Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kama dole na dago kai gurin mijin yar sokoto nace hayatudeen sai nai murmushi.
Nace kayi a hankali da kudin mutane don ka kusa fadawa cikin hau, ilwala,I.
Yace subbahanallahi ni kuma ya gyara zaman shi nace kwarai kuwa don akwai wani arne dake son ku hada halaka dashi kada ka soma arne ba abin yarda bane makiyan ku ne basu da tsoron Allah ko kadan atare da su.
Matar da iyayyen ka ke son ka aura kayi a hankali babu babu babu lafiya ba alheri a tare da ita ko kadan.
Gidan da kake son saye a garin ku an yaudare ka na guri bane mai kyawo shiyasa maigidan ke son sayarwa akwai huwa,i gurin bai bari kowa ya zauna don shi keda gurin sa.
Tsohuwa tsohuwa kin bar gida har gidan ya zama maboyan shedanu makwabciyar ki ta samu gurin aje ruhin yan adam yan uwanki ko zaku koma cikin gidan nan yanzu sai anyi burgan sa sosai.
Don ta samu dama da furin boye sirin ta a gidan ki don gidan yai mata dadi agidan ki suke meeting din su na mayu unguwar ku.
Abba yaron kirki saidai kassh akwai shedanun yara dake sa ido gare ka amma bazasu iya ba don kafi karfin su da tuni sun gama da kai don akwai baiwa a gareka nan gaba mai tarin yawa.
A garinku makwaciyar ku tasan da wanan tarin baiwa taso ta gama da yaron tun yana a cikin godiyan mu .
Sai dai hakan bazai yiyu ba don abubuwan dake a tare da godiyan mu bazasu bari a lokacin a cuci jinin su ba.
Godiyar mu mu tana da matukar kirki amma ke tsohuwa mai kalwa ta cusa maki mumunan ra, ayi a kan ta haka yasa muka gwada maki ba ai wa godiyar mu haka.
Yanzu kin ganan wa idon ki gaskiyar alamarinta don haka sai dai idan halinku na yan adam ne ya taso maki kuma don har gobe baki daina hassadan ta ba a ran ki .
Don kina ganin kamar ta taushe maki baiwan danki ne tafi shi arziki yanzu kin manta abin daga Allah yake.
Zamu koma don haka ke yar sokoto gare ki don godiyar mu ta yarda dake amma kina kyashi akan ta kina yada magana wanda bai dace ba akan ta, kiyi hankali da fushin mu watarana kada mu waiwaye ki akan hakan.
Sai watarana ku ceci rayuwan marikin godiya don shi yai muna katsalandan a rayuwan mu ba komai ba.
Tsit falon yayi yayin da nake sake wani irin atishawa mai karfi har sau uku daga inda nake kwance.
Sun tafi yar sokoto ta fadi haka nan tare da kiran sunana maman Abba sannun kinji.
Na gyada mata kai kawai alaman amsawa tace bari na baki ruwa ki wanke fuskan ki.
Ina tashi da kamar minti uku Umma tace dani maryam kin san sui, ifil hayat jinnu oud na kada mata kai alaman nasan shi.
Tace sunce ki shafawa mijin ki tare da hayakin shi yanzu wai ba na asibiti bane gamo yayi da su a daren jiya.
Da sauri na dago kaina na kalli Umma nace gamo kuma Umma a ina ya gamu dasu.
Sai na fashe da kuka tace haba nace Umma ni ina fama da haka ace kuma yau baban Abba shima abin ya shafe shi kuma.
Tace basu shige shi ba sun dai bashi tsoro ne kawai sukace don ya gan su ya haska masu haske akan su.
Lokacin wai akwai tsohon sarki a waje yana shan iska shi kuma ya biyo gurin su.
Da sauri nace baba ke nan ba kanin baba malam mahaifin mukkadarasiyya.
Kallo na suke da mamaki nace tabbas yana kasan nan yazo ziyar na san da hakan nasani kuma sunce mu kiyaye su har ya wuce.
To yanzu dai idan kina iya tashi ki tashi ki dauko maganin kiwa mijin ki yadda suka ce.
Na yunkura zan tashi naji wani irin jiri ya kwashe ni da sauri na koma na zauna inda nake zaune da farko na dafe kaina.
Yaya dai kuma suka tambaye ni kusan a lokaci daya nace babu komai jiri nake ji kawai sannu suke min.
Sai bayan dan wani lokaci na mike zuwa daki na shiga neman maganin wanda sune suka bani shi dama.
A hankali na yaye bargon da yake rufe dashi nakai hannu a jikin shi jikin nashi yai wani irin mugun zafi sosai.
A hankali na soma shafa mai na daba mai ta gurin hancin shi da kunnuwan shi da saman kan shi.
