Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

10/5/23, 9:15 AM - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more.
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: MIJIN TACE

( Love and romantic fictional story)

PG 1_2

Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda fari kal sai shining yake. Dinkin shaddan zariya ne wato rigar ta wuce masa guiwarsa da kadan, ta bala'in yimasa kyau da fidda kyakkayawar farin fatarsa mai shan hutu yadda yakamata. Kasancewar yau ranar juma'ah ne rike yake da jakar aikinsa da kuma dadduma fari mai kyau sai tashin kamshi yake mai sanyi da dadin shaka. Dogo ne shi din mai faffadar chest, yanada jiki dan madaidaici ba mai yawa ba gwanin sha'awa. Fuskarsa dogo ne mai dauke da bakin gashin gemu wadda ya hadu da sajensa. Ba murmushi yakeba amma bazai hana mutum ganin twin dimple dinsa ba. Idanunsa farare sosai eyeballs dinsa kuma brown ne. Gashin kansa baki wuluk dukda akwai hula akansa amma bai hana gashin Kannasa bayyana ta kasan keyarsa ba, akwance yake luf mai laushi dashi.

Saukowa yake ahankali daga saman bene cikin tafiyarsa ta kasaita wadda yariga yazame masa jiki. Kana kallonsa kaga miskilin mutum mai ji da kudi da duk abinda mutum mai jida jini ajiki zaiyi takama dashi. Babban falon kasa yasauko anan yasamu umminsa tana zaune tanacin tuffa. Zama yayi kusa da ita amma baice komai ba. Itama kallonsa tayi ta dauke kai tacigaba da cin apple dinta. " ummi good morning" idan ba ummi dake kusa dashi ba babu wadda ya isa yace yaji abinda yafada saidai in alajani ne shidin. " morning Aryan " tafada itama cikin sakin fuska. Itakam tunda Allah yayi ta bata taba ganin miskilin mutum irin Aryan ba ko abbansa albarka a wannan gefen dan shi halin abbansa ya dauka. Sun dau kusan five minutes babu abinda yace mata itama kuma batacemasa kala ba. Can dai taga inhar ba itace tai masa magana ba babu abinda zai kara hadasu sai dai ya kissing goshinta yayi tafiyarsa. " Aryan breakfast na dinning, ko yau ma bazakaci ba"? Ta tambayesa tana tsaresa da idanunta kamar bazai ce komai ba amma daya kalli fuskar ummin saiyace" OK" ya yashi kamar wadda kwai ya fashewa aciki, Shifa yariga ya koya wa body system dinsa rashin karyawa da safe sai dai yasha coffee amma ummi takasa gane hakan. Zama yayi akan dinning din ya faki idon ummi ya hada coffee kawai ya dau slice din bread guda daya yaci. Bata cemasa uffam ba as long as dai yasa wani abun acikinsa. Yana gama ci kamar kullum yazo ya sumbaci goshinta sannan ya dau jakarsa ya fice. Wurin motocinsa ya nufa ya dau motarsa mai kirar Bugatti horn daya yaiwa maigadi da Sauri ya wangale masa gate ya fice.

