Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

se shatato kwalla take hannu ta akan cikinta dayan kuma ta rufe baki, yanda take matsa cikin ya tabbatar masa da tana jin zafi ya saka shi cewa ta tashi ta biyo shi yayi gaba tana binsa a baya a dudduqe, seda ya kashe fitilun ya kulle qofa kafin suka shiga motarsa, wallahi badan yana tsoron kar wani abun ya sameta Allah ya kamashi ba da barinta zeyi jikinta ya gaya mata. Haka ya sake fita daya saura suka nufi Asibiti shi yana jera tsaki ita tana kuka qasa qasa.

Basu bata lokaci ba dan an tabbatar musu babu komai motsawa gurin yayi amma dai ta kiyaye irin hakan, Allurar kashe zugi suka mata kafin suka kamo hanya kamar abokanan gaba har suka zo gida yana tsayawa ta wuce sedai tuna bata da key ya sakata rakubewa tana satar kallonsa. Har ze shige part din Asma’u shima ya tuna da bata dakko key dinba dan haka ya qarasa ya bude mata qofar be amsa Nagode din da take ce masa ba ya wuce abinsa.

Kitchen ya fara tsaya wa ya dauki Yoghurt me sanyi kafin ya hau saman, beyi zaton samun Ma’u a dakin ba amma yana budewa qamshin Airfreshner dana turarukan baccinta suka masa sallama besan sanda ya fara sauke aji yar zuciya ba dan har ga Allah qanshin sun san yaya masa rai.

Akan dan teburin da yake dakin ya ajiye yoghurt din da tarkacen keys dinsa da wayoyi kafin ya cire rigar sa ya shiga toilet. Wanka yayo da alwala, bayan ya fito ya shafa mai sama sama ya zura jallabiyya Ya fesa turare lokacin har biyu ta gota kafin ya kalli Gabas ya tada sallah.

Raka’a biyu yayi a sujjadarsa ta qarshe ya dade yana yiwa Allah kirari kafin ya dora da istigfari tareda neman zabin Allah akan dukkan al’amuransa ya rufe da salatin Annabi kafin yayi tahiya ya sallame. Ya dan jima hana lazimin La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin har seda bacci ya fara fuzgarsa sannan ya tashi yana jin nutsuwa na saukar masa. Seda ya sha yoghurt din dan yunwa yake ji sannan ya kwanta ya juyawa Ma’u da bata san da dawowarsa ba baya.

A kusan tare suka farka da Asuba, ya cuna baki Gabas ta cuna Yamma kafin ya miqe tayi wuf ta shige toilet tayo fitsari tareda chanza pad ta koma ta kwanta kafin ma ya gama shirin Masallaci bacci ya sake kwasheta.

Da safe ma haka suka tashi, ya hada fuska tam yana zaune a palour yana kallon labarai ita kuma tana ta kaimawon hada masa breakfast, bayan ta gama ta masa magana daga “Toh” be sake ce mata komai ba kuma be motsa ba se itama ta share kawai dan dai fushin ai ba nata bane, idan kuma zancen komawa ne ai indai yar gaskiya za’abi batayi laifi ba. Dibar Abincinta tayi ta wuce dakinta taci, bayan ta gama ta fito sukayi kici bus ze shiga zata fito ta rabe masa ya wuce kafin ta fito.

Abincin ta fara dubawa taga yaci da yawa ma tayi dariya a fili tace “na zata shima cikin fushi kake dashi ai” ta shiga tattarewa ta sauka qasa da kayan. Tana cikin dauraye kwanukan taji motsinsa ya bude qofa, ta window ta ga fitarsa tana ganin yanda yai diri diri a tsakanin parts din me kuma ya tuna ya wuce ya kunna motarsa ya bar gidan.

Ragowan Abincin ta juye ta yafa mayafinta ta kaiwa Amirah. Tana zaune a palour tun jiyan a nan ta kwana sallah ma duk anan tayi kuma har lokacin bata kwashe kwanukan jiya ba ga plate din data sake cik tuwo bayan sun dawo shika a bushe.

Ba qaramar kunya ce ta kamata ba ganin Asma’u, duk se taji ta muzanta saboda yanda Asma’un ta sheqa wanka da wata Atamfa doguwar riga se qanshi take ita kuwa tama zaune cikin kwanuka da kayan jiya a jikinta seta hau soshe soshen tana gaida Asma’u da tayi mirsisi kamar ma bata ga komai ba.