Bai fi minti goma ba ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi cikin murya kamar ihu yace maryam maryam nagan su tabbas BA MU KA DAI BA NE A GIDAN NAN.
Nace haba ya Isa mana haka kayi shiru Allah yabaka lafiya ya koma ya lumshe idanuwan shi a hankali sai kuma ya koma barci mai nauyi.
Haka yasa muka barshi ya samu barci da kyau muka dawo falo sai lokacin ne yar sokoto da mijin ta sukai muna sallama suka tafi gida.

****** ********* ******
A gidan su maigidan ke cewa murjan wai kin san ban taba yarda da zance wasu jinnu ba can sai yau din nan.
Mata kamar ibishiya komai da ta kalli mutum tasani akan shi haka ?
Kai dai ka fadi haka ni babu ruwana wallahi kadai ji warning din su kai min yanzu don haka koda gigin barci ba zan kara maganan ta bani.
Dama Anty hauwa ce mai kawo maganan niko nake zakewa na yi daga yau kuma na dai na indai ni murja ce.
Sai lokacin ta juya gare shi tana cewa ashe kai har aure ake nema ma ban sani ba a gida ?
Yace kai zancen anty Fatine fa wata wai diyar kanin mahaifin mijin ta shine wai ta kama min ita na kara.
Yanzu ai dai kaji in kunne yaji gangan jiki ya tsira yace ai dole sai na bincika.
Yace haba no warder ashe gidan nan sukace na kawo kudi a yadda na taya ashe sun san sherin dake gidan suke son lakaka min shi.
Yar sokoto tace to wani mutum ne ke son cutanka da suka ce yace bakowa bane Devid ne na fahinci haka tun soma maganan ta.
Dama shakiyi ne shi yana da alaman yaudara tare dashi Allah dai ya rufa min asiri ban zurma a hannun shi ba da wallahi ya cuce ni har abada.
Nan dai suke ta magana akaina har ya shirya a makare ya fita zuwa office don ya makara ranan kan case din mu.

Baban Abba bai falka ba sai guraren karfe daya na rana ya tashi daga dogon barcin da yayi.
Koda na shiga ya hada wani irin zufa sharkaf dashi kamar ba shine ke rawan sanyi ba da safe haka na.
Jin muna magana dashi Umma dake cikin matsanacin damuwa ta fado dakin tana fadin ya tashi ne ?
Nace ya falka Umna wai wanka yake son yi ko zai ji dadin jikin sa.
Bathroom na shiga na hada mai ruwa ya mike dakyat jikin shi babu lakka daganin yadda yake tafiya zuwa ban dakin.
Yana fitowa tare da alwala yai sallah nai mai maganan abinci yake cewa nabashi tea kawai yasha a lokacin.
Falo ya fito anan na samay shi nafito da kayan tea na hada mai tea mai kauri ya sha ya koma saman three seater ya kwanta sai faman sannu umma take mai a raina nace uwa ke nan.
Wanan abin na juya daki na dauko da niya na na kara shafa mai da sauri ya cire hannun shi da ya kare fuskan shi dashi yana cewa maynene haka kuma ?
Umma ce ta tare ni da fadin tsaya mana ta shafa don Allah ko zaka kara walwalewa.
Yace may ye shi din kuma tace kai dai bari ta shafa ma kawai badon Allah ya taimake mu tana dashi ba a gida yaushe zamu samay shi har aima amfani dashi kaji sauki haka ?
Murmushi yayi tace ke shafa mai kinji ban tsaya ba na fara shafa mai turaren maganin a jikin shi.
A hankali naji yana sauke wani ajiyan zuciya zakace ko yai nisa ne ga tunane a lokacin.
Idanuwsn mu a kan shi wani sabon barci ne ya dan kara daukan shi a gurin bai falka ba wanan karon sai karfe biyar na yammaci.
Yai sallah na gabatar mai da abinci yace maryam bar abincin nan please bakin nan nawa babu test ko kadan.
Nace ai dole ba karamin jin jiki kayi ba ai Allah dai ya kawo saukin alamarin ai.
Da asibiti muka tafi da kana can killa ma sai sun rike a can su kwantar da kai a yanayin da ka kwana ciki.
Kwanan shi biyu ya walwale ya koma kamar baiyi ciwo ba ma alokacin ya koma normal life din shi.

****** ********* ******
Kudi na tsab na hada nakaiwa hajiyan controler taban kayan da sai dana gigice don yawan su.
Na kalli yawan kayan da akace wai duk a matsayin nawa suke nan na fara kasuwanci sosai ba kama hannun yaro.
Allah ya kama min abin sosai har manyan mata suka san da zamana moton da nake shiga na sayar na tura kudin a gyara gidan mahaifina dashi.