*******
"Mama dan Allah kiyi haquri wlh bazan kara ba" wata yar budurwa nagani tsungune tana rokar wata mata wadda babu kwayar imani a idonta sai huci take kamar wata zaki. " shegiya kawai dama abinda kike zuwa makarantar kiyi kenan kullum saikin dade ubanwa kika bari zai miki abinci kidawo kici sannu yar shugaban kasa" yarinyar dai batace komai sai kuka take dan ko tasha na jaki ahannun wannan matar. Wata budurwa ce ta shigo tana wani rangwada kamar taliya gashi ita ba auki ba" mama wlh kece ma kikabar tar hartake zuwa wani makaranta shegiya mai kama da aljanu, wlh daddy ma yanada laifi sai wani rawar jiki yake akanta kai kace itakadai ya haifa" " ke Nuwaira ki saurare ni kiji, daga yau saiyau kika kara bari biyu tamiki awaje sainaci uwar uwaki wadda ke kwance akasa, tashi ki bacemin anan yar iska kawai"mama tafada tana hararar ta. Sum sum Nuwaira ta mike tana tafiya har ta shige dan dakinta kamar ba 'yar mai gidan ba. Kan gado ta fada tana kuka irin wannan qaddarar rayuwartata, ace marainiya kuma batada gata duk da tanada uba? Lallai uwa rahama ce. Kusan minti goma kafin ta mike tawuce bathroom danyin wanka tariga tasan tayi lattin zuwa makaranta dan haka yau tama fasa bazata je ba kasancewar yau Friday kuma short day ne. Shiri tayi cikin wata doguwqr riga ja ya matuqar fidda mala malanta, Allah yawa Nuwaira baiwar shape ga kyau komai yaji zam zam. Gashinta takama ta tufke da ribon sannan ta kitsa jelar tabarshi yana yawo agadon bayanta. So dayawa mama takan aske mata gashin kanta amma kuma maishi maishine baya daukar lokaci yake dawowa. Bata fito daga dakin ba saida ta tabbatar mama ta fita itada Maimoon(wannan budurwar ta dazu). Abinci tadora akan gas sannan tacigaba da gyaran gida ta sa kamshi tako ina. Ba ita ta gama aiki ba sai wuraren karfe sha daya. Dakinta ta koma ta kwanta babu bata lokaci bacci yadauketa.

********
Tunda ya shiga office dinsa babu abinda yayi, yau jinsa yake kamar bashiba, kwata kwata yakasa gane kansa tunda yatafi gidan anty Aisha(kanwar Abba), tunda lubna ta masa wannan karuwancin nata data saba bai kwana cikin koshin lafiya ba. Aryan mutum ne mai tsananin sha'awa amma hakan baisa yafada ga hangar banza ba. Shima karankansa yasan aure yake buqata amma baisan meyasa babu macen da tai masa har yanzu ba. Shi gani yake kamar ma ai rainin hankali ne da kuma zub da girma yaje wurin mace yace mata yanasonta. Mata dayawa suna kawo masa hari, dana kwaran dana banza amma duk cikinsu babu wacce tayi mai. Sam baya kaunar zuwa gidan anty Aisha saboda karuwar yarta lubna. Kuma ahaka wai takeso ya auri yarta da wannan mummunan dabi'ar kuma ya tabbata an dade da maida lubna cikakkiyar mace tun kafin tayi aure(wa iya zubillah). Haka yaita juyi akan kujerarsa yana sake sake azuciyarsa har lokacin sallan juma'a yayi ya wuce masallaci.

*****
Nuwaira abirkice ta tashi tana rarraba idanu kamar an kama kwarto adaki ,jin horn din mama. Karamin wayarta ta duba taga karfe biyu harda kwata" Alhamdulillah Allah yasa na gama abincin da irin wulakancin dazan sha Allah kadai yasani" tashi tayi ta wuce bayi tai alwala sannan tazo ta tada sallah. Tana cikin sallah Maimoon tashigo dakin tana wani yatsina fuska kamar an jefota cikin kashi. Ganin Nuwaira na sallah yasata sakin tsaki dan ita ba sallan ne agabanta ba, zama tayi akan dan karamin gadon dake dakin tana jiranta ta idar da sallah. Bayan ta idar ta juyo ta kalli maimoon dake dannan wayarta tace" ya moon kundawo"? Harara moon din ta watsa mata tace inda ban dawo ba zaki ganni munafuka kawai. Babu abinda Nuwaira takara fadi dan inda sabo tariga ta saba da irin wulakancin da ake mata agidan, daddy ne kadai gatanta shima din saiyana gida yanzu kuma bayanan yayi tafiya baya kasar. Moon tace" inkin gama tunanin banzan naki sai kije ki gyara kajin da muka siyo nida mama kuma ki tabbata kin gama da wuri dan yau Daddy zai dawo. Da sauri Nuwaira ta kalli moon tace " ya moon da gaske"?harara ta gallara mata tace" a'a da wasa, noor kifita idona wlh, zancin uwarki tom" bakinta taja tayi shuru amma cikin zuciyarta sam batasaon zagin mahaifiyarta da sukeyi, tariga fa tamutu to mai kuma tamusu. Haka dai ta mike ta dan gyara dakinnata sannan ta wuce kitchen. Kaji tagani anyanka amma ba'a fige ba sunkai kusan biyar kuma broilers ne, kamar tayi kuka amma kotayi wa zai share mata hawayen. Haka tasa ruwa awuta na fige kajin ta jira yayi zafi sannan tafara fige su. Bayan tagama figewa ta dau wuka ta fara yankawa cikin kwarewa da alama ba yau ta fara yanka kaji batare da wani yasa mata hannu ba. Tana cikin yankawa cikin rashin sa'a wukar ta taba hannunta ihuu tayi" aaaaaaaaaa inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun".......


Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j

MIJIN TACE

PG 3_4

Da sauri Mama tashigo kitchen din jin ihun Nuwaira tace" ke menene kike ihu gamo kikayi? Hannun daya yanke Noor ta nunawa mama tana kuka. Noor batada wiyan kuka ko kadan da dauriya musamman abinda zai taba lafiyar jikinta. Harara mama ta watsa mata sannan tace" toh shikenan sarauniya Nuwaira tashi ki tafi ni zan karasa kinji" gatse taimata amma baiwar Allah bata ganeba, tashi tayi zata tafi mama tajawo jelar gashinta ta kifa mata lafiyayyar mari" au wato tafiyan zakiyi da gaske? Fada miki akai ko mutuwa zakiyi zaki bar wurinnan wlh sai kin karasa shi kuma babu mai taimakonki, ai tunda kika biyewa ubanki kika ki tafiya wurin kanwar uwaki keda wahala kunsa kafar wando daya kenan yar iska kawai"mama tafada tana jan Nuwaira har wurin naman tacigaba da yankawa. Nuwaira ko kuka kawai takeyi tasan babu abinda zatafadawa mama dazai hanata barinta, haka ta cigaba da lallaba yatsan tana pieces din kajin harta gama tana ta kuka, yatsan shima dayasha wahala harya daina zubda jini sai zogi dayake mata. Bayan tasa kajin awuta ta wuce daki tacigaba da rera kukanta.

*******
Bai dawo gida ba sai karfe biyar. Nana kawai yasamu afalo tana danna waya. "Ya Aryan sanny da dawowa" ko kallanta baiyi ba kawai ya daga kai alamar amsawa sannan ya wuce dakin ummi. Tana zaune tana ninke kayan da aka wankemata taji sallamarsa ciki ciki, amsawa tayi tace "babana harka dawo"? Ta tambayeshi cike da kulawa bai amsa ba kai kawai ya daga mata yaddaa yayiwa Nana afalo. Zama yayi kusa da ita yacigaba da tayata ninke kayan babu mai magana acikinsu. Bayansun gama tajuyo ta kalleshi cikeda da damuwa tace" Aryan " dagowa yayi ya kalleta da milky eyes dinsa alamun amsawa " Aryan dan Allah yaushe zakayi aure, girma fa kakeyi ba yaro kake zama ba, Allah ina tsoron ranar da abbanka zai dauki mataki cos he's been warning you, you'll be 33 this year amma Sam ko ajikinka kamar baima dameka ba" Aryan da tunda tafara magana idonsa ke kasa baice komai ba Shifa bai ki ya dauwama ahaka ba indai danya je wurin wata yace yana sonta ne to yayafe. Baice da ita komai ba harta gama magana iska kawai ya furzar daga bakinsa sannan yace" ummi kitayani da addu'a Allah ya zabamin mafi alkahiri kawai" baki galala take kallonsa ita abinnan fa ya fara isarta tace" wlh kana wasa kanaji kana gani Abba zai aura ma Lubna"dummm kirjinsa yaji ta buga Lubna? Yarinyar da bayaso ma yaji ankira sunanta, shi arashin sa'a ne ma ya tarar da ita agida jiya. Baice komai ba kamar yadda ya saba kawai ya mike ya sumbaci mamansa yafita adakin.