Kayan ta dire mata tana cewa ta juye ta bata kwanukan kafin ta duqa ta kwashe na jiyan a ranta tana cewa “Na san darajarsu bari na kwashe abuna” bata ko saurari Amiran dake cewa ta barsu yanzu zata tashi ta wanke ba, ganin haka yasa ta tashi ta shiga kitchen ta juye ta daurayo kwanon da zallar ruwa ta kawo mata. Karba Ma’u tayi tana cewa “se ki nemi abinda zaki ci da rana tunda naga kin warware” tayi waje abinta.

Wannan abincin taci tayi nak sannan ta tashi ta dan tattare gurin ta shiga dakin ta tana qarewa Hadadden Gadonta da aka rushe bedside din kallo. Ita dai yan sunan nan sun cuceta wallahi dan dai bata hango ranar da Yaya ze sake mata wasu kayan ba yanzu ma ta samu ya haqura ya sakko daga fushin nan ma kafin wani zance ya biyo baya.

Wunin ranar zir Bashir a waje yayi shi, itama Ma’u bata zauna ba ta fita harhado sauran kayayyakin da take buqata da ba’a samu acan dan haka se yamma lis ta dawo bayan ta biya ta dakko yara. Koda suka dawo ma basu zauna ba kayansu suka hade tsaf dan gobe Sunday tanason suje su wanke kai da kitso Monday se Lagos.

Sanda Bashir ya dawo yaran sun kwanta Amnah ce kadai idonta biyu tana karatu dan da sun koma sati biyu zasu fara SSCE, da niyya tijara idan basu dawo ba ya shigo gidan se Allah ya ceci Ma’u tana kitchen ta jiyo Amna na gaishe shi yana tambayarta yaushe suka dawo tace dazu. Kitchen din ya leqa suna hada ido ya wani qara shan kunu tayi masa sannu da zuwa ya daga kai ya fice ya haye sama qasan ransa yaji dadin ganinta.

Seda suka zo kwanciya ta gama duk hidimominta taji muryarsa yana cewa “akwai abinda kuke buqata ne?” Seta dakata daga saka hular da takeyi ta kalle shi yana zaune a bakin gadon yanda yayi maganar yana fuskarta wani guri daban, kallo daya zaka masa kasan akwai abinda yake damunsa gaba daya yayi laushi.

Kusa dashi ta koma ta zauna, seda ta shagwabe fuska sosai ta tara kwallar qarya a idonta kafin ta riqo hannunsa, waiwayowa yayi seda ta tabbatar ta saka kwayar idon ta cikin tasa yanda baze iya kaucewa ba sannan tafara magana tana cewa

“Haba Baban Ali Haba Na Ma’u wai fushin ne haryanzu ina kake so na saka kaina naga haske bana ganin Murmushin ka? na tuba nabi Allah kayi haquri indai batun Tafiya a motane na yarda gobe muyi asubanci mu tafi idan kana tare damu nasan babu abinda ze same mu se ikon Allah”.

Duk yanda yaso ya janye ya kasa dan riqon da tayi masa da kaifin idonta yayi tasiri a jikinsa, daman dauriya ce kawai amma yana buqatar ta, yana buqatar me kwantar masa da hankali kuma Ma’u ita kadaice duk damuwar daya shiga a duniya take iya magance masa ita har in yana tare da ita tana saka shi ya manta komai sedai daga baya ya tuna shi yasa duk sanda matsala take tsakaninsa da ita yake ji kamar ya zauce dan babu me masa magani.

Fuzgota yayi jikinsa ya mata ruqo me tsauri tana jin yanda zuciyar sa take bugawa jikinsa har wani rawa rawa yake, cikin dasashshiyar murya yace “Badake bake fushi ba Ma’una, me yasa, meyasa ita bazata ji magana ta ba me yasa koda yaushe take sakani ciwon kai”.

Seda Ma’u ta murguda baki ta harareshi dukda be gani ba a zuciyar ta tace “taya zan sanin maka ba kai ka kwasowa kanka ba” a fili kuwa seta qara riqeshi cikin kwantar da murya tace “Kayi haquri” . Yanda ta fadi haqurin yasa yaji tamkar ta watsa masa ruwan sanyi a zuciyar sa, kissing goshi ta yayi kafin yace “Na haqura Yar Aljanna”.

