Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sakeshi akasa, kansa ne ke wani irin bugu kamar zai tarwatse, kanwarsa uwa daya uba daya ta gama dasu, ta lalata sunan family dinsu. Kunyar Daddyn Lubna duk ya mamayeshi tunda ya sanar dashi abubuwan da suka aikata. Bai tsaya a iya nan ba, hatta zamansu a gidan honorable duk babu wadda baisani ba, ga kuma cikin Lubna wannan ma bashi bane ya dame shi ba tunda yasan halin Lubna, amma Anty Aisha gode gode da ita ace tana aikata zina? Wa iyazubillah. Aryan da Noor sukayi saurin zuwa wurin Abba suna tambayansa lfy, Anty Aisha da Lubna sun gama shan jinin jikinsu babu makawa asirinsu yagama tonuwa. Daddyn Lubna ne ya fara magana" assalamu alaikum, Ku gafar ceni mun zo batare da sanarwa ba, naga kamar Alhaji yana cikin wani yanayi dan haka nizanyi magana game da abinda yake kasa amma kafinnan muna da baki da zasuzo" yana gama magana wayar Abba yayi ringing, mikewa yayi ya fice daga falon, minti kadan sukaji sallaman Abba gefensa kuma Baffa ne da Alhaji Jibril mai bin Abba. Lallai akwai babban abinda yafaru, basuyi tsammanin ganin Baffa agidan ba musamman ma da basu dade da dawowa daga Adamawa ba. Gaba daya in ka kalli fuskokinsu zaka gane cewa ba lfy ba. A three seater cushion Baffa da Abba suka zauna, two seater kuma Alhaji Jibril neda Daddyn Lubna, Aryan kuma na zaune a one seater. Baffa ya bukaci kowa agidan ya taho falon. Babu musu kuwa duk suka nemi wuri suka zauna,Noor kuma ta haye sama ta tasshi Nana daketa baccin huce haushi. Saukowa sukayi suka nemi wuri kusa da kafan ummi suka zauna. Anty Aisha da lubna sun kame a tsaye sun kasa zama, wani tsawa baffa ya dakawa Anty Aisha ba shiri ta zuba akasa, tun ba yau ba suna tsananin tsoronsa musamman ita Anty Aisha, Lubna ma ta nemi wuri ta zauna kusada mahaifiyarta. Baffa ne ya fara magana, duk abinda yafaru tsakanin Daddyn Lubna da Anty Aisha na sakinta dayayi da kuma cikin dake jikin Lubna da kuma zamansu a gidan Honorable Musa duk ya fada, babu abinda ke tashi sai salatin da ummi keta zubawa, Nana da Noor kuwa sai zabga murmushi suke, wannan lamari ba karamin dadi yamusu ba, ita Nana tana murmushin asirinsu ya tonu, Noor kuma tana murmushin cikin dake jikin Lubna, ko ta halin 'ka'ka ai tasan Aryan bazai taba kallonta ba, dacan ma tana kishine saboda bata san halin lubna ba. Sosai Anty Aisha ke kuka kamar na Allah amma babu wadda kukan ya taba, taso tayi musu akan alakarta da Honorable amma Abba ya katse ta ta hanyar playing discussion dinsu dashi da Honorable a wayarsa, abun ba dadin ji inji ustaz. Bayan Baffa yagama magana sannan ya yanke hukuncin cewa abinda addini ya ce ayiwa duk wani mai zina shi za'ayiwa Anty Aisha da Lubna, if possible kuma in aka kama wannan samarin da Lubna ke hulda da su za'ayi filing case akansu tunda ba lallai iyayensu su yadda ayanke wa yayansu hukuncin da addini ya ce ayiba. Shikuma Honorable sun barsa neda Allah, danko duk magidanci mai zina hukuncinsa kisa ta hanyar jifa, toh ammafa a wannan kasar duk wannan ba damuwa bace, sai aga magidanci na zinace zinace da yayan mutane amma instead ayi masa hukuncin daya dace saima abasa goyon baya. Tun daga nan gidan duniya Allah zai fara nuna masa sakayyan abinda ya aikata. Itakuma Lubna Baffa yace saita haife abinda ke cikinta, kuma bayan ta aihu za'ayi DNA test agwada samarinta wadda jininsa yazo daya da abinda ta Haifa za'a daura mata aure dashi,kuma bayan ta aihu tas za'a zaneta bulala dari kamar yadda shari'a yace ayi tunda ita budurwa ce. Anty Aisha kuma zai tafi da ita can Adamawa, acan za'a yi mata hukuncinta na jifa har lahira(wa iyazubillah, Allah ka tsare mana imaninmu). Wani irin ihu Anty Aisha ta kurma nan da nan tafara bori akasa kamar mai sabon hauka, bawai batasan hukuncin dake kanta bane a matsayin matar aure mazinaciya, saidai tsoronta jifannan nanne daza'ayi mata har lahira, wani irin radadi ne zataji kafin rai yayi halinsa. Rokonsu tafara yi tana cewa laifin Lubna ne data hadata da honorable (kuji fa). Sai yanzu bakin Lubna ya budu , kallon mahaifiyarta tayi da jajayen idanunta tace" amma mommy Allah ya isa tsakani na dake, wlh nikam banyi sa'ar uwa ba, kaicona da halin ki mommy, duk fa laifinki ne, tun ina shekara goma sha hudu kikafara introducing dina to porn videos kikace karna baki kunya a idanun mijina gara na fara koya tun yanzu, da banyi aure da wuri ba kuma ni nasan inada karfin sha'awa shine nafara bin maza, ko dana fada miki sadiqboii ya kawar da budurcina ai cewa kikayi ya naji abun da dadi ko akasin haka, banyi mamaki ba saboda nasan dama tuntuni kina burin nasan maza, ko