Wanene Aryan?

Muhammad Aryan Abdul azees shine ainahin sunansa. Mahaifinsa Alhaji Abdul azeez Muhammad wadda suke kira da Abba babban architect ne mai zaman Kansa wadda ke harka da yan kasan waje. Yanada branches din company dinsa akasashe daban daban harnan gida Nigeria. Su asalinsu yan adamawa ne fulanin asali. Abba su uku ne awurin mahaifinsu Alhaji babba wadda suke kira da baffa. Shine babba sai kaninsu Alhaji jibril sai autarsu Anty Aisha maman lubna. Dukkansu sunyi karatu kuma Alhamdulillah kowa nada rufin asirinsa daidai gwargwado. Abba yayi karatunsa na university a madina. Anan yahadu da ummi wacce asalin yar can ce. Itama karatun takeyi inda take karanta Islamic studies. Sun fara soyayya kamar wasa harta kaiga aure dayake familyn ummi basuda wulakanci kuma sun yarda cewa babu inda aure bayakai mutum dan haka suka yarda suka baiwa Abba aurenta bayan ummi tagama makaranta shikuma Abba alokacin yadawo Nigeria harya dan fara aiki akarkashin wani company agarin abuja. Sun dau kusan shekaru uku kafin Allah yabasu dansu Aryan. Alhaji jibril kanin Abba shikuma lecturer ne yana aiki a adamawa. Anty Aisha kuma tana aure a abuja inda take auren wani babban custom officer. Aryan yayi makarantarsa ta boko da arabiyya gaba daya a Saudi wurin iyayen ummi. Tun yana karami ba ma'abocin magana bane irin mahaifinsa. Yanada San girma shiyasa ko cousins dinsa na can wadda ya girma basa ganin murmushinsa. Once in a while yake murmushi shima din sai in wani abun dariya akayi sosai. Yana makarantar secondary school aka haifi Nana khadija kanwarsa. Baida wani aboki sai muhseen yaron kanin ummi wadda aka haifesu lokaci daya banbancinsu watanni ne. Bayan ya gama secondary kakanninsa suka tura shi UK a can yayi university dinsa inda yakaranta engineering. Bayan ya gama makarantarsa yadawo wurin iyayensa a abuja wadda baiso hakanba danya saba da kakanninsa. Har I yau Aryan baida budurwa kuma bai taba soyayya dawata ya mace ba. Hakan na bala'in ciwa iyayensa tuwo a kwarya musamman ummi dansun kosa suga jikokinsu kuma Nana batai wani girman dazasu tilasta mata aure yanzu ba. Yana aikinsa a babban company dinsa wadda babansa ya bude masa, ayanzu shima yanada branches a wasu yan kasashen yanada company a Dubai Inda ake producing abayas da kayan maza iri iri masu kyau. Abokan aikinsa suna kiranshi da Young billionaire wadda kuma haka dinne amma shi kam bai damesa ba.

Cigaban labari

Wanka yayi yafito dagashi sai towel daure a kugunsa. Faffadan kirjinsa babu ko alaman gashi sumul yakesai ruwa dake bin jikinsa. Aryan shi ake kira da every woman's dream. Komai nashi yayi masha Allah. Shiryawa yayi cikin kananan kaya ya murje jikinsa da signature perfume dinsa mai sanyin kamshi. Gado hau ya dau wayarsa yana chatting da abokinsa muhseen.

*******
Sai kusan maghrib Nuwaira tagama aikin abinci da komai. Hadadden abinci ta shirya. Nuwaira ta iya girki sosai sakamakon catering school din da daddy yasata. Kuma mama tana koyamata girkin amma maimoon babu abinda ta iya sai dafa indomie kuma hakan bai taba damun mama ba asalima itace ta goya mata baya. Wanka tayi ta shirya cikin lace blue yayi mata kyau sosai abun ba'a magana. Tunda ta fito daga daki mama da maimoon suke aikamata da sakon harara dan kishin kyau irinna Noor. Kafa maimoon tasamata daidai tazo wucewa timmmm kakeji akasa. Dariya suka fashe da shi itakuma ta mike takoma daki tana kuka.....

Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j

MIJIN TACE

PG 5_6

Haka Noor taita kuka amma babu mai rarrashinta. Itafa badan daddy dayaki barinta ta koma gidan anty jamila kanwar ammintaba wlh da tuntuni tatafi tagaji da irin muzgunawar dasuke mata. Bata kara fitowa ba saida taji horn din motan daddy da alama driver dinsa ne yaje ya daukosa. Da gudu ta Sanya hijab ta fito harabar gidan. Su mama da maimoon suna ganinta suka wani tabe baki tunda yanzu babu abinda suka isa su mata agaban daddy. Yana fitowa daga mota da gudu ta shige jikinsa tana murna. " oyoyo yar lelen daddynta" yakike? Ya tambayeta cike da so da kauna." Lfy lau daddy I missed you " " missed you more yar lele" mama da maimoon kamar su fashe dan haushi. Mama ce tai saurin barin wurin dan inta kara minti biyu awurin tana iya fadamusu maganan banza daga daddyn har Nuwaira, maimoon ma ta take mata baya tana gunaguni. Shiko Daddy duk ya kula da change in mood dinsu amma ya basar ya cigaba da hira da yar lelensa. Sunkai five minutes awaje kafin suka shigo, lokacin babu kowa afalo. Wucewa yayi dakinsa Noor tana biye dashi har suka shiga. Tana aje masa jakansa tafice danya samu ya huta. Tana fitowa taci karo da mama tana aika mata wani irin kallo da ita kadai tasan meyake nufi jan hannun Noor tayi dan kar daddy yaji muryanta, maimoon kuma ta toshe mata baki ta baya suka wuce da ita BQ din gidan. Suna shigowa suka saketa tana kuka tana rokonsu dan tasan abinda zai biyo baya. Wani farin kyalle maimoon tasamu ta dauke mata bakinta dashi mama kuma ta zaro wani belt wadda ake hada injin nika dashi. Noor jin saukan wannan belt din suma ne kawai batayi ba dan atsakiyar bayanta tajishi unexpectedly, gashi babu daman ihu dan bakinta arufe yake. Haka sukai mata dukan fitan hankali iya san ransu duk sun kumbure mata jiki ko ina yayi jaa abinka da farar mace. Haka suka barta awurin suka kulle kofa ta waje. Tayi kuka harta godewa Allah batamasan lokacinda baccin wahala yasaceta ba.

******
Yau Saturday kuma ba aiki yasa babu inda yatafi. Tun bayan breakfast yakoma daki. Sanye yake cikin 3qtr da singlet ya fito da murjajjen jikinsa waje sai kamshi yake ta bazawa. Aryan badai san tsafta ba. Ko ina kamshi yake adakin gashi fesfes kuma shida kansa yake gyara dakinsa danba kowa yakeso ya shigo mai daki ba. Zaune yake akan gado ya jingine bayansa da gadon ya mike kafarsa yana aiki a laptop dinsa. Typing yakeyi cikeda kwarewa gwanin sha'awa. Wayarsa ce ta fara kara dubawa yayi muhseen ne ke kiransa. Dagawa yayi, karon farko danaga yayi murmushi wadda ya bala'in masa kyau. Larabci kawai suketa bugawa su suka san mesuke cewa. Sun dau kusan mintuna goma sha biyar suna waya kafin ya katse. Da alama hirar dasukayi ya masa dadi dan sai murmushin gefen baki yakeyi lokaci zuwa lokaci.

