Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar tasan shine, damtsen hannunsa ta kama da karfi sosai, hannun yayi wani sanyi, gashi yanzu hoto kawai na shirin daukar ran matansa inaga kuma sun hadu ido da ido, fatarsa kawai shine ayi mata cs din lfy, Ammi da sunaina sun shiga wurin Doctor ana duba sunaina saboda ciwon mara daya addabeta tun jiya da daddare, ashe period dinta ne,irin yara masu fara menses da wurine. Basu fito ba har aka shige da Noor dakin theater,wani kujera ya samu abakin kofar ya zauna ya dafa kansa dake masa ciwo sosai. Daddy ma yafito idanunsa duk sun kumbura sunyi ja abunka da farin mutum har fuskarsa tayi jaa,bawan Allah. Zama sukayi akujera daya da Aryan babu mai cewa uffam. Ko lokacin da su Ammi suka fito, sunaina kadai aka kai gida, itakuma Ammi ta zauna anan asibiti, duk yadda Daddy yayi da ita ta tafi amma ta kiya, tace saitaga matar wannan matashin, babu yadda ya iya haka ya kyaleta, zama tayi kusada Aryan tana masa magana kasa kasa, jiyake kamar Noor dinsa ne ke magana saboda muryarsu Sak iri daya, shidai baice komai ba, addu'a kawai yake azuciyarsa. Lokacin sallan zuhr yayi still basu fito daga operation room dinba. Hannunsa Daddy yakama kamar karamin yaro suka tafi masallaci, basu dade da tafiya ba doctor ta fito tana nemansa, Ammi ce ta mike tayi magana da ita,"are you her mum" doctor dinta tambayeta, batayi tunanin komai ba tace ehh,nodding kai tayi tace" dama jini muke buqata, ban sani ba ko blood group dinku yazo daya da nata, are you O- "? doctor din ta tambayi Ammi, da sauri Ammi ta gyada kanta alamar ehh, what a coincidence, bata Santa ba amma ikon Allah jininsu yazo daya, basu bata lokaci ba aka gwada jinin, within fifteen minutes aka debi jininta, su Aryan sundawo basu ma nemi Ammi ba, babu wadda yake hayyacinsa dagashi har Daddy. Can cikin theater kuwa anyiwa Noor alluran pain relieve, amma ko ajikinta sai kiran Aryan take, kowa na mamakin wannan soyayyar dake tsakaninsu, taki natsuwa sai juyi take da kafarta ita lallai akira mata Ya Aryan dinta, wata nurse ce ta fita ta sameshi awaje yana kai da komowa, apron da hulan theater ta mika masa ya sanya suka shigo tare, idanunta na kan kofa tana ganinsa tafara miko masa hannu tana Baby love, ta basa tausayi duk ta galabaita ta fita hayyacinta, ba tareda bata lokaci ba aka fara mata aikin, hawaye ne ke gudu a kumatunsa ganin yadda ake fede matarsa ba imani injishi😂😂, baby daya aka fara fiddawa dan karami dashi fari tass da sauri aka nadeshi cikin towel wata nurse ta karba, dayan babyn aka fitar shima baby boy kamar wancan girmansu daya in akwai bambamci ma kadan ne, fari tasss Masha Allah, kamar wancan ma wannan aka nadeshi cikin towel, aka dinke Noor wadda by now jikinta yayi lakwas. Aryan yama rasa mezaiyi, farin ciki ko akasin haka, yana farincikin successful operation din matarsa, ga kuma bakin cikin halinda take ciki. Tsaf aka gyara babies din aka sanya su cikin incubator duk da sunada dan girman su daidai gwargwado, at least kowannensu yana weighing 2.3kg, Noor batayi wasa da abinci ba ai dole yara sufito da girma wannan inda sun kai watanninsu ai dole nema ayimata cs dan bazata iya aihuwa dakanta ba. Itama aka gyarata aka kai VIP room na hutu kamar dakin amarya komai tsab tsab. Daddy dake waje da Ammi bayan ta fito daga dakin da aka debi jininta sunyi tsuru tsuru suna jiran afidda Noor daga dakinta. Kiran Ammi akayi awaya ta fita lokacinne kuma aka fitar da Noor daga theater, da sauri Daddy yasa aka shige da ita kafin Ammi ta dawo. Da kyar Daddy ya lallaba Aryan ya koma gida yayi wanka ya canza kaya he looks tattered. Can Ammi tadawo tace" naga yaron ya tafi an fitar da ita ne"? Gyada kai Daddy yayi, sujudush shukur Ammi tayi tana godiya ga Allah, taso shiga dakin amma Daddy yaki yace doctors sunce tana buqatar hutu, haka ta haqura ta ce zata tafi gida amma anjima zata dawo.