Cikin tsananin farin ciki ta dago ta kalli kyakykywar fuskarsa tace “To Na kawo maka abinci, yau duk nasan baka ci komai ba ga fuskar ka nan ta nuna”.

“Muje ki bani” ya fada yana daga ta gaba daya, seda suka sauka har qasa sannan ya ajiyeta Amnah da ta gama hada littattafanta zata shiga daki tayi saurin saka littafin a fuska tana tafiya da baya da baya. Rankwashi ya kai mata da wasa cikin harshen turanci wanda dashi yakewa yaran magan yace “gidan ku me kike yi anan baki kwanta ba haryanzu”

Dariya tayi ta dan janye littafin tace “Abbi karatu Saura two Weeks mu fara WAEC fa”

“Ok maza je ki kwanta karki manta kiyi Addu’a” ya fada yana zama akan kujera, seta juya tana cewa “Good night Abbi”
“Good night Amna” ya fada daidai sanda Asma’u ta fito da plate din daya zubo masa dambun couscous se kunun aya a Jug.

“Good nigh Mami” Amna ta sake fada, seda Ma’u ta ajiye kayan akan centre table kafin tace “Good night Amnan Abbi”.

Dariya Bashir yayi yana cewa “fadi ki qara kam Amnan Abbi” murmushi kawai tayi, a ranta tana jin dadi yanda Bashir ya dauki qanwar tata tamkar yar da ya haifa a cikinsa dan gani take kamar yana mantawa ma ba yarsa bace, tunda riqon Amna ya dawo hannunta be taba sauya wa daga yanda ya karbi yarinyar ba ko a fuska, komai ya tashi yiwa yaran itace farko a matsayin first born dinsa. Cikin dadin rai yaci abincinsa ta tattara suka wuce Aza rum.
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 24


Gombe
Bayan Naziru ya kaimu Airport kai tsaye kasuwa ya wuce ya siyi duk abinda Bashir ya gaya masa ya kaiwa Amirah. Tana zaune a palour bayan ta gama kukan ta yai sallama ta amsa fuska a kumbure be kulata ba ya shiga kwaso kayan da taimakon Almajiran daya kira suka shigar mata da su Kitchen.

Har ya gama bata ko sake kallonsa ba dan haushin sa takeji tasan shi yake qara zuga Bashir din ma akan komai, seda ya kai qofa ta tuna da zancen waya seta miqe da sauri tabi bayansa tana kwalla masa kira ya kuwa shareta kamar beji ba seda yaje gurin mota tana biye dashi.

“Meye kike bina kamar naci miki Bashi” ya fada yana harararta, inda haka kawai ne seta rama amma tunda abu take nema seta karyar da kai tana cewa “Dan Allah Yaya Naziru waya zaka siyo mun da layi”.

Seda ya harareta kafin yace “waya? Me zakiyi da waya ina taki?”

“An sace” ta bashi amsa kai tsaye.
“Toh ai shikenan gara da aka sace, kuma ni sa’an kine ko dan aikenki da zan siyo miki waya ke baki da qafa ko baki san inda ake siyarwa ba” Nazirun ya fada. Seta marairai ce tana cewa

“Dan Allah ka taimaka mun Yaya”. Kwafa yayi kafin yace

“Kawo kudin toh badan halin ki ba”

“Nagode” ta fada kafin ta qirgo dubu biyar da dari biyar ta bashi, ya karba ya irga ya kalleta yace

“Saboda a gidan ku ake qera wa ko waye ze siyar miki da wayar dubu biyar”

“Yaya Tecno fa me keypad ai bata wuce haka ba”

“To se kije ki siyo kin tsaya kina batamun lokaci” ya fada yana miqa mata kudin, setayi saurin dakatar dashi tana cewa “yi haquri dan Allah nawa ce se na ciki”

“Dubu goma ce sannan ki bada dubu biyu kudin mai tunda babu siyo miki waya a lissafin da aka mun. Ba yanda ta iya tana ji tana gani ta zare dubu goma sha biyu da dari biyar ta bashi ya tafi, idan da abun nata da mutunchi tasan a kyauta ma siyo mata zeyi amma yanda tasan yana jin haushinta ma tayi mamakin da yayi saurin karbar aiken.

