Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita, bude ido tayi tana kalle kalle kawai idanunta yasauka a kan Daddy wani irin kuka ne ya taso mata amma baya fita saboda oxygen din dake bakinta da sauri Daddy yakira Doctor suna shigowa suka samu takara sumewa dirshan Daddy yakara zama akasa yafashe da wani irin kuka kamar ba babban mutum ba, wlh idan wani abu yasami 'yarsa bazai taba yafewa mama ba yarasa dansa abaya amma yanzu bazai iya daukan rashin Nuwaira ba. Doctors sunyi iya kokarinsu amma Nuwaira bata farka ba. Doctor samir ya kalli Daddy yace Alhaji kasameni a office dina. Daady yatashi yabi bayansa kirjinsa na bugun uku uku meyasami Noor dinsa, office dinsa suka shiga yaja wani kujera yazauna agaban doctor din. Doctor ya kalli Daddy yace" Alhaji ita wannan yarinyar bata da yan uwa ne"? Ya yasauke nannauyar numfashi yace" batada uwa ni kadai takeda shi anan garin" " to babu wadda yake tare da ita agida ne ko kuwa Ku dai kuke zama" ya kara jefo masa tambayar " she's together with her step mum and her step sis" abinda doctor ke jiran yaji kenan dan shatin dukan dayagani a jikin Noor yasan dole akwai wadda sukayi sanadin haka" Alhaji bazan boye maka gsky ba amma 'yarka tana dab da fadawa cikin depression kuma inaganin ta dade tana ajiye abu azuciyarta wadda hakan shima yaso janyo mata hypertension amma munyi iya kokarinmu kuma zamu dorata akan magunguna ingantattu insha Allah zata samu sauki" kuka kawai Daddy yakeyi yanzu yana zama da 'yarsa shekara da shekaru amma har ta shiga wannan damuwar baisani ba? Anya ba haqqin Noor yadauka dayaki barin anty jamila ta dauke ta ba, yasani anty jamila zata kula da ita sosai fiye da yadda shi zaima kula da ita. Maganan doctor samir ne yadawo dashi" gsky Alhaji ina baka shawaran in Allah yabata lfy kakai ta wani wuri ko wurin yan uwanka wadda ka tabbata zata samu kulawa awurinsu akaita can kafin Allah yabata lfy" ko da doctor bai fada shi abinda ma ya yanke kenan inbahaka ba mama na dab da kashe masa 'yarsa. Godiya yayi wa doctor ya fita zuciyarsa na kuna.

Haka ya kwana cikin dacin rai yana salloli da addu'o'i. Noor ko bata kara motsawa ba har washe gari.

Su anty jamila da sassafe suka dau hanya zuwa kano dan hankalinta ko kadan yaki kwanciya jitake ajikinta wani abu yasami Noor dinta. Sun iso kano kusan karfe goma da rabi na safe. Taxi suka tare zuwa hotoro angwan su Noor itada mijinta Alhaji Saif. Suna isowa suka sallami taxi din suka knocking gate amma babban gashin hankali suka tarar inda maigadin yake fadamusu abinda yafaru. Anty jamila bata san lokacin data fashe da wani irin matsanacin kuka ba. Yanzu abinda yasami Noor dinta kenan shine Ya Nasir ko ya fada mata(haka take kiranshi). Mijinta ne ya tare taxi suka tafi asibitin da maigadin yafada musu. Suna isowa ta shige da gudu tabar mijinta yana sallaman mai taxi. Daddy tagani abakin kofa yana magana da wata nurse shima yana ganinta yayi mamaki sosai danko babu wadda yafada wa cewa suna nan "yanzu ya nasir ka kyauta kenan, 'yata tana asibiti shine ko ka kirani kafada min"? Anty jamila tafada tana kara rushewa da wani kukan. Hannunta yaka ma zuwa dakin da nuwaira ke kwance kamar ba itaba. Duk ta rame tayi fayau fuskarta kamar babu jini bakinta ya bushe. Matsowa kusa da gadon anty jamila tayi tana kuka ta kamo hannun Noor tana murzawa ahankali. Alhaji saif ne ya shigo ,shima saida jikinsa yayi sanyi ganin Noor kamar babu rai ajikinta. Haka kowa yazauna adakin jugum jugum babu mai magana acikinsu. Kusan 30 minutes anty jamila taga Noor tafara motsawa ahankali da sauri tamike takoma kusa da ita tana murmushin jin dadi. Har Noor tagama bude idanunta tasauke su tas akan anty jamila sannan tafara bin kowa adakin da ido hawaye na bin gefen fuskarta a lokacin doctor yashigo shima yaji dadin ganin tafarka. Dubata yayi sannan yacire oxygen din abakinta yanzu numfashinta ya normalising. Kowa a dakin murna yakeyi Noor tasamu lfy, kokarin tashi tayi anty jamila ta taimaka mata ta zauna tana sauke numfashi awahale. " Ku hada mata tea mai dan kauri abata amma karku bata solid food yanzu sai zuwa anjima" doctor yafada tare da ficewa daga dakin. Tea anty jamila tahada mata dama akwai kayan da Abba ya karya dashi adakin, ahankali takebata tea din tana kurba har ta gama sha sannnan ta taimaka mata tayi brush tawanke fuska. Abba ya matso kusa da ita ya tambayeta ya jiki kai kawai ta daga masa alaman amsawa ,shima uncle saif ya gashsheta.

