Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ummi, adaddafe ta nufi kofar tabude, shima daidai nan ya bude kofa ya fito, salati kawai yakeyi tasa ta sameshi. Akasa ta sami ummi yana zirga zirga, " ummi" tafada cikin muryan kuka, ummi ta kara so ta rungumeta tana rarrashinta. Jikinta har bari yakeyi, zaunar da ita ummi tayi tana rarrashinta. Saukowa yayi ya zauna a cushion din dake facing dinsu ya rafka uban tagumi. Ummi kam ko ba'a fada mata ba tasan meyafaru dan Doctor Amina ta sanar da ita. Mikewa tayi ta kai Noor dakinta ta shirya mata kayanta cikin akwati dan da ita zata tafi tana buqatar kulawa sosai. Saukowa tayi ta barta adakin, har yanzu yana zaune awurin ya rafka tagumi yana danasanin aikata wannan abun. Fada ummi tamasa sannan ta sanar dashi akan zata tafi da Noor gida. Da farko ya so yayi jayayya amma data bude masa wuta tayi masa tatas haka ya ja baki yayi shuru ya zuba wa sarautar Allah ido. Komawa ummi tayi ta sauke da akwatin Noor da ita Noor din, sai dingisawa takeyi abun tausayi, ko kallonsa ba tayi ba ta fice har wurin motar ummi. Kamar zeyi kuka haka yakeji, har suka shige motar suka bar gidan. Zama yayi dirshan akan stairs din entrance din yana jin yadda kansa ke masa" inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uunn, what have I got myself into" ya kai kusan mintuna goma awurin kafin ya mime jiki ba kwari ya shige ciki.

Not edited

COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/1/23, 8:16 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 45_ 46

D͟✯Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯SW͟R͟I͟T͟E͟✯S͟

Suna isa gida ummi ta fito ta zagaya sannan ta taimakawa Noor dan bata iya takawa da kanta. Ba karamin haushi Aryan yabawa ummi ba, wannan ai mugunta ne, koda ace bai taba wannan abunba amma ai kamata yayi ace yabita ahankali tunda itama farkon yinta kenan. Wato shiga doki ko. Adakin ummi zata zauna dan haka can ummin takaita. Toilet tashiga tahada mata ruwan zafi sosai sannan ta zuba wasu magunguna da zai taimaka mata ya rage radadin datakeji sannan ta fito ta taimakawa Noor din tashiga, sosai ta gasata dan so biyu ta canza ruwan kuma Alhamdulillah yanzu tadan ji sauki. Koda tafito ummi tariga ta fita adakin can ta dawo da tea mai kauri da zafi a cup da kuma peppersoup na kifi da chips tabawa Noor, saida ta make sure taci sosai sannan ta barta. Zani da riga ta sanya ko pant batasa ba saboda irin zafin da kasanta kemata. Kwanciya tayi tana maida numfashi, da zaran ta tuno da abinda yafaru sai ta fashe da kuka tana masa Allah ya isa. Ita a tunaninta muguntarsa ne kawai ba haka abun yake ba. Da har ta fara tunanin kila canzawa yayi ashe dai duk wannan abubuwan dayake mata dan wani tarko ne nasa daya shirya mata. Bacci mai nauyi ne yayi awon gaba da ita inda ta kwanta da bayanta ta bubbude kafafu amma taja bargo ta rufu dashi.