Aryan kuwa yana isowa gida yayi wanka sannan yasamu ya dan huta, wayarsa ce tafara ringing yama mance yabarta agida. Har kusan ten missed calls ummi tamasa dan dama haka takeyi, kowani awa daya take kiran Noor taji ya lafiyar jikinta, toh data kirata dazu ba'a daga ba yasa hankalinta tashi musamman kuma data kira Aryan har ten missed calls shima bai daga ba. Yanzu ma data kirashi tana tunanin zuwa gidan ne in bai daga ba amma kuma Alhamdulillah sai yanzu ta sameshi, cikin tashin hankali take tambayarsa lfy, bai boye mata komai ba ya fada mata abinda ya faru amma banda maganan Ammi, tundaga waya tafara masa fada akan meyasa bai kirata ba tun kafin su tafi asibiti har saida aka gama komai, ummi bata san cewa shima ba'a cikin hayyancinshi suka tafi hospital din ba. Nan da nan labarin aihuwar yafara zaga dangi na nesa dana kusa. Su Anty Jamila kan kace me suna asibiti amma anki barinsu suga babies saidai Noor itama din saidai abakin kofa zasu tsaya dan ba'ason hayaniya. Aryan ma yanzu ya dawo asibitin, kwata kwata bashi a hayyacinsa Ummi dataso yimasa fada insuka hadu a asibitin saikuma ta fasa saboda ganin yanayin dayake ciki. Suna wannan yanayin, labari ya iskosu Lubna ma ta sauka tahaifi danta namiji kuma suna lfy, anyimata Allah ya raya amma babu wadda yaje duk suna nan ana dokin ganin twin babies. Babies din are doing fine ma kamar ba bakwaini ba, ana sa ran nan da kwana biyu ma a ciresu a kwalbar in mahaifiyarsu ta farka kuma babu damuwa ana iya sallamansu.

