Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara rigar jikinta tayi murmushi wadda ita kadai tasan ma'anarsa tace" dukan daka min ba mancewa nayi dashi ba, kuma yanzu na dauki fansata kajira kaga abinda zanyi wlh saika regretting taba jikina dakayi da sunan duka" tana gama fadin haka ta fice fuuu kamar balbela. Tana fita ta fashe da dariya harda rike ciki, wani ma'aikacin office din wadda cleaner ne ya fito daga wani corridor shima yana murmushi, wani waya ya mika mata ta kunna video din abinda suka gamayi da Aryan yanzu, dariya ta kuma fashewa dashi ta bude jakarta ta zaro rafar one thousand guda biyu ta mikawa mutumin. Har kasa ya tsunguna yana godiya tawuceshi tayi tafiyarta.


Aryan abun duniya ta isheshi,yama rasa mezeyi yasamu sukuni, ya akayi Lubna taci nasara akansa. Dukda Ac dake office din bai hana zufa karyo mai ba. Dayaga zaman office din zai gagareshi ya mike ya dau duk wasu abubuwansa yafice, kana ganinsa kaga wadda baya hayyacinsa. Abakin kofa yaci karo da shareef amma ko kallonsa beyiba.

Yana isa parking lounge ya figi motarsa da gudu mutane na kaucewa dan yadda sukaga driving dinsa sunsan ba klau ba. Tafiya kawai yakeyi ko traffic light baya kallo, ikon Allah ne kawai ya kaisa gida lfy, yana Shiga babu kowa afalo dan haka ya wuce daki. Kayansa ya tube dagashi sai guntun wando ya shige bathroom dinsa. Shower ya sakar wa kansa dan Kansa wani irin juyi yakemai bana wasa ba, inama zai iya ihu amma babu dama, hannunsa yasa ya bugi bango yana jujjuya kansa, tsanar Lubna da mahaifiyarta na kara ruruwa azuciyarsa da ruhinsa baki daya, ya kai kusan awa daya kafin ya fito, ko towel din jikinsa be kunce ba ya kwanta flat akan gadonsa yana kallon POP din dakin yana tunani. Kardai yarinyar nan plan ta hada masa tana kokarin tarnishing image dinsa, lallai kuwa dashi take zancen, zai nuna mata yafita hauka itada mahaifiyarta. Yana wannan tunanin aka kira sallan zuhr ya mike jiki ba kwari ya fice ya tafi masallaci.


Itakuwa Lubna editing video dintayi inda wurin kissing din kawai za'ana gani banda inda ya tureta sannan ta sake a shafinta na twitter. Minti goma yayi wuya video yafara yawo a ko ina, mutani sai zagin Aryan sukeyi wasu na cewa awaje yana wani jijji da kai abayan fage kuma ashe tantirin dan iska ne, wasu kuma suna cewa basu yarda ba sharri akemasa, itakuwa Lubna wani irin dadi taji harda nunawa Anty Aisha wacce tamafi Lubna murna.

Nana na cikin kallo awaryarta tana scrolling Twitter dinta kawai aka hasko mata wannan video din, batasan lokacin data saki ihu ba tana girgiza kai, da gudu ta sauko daga kan gadonta tanufi dakin Aryan, abakin kofar falo taci karo dashi yadawo daga masallaci, hannu na rawa ta mika masa wayar, wani irin dummmmm zuciyarsa tayi, kansa ya fara juyi, ashe zarginsa daidai ne, besan lokacin dayayi wurgi da wayan ba, Allah ya taimaka yafadi akan carpet babu abinda yasameshi. Su ummi da Dada suka fito daga daki dan sunji ihun Nana, ummi ce ke tambayar Nana meyafaru amma ina kuka kawai Nana keyi kamar anmata albishir da mutuwa, Dada ta kalli Aryan wadda ke tsaye kamar mutum mutumi idonsa sun kada sunyi ja jawur. " subhanallahi, karamin maigida lfy, meke damunku dan Allah kuyi magana mana, ke kazar makota meke faruwa, wani ya rasu ne" tadinga jero musu tambayar amma babu wadda ya tankata awurin. Ummi ce taji kamar karar abu awaya ta kalli kan carpet taga wayar Nana, zuwa tayi ta dauki wayan, abinda taganewa idonta ne yasa ta sakin wayan akasa wannan karon ya fadi akan tiles screen ya fashe. Kafafunta ne taji bazasu dauketaba kawai tanemi wuri tazauna akan carpet din tacire dan kwalin kanta tana fifita dashi, hawaye kuma na zarya daga idanunta,amma Lubna da anty Aisha sun cuceta dan bazata taba yarda da wannan ba, tasan halin kowanne acikin yaranta kuma tasan sarai sharri akawa Aryan.

