Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

furtawa yana yamutsa kwantaccen gashin kansa. Da kyar ya mike ya shige bathroom danya watsa ruwa.

******
Bayan sun dawo gida tayi wanka ta rama sallolin da ake binta sannan tayi shirin kwanciya. Anty Jamila ce ta shigo hannunta rike da glass cup cike da ruwa aciki dakuma magungunan Noor. Noor na ganin maganin a hannunta tafara yamutsa fuska tana turo baki gaba. Itafa in akwai abinda ta tsana to magani na cikin su. Saida aka lallabata sannan tasha maganin tana kukan shagwaba. Batawani jimaba bacci ya dauke ta.


******
Washe gari da sassafe Mahmud yakama hanyar gidan Daddy dan yanzu wulakancin Moon yafi karfin tunanin me tunani. Jiya da abokan sa suka zo babu irin rashin mutunci da Moon bata musu ba, daga karshe ma fushi sukayi suka bar gidan ko abincin dayasiyo ma basuci ba. Tuki yakeyi amma zuciyarsa cike take da bakin cikin matarnasa. Abakin gate din gidan ya tsaya yayi horn. Megadi ya budemasa gate din ya shigo. Mamaki ne ya kama su daddy ganin surukinnasu da sassafe dan alokacinma breakfast sukeyi. Hararan takaici Mama ke ta aikawa Mahmud tunda ya shigo. Tsugunnawa yayi har kasa ya gaidasu Daddy cike da girmamawa. Kujera daddy ya nuna masa ya zauna. Bayan sun gama cin abinci Mama taki matsawa awurin dantanaso taji meke tafe da Mahmud din, tasan zuwansa da sassafennan ba alkhairi bane. Mahmud kansa na kasa yafara maidawa Daddy abinda Moon tamasa. In ran daddy yayi dubu to ya baci, mikewa Mama tayi da sauri tace" kaga Ahmad kake ko Mahmud whatever, wlh karyanka kace zakazo har cikin gidana kazo ka aibanta min 'ya, wlh kayi kadan, danma ka gode mun baka ita shine harkanada fuskar zuwa kaci mana mutunci ka zageta iyye"? Saikuma tajuya kan Daddy wadda mamaki yama gama rufesa tace" Nasir kagani ko, kaga abinda nake gudu ko,na tabbata da ka aurawa Moon wadda takeso daba haka ba amma dama Ku maza halinku day..." Bata gama rufe baki ba daddy ya daka mata tsawa yace"ke Hamida ki iya bakinki, ni yazo ya sama bakeba, what gives you the right to talk before me" shi Mahmud mamaki halin Mama yabasa, ashe dai Moon ba akasa ta dauka ba, lallai in babba ya yadda girmansa karami zai hau kai ya taka. Shidama yasani ma bezo ba inda yasan outcome din kenan. Daddy yajuyo ya kalleshi cikeda tausayi yace" Mahmud jeka, insha Allah zuwa anjima zanzo har gidan nasami Moon din kaji"? Kai kawai ya daga sannan ya mike jiki a sanyaye ya fice daga falon, Mama kuma tana rakasa da wani irin kallon tsana. Bankadeta daddy yayi ya wuce ta gefen ta yana mamakin irin rashin kamun kai na Mama. Tsaki tayi ta zauna tana surutai da zage zage.

*******
Yau beje aiki ba, haka kawai yaji ma zaman Nigeria ya gunduresa tunda maganar auren nan yataso. Wayarsa ya dauka ya kira Muhsin abokinsa ya narrating masa danshi kadai yake iya sharing problem dinsa dashi, ko Shareef ba kullum yake fada masa damuwarsa ba. Instead muhsin yaji tausayinsa saima dariya daya dinga masa yana masa sharri akan saisunzo cin shinkafan biki. Ransa sosai ya baci daga bayama ya kashe wayar yanajin ransa na kara baci. Shifa tunkafin ayi aurenma yaji ya tsani yarinyar bamayason ganin kalarta.