Ciki ta koma ta tafasa ruwan zafi ta dakko kayan Tea a siyayyar da ya yo mata harda bread ta zauna ta karya, tana zaune a gurin ya dawo ya miqa mata leda da kwalin wayar a ciki da layi harda katin dubu daya ta karba tayi godiya harya juya ta kuma tsaida shi tana cewa

“Dan girman Allah yaya ka roqar mun Yaya Bashir ya bari naje na ga Iman kaga fa tun da aka kaita Asibiti banje ba”.

Wani banzan kallo ya mata kafin yace “karki rainamun hankali dan kin ga na biye miki malama, dacan baki san tana Asibitin ba se yau? To bari kiji ya gayamun sharadin daya gindaya miki kuma wallahi na baza CIDs a layin nan ki sake ki fita dan nasan ba tunani ne dake ba tsaf za’a iya zugaki ace ki fita ai be sani ba kinga kuwa auranki ya mutu” yana gama fada ya juya ya fice yabar Amirah da baqin ciki ya cika mata ciki kamar tayi bindiga.

Dakinta ta shiga tana duba wani littafi da ta kwafe numbobinta a lokacin Ummi nata mata iskanci wai rashin aikin yi me sa hauka gashi yanzu ze mata rana. A garin neman littafin ta samo tsohon layin ta da ba sosai take amfani dashi ba, da murna ta saka tana Addu’a Allah yasa basu kulle shi ba ai kuwa tana gwada kira ya tafi amma babu kati seta loda katindaya siyo mata ranta fes ta samu numbobin harma da wasu masu amfani da bata dasu a wancan layin.

Ummi ta kira ta hadata da Addah, tiryantiryan Addah ta bata labarin yanda akayi anje an siyar da gida miliyan uku da dubu dari shida, an biya me Gwal kudinta Miliyan Daya da dubu dari tawkas da Arba’in dan seda ta kawo resit din sarqar aka je da warin dan kunne gurin masu gwal suka fadi nawa gram din sa yake sannan aka buga lissafi a gurin aka siyar da warin ma aka bawa Addah kudin.

Ragowar masu bashi ma tas seda Alhaji ya cire wa kowa aka biya dan abinda yai saura kuma ya riqe a hannun sa yace ze saka mata a kasuwa, ta qarasa tana cewa “Nayi baqin ciki amma dai hankali na ya kwanta da yanzu qila ina firzin, yanzu idan an kwana biyu kuma se muga yanda za’ayi ki maida abubuwan da aka lalata miki yanzu dai ki kwantar da kai ku shirya da Bashir dan a jikinsa zaki samu ni kuma zan nemo mana hanyar da zamu bi ta qarqashin qasa a samu komai daidai ba matsala”.

Sallama sukayi Addah na gaya mata kartazo gida yanzu ta bari se an kwana biyu tukunna se a sannan ta gaya mata yanda sukayi da Bashir.

“Ki rabu dashi, lambo zamu musu dagashi har uban naki zan nemo mana inda za’a tasar mana kansu dan shi kansa Alhajin shi ya siyi gidan sena san yanda na dawo da abuna amma yanzu muyi luf tukunna, zan turo miki Ummi seta taya ki zama. Waccen Magen yar kuma gara ki barta a Asibitin ma in aka dawo miki da ita qarin wahala ne” .
Da haka sukayi sallama ta dan ji dama dama tunda an kashe waccen babbar wutar.

LAGOS

Kusan kwanan zaune Bashir yayi dan farkawata biyu ina ganinsa ido biyu yana faman tunanin da ban san koh na menene ba, yo ina dalili haka kawai ze saka kansa a damuwa akan abinda yasan bame yuwuwa bane ba ma. Ko masallaci basu fita ba a gida sukayi sallah yana idarwa kuma ya koma ya kwanta, ganin haka yasa na fita na fara hadawa yara abin kari su kuma suna shirin makaranta.

Indomie na soya musu dan har na dakko doya Abdallah yace bazasu ci ba sauran ma suka amsa Aliyu daya baya cin soyayyar Indomin na soya masa kwai ya hada da Bread suka karya. Har suka gama ba Bashir ba labarin sa, se na miqe na shiga dakin dan in gaya masa sun shirya fa.

Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu biyu na shiga.
“Baban Ali lafiya dai baka shirya ba ga yara can suna jiranka” na fada ina zama a gefensa. Beyi magana ba ya tashi ya shiga Toilet minti kadan ya fito yana goge hannunsa da qaramin Towel, Rigar jikinsa ya cire ya dora Jallabiyya akan dogon wandon sannan ya dauki key da wayar sa ya fita yana cewa “kiyimun kunun gyada da kosai” ya sa kai ya fice.