Wuraren karfe bakwai bayan maghrib Daddy na asibitin duk suna zaune a agaban dakin dasu twins din Anty Jamila dasu Ummi dasu Nana su Ya Shareef su Na'ima duk suna zaune wasu suna tsaye har yanzu Noor bata farka ba. Sallama sukaji gaba dayansu suka dago suna kallonta, rike take da basket din ruwan zafi ga su bread da kayan tea, Daddy salati yafara a zuciyarsa, shikenan magana ya kare, Anty Jamila zumbur ta mike tana murtsuke idanunta, ita kanta Ammi dataga Anty Jamila awurin sai ta rude, su Ya Shareef kowa bakinsa abude yake kallon matar dake gabansu, Aryan duk wannan ba shine agabansa ba, iyanzu hankalinsa yafara tashi meyasa har yanzu Noor dinsa bata farka ba gashi anki barinsu su ganta, bini bini ya mike yana lekata ko ta farka. Anty Jamila ragab ta samu wuri ta zauna tana ambaton inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Sallallami kawai ke tashi from every angle, Ammi ta karaso inda Anty Jamila ta zube ta riko hannunta, a tsorace ta fizge hannunta dan har yanzu bata yarda da abinda idanunta ke ganemata ba, Hanan da Hanifa suka taso zuwa inda su Anty Jamila ke zaune, dafa Ammi sukayi dukkansu biyun idanunsu sun cicciko da kwalla, mikewa Ammi tayi ta rungumosu ajikinta sai suka fashe da kuka, babu mai rarrashin wani, Anty Jamila ma ta mike ta rungumesu atare sai suka cigaba da kukan. Ummi da Nana na tsaye suna kallon ikon Allah, kenan ammin Noor tana raye,wani iko sai Allah,da sauri Aryan dake tsaye ajikin kofar dakin Noor ya juyo yana kwalawa nurses kira akan ta farka, mutanen dake wurin kowa ya juya da sauri zuwa kofar dakin, nurse da doctor ne suka shiga dakin, kowa na lekenta ta kofa masu farinciki nayi masu hawaye nayi, Ammi ta kosa taga wacece aciki, acan ciki kuwa, Noor ta farka amma ba'a bari ta mike ba saboda aikin dake jikinta sai ta releasing air kafin tafara motsawa, suna fitowa aka basu daman su shiga amma two at a time, Aryan bai bari ta karasa magana ba har yana bangajeta da sauri ya kusa kai ciki, Noor ba ganinsa ta fashe da kuka, rungumeta yayi yana jin wani sanyi, sai yanzu yakeji kamar an sauke masa wani gamu a zuciyarsa. Kuka takeyi yana bubbuga bayanta yana rarrashi, sauran mutane awaje sun kagu su shiga su ganta amma Aryan baima da niyyar fitowa, Daddy bayaso Ammi ta hadu da Noor yanzu gudun abinda zai biyo baya. Kusan thirty minutes kafin Aryan ya fito, su Anty Jamila da ummi suka shiga, haka suka dinga shiga suna fitowa kafin daga karshe Daddy shima ya nufi hanyar shiga, ga mamakinsa sai ga Ammi abayansa itama zata shiga, ya riga yasawa ransa komai yazo karshe dan haka ba tareda musu ba suka shiga tare. Noor na kallon kofar,Daddy kawai ta gani bataga matar dake bayansa ba, har ya iso bakin gadonta ta kafeshi da gajiyayyun idanunta, ahankali Ammi tafito daga bayan Daddy, suna hada ido da Noor kowannensu yaji zuciyarshi ta buga. Noor na kallonta amatsayin gizo take mata, itakuma Ammi tana mamakin ganin Noor, kenan itace tabawa jini dazu ,kenan yartace ta aihu, kenan wannan matashin shine mijin Noor dinta. Kuka Noor ta fashe dashi ta kankame rigar Daddy tana cewa" Daddy ka taimaka min banaso na mutu yanzu, ance in lokacinka ya kusa mutanen dasuka mutu suna zuwa maka a matsayin fatalwa, Daddy banaso na mutu yanzu babies dina da Ya Aryan wazai kula min dasu" kamo hannunta Ammi tayi da sauri ta fizge, tsabar tsoro batama lura cewa in fatalwar gaske ne jikinsu bazai mannu ba, itakawai kallon fatalwa takewa Ammi. Matsawa Daddy yayi yabawa ammi space, wani kallon zamu hadu dakai Ammi tayiwa Daddy da sauri ya juya ya fice adakin yana dan sakin ajiyar zuciya. Noor fa taki Ammi ta tabata, da kyar Ammi tasamu ta kwantar da hankalinta bayan ta kira sunanta, shiru tayi tana kallon idanun Ammi, so take ta gasgata abinda take gani, mintsilin Ammi tayi har saida tace aushh, da gaske fa amminta ne agabanta, amminta bata mutu ba. To ya akayi haka bayan a idanunta ta daina numfashi. Rungume juna sukayi suka fashe da kuka, duk sauran suna tsaye bakin kofa suna kallonsu cikeda burgewa. Farin ciki double double kenan, ga Ammi tadawo Allah zai kawo musu karshen Mama, gakuma aihuwar da akayi masu, a ranan Ammi ce ta kwana da Noor taki kowa ya zauna da ita sai amminta, hatta Aryan jan ido tayi masa a haka bai haqura ya tafi ba, abakin kofar dakin ya zauna yana dan gyangyadi, Ammi na zaune bakin gadon Noor itakuma tayi bacci anyi mata allura dan haka basuyi wani hira ba duk da Noor taso suyi, shafa kanta takeyi ahankali, har yanzu Noor bata canza ba akwai surutu. Yau Allah ya nuna mata gashi ta zama kaka. Saidai kuna tana ta zuba ido kozata ga autan maza suhail har yanzu bata ganshi ba. Gobe zata tambayi Daddy.