******
Kwatakwata ya rasa me kemasa dadi tun bayan tafiyansu. Kwance yake kan gado ya dafe kansa ya hannayensa, dukda yasha magani amma still zafin bai ragu ba. Yaso ace shi zai kula da kayansa tunda shi yayi barnan amma ummi bata bashi dama ba. Shi yanzu ya akeso yayi, an dandana masa Zuma kuma andauke ta. Irin kallon dayaga Noor take mai tabbas yasan wannan kallon kiyayya ne, da kyar ya samu ya shawo kanta gashi kuma ankoma gidan jiya, yama rasa mafita sai juyi yakeyi kan gado gashi dai yanajin bacci amma yakasa, kuma ko abinci bai ci ba. Ahaka yaita juyi har aka kira sallan zuhr sannan ya mike ya shiga toilet yayi alwala ya fita. Koda ya idar ya dawo gida, shareef ya kira kuma bai boye masa komai ba dan ahalin yanzu idan yace zai boye masa to shine zai cutu,sosai shareef ya tausaya wa Aryan amma kuma ya tausaya wa Noor, duk da matarsa ta girme mata a shekaru amma still bai hanata jin jiki ba balle kuma karamar yarinya kamar Noor ga Aryan din ba kadan ba. Shawara yabashi akan karya tafi gidan ummi yabari saita sauka in ba haka ba wani ruwan zai kuma ballowa, ba umminba ba Noor ba. Haka yayi haquri ya zauna duk tunaninsa akanta ko ya take ciki yanzu. Da kyar yasamu ya hada coffee yasha da biscuit. Har dare babu canji a yanayinsa hakanan ya kwana cikin dacin rai da kunci.

******
Washe gari fa Aryan ya kasa daurewa dole ya shirya da sassafe wuraren karfe bakwai ya tafi gidan ummi. Lokacin suna karyawa da ummi da Nana da Abba wadda yadawo jiya amma babu Noor acikinsu, sam basuyi tsammanin ganinsa ba da sassafennan amma banda ummi,har yanzu Nana da Abba basusan meyafaru da Noor ba saidai sunsan tana gidan kawai batada lfy ne tunda ummi ba barinta tayi ta fito daga dakin ba. Duk ya bi ya sukurkuce a yini daya, duk yadda Abba ya tambayesa amma yaki bashi amsa tunda ya lura cewa basusan meyafaru ba da alama ummi ta rufa masa asiri. Koda ya gaida ummi lfy kawai ta ce masa a takaice. Sai wuki wiki yakeyi da ido alaman akwai abinda yake nema kuma ummi ta lura da hakan, wannan yasa ta mike ta nufi dakinta, yana ganin ta mike ya bi bayanta. Har suka iso bakin kofar dakinta zata shiga ta juya tagansa atsaye a bayanta yayi wani fuskar tausayi, abun har dariya ya so bawa ummi amma ta dake, wai yau Aryan ne ke wannan irin abun saboda mace,macenma dayace bayaso. Lallai wani abun sai Allah. " kar ka kuskura ka shigo min daki na fada ma, dama mu mukayi laifin aura maka ita dukda ka nuna bakaso, toh yanzu ka nuna mana a aikace kuma nagode, saidai fa kasani, ba kyaleka zanyi ba,bar ganin ban fadawa abbanku ba dakaina zan dau mataki akan ka,wlh Aryan koda wasa naga kafanka adakina wai ka shigo wurin Noor toh duk abinda na maka kai kajawo" tana gama fadin haka ta shige dakin harda sa key. Harga Allah he misses his wife so much bazai iya juren wannan horon ba, ayimasa koma menene amma kar a hanashi ganin Noor dinsa. Haka ya juya jiki ba kwari ya sauko falon kasa, Nana ta riga ta tafi makaranta, Abba ma ya fita, haka ya zauna afalo ya kura wa TV ido amma azahiri ba kallon yakeyi ba.

Yau kwana uku kenan yana sintiri agidan ummi amma ko sau daya bata taba bari ya hadu da rabin ransa ba. Ayanzu Noor kam garau take jinta danba karamin gyara tasamu awurin ummi ba. Bata aikin komai kuma babu inda take zuwa kullum tana daki, saidai in Nana tadawo shine zata tafi dakinta suyi hira,ammafa sai in ummi ta lura baya gidan shine take bari ta fito. Ita yanzu tama mance da wani Aryan,sabuwar rayuwarta ta bude taci tasha takwanta. Ummi tama dauka irin kozata yi tambayarsa kosau daya amma kamar tama mance da batunsa. Bayan sallan isha kowa ya hallara a dinning ana cin abinci amma as usual Noor bata wurin, sallaman habu driver sukaji, shigowa yayi da akwati niki niki, ummi ce ta tambayesa kafin yabata amsa saiga Aryan da wani ahanunnsa shima ya gunguro ya shigo. Murmushi Abba yayi dan ayanzu kam yasan meya faru kuma wannan hukuncin da ummi tadauka akansa ai gani yake kamar yayi tsauri, gyara akeso ba batawa yakamata ayi ba. So sone fa amma sonkai yafi, ai koda Noor amatsayin ya ce agaresu amma Aryan ma da ne na jini awurinsu dan haka wannan hukuncin baiyi ba. Tamke fuska ummi tayi ta mike tsaye tana kallonsa tace"me nake gani haka,lfy Aryan tafiya zakayi" bai bata amsa ba ya wuce wurin Abba yace" Abba nadawo gidanmu da zama", Nana batasan lokacin data fashe da dariya ba harda shakewa dan akwai abinci a bakinta. Kamar ummi zata fashe haka ta nufi inda yake zaune ta kamo collar din rigarsa ta mikar dashi tsaye tace" wasa ma kakeyi, maza ka mike ka kwashi kayanka kabar gidannnan, Aryan kana wasa dani fa, zan saba maka fa" Abba ne ya dakatar da ita ta hanyar fadin" ummu sulaim dan Allah stop it, horon yayi haka mana, yanzu kawai sai Dada tazo ta daukeki tahanani ganinki angaya miki zan iya zama ne" babu yadda ta iya haka ta kyaleshi amma ba dan ta haqura ba. Wani dadi yaji, at least koma menene yanzu yasan suna gida daya da Noor dinshi, har wani murmushi jin dadi yayi. Bayan sun watse kowa ya tafi dakinshi saiya rage daga shi sai Abba, nasiha yamishi sannan suka cigaba da hira kamar wasu abokai harda wani tafa hannu, har wani wai sirrin su na maza Abba ke fada mai da yadda yake bi da ummi in tana fushi dashi. In kaga Aryan yana dariya bazaka taba cewa shi bane, dama da abbansa kadai yake irin wannan dariyan sai muhsin wani lokacin kuma da Shareef. Har wurin karfe sha daya sannan suka sallami juna kowa ya tafi dakinsa.

In Abba na gari to adakinsa ummi take kwana, dan haka karfe goma tafita tabar Noor wadda lokacin hartayi bacci. Ayanzu da Aryan yake gidan tama rasa wani mataki zata dauka dan ganin bai hadu da Noor dinba, amma tana tsoron kada ta rufe dakin kuma da daddare Noor tafarka tana buqatar wani abu dan haka tabar dakin abude. Cikin dare wuraren karfe biyu wani irin yunwa ya farkar da ita, mikewa tayi ta sauka daga kan gadon ta dau mayafin wani abaya dinta ta sa akan kayan baccinta riga da wando, wandon iya guiwa ya tsaya mata kuma ya fidda shape dinta sosai hakama rigar. Bedroom sleepers dinta ta sanya ta fito, babu haske afalon dan haka ta laluba ta bango har ta kai makunnin wutan ta kunna, sannan ta shige kitchen. Dan zama tayi a island din kitchen din na wasu mintuna kafin ta mike ta dau tukunya zata dafa indomie. Har ta daura ruwa kan gas kawai aka dauke wuta, kuma it's rare ayi hakan dan 24/7 ne. Bata damu ba dan tasan ana iya dawowa dashi nan da wasu yan mintuna. A tsaye take hasken wutan gas ne kawai kedan haska kitchen din shima ba sosai ba. Ba zato ba tsammani taji arungumeta ta baya, har zatayi ihu yayi saurin sa hannu ya toshe mata bakinta, zufa ne ya shiga ketowa daga saman fuskarta a tunaninta wani dodo ne dan ita bata San Aryan ya zo ba,kuma batasan da sintirin dayakeyi agidan kullum ba ita tama dauka tunda ya aiwatar da abinda yake so ai shikenan ya fita harkanta. Hawaye tafara yi dan ba bakin kuka sai mutsu mutsu takeyi amma mutumin yaki sakinta. Cizo ta gatsara masa a lallausar fatar hannunsa, ba kadan yamasa zafi ba har saida yace"ouchh,calm down Noor it's me" yayi maganar cikin whispering. Jin muryan mutumin data tsana ayanzu yasata yin amfani da dukkan karfin da Allah Ya bata ta tunkude shi ta juya aguje zata bar kitchen din dukda duhun dake ciki, aikuwa goshinta ya garu da cabinet din glass din dake sama, toshe bakinta tayi dan kar kukanta ya fita amma fa sosai taji zafin abun,da sauri ya matso inda take ya rungumo abunsa ajikinsa har wani sauke ajiyar zuciya yake. Wayarsa ya fitar ya kunna hasken flashlight, haska goshinta yayi yaga har wurin yadan taso ya kumbura gashi yayi ja abunka da farar mace. Kuka kawai takeyi tana kokarin kwatan kanta amma bai bata damar hakan ba. Da ita ajikinsa ya matso ya kashe gas din data kunna da tuni ruwan ya kone a tukunyar har ya fara wari," wlh ka sakeni ko nayi ihu komai darennan, zan tara maka mutanin gidannan wlh ka kyaleni, mugu kawai wadda kamun ranan bai isheka ba shine kadawo ka kara min wani muguntar azzalumi kawai" runtse idanunsa yayi da karfi dan maganganunta tamkar wani mashi haka yakejinsa. Bai saketa ba, haka ya dagata cak kamar jaririya ya manna kanta da kirjinsa yadda bazata iya ihu ba, haka ya fito daga kitchen din ya haura sama zuwa dakinsa, yana shiga yasa key akofar ya cire, daidai lokacin aka dawo da wuta. Direta yayi saman gado yana karewa innocent beautiful face dinta kallo kamar ya shekara bai ganta ba. Wani irin dadi yakeji yau yaga rabin ransa, yana juyawa ta mike ta nufi hanyar kofa bai hanata ba amma tanazuwa taga ai kofar akulle take, juyowa tayi ta zo gabansa tafara dukansa akirjinsa tana ya bude mata kofa ta fita, bai hanata dukansa ba har saida tayi ta gaji sannan ta kyaleshi, jawota yayi ya runguma a faffadar kirjinsa yana shafa kanta zuwa bayanta. Kusan five minutes suka dauka yana shafa mata baya ahankali har ya fara jin saukar numfashinta alamar tayi bacci. Kwantar da ita yayi kan gadon shima ya hau, jawota yayi jikinsa sosai kamar wani zai kwacemasa ita sannan ya kashe wutan dakin yaja musu bargo, minti kadan shima baccin yayi awon gaba dashi. Zai iya cewa tun dayake bai taba bacci mai dadi irin na yau ba, bacci ne mai cike fa natsuwa, kwanciyar hankali da kuma nishadi. Karfe hudu daidai tafara farkawa kafin shi. Jinta tayi ajikin mutum, aiko tana ganinsa ta mike azabure tana goge idanunta dan ta dauka ba daidai suke gane mata ba. Duka takaimasa a kafadarsa wadda yasa ya mike a dan zabure yana addu'a, ganin ta azaune yasashi mikewa shima yazauna, wani irin kallo mai cikeda takaici take binsa dashi idanunta suna kawo ruwa,shikam wannan kin datake masa yafara bashi tsoro fa" kaa bude mun kofa na fita, wai meyasa kake son bakanta min ne,mena maka dan Allah, bazan taba yarda da kai ba, kuma bazan taba yafe ma abinda kamin ba azzalumi" " Nuwaira ni mijinki kike kira da azzalumi, yanzu danna karbi haqqina kike gayamun wannan maganganun.." Bata bari ya karasa maganarsa ba tadaga mai hannu alamar ya dakata tace" kaga malam ba wa'azi zakamun ba. Yanzu kasan da haqqin naka mtcheeeew"(kaii wannan hegiyan yarinyar akwai kwarin ido da tsiwa😒😒, ke yanzu Aryan ya zuba miki wannan kafcecen hannun nasa ba saidai Daddy ya nemo wata ba, kinma gode yana lallaba ki😒😂). Jikinsa duk yayi sanyi haka ya mike ya dauko key ya bude mata kofar, kamar zata hankadeshi haka ta fice daga dakin ko kallonsa batayi ba, shikam da ido yabita har ta shige dakin ummi, kai kawai ya girgiza ya koma ya shige dakinsa.
(Allah sarki Aryan, so sadd🥺🥺)

*******
Haka ya shafa sati daya agidan babu wani canji saima abinda ya karu, kullum rashin mutuncin datake masa daban ne, har numberta ya karba awurin Nana,data gane cewa shine ai da sauri ta blocking dinshi. Duk yabi ya rame ya sawa kansa damuwa, bawani cin abinci yake ba, kullum cikin tunani yake kuma ya daina zuwa aiki. Wasu lokutan in ya fito yaganta a dinning tana cin abinci yakan zo yasa spoon shima zaici amma saita mike tabar masa wurin. Yanzu kam abun yafara damun ummi tunda ai koma menene yanzu yakamata ace tayafemasa, babu wadda baya ganin irin son da Aryan kewa Noor saidai ita. Nana ma tamata magana harta fita harkanta amma ko ajikin Noor, acewarta inda taji abinda taji kila saita ma tsaneshi fiye da ita Noor din. Duk yadda ummi taso ganin ta shawo kanta amma hakan ya faskara.

Kwance take akan gadon ummi bayan ta dawo saga makaranta tana chatting taji sallamarsa, kawai dan darajar sallama yasa ta amsa masa ciki ciki, Aryan ya fada sosai kuma ya dushe kamar ba Aryan Basamude ba. Zama yayi agefen ta yana kallon ta fuskarsa abun tausayi, itako juya masa keya ma tayi ta kashe wayan ta rufe ido kamar tana bacci. "Noor, pls stand up I want us to talk" kamar bazata tashi ba haka tamike ta zauna kamar wadda kwai ya fashewa aciki. Kallonsa tayi sau daya ta kauda kanta, murmushi yayi wadda yafi kuka ciwo yace" I want you to tell me what is it you want, kuma namiki alqawari ni Muhammad Aryan zan miki as long as baifi karfina ba" kamar jira take yayi mata wannan tambayar tace" ka sawwaka min" dammm haka yaji a kirjinsa, saki?? Noor ne ke cewa ya saketa," Noor kinsan me kike cewa kuwa? saki fa kikace inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun, har ya kai wannan stage din Nuwairaaaa??? Muryarsa na rawa kamar zaiyi kuka yakarasa maganarsa. " kwarai kuwa nasan abinda nake cewa, menene amfanin zama da mutumin daba sonka yake ba, ni bazan zauna dakai ba ka halaka ni" yama rasa me zaice kawai yace" tunda abinda kikeso kenan, zan miki amma kibani lokaci insha Allah you'll get what you want" har wani ajiyar zuciya tasauke (amma anyi dakikiyan yarinya anan, kai kubani oraimo cord na wiping dinta dashi kila ta dawo hayyacinta😠😠). Haka ya mike jiki asanyaye ya fice daga dakin. Gyara kwanciyarta tayi ta cigaba da chatting dinta harda kyalkyalewa da dariya.

Aranan Aryan ya tattara ya koma gidansa,babu wadda baiji haushin Noor aranan ba hatta ummi, yanzu ummi tayi dana sanin daukota datayi kuma bata barta ba saida tamata fada sosai amma ba'a matsayin umar miji ba saidai amatsayin uwa. Jikinta yayi sanyi saidai fa har yanzu tana kan bakanta.

