Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nana ta kira wayar Noor yafi so akirga amma switched off dan tunda aka fadawa Noor maganan aurenta ta kashe wayarta. Sunyi taro lfy antashi inda gobe kuma zasuyi Arab night.


Yau Thursday, agefen su Anty Jamila kuwa shirye shirye akeyi na henna party din Noor. Kwararrun masu lalli aka kawo. Hanan da Hanifa sune kadai kawayen Noor saikuma wasu yan uwansu sa'anninsu. Noor aka fara wa lalli, inda aka tsantsara mata Jan lellenta me kyau babu ko digon baki. Farar fatannan nata ya bala'in haska lallen yai kyau sai tashin kamshi take, dan tunda tadawo take kan hayakin turare wadda Hjy balaraba tabata. Kowa saida yayi lallin har kusan karfe sha dayan na dare ana kan lalle, wasuma har sun fara bacci. Ranar Friday ne za'ayi dinner din Ya Shareef inda Noor kuma sai Saturday bayan daurin aure da daddare.


Su Anty Aisha sunyi iya kokarinsu naganin sun ruguje duk wata shirin da akeyi amma ko fuska basu samu ba a gidan ummi. Yan uwa gaba daya sun San halin anty Aisha shiyasa babu wadda ya sake da ita. Itakuwa Lubna ganin babu abinda zasu samu agidan illa disgrace yasa taja mamanta suka bar gidan suna bakin cikin kubucewar Aryan daga tarkonsu.

Su ummi sunyi taron Arab night dinsu da daddare, inda da kyar aka shawo kan Aryan ya taho wurin taron. Farar jallabiya dakuma hiram yasa mai matuqar kyau ash colour abokansa kuma suka shirya cikin jallabiya kawai, kowannensu da rawanin larabawa suma sunyi kyau. Muhsin sai faman Satan kallon Nana yake, itama data lura da hakan sai ta dena sakin jiki awurin taron harga Allah ya burgeta amma ganin idon Boss Aryan bazaisa tayi wannan gangancin sakewa da Muhsin dinba dukda cewa dan uwansu ne.

Washe gari

Agidan amarya Na'ima kuwa, kwalliya aka mata me kyau dan na'ima itama akwai kyau masha Allah. Shiri tayi cikin wata princess gown purple colour anyi shirin zuwa dinner. Bini bini tana waya da Ya Shareef ana hiran love kawayenta sai zolaya suke mata itakuma tana basu amsa bako kunya.

Ango shareef shima ya shirya cikin dakakkiyar shaddarsa light purple yayi kyau Masha Allah. Agidansa ya shirya dan tun ana sati daya da bikin yakoma kwana awurin dan baki har cikin dakinsa suke kwana. "Aryan pls get up and get ready now, meye haka pls dude ka tashi mana" Aryan dake zaune yana latsa wayarsa dagashi sai guntun wando da singlet kaya kawai zesa danya riga ya yi wanka. Su Muhsin suma suna cikin abokan Shareef tunda beda aboki sai Aryan shiyasa suma suka masa kara. Su sunma gama shiri cikin shadda light blue wadda anko sukayi Aryan kawai ake jira. Da kyar ya mike shima ya dau goggagun kayan nasa ya Sanya. Yayi kyau sosai kamar shine angon, ya shareef ya kalleshi yace" Allah sarki ango ango, gobe muma war haka muna shirin zuwa naka" suka fashe da dariya suna zolayarsa, ko ajikinsa dayaga zolayan bame karewa bane yace" seriously guys, in baku dena ba zan fasa tafiya and I mean it" haquri suka shiga basa. Bayan ya gama shiri duk suka fito daga harabar gidan. Motocine masu ji da nera guda biyar manya manya suka jera Kansu suna jiran ango. A wata farar Bugatti din Shareef suka tafi shida Aryan. Su Muhsin da abokansa biyu kuma suka shige na bayansu, saikuma bodyguards asauran motoci ukun suka fara tafiya zuwa inda za'ayi taron.