Cikin ikon Allah washe gari aka samu Noor ta releasing air kamar yadda ake buqata in akayiwa mutum operation. Tea mai kauri doctor tasa aka hada mata, Tass ta shanye saboda yunwar dake addabarta, babies ma Masha Allah sunyi lfy babu wani damuwa, karfe goma aka fitar dasu, amma ba'a bari anyi jagwalgwale dasu, Aryan aka bawa na farkon Ummi kuma ta karbi dayan, sunyi matuqar kama da Aryan kamar shiyayi kaki ya fiddasu, kwantancen gashin kansu sak na babansu kalar ne kawai na mamansu baki wuluk dasu, eye colour dinsu ma irinna Aryan ne irin sharp brown dinnan. Sai mamulan hannu sukeyi alamun suna iin yunwa, lokacin kuma Noor tayi bacci bayan ammi ta taimaka mata tayi wanka. Kamar jiya yau ma kowa na asibitin, tuni Dada ta dau hanyar Abuja itada sauran matan gidan su matan Alhaji Jibril da matan kanne da yan uwa. Abun ba'a magana mutum zai dauka biki ake a asibitin. Bayan asr aka sallamesu, Ammi ta nemi alfarmar abata Noor tayi wankan jego agidanta, ba haka Aryan yaso ba amma yana jin nauyinta dan haka ya yarda. Tare suka tafi gidan ammin bayan sallan maghrib kowa ya tafi gidansa amma banda su Hanan da Anty Jamila. Dada na saukowa garin Abuja tace lallai saidai akaita gudan Ammi tunda anan akace ankai Noor. Karfe tara saiga Aryan da ledoji niki niki ya kawo, har dakin Ammi ya shiga, babu kowa adakin sai Noor dake kwance kan gado ga twins dinta agefe sai tsala ihu suke amma ko ajikinta, Dada ce ta fito saga toilet hannunta rikeda zaninta under skirt ne kawai ajikinta sai zanin rigar, ta fitone da Sauri saboda jin ihun yara, tace itace zatayi mata wankan jego, dan haka anan zata zauna. Ga mamakinta saiga Aryan akan gado ya dau 'ya'yansa both hand yana rarrashinsu Noor na kwance still bata motsa ba. " wai yar nan meke damunki, tun jiyan Allah akace min yarannan basu ci komai ba amma ke ko ajikinki, bazaki taimaka kibasu nono ko zasusha suyi shiru ba" Dada ta fada tana karbar Hussain daga hannun Aryan, in ran Aryan yayi dubu toya baci, shi ai bemasan cewa basuci abinci ba har yanzu daya sata agaba har saita basu. Ammi da sunaina suka shigo hannayensu dauke da tray na abinci, Noor na ganinsu ta mike ta gyara zama taga abinci, ashe dai har yanzu. Haba Dada ta rike tana kallon ikon Allah, wato ita ta cikinta ta sani amma bata 'ya'yanta ba, ahankali ta dafa gado ta mike ta sauko kasa kan carpet dan har yanzu ciwon nata bawai warkewa yayi ba, baje kafafu tayi kan carpet tayiwa sunaina nuni da gabanta akan ta aje mata tray din, ita Ammi abunma dariya yabata, ana masifa tabawa yara nono amma ko ajikinta ita kawai cikinta tasani. Tsaki Dada tayi tace" ai shikenan, Ku barta karku kuma cewa ta basu, idan suka isheta da zafi zata basune, kunjimin ja'irar yarinya ina yabonki sallah ashe ko alwala ma baki iya ba" mikawa Aryan Hussain tayi ta fice daga dakin tana surutai, Ammi da sunaina ma suka fice suka barsu su kadai. Zama yayi agabanta yadora babies dinsa kan ciya yana jijjigasu yana rarrashinta kan tabasu nono, turo baki tayi tace" Baby, kaga yarannan kadan ya rage su jefa ni duniyar da Ammi ta leka ta dawo, ni bazan shayar dasu ba ni yunwa ma nakeji" haushine ya kamashi, me take nufi bazata shayar dasu ba, watabari ya shayar mata dasu, a dan tsawace yace" Noor are you serious, wazai shayar miki dasu, ke baki tausayin bayin Allah ne da halin dasuke ciki, tun jiya fa rabonsu da cin abinci, ke bagashi ana kawowa kika fara afka ba, toh sukuma mekikeso suyi, plsss love kibasu nono kinjii plsssss" ya ja karshen maganar cikin sigar lallashi, narai narai tayi da ido tace" toh amma bari nagama shan tea dinnan karyayi sanyi" gyada kai tayi alaman ya yarda sannan yaciba da wasa da yaran, iyanzu sunyi shiru sai ajiyar zuciya suke saukewa alaman sunci kuka sun gode Allah. Bayan tagama sha ta karbi Hussain daketa mamula hannu, farar t-shirt ne ajikinta daga waje ma ana hango farin bra din dake ciki, dago rigan tayi zuwa saman chest dinta, mukut Aryan ya hadiye yawu, sun cicciko bulbul Masha Allah ba haske har wani shining sukeyi, ita kanta zafi yake mata saboda ruwa ya cika fam, abunka da Sabon shiga tama rasa ta ina zata fara bashi, ciro guda daya tayi ta kai masa saitin bakinsa, aiko caraf ya cafke yafara zukowa, ihu tayi tareda salati ta fuzgo bakin nononta daga bakinsa, aifa yaro ya tsala ihu inyaaa inyaaa, Ammi ta shigo da sauri tana tambayar lfy, Aryan ne ya fada mata gashi gashi, fada tashiga yiwa Noor tace" haka kowace mace ta fara, kuma zaki saba nan da wani dan lokaci, ai zafinnan zai marine inkika hanasu sha garama ku taimaki juna su rage miki radadi" tana fadin haka ta fice tana fadin Daddy ya sangarta Noor dayawa. Itako Noor tana matsar kwalla haka ta daure tasamasa abaki yana zukowa, yana sha tana kuka Aryan na rarrashi, saida ta basu suka koshi sannan suka kwantar dasu suka cigaba da hiransu. Karfe goma da rabi ya koma gida cikeda kewar matarsa.