Don na samu kyautan mota tagani ta fada daga gurin gwauna don yanzu zance na zama tankar yar gida a gurin su.
A cikin haka wata rana suka bugo min waya wai Adisatu ta haihu a Niger nai matukar farin ciki sosai da samun wanan labarin.
Ga matar gwauna tace tare zamu yafi Niger suna da ita don Adisatu tace azo dani wai.
Suna saura kwana biyu muka bar kasan nan zuwa kasan Niger a tare da aminiya ta yar sokoto da tai min rakiya.
Munga daula sosai a gurin wa yan nan mutane nayi mamaki daganin haka don a yadda muke jin labarin wai kasan basu kai kasan mu Nigeria arziki ba.
Sai gashi mu munga sabanin hakan gare su ko don gidan masu akwai ne muka tafi oho ?
Zan iya cewa wata kila su arzikin su na gado ne don duk dan wanan zurian idan ka ganshi kaga masu akwai.
Don munga karyan gwalagwalai a gurin su duk wacce zata shigo acikin dakkakiyar shedda ce ga sarka da yan kunne da munduwa duk na zinare.
Muma mun lakaci arziki don akwati guda na irin tufafin su na samu ta ranadar min na fitan suna da zan saka ajikina.
Ganin nazo da yar sokoto itama sai ga nata daga cikun nata tufafin bazakace an taba amfani dasu ba ma ajiki.
Duk wacce tazo zakaji Adisatu tana fadin ga sisters din ta daga Nigeria suka zo suna sai kaga ana mutunta mu da ta fadi hakan.
Mun saje dasu sai ka dauka muma yan kasan ne saboda irin tufafi na alfarma dake a jikin mu.
Ko wani kaya yasha aiki har kasa dashi da zani har dan kwalin su ga gwal a wuya yana muna sheki.
Washe gari ne da dare ta gabatar dani ga maigidan ta wanda da ka gan shi basai an fada ma ba kaga buzu sak dogo siriri dashi amma akwai naira.
Adusatu ce ke gabatar damu tana nuna matar gwauna yace ai yasanta yace yaya maigidanta yace yayi tafiya bai samu zuwa ba ko ?
Tace hakane yaso zuwa amma tafiya ya kamshi tare da shugaban kasa sunfita zuwa waje.
Tace hone ga malama maryam daga Nigeria da na tafi gurin ta kwanan baya kan matsalan mu.
Ya dago da sauri cikin harshen hausa mai surki da yaren su na can yake cewa au wanan ita ce kika tayar min da hankali akan ta sai kin shiga nigeria kin ganta ?
Tace kuma zuwan yai muna amfani ba don gashi yanzu Allah ya azurta mu d Abdoullah.
Nan muka gane sunan da dan ta yaci watau Abdoullah.
Murmushi yayi yace malama mun fa gode Adisatu kin san rigima gareta a lokacin naso ta bari muzo tare amma ta matsa dole ita zata fara hanya.
Ya kara min godiya tare da yaba ma kokarin da akai masu yace zan iya cewa tun wanan lokacin komai a garemu Alhamdullahi.
Muma muka gode mai ga irin halarcin da yai muna na sakon daya aika min dashi daga baya yace haba haba wanan ba komai bane ai.
Muna kokarin mikewa mu bar falon ne nace sai dai akwai matsala dana hango wanan bakin dokin da aka shirya ma zaka hau kada ka haushi saida safe kasa a shirya ma farin adaidai lokacin da kake kokarin fitowa.
Kallona yayi cikin mamaki yace cikin yar murya kina nufin dokin da zan hau gurin kilisa gobe gurin suna nace shi din.
Ikon Allah ke nan da a kwai matsala ga bakin dokin nawa ke nan ?. Nace kwarai kuwa don yau sati daya ana asirce shi don jiran wanan ranan gare ka.
Cikin mamaki ya kara cewa ko zan san wanda yai wanan abin haka ?
Nace Allah zai baiyyana mai shi ta hanyan jarabtan shi da irin ciwon da mai shi yaso kayi ne don kaikayi zai koma ga mashekiya tun a gurin taron zai yanke jiki ya fadi a haka zaka gane maishi.
Muka barsu da matar shi cikin matukar mamakin abinda na fasa masu zai faru.
Bayan fitan mu yake cewa anya Adisatu wanan zancen gaskiya ne kuwa dokin da ko yaushe nake hawan shi tafiyan nan da nayi ne kawai ban haushi ba
Tace kadai yi hakkuri kayi yadda tace ma mu gani don gujewa wahalan rayuwa.