Dada kam tayi magana harta godewa Allah kawai sai itama ta joining dinsu tafara kuka wiwi tanacewa" wlh in tsohona ne ya mutu Ku fadamin tun yanzu nima na bishi yiiiiii yiii" tana kuka tana fyace majina abun tausayi abun dariya. Shiko Aryan wani irin juyi yaji kansa namasa ahankali yafara takawa har cikin dakinsa yana shiga ya murza key akofa. Gaban dressing mirror dinsa ya nufa, da wani irin karfi ya daki mirror din tarwas ya fashe hannunsa yafara jini kayan kan dressing mirror din yafara watsi dasu yana harbe harbe. Su ummi suna falo sukaji karar fashewar abu, da gudu suka nufi bakin kofan dakin amma sukajita akulle, kaya kawai yake zubarwa akasa,ummi ce tafara dukan kofan tana cewa" Aryan pls don't harm your self wlh nasani sharri akamaka I trust you,pls son ka bude kofar dan Allah " Nana ma na ihu tana dukan kofar tace"Ya Aryan dan Allah karka harming kanka, pls open the door" Dada tama rasa mezata ce dan babu abinda ta fahimta sai kuka itama ta keyi tana karamin maigida ka bude kofarnan karka wakanka illa" duk abinnan da sukeyi awaje ko gizau Aryan beyiba, in akwai abinda ya tsana shine a tarnishing image dinsa yanzu kuma Lubna tashiga inda bazata iya fitowa ba dan babu makawa saiyayi maganinta. Jirinda ya dibesa ne yasashi zama akasa ya kama kansa dake barazanar fashewa.


******
Noor na kwance akan gado bayan ta idar da sallah suna hira itada Hanifa sukaji salatin Hanan. Juyowa sukayi suna kallonta Noor tace"ke miye haka meya faru zakina wa mutane salati" wayan hannunta ta mika musu wayan. Zaro ido Noor tayi ta kara zooming vidoen da kyau, haka kawai taji kamar wannan videon ba gsky bane," kai wlh niban yarda da wannan video dinba, sharri kawai akemasa kuma sai Allah ya tona asirin mugaye" hanifa ta fada tana girgiza kai. Waya Noor tadauka takira Nana amma wayanta is unreachable daga bayama saitaji wayan akashe, haka kawai saita tsinci kanta dajin tausayinsa duk da batasan ko gsky bane amma ita zuciyarta yafi bata sharri aka masa. Haka suka zauna adakin sunyi jugum jugum kamar anmusu mutuwa.


Ya Shareef ne yana kai kawo a office dinsa kana kallonsa kaga tashin hankali kwance a fuskarsa. Knocking secretary din Aryan yayi ya shigo yacewa Shareef"sir, yan press ne agaban company din suna fadin lallai sai ankira musu sir Aryan" a fusace yafita daga office din ya sauko har kasa yasami journalist sunyi cirko cirko suna fada da securities abakin gate din company din. Suna ganinsa camera yakoma kansa kit kit kawai kakeji ana daukansa hoto," wai Ku wasu irin marasa hankali ne, Ku bazakuyi bincike ko abu yakasance gsky bane kafin Ku fara sintiri agaban office din mutane"? Daya daga cikin yan jaridan yace" dama Mr Aryan womaniser ne amma yake wani acting kamar boss agaban mutane" sauran ma suka fara shewa kowa na fadin abinda yazo bakinsa. Sosai ran Shareef ya baci dan wannan rashin mutunci ne ga abokinsa, juyawa kawai yayi jiki a sanyaye ya koma cikin building din yana hada hanya saboda bibbiyu yake gani. Kayansa ya hada ya fito sannan ya dau motarsa yafice ta back gate inda babu mutane sosai.


Su ummi da Nana suna zaune afalo sunyi wujiga wujiga kamar masu zaman makoki, kowa da abinda ya damesa, sunyi juyin duniya Aryan ya bude kofarsa amma yaki gashi babu me spare key acikinsu, Abba ya kira wayan ummi kamar bazata dauka ba saikuma ta dauka tayi sallama da dasashshiyar muryanta data sha kuka" dear Dan Allah karku bari komai ya dameku, ganinan ahanya insha Allah, hope Aryan is okay"? Ya tambayi ummi cikin tashin hankali, ummi ba bakin magana kawai ta kara fashewa da kuka, kit Abba ya kashe wayar dan baya kaunar jin kukan ummi, Nana yakira dan ya fada mata ta kula da ummi dan tanada hawan jini, amma saiyaji wayar akashe.


Horn Shareef yayi a bakin gate din gidansu Aryan mai gadi ya wangale masa gate din yashigo. Yana shiga falon bakinsa dauke da sallama yagansu ummi zaune shiru shiru, suna ganinsa suka mike, Nana tazo wurinsa tace" Ya Shareef dan Allah kabude kofar dakin Ya Aryan karya illata kansa plss" babu musu yanufi kofar dakin shima hankalinsa atashe, wani wawan duka yakaiwa kofar tabudu, zaune suka sameshi akan gado yakama kamsa da hannu bibbiyu ga jini duk ya bata masa jikinsa, ummi naganinshi takaraso dagudu ta rungumeshi tana kuka, dagowa yayi da jajjayen idanunsa kamar wuta ya kallesu one by one sai kuma ya kara dukar da kannasa. First aid box Nana ta dauko ta mika wa Ya Shareef, ahankali ya tako har gabansa ya tsuguna ya kamo hannun yafara dressing dinshi harya gama,Nana kuma ta kira mai aiki suka hadu suka fara gyara dakinnashi tsaf tsaf. Abba ne ya shigo da sauri bakinsa dauke da sallama ya karaso gaban Aryan ya kama hannunsa yace" Karka damu babana, your reputation won't go down the drain, nidakaina zan koya wa Aisha da 'yarta hankali" sai yanzu Dada tagane inda maganar ta dosa tace" yanzu dama Aisha da wannan shegiyar 'yartata itace sanadiyyar shiga wannan halin dayayi, aiko babu mai tabamin maigida yazauna lfy"sannan ta kalli Nana tace " ke kazar makota dauko mun wayata adaki kikira min Aisha inason ganinta yanzunnan"babu musu Nana tayi abinda Dada ta umurceta bayan ta dauka wayar ta dialling numbern Anty Aisha, tana daukawa tamikawa Dada ko gaisuwarta Dada bata amsa ba tace" kizonan gidan yanzu ina buqatar ganinku keda wannan yar iskar yartaki" kit ta kashe wayar bata jira me Anty Aisha zatace ba.