*******
Yau jikin Noor yayi sauki sosai tunda bata tafi makaranta ba, tare ma sukayi girki da mai aikin gidan dan jikinta yasaba da aiki kuma dukda watannin data dauka agidannan sam bata zama me kyuya ba. Ko kallon abincin ma batayi ba sai aikin cin snacks dama aikin kenan. Inkuma zata ci abinci toh ba sosai ba.


Da yamma Daddy ya tafi gidan Moon kamar yadda ya fada yamata tatas harda kukanta kamar na Allah. Sosai yaja mata kunni akan 'batawa miji rai, amma kamar ma ya shige ta wannan kunnin ne ya fita ta wancan.


Yau polisawa suka raiding wani club inda aka kwashe yan mata da samari gaba dayansu. Wani irin bad party suka hada harda su Lubna. Sunan party din wai *Wild and wet party" wasannin banza akeyi marasa kyan gani. Maza ne da mata ke masha'ansu son ransu. Wani acikin ma'aikatan wurinne ya kira polisawa ganin wasan na wuce gona da iri dan wasu tantiran har zina sukeyi agaban mutane. Lubna kuma da wani bad guy aka kama toilet suna zina, babu kayan kirki ajikinta haka aka jasu zuwa motan polisawan tanata wasu surutai cikin maye.(Wa'iyazubillah, Allah ka karemana imaninmu, ka kare mana 'ya 'yanmu da kannenmu).


********
Lokaci ba wiya, yau yarage wata daya bikin su Noor da Ya Shareef. Akowani bangare anfara shirye shirye ba kama hannun yaro. Ummi dakanta tatafi Dubai da wata kanwarta Anty Ounaisa, siyayya me tarin yawa sukayi na kayan lefe inda aka hada lefe kusan akwatuna guda 24. Komai dam dam ba'a magana. Sunkai kusan kwanaki uku kafin suka dawo. Nana karan kanta batasan da maganan bikin ba.

Hakan ya kasance a gefensu Anty Jamila, siyayya sosai sukeyi harda 'yan uwansu Daddy su Anty umaima. Wata kawar Anty Jamila Hjy Balaraba itace aka bawa hidimar gyaran jiki Noor. Hjy balaraba matace wayayya wacce tasan kan jikin mace dakuma gyara. Daga Sudan take amma tana aure anan Nigeria itama a Abuja take da zama. Har yanzu Daddy ko uffam bai fadawa Mama ba akan bikin. Noor kuwa bama tasan wainan da ake tauyawa ba. Karatunta takeyi sosai saboda sunkusa fara exams nan da sati biyu zasu tafi 200lvl.

Oga Aryan shima yadda take a wurin Noor hakan takasance agefensa. Shiyama mance da wani aurensa da za'ayi. Aikinsa yakeyi cikin kwanciyan hankali yariga yagama planning irin wulakancin dazeyiwa so called amaryartasa.(kardai ka tabo kawar Dada yawwa,hatta mu tsoron masifan ta muke ehe)


Ya Shareef andage sai suburbuda love akeyi da matarsa to be Na'ima. Shima shirye shiryen yake haka zalika Na'iman.