Buki ne sosai akeyi anci ansha anyi karyan arziki ko wace mace a gurin takai ta isa anan naga wanan masifaffan kakar tasu da ta sa Adisatu a gaba kan auren ta da mijin ta don basu so shi ya aureta ba sai daga cikin tsatson ta .
Tsohuwar na gani na ta kasa dauke idon ta a kaina ina ganin ta kira wata hadimarta tana tambayan ta ko ni wacece
Wacce ake tambayan take cewa daga Nigeria muka zo wai yan uwan Adisatu ne dake can.
Ta dago kai ta kalle ni na sake mata wani lalausar murmushi mai sake ma,ana ga maishi don karyan su ya kare ke nan.
Can maza suka fito saman dawa kan su sun saka mijin adisatu a tsakiya daga shi har dokin shi sun sha kwalliya sosai.
Sun na rafe suna dagawa mutane hannu har lokacin da suka karaso daidai wani rufa sun dan bada baya gurin wani mutum maji karfi daga mutanen dake zaune saman kujerun alfarma ya yanka wani irin ihu.
Take hankalin kowa ya koma furin shi nan ya zube a kasa wani farin kumfa yana fitowa daga bakin shi.
Aka kwashe shi zuwa ciki nan taro ya hargitse yan uwa da abokan arziki sai cewa suke subbahanallahi hamma alkasim ne .
Daga saman dokin da yake yakai idon shi a rufan da muke muna zaune saitin bayan matan shi idanuwan shi a kaina kai kawai na daga mai alaman hakane.
Haka aka karasa wanan bukin cikin sabon tashin hankali kakan su mai fada aji duk ta rikice ta rude sai cewa take a taimake ta bata son ta rasa alkasim din ta.
Komai yadda nai masu baya ni ya kasance masu Allah ya taimake su ba hamma Haroon ne ya hau dokin ba da sai buzun shi.
Don su bakin cikin su ya fara samun magaji ba zasu kai fa samun cin dukiyan shi ba da suks so shiyasa aka yanke shawaran a nakasa shi kowa ya huta.
Mun dawo gida da tarin saifa fam a tare da mu inda ban iso gida ba sai da matar gwauna tasa aka canza min kudin yakoma har miliyan uku da rabi namu na nan kasan.

****** ********* ******
Yanzu al, amari na zance Alhamdullahi ga karatu na koma inayi ina son hada digree dina don na rike kwalin a hannu na.
Ga harkan kasuwanci na abin ba, a cewa komai ba kasafai nake samun tsayawa yin aikin jinnu ba sai idan mutum ya tsurani ya zama dole nakeyin sa.
Nayi kudi fiye da tsanmanin mutum a wanan fannin na alamarin jinnu din dake kaina har yakai nakai yan uwana saudiya don sauke farali.
A shekaran da ya kewayo kuma maigidana ya samu cigaba don controler ya dauke shi ya mayar dashi Abuja suna aiki tare.
Shekaran da ya wuce ne na kara haihuwa lokacin na gama karatuna ranan suna mutane suna ganin bakin fuska dasu mukayi shagalin buki sai dai basu san iyalin baba malam ne dana mai shagona da su mukkadarasiya suka zo min wunin buki.
Yanzu idan kin ganni na koma wata hamshakiya dani ba kasafai nake son ina al, amarin jinnu ba duk da har wanan lokacin da nake baku labarina suna tare dani babu abinda ya canza a gareni na al, amarina dasu ban dai da lokacin yin wanan harkan ne don irin ci gaban rayuwan dana samu a yanzu din.

Da fatan yan uwa zasu dinga kiyayyewa a gidajensu da tsaron lafiyan mu dana yaran mu don kaucewa shiga hakkin wasu da bamu ganin su.
Amma su suna ganin muna ganin su da gangan muke shiga hakkinsu.
Na tabbatar da zamu kiyaye rayukan mu daga abubuwan da sunna ya koyar damu mukai watsi dasu insha Allahu babu abinda zai samu rayuwan mu.
Don wanan matsalar a yanzu babu family din da basu shafi wani ba amma mu bamu sanin hakan don ba ganin su mukeyi ba.

Nima zainab ina ce maku anan zan talaita maku labarin maman Abba don samun ci gaba da sabon novel dina dana farawa mosaya na da fatan Allah ya tsare ya kare muna rayuwan mu dana yayan mu da yan uwan mu musulmi.
Nagode kwarai da so da kaunan da kuke nuna min a kullun da dan lokacin da kuka bamu gurin bin karshen wanan labarin.
Allah ya kare mu ya tsare mu sai kuma wani lokaci idan Allah yakai rayuwan mu lafiya nagode nagode kwarai gareku yan uwa musulmai ga fahintar sakon mu a gare ku ma,assalam.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment