu san wani abu wai shi yan ubanci a gidan mu ba mun tashi tamkar tsintsiya baka taba banbance yan wannan daki dan kowa inda yake so yake warkajamin sa.

Dukda kasancewar Baffa beyi boko ba amma yayansa ya bamu damar yin ilimi iya yanda kaso kuma mata da mazan mu, baya tsawwalawa, dukda anayiwa mata auran wuri a lokacin sam shi babu ruwansa idan yayyen mu mata sun gama secondary school yana basu zabin aure ko makaranta wanda kika dauka shi zakiyi dan

Please Login or Register in order to submit comment