Yau Hjy balaraba tazo gidan Anty Jamila dan yau zata tafi da Noor gidanta har zuwa lokacin bikin, dan sai ana kwana biyar da bikin zata dawo gida. Daga can zatana zuwa makaranta. Bayan su Noor sun dawo daga makaranta, taci abinci Anty Jamila tace da ita" habibty shiga ki hado kayanki a akwati, zikibi Hjy balaraba akwai gyaran danakeso tamiki kinji" babu tunanin komai aranta ta mike ta shiga dakinsu tafara shirya kayanta a dan akwatinta. Tana cikin shiri su Hanan suka shigo, hanifa ta zauna abakin gado tace" Noor wani irin gyara za'amiki, nifa nasan Hjy balaraba gyaran amare takeyi" harara Noor ta watsa mata tace" toh sai akace miki ni amarya ce, halan kawai wani abun daban zata mun" kyaleta sukayi amma tabbas sunfara zargin wani abu, aide in bikin Ya Shareef kadai za'ayi meyasa za'ana kawo kayakin kitchen dasu abubuwan da'ake siyowa amare. Haka tagama shirinta sannan ta rolling dankwalin abayanta akai ta dau wayarta ta sallami su Hanan tafice falo zuwa wurinsu Anty Jamila. Hjy Balaraba kam tanata mamakin kyawu irinna Noor saikace ba bahaushiya ba dan ita atunaninta Noor din bahaushiya ce. Har waje Anty Jamila ta rakasu sannan tadawo ciki bayan sun tafi. Agaban wani tangamemen gida Noor taga sun parking. Sosai tayi santin kyawun gidan. Babban gida ne da part guda biyu sama da kasa. Afalo taga wasu yan mata guda hudu suna zaune suna hira, tunda su Noor suka shigo suke kallonta, kunya ne ya rufe Noor da irin kallon dasuke binta dashi. Awani dan madaidaicin daki Hjy Balaraba ta sauki Noor. Daki ne hadadde sai tashin kamshi yake, dama tunda tashigo gidan takejin wani irin sanyi da kamshi yana ratsa gaba daya ilahirin jikinta. Wani dan madaidaicin gado ne adakin sai wardrobe mai kofa biyu, sai kuma dan dressing mirror, komai na dakin tsaf tsaf." Kije kiyi wanka ki huta anjima zamu fara abinda yakawomu kinji 'yata" kai kawai Noor ta gyada sannan ta fara warware dankwalin abayan dake kanta. Take dogon sumanta ya warware har gadon bayanta. Wardrobe din dakin ta bude taga anjera towel kusan guda biyar, wani pink baby towel ta dauka ta wuce toilet. Sabulan wanka da kuma turaruka masu kamshi tagani, ruwan wanka ta hada a bathtub din mai dan zafi sannan ta shige tafara cuda ko wani lungu da sako na jikinta. Ta dau kusan minti ashirin sannan ta dauro alwala tafito. Wasu mayuka masu kyau tagani anjera asaman dressing mirror, dayake ana zafi shiyasa batama shafasu ba. Akwatinta tabude tafidda wata doguwar riga mai dan kauri tasanya. Doguwar hijab dinta ta fitar dan lokacin har anfara kiran sallan maghrib. Sallaya ta shimfida ta tada sallah. Bayan ta idar ta zauna a wurin har akayi sallan isha sannan itama tayi. Tana idarwa taji anbude kofa anshigo, wata yar budurwa ce akalla zata kai shekaru 16 ta shigo hannunta dauke da basket na abinci" gashi mama tace kici saiki fito kisameta afalo" Yar budurwar ta fada tana sakarwa Noor murmushi. Gyada kai Noor tayi itama tana murmushi. Bayan ta idar da azkar ta cire hijab din jikinta, basket din abincin tajawo gabanta, kuloli guda uku ne, daya farfesun kaza ne wadda yaji kayan hadi na musamman sai tashin kamshi yake, dayankuma fried pasta ne dayaji kayan lambu da su hanta, na ukun kuma chips ne akasoya da kwai incase bazataci fried pasta dinba. Kunun aya mai sanyi ne a jug shima yaji kayan hadi na musamman. Plate ta ciro ta zuba farfesun nan da chips taci, batawani ci sosai ba amma tas ta shanye farfesun danba karamin dadi yamata ba. Kunun ta diba cikin cup tashanye sannan tayi gyatsa tace Alhamdulillah. Basket din ta dauko ta fito daga dakin ta wuce falo. Azaune taga Hjy Balaraba da wannan yan matan data gani lokacin dasuka shigo. Mikewa Hjy Balaraba tayi takallesu tace" mujenku ba" dukkansu harda Noor suka bita zuwa wani daki mai girma sosai sai tashin kamshi yakeyi, duk cikin dakunan gidanma kamar wannan yafi kamshi. Towel taba kowannensu tace su tube su daura. Da mamaki Noor takarbi towel din azuciyarta tace" toh babban magana, ko me zamuyi oho". Kowacce acikinsu ta tube ta daura towel din amma banda Noor wani irin kunya takeji. Hjy Balaraba tayi murmushi tace "'yata karki damu aiba awuri daya za'a muku gyaran ba" abayan wani kofa ta labe ta tube kayan sannan ta daura towel din wadda iya rabin cinyarta ya tsaya. Bayan ta fito kowa yadinga kallonta suna mamakin irin wannan kyau ga kuma shape kamar ita tayi kanta. Su biyar ne so kowacce da dakin da Hjy Balaraba tanuna mata ta shiga. Hjy Balaraba itada kanta zatayiwa Noor gyaran dan haka, wasu kwalabe ta dauko da alama turaruka ne aciki ta mike wa Noor tace ta shafa su ajikinta. Babu musu Noor ta karba tana shafawa ajikinnata. Wani irin kamshi na musamman turaren keyi me dadin shaka,har wani lumshe ido Noor keyi tana cigaba da shafa turaren ajikinta. Bayan tagama saida tashafe kusan 30 minutes kafin Hjy Balaraba tafara shafe mata kwabin dilka akowani bangare na jikinta, lungu da sako, kunya kamar ta kashe Noor dan warware towel din tayi. Bayan angama shafeta da wannan kwabin kuma ta dauko wani abu a kofi tabawa Noor tasha, da dardar takarbi abun amma jin yayi mata dadi takafe bakinta ta shanye shi tas harda tande baki, wani tsumin Hjy Balaraba ta kuma bawa Noor tasha shima kamar waccan yanada dadi sosai. Wani inji Hjy Balaraba tasata ta shiga, abun za'a iya kiranshi da steaming machine, takai kusan awa guda aciki kafin machine din ya mutu dakanshi. Haka Hjy Balaraba tadinga durje wannan dilkan daga cikin Noor tas sannan tasata tashige bathroom din dake cikin dakin datyi wanka. Tun a wannan ranan Noor tafara ganin changes ajikinta, saitaji tayi wani irin sumul kamar ba itaba. Data fito daga dakin taduba katuwar agogon dake falo taga sha daya saura. Tana shiga dakin da aka sauketa bata wani dau lokaci me yawa ba bacci ya dauketa. Washe gari da safe tana cikin shiri Hjy Balaraba ta shigo dakin hannunta dauke da Kofi da kuma wata yar jaka ta mikawa Noor. Nonon rakumi ne fresh tabata saida tashanye tas sannan Hjy Balaraba tace" ga wannan jakan, hijab ne da niqab shi zaki sa saboda ba'aso mace tana dilka kuma tana shiga rana. Amsa Noor tayi ta bude jakan, farin hijab ne da niqab me kyau aciki. Babu yadda ta iya haka nan tasa shi amma kuma ba karamin kayu tayi ba kamar wata balarabiya.


Yau mamaki kamar ya kashe Nana ganin irin kayan da su ummi suka dawo dashi, datayi tambaya sai suka ce mata na wata yar uwarsu ce a saudiyya. A makaranta kuma data ga Noor da hijab da niqab sai abun ya kara kulle mata kai danta tambayi Noor saitace mata wai dilka ake mata. Bata kara cewa komai ba tasan sarai komai da lokaci zai bayyana.


Oga Aryan fa tunda yaga su ummi sun dawo daga Dubai da wannan kaya tukuru'u sai hankalinsa yakara tashi, lallai ba wasa akemasa agidannan ba. Shi ko amafarki betaba ganin inda akayiwa namiji auren dole ba amma gashi akansa za'a fara. Bakin ciki kamar ya kasheshi.


Moon kuwa babu abinda ya ragu sema wadda ya karu cikin rashin mutuncin datakeyiwa Mahmud. Kuma tanayine danta samu goyon baya dari bisa dari daga wurin mahaifiyarta. Shiko Mahmud ba karamin damuwa yake ciki ba kuma be taba fadawa iyayensa ba. Yanzu ko sha'awarsa ta motsa Indai ba danne Moon din zeyi ba to saidai ya mutu amma ko ajikinta.



Yau sati biyu kenan da akeyiwa Noor gyaran jiki kuma sosai ta canza dan jikinta kamar wani kwai, ga tsumin da Hjy Balaraba kebata wani lokaci saita rika jin wani feeling na taso mata saita rasa yadda zatayi. Yanzu sun fara exams wadda by the end of next week zasu gama. A yanzu kam Noor tafara zargi akan wannan gyara da ake mata dan ita a iya saninta amare kadai akewa wannan irin gyaran. Toh amma meyasa babu wadda yamata maganan, kuma ai ita batada wani saurayi balle ace har ansa mata rana.