Itakuwa anty Aisha tana aje wayar ta kalli Lubna wadda itama ke kallon mamannata tace" kishirya Dada na neman mu yanzu" wani irin yamutsa fuska Lubna tayi tace" nidai gaky banida niyyan zuwa gidan kije ke kadai" dakuwa Anty Aisha tamata tace dole saisun tafi tare, babu yadda ta iya haka ta shirya suka taho. Afalon suka zauna daidai nan su ummi sun fito daga dakin Aryan bayan sun samu ya kwanta, ummi naganin Anty Aisha tawatsa mata wani irin kallon tsana tawuce sama dan bazata iya zama afalon ba zuciyarta na iya bugawa, Anty Aisha ko ajikinta kamar ma basusan meyafaru ba. Dada ce tafara magana tace" Aisha duk cikin yarana babu wadda ke bani ciwon kai tun kuna kanana kamar ke, kin masance mara ji sosai gashi kin haifi 'ya kamarke mai bakin hali babu abinda ta rage ki dashi " Lubna ko ajikinta saima latsa wayar ta datakeyi, wani irin tukukin bakin ciki ne ya mamaye Nana har batasan lokacinda ta taso tayi kan Lubna ba, wayar hannunta ta kwace tayi jifa dashi pas pas pas haka kakejin karar fashewa, afusace Lubna ta daga hannu zata mari Nana taji ankama hannunta, juyowan dazatayi taga Abba, saukan marin dataji afuskarta ne ya Sanyata faduwa akasa ta dafe kuncin nata, batayi aune ba takarajin saukan wani lafiyayyar marin guda biyu both sides din fuskarta. Duka sosai Abba ya rufe Lubna dashi harsaida Ya Shareef yafara kamashi yana bashi haquri, Dada kuma sai "karamata shegiya" kawai take fada, Anty Aisha tama rasa mezatayi. Haka Abba yamata lilis sannan ya nuna tada yatsa yace" daga yau karna kara ganin kafarki agidannan, ke kuma Aisha koda bakin wasa karki kara kirana awaya kuma kar na ganki agidana babu ni babu ke"mikewa Anty Aisha tayi tace" shikenan tunda haka kukace, damani na dade da Sanin cewa baku kaunata nida 'yata dan haka natafi yaya kuma bazaka kara ganina a unguwarku bama balle gidanka" tana gama fadin haka ta ja Lubna suka fice ransu fes tunda sun dau fansa akan Aryan, ko abanza sun batamasa suna agari.

Wunin ranan babu wadda yayishi cikin dadin rai musamman Aryan,wani irin zazzabi ne ya rufeshi amma saboda kafiya da dauriya irin tasa babu wadda yasani. Haka ya kwana idonsa biyu sai gabannin asuba bacci mai nauyi ya daukeshi.


Washe gari

Su Noor sun tafi gidansu, sosai 'yan uwan Daddy sunyi murnan ganinta amma bandasu Mama da yan uwanta dakuma Moon, ko ajikinsu haka suka sake da yan uwa anata hira, abinda ya kara tunzura Mama kenan amma babu daman yin wani abu ga idon jama'a. Noor na kitchen tana shan ruwa Mama ta shigo babu kowa a kitchen din saisu biyu, dogon gashinta ta kama taja harsaida tayi ihu Mama tace" naga alama yanzu kinyi gashin hammata har wani kallon kasa kasa kike min, toh wlh zanyi maganinki, kinmance daddyn naki dani yake zama kinsan sarai abinda zan iyayi masa" cikin tsoro Noor tace" Mama Dan Allah karkimasa komai wlh in baki so ma ayi bikin dani ko yau sai mukoma amma na rokeki karkiwa daddyna komai" murmushin mugunta Mama tayi dan dama tsoratar da ita kawai take sonyi tace" inhar bakiso namasa komai toyazama dole kibar garinnan gobe inba haka ba..." Saitayi dariya mai sauti tafice daga kitchen din. Awurin Noor ta tsuguna tana rera kukanta tana ayyana irin rashin imani na Mama. Haka taci kukanta tafito tasamesu Anty Jamila tace lallai ita bazata zauna agarinnan ba. Sunyi sunyi da ita ta fada musu menene amma taki, haka suka kyaleta suka shirya suka bar gidan, suna isowa gida suka fara shirya kayansu. Anty Jamila taso fadawa daddy maganar komawarsu amma Noor ta hanata.


Yau zazzabin Aryan da sauki. Shida shareef tun safe suke office dinsu suna bincike akan wadda ya dau video dinnan. Suna zaune a office din wata ma'aikaciyar company din ta shigo bayan ta dau excuse. Zama tayi sannan ta mika wa shareef wayarta ,cikin mamaki yace" a ina kikasamo wannan videon" ma'aikaciyar mesuna Ramlat tace" nazo submitting wani file ne a office din sir kawai sainaganta tana masa magana shine naji abinda suke planning nace bari inyi video. Aryan ya dago kansa da Sauri jin maganar ramlat, hannu ya mika wa shareef yabasa wayar, videon Lubna ne da wannan ma'aikacin dasuka hada baki lokacin da suke planning abinda suka aikata. Wani irin murmushi ne ya subucewa Aryan, ba shareef ba harta Ramlat saida sukayi mamaki, dama Aryan na dariya? Mikewa yayi da Sauri ya fice a office din bayan ya tura videon awayarsa.