Noor ne zaune tagama shiri tana jiransu Hanan su gama shirinsu. Wani material royal blue kowaccensu tasaka da alama anko sukayi. Kayan ya bala'in fitting Noor, ga dankwalinta da tayi simple dauri dashi yayi kyau, fuskarta ba makeup amma annurin fuskar amare ya kawata fuskartata. Tulun gashinta yana cikin dan kwalinta bata bari ko tsini daya ya fito daga ciki ba. High heels ne akafarta fari me kyau. Suma su Hanan sunyi kyau kowa da irin tata kwalliyar gwanin sha'awa. Muryar Anty Jamila sukaji tana kiransu su fito. Kowa yariga ya fito lokacin da suka fito daga dakinsu yayinda wasuma harsun tafi. Amotarsu suka tafi inda Noor dakanta take tuki har suka iso babban hall din daza'ayi taron. Ko ina ya hadu sai tashin music akeji.


Motar amarya ne ya shigo inda hankalin kowa ya koma Kansu. Har gaban motar Ya Shareef ya tafi ya bude wa amaryartasa dakansa. Ahankali suka tako har entrance din hall din suna rike da hannu juna kowa nata santin irin kyawun da sukayi. Su Noor kuwa sun iso su hanifa suka tafi wurin amaryarsu itakuma Noor ta tsaya a jikin motar tana rera kukanta, kenan itama gobe zata zama matar wani. Dayake wurin akwai dan duhu shiyasa bata ga wucewarsa ba. Shikuwa Aryan motar dasukazo aciki ya shiga ya zauna. Sheshshekan kuka yakeji kasa kasa shi ya Sanya ya dago kai ya kalleta. Juya baya tayi ta manne da kofar motan tana kukanta tsakani da Allah. Tsaki yayi ya mayar da kansa ya kwantar ajikin kujeran motan yana tunani. Har kusan mintuna goma amma bedena jin kukanta ba. Fitowa yayi ya zagayo har inda take ya kafeta da ido kamar yaso ganeta amma kuma fuskarta na manne da glass din motar."wai meyasa Ku mata bakuda wuyan kuka ne, Ku abu kadan kesaku kuka, mukuma damuke cikin damuwa kullum muceme, mtscheeew" tunda ya fara magana tayi shiru tana sauraransa kamar taso gane muryarsa, daga kai tayi karaf idanunta suka sauka acikin nasa, sunkai minti biyu suna kallon junansu, shi ya fara janye idanunsa sannan itama tayi kasa danata, haka kawai taji yayi mata kwarjini, share hawayenta tayi ta juya zata tafi taji yace" nonsense " juyowa tayi ta murguda masa baki hadi da harara, dayake akwai reflection na haske kadan awurin yasa yaga abinda tayi masa, tana ganin ya nufo ta tajuya zata gudu cikin rashin sa'a takalminta ya goce, harta gama sallamarwa zata jita akasa sai kawai tajita a hannun mutum. Shima karan kansa besan ya akayi yayi saurin tarota ba, kusan thirty seconds amma besake ta ba, wani irin yanayi ta tsinci kanta acikin da sauri ta zare jikinta daga rikon dayayi mata tana turo karamin bakinta gaba. Bakin ya kama yaja da dan karfi tasaki kara tace"mug.." Bata karasaba jin ya kama hannunta ya murguda abayanta. Ihu tayi da Sauri yasaketa yabar wurin kamar mara gsky😂😂. Da Sauri itama ta shige hall din. Anriga anfara taron, wuri ta nema ta zauna kusa dasu Hanan suna tambayarta inata shiga, bata amsa musu ba tacigaba da kallon abinda akeyi. Har aka gama taron amma bekara shigowa ba. Taro ya watse lfy saikuma gobe in Allah ya kaimu daurin aure muzo muci rengem rengengem.




