Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sexy eyes dinsa. Sosai yake kallanta kamar yaga wata hurul ain lols. Bazai taba mancewa da wannan fuskarba, kenan itadin budurwar shareef ce. Amma kuwa in haka ne ba karamin shirme yayi ba, wani irin haushin Kansa ne ya kamashi. Dama saboda ya dade bai fita shan iska bane yasa ya fito ya bi shareef din, ashe abinda zai tarar kenan.

Sosai yake kare wa fuskarta kallo kamar ya tuno wani abu saiyayi saurin janye idonsa sakamakon kirjinsa dayaji yana dib dib dib. Itace mace ta farko a fadin duniyarnan daya taba daga hannu akanta, ko Nana iyakanshi tsawa amma baitaba kai hannunsa jikinta ba. Karamin bakinta ya kara dago kansa ya kalla azuciyarsa yace" sai shegen tsiwa amma sai tsoro" yafada yana smirking.

Saida suka karaso motan sannan ya daina kallonsu yamaida hankalinsa kan wayarsa yacigaba da latsawa. Koda suka shigo Noor tayi kokari wurin ganin fuskarsa amma still batayi nasara ba danya juya fuskar yanzu yana fuskantar waje.


Suna isowa gaban gate din gidan Ya shareef ya dropping dinta sannan suka juyo suka dawo office. Suna fitowa lokacin ana kiran sallan asr, hakan yasa suka nufi masallacin dake company din.

Bayan sallan asr, Ummi neda Nana suna hira afalo kadan kadan sai Dada tashigo. Danneman tsokana tazauna a gefen Nana a cushion mai zaman mutum daya, tasan sarai cushion din bazai daukeau ba amma dan tsaban neman magana irinta tsohuwar haka taki. Ummi kam tanata kunshe dariyarta dantasan yanzu za'a fara wani Sabon dramar. Aikuwa bata gama tunani ba taji Nana timm akasa tazauna da duwawunta ta saki wata kara, Dada kuma na dariyan mugunta tace" kingani, sai ance kuci tuwon dawa da masara kuce Ku ko sunayen baku sani ba sai wannan tsutsan, gashi tuwo yakada indomie" tafada tana kara fashewa da dariya harda kama cikinta. Nana kamar tayi kuka tace" wai ke meyasa kike son shiga harkata ne iyye, wlh saina fadawa tsohonki" murguda baki Dada tayi sannan tace"ahap, nabarmiki shi in dai wannan ne, mazanyi da tsohon jini bayan ga wannan dan albarkan kyakkyawan saurayin nawa" darawa sosai ummi tayi harda Nana dan yadda Dada tayi maganan abun dariya sosai. Suna cikin hira Abba yashigo dauke da suitcase dinsa, da sauri ummi tanufeshi ta rungumeshi tare da karban suitcase din ahannunsa, ko kunyan su Dada bataji ba, Dada dai inda sabo tariga ta saba kuma yana daya daga cikin abinda yasa bata son zuwa gidan.

Abba karasowa yayi hannunsa rike dana ummi ya iso falon tare da gaida mahaifiyarsa. Amsa masa tayi cikin sakin fuska. Nana ma ta gaida shi sannan ya haura sama ummi na biye dashi.

Nana da Dada kadai aka bari a falon sai faman hantarar junansu suke kamar yadda suka saba. Suna cikin haka sukaji horn din mota alaman Aryan ne ya dawo. Nana ta dubi suturar dake jikinta ta tuna abinda yafaru tsakaninshi da ita aikuwa a saba'in ta mike tayi hanyar dakinta. Sosai Dada tayi dariya tace"shegiyan miya kince bakyaji".



Tunda su hanan suka dawo daga evening lectures suketa santin wayan Noor dukda kuwa iri dayane da nasu amma Kunsan sabon abu da daukan ido. Haka sukayita surutu har aka kira sallan maghrib sannan kowa ya tashi din gabatarwa.