SHARE AND COMMENT

REEMAH ✍️
10/9/23, 2:19 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH


PG 21_ 22


Yana fita a office din still fuskarsa dauke da murmushi amma yana ganin yadda mutane ke kallonsa ya gimtse fuska yadawo real Aryan dinsa. Yana isa motarsa yaji shareef na kiransa, ko juyowa beyiba ya shige abinsa, da sauri shareef shima ya shige side din me zaman banza. Babu wadda yayi magana acikinsu driving kawai yakeyi hankalinsa kwance. A bakin gate din gidan Anty Aisha yayi parking yafito, sosai shareef yayi mamakin ganin inda sukazo azuciyarsa yace"sabon drama chapter two" shima ya fito ya bisa har cikin gidan. Luckily kuwa yasamu Lubna tana gida. Anty Aisha da lubna suna zaune afalo sukaji an bankado kofa anshigo amma basuji lokacin dayayi sallama ba. Arazane Lubna tamike ganin wadda ya shigo dan babu alaman wasa a fuskarsa saidai wannan karon idanunsa basuyi ja ba. Anty Aisha ce ta daka masa tsawa a lokacin daya nufo Lubna gadan gadan kamar wani zaki amma ko ajikinsa, gudu take shirinyi shikuma ba girmansa bane yafara tsere da wata, watanma Lubna. Wani banana peel din data gama ci a plate ya dauka ya hurga agabanta batayi aune ba taji ta taka bawon ayaban, suuuuuu kakeji timmmm Lubna tafadi akasa tasaki wata uwar ihu ko salati babu(anya ma tasan me salatin yake nufi😒). Hannunta yakama ya matse da kyau ya matse mummunan bakinnan daya kai masa hari ya matse, garin kwatan bakinta daga rikon dayayi masa ta gurje shi da haqoranta. Wani leda ya fitar daga aljihun suit dinsa,( inna lillahi Aryan beda mutunci kai jama'a😂😂) kasa ne dam acikin ledan yafasa ta sannan ya diba yafara dirje bakin Lubna dashi tana ihu, Anty Aisha tayi kansa zata hanasa abinda yakeyi amma Shareef yamata wani wawan riko dabazata iya kwatan kanta ba. Saida ya karar da kasan nan tas a bakinta wadda saida ta hade wani tana kuka kamar zata hadiye ranta sannan ya saketa yana sakin kyakyyawar murmushin muguntannan nasa. Sink area dake dinning ya nufa ya wanko hannunsa sannan yanufi hanyan waje, shareef ma ya sake Anty Aisha yabisa a baya. Suna shiga mota yace" I'll send you that video kasa a goge waccan sai a uploading wannan kuma a account din datayi amfani dashi nakeso a sa which means her account is gonnan be hacked" kai kawai shareef ya gyada sannan ya kunna motarsa suka bar wajen. Wani irin nishadi yakeji aransa yanawa Allah godiya daya wankeshi.


Itakuwa Anty Aisha wurin Lubna tanufa wacce keta birgima a kasan tiles kamar me sabon ciwon hauka tana Allah ya isa. Da kyar ta yadda ta tashi tawuce bedroom dinta tayi wanka ta wanke bakinta wadda keta mata zafi kamar me,danyaji mata ciwo abakin. Tanayi tana kuka. Lallai muguntan Aryan baida part two, ita wlh bazata kara wani plan akansa ba kar yazo wani karon ya mata illa ajiki.(😂😂😂Lubna anyi laushi shegiyan miya).