Sai kusan la'asar doctor yakara dubata kuma Alhamdulillah jikinta yasami sauki sosai amma sai gobe zaiyi sallama. Abba yace" shalele insha Allah ana sallamanki bazaki koma wannan gidan ba zaki bi antyn ki abuja kinji"? Murna sosai wurin Noor Allah ya mashi addu'arta. Sosai suma su anty jamila sukayi murna at long last Abba ya yarda Noor takoma abuja tareda su. Haka sukayita hira gwanin sha'awa.

********
Yau Abba yadawo daga kasar turkey. Gaba dayansu suna dinning anacin lunch babu wadda ke magana sai karan plate da spoon. Bayan sungama cin abinci aka bude sabon shafin hira Abba ke tambayan Aryan " babana ya maganan ginin gidanka, nafa gama design din kuma nabaka amma baka kara min magana ba anfara gininne? "Ba'a fara ko ba amma ina sa ran insha Allah by next week zasufara, contractor din yamin magana cewa nayi masa uzuri akwai wani aikin dasukeyi ne amma by next week insha Allah" kai kawai Abba ya gyada shi so yake agama ginin Aryan din kafin ya bullo masa da maganan aure amma yanzu inya mai magana saiya fara kwana kwana yana waskewa har a share maganan. Nana tace" Abba next week matric dinmu fa kuma nasan zakace baka gari dan Allah ka attending kaji abbana" ta fada tana shagwabe fuska irinna autanni. "Karki damu shalele insha Allah zamuzo " Abba yafada yana shafa kanta. Shiko Aryan in akwai abinda bayaso shagwaba ne, abokinsa na wurin aiki shareef na yawan fada masa cewa inyayi aure kuma yasamu matar da ta iya shagwaba abin zai birgeshi, anya? Hmm Aryan kenan. Ummi na magana da Abba tace" kaga dear in aka gama ginin gidan Aryan kaga sai asami abban lubna da maganan auransu koko? Annurin fuskar Aryan da Abba ya dauke kamar an dauke wuta. Itafa ummi da gaske tayi maganan dan sam batasan halin lubna ba amma Abba da Aryan sunsani. "Dear dan Allah karki kara min wannan maganan ni naki jinin auren dangi" Abba yafada. Aryan mikewa yayi yabar musu falon dan miskilancinsa ma babu abinda zai iya cewa ummi. Nana ma tashi tayi tabarsu awurin dan harga Allah ta tsani lubna amakaranta daya suke kuma tana ganin dukkan abinda takeyi kama daga rungume rungumen mazan datakeyi ko agaban uban waye amma itama bata fada wa ummi ba amma fa tayi alkawarin inhar aka tilasta wa Ya Aryan auren yar iskannan saita fada musu dan har video take mata in tana wannan shashancin as evidence. Abba yakara warning ummi karta kara masa maganan auren Aryan da Lubna amma sam bai nuna mata dalilinsa nayin haka ba, shiko kadan bai ki jinin auren dangi ba kawai sabida lubna ne da uwarta. Kullum sai anty Aisha ta kira ummi tafada mata maganan banza cewa ita ke hana Abba ya aura wa lubna Aryan shiyasa itama ummi takeso taga ko zata iya shawo kan uban da dan ko Allah zaisa su yarda gashi kuma batayi nasaran hakan ba. Halin Abba da Aryan sai Allah saikace yan biyu.