Yau Monday kuma yau Noor zata fara zuwa school. Sosai take Allah Allah asuba tayi itama tashirya kamar kowa. Tun 4:30 ta farka,tayi sallolinta kamar yadda tasaba akowani rana sannan tayi karatun Qur'an har saida aka kira sallan asuba. Bayan ta idar tashiga bayi tayi wanka da brush. Tana fitowa ta tadasu hanan Wanda keta bacci kamar gawa. Gaban dressing mirror ta nufa ta zauna tafara shafa body lotions masu sanyin kamshi. Bayan tagama ta wuce wurin wardrobe wadda aka raba musu su uku kasancewar wardrobe din mai mabudi Tara ne kowa da uku uku. Side din da kayanta ke ciki ta bude, komai tsab tsab sai tashin kamshi yake irin na turaren kayannan. Noor akwai son kamshi ga tsabta malam. Gsky wadda ya sameta amatsayin mata ya taki sa'a babba. Hannu tasa ta zaro undies dinta da corporate wear din da zata sanya kasancewar akowani makaranta dress code din law students kenan white and black ko dark blue.

Bayan ta gama shiryawa cikin bakin sket dinta high waist da rigarsa fari mai long sleeve har wrist dinta. Rigan irin mai button daga sama har kasannanne. Sosai kayan ya amshi jikinta yayi das das, baiwani matseta ya fidda surarta ba. Dogon gashinta wadda yake baki sidik gashi silky ta taje sannan tashafa man kai mai kamshi ta tufkeshi da ribbon dinta ta kitsa jelar wadda yake rito a gadon bayanta tayi donot dashi. Wani farin hula mai kyau plain babu ado ajikinsa ta sanya akan ya rufe gaba dayan gashinnata. Su hanan sai wow wow wow suke kamar motan polisawa suna yaba kyawun da Noor tayi. Ko ajikinta danta saba da wannan shirmennasu. Wani bakin gyale pashmina ta dauko sannan tayi rolling shi, tadan gyara girarta ta sanya wet lips ta feshe dukkan jikinta da turare masu kamshi da tsada.

Sabuwar jakan makarantar da suka siyo ne ta dauko ta zuba sabobbin takaddunta aciki sannan ta dauko abubuwan da baza'a rasa a jakan yan makaranta ba sannan ta dauko sabuwar wayarta shima tasaka aciki. Su hanan suma lokacin harsun kammala shrinsu kasancewar suna da class din safe. Fitowa sukayi dukansu uku daga dakin suka nufi dinning area. A can suka tarar kowa ya hadu awurin su kadai ake jira. Anty jamila wani irin dadi taji dataga Noor awannan shigan tayi bala'in kyau. Zama kowannensu tayi suka serving kansu suka fara cin abinci. Uncle saif ne da Anty jamila suka fara gamawa sai Ya shareef shima ya mike yabarsu su uku awurin suna kan cin abincinsu. Suma suna idarwa suka mike sannan suka sallami, iyayensu,Anty Jamila tabawa kowannesu 3k pocket money banda wadda ake turamusu a account. Suna fita suka nufi wurin motarsu kirar range rover na manyan yaran abuja. Hanifa ce ta tuka su yau inda Noor ke zaune abaya, Hanan kuma na zaune a gefen mai zaman banza, suka nufi makarantarsu wato Nile university Abuja.


Yau bai tafi aiki da wuri ba kasancewar yau za'a fara ginin sabon gidansa wadda ke Asokoro. Babban fili ne wanda akalla zai kai acre daya da yan kai. Masu aikin gini ne sunkai kusan talatin kowa da abinda yakeyi anata faman aiki. Sanye yake cikin wani dark blue jeans da farin riga gabansa anyi rubutu da blue ink anrubuta"THE BOSS"face cap blue ne ya sanya akansa wadda yarufe kusan rabin fuskarsa, wasu fararen Snickers na company din Nike ne akafansa yayi kyau sosai. Black shades dindake idonsa ya kara bayyana irin kyawun da yayi sai tashin kamshi yake Masha Allah. Magana contractor din ke masa yayinda yake rike da design din katafaren gidan daza'a gina yana masa bayani. Shiko oga babu abinda yake cewa sai gyada kai yakeyi. Sai kusan sha daya da wani abu yabar site din ya tafi office dinsa.