Anan kuwa Lubna a gida ta aihu, Anty amarya ce ke kula da ita. Itama yaronta yayi girma sosai tunda shi gaki watanninsa, da kallon yaron ta gano wanene babansa, yayi baki kamar sadiqboii komai nasa ya kwaso babu kamanninta afuskarsa, dukda shi sadiqboii din kyakyyawar ne ba laifi saboda black beauty ne. Da kyar ta yarda ta shayar dashi, haka kawai take jin tsanar yaron a ranta, tsanar datakeyiwa mahaifinsa ne ya shafe shi, sosai Daddynta yayi mata fada kafin ta yarda ta shayar dashi. Babu wani danginta dayazo dubata, tunda taji Noor ma ta aihu sai jininta yayi sanyi, tasan itada ganin wani family member dinta kila sai bayan suna, Allah sarki, da ta aihu ta hanyar aurene da kila yanzu itama ana nan nan da ita kamar yadda akayiwa Noor. Rayuwa kenan, abinda ka shuka shi zaka girba.


Acan gidan Ummi su matan Alhaji Jibril suka sauka da sauran mutane banda dada dake gidan ammi, kafin the next day suma sutafi ganin babies. Ummi tayi kokari sosai wurin ganin ta providing dinsu da duk wani abinda suke buqata. Sunji dadi da akace ammin Noor tadawo dama sunji tausayin yarinyar lokacin dasuka ji cewa Amminta ta rasu shekarun baya. Kowa ranan ya kwanta cikin farin ciki.