Washe gari tunda asuba wurin karfe biyar, Noor nacikin baccin gajiya taji ana mata wanka da turare ajikinta. Farkawa tayi tagansu Hanan ne rikeda kwalaben turare sunata fesa mata. Kuka kawai ta fashe dashi inda su hanan ma suka rungumeta suma suka fara kukan. Anty umaima tashigo ta gansu ahaka, haba tarike tana kallon ikon Allah saikace yan uku. Kuka sukeyi sosai da kyar ta iya rarrashinsu. Sannan tasa Noor taje tayi wanka da alwala anfara kiran sallan asuba. Karfe bakwai daidai Anty Jamila tashigo da cup ahannunta, nonon rakumi ne fresh tabawa Noor bayan tagama sha tamika mata gumba tace taci, mutuniyar taku yau tafara cin gumba mekuwa zatayi atake tacinye guda uku tana tande baki. Anty Jamila cikeda mamaki take kallon Noor azuciyarta tace" ayya yarinya zakiyi bayani". Wata karamar akwati irin na uku acikin set dinnan Anty umaima ta shigo dashi ta aje, sannan tasa Noor takara yin wani wankan bayan ta hada mata su turaruka acikin ruwan. Tunda tafito taketa baza kamshi, kwata kwata batada walwala, idanunta sun kumbura dan ko jiya baccin datayi na wahala ne bayan tasha kukanta iya son ranta. Lokacin har karfe takwas yayi wata atamfa Hanan ta fitar mata dashi ja da milk tasanya. Sosai kayan ya amshi jikinta tayi kyau, gashinta daya sha gyara sai sheki yakeyi, dayake gashin akwai tsantsi shiyasa ba ayi mata kitso ba, daurin kallabi hanifa tamata, saida rana makeup artist zatazo tayi mata kwalliya. Anty jummai autarsu Daddy ne ta shigo hannunta dauke da basket na abun kari. Plate ta dauko mai zurfi ta debo cida kazan da akayiwa Noor tamika mata tace gashinan tas saita cinyeshi, su Hanan suna ta kallon Anty jummai akan suma zasu ci haka nan ta hanasu. Da kyar Noor ta iya cinye wannan , sannan ta zubo mata kunun gyada tace shima ta shanye tas, aikuwa turawa kawai takeyi amma kamar tayi amai dan yadda ta koshi. Bayan tagama ci Anty jummai ta kwashe kayan ta fitar dashi.



Karfe Tara da rabi mutani harsun fara hallara a central mosque dan a masallacin za'a daura auren. Manya manyan kasa masu fada aji wasunsu harsun fara zuwa. Anan gidan Shareef kuwa duka angwayen suke da abokansu. Suma har sun shirya amma oga Aryan na kwance akan gado ko kaya besaba jallabiyace ma ajikinsa. Muhsin ya kalleshi yace" haba Aryan, pls get up and get ready, the nikah is by ten thirty and here you are acting as if it's not your wedding" tsaki Aryan yayi ya mike yana jan guntayen tsaki ahankali har ya gama shiri cikin wata fara shadda getzner me kyau. Dinkin babban riga ne amma na zamani yayi kyau, hularsa ma fara mai digon baki sai takalminsa itakuma baka half cover na company din Louis Vuitton. Agogonsa Rolex ya dauka ya daura a tsintsiyar hannunsa sannan ya dau turarensa mai bala'in kamshi ya fesa nan da nan ko ina ya amsa, sai ga Angon Noor ya fito kamar wani tauraro sai haskawa yakeyi. Shima shareef irin shirin dayayi kenan abun ba'a magana sunyi kyau sosai da sosai kamar asacesu agudu. Abokan ango suma sunyi kyau cikin shirinsu na shadda milk colour. Ahankali suka fito zuwa wurin motocinsu, Wasu yan banzan G- wagon bakake ajere suna jiransu. Cikin takunsa na isa da kasaita ya isa wurin motan wani bouncer ya bude masa ya shige, suma sauran suka shiga sauran motocin aka kama hanya zuwa wurin daurin aure.