“Ko ba kunun gyada da qosai” na fada a fili ina hararar qofar daya fita, gadon na shiga gyarawa, babu dattin komai a dakin dan haka na dauke robobin ruwan da muka sha da dare na fita dasu. Seda na jiqa wake wanda daman bayarwa nake da yawa a gyara a surfa mun se a shanya shi ya bushe idan na tashi amfani kawai jiqawa nake na markada. Na debi gyada da farar shinkafa suma na jiqa.

Palour na koma na gyara palour da Dining din tsaf na kunna turaren sannan na shiga wanka. Riga da Zani na saka na Atamfa na kashe dauri jelar kitson da aka mun two step sun zubo kan bayana. Juyi nayi a gaba mudubin nida kaina na burge kaina bare kuma Bashir ya ganni dukda ba cewa zeyi nayi kyau ba amma nasan har ransa ze yaba ai.

Seda na markada gyada da shinkafar na saka danyar citta da kanumfari dan kadan dan kar yayi baqi sannan sake wanke blander na zuba waken na markada shi da attaruhu da Albasa se yar tafarnuwa. Kunun na fara damawa bayan yayi kauri na zuba ruwan lemon tsami yayi fari tas gwanin sha’awa na juye a Flask ragowar kuma na zuba a Wani qaramin flask din da niyyar na kaiwa Anty idan na gama.

Ina ajiye Flask din kunun akan Dining Bashir ya shigo da sallama ciki ciki na amsa ina kallonsa tareda yi masa sannu da zuwa.
“Yanzu zakaci na siya qosan?” Na tambaye shi, se ya girgiza mun kai yana cewa bari nayi wanka tukunna ya shiga daki na bi bayansa.

Seda ya fara shafa mai bayan yayi wankan na fita na dora ma suya na yanka Albasa sannan na shiga buga qullina sosai bayan na saka kwai guda daya saboda ya qarawa qosan laushi, gishiri na saka da daskomiya dan kadan se Albasa dana yanka qanana na shiga suyar qosan, gaba daya kasko biyu da dan kadan nayi dan bashi da yawa, ina kwashe na qarshen na jiyo shi yana kira na sena kashe wutar na juye a Bowl na dakko na fita palour.

Yana zaune a Dining din ya saka Jeans blue da Farar Short sleeve a gabanta an rubuta “HANDSOME” na kalleshi da murmushi nace “handsome indeed”. Murmushin ya mayar mun na ajiye kwanon na jawo Babban Mug na tsiyaya masa kunun na saka Sugar yace na saka masa Madara a raina nace “sarkin son dadi” na gama na tura masa komai gabansa harna zauna na tuna da kunun Anty sena miqe ina cewa
“Bari na kaiwa Anty kunun nan”.

A bakin qofa na miqa mata na juyo duk yanda ta keta magiyar na shiga amma naqi dan nasan in muka zauna qilan se Bashir ya biyo baya. Bayan na koma zama nayi nima na zuba kunun ina juyawa na kalle shi nace “Wai yau hutu ka samu ne bazaka office ba?”

Seda ya cinye qosan bakinsa kafin yace “Eh zamuje fieldwork ne Delta so an banu kwana biyu mu shirya”
“Toh Allah ya taimaka” na fada naja kununa da qosai na fara ci. Ya rigani tashi daga wurin nima ina qarasawa na kwashe komai naje Kitchen na ajiye dan na gaji gaskiya tun asuba idan na huta anjima na wanke su.

Kan Three sitter na kwanta ina cewa “wash na gaji wallahi anya bazan nemi me aiki ba”
Hankalin sa nakan Tv ya ce mun “idan da takura se ki nema din ai amma bame kwana ba”

“Nima ai bana son me kwanan, abinda yasa ma ban damu dame aikin ba kaga ba wuni muke a gidan ba zaman gaba daya weekend ai” na fada ina gyara kwanciya ta yanda zan kalli TV dakyau.

“Hakane” ya fada, se ya juyo yana kallona kuma yace “me kika yanke akan maganar mu?”

Kallon rashin fahimta na masa, ya gane hakan se yace “maganar da mukayi jiya da daddare nake nufi kin gama shawara?”