********
Noor na hada kaya tana kuka amma Sam taki fada wasu Anty Jamila meke damunta. Ita Anty Jamila wani bangare na zuciyarta ma murna takeyi dama bason attending bikin take ba dande kawai yakama dole ne. Su Hanan sunshiga damuwa tunda suka ga 'yaruwarsu cikin rashin walwala. Haka suka zauna babu wadda ke magana acikinsu. Ko dan abincin nan ma Noor taki ci haka suka barta amma badan sun so ba.


******
Ummi suna zaune adaki itada Dada da Nana kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa sukaji sallaman Aryan, dama tun kafin sutashi daga bacci yafita a gidan. Da sauri ummi ta mike tana amsa sallamarsa. Mamakine a fuskarsu ganin murmushi afuskarsa, ummi tace" Son karde abunnan ne yafara affecting dinka harka fara dariya baka sani ba, nashiga uku Allah ya isa tsakanina da lubna tasa dana yafara zama tababbe"(toh kunsan abinda ba normal bane dole akirashi da abnormal ai, Aryan besaba murmushi ba inba wani dalili saikuma gashi yau yana murmushi free of charge). Kama hannunta yayi suka zauna abakin gado,su Nana da Dada sun zuba musu ido suna jiran jin mezaice musu, juyowa yayi ya kalli Nana yace " check your Twitter, search that useless girls page and see" da sauri tayi abinda yasata, wani irin tsallen murna tayi tana hamdala, ummi ta karbi wayan itama ta kalla dan lokacin har an goge waccan ansa wannan na wayan Aryan. Sujudush shukr ummi tayi tana godewa Allah daya wanke danta daga wannan gagarumin sharrin. Dada akaba wayan itama ta kalla tace" shegiya Lubna kalli kayan ma dake jikinta, ohh ni yanzu irin tarbiyyar da Aisha tabawa yarta kenan, hmm lallai tajira sakamako" haka sukaci gaba da godewa Allah shikuma Aryan ya fice yabarmusu dakin ya wuce na sa. Ya na shiga ya rage kayan jikinsa ya shige bayi, abakin shower ya tsaya ya kunna warm water, ya kusan minti goma ruwan na dukan jikinsa sannan yayi wanka ya dauro alwala yafito. Jikinsa ya daure da towel looking sexy as always yana tsane gashin kansa daya jike da ruwa sannan ya shafa mai ya fesa turare yasanya dogon crazy jeans da singlet ya fito falonsa ya zauna yana latsa wayarsa.


******
Washe gari da sassafe su Anty Jamila suka kamo hanyan dawowa, Noor takiyin magana sai kuka, at this point Anty Jamila jikinta ya gama bata cewa Mama ce silar kukannan na Noor, Allah wadai da irin halin Mama tadinga yi tana rarrashin Noor harsuka iso garin Abuja karfe shabiyu daidai. Suna isa gida tawuce daki, kayanta ma su Hanan ne suka shigo dashi, kukanta tacigaba da rerawa tana kiran sunan Ammi tana rungume da hotonta. Daddy ne ya kira Anty Jamila shine take shaida masa abinda ya faru, ko kadan beji dadi ba amma ya roketa dan Allah ta kula da Noor.


Abba tunda yaga wannan videon shima yadinga hamdala yana godewa Allah daya wanke dansa.


Agurguje pls

Yau juma'ah kuma yau ne jama'a suka shaida daurin auren Maimuna Nasir da angonta Mahmud Ja'afar. Sosai tasha kuka lokacin da za'a kaita harta bawa mutane tausayi, Mama kam kuka ba'a magana yau ta rabu da tilon 'yarta kenan fa, sosai sukayi kuka kafin aka samu aka raba Moon da mamarta sannan aka shige da ita mota aka kaita sabon gidanta mai kyau Masha Allah. Saida mutane suka watse ango yashigo shima bayan ya sallami abokansa. Wani irin tukukin bakinciki taji alokacinda daya shigo. Mahmud mutum ne kamili kuma yanada haquri, shima yanada kyawunsa iya gwargwado. Da Kyar ta yarda sukayi sallah(toh ko agida batayi balle kuma yanzu ta auri ustaz). Bayan sun gama cin Kazan amarci wadda kusan meyawan ango ne yaci dan ita takici sosai. Abubuwan dataga yana mata wadda hankali bazasu dauka bane yasata kuka tana rokonsa, yanzu idan ya rabata da kimarta, salis ya kubuce mata fa kenan, shiko Mlm Mahmud Sabon shiga ai duk haqurin duniyarnan babu wadda yaji, haka ya afkawa yar gaban goshin Mama tana kuka tana Allah ya isa.


