Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shiko Aryan da wannan dattijuwar matar sai murmushi sukeyi ganin yadda Noor takasa yarda da abinda ke gabanta. Dagowa tayi ahankali ta taba Aryan dake gefenta sannan ta kalleshi tace" baby love wannan fa"? Sassanyar murmushi ya sakar mata sannan ya nunata da yatsarsa manuni ya nuna jewelry din alaman nata ne. Da sauri ta juya idanunta kan box din ta dauka ahannunta tace" nawa"? ya gyada mata kai alamar ehh yana murmushi. Wani irin tsalle ta daka ta mike tsaye da sauri shima ya mike yana cewa" baby take it easy, bafa ke kadai bace", dariya wannan matar tayi tana kallon ikon Allah awurin wannan ma'auratan. Murna sosai wurin Noor ba'a magana, rungumeshi tayi tana hawayen jin dadi, shima rungumeta yayi yana kara fada mata kalamai masu kwantar da hankalin mace. Haka suka jima awurin kafin daga bisani suka kama hanyar gida wadda tuni wuri yayi duhu saboda maghrib daya gabato


***********
Lokaci ba wuya, yau sun kammala jaraba wansu wadda kuma ana sa ran za'a fara azimi kwana biyu masu zuwa. Shirye shirye kowani musulmi keyi dan tarban wannan wata mai cikeda tarin albarka da alkhairi. Hakan ya kasance agefen su Noor da Aryan dinta inda kuma suke kula da dan cikinsu kamar kwai. Baya bari koda tsinke ne ta dauka, ita kuma bata saba da zama haka kawai ba. Duk lokacin dayake gida toh shi zaiyi mata komai, lokacin kuma da bayanan, dan karma tayi aiki haka zai dauketa ya kaita gidan ummi, saida yamma in ya taso daga aiki zai biya ya dauke ta tunda Hutu sukeyi. Yanzu major concern dinsa shine maganan azimi, hankalinsa bai kwanta akan tayi azimi wai saidai tabari saita aihu saitayi ramako. Dukda yadda ummi ke tausayin wannan yanayin nata ammma hakan bai hana ta musa da wannan shawaran nasa ba. Ai ita mai dauke da cikin ba cewa tayi cikin na bata wahala ba balle ace ta huta tunda cikin ba wani girma yayi ba gara kawai ta daure tayi aziminta. Allah ne kadai yasan nan gaba, amma in Allah yabata yaro mai uban tsotso ai wahalan dazata sha nan gaba saiyafi na yanzu. Itama Noor din bata nuna damuwarta akan hakan ba, tukunna fa cikin ya cika wata daya da sati daya, babu yadda ya iya haka ya kyalesu ganin sun masa taron dangi. Daddy na gari shiyasa suka shirya ranan da za'a kama azimi wadda ya kasance ranan Friday ne zasu kai masa ziyara har kano, dama shi kadai ne basuyi masa albishirin cikin Noor ba dan kunya Aryan yakeji, yaza'ayi ya kira mahaifin matarsa yafada masa cewa yawa yarsa ciki, ai sai girma ya fadi. Murna a wurin Noor ba'a cewa komai. Ita sam Mama bata gabanta, Ya Moon dinnan dai kamar dama can suna shiri, duk ta mance da irin wulakancin datayi mata abaya.


*********
Tunda Daddy ya sanar da Mama zuwan Noor da mijinta take ta mita wai akan me zatazo da mijinta tunda ai basu gayyaceta bikinta ba, dan haka ita babu wani abinda zata shirya musu na tarban baki. Daddy baice mata komai ba saboda dama suma bazasu bukaci wani abu ba tunda za'a shiga azimi ne. Haka yagaji da mitarta ya fice agidan yabar mata. Ba kadan ta harzuqa da wannan batun na zuwan Noor ba, kuma tasha alwashin saitayi musu rashin mutunci itada so called mijinnata, ko da yake kila wani ustazun aka kakaba mata yadda akayiwa Moon dinta. Allah sarki yarta tilo, tun ranan data bar gidan bata kara saka ta a idanu ba. Gashi kullum haka take kallon kiranta na shigowa yana katsewa amma bata taba daukawa koda gaisuwa ne suyi ba.

*************
Yau Anty Jamila ta dawo daga wani Dan tafiyar da tayi zuwa Dubai duba wani yaron aminiyarta da aka masa aiki a zuciya. Daganan kuma tayi siyayya masu tarin yawa inda ta siyo komai iri daya kashi biyu na jarirai unisex. Sosai take zumudin zuwan jikokinta, kayaki masu tarin yawa ta hada musu, amma na Noor yafi yawa dan yadda take jin yarinyar har cikin ranta. Aranan Ya Shareef yakaiwa Na'ima nata inda take ta zabga uban godiya. Na wurin Noor kuma aka ajeshi a matsayin surprise danba shikenan ba. Akwai wadda uncle saif shima zaiyi daga nasa bangaren, ga kuma na big aunties su Hanan da Hanifa wadda sukeji kamarma yaran sun rigada sun iso. Kullum ana sintirin zuwa gidan Noor su da Nana da yasmeen, dan adubata, akwai lokacinda Aryan yamusu wankin babban bargo wai suna damun honeypot dinsa, haka suka dan dage kafa amma kwana biyu aka cigaba da zuwa.


**************
Dada a Adamawa tunda taji batun cikin Noor ai ta kasa tsaye takasa zaune. Kullum cikin waya da kawallinta take ana tambayar lafiyar dan Baba, sunan datasawa cikin Noor kenan. Badanma ance tabari zasu zo cikin Ramadan ba da tuni tayo na Abuja, wai ita zatazo ta taya Noor laulayi, saboda tasa musu ido ko dan wannan jarababben Aryan din, wai ita dama ta lura Allah yayi jarababbe awurin. Kawai dai saboda baida mata ne alokacin shiyasa hakan bai nuna ba. Cewa tayi" ayanzu datake sabuwar shiga kamata yayi ya daga mata kafa sai lokacin data aihu" tab aikuwa tana fadawa Aryan wannan maganan ba kunya yace mata to ta Allah ba tata ba, saida sukayi baram baram awaya inda Dada ke fada masa shima yana maida mata yadda suka saba.


Wani irin shegiyar jaraba ne da Noor kwana biyunnan wadda hatta Aryan mamakinta yakeji. Ko tsakiyan dare in suna bacci haka zaiji tana lalubarsa, shiko ba karamin dadi hakan yake masa ba danshima AAA ne a wannan harkan, shiyama dauka dole zai daga mata kafa kamar yadda Dada ta fada amma Noor tafi yadda yake tunani. Wani lokacin inyaso gwadata duk da shima yanaso, inyace mata ba yanzu ba ta dinga kuka kenan tana cewa shikenan saboda yamata ciki ya daina sonta. Ba karamin dariya hakan ke basa ba, saikuma ya sha wahala kafin yake iya shawo kanta ta sauko su daidai ta. Har wani fresh dukkansu suka kara, ga haske mai kyau, rayuwa sukeyi cikeda soyayya da kwanciyar hankali. Amma abinda Noor takasa ganewa, tun bayan zuwansu Anty Aisha da Lubna wannan ranan basu kara zuwaba. Kuma akwai lokacin data tambayi Nana akansu tace mata tayi hankali dasu dan ba kananan munafukai bane. Ita dai ayanzu daidai take da duk wacce tace zata sa ido kan mijinta cos he's her's alone, itace mai shi kuma itakadai keda ryt akansa. Balle ma da cikinnan bini bini tana mood swing, Aryan ne kadai ke iya shawo kanta, wasu lokutan ma in tana fushi akansa take saukewa taita zazzaga masa ruwan masifa, haka zai shiga damuwa har saiya bata tausayi, dakanta zata dawo tana lallaminsa kamar jariri.