Yau anty Aisha taji dadin jikinta dan haka ta kira kawarta hajiya shamsi akan sutafi wurin boka gangaran su amshi maganin daya hada musu. Itako Lubna duk abinda mamanta keyi dariya ma yake bata dan kuwa in Aryan ne gani take kamar ta riga ta gama samunsa dan ta hanyar Dada zata bi tunda yanajin maganarta, kuma suna mutunci da Dada dan ita Dadan batasan halin Lubna ba. Dayake anty Aisha tasan halin mahifiyarta yasa ta gargadi lubna sosai kan abinda take shirin yi" karfa ki mance mahaifiyata ce kuma tana saurin kama mutum in baida gsky, wlh kul dinki tom" itako babu abinda yadameta dantasan shirin data hadawa Aryan.( Niko nace wlh kwalelenki,Aryan na mace mai daraja ce ba kazama tantiriya irinki ba, bolar tasha).

Tunda su Noor suka iso harabar makarantar dalibai maza da mata sai kallonta suke kowa na yaba irin kyawun da sabuwar dalibannan tayi. Itako jikinta har wani irin kunya takeji dan bata saba ba. Haka kawai ta tsinci kanta da binsu Hanan department dinsu. Saida suka rakata department dinta tayi clearance sannan suka barota bayan sun hadata da wata yarinya mai suna yasmeen itama tana law dinne. Suna zaune a lecture hall itada yasmeen suna dan taba hira kadan kadan Nana tashigo. Yasmeen naganinta tamike ta rungumeta tace"bestie ai na dauka yau bazaki zo bane" murmushi Nana tayi tana kallon Noor wacce itama murmushin takewa Nana. Hannu tabata sukayi musabaha sannan yasmeen tace"Nana this is Noor and Noor this is Nana my one and only best friend " murmushi sukawa juna haka kawai Nana taji Noor ta kwanta mata arai, gatada kyau kamar wata balarabiya. Zama sukayi alokacinda lecturer yashigo yafara gabatar da lectures dinsa. Sosai Noor tagane abubuwa sosai. Bayan wannan lecturer din yafita babu bata lokaci wani ma yakara shigowa. Sai da sukayi lectures uku ajere sannan suka fito sallan zuhr. Hanan ne ta kira Noor awaya ta tambayeta a ina take ta fada mata. Bayan mintuna kadan su hanan suka karaso wurin itada hanifa. Tare sukayi sallah dukkansu biyar din sannan suka wuce canteen dan nemawa cikinsu haqqoqinsu.

Sai bayan sallan asr suka taso daga school. Aranan aka qulle qawance tsakanin Noor da yasmeen da Nana dan duk kansu daya ne. Wannan karon a hanyar dawowansu Hanan ce tayi tuqi sunata wa Noor tsiya akan sun zama direbobinta. Agaban dominos pizza suka paka mota sannan suka fito dukkansu uku suka shige ciki.


Agaban coldstone ya paka motarsa dan yau haka kawai kwadayin ice cream yataso mai. Yana fitowa ya shiga yai ordern ice cream flavors guda uku. Su hanan suna fitowa hannun kowaccensu rike yake da ledan kayan kwalama aciki suka shige coldstone wanda ke manne da dominos pizza. Daidai shikuma zai fito suka ci karo da Noor ledan hannunsa ya watse akasa itama ledan hannunta suka zube akasa, pizzan dake kwali ya bude tarwas zai gashi a kasa kuma wurin akwai dan kasa na takalman mutane. In ranta ya yi dubu to ya baci hakan shima, "wai wannan wani irin.." Shuru tayi sakamakon ganin mutumin da bazata taba mancewa da fuskarsa ba yana tsaye yana kallonta cikeda takaici da haushi. Bakinta ta tsuke tayi shiru ta kalli tafin hannunsa daya wankemata mari dashi, take wani irin tsoronsa yashigeta dan bazata taba mancewa da zafin hannunnannasa ba. Kuut ta hadiye wani yawu tana tunanin kalaman data furta dazu tana kokarin tunawa ko ta kara furta wani kalman zagi kar irinnan ranan takara karban one blow seven die lol😂. Shiko tsaban haushi ma baisan mezaice da ita be sai kallonta kawai yakeyi yana tunanin wannan wani irin kaddara ce take hadasu akaro na uku.

Su hanan kam sai kunshe dariyarsu sukeyi dan ganin yadda Noor ta tsuke bakinta tayi shuru alaman ta tuna da Marin data sha kwanakin baya. Wani dogon tsaki yaja yatafi abunsa baibi takan icecream din ba dansaiya ji duk ya fita masa arai. Hannunta hanan taja suka tafi cikin coldstone din, sai ayanzu bakinta ya bude tana surutan da babu amfani dan wadda yakamata yaji yariga ya tafi. Bayan sun siya abinda sazu siya suka wuce gida.

Yau ummi da Dada sunsha hira sosai awurin Nana akan Noor. Duk da ummi bataganta ba kawai saitaji ta kwanta mata arai itama.

Yana faka motarsa ya wuce dakinsa dan lokacinda ya shigo babu kowa a falon. Wanka ya shiga tareda yin alwala dan maghrib takusa. Yana fitowa yasanya wani white jeans da singlet sannan ya feshe jikinsa da sassayan turarensa ya zauna abakin gado yana sipping malt din da ya fitar daga dan karamin fridge din dake dakinsa. Har aka kira sallah sannan ya sanya farin jallabiya mai dan transparent har ana ganin singlet da wandon daya sa ya kara feshe jikinsa da turarensa masu kamshi, ya sanya hularsa taba kaji hadisi yafice daga dakin. Afalo yasamu ummi tafito daga kitchen, gaida ita yayi sannan ya wuce masallaci itama yawuce sama domin gabatar da sallah.



SHARE AND COMMENT


REEMAH✍️
10/8/23, 5:36 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 15_16


Yau sati biyu kenan da Noor tafara zuwa school kuma sosai lectures yayi serious dan tun kafin abata admission anfara karatu. Bata da wani time sai in sallah zatayi ko kuma in abinci zataci. Abun har mamaki yake bawa mutanin gidan, Ashe haka Noor take son karatu?

Sun dawo gida around 5:15pm, bathroom tawuce tayi wanka tafito sannan ta sanya kananan kaya marasa nauyi kasancewar yau ana zafi. Wayarta ta dauka ta shiga WhatsApp wadda ba kowani time take shiga ba sai in tana free. Group chat suka bude ita dasu yasmeen da wasu yan departmentment dinsu maza da mata. Bata cika magana a group din ba sai in ya kama dole. Nana ce ta kirata" hello dear kun koma gida lfy" abinda Nana ta tambayi Noor kenan. Wannan murmushin nata mai tsananin kara mata kyau tayi sannan tace " lfy lau dear, yasu ummi"? Nana ta amsa mata da lfy lau. Duk abinda suke fadi awaya agaban ummi dan suna zaune ne afalo itada Nana.

Haka kawai ummi taji tanaso taganta dan ba karamin kwanta mata arai tayi ba duk da bata taba ganinta ba. Suna gama wayan ummi tace" da alama kawance mai zurfi yashiga tsakaninku ko Nana "? Murmushi Nana tayi tace" wlh sosai ummi, Noor is a kind person tanada dadin zama Sam ba ruwanta wlh gashi tanada ilimi " wani irin murmushi ummi tayi wadda ita kadai tasan ma'anarsa. Sallamansa ne suka jiyo ciki ciki. Cikin takunsa na isa da daukar hankali ya karaso cikin falon. Zama yayi kusa da ummi ya sumbaci hannunta. Shafa Kansa tayi cikeda kulawa." Welcome, ya aiki" ummi ta tambayesa. Kai kawai ya gyada amma baice kala ba. Sanin halinsa yasa ummi ma tafita harkansa tacewa Nana takawo masa ruwan sha. Mikewa Nana tayi ta wuce dinning, wani drawer na glass ta bude ta dau glass cup sannan ta tsiyaya masa ruwan sanyi daga dispenser ta kawo masa. Amsa yayi ya kurbe duka sannan ya mike ya wuce bedroom dinsu.

Daddy ne zaune a kan sofa yana waya da kanwarsa Anty umaima inda suke magana akan kayan dakin Moon tunda Daddy ya lura mama ko maganan ma batayi. Fitowa tayi ta zauna daidai kafarsa har ya gama wayan " menene Moon"? Ya tambayeta cike da son yarsa, kuka tafashe masa dashi tace" Daddy dan Allah kamin rai wlh banason shi bazan iya zama dashi ba , kadubeni da idon tausayi ka yafemin abinda namaka wlh bazan kara ba amma Daddy kar ka min auren dole" sosai Daddy yaji jikinsa yayi sanyi amma babu yadda zaiyi, magana yariga yayi nisa kuma shida Kansa ya bada aurenta babu wadda ya tilasta shi, shafa kanta yayi sannan yace"Moon kiyi haquri, nariga na gama magana, kuma banayi hakan bane don bana sanki, nayi ne donna nuna miki cewa na isa dake da mahaifiyarki, insha Allah nan gaba zakiyi alfahari da wannan zabin kinji"? Shiru tayi tana sauraran sa amma Sam zuciyarta ta riga ta gama kissima mata abinda zatayi, ai saurayinta Salis yace koda wadda za'a aura mata ya saketa shi zai aureta dan haka ko Daddy ya daura mata auren sosai zata wulakanta mijin nata har ya gaji don Kansa ya saketa. Shiko Daddy kamar ya harbo jirginta yayi murmushi irinta manya yace"kuma Moon abu na karshe, ko bayan aurennan ban yarda ki ce zakiyiwa mijinki wulakanci don baki sonsa ba, inko kikayi hakan to tabbas duk abinda yabiyo baya ki zargi kanki" wani irin marayan kuka ta kara sakewa danji take in har bata auri Salis ba mutuwa zatayi. Mama ce ta fito daga dakinta da sauri jin kukan Moon, kallonta Daddy yayi ya dauke kansa, wani irin kallo ta watsa masa tace" amma Nasir yau na kara tabbatarwa baka kaunata da ni da 'yata, in akwai adalci a hakuncinka meyasa bazaka aurar dasu duka ba harda ita 'yar gaban goshinnaka"ta karashe tana huci, kallonta Daddy yayi amma still baice komai ba cos there's no point talking to someone with half brain, yo half brain mana, me Noor tayi masa da zai mata auren dole, ai Moon laifi tayi shiyasa ya yanke mata wannan hukuncin, kuma baya fata koda amafarkinsa ne ya wa Noor auren dole because she deserves all the goodness in life. Daya gaji da surutan Mama, mikewa yayi ya fice waje dan dama maghrib ta gabato.


Yana fita Moon ta mike ta rungume mamanta tana kuka, bubbuga bayanta Mama tayi tana rarrashinta tace" karki damu Moon inhar baki yarda da wannan auren ba babu mai tilasta miki wlh babu" sosai Moon take kuka kamar an aiko mata da sakon mutuwa. Da kyar mama ta iya rarrashinta har tayi shiru sannan ta kama hannunta suka wuce dakinta.


Washe gari, Anty Aisha da Lubna suka shirya da nufin zuwa gidan ummi dan gaida Nana wadda azahiri manufarsu daban ne. Maganin da Anty Aisha ta karbo awurin boka shi takeso tayi amfani dashi wa Aryan.(hmm anya kuwa wasu suna tsoron haduwarsu da Allah🤔).
Tunda suka shigo Nana da lubna suke wa junansu wani irin kallo dasu kadai suka San ma'anarsa. Yau sabida wani makircin, Lubna harda jalbab dinta. Fuska babu yabo ba fallasa ummi suka gaisa da Anty Aisha. Dada kuwa bawani fuska tasakewa Anty Aisha ba dan ta San yarta sosai. Anty Aisha akwai gar gar kuma tasan sarai halinta 'yarta ta dauko, mutum mai hali duk yadda yaso boye halinsa dole sai kadan daga ciki ya bayyana.