Karfe goma da rabi daidai mutani suka shaida daurin auren Muhammad Aryan Abdul Azeez da amaryarsa Nuwaira Nasir saikuma Ibrahim saifullah da amaryarsa Na'ima Abdul Ganiyy. Iyayen amare da ango suka fara gaisawa da junasu ana farin cikin wannan zumunta da aka kulla. Maroka suka fara waka suna shewa. Aryan na tsaye shida Shareef wadda baki yaki rufuwa. Aryan kuwa kansa ne yaji yana masa wani irin juyi nan da nan yaji gaba daya tsayuwa a wurin ya gunduresa. Motarsa ya shige bema bi takansu Muhsin daketa kiranshi ba ya ja motar aguje yabar wurin.



Su ummi tunda suka ji andaura auren suketa murna. Nana kuwa a wannan lokacin damuwan dake tare da ita yafi murnan datakeyi dan har ila yau Noor bata kunna wayarta ba, gashi batada numbern yan biyun Anty Jamila. Gaishe gaishe aketayi mata na guda agida su Dada baki har kunni yau mijinta ya angwance( akan Dada nafara ganin ana murnan karuwar auren miji😂).


Gudan da Noor taji anata yine yasata tabbatarwa cewa yau andaura aurenta da wani wadda batasan ya kammaninsa yake ba. Kuka takeyi tana tunanin makomar rayuwarta, ita ajikinta tanajin cewa wannan journey din is full of hurdles, bata taba soyayya ba batasan yazata fara ba, batasan me aure ta kunsa ba farinciki ko akasin haka, wuya ko dadi duk wannan bata sani ba. Tayi kuka harta godewa Allah. Anty Jamila ce ta shigo da wata matashiyar budurwa daga gani makeup artist ce dan da akwatin kayan kwalliya tashigo. Wanka Anty Jamila tasa Noor takarayi da alwala, bayan ta fito ta zauna aka fara tsantsara mata bridal makeup dinta me bala'in kyau. Basu wani jimaba aka gama, Hanifa ta fidda mata wata peach colour lace dinkin riga da skirt fitted dinki. Kayan daram ya zauna ajikinta dukda dan raman datayi. Dauri me step step aka mata yayi kyau, sannan ta feshe ta da turare. Hotuna aka fara daukanta kit kit amma ko murmushi a fuskarta babu. Karfe biyun rana aka canza mata wata wankan inda ake shirin tafiya da ita gidan ummi daga can zasu wuce wurin dinner. Ash colour lafaya aka daura mata da silver coloured takalmi da purse dinsa, tayi kyau sosai. Motocin daukar amarya sun jera kansu suna jiran fitowar amarya. Su Anty umaima ne suka kamo hannun Noor suka fito da ita bayan angama mata nasihar zaman aure. Anty Jamila bata bisu ba dan za'a kawo amaryar ya shareef. Saida sukayi da kyar sannan Noor ta yarda ta shiga motan. Kanta akan guiwarta tana rera kukanta harda kiran Amminta, lallai uwa rahama ce ta tabbata da mahaifiyarta na raye da baza'a taba mata auren dole ba. Abakin gidan ummi aka faka, horn drivovi sukayi mai gadi ya wangale musu gate suka shiga. Dayake Noor kanta na kasa shiyasa bata lura da Inda sukazo ba. Motarsu Hanan na shiga suka ga gidan da aka kawo Noor mamaki fal ransu, cikin farin ciki hanifa tace" Hanan kardai Aryan ne angon Noor" itama Hanan cikin farinciki tace "Allah yasa, kai amma danaji dadi, wannan cat and rat din zanso naga soyayyarsu" murna afuskar yan biyun anty jamila kamar suyi tsunsu suje wurin Noor, zasuso suga fuskar Noor da Aryan lokacin dazasu gane cewa yanzu su ma'aurata ne.


Aryan tunda yabar wurin daurin aurennen su Muhsin keta kiranshi daga baya ma sukaji wayarsa a kashe, yana gidansa kwance akan gado yana tunani, bakin ciki duk ya mamaye shi, yanzu fa shi magidanci kenan, yanzu wata mace na karkashin shi kenan, "Ya Allah" ya furta yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa. Tunawa dayayi cewa akwai dinner anjima yasa bakin cikinsa kara habbaka.