lokacin danaji wa'azi nayi kokarin barin wannan abun na gagara saboda na saba, ko sau daya baki taba tsawa tarmun ba saima bani goyon baya dakike shine yau zakice laifina ne, Allah ya isa wlh Allah ya isa" kowa afalon jikinsa yayi sanyi jin furucin Lubna, tabbas Anty Aisha ba uwa ta gari bace, babu da ko 'ya aduniya dazatayi addu'ar samun mahaifiya kamarta. Sai yanzu Lubna tasamu daman yin kuka, wani irin kuka mai radadi takeyi, saida kowa yaji tausayinta banda Aryan, Noor kuwa itama jijikinta yayi sanyi, dama batasan labarinsu ba sai yanzu. Aryan ne farko ya mike yabar falon yakoma garden din gidan yacigaba da latsa wayarsa,message yayiwa Noor amma dayake wayarta baya tare da ita bata gani ba. Haka taro ya tashi bayan Alhaji Jibril ya rufe taron da addu'a, su Baffa suka wuce hotel shida Alhaji Jibril inda gobe zasu wuce Adamawa da Anty Aisha, Lubna kuwa mahaifinta ya nemi alfarmar zai koma da ita gidansa acan zata aihu sannan ayi aurenta da uban dan dake cikinta, Anty Aisha daketa sambatu kuma aka koreta zuwa dakin dasuka sauka kafin gobe. Ummi jiki asanyaye ta mike ta haura sama, Nana ma duk tausayin Lubna takeji, ashe duk ba laifinta bane laifin mahaifiyarta ne. Sai falon yarage daga Noor sai Abba da ya dafe kansa yanajin wani irin radadi azuciyarsa, kenan hukuncin kisa ya hau kan tilon kanwarsu, inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Ahankali ya mike yana tangal tangal yawuce dakinsa sai yarage Noor ita kadai. Tama mance da Aryan dake garden sai yanzu ta tuna ai dazu tagansa ya fice daga falon yo ina yatafi. Mikewa tayi ta fice daga falon tana gyara mayafin kanta. Dubashi tafara yi a compound din gidan,kuma ga motarsa yananufin bai fita ba yana gidan. Har zata koma ciki sai taga kafarsa daya mike a garden, ahankali ta shiga sai tagansa gishingide akan kujera kamar yana bacci amma ba baccin yake ba, har takai gabansa amma bai motsa ba, hannu tasa ta waving fuskarsa taga ko idanunsa zaiyi motsi amma baiyi ba, hakan yasa ta dauka bacci yake, har ta juya zata tafi sai taji ya jawota zuwa jikinsa ta fada saman laps dinsa, hannunsa ya zagayo kan waist dinta yana kare mata kallo, itakuma hannunta daya na dafe da kirjinsa dayan kuma ya tallabo kansa,matse fuska tayi kamar har yanzu fushi take dashi bayan kuma ba haka bane. Kashe mata ido daya yayi ai batasan lokacin data fashe da dariya ba, shikam sai kallonta yakeyi, she looks so cute whenever she smiles. Sai da ta tsagaita dariyan sannan tace" I'm sorry for what I did to you in the morning, and I'm so proud of you for proving me wrong akan abinda na zargeka dashi, I'm sorry bazan kara...." duk abinda take fada idanunsa nakan bakinta kafin ta karasa kawai taji saukan labbansa akan nata, saida yayi mai isarsa sannan ya cire bakinsa ya ruko fuskarta da tafukan hannunsa yana murzawa ahankali cikin whispering yace" I missed you honey, I missed everything about you, I missed your lips, I missed my twins(boobs), I missed my honey pot, I missed all of you" ba karamin kashe mata jiki yake ba da wannan kalaman nasa ba, lower lips dinsa yakama yana tsotsa dan tsabar jaraba, nan kuwa Noor tagane meyake nufi da hakan, mikewa tayi zata tsere ai kuwa ya cafkota ya dawo da ita, sai wiki wiki takeyi da ido alaman rashin gsky, lakace hancinta yayi yace" yaushe aka haifeki, nizaki nunawa wayo ba" boye fuskarta tayi akan kirjinsa kamar ta tuno wani abu kuma saita dago idanunta sunyi narai narai kamar zatayi kuka, hankalinsa ba karamin tashi yayi ba yace"baby lfy, menene, pls ki fadamun" cikeda shagwaba tace" baby Allah Lubna tabani tausayi, kamar na zubda hawaye, Anty Aisha bata kyauta ba" basar da maganan yayi bawai dan bayaso ayita ba sai dan kawai baya ra'ayi a wannan lokacin, mikewa yayi da ita daga jikinsa ya kamo hannun ta zuwa cikin gidan, abakin kofa sukaci karo da Anty Aisha da trolley din kayanta zata gudu, da Sauri Aryan ya koma ya kulle main door din falon, sannan ya cire makullin. Kamar zatayi hauka ba karamin haushi yabata ba" yanzu Aryan har rashin mutuncin naka yakai haka, za'a kashe Aunt dinka amma bazaka bari na ceci kaina ba, jifa fa ka kosan zafinta kuwa"? smirking Aryan yayi ya karaso dab da ita kamar zai maida ta jikinsa yace" lokacin da kike aikata wannan kazantan aikin, baki tuna da consequences dinba"? Hannu tasa akunne ta fasa uban ihu kamar yace shi da kansa zai kasheta, juyawa tayi ta shige daki tana zagin Aryan. Kama hannunsa Noor tayi zuwa dakin ummi. Basu sameta adakin ba amma sunji motsinta a toilet, sallama yayi mata ya wuce masallaci shida Abba wadda gaba daya kamar ma zazzabi ne ke neman kamasa.


*********************
Washe gari da kyar su Baffa sukayi kafin Anty Aisha tashige motar, Abba da ummi har kuka sukayi, sai ta basu tausayi gashi ance ba'a tausayin mazinaci, basu tsaya ganin tafiyarsu ba. Nana ma kwata kwata bata fito ba. Ko a mota babu irin muzuran da batayi musu amota ba, Baffa karan kansa dannewa kawai yake amma shi kadai yasan yadda yake jin zafin hukuncin da za'a yankewa tilon diyarsa, ba'a maganan ma Alhaji Jibril duk da Anty Aisha tafi sabawa da Abba amma ai jini ba wasa bane.


Koda suka iso Adamawa, tsab Dada tace Anty Aisha bazata kara kwana daya agidanta ba, Baffa neya dakatar da ita yace" haba habiba, da wanne zataji, zafin hukuncin dake kanta ko kuma tsinuwarki akanta" fada sosai yamata kafin ta dauko saikuma ta fashe da kuka ta rungumo Anty Aisha wadda itama kukan takeyi" Aisha na dade ina gargadinki akan wannan abinda kike aikatawa, Allah yasani nayi iya kokarina awurin tarbiyantar daku, kullum ina sakaku cikin addu'o'ina, amma kedin kinfito daban cikin yayana kamar anmin musanyan ki, gashi yau kin aikata abinda da tun daga gidan duniya zaki fara shan azaba, wayyo Allah nikam ina zansa kaina naji dadi" Baffa dake controlling kansa baisan lokacin da ya fashe da kuka ba, Alhaji Jibril shima da hawaye ke kwance a idanunsa yashiga rarrashinsu, kuka mai tsuma zuciya ne ya barke a falon na Dada, kowa da abinda yakeyiwa kuka, kukan rabuwa kukan abinda Anty Aisha ta aikata. Mutanin gidan duk suna tsaye bakin kofar falon sunajin abinda suke fada, ga makota da suka shigo compound din gidan kowa da abinda yake fada, wasu suna jimamin wannan al'amari, wasu kuma suna Allah wadar da hali irin nan Anty Aisha, babu wadda baisan halin Dada ba, dan haka babu wadda ya pointing accusing finger akanta,hausawa sunce ka haifi yarone amma baka haifi halinsa ba. Malam Gwani, babban malamin garin adamawa aka kira, yayiwa Anty Aisha Nazi's masu tasiri azuciyar dan Adam, ba ita kadai ba kowa saida jikinsa ya yi sanyi. Bayan ya gama kuma ya sanar cewa gobe za'a hadu abayan gari za'a yankewa Anty Aisha hukuncinta kamar yadda musulunci ya fada. Wunin ranan babu wadda ya runtsa agidan, Dada taci kuka har kamar yaso ya affecting mental health dinta saboda stress, Anty Aisha kuwa kwana tayi akan sallaya tana jera nafilfili da istighfari, hakan ya kasance agefen baffa.