Washe gari yakama Thursday, gaba daya al"'umman musulmai a duniya suka tashi da azimi. Kuma aranan su Noor sukayi tashin safe bayan suhur basu kara komawa bacci ba saboda ta jirgi zasu tafi kuma jirgin zai tashi karfe bakwai ma safe ne. Sun gama shirinsu tsab, sunyi bala'in kyau inda Noor taci wankanta cikin tsadaddar lace brown shikuma ya shirya cikin shadda half jumper milk colour uban ubansu, sai zabga kamshi sukeyi kana ganinsu kaga perfect couples wadda sukayi bala'in dacewa da junansu. A airport ma duk inda suka gifta kallonsu ake, hannunsa cikin nata sai zuba masa shagwaba take, har lokacin tashinsu yayi, a business class nasu sit din yake, bayan kowa ya shiga, jirgi ya daga zuwa sararin samaniya. Karfe tara daidai tamusu agarin kano, Daddy dakansa yazo daukansu. Ba karamin dadi Daddy yaji ba ganin shalelensa, ga kuma yadda tayi kyau alamar tana samun kulawa a wurin mijinta da yan uwansa. Itama tayi kewar mahaifinnata shiyasa lokacin data gansa ta rungumeshi tana kuka. Shikam Aryan hannu suka sha da Daddy kamar wasu abokai, Noor tayi mamakin yadda suka saba tunda ba gari daya suke ba inda Daddy yayi mata bayanin ai kusan kullum sai sunyi waya dashi. Ba karamin dadi Noor taji ba, take soyayyar mijinnata ya kara nunkuwa ninkin baninki a zuciyarta. Suna shigowa layin unguwarsu Noor kirjinta yafara dukan uku uku, nan da nan kuma yanayinta ya sauya wadda har saida Aryan ya lura da hakan amma baice komai ba. Horn Daddy yayi mai gadi ya bude masa gate ya shiga. Bayan yayi parking suka fito, hannunta cikin na mijinta, ta gefen ido Daddy ya kallesu yasaki murmushi yana jin dadi. Har falon Daddy suka shiga amma bata ji motsin kowa agidan ba kamar ba mutane, kuma Mama na nan tasan sarai da zuwarsu amma ta kame adaki. Daddy ne ya shiga dakin ta dan sanar da ita zuwansu amma abun mamaki ta fada masa maganar da saida yaji zuciyarsa na tafar fasa, controlling kawai yayi saboda su Aryan dake gidan. Kamar bazata fito ba bayan fitar Daddy daga dakin saikuma ta mike kamar an mintsineta ta yafa gele ta fito. Ba sallama ta shiga falon inda karaf idanunta yasauka cikin na Noor wadda ke kwance kan kafadan Aryan tana masa kukan shagwaba kasa kasa, ganin Mama datayi yasata shan jinin jikinta saboda yadda take jifanta da wani irin kallon tsana. Ahankali ta maida idanunta kan Aryan da shima kallonta yake, kuma kallon sani yake mata. Saida gaban Mama ya fadi damm, tabbas fuskarsa yamata kamar ta taba ganin shi awani wuri can baya amma ta mance a ina. Wannan yasa rashin mutuncin da shirya yiwa Noor ya koma ciki dan kana kallon fuskar Aryan yadda yake amurtuke Kasan babu wasa a tattare dashi, balema yadda taga yana wani nan nan da Noor din kamar kwai, yarinyar da batafi ta tattaketa kamar tuwo awurin ba. Gaida ita Aryan yayi still yana so ya recalling inda yasanta amma yakasa, amsa masa tayi ciki ciki, duk tabi ta tsargu da yadda yake mata kallon tuhuma. Toh kodai sun taba haduwa acan baya ne....


COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/1/23, 8:16 PM - Reemah: 🌼 MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 53_ 54