Anty ounaisa na Anty Raihana su suka shige da Noor har cikin dakin ummi. Su hajiya Dada anci wankan lace ga wani daurin da aka yishi tundaga baya zuwa gaba adole anyi kyau, itama Hajja irin wankan datayi kenan, Dada ce ta mata irin daurin kanta sunata kashe hotuna a wayar Hajja. Nana tunda taji ankawo amaryar Ya Aryan tafito daga dakinta, turus tayi ganinsu Hanan sunnufo dakinta. Da mamaki a fuskarta take kallonsu to mekuma sukeyi anan, da sauri hanifa takamo hannun Nana tashige da ita daki ta zaunar akan gado tace"yanzu Nana dama kinsa yayanki Noor zai aura shine ko ki fada mana" tsalle Nana tayi ta mike daga kan gadon tana zaro ido waje tace"what?? Dan Allah dagaske kike"? Hanan ta gyada mata kai alamar ehh. Wani irin ihu tayi tana murna harda rawanta. Sukuma sunata mata dariya, hanyar waje ta nufa zata dakin ummi, su hanan suka hanata sukace tabari manya ne adakin ana mata nasiha. Da kyar ta yarda ta zauna.

Itakuwa Noor kanta na cikin lafayanta anja matashi har kasan fuskarta, kamar amafarki taji ummi nacewa "Masha Allah yau Allah yanuna min auren Aryan, ga matarsa agabana Alhamdulillah"mamaki ne ya kama Noor kai kila kunnenta ke jiyo mata ba daidai ba. Ummi ce ta karaso ta rungumeta tana mata marhaban. Zama tayi akasan gado gefen su Dada, Hajja ce ta jawo gelen ta zuwa sama, ido hudu Noor tayi da ummi wacce kemata murmushi. Dummmmm zuciyarta tayi, hawayene yafara taruwa a idonta. Me hakan ke nufi, Basamude aka aura mata????(sunan data sawa Aryan kenan😂😂😂)


Gan gan gan wasa farin girki.


COMMENT AND SHARE



REEMAH✍️
10/14/23, 7:19 PM - Reemah: Ina muku godiya akoda yaushe da kwarin guiwa da kuma addu'o'i dakuke mun. Ina sonku sosai my fans. Allah yabar zumunci.


🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH


PG 29_30

https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


Murmushi ummi tayiwa Noor wadda tuni hawaye yafara zarya a idanunta. Maganan zuci takeyi,"ya akayi hakan ta faru, itadai tasan basamude baze taba cewa yana sonta ba duba da yadda kullum in suka hadu suke gwabzawa, kenan shima auren dole akamasa, lallai akwai chakwakiya, ahaka ma kenan yana cin zalinta balle kuma yanzu tana karkashinsa" wani irin kuka tafashe dashi gabadaya mutanin dakin suka rude kodai kukan barin iyaye ne. Dada ta taso tazo kusa da ita tanata bata baki har tayi shiru sai ajiyan zuciya datake saukewa akai akai. Sosai manya suka mata nasiha amma ba fada dan karta kara wani kukan. Gabadaya dakin babu wadda yaki Noor sai tsantsar soyayyarta daya darsu a zuciyoyinsu. Anan dakin ummi tayi sallan asr bayan mutane sun fita yarage daga ita sai su Hajja wadda ke can suna yaransu na fama da Dada. Bayan ta idar da sallan ta zauna akan sallaya ta rafka tagumi tana tunanin makoman wannan aure. Wani irin zama zata farayi da basamude dan harga Allah karfin hali kawai takeyi intana masa wasu ababen,harga Allah tsoronsa takeji wadda bazai iya misaltuwa ba. Ahaka Nana tashigo dakin amma Noor bata sani ba. Kawai ji tayi an rungumeta ta baya. Ganin Nana ce yasata kara hade rai tana cin magani. Murmushi Nana tayi tasan dama hakan zai faru tace" haba dear wlh Allah kinji nima be dade dana sani Ya Aryan zeyi aure ba kuma wlh koda nasani bansan kece ze aura ba, dama kuna soyayya da shi shine ko ki gisting dina ko" wani irin kallo ta watsa wa Nana daketa zubo sharhi kamar computer tace" Dan Allah Nana just go I want to be alone, ni sai yanzu ma nasan sunan yayannaki balle aje maganan soyayya dashi, ke kullum ma inmuka hadu wlh fada ke rabamu" duk wannan maganan dasukeyi kasa kasa sukeyinta yadda su Dada bazasuji ba, Dada ce tace"ke kazar makota dallah tashi kibar yarinya ta huta, sai hegen shishshigi kamar kyanwa" turo baki Nana tayi ta mike ta fice daga dakin ta banko musu kofa. Murmushi kawai Noor tayi taciga da tunaninta.