*****
Daddy tunjiya bai kara ganin Noor ba daya tambayi mama saita mata sharri wai ai shine bai taba lura ba amma kusan ko wani dare saita fita kuma itama batasan ina takezuwa ba. Daddy bai yarda da maganan mama ba dan yasan irin tarbiyyar dayawa yaransa biyu Moon da Noor. Hankalinsa bai kara tashi ba saida yaga har karfe goma na safe amma babu Noor ba labarinta. Wayarta ya dinga kira amma ba'a amsa ba kuma kiran na shiga. Mama da moon idan suka kalli juna saisuyi murmushin mugunta. Daddy kuwa hankalinsa ya matuqar tashi, to ina zata bayan jiya ya rabu da ita salin alin. Fita yayi harabar gidan su mama suka biyoshi da gudu suna tambayarsa ina zaije, karfa yaje yaduba BQ kuma asirinsu ya tonu. Aikuwa basu gama tunani ba sukaga ya nufi BQ din. Mama ce tai saurin shan gabansa tana fadin ina zaka, ko kallanta baiyi ba ya ratsa ta gefenta ya nufi kofar BQ din. Ihun maimoon dasuka jiyo ne ya hanashi bude kofar, itako moon tayi hakanne dan kar daddy ya bude kofar. Zuwa sukayi wurinta shida da mama suna tambayarta lafiya. Kafa ta nuna musu wai tuntubi tayi, badan daddy ya yarda ba kawai ya taimaka mata suka shiga falo mama kuma na murmushin mugunta.

Itako Noor tun jiya jikinta yayi tsami sai kuka take ta na addu'a Allah yakawo mata wadda zai fitar da ita. Tanajin muryan mama dana Daddy amma baza ta iya magana ba dansun daure mata hannu da bakinta, daga baya kuma saitaji tsit babu kowa awurin. Kuka takeyi Allah ya dauki ranta ta huta da wannan azaban datake sha a hannun kishiyar uwa...

*******
"Dear wlh ni ina ta mafarkin ya rahma kuka takeyi tana cewa zasu kashe mata 'ya" anty jamila kanwar ammin Noor tafada wa mijinta kamar zatayi kuka" jamila karki damu ai nasan nasir bazai bari komai ya sami Nuwaira ba. Amma ni na miki alkawari in har muka tafi kano gobe zamuje mu duba ta, idan mukaga bata samun kula to tabbas yazame mana dole mu dawo da ita nan abuja kinji? Kai kawai ta gyada masa amma zuciyarta sai faduwa yake kamar wani abune ke shirin faruwa da Noor dinta. Haka yaita tausarta har tadan kwantar da hankalinta.

******
Daddy kuwa hankalinsa a matuqar tashe yake dan har bayan la'asar babu Noor babu labarinta. Tunda ya fita sallah la'asar bai dawo ba sai kusan karfe biyar da rabi. Yana shigowa ya kalli BQ din ya tuna abinda yafaru da safe. Haka kawai yaji hankalinsa bai kwanta da abinda mama tafada masa ba. To kodai ya duba wurin yagani? Haka kuwa akayi ya nufi wurin amma saiyaga kofar akulle. Lekawa yayi ta window zuciyarsa tabuga dammmm. Noor? Abinda yafada kenan a matuqar razane. Da sauri ya koma wurin kofar ya daki kofar da kafarsa aikuwa ta bude dantaji bugu. Noor kwance take akasa numfashinta na fita sama sama ga jini abakinta da alama aman jini tayi danko ina ya baci da jini, ga kuma jikinta daya nuna zanen bulala rada rada. Da sauri yayo kanta ya dauketa kamar jaririya ya fito cikin gidan. Mama ce ta fito da sauri dan ita tama mance da zance Noor tun bayan abinda yafaru da safe. Daddy tagani da Noor ahannu yana kuka kamar ba namiji ba. Ko kallanta baiyi ba ya bude motarsa yasata sannan yayi horn maigadi ya bude masa da sauri dan shima yaga abinda yafaru. Gudu sosai yakeyi ikon Allah ne kawai yakaisu lfy. Wani private hospital ne babba yakaita aiko babu bata lokaci aka fara bata taimakon gaggawa. Sun dade akanta kafin ta dawo normal. Oxygen suka sa mata sabida numfashinta da baya fitowa da kyau dama kuma tanada asthma. Daddy sai kuka yakeyi yana Allah ya isa ga Wanda yayiwa 'yarsa haka. Anan ya wuni amma Noor bata farfado ba.