Su Anty Jamila kam shiri akeyi bana wasa ba. Komai na gidan amarya ya gama haduwa saura aje a shirya mata su. Yanzu kam su Hanan sunsan da maganan bikin dan Anty Jamila ta fada musu kuma ta gargade su akan fadawa Noor hakan yasa suka ja bakinsu sukayi shiru, amma ba karamin tausayi Noor tabasu ba, a wannan zamanin yaushe ake wani yayin auren dole, yo auren dole mana tunda ita amaryar bata sanda bikinta ba.



Agurguje


Yau saura sati daya biki mutani har anfara cika a gidan ummi hakazalika bangarensu Anty Jamila dan anan Abuja za'a daura auren. Mutanin saudiyya suma wasunsu harsun fara zuwa, mutanin Adamawa ma haka duk anfara zuwa. Kankace me gida ya fara cika saikace gobene bikin. Aryan tunda yaga haka saima yadena kwana agidan, yakoma sabon gidansa yana kwana dan har ankai jeren Noor sun Anty umaima da sauran yan uwa. Saidai part dinsa komai shi da kansa yayi. Ummi ba tace masa komai ba duk da tana sane yadena kwana agidan. Su Dada da hajja mahaifiyar ummi anhadu sai gwaranci sukeyi, ita Dada tana Hausa itakuma hajja tana larabci, haka ake musu dariya insuka fara hiransu kamar sunajin mesuke cewa.


Anty Aisha da lubna tunda sukaji labarin auren Aryan suka fara sabon bori akan lallai saisunkawo cikas a wannan bikin. Anty Aisha sai kumburi takeyi tana fashewa akan meyasa Aryan zai auri wata ba yarta ba(🙄🙄ba zance komai ba fans din MJIN TACE su zasu baki amsa).



Yau Noor zata koma gida tama riga tagama kimtsa kayanta. Da rana su Hanan dakansu sukazo suka dauke ta. Tunda su ka shigo gidan take mamakin yadda aka canza abubuwa dayawa na gidan, ga mutane ko ta ina hayaniya na tashi. Tunda su ka shigo falon mutani suka fara guda, gabanta ne taji yayi ras, Allah yasa de bada ita akeyi ba. Anty Jamila ce takama hannunta zuwa falon uncle saif. Mamaki ne ya kamata ganin daddynta suna hira da uncle saif din. Da gudu ta fada jikinsa ta rungumeahi tana jin dadi. Shima Daddy rungumeta yayi, sun dauki kusan two minutes kafin suka zauna. Daddy yakamo hannunta Noor da kyau cikin nasa yace "Nuwaira" ahankali ta furta na'am. Ya kara matse hannunta cikin nasa yace" lallai kincika 'ya tagari me bin umurnin iyayenta kuma nasan duk alfarmar dana nema awurinki bazaki taba cemin a'a ba" jikin Noor duk yayi sanyi dukda batasan inda maganar Daddy ya dosa ba. "Noor na miki miji kuma yau ya rage kwana biyar kacal da daurin auren ki" dammmmm haka Noor taji gabanta ya fada, kenan duk zarginta yazama gsky, inna lillahi wa inna ilaihí raaji'uun. Wasu zafafan hawaye taji yana gangarowa daga idanunta, Daddy yayi ajiyar zuciya yace" Noor kin amince da zabin daddynki"? Kusan minti biyu shiru kafin ahankali tadago da jajayun idanunta ta kalli daddy ta bude baki ahankali tace".........



COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/14/23, 7:19 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH



PG 27_ 28



Ahankali tace " na yarda Daddy na" sai kuma ta rushe da kuka me sauti, Anty Jamila ta taso takamata suka fita daga falon, Daddy yabita da kallon tausayi yana mejin zafi azuciyarsa. Suna shiga daki ta kwace jikinta daga rikon da Anty Jamila tamata ta kwanta saman gado tana kuka mecin rai. Su Hanan dama sunsan hakan zata faru, da kyar suka rarrasheta tayi shiru.