******
Mama da maimoon ne afalo sunyi tsuru tsuru da ido tun jiya da daddy ya tafi asibiti da Noor bata kirashi ba kuma shima baikirata ba. To me zata cemasa? Ya jikin Noor bayan tasan ita tasata awannan halin? Itafa addu'a ma takeyi Allah yadauki ran Noor kowa ma yahuta(Allah yafiki mama). Maimoon ko wayarta ta dauka tacigaba da game dinta kamar babu abinda ya dameta da ciwon yar uwarta.( Allah ya kyauta)

********
Anty Aisha ce zaune a babban falon ta a sama tana waya da wata kawarta naji tana cewa" ki kyale yar banza wlh sai Aryan ya auri lubna, yo in naka bai rufa maka asiri ba na wajene zai rufe maka? Yanzu ki kalli lubna wani namiji ne bai san halinta a waje ba kuma na tabbata bazasu yarda su aureta ba.In ba rufa rufa nayi naga Aryan ya aureta ba haka zan zauna da yarinya gode gode agida? Hajiya shamsiyya wadda suke waya da ita tace" haba Aisha saikace anmiki asiri,yanzu wannan matar mai kama da aljanu ne tafi karfinki? Malam gangaran ai shine mafita kawai muje wurinsa amana maganin 'yan taurin kai" dariya anty Aisha taayi kamar wata tsohuwar mahaukaciya tace" shiyasa nake yinki shamsi kinsan duk wata hanyar da zamuyi mu magance matsala, gobe zanzo saimu tafi wurinsa" ahaka suka shirya yadda zasu tafi wurin boka (wa'iya zubillah. Allah ya wadar da iyaye mata masu wannan halin Allah kamana katangan karfe da mugu). Tana aje wayan lubna tashigo fuuu babu ko sallama tana wani kumbure kumbure " nifa mommy Allah na gaji da irin halin da Aryan ke nuna min haba. Saikace banida gata, duk mazajen danake nima shikadai naji inaso tsakani da Allah amma kuma ace yaita juyani kamar waina? Anty Aisha takamo hannunta tazaunar da ita " karki damu yar mommy munkusa yin maganin dan banzan ai badai ko kula ki bayayi ba toh daga gobe zai fara kula ki kinji? Murmushi lubna tayi tana jin dadin maganan mommyn nata. Hmmm ba gilin gilin ba tayi mai, wasa kukeyi da yaron malamai masu hadda fa.

Ya wasan zata kaya ne tsakanin su anty Aisha da Aryan? Shin zasuyi nasara? Zamuji agaba insha Allah.

Happy independence.🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬 Allah ya bamu zamu zaman lafiya a kasar mu Nigeria ka bawa shugabannin kasanmu ikon yin adalci atsakanin mu.

Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 9_10

Washe gari aka bawa Noor sallama ko gida Daddy yaki barinta ta tafi. Daga asibitin Daddy yasa driver dinsa yakaisu anty jamila abuja tunda ta jirgi sukazo to yanzu kuma da Noor zasu koma, gashi itakuma batada passport. Tayi kuka sosai saboda zata rabu da daddynta sanadiyyar su mama. Anty jamila nata rarrashinta har suka shige mota. Ahanya ma taki cin wani abu sai ajiyar zuciya takeyi alaman tasha kuka. Sun iso garin Abuja misalin karfe 12:00pm, straight gidan uncle saif suka tafi. Yaran anty jamila hanan da hanifa wadda suke sa'a da Noor sunyi murna sosai ganin abokiyarsu kuma 'yar uwarsu. Itama Noor dintayi murna atleast yanzu zata huta ta sake. Cikin dakinsu su hanifa suka kaita sunata janta da hira, anty jamila ce ta shigo hannunta rike da tray din abinci. "Noor taso kici abinci kisha maganinki na rana" anty jamila ta fada tana ajiye trayn agefen gado. Noor turo dan karamin bakinta gaba tayi,itafa harga Allah batasan magani. Dariya su hanifa suke mata itakuma sai shagwaba take zubawa anty jamila(hmm su Noor abin nema yasamu) wacce keta lallabinta taci abinci, abakinta ma take bata har tagama cin abincin, sabon drama akayi kafin ta yarda ta shaa magani. Bayan tasha anty jamila tasa Noor taje tayi wanka hanan kuma ta fiddo mata da wata doguwar riga mai kyau blue colour yasha adon white stones. Fitowa tayi da towel daidai kugunta tana tsane dogon sumanta. Su hanan da hanifa baki galala suke kallon Noor, gsky Allah yayiwa Noor baiwar diri kaiii. Itako bama ta kula da kallon dasu hanan suke mata ba. Zama tayi ta shafa mai ta dan murje fuskarta da powder ta sha fa lipstick, asananne hanifa tayi magana"wlh Noor duk mijinda yasameki ba karamin sa'a ya kwasa ba, kalli bombom dinki saikace kinsa tintin wann.." Shiru tayi sakamakon bige bakinta da hanan tayi" kincika surutu kamar wani tsohon radio, fadi ba'a tambaya ba" itako hanifa sai aika mata da harara takeyi tana rike da labban bakinta, Noor sai dariya takemusu, fadansu na birgeta baya wuce two minutes sun shirya. Ahaka suka cigaba da argument dinsu itako Noor sai kallon drama take tana dariya.

******
Daddy bai koma gida ba saida yagama yanke hukuncin dazai dauka akansu mama. Yasan weakness dinta kenan 'yarta kwaya daya wato maimoon dan haka da ita zaiyi amfani ya koya mata hankali. Gidan wani abokin aikinsa alhaji ja'afar yatafi. Maigadin gidan ne ya bude masa gate bayan yayi horn, dama yariga yasanar da abokinnasa zuwansa dan haka ya samesa agida. Yasamu tarba mai kyau awurin uwargidan alhaji ja'afar. A babban falon sa na baki daddy yazauna bayan an sanar dashi ga alhaji nan zuwa. Wani dattijo ne mai kimanin shekaru 60 yashigo falon dauke da sallama abakinsa. Hannu suka sha da daddy irinna abokai dinnan. Uwar gidan alhaji ja'afar hajiya halima ta gabato masa da abin motsa baki ,tare sukaci shi da alhajin suna hira. Bayan sun gama ci Daddy yace" alhaji dama da wata magana nazo dukda ba sabuwar magana bace, magana ne wadda aka dade anayinta amma sanadiyyata aka watsar dashi. Wato alhaji dama abaya nayi tunanin Sam bazanyiwa yarana auren dole ba amma kuma a halin yanzu, yara sun zama abinda suka zama sakamakon wasu iyaye matan." Tuni alhaji ja'afar ya harbo jirgin daddy amma baice komai ba sai murmushin dake dauke afuskarsa. Daddy yacigaba da cewa" inhar bazaka ki ba alhaji kamar yadda kanema abaya yau gashi nima ina neman alfarma, ina nemawa 'yata maimunatu auren danka Mahmud " murmushin fuskar alhaji ne ya fadada abinda yadade yana so gashi yau Allah yabasa aruwan sanyi. " wlh ni na dade da yarda da wannan zancen, ai dama tuntuni da yanzu ma anyi auren domin ba karamin so naga Mahmud yakewa maimoon ba amma Alhamdulillah, saidai kuma wani hanzari ba gudu ba, ina fatan ita yarinyar zata yarda" "ai karka damu alhaji tunda ni nazo na nema aikasan babu wata matsala insha Allah" haka sukacigaba da tattaunawa akan yan uwan alhaji dazasu zo su nema auren Mahmud din officially. Sai dayayi sallan la'asar yabar gidan yanata sake saken yadda sai bullowasu mama da maganan auren.