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

Duk wani motsin Mama akan idon Aryan takeyinta. Sai yanzu yafara recalling inda yasanta. Itace matar dayafara tsana aduniya tun abinda ya kamata tana aikatawa. Batada tsoron Allah ko kadan a zuciyarta. Allah dai ya taimaketa kar tayi wani abunda zaisa ya harzuqa ya tona mata asiri, baiso allah ya kara hadashi da ita ba tun shekaru goma sha daya dasuka wuce. Tunda Mama ta kalleshi bata kara dago idanunta ta kalleshi ba. Itama yanzu ta ganeshi. Tsoro ne ya bayyana karara a idanunta, meyasa Allah zai hadata dashi a yadda take ta rokon Allah ya rabata da shi. Yanzu dama shine mijin Noor, lallai tata ta sameta idan batayi hankali dashi ba. Noor kam duk bata lura da wannan kallon kurillan da mijinta keyiwa Mama ba, ita sam bata ma dago ta kalli Mama ba saboda tsoronta takeji bana wasa ba. Kanta na gishingide a kafadar Aryan inda hannunta ke cikin nashi yana murzawa ahankali. Wani irin bacci takeji yana fuzgarta, suna cikin wannan zaman shirun Daddy ya fito daga dakinsa yana sakin lallausan murmushi ganin shalelensa. Zama yayi a cushion yana kallonsu cikeda birgewa. Soyayyarsu na matuqar kayatar dashi duk da baisan yaushe har wannan shakuwar tayi nisa a tsakaninsu ba. Mikewa Mama tayi zata bar falon dan ji take kamar ta zauna ne akan kaya, duk jikinta yagama mutuwa. Tabbas in Aryan ya tona mata asiri yanzu, to ta sawa ranta zaman gidan Nasiru ya kare, gashi babu babban abinda take tsoro kamar saki. Babu wadda yabi ta kanta har ta fice daga falon. Hira su Aryan keyi jifa jifa da Daddy tunda bawani sabawa sukayi ba. Kiransa ma da Aryan keyi gaisuwa kawai sukeyi shikenan, "wai meke damun Noor ne, naga tunda kukazo take ta faman bacci" Daddy yayi magana yana kallon Noor dake kwance kan three seater ta aza kanta saman cinyar Aryan tayi matsashin kai dashi. Murmushi Aryan yayi yace" amm Daddy dama.." Sai yayi shiru yana shafa kanshi, kamar Daddy yasan meyake nufi tunda yaganshi sai faman noke noke yakeyi, aikuwa tsab ya dau haske. Kafin Aryan yayi magana yaji Daddy yace" Masha Allah, Allah ya sauketa lfy" dukar da kai Aryan yayi duk kunya tagama rufeshi. Daddy sai mamakinsa yake, kamar ba Aryan dinnan ba da uncle saif yabashi labarin shi. Gsky yayi murna da irin kulawar da Aryan kebawa Noor koma agaban uban waye.


Kusan karfe biyun rana suna gidan, Daddy da Aryan sun fita zuwa masallaci inda suka bar Noor anan gida tare da Mama, Aryan hankalinsa duk yaki kwanciya ganin yabar babynsa itakadai da wannan muguwar matar mara imani a zuciyarta. Tabbas yasan wannan matan ba itace ta haifi babynsa ba. Sam Noor bata dauko halinta ba. Kana kallonta ma kasan bame kirki baci no matter yadda taso ta canza yanayin fuskarta. Allah Allah takeyi sudawo gida wurin honeynsa. Suna idarwa suka dawo, tundaga bakin gate ya ciro wayarsa daga aljihu yafara kiran Noor, lokacin tana sallah adakinta na da. Har wayan ya katse bata dauka ba, hankalin aririnku mezaiyi inba tashi ba, gudu gudu sauri sauri ya shige gidan yana kiran Baby love. Abun har mamaki yabawa Daddy, waishi Aryan ko irin kunyan suruki baya ji, sai faman kiran baby love yakeyi a gabansa. Fitowa Noor tayi daga daki a rude jin irin ihun sunanta da Aryan keyi, daidai lokacin Mama ta fito daga daki Daddy ma lokacin ya shigo falon. Aryan na ganinta ya jawo abunsa ya rungume tsam yana sauke ajiyar zuciya kamar wadda yayi gudu mai nisa." Baby love are you alright? I hope babu abinda wannan matar tamiki ko" yafada yana kallon Mama. Tashin hankali da ba'a samashi date. Me Aryan ke nufi da babu abinda tayimata, Noor ta tambayi kanta a zuciyarta, dama yasanta ne. Mama kuma tasha jinin jikinta ta kame a tsaye tana kallonsu musamman Aryan da shima ita yaje kallo still yana rungume da Noor, gyaran murya Daddy yayi wadda yasa suka rabu daga rungumar dasukayiwa juna. Murmushi Daddy yayi, wani gefe na zuciyarsa kuma yana ayyana maganan da Aryan yayi, shima mamaki yake Aryan ya taba sanin Mama ne. A iya saninsa yau suka fara haduwa tunda bikinsu ma Mama bata tafi ba. Zama Aryan yayi ya kamo hannun Noor suka zauna a cushion tare. Mama kam juyawa tayi ta Shiga daki, zufa na tsatssafowa daga jikinta. Gsky in batayi da gaske ba Aryan zai iya jagalo mata tsiya.