Abangaren su ummi kuwa anata shirin shagalin daza ayi, kama daga su Arab night, su mother's day,dinner da kuma walima. Suna zaune a daki sun baje wasu kaya masu kyau itada kannenta biyu mata Anty ounaisa da Anty Raihana suna dubawa. Nana ce ta shigo tana ta bori dan yanzu takeda labarin cewa yayanta ne zeyi aure. Wuri tasamu ta zauna kusa da Hajja tace" yanzu ummi dama Ya Aryan ne zeyi aure ina matsayin kanwarsa kwaya daya amma ace ko labari banda shi"? Dariya su Ummi suka fashe dashi dan yadda tayi da fuskarta ita adole tana fushi, ummi ba komai yasa tayi hakan ba dande kawai karta fadawa Noor cewa auren yayanta za'ayi itakuma Noor ta zargi wani abu shiyasa. Fushin Nana be wani lasting ba ganin uban kyawawan kayan da aketa budewa, su Arabian gowns ne masu kyau wadda kudinsu sun fallasa Kansu da Kansu. Wani royal blue abaya Nana ta daga tace" ummi wlh wannan kayan inama ace ta Noor ce daba karamin amsarta zeyi ba" ummi ta juyo ta kalleta, ko de tasani ne? Amma babu alaman hakan a fuskarta. Haka sukayita bude kayan suna yaba kyawun dayayi, Dada da Hajja sun juya nasu side din suna gwarancinsu na fama sai faman kyalkyata dariya sukeyi idan dayansu yafadi wani kalma me ban dariya.


Agefen ango kuwa abokansa daga Saudi su Muhsin da abokansa biyu ne suna hira wadda shikuwa jinsu kawai yakeyi ko kala bece musu ba. Muhsin ya kalleshi yace" wlh Aryan tsab wannan banzan halinnaka zai bace, bari akawo maka amaryarka I bet you saita maida kai MIJIN TACE, cos you'll be heads over toes for her" dariya wa'nnan biyun suka fashe dashi, Aryan wani dogon tsaki yayi shi duk abun duniya ta issheshi, shi meyasa ma becewa Abba bai amince da wannan auren ba, ai kowa yanada freedom of speech dinsa. Knocking sukaji akofa, Muhsin yatashi yabude, Nana ce tsaye abakin kofa se turo baki takeyi ita zata zo ta nunawa Ya Aryan fushinta akan cewa meyasa be fada mata aure zeyi ba( wannan 'ya kodai tamance da halin yayannata ne), yadda Muhsin ya kafeta da ido kuma yaki bata hanyan wucewa ne yasata tsarguwa. Aryan na lura da yadda Muhsin din yake kallon Nana daka mata tsawa yayi yace " what are you doing here" afirgice dukkansu suka juyo suka kalleshi kamar ma bashi yayi maganan ba ya maida idonsa kan wayarsa yana latsawa, da sauri Nana ta juya aguje tabar wurin azuciyarta tana cewa" toh ni nasa ummi tace ka dawo nan gidan sai bayan biki dazakazo kana wani haurawa kamar flour, garama kayi auren ka ficewa mutane agida". Wani shu'umin murmushi Muhsin yayi yajuyo ya shiga falon yana kallon Aryan yace" Nana has grown so much, she looks cute how I wish nima na samu chance" harara da Aryan ya watsa masa ne yasashi tuntsirewa da dariya yace"Allah yasa ba kaibane babanta, ina iya zuwa wurin Uncle yanzu kuma nasan ba hanani zeyi ba" tsaki yayi ya mike ya shiga dakinsa yana banko musu kofa. Dariya daya daga cikin abokan Muhsin yayi me suna Lukman yace" this guy is really funny".