Yana isa gida ko ta kansu baibi ba, itama mama ko ajikinta tunda dai bada Noor ya dawo ba. Maimoon ma sai murna takeyi tace " mama wlh bakiji wani irin farincikin daya ziyarci zuciyata ba da wannan shegiyar bata dawo ba, amma saidai matsalata daya yanzu wazai rika yin aiki da girki kingafa niba iyawa nayi ba" mama ta mata hararan wasa tace" karki damu nayiwa hafsu magana gobe zata kawomin masu aiki guda biyu" murna wurin maimoon kamar me(ayya yarinya kin kusa kuka). Daddy ne ya fito yawuce su ya tafi dakin Noor yana waya da ita tana fada masa inda ta ajiye takardun makarantarta wadda za'a yi amfani dasu wurin nema mata anan Abuja. Da harara su mama suka rakashi dashi harya bacewa ganinsu. Tsaki maimoon tayi tace"wlh mama duk da yarinyarnan tabar gidannan amma da alama bazata bar min babana ba, haba yanzu kuma metakeso Allah kadai yasani"mama bata ce da ita komai ba tana wani kunkuni wadda ita kadai tasan me take fada.

********
Su anty Aisha ne da kawarta Hajiya shamsi a gaban boka gangaran, anty Aisha ce tace" boka dama yaron dan uwana ne bayason yata itakuma tana sonsa gashi mahaifiyar yaron itama ta bada nata gudunmuwan wurin hana dan uwana yarda da auren yaren, nikuma harga Alla..." Bata karasa ba sanadiyyar tsawan da boka yamata" ke!!! Karki kara kiran min sunan wani Allah anan aida kinsan dashi bazaki zo nan ba"anty Aisha ta tsorata da sauri tace"kayi haquri boka"(hmmm). Boka yayi wasu incantations(addu'o'insu na bokaye) amma sam baiga wadda yakeso yagani ba hasalima saiwani haske yake gani amma dan ya riga kware acuta yayi kamar yaga komai yace" shikenan wannan aikin ai mai sauki ne amma yanzu ki ajje min dubu dari biyu wadda zan aiki aljani zuruu yayimin wata siyayya"(kunji wani karya, ashe aljanu ma nazuwa shopping mall😂😂). Babu wata wata anty Aisha ta zaro bandir din dubu daya guda biyu ta ajemasa agabansa. Hajiya shamsi tace" toh boka yaushe zamu karbi magungunan, ko yanzu aljani Zuruu zaije yayi siyayyan yakawo ka hada maganin"? Boka ya watsa mata wani kallo tayi saurin tsuke bakinta shikuma yace" zuwa sati mai zuwa zaku iya zuwa ku karbi maganin" godiya suka masa suka fito daga dan bukkan nasa wadda ke saman wani tsauni, ahankali suke gangarawa gashi sunci uban takalma na manyan matan Abuja, wani dan dutse ne anty Aisha ta taka suuuuuu kakeji tana tafiya kasa da sauri kamar ta hau lilon sliding. Dariya ne yaso kama hajiya shamsi amma ta dake tadan kara Sauri harta karaso wurin anty Aisha wacce tuni takai kasa sai rike kwankwaso take tana yatsina fuska alamun zafi. "Sannu ya akayi hakan yafaru" hajiya shamsi tafada tana taimakawa anty Aisha ta mike. Ahankali ta taka har wurin motansu sannan hajiya shamsi ta tada ita suka tafi.