Kasancewar yau Saturday ne kuma yana gida dan gabadaya motocinsa na car park yasa Lubna ta faki idonsu ummi tawuce dakinsa. Knocking tayi amma shiru kamar babu kowa a part din. Tura kofar tayi ga mamakinta abude yake, tana shigowa ko sallama babu takusa kai cikin falon. Babu kowa aciki sai karan Ac da kamshin air freshener. Kofan dakinsa ta kalla, ahankali ta ke takawa cikin kissa har bakin kofar dakin. Turawa tayi ahankali tashige. Kwance yake akan gado dagashi sai 3qtr babu riga ajikinsa. Alumshe idanunsa suke kamar wadda ke bacci amma ba baccin yakeyi ba. Jalbab din jikinta ta zare take surar jikinta ya bayyana. Wando ne matsatsse ajinkinta da wani half vest kusan rabin boobs dinta awaje yake. Wata irin tafiya take komai ajikinta yana rawa harta iso gaban gadon. Kyakkyawar fuskarsa ta karewa kallo, idanunta ne ya sauka akan faffadar kirjinsa wadda yake sumul kamar bayan kwai babu alaman gashi. Take wani irin feeling ya taso mata. Duk abinda takeyi Aryan na ankare da ita dan tun shigowarta yaji motsi amma be motsa ko kadan ba. Hannun ta takai kan kirjinsa da zummar yimasa wani abu ya cafke da sauri, tsananin bakin ciki da haushi hadi da takaice yaji ya ziyarce shi akanta, take wani irin tsanarta ya darsu a zuciyarsa, me ma zai mata yaji sanyi azuciyarsa, wani mugun kallo ya watsa mata da lumsassun sexy eyes dinsa wadda ya dan fara canza kala, hankadeta yayi harsai da tafadi akasa. Mikewa yayi ya nufi kofar dakinsa ya murza key dan yau insha Allah saiya koyawa Lubna hankali kila akansa bazata kara taba namijin daba muharrraminta ba. Itako shu'umar mikewa tayi still bata daddara ba wani irin tafiya na daukan hankali takeyi ita adole she's looking sexy dinnan duk tunaninta biye mata zaiyi shiyasa ya sanya key akofar. Murmushinsa mai tsananin kyau yayi sannan ya raba ta gefenta ya wuce cikin closet dinnsa ya sanya singlet ya dora ash jallabiya akai sannan ya zaro wani skin belt dinsa daga ma'a daninsa, abayansa ya boye belt din ya fito daga closet din. Mamakin ganinsa da kaya ajikinsa Lubna tayi, kenan yanada ulterior motive shiyasa ya kulle dakin. Baya ta fara ja kadan kadan shikuma yana jara matsota har yazo inda take. Bata ankara ba taji belt atsakiyan skin din bayanta. Wani irin zafi taji ya ratsata wadda tunda take bata taba jin irinsa ba. Ihu ta kurma gaba daya gidan ya amsa.

Su ummi suna falo suka jiyo ihun Lubna, a zabure Anty Aisha tamike tana waige waige kozata kara jin ihun, aikuwa takara ji na yanzu ma yafi na dazu, da gudu suka nufi dakin aryan dan anan ne ihun ke fitowa. Suna zuwa sukaji ihun Lubna da kyau alamar jibganta akeyi, Dada ta kama handle din kofar amma tajishi akulle. Babbuga kofar suka farayi amma bai bude ba.