After three suka isa gidan Moon bayan sun bar gidan Mama. Sosai Moon taji dadin ganinsu, har rungume Noor tayi tana kuka tana neman yafiyan abinda tayi mata. Itama Noor din kuka takeyi tana jin son yar uwarta har cikin zuciyarta. Ba karamin dadi Daddy yaji ba, at long last Moon tayi hankali ta dawo kan hanya. Lokacin da suka zo Mahmud baya gida, kiransa Moon tayi ta sanar dashi zuwansu Noor, batare da bata lokaci ba saiga Mahmud ya iso. Sosai yayi murnan ganinsu, dayake aririnku ba mai son yawan magana bane, gaisuwa kawai sukayi, ba'a kara jin muryarsa ba kamar baya falon. Amma bini bini da sun hada ido da Noor saiya kashe mata ido daya, itakuma tayi masa murmushin nan nata mai bala'in tafiya dashi. Duk wannan abinda sukeyi a kan idon Moon da Daddy, Moon har saida taji wani iri a zuciyarta, duk da yanzu tana tsananin son mijinta amma saida ta kyasa da mijin Noor, komai nasa ma dabanne, from the way he dresses,talks, moves, walks, his gesture everything about him is utterly perfect. Inama inama( ke malama ki kama gabanki, kafin fans din Noor suyi rugurugu da bakinki). Sunyi hira sunyi wasa gwanin ban sha'awa. Aryan yayi mamaki yadda sam Noor bata nemi abinci ba dukda wannan uban cin nata, sai kuma wani zuciyar yace mashi ai abun sa rai ne, lokacin saboda taga bakinta abude.yake ga kuma abinci shiyasa.


Karfe biyar da rabi suka kama hanyar airport, Daddy ne ya kaisu, har kuka saida Noor tayi lokacin dazata rabu da daddynta. Karfe shida jirginsu zai tashi, kuma yana nufin zasuyi buda baki a jirgi kenan. Saida jirginsu ya tashi sannan Daddy ya koma gida cikeda kewar shalelensa.

*******************

Kwance take kan kirjinshi bayan sun gama aikata masha'ansu. Sai wani narkewa take masa kamar karamar yarinya, tunda ya kwallafa rai akanta har saida yasamu ya biya buqatarshi da ita. Anty Aisha yanzu har tazama yar hannu awurin wannan dattijon mutumin daya daukosu zuwa farm house dinsa. Sosai suke holewarsu, ko azimi ma basu dauka ba itada shi harda Lubna dama kuma wannan ba damunsu yayi ba musamman ita Lubna. Har aka kira sallan maghrib suna kwance ko ajikinsu, sunma koma round kusan na biyar kenan, komai zafi zafi sukeyi kamar kananan yara, wa iyazubillah.


Can na hango Lubna itama, ta zuba uban goho sai aikata fasikanci sukeyi itada wannan shegen daya tona mata asiri wurin dad dinta. Har yanzu kuma cikin jikinta bata yi aborting dinshi ba. Ita kanta ko za'a kasheta bata San wanene taka maiman uban dan cikinta ba, saboda bada namiji daya take kwanciya ba. Yanzu sunma daina haduwa da mommynta kowa harkan gabansa yakeyi. Asati baikai sau biyu suke haduwa ba, wasu lokutan ma wannan dattijon mai suna Honorable Musa har daukanta yakeyi yakai wurin wasu abokansa suma dandani zumar jikinta, yanzu ko ta ina kudi kawai ke shigowa musu, basuda wani matsalar rayuwa, suci susha subude kafa wa mazajen banza, sannan suyi bacci shine aikinsu. Har dadi sukeji ma da mijin Anty Aisha ya saketa, ahaukansu wai THIS IS THE REAL LIFE.