*******
Yau Dada tayiwa su ummi zuwan bazata wadda hakan yabasu mamaki sosai, Dada dasai an kai ruwa rana take yarda tazo hutu anan Abuja yau saigata batare da katin gayyata ba. Sosai su ummi sukaji dadin zuwanta dan Dada akwai dadin zama amma fa akwai surutu kamar ba bafulatana ba duk abinda yazo bakinta ita babu ruwanta fada takeyi. Nana ce tashigo dakin ummi dake anan Dada ke zama duk lokacin data zo. Sanye take da wani gubyun wando dadai guiwarta sai riga armless da kadan ya rufe cibiyarta earpiece na kunninta tanajin waka, tunda ta shigo Dada ke watsa mata kallon rainin wayo dama bawani shiri sukeyi ba insuka hadu kamar cat and rat" aikin kenan, babu abinda kika iya sai shiri cikin kananun kaya saikace jikar mongo park , kin aje kafa kamar ta sauro babu wani auki kullum saicin taliyan tsutsa(indomie)" itako Nana ko ajikinta dan itama yan surutun basa kusane dasun kwasheta da Dada. Ummi kam babu abinda tafada dan inda sabo tasaba da wannan hayaniyar tsakanin Dada da Nana, intazo to fa kullum cikin raba fada take tsakaninsu kamar 'yan biyu. Aryan ne ya shigo sanye da suit dark blue yana rike da briefcase dinsa da alama yanzu ya dawo daga aiki. Nan da nan ko ina ya gauraye da daddadan kamshin turarensa. Fuskarnan murtuk babu alaman dariya. " oyoyo dan gidan azeezu, miji agidan Dada makiyanka sun buga dakai sun kasa" yariga ya saba dajin wannan kirarin dan haka murmushin gefen baki kawai yayi, zama yayi kusa da ita yayi magana cikin hausansa mai kama da larabci yace" wifey yau kece a bait dinmu" saikuma tayi narai narai da fuska kamar zatayi kuka tace" yanzu mijin wai ace ban isa nayiwa wannan yarinyar mai kama sa kwarangwal magana ba saita wani hauni da ihu saikace zatacire dan tsohon dodon kunnena" idonsa ya mayar kan Nana danya San da ita Dada keyi shigan dayagani ajikinta ne yasa ya gane abinda Dada ke nufi"hey, will you get out and change this useless outfit of yours " yadaka wa Nana tsawa wadda hakan yasata fita da gudu kamar zatayi kuka. Itakuma Dada tayi wani murmushin jindadi tace" yawwa ko kaifa mijin shiyasa nake kara sonka kamar na tare agidanka amma babu daman yin haka Kasan ance fas lo ( first love😂) yafi Shiga rai tokaga babu yadda zanyi nabar wannan tsohon" shi maganarta ma dariya yabasa kawai ya girgiza kai, sai lokacin ya lura da ummi dake zaune acan gefen gado dan tunda ya shigo idonsa ke kan Dada, gaida ita yayi sannan yamike ya wuce bedroom dinsa.

Yana Shiga yafara tube kayan jikinsa har yarage dagashi sai boxers sannan ya wuce bathroom yadan watsa ruwa. Yana fitowa ya dau wayarsa ya kira ummi akan Nana takawo masa abincinsa daki. Yana aje wayar ya cigaba da shafa mansa ya fesa turare,closet dinsa ya nufa inda yake ajiye kananun kayansa yabude yadau 3qtr da wani polo green yasanya. Yana fitowa daga closet din daidai Nana tayi masa knocking tashigo da abincin. Har zata fita yace"ke" juyowa tayi atsorace dan yadda ma yakirata bataji da kyau ba inkuma ta fita binta zaiyi ya kifa mata mari akan meyasa batazo ba kuma taji ya kirata, ohhh Ya Aryan sai Allah. " ki fita harkan Dada, whenever she complains to me about you again sorry to say, RIP" yamata alama da hannunsa yana yanka wuyarsa, atsorace tagirgiza kai tafice dagudu tabar part dinsa ma. Murmushin gefen baki yayi ya zauna yafara cin abincinsa.