*******
Yau Saturday da sassafe ya fito cikin track suit dinsa me kyau white and black yafita jogging. Yana dawowa karfe bakwai yawuce dakin exercise dake BQ din gidan yafara daga karafunan nan nasa masu hegen nauyi kamar ana basu abinci. Bayan ya gama yafito ya shige bedroom dinsa yayi wanka yashirya cikin kananan kaya masu laushi sai sheki yakeyi da baza kamshi. Yana fitowa yasamu anriga ankawo masa fruit salad dinsa wadda ya kunshi different types of fruit kama daga su grape, apple,kankana,abarba,lemu da sauransu. Bayan ya gama ci yafara aiki akan laptop dinsa. Kwatsam kawai tunanin Noor yafado masa lokacinnan daya matse bakinta tana ihu, besan lokacinda yasaki tsaki ba yace" foolish girl".

Su ummi suna zaune a falon Abba ita dashi suna hiransu yace " dear yanzu gidan Aryan ya kammala amma kinga yaronnan ko maganar fidda mata bayayi nina rasa meke damunsa wlh." Ummi tayi murmushi azuciyarta tace" Alhamdulillah this is the right time" sannan tacemasa" dear dama akwai wata yarinya wlh har cikin raina nake jin ta kuma nakewa Aryan sha'awarta" da mamaki Abba yakalli ummi yace" wacce yarinya kenan"? wata kawar Nana ce course mate dinta ce" Abba yace" kardai wannan yarinyar da Nana ke yawan magananta Noor ko"? Da sauri ummi ta gyada kai tana murmushi,Abba ya sauke ajiyar zuciya yacemata" shikenan ai takwana gidan sauki insha Allah innayi bincike nida kaina zansamu iyayenta namusu magana" sosai ummi tayi murna da response din Abba, babu abinda zatafi so ayanzu kamar taga Noor tazama matar Aryan dinta..


Su Anty Aisha anyi bakin ciki har an godewa Allah, Aryan ya dukesu kuma yahanasu kuka, Lubna tayi mamakin yadda Aryan yasamu wannan videon dan saida ta hada baki da yan control room ankashe kowani camera a company din. Lallai Aryan yacika dan duniya.


Kuyi haquri da wannan plss


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/12/23, 6:20 AM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j

🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH


PG 23_24



Yau hutun su Noor yakare zasutafi school dan yau Monday ne. Ta gama shirinta cikin corporate wear dinta mai kyau. Dark blue straight skirt ne da white shirt me long sleeve, rolling tayi da dan karamim veil dinta shima dark blue sai kuma takalmin kafarta low pass shima dark blue tayi kyau sosai dukda babu makeup a fuskarta illa powder sai kwalli da kuma transparent lipgloss. Bisaga umarnin addini Noor bata sa turare, in har zatasa to wadda ita kadai zata rika shaka ne sai in mutum ya matso kusa da ita shine zaiji. Ayanzu itama ta kware a tuki dan haka yau itace zata tukasu zuwa school. Motarsu sabo mai kyau da uncle saif ya siyamusu sakamakon result dinsu dayayi kyau, dashi zasu tafi. Hanan na gefen mai zaman banza, hanifa kuma na baya, tuki takeyi cikeda kwarewa ahankali har suka iso harabar makarantar. Ahalin yanzu Noor ta saba da irin kallon da ake binta dashi a duk lokacin data shigo makaranta, ba maza kadai ba har Mata. So dayawa mazaje nakawowa Noor tayin soyayyarsu amma kamar ma basu isheta kallo bane,batasan me ake nufi da soyayya ba dan agida Mama bata sake mata

Please Login or Register in order to submit comment