*******
Yau sofiyya matar Mahmud ta tashida matsanacin ciwon jiki ga kasala datake ji ako wani bangare najikinta, Mahmud bai wani bata lokaci ba yakaita asibiti aka mata gwaji inda aka gano malaria ne da typhoid yayi mata yawa a jikinta magunguna aka prescribing mata sannan suka dawo gida. Ba haka Mahmud yaso ba ya dauka laulayin ciki ne ashe ciwon sauro ne😂😂. Moon kam tana gidanta cikin kwanciyar hankali yanzu take zama da mijinta, yanzu kam ba laifi tana iya kokarinta gurin ganin ta faranta masa sannan kuma ita da kanta take girka masa abinci inda ta koya daga wurin wata kawarta wacce keda catering school. Abun ba'a magana, wannan canjin nata ba karamin dadi yayiwa Mahmud ba, amma fa har yanzu ko gate din gidan kishiyinta bata taba takawa ba kuma tahanashi karma ya kawo ta. Tunda Mama ta hanata zuwa gidanta bata kara zuwa ba saidai ta kira ta shima din saiyayi ringing harya katse amma bazata daga ba. Haka ta haqura tabarta tasan halin mama sarai ko badade ko bajima zata nemeta da kanta. Daddy baya kasan tun lokacin daya musu sulhu suka koma gida tun lokacin yayi tafiya kuma bai dawo ba har yanzu.

*****
The following week Aryan ya koma aikinsa yanzu ya nemawa kansa salama da al'amarin Noor, ya fawallawa Allah komai. Dan koda yakoma gida yayi iya kokarinsa wurin ganin ta canza ra'ayinta amma ko kadan haka baiyu ba. Yanzu next shirinsa shine zai koma can Dubai company din Abba anan zai cigaba da zama kuma kafin ya tafi zai bawa Noor abinda ta buqata, company dinsa na nan Shareef zai managing dinshi saidai ya rika zuwa time to time yana dubawa. Shiri yakeyi yanzu inda harya handling wa shareef duk wani abunda yakamata ya handling masa. Karfe biyar daidai ya tashi a office, bai tafi gidansa ba ya tafi gidan ummi. Abba ma nagida dan hakaa yana shigowa ya wuce part din Abba. Bayan ya gaidasu shida ummi wacce dama tana falon tuntuni suna hira itada Abba kuma magana ne akan Noor dan har sun fara tunanin koza asa iyayenta a maganar ne, har yanzu dai kamar da Aryan bai karu ba saima kara ramewa da yayi,idonsa sun fito gwalagwala, asanyaye ya fara magana ya sanar dasu decision dinsa, basu nuna masa kin amincewarsu ba saima fatan alkhairi da sukayi masa, sunyi hakkanne saboda suna jiyewa Kansu abinda zai biyo baya idan Aryan ya fada cikin wani hali, tunda ita matarsa bata sonsa amma ai su iyayensa suna sonshi dan haka gara sumasa abinda yakeso kozai samu kwanciyar haankali. Noor na tsaye abakin kofa tana jin abinda yake fada, haka kawai ta tsinci kanta awani yanayi mara dadi,sai taji bataso ya tafi, dama ummi ce ta kirata, datazo shiga kuma saita jiyo muryarsa yana magana da iyayennasa,jin motsin kofa yasata zabura, tunda ya kalleta sau daya bai kara kallinta ba haka ya fice daga gidan ya barta da guzurin kamshinsa mai sanyi. Bata shiga falon ba tajuya takoma daki ta kwanta, jitayi hawaye na zuba daga idanunta(na yaushe kuma), meyasa ya kalleta sau daya ya juya kansa, badai ya dena sonta ba, wani irin kuka ne ya taso mata, ita kanta aka tambayeta meyasa take kuka bazata iya cewa ga dalili ba amma tabbas tasan bata cikin yanayi mai dadi.

Duk wannan abinda yake faruwa su Anty Jamila basuda masaniya akai dan su ummi basu fada musu ba, kuma Noor ma bata nuna cewa akwai wani abu akasa ba.