Na gano me yake nufi se nayi murmushi nace “Wai maganar Iman? To tunanin me zanyi ai tun jiya na gaya maka amsata ko” na fada ina kafe shi da ido kamar yanda yake kallo na shima, se ya sauke numfashi ya dan zamo gaba yana hade hannyensa guri daya yace

“look Ma’u Alfarma zakiyi mun ki karbi yarinyar nan, kinsan uwarta sarai ba wai nutsuwa ce da ita ba bare har ta iya kulawa da wani halayenta duk se a hankali. Yarinyar nan mace ce karta tashi taga abinda takeyi ta dauka daidai ne, bana so ta tashi daban da yan uwanta ina so ta samu kula da tarbiyya irin daya....”

“Anzo dai dai gurin” na raya a raina ina sheqa murmushi, tashi nayi dakyau na zauna kafin nace
“Wai tsaya Baban Ali, da baka yarda da tarbiyyar ta ba ka aureta har ka hada zuri’a da ita”, se ya watsa hannu ya koma cikin kujerar sosai kafin ya juyar da kai gefe daya yace “ba haka nake nufi ba, beside Amirah ai tarbiyyar kice itama kawai.....”

“To ai ka gama magana, tarbiyya tace kaga zata koyar da ita harda qari ma ko, sannan idan ma wani hali ne da ita na daban da baka so yarinyar ka ta dauka ai aikin gama ya gama tunda har ta dauki cikinta jininsu ya gauraya ta haifeta sannan tasha Nononta duk wani halayya kuma ai ta gama diba sedai ai fatan na kirkin su rinjayi na banza ko?”

Zancen gaskiya ka bar mata yarta, nasan ma duk wannan maganar da kake bata sani ba dan bazata yarda ba itama. Babu uwar da tana ji tana gani za’a rabata da yarta hakanan ba wata gagarumar jinya ba ko mutuwa kai ko mahaukata se anyi da gaske ake iya raba su da Yayan su bare ita yar tilo haihuwar farko ko nicefa bazan baka ba.

Idan Dan rashin lafiyar ta ne Allah ya hore maka ai ka barta a Asibiti suyi ta kula da ita har zuwa sanda suke ganin tayi kwarin da zata juri ko wanne kalar yana yi amma ba maganar ka bani ita, nawa ma idan za’a ragi wasu aciki bayarwa zanyi”.

Shiru yai yana kallona harna dasa aya ina sake turo dankwalina gaban goshi, ajiyar zuciya yayi kafin yace “yanzu dai bazaki karba ba kenan?”

“Allah me iko, da Hausa fa nayi maka jawabi dalla dallah amma kake sake tambaya ta kuma?”

“Eh saboda kinsan ni bana son dogon surutu, amsa daya nake buqata Eh ko Aa kawai” ya fada a dan hasale alamar ya fara barin cool site dinsa ze koma Bashir dinsa na gaskiya, se kuwa na tura baki gaba nace “Toh a taqaice dai bazan karba ba”.

“Shikenan, amma ina da ikon da zan kawota cikin gidan nan ko tunda gida nane” ya fada yana miqewa, nima sena miqe tsaye jin wani qundumemen rainin wayo,

“Tabbas gidanka ne ka isa ka dakko kowa nene ka kawo shi ciki, zaka iya kawo ta tunda itama gidan ubanta ne ai se ka hado dame kular maka da ita, ko kuma kai zaka aje aikin ka ka zauna rainon duk ba matsala ta bace ni” na fada ina dauke kai gefe, ina jin yanda yake qare mun kallo kafin yaja tsaki tareda sakin kwafa ya shige daki na rakashi da harara ina cewa a fili

“Wallahi ba tsaki ba kome zakayi sedai kayi, bazan karbi raino ba, rainon ma yar Amirah yarinyar da duk zamana da ita idan dana ze tsaga guri saboda kuka bazata dauke shi ba balle aje ga tsarkin kashi ko wanka shine ni ga jaka yanzu ta haifa za’a dakko a kawo mun in riqe mata toh ko daga turu aka kuntota qarewar rashin nutsuwa sedai duk handa za’ayi ayi”. Tsaf nasan yaji ni dan da qarfi nayi saboda yajin, na koma kan kujera na zauna, se kuma na miqe na dakko wayata na dokawa Dadar su kira dan fa karma inji wata magana daga baya.

Ringing biyu ta dauki wayar, a taqaice na gaisheta ta amsa kafin na shiga koro mata jawabin yanda mukayi da Bashir, na rufe da cewa “Iya gaskiya ta na fada

Please Login or Register in order to submit comment