Karfe shida na yamma daidai su muhsin suka shiga haraban gidan Aryan dansun tabbata anan yake, aikuwa suna shiga falo suka sameshi yana saukowa da alama fita zeyi. Kotakansu bebi ba ya zo wucewa Muhsin ya kamo hannunsa yace" dude where are you going? we need to start preparing for the event" tsaki Aryan yayi ya kwace hannunsa yace" what event" da mamaki su lukman suke kallonshi,Ameer dayan abokinsu yace" your dinner of course" shi sai yanzu ma tuna da wani dinner, kuma ummi tace idan beje ba saita saba masa, juyawa yayi ya koma sama ya banko musu kofar suna tsaye sincika tab da mamakin Aryan.


Bayan sallan isha me makeup tazo tafara yiwa Noor makeup. Bawani makeup bane sosai aka mata amma ta hadu iya haduwa. Ummi ce ta shigo da wani katon jaka da alama kaya ne acikinta. Bayan sun gama makeup din ummi ta fidda wata katuwar princess gown white and golden colour sai walwali yakeyi yaji adon stones da patterns. Wani takalmin ta kara fitarwa me kyau golden colour shima, sai case na jewelry mekyau na gold gwanin sha'awa. Bayan noor tasa kayan nan saitafito real princess din Basamude lols. Tayi kyau sosai kamar angwada ta kafin akayi dinkin kayan. White dankwali mai tsantsi aka daura mata inda kafin ayi daurin saida aka mata doughnut da tulin gashin kanta. Wasu turarukan larabawa masu tsadan gaske ummi ta fitar ta fesa wa Noor ko ina ya dauki kamshi mai sanyi da dadin shaka. Hajja ta mikawa ummi wani dan karamin case na agogo, lokacin da ummi ta bude wannan case din hatta Noor saida ta yaba da kyawun agogon nan, diamond wrist watch ne me kyalli sai wani shining yakeyi, a tsintsiyar hannunta ummi ta daura agogon yazauna cas dashi. Masha Allah tabarakallah kawai Noor ta hadu iya haduwa, wani golden net ne kamar niqab amma na rabin fuska ummi ta daura wa Noor, idanunta kawai za'ana gani amma ba lallai kasan wacece ba saidai inka kure kallonka. Nan take kamannin Noor ya bace, godiya Noor tayi azuciyarta dama bataso basamude yaga fuskarta Karya fara cin zalinta tun a hall din dinner😂😂 Dada ce ta shigo taci adonta cikin golden colour lace tayi kyau gwargwaronta sai kara yakeyi yana damun kunnin mutane, Masha Allah kawai tadinga fada lokacin data ga Noor. Ummi takamo hannunta suka fito falon kasa inda su Nana dasu Yasmin da Hanan suke. Da gudu suka karaso wurin Noor aka fara kit kit ana daukanta hotuna. Muhsin ne ya shigo yace motoci suna waje ana jiran amarya. Ahankali suka kamo hannunta har suka fito haraban gidan. A wata farar limousine mai kyau tasha adon flowers suka nufa da Noor, haka kawai taji zuciyarta na dukan tara tara. Ahankali wani bouncer ya budewa Noor kofan baya ta shige, har ta zauna bata lura da mutum a dayan gefen ba. Shima kuma tunda ta shigo baiko kallo gefenta ba. Ummi ce ta fito ta mikawa Noor purse dinta golden colour sannan aka rufo kofar. Gaba dayansu zuciyoyinsu cike take da fargaba, sai daya dan motsa kafin Noor tasan cewa akwai mutum, ga kuma kamshin turarensu daya garwaye yabada wani irin kamshi mai ma'ana. Aryan kuwa har bemaso ya motsa dan gani yake kamar jikinsa