*********************
8:30pm suka shigo gida, bayan drivern ummi ya daukosu daga airport shikuma ya koma gida. Lokacinda suka shigo Noor nata kwasan baccinta, Aryan ne ya daukota daga motar ya kai ta dakinsa. Shida kansa yayi musu wanka, sai zuba shagwaba takeyi wai ita tagaji tanajin bacci da yunwa, da kyar ta yarda yayi mata wanka ya sanya mata kayan bacci, dayake yanzu tadena kwana adakinta saidai in baccin rana zatayi, shidinma sai in ya kasance ba Aryan a gida, saikuma in zata sa kaya. Bayan ya kwantar da ita yawuce kitchen, tunda bawani gwani bane wurin girki kawai ya hada mata tea cikin wani katon cup, dan karamin aikinta ne tace yayi mata kadan inya hada a karamin cup, bread half loaf da kuma kwai daya soya yasa a plate ya dauko a tray ya fito daga kitvehn din ya haura sama. Lokacin daya shigo harta fara bacci, tayi dai dai akan gado ta rungume pillow akirjinta kamar wata baby haka take bacci, so cute. Tsayawa yayi akanta yana kallon yadda ta tsuke dan karamin bakinta, murmushi yayi yadan rankwafo ya manna mata kiss agefen kumatunta. Jin saukar lips dinsa kan cheeks dinta ta sanya ta bude gajiyayyun idanunta, shafa lallausan sajensa tayi tana murmushi, itama kiss din ta manna masa a cheeks dinsa tace" I LOVE YOU SO MUCH ARIRIN NOOR" abunma dariya yabawa Aryan wai ARIRI sai kace wani karamin yaro. Taimaka mata yayi ta zauna dakyau akan gadon, tray din daya kawo, zaro ido Noor tayi tace" Baby love wazai shanye tea dinnan, kalli fa saikace wani basamude ne zaisha" dariya yayi yace" au yau kuma, ai na dauka kinbar kiran wannan sunan na basamude ashe dai yana bakinki" kallon mamaki tabisa dashi tace" dama kasan ina kiranka da Basamude ne" gyada mata kai yayi, kunya ya rufeta ta rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shafa sumar kanta yayi yana murmushi sannan yafara feeding dinta. Saiga Noor datace tea yayi mata yawa, tas ta shanye shi, bread dinma baifi slice hudu ya rage ba, kwanma haka tas ta cinye shi. Sai zolayarta Aryan ketayi mata tana kukan shagwaba wai ai ba ita bace ta cinye, babynsa ne aciki ya shanye. Haka suka kwanta jikin juna suna zuba love dinsu har bacci ya daukesu.