Ammi fa ta addabi Daddy lallai saita ga suhail dinta. Tun yana kaucewa har kawai ya sanar da ita maganar mutuwarsa, sunyi sa'insa sosai dan Ummi ta fusata akan rashin gaya mata da baiyi ba. Daren ranan su kadai ne basu kwanta cikin dadi ba.


COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/15/23, 8:36 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 63_ 64

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

Karfe bakwai yayiwa Aryan agidan Ammi, Dada abun duniya ya isheta taita addabarsa wai akanme zai wani zo musu da sassafe jarababbe, shidai ko ajikinsa yana rike da Hussain wadda yagama shan nono yana wasa dashi, Noor kuma na feeding hassan. Ammi ce tayi sallama itada sunaina suka shigo da tray na breakfast an shake shi da kayan ciye ciye maisa yawun bakin mutum tsinkewa, aiko tunda Noor taga ankawo abinci ta mikawa Aryan babyn ta sauko kasan carpet din dakin ta baje aka fara Sana'a. Kwata kwata bata wasa da wannan fannin musamman ma yadda yaran ke tsotso sosai. Da misalin karfe goma su Anty Jamila da sauran mutane su matan Alhaji Jibril da sauran matan gida aka taru agidan Ammi anzo ganin babies. Gaba daya ranan Noor tana daki itada Aryan dayayi male male kan gadon Ammi kamar dakin uwarsa,ko kunya bayaji haka su Anty Jamila zasu shigo da babies in za'a basu nono suna gama sha kuma za'a fitar dasu. Ammi karan kanta dataga dai Aryan baida niyyar tafiya saita bar musu dakin gaba daya. Dada kuwa tayi mita ta gaji ta fita harkansa. Sai shagwaba Noor ke zuba masa shikuma yana biye mata saikace karamar yarinya, yo karamar yarinya mana mutum ya aihu amma yarinta yaki barin kansa. Shi da kansa ya taimaka mata tayi wanka, haka zai kulle kofar dakin da key har sai sun gama abinda sukeyi sannan ya bude. Da yamma kuwa kowa ya watse saiya rage Ammi da Anty Jamila da sunaina, Dada tabisu matan Alhaji Jibril dan cewa tayi rashin kunyan Aryan yafi karfinta bazata iya zama ba😂😂.

Sai sha dayan dare yabar gidan, shidinma saida Anty Jamila tasashi agaba dan ta lura baida niyyar tafiya ma gaba daya.

Sosai Noor da babies din ta suke samun kulawa yadda ya kamata, babu abinda takeyi daga ci sai sha saikuma bacci,Allah ma ya taimaka yaran basuda rikicin dare dan haka suke baccinsu hani'an. Ammi tadawo kwana da ita in case koda yaran suna buqatar wani abu da daddare.