*****
Ummi da Nana suna zaune suna hira wayar ummi yayi kara alaman sako ne yashigo. Da sauri taduba kamar dama jiranshi takeyi, aikuwa ta fadada murmushinta sakon Abba ne ya shigo akan gobe insha Allah zai dawo. Nana tace"ummi lafiya kike murmushi" murmushin wasa tamata tace " mijina ne zai dawo gobe shiyasa nake murna". Dariya Nana tayi danta saba da ganin irin wannan tsantsar soyayyar da iyayenta ke nuna wa juna, itama addu'a takeyi Allah yabasu abokan zama haka musamman yayanta wadda yake buqatar wacce zata tarairayeshi tabasa kulawa na musamman. Haka ummi takira Salisu driver tayimai list din abubuwan dazata buqata dan girkin tarban mijinta sannan tace Nana tabishi, haka sukatafi itakuma tacigaba da wasu abubuwan.

******
Abba ya turowa Aryan sako akan zai dawo gobe, yasaba da abbansa sosai kusan shine abokinsa anan Nigeria sai kuma wani abokin aikinsa shareef tunda har yanzu yaki sakewa da mutanin Nigeria. Kakanninsa ma dake Adamawa Baffa da Dada suma yana matuqar sonsu dan basu da damuwa musamman Dada tanada wasa da dariya irinnan kakanni da jikoki, tun bai iya wasan ba har ya koya dan takan zo ta kwana biyu anan abuja. Wasu gidaje yake dubawa a laptop dinsa, gidajen kamar ba a Nigeria ba sunyi kyau sosai shi akabawa contract din komai daya shafi electricity da kuma technological abubuwan dake gidan dan haka yamaida hankalinsa, gidajen na wani babban mutum ne a masar. Wayarsa tayi kara ya duba yaga Anty Aisha ce ke kiranshi tsaki yayi kamar bazai amsa ba sai kuma ya amsa amma baice komai ba" hello" naji an fada. Cire wayar yayi daga kunninsa ya duba number da kyau kamar ba wacce ta jira bace ke magana" hello "ta kara fada " hello"shima ya fada....


Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 7_8

Aryan bai kara magana ba sanin wadda ta kira, wayan na kunninsa har kusa two minutes amma babu wadda yakara magana daga dayan bangaren, kitt yaji an kashe wayar tsaki yaja ya jefar da wayan yayi kwanciyarsa dan dama ya gaji da typing din dayakeyi a laptop din. Wato dai tunda ya blocking Lubna a wayarsa shine ta dau na mamanta danta dameshi? Lallai yarinyarnan yasakemata fuska sosai in ba haka ba to mazajen data kebi basa biya mata buqata yadda takeso ne dazata wani dami rayuwarsa? Haka dai yaita tunani yana jan guntun tsaki har bacci yadaukeshi.

******
Noor bata farka ba har daddy yaje yayi sallan isha'i. Su mama bama suyi gigin zuwa dubata ba dan sunsan halin daddy kuma sun tabbata yanzu yariga yasan waya mata wannan abun. Shima daddy ko takansu baibi ba. Ya bari ne Noor tasami lfy dan a yanzu ma baima san wani mataki zai dauka ba, mama ta dade tana tsiyanta tun ammi na raye amma dayaso ya dauki mataki sai ammi tahanashi, wani zazzafan hawaye ne suka sauko masa yai saurin sharewa. Noor ne tadan fara motsi hakan yasa yai saurin tashi ya matso kusa

Please Login or Register in order to submit comment