Karfe bakwai washe gari aka tafi da Anty Aisha wanni babban fili abayan gari inda jama'a kowa ya kwaso dutsunansa a hannu, yara, matasa, manya gabadaya maza da mata suma sun tafi. Dada da matar Alhaji Jibril Lubabatu da kuma yaranta mata wadda kananu ne su kawai aka bari agida. Tun kafin su tafi, Dada ta rungume Anty Aisha kamar bazata saketa ba. Dasuka iso wurin kuma har an tona ramin daza'a sata, tana ganin wannan ramin tsabar firgici ta yanke jiki ta sume, ba'a yafa mata ruwa ba haka aka sanyata cikin ramin, kanta kawai suka bari awaje,Baffa na rikeda dutse ahannunsa Malam Gwani yace dashi shi zai fara jifan kafin kowa, bismillah ya furta sannan ya jefeta dashi, direct kunninta ya sauka, ai ko saiga jini shaa kamar ankunnan kan famfo, azabure ta dawo hayyacinta, bata gama recovering daga wannan pain dinba mutane suka fara jifanta tako ina, ihu takeyi tana neman dauki amma sam babu wadda ya sarara mata, yara sai kuka sukeyi basu taba ganin wannan abunba, mata ma haka, mazanne dai duk da wasunsu jikinsu ya mutu amma sam bashi yasa suka bar jifanta ba tun tana kuka da ihu harsukaji tsit. Babu wadda zai ce Anty Aisha ce, idanunta biyu duk sun tsiyaye, jini ya kulle ko ina afuskar, Baffa ya durkusa awurin yafashe da kuka har wani girgiza yake, mutanen wurin kowa jikinsa yayi la'asar. Haka aka cirota aka mata sutura sannan aka sallace ta. Dada tayi kuka har saida jininta ya haura aka kwantar da ita amma agida, har ruwa aka Samata. (Allah ya jikanki Anty Aisha, Allah ya yafe miki kura kurenki,Allah yasa karshen wahalan kenan😞😞)