Tafiyarsa saura kwana biyu daga yau, shiri yakeyi, wani tunani ne ya fado masa why not ya gwada kiranta koda one last time ne. Hakan kuwa yayi ya dau wayarsa ya dialling numbern ta, abun mamaki saigashi ya shiga, wani irin farin ciki yaji kamar yayi tsalle yayi rawa, har ya kusan tsinkewa ta dauka, shiru sukayi dukkansu suna jin saukar numfashin juna ta wayar, shi ya fara katse shurun ta hanyar cewa" are you sleeping"? Um um kawai tace, bata kara cewa komai sai taji yace" I'll be leaving for Dubai in the next two days insha Allah, nasan kina jiran sakonki, don't worry I won't leave without giving you that" duk wannan maganan dayakeyi hawaye ne kawai ke zarya daga idanunta, tana so tayi masa magana amma takasa, har wani daci daci takeji a makogwaronta, harya gama maganarsa ba tace kala ba, murmushin yake Aryan yayi dama yasan har yanzu bata canza decision dinta ba, amma ya zaiyi tunda ta nema dole ya bata. Yana cikin wannan tunanin yaji kit ta kashe wayar. Abangaren Noor kuwa ta kashe wayanne saboda wani kuka daya taso mata kuma bataso yaji, zata iya cewa ahalin yanzu bata buqatar wannan abinda tace masa tanaso, idan fa yatafi shikenan magana ya kare,ya rabu da ita kenan, to ya zatayi bayan shita fara saninsa a matsayin da namiji, bata tunajin zata iya wani auren kodasun rabu,idanfa ya saketa yana nufin yanzu tazama karamar bazawara at nineteen years. Kuka take sosai kamar ranta zai fita. Tashi tayi daga kan gadonta ta shige toilet lokacin karfe sha daya na dare. Bayan ta fito ta shimfida sallaya ta kabbara, bayan ta idar da nafilolinta ta zauna ta dinga jero addu'o'i har Allah yasa bacci ya dauketa saman sallayar.


Mu hadu gobe insha Allah.


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
11/1/23, 8:16 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 47_ 48

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

I DEDICATE THIS PAGE TO THE WHOLE OF MIJIN TACE FANS. GODIYA NAKE DA ADDU'O'INKU, ALLAH YABAR ZUMUNCI. LOVE Y'ALL❤️❤️❤️

Cikin baccinta tayi mafarki wai ya tafi kuma kafin ya tafi saida ya bata takardan ta. Azabure ta mike daga kan sallayan, wani irin zufa yana ketowa daga fuskarta, jikinta gaba daya ya dau rawa kamar mazari. Agogon dakin ta kalla, karfe biyu saura. Mikewa tayi ta shige toilet ta dauro alwala sannan ta fito tafara sallah. Cikin sujjada kawai ta tsinci kanta da yin kuka akan kar ya tafi,addu'a takeyi hadI da kuka kamar ranta zai fita, toh meke sata kuka ko dai sonshi take? Wannan ne har yanzu bata iya tantancewa ba. Koda ta idar bata koma bacci ba, zama tayi a kan sallayar tana karatun Qur'an kuma Alhamdulillah tadan samu natsuwa. Bata koma bacci ba har aka kira sallan subh sannan ta mike tayi. Tana idarwa takoma kan gado,minti kadan bacci ya kwasheta.

Agefen Aryan shima kusan hakan ta kasance. Baiyi bacci daren jiya ba, kusan da zazzabi mai zafi ma ya kwana. Gashi ya kashe wayarsa. Bai samu ya tafi masallaci ba dan jikinsa ba kwari, rufuwa yayi da bargo jikinsa na rawa sosai. Da kyar ya iya daukar wayarsa ya kunna, number din Shareef ya dialling bugu uku ya dauka. Jin muryan Aryan yasan ba lfy ba dan sosai muryar nashi ke shaking. Aiko babu bata lokaci shareef ya iso gidan da wani likita, dubashi yayi inda yagano cewa stress ne da kuma

Please Login or Register in order to submit comment