Yau su Anty Jamila suketa shirye shirye za' a kawo lefen Noor, wasu kuma zasu kai lefen Ya Shareef. Tunda safe aketa girke girken tarban baki. Sai karfe sha biyun rana aka fara kawo lefen Noor, yan uwan ummi mata biyu da kuma yan uwan Abba sukuma kusan rai bakwai, motocine manya manya range rovers guda shida kowani mota dauke yake da akwatuna guda four. Basu gama parking ba sukaji horn alaman wata motarce zata shigo, mamaki ne yakama mutanin dake wurin ganin wata dankareriyar mota kirar latest Mercedes benz fara uban ubansu an nadeta da fulawowi jajaye ta shigo. Driver din daya tuko motar ya fito ya mikawa Anty ounaisa key din motan. Bayan angama shigar da akwatuna daddaya har guda 24 kowa ya hallara afalon tarban baki ana kallon kaya. Babu wadda beyi santin kayan dake cikin akwatinnan ba, kayane ingantattu tsadaddu kyawawa masu daukan ido. Bayan angama duba kaya su Anty ounaisa suka nemi akawo musu amaryarsu suganta. Babu musu Anty umaima ta mike ta fice daga falon zuwa dakinsu Noor. Tunda ta hangeta ana tsantsara mata makeup taketa furta masha Allah tabarakallah. Light makeup ne amma bakuga yadda ta hadu ba, wani sea green lafaya take sanye dashi yayi mata kyau sosai. Anty umaima takamo hannunta suka fito harzuwa cikin falon. Suna shigowa hankalin kowa yadawo Kansu. Duk da kan Noor akasa yake be hanata ji ajikinta cewa ita ake kallo ba. Saida suka karaso har gaban Anty ounaisa sannan ta zauna akasanta. Kamo hannun ta Anty ounaisa tayi tadan ja gelen zuwa baya dan fuskarta ya bayyana da kyau" tabarakallah ahsanul khalikeen" su Anty ounaisa suka furta lokacin dasuka ga fuskar Noor. Kunyane ya kama Noor ta duke kanta tanajin bugun azuciyarta na tsananta. Muryar Anty ounaisa yana mata yanayi da wadda tasani amma kuma tamance da wa dan bata kalli fuskar Anty ounaisan ba. Rafar five hundred guda biyu ta ajewa Noor akan cinyarta ta kuma kamo hannun Noor ta dunkula mata key din wannan hadaddiyar motar dasuka shigo da ita dazu tace" wannan kyauta ne daga garemu yan uwan megidanki, Allah Ya baku zaman lfy ya kauda sharri atsakaninku" kowa a falon ya amsa da Ameen. Sun kara kusan mintuna ashirin kafin suka tafi. Makullin motan Noor ta mikawa Anty Jamila ajiya. Bayan ta koma dakinta tacigaba daga inda ta tsaya wato sana'ar kukanta dama karfin hali kawai tayi da bata fashe musu da kuka a falon ba.

Acan gidan Amaryan Ya Shareef ma hakan ta kasance, ankai lefe, akwatuna masu kyau guda goma sha biyu. Murna akan fuskar wannan ahali ba'a magana dan suna da yakinin cewa yarsu tayi dacen gidan miji.

Har I yau mama batada labarin bikin Noor Dan Daddy da yan uwansa babu wadda ya fada mata, shi Daddy ma cewa yayi sai bayan bikin kafin ya sanar da ita. Yau Moon takawo mata ziyara sai kwanciya take tayi ga kuma bala'in kwadayi har Mama tafara zargin kode Moon nada shigan ciki ne. Moon na cikin cin Apple Mama ta shigo falon tace" ke Moon anya ba cikine da ke ba"? Sai shegen kwadayi kike tayi tunda kikazo Allah yasa ba abinda nake tunani bane. Da sauri Moon ta mike tace" Mama dan Allah karki kara min wannan mummunan fatan, ni ban shirya aihuwa da wannan mutumin ba, wlh inma shine zubar dashi zanyi" dariya Mama tayi tace" yawwa ko kefa ai shine magana, ina ke ina hada jini da wadda aka miki auren dole dashi " haka suka cigaba da hiransu.


Washe gari akayi mother's day agidansu ummi. Dayake farfajiyar gidan nada matuqar girma, kwararrun designers aka kawo suka decorating ko ina gwanin sha'awa. Taron mata ne kawai dan haka maza basu zo ba.

Please Login or Register in order to submit comment