zai taba nata, hakan ta kasance a bangaren Noor. Bayan sauran mutane sun gama shiga nasu motocin aka fara tafiya ahankali cikin convoy. Har suka iso inda za'ayi taron babu wadda yayi kwakwkwaran motsi acikinsu sai yanzu da'aka taka birki suka tafi gaba dukkansu. Tsaki Aryan yaja yakoma da baya inda itakuma matar Basamude kawai ta jingina kanta da guiwa tafara hawaye, hausawa sunce me neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki lols. Sheshshekan kukanta dayaji ne yasashi juyowa ya dan kalleta, kanta kawai yagani dake hade da guiwa, cikin Bacon rai yace" ke wlh idan kika fara mun wani kukan munafirci anan zan babballaki stupid" babu shiri Noor ta hadiye kukanta sai hawaye kawai. Ahaka suka zauna har kusan 30 minutes kafin sukaji an bude kofa. Anty Jamila ce ta kamo hannun Noor tafito da ita, tana ganin Anty Jamila ta rungumeta ta fashe da kuka sai aikin rarrashi Anty keyi. Shikuma daya fito ta dayan side din su muhsin suna tsaye agefensa sai wani cika yake yana batsewa, Anty ounaisa ce ta zo ta kamo hannunsa ta zagayo dashi har wurinda Noor take tsaye bayan Anty Jamila ta rarrasheta tayi shiru, hannun Noor Anty ounaisa ta kamo ta saka acikin na Aryan, atare sukaji wani irin shock mara misaltuwa, zuciyoyinsu yafara bugawa da sauri sauri, Noor taso janye hannunta amma sai taji ya matse matashi da karfi har saida ta saki kara shikuma yawani harareta ta kasan ido. Sai yanzu ma Noor tadan kalli gefen dayake tsaye, sanye yake cikin white shadda anyi masa ado da gold design, takalmin kafarsa kuma farace tas full cover, agogon hannunsa ma golden ne, sai baza kamshi yakeyi. Ahankali suka fara takawa har cikin hall din wadda yagaji da haduwa dan kwararrun designers aka kawo suka decorating wurin. Komai na cikin wurin anmishi ado da white and gold ne. Cool romantic music ne ke tashi alokacin dasuka shigo, hasken hall din ya koma kansu, sai tafi akeyi raf raf raf kowa na yaba irin kyawun da sukayi. Can na hango su hajiya Dada da Hajja akan high table anwani sha kwaliyya harda dan madubinsu na fashion a ido. Ahankali ango da amarya suke takowa inda abokansu ke take musu baya, Muhsin da Nana sun tsaya ne a layi daya, Hanan da lukman kuma na baya sai hanifa da Ameer saikuma yasmeen da saurayinta, har suka kai sit dinsu kowa na tafi. Zama tayi kafin shima yazauna duk wannan abinda akeyi babu wadda yadago ya kalli wani acikinsu. Mc ne yafara gabatar da abinda ya kawosu anata welcoming iyaye da abokan arziki kafin yace abokan ango da kawayen amarya sufito suyi rawa aka sa musu wakan burna boy me taken it's plenty. Sosai suka tika rawansu inda su kawayen amarya sunfi zaqewa abokan ango kuma sai shirme suke wai ana rawa, iyaye ne da yayyi suka fito aka fara watsa musu kudi sukuma sun dage ana ta bada styles din rawa. Bayan sun koma sit dinsu kuma mc yanemi amarya da ango sufito suma suyi rawan, dammm haka sukaji zuciyarsu ta buga, Aryan yace what?? Impossible, hada idon dayayi ne ummi wacce ke zaune dan nesa dasu yasa ya tashi yana

Please Login or Register in order to submit comment