*******
Noor ne dasu hanan zaune afalo suna shan fruits suna dan hira. Wani matashin saurayi kyakyyawa chocolate color yanada dan jiki kuma baida tsayi sosai yashigo da sallama abakinsa duk suka jiyo suka kalleshi, ido ya zaro waje ganin Noor. Da sauri yakaraso yazauna baima amsa gaisuwarsu hanan ba" Noor kece agidanmu yau? Noor batace komai ba sai murmushi kawai data keyi tace"Ya Shareef ina wuni" lfy lau yar lelen uncle nasir. Shareef ya amsa mata. Yayi mamakin ganinta a gidan gashi kuma duk ta rame fiye da yadda yasanta ada. Shareef shine babban yaron anty jamila wadda ke aiki a company din Aryan kuma abokinsa. Su hanan sukace" Ya shareef kashigo muna gaidaka amma ganin Noor saikayi kamar baka sanmu ba" Murmushi mai sauti yayi yace" to ba dole ba ai abin mamaki ne naga lelen uncle agidanmu kuma nasan ba hutu tazo yiba tun da har yanzu ana school." Itadai Noor bata kara cewa komai ba sai murmushinta mai bayyana tsananin kyawunta take. Anty jamila ce ta shigo falon tasamesu suna hira Ya shareef ya gaidata yace" mum yau kawai saiga Noor a Abuja" anty jamila tazauna kusa da hanan tace" ehh wlh dogon labarine dazu muka zo da ita nida dadyynku"bai kara tambayarta komai ba kawai suka dasa sabuwar shafin hiran harda noor aciki, itafa Noor talkative ce saidai intana wurin da bata samu sakewa ba shine za'a ganta tayi shiru. Har maghrib yayi sannan kowa ya mike dan gabatar da ita.

******
Bayan isha'i su Daddy suna zaune a falo shida Mama wadda yanzu tagama sake ranta akan babu wani matakin da Daddy zai dauka akansu saboda abinda sukayiwa Noor. Daddy kamar yasan abinda take tunani yace" hamida kiramin maimuna" kamar bazata motsa ba sai kuma tatashi tafara tafiya kamar wadda kwai ya fashewa aciki tanufi dakin maimoon. Akan gado tasameta tana waya da saurayinta salis." Ke maimoon daddynki yana kira" tsaki moon taja tacewa saurayinnata tana zuwa daddynsu yana kiranta. Mikewa tayi tabi bayan mama sukazo falo. Zama moon tayi akan cushion kusa da mama Daddy ya kallesu ya dauke kai. Ko mai zaice musu oho, abinda su mama suke tunani kenan. "Ke maimuna ya sunan wannan saurayinnaki"? Daddy ya tambayi maimoon take tafara murmushi dan once in a blue moon daddy ke tambayarta maganan samarinta" daddy salis" gyada kai daddy yayi yakara tambayarta"kuna tare har yanzu ko kuwa"? Da sauri mama ta tari numfashinsa tace"ai har gobe suna tare soyayya kuma sai abinda yakaru yanzu ma dashi take waya adaki" shiko daddy kamar abinda yakeso yaji kenan yace" shikenan, daga yau kice masa karya kara kiranki, kice masa babanki yamiki miji" dammm haka zuciyoyin mata biyun ya buga" kan bantan uba, toh wlh nasiru baka isa ba, kayi kadan, yar tawa kwaya daya jal zakawa auren dole?itako moon kuka ta fashe dashi tana cewa bata yarda. Tsawa yadaka musu yace" karku yarda kumaidani sha sha sha, nasan abinda nakeyi sarai, ok wato yarki itace gwal, Noor kuma jaaka ko? Toh wlh bari kuji na fada muku nariga na gama maganar dazanyi kuma babu wanda ya isa yasa na canza maganata"mama ta mike tsaye tana buga kirji tace"ni hamidatu na isa nasa ka canza maganarka naka wasa ne , wlh dani kake zance nasi.." Bata karasa ba taji saukan lafiyayyun maruka guda biyu afuskarta, Daddy yace" badai kina takama da kinada yan uwa masu karba miku baki ba? to shikenan mu zuba mu gani, wlh thumma billahi idan kika yi gigin shiga hanya ta

Please Login or Register in order to submit comment