Koda labari ya riskesu cewa anriga anyi jana'izar Anty Aisha, ba karamin tashi hankali Abba ya shiga ba, nan take jininsa ya hau har saida aka kwantar dashi a hospital. Ummi ma tayi kuka kamar me harda Nana. Lubna ma a can ba karamin tashin hankali ta shiga ba, Daddyn tane yaita tausarta har saida hankalinta ya kwanta. Rashin uwa koda wani irin hali gareta ba dadi, gashi kuma sun saba da juna. Ya Allah!!


Ko da Aryan da Noor sukaji labarin suma sai jikinsu yayi sanyi, ga halinda Abba yake ciki a asibiti, haka suka shiryaa suka tafi gaidashi. Da yamma aka sallameshi bayan anga jikinnasa yadan yi sauki, za'ana zuwa ana dubashi agida. Da yamma su Noor suka tafi gida.

****************
Kwance suke akan gadonsu, tuni Noor tayi bacci sai faman sauke ajiyar zuciya take, inda shikuma wayarsa na ahannunsa yana scrolling WhatsApp messages dinsa. Number secret investigator dinsa yagani kuma ga unread message sannan da alama ba yau ya turashi ba jiya ne. Shiga yayi yaga ai hotuna ya turo masa, tapping hoton yayi ahankali yafara downloading hoto daya ne ya downloading, wata mata ce fara Sol jikinta sanye da lafaya tayi matuqar kyau kamar ka wanke hannu kafin ka taba, mikewa yayi zaune yana zooming hoton da kyau, suna yanayi sosai da Noor kamar kaki tayi, zuciyarsa na ayyana masa abubuwa dayawa, he just hopes abinda yake tunani hakane, amma ai dafarko yace masa a iya bincikensa mahaifiyar Noor ta rasu, ga kuma wannan, toh kodai sister dinta ne, saikuma ya tuna da Anty Jamila is her only sister, hakan nan nufin Mom in-law dinsa na raye, wani kayataccen murmushi yasaki wadda ya bala'in masa kyau, har ya hango Noor ta hadu da Amminta. Deciding yayi bazai fada mata ba har saiya kammala bincikensa kuma alqawari yayiwa kansa cewa saiya tona asirin Mama. Jawota yayi jikinsa ya gyara musu kwanciya sannan yayi addu'a ya tofa mata yayi musu light off.