Ana gobe suna, su anty umaima sun iso daga kano, gidan Ammi yacika makil da jama'a, wasu kuma suna gidan Ummi, wasu na gidan Anty Jamila. Noor tasha kwalliya cikin wata atamfa Holland blue mai ratsin black and white anyi masa adon flowers yasha stones agaban rigan,kayan dinkin riga da Zani ne amma skirt rapper yayi mata kyau sosai kamar bamai jego ba saita zama wata yar sweet sixteen da ita. Zaune take kan carpet ta baje kafa tana shan farfesun kan rago wadda yasha kayan hadi sai tashin kamshi yake, ga kuma chips din ta agefe da kwai sai tea kakkaura( kai Noor Allah yasamu adanshinku). Anty Jamila na dressing yara wadda akayi musu wanka sai tsala kuka sukeyi ana gasa musu cibi dan ya riga ya fadi tun jiya. Sallama sukaji, da sauri. Noor ta dago tana kallonsa, yayi bala'in kyau cikin wani half jumper blue colour yasha aiki mai kyau, ga hulan zanna bukar daya zauna das akansa kamar akan akayita, tundaga bakin kofa akejin kamshin turarensa wadda nan da nan ya mamaye dakin, wani irin murmushi ya sakar mata tareda winking idonsa daya, batasan lokacin data sauke kai kasa tana sakin murmushi ba, Anty Jamila da tuni tagama shirya yara tazauna tana kallon ikon Allah, ko ma ya san da ita adakin, shi kawai matarsa, ikon Allah. Karasa shigowa yayi saiga su Ya Shareef dasu Ya muhsin suma sun biyo bayansa suna jan akwatuna bibbiyu ahannunsu. Can saiga Nana da hanan suma sun shigo da daddaya, baki sake Noor ke kallon jerin akwatuna kamar na amarya. Bata gama tunani ba saiga Hanifa da yasmeen suma sun shigo da guda daddaya. Sallamansu Anty ounaisa da su Anty laila suka jiyo daga bakin kofa, wani tsalle Noor tayi ta mike zata karasa bakin kofa kafin su ida shigowa aikuwa unluckily ta harde kafa, da sauri Aryan ya tallabota ta fada saman wide chest dinsa, kallon juna suka shiga yi kamar yau suka fara ganin junansu, sun mance da mutanen dakin sun shagala da kallon juna, kit kit kit sukaji ana daukansu hoto, da sauri ta dago daga kirjinsa tana boye fuskarta atafin hannunta, shima shafa keyarsa yayi dan borin kunya, Ya muhsin ne ya sheke da dariya yace" lallaima Aryan, you've got some nerves, wannan irin rashin kunyan har gaban su abla hmmm" saikuma yakara fashewa da dariya su Ya Shareef ma suka dauka, su dai matan babu abinda sukace saima wuri dasuka samu suka zauna aka fara bude akwatunan da aka kawo. Da sauri Noor ta fice adakin shima yabi bayanta. Kayane sosai nagani na fada kamar na amarya, akwatuna guda takwas ne, hudu na Noor, hudu na babies, atamfofi su leshi gasu materials su abaya, kamar dai yadda akeyiwa amarya. Abun ba'a magana. Suna budewa ana hiran yaushe gamo, inda Ya muhsin yaja Nana suka bar dakin, Ya Shareef ma yaja Na'ima suka fice kowa yanemi nasa lungun ana shan love. Su hanan kuwa an zagaye baby, kowa na fadin sunan da za'a bawa yara suna ta argument tsakaninsu.


A garden din gidan su Noor da Aryan suka zauna,hira sukeyi gwanin sha'awa inda yake fada mata yadda yayi missing dinta atare dashi, gashi Ummi tace mai bazata dawo ba sai tayi arba'in. Itama harga Allah tayi kewarsa amma babu yadda ta iya, tana tsoron yiwa Ummi jayayya ne kawai. Haka yayita zuba shagwaba tana rarrashinsa, har ya bata tausayi, da kyar yake iya bacci dan ya riga yasaba dajinta ajikinsa itama kuma haka amma ita tana baccinta me kyau ma. Saida aka kira sallan zuhr sannan takoma cikin gida shikuma ya tafi masjid. Bayan sallah, masi lalle tazo tayiwa Noor kunshi.


Washe gari ranan suna, tunda safe karfe tara motoci suka fara hallara a gidan kamar biki akeyi. Manya manyan matan Abuja su kawayen ummi dasu Anty Jamila ga kuma matan abokan Daddy, Abba, da uncle saif duk sunzo da 'ya'yansu mata. Mai jego taci kwalliyarta anyi mata jan lalle yayi dark maroon sosai ga kuma bakin design din da aka mata yayi kyau Masha Allah, gashin kanta yasha gyara saboda tsayinsa yahana ayi mata kitso ga kuma tsantsinsa. Taci wanka cikin white shadda da akayi masa aiki da golden zare, an kashe mata dauri mai step step, ga gold jewelry din da Aryan ya siya mata ta sanya yayi kyau, babies ma sunsha kwalliya cikin kaya iri daya white and gold colour na baby boys. Kowa na santin yaran amma ba'a bari ana daukansu ana jagwal gwala su, suna kwance cikin baby bed dinsu

Please Login or Register in order to submit comment