Saida yamata duka black and blue tayi laushi sosai dan ba karamin fasa mata jiki yayi ba. Ko kwakkwaran motsi bata iyayi sannan ya wuce ya shige toilet ya wanko fukskarsa ya fito. Abakin kofa ya ganta tana kokarin bude kofar amma babu key. Tana jin motsinsa takara kurma wani ihun tana ataimaka mata zai kasheta. Wayansa ya dauka a side drawer din gadonsa sannan ya dau key din motarsa da key din dakin, kwallo yayi da ita aikuwa ragab sai gata ta bugu da dressing mirror dinsa goshinta ya fara fidda jini. Ko kallonta baiyi ba dan zuciyarsa wani irin tafarfasa yakeyi shi inta shinema wannan dukan dayamata kadan ne.

Anty Aisha sai kuka takeyi wai zai kashe mata tilon 'yarta. Sukuwa su ummi ko kala basu ce da ita ba harda Dada. Itakuwa Nana wani irin farin ciki takeji yau Ya Aryan ya gyara wa Lubna zama. Suna wannan tunanin ne suka ji anbude kofar dakin. Yana fitowa ko kallansu baiyi ba yasa kai zai fice ummi tace"dakata Aryan,where do you think you're going"? Baiso ummi ta tsayar dashi ba, bai tafi ba kuma bai juyo ya kallesu ba. Dada ce tace"ummu sulaim kyaleshi yatafi duk abinda yamata ita tajawo wa kanta" yana jin maganar Dada ya fice abunsa. Anty Aisha da gudu ta shiga dakin ta tadda Lubna acan gefen dressing mirror ko kwakkwaran motsi batayi. Da gudu ta yo kanta tana kuka. Su ummi ma suka shigo inda duk jikinsu yayi sanyi. Amma ummi tayi mamakin ganin irin shirin da Lubna tayi, kenan abinda tasa kenan yasa ta sanya jalbab akai? Hmm. Da kyar suka taimaka wa Anty Aisha ta mikar da Lubna har wurin motar ta. Babu wadda yabita acikinsu sai ummi dan Dada tace babu inda zata hakama Nana. Asibiti suka wuce da ita suna zuwa aka shigarda ita emergency.


Noor da Hanifa da Hanan sune a kitchen yau ana girki. Dama haka Anty jamila ta koyar dasu, duk ranan weekend suke abincin gidan acewarta bata yarda ta aurar da 'ya miji ya dawo da ita sabida rashin iya girki ba. Hadadden chicken biryani suka hada da fatoush salad da kuma brazilian lemonade. Noor itace ta hada snacks inda tayi meat pie dasu samosa. Ko ina a kitcehn din sai tashin kamshi yakeyi. Sunayi suna taba hira gwanin sha'awa. Suna gamawa suka shirya akan dinning sannan suka wuce dakinsu dan lokacin sallan zuhr yayi. Wayan Hanan ne yayi kara ta dauka tana wani kashe murya ta fice daga dakin. Dariya su Noor suke mata itada Hanifa. Bayan sallan zuhr suka hallara a kan dinning dancin lunch. Sosai sukayi santin snacks dinda Noor tahada musamman meatpie din wadda yaji wadataccen nama acikinsa. Bayan sun gama ci suka koma falo aka kunnan tv, su uku kawai aka bari a falon. Wani romantic indiam film ake nunawa inda Noor tamaida hankalinta sosai kamar me daukan darasi. Nuwaira kenan.

Tuki kawai yakeyi amma harga Allah bemasan ina zai tafi ba dan wani irin tukukin bakin cikine ke cinsa aciki. Kanwar bayansa itace babu kunya takeso yayi iskanci da ita? Lallai 'yan matan nigeria daban suke da matan saudi. (Hakane?). Asokoro ya wuce inda ake gini gidansa, anyi nisa sosai aginin inda ake matakin roofing din gidan. Sosai gidan ya hadu tunma kafin akarasa. Wani masallaci dake kusa da gidan ya wuce yai sallan zuhr sannan ya dawo site din yana kallon yadda ma'aikata keta aikinsu cikeda kwarewa.


Su Lubna kuwa angama dressing ciwonta an maida ita wani special room. Hannunta daure da bandage dan har karaya ta samu ga goshinta daya fashe shima an daura masa bandage. Anty Aisha tayi kuka harta

Please Login or Register in order to submit comment