**************

After 2 month

Ranan wani Wednesday Na'ima ta yashi da matsanacin ciwon mara, Shareef bai bata lokaci ba ya hado kayan baby da duk abinda ake buqata a asibiti, ya sunkuci matarsa zuwa mota, duk yabi ya susuce yarasa mezaiyi, yadda ya figi motarsa maigadi karan kansa yasan ba lfy. Cikin ikon Allah suna isa asibitin batafi 30 minutes ba ta suburbudo mana katuwar kyakkyawar baby girl fara tas da ita Masha Allah. Murna wurin Shareef kamar me, nan da nan yafara kiraye kiraye yana sanarwa maganar aihuwan. Kan kace me su Anty Jamila dasu Hanan sun iso harda uncle saif. Noor na aiki a kitchen yaya Shareef yakirata ya sanar da ita, wani ihu ta saki tana rawa, Aryan dake zaune afalo yau baije aiki ba ya mike da Sauri a saba'in ya iso kitchen din arude yana tambayarta menene. Tsalle tayi ta dire jikinsa da dan matashin cikinta daya fara fitowa harma yafi watanninsa,dan yanzu cikin na wata hudu kenan. Akunne ta rada masa cewa sun samu karuwa, shima tsananin farin ciki ya rufeshi sai juyi yakeyi da ita kafin daga bisani ya direta akasa. Ai girkin da Noor batayi ba kenan, suka wuce upstairs sukayi wanka tare suka shirya straight sai asibiti. Da suka iso ma har an sallamesu suna shirin tafiya gida, mutane sun cika kamar biki akeyi, family din Na'ima ba magana, kowa tsantsar farin ciki ne kwance a fuskokinsu. Anty Jamila ne ke rike da babyn. Noor na zuwa ta karbi babyn daga hannun Anty Jamila taki wani ya karbeta. Haka suka tafi gida Noor na rike da babyn a motar Ya Shareef. Ranan Aryan bai samu hankalin Noor ba, ta kame a dakin Anty Jamila inda Na'ima ta sauka kenan sai hira sukeyi tamance da bawan Allah gashi komai beciba. Suna cikin hira Na'ima tace" kai wlh aihuwa da wahala, kamar zata tsage mun gabana, sainaji kamar mutuwa zanyi, wai masu haifen yan biyu suna kokari" tunda tafara wannan maganan jikin Noor yayi sanyi, nan da nan idanunta suka kawo ruwa,saitaji zaman gidan ma ya isheta, duk sun lura da canjin yanayinta, mikawa Anty Jamila babyn tayi lokacin har an idar da sallan isha'i, sallama ta musu ta fito daga dakin, duk sai Na'ima taji bata kyauta ba, dama batayi maganan ba agaban Noor gashi yanzu baiwar Allah duk ta tsorata. Noor kuwa wani irin haushin Aryan takeji, duk saboda shi gashi yanzu zata je tayi bayani a labour room. Fitowa tayi harabar gidan ko takansu Hanan bata bi ba, yana tsaye da Shareef suna hira a car park inda motarsa yake ya hangota dayake akwai haske a farfadar gidan, kamar zata fita har takai gate taji ya rukota, juyowa tayi tana ganinsa ta fashe da kuka kamar karamar yarinya harda bubbuga kafa akasa, bawan Allah saiyabi ya rude ya shiga tambayarta meya faru amma taki fada masa saima kara gunjin kukan datakeyi. Shareef na tsaye yana kallon ikon Allah, wai Aryan ne ke wani rawan jiki akan mace, lallai Noor ta ciri tuta. Shiko Aryan dayaga kukan nata bamai karewa bane sai kawai ya dagota kamar jaririya tana wutsil wustil da kafa amma yaki saukanta har saida ya zaunar da ita cikin mota sannan ya yiwa Shareef sallama ya shige. Ko ahanya taki yin shiru, agefen titi ya faka motar yayi tagumi yana kallonta, ko menene ke damunta Allah kadai ya sani. Da taji kamar ya shareta ne sai ta dago da jikakkun idanunta ta kalleshi tace" ai dole ka shareni, tunda bakai zakaji zafin aihuwan ba" mamaki ne ya kamasa ashe Almatsutsan ne akusa no wonder. Kamo hannun ta yayi cikin kulawa yafara murzawa ahankali yace" Baby love wayace miki aihuwa nada zafi,inma yanada zafi saidai yayiwa wasu matan amma ban dake pls ki kwantar da hankalinki insha Allah zaki aihu lafiya kinji" harara ta watsa masa da rinannun idanunta hakan har ya kusan bashi dariya amma ya matse kafin ya bullo wani ruwan, cikin sheshshekan kuka tace" ai dole kace bazaiyimin zafi ba tunda su mata ne nikuma mata maza, ko dayake ba laifinka bane laifina ne dana bude maka kafa kayi min ciki yiiiii wayyo nii Nuwaira na debo wa kaina ruwan dafa kaina yii wiiii wayyooo daddyna" Aryan baisan lokacin daya fashe da dariya ba dan maganarta ba karamin bashi dariya yayi ba, jin haka kuwa yasa Noor kara fusata takara fashewa da kuka harda shure shure, tayar da motar yayi baice da ita komai ba har suka karaso cikin gidan, fitowa yayi ya zagaya sannan ya daukota lokacin har tayi bacci ga danshen hawaye a gefen fuskarta.


COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/15/23, 8:33 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 59_ 60

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

Washe gari, agidan Anty Jamila Noor ta wuni tare da baby, ta hakimce akan gado yadda kasan itace mai jegon, baby bata zuwa wurin mamanta sai in nono zata sha ko kuma za'a canja mata diapers, Noor da karambani ma wai ita zata canza mata bacin kuma ba iyawa tayi ba. Duk wani abun da aka kawowa na'ima sai in Noor bata wurin amma da ita za'a sude kwano, bini bini zaka ganta da plate shake da kayan makulashe. Ko takan Aryan bata bi ba dan fushi takeyi da shi tun jiya har yanzu, bawan Allah yayi iya kokarinsa wurin ganin ya shawo kanta amma sam taki, dayake yana office shiyasa yaita kiranta a waya amma bata picking ba, daga karshe ma kashe wayar tayi gaba daya. Su Ummi da Nana ma anan gidan suka wuni ga sauran yan uwa dake zuwa barka daga family din Na'ima harda na su Shareef. Da yamma da Aryan yazo su tafi kememe Noor taki wai ita anan zata kwana, yayi rokon yayi fushin amma ko ajikinta, kamar zaiyi kuka kuma yau yanaji bazai iya haquri ba, kwana nawa kenan take gudunsa Allah kadai yasan dalili amma yau kam gsky yakai makura, kota karfi zai amshi abunsa saidai kuma yana tsoron magiyan da zata yi masa. Hakanan ya danna zuciyarsa badon yaso ba yabarta agidan yakoma gida. Cikin dare wuraren karfe goma tana dakinsu Hanan taita juyi akan gado tama rasa meke mata dadi, ta riga ta saba da kwanciya akan kirjinsa suna manne da juna, tana cikin wannan mutsu mutsun taji wayarta tafara kara, dagawa tayi ta kara akunninta, sallama yayi cikin cool voice dinsa kana ji kasan baya cikin jin dadi, amsawa tayi bata kara cewa komai sai taji yace" Baby love yanzu kin kyauta mun kenan? I know you're also missing me amma kika zabi ki quntata min ki kuntata wa kanki, normally by now dakinyi bacci amma saboda rashina akusa dake gashi har yanzu you're still awake, Dan Allah Babyna nazo yanzu mu koma gida plsssss" yadda ya karaso maganan har saida taji tsigar jikinta ya mike, bata ce masa komai ba kawai ta fashe da kukan shagwaba, " Baby love what is it? Ko ba kyaso nazo ne" da Sauri a tace " inaso, I'm also missing you" murmushi yayi dama yasani, karambani ne kawai yasa tace zata kwana anan amma shiyasan bazata iya ba, ko da baikirata ba zata kira shi ne. Baijira takara wani maganan ba yasauko daga kan gadon da Sauri, 3 qrt ne kawai ajikinsa ya dau T-shirt dinsa yasa sannan ya dau p cap da palm shoes dinsa yadan feshe jikinsa da turare ya dau key din motarsa ya fice. Acan gidan Anty Jamila kuwa, kowa yayi bacci banda Noor, har ta gama shiryawa cikin kayanta datazo gidan dashi da safe, fitowa falo tayi tana zirga zirga kafin yazo, tana tsaye taji ringing din wayarta dake hannunta ,da Sauri ta bude kofar falon ahankali ta fita, baba mai gadi yana kwance kan bench dinsa ya kafa radio akunne yanaji, bataso tashinsa ba amma babu yadda ta iya saboda anriga an kulle gate, tashinsa tayi ya bude mata yana tambayarta ina zata, cemasa tayi duk wadda yayi tambayarta yace masa mijinta ne yazo ya dauketa sun koma gida, baba maigadi sototo yayi ya tsaya yana kallon wannan rashin kunya na yaran zamani, da niyyar kwana fa tazo amma da tsakar darennan mijinta yazo daukarta saikace bada izininsa zata kwana ba. Tana fita ta hango motarsa tsaye abakin gate, dake dama akwai haske sosai a street din, yana tsaye ya nade hannunsa akirjinsa yana jiran fitowarta, tana ganinsa ta karaso da gudu ta shige jikinsa tana maida

Please Login or Register in order to submit comment