******************
Yau sati biyu kenan da fara azumi, abun mamaki Noor batasha ko daya ba. Dukda gsky tana jin jiki amma still haka take dagewa tayi. Yanzu haka shiri sukeyi akan tafiyarsu adamawa wadda nan da kwana biyar ne. Sunyi siyayyan abinda za'a kaiwa yan uwa acan, na Hajiya Dada da Baffa dabanne. Yau agidan Anty Jamila ta wuni,karfe hudu babynta yazo daukarta dan shirin bude baki. Koda suka koma gida, tube kayansa yayi dagashi sai short da singlet ya shige kitchen, ba ita tayi girkin ba, itadai tana basa instruction ne shikuma yana girki. Gwanin ban sha'awa. Sai kusan maghrib ya kammala girkin sannan suka haura sama sukayi wanka, shiryawa yayi cikin jallabiya yawuce masallaci lokacin har an fara kiran sallah. Sai bayan sallan isha'i yadawo, shima din yana ganin yayi lattice saboda yasan bazata ci abinci ba saida shi. Aikuwa kamar yadda yayi tsammani, cornflakes ya sameta tanasha taki cin saida yadawo sannan sukaci. Kullum yanaso yayi mata maganar Mama amma sai ya mance, bayan sun gama cin abinci suna hira a falo yace" baby love, wannan matar da ba gani agidan Daddy itace Ammi"? Jin wannan tambayarta tashi yasata mikewa zaune da sauri tana kallonsa, mekuma yakawo maganar Mama acikin hiransu. Ganin yadda yanayin fuskarta yacanza tagane cewa ba ita bace, shima yayi wauta daya tambayeta, ai inda mahaifiyarta ce, dasuka tafi gidan yakamata ace yaga suna wasa da dariya amma shi akasin haka yagani. Ahankali hawaye yafara taruwa a idanunta ta gyada masa kai alaman a'a sannan takoma ta kwantar da kanta a cinyarsa. Lokaci kadan Aryan yabi ya rude ganin halinda ta shiga daga tambayarta, tabbas yasan akwai matsala. Kuka sosai Noor ta fashe dashi dan Aryan ya fama mata inda yake mata ciwo, ba kasafai takeso ana tuna mata maganar Ammi ba saboda abun tamkar sabo haka yake dawo mata. Rarrashinta ya shiga yi yana bata haquri kamar shima zaiyi kukan. Saida tayi mai isarta sannan ta tsagaita kukan tana ajiyar zuciya. Rungumeta yayi tsam ajikinsa, bai kara tambayarta ba amma yasawa ransa cewa in har wannan matar itace sanadiyyar kukan rabin ransa yayiwa kansa alqawarin wannan abinda ta danne azuciyarta saiya tonoshi. Itakam Noor daga ajiyar zuciya har bacci ya dauketa.

**************
Agurguje

Tun karfe shida na safe suka kama hanya zuwa Adamawa. Convoy sukayi na kusan motoci guda shida, biyu nasu ummi da su Aryan biyun baya dana gaba kuma na securities ne da Abba yasa suyi tsaron lafiyarsu. Su Aryan su kadaine amotarsu inda ummi kuma da Nana saida Abba suna nasu motar. Abba baiyi mamakin kin Anty Aisha ba daya fada mata maganar tafiyar. Har yanzu kuma baisan da maganar sakin ta da mijinta yayi ba. Karfe biyun rana suka iso garin adamawa. Family haiuse ne babba gidan, kowa da sashinsa tare da matarsa da yaransa. Part din Abba wadda ke gidan aka sauke musu kayansu. Dada kamar ta zuba ruwa akasa tasha saboda murnan ganin kawallinta. Ita sam su Abba ma basune agabanta ba, sai nan nan take da Noor. Tama hana Aryan rabewa da matarsa, shikuwa kamar ya sa hannu akai ya kurma ihu, dakin Dada Noor ta sauka, anan tayi sallar la'asar tayi wanka, daganan kuma ta bingire da bacci.l, babu wadda yayi tambayarta. Duk sintirin da Aryan keyi afalon Dada amma sam taki barinsa ya shiga dakinta,"aina samu daman yin maganinka kenan, badai ni kake fadawa magana awaya ba, toh Allah ya jawoka har inda nake, yanzu kuma sai yadda nayi da matarka" akule Aryan yake, yanaso yaga babynsa amma wannan tsohuwar matar taki basa dama, rabonsa da ita tunda suka iso, gashi yanzu har an fara shirin shan ruwa. Su Abba suna can suna hira shida baffa dasu alhaji jibril kanin Abba, hira sukeyi na yaushe gamo. Sai kusan sallan maghrib kowa yawuce part dinsa.

Abu kamar wasa har aka sha ruwa Dada taki barin Aryan ya kebe da Noor, abun harya bata masa rai yafice daga part dinsa ya wuce part din Abba, dakin da aka saukesu ya shige yayi wanka ya fito da towel daure akugunsa, Allah sarki Noor dinsa da tana nan da yanzu tare zasuyi wankansu. Gsky Dada ta taro match. Dole nema kawai yasan yadda zaiyi ya jawo Noor dakinnan inba haka ba bazai iya bacci ba. Sharp sharp ya shirya cikin kayan baccinsa riga da wando white colour mai ratsin blue yayi kyau sosai. Wani idea ne ya fado masa, bude akwatinsu yayi dama kayan Noor ahade

Please Login or Register in order to submit comment