Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarta bata da lafiya ne yasa bazata samu zuwa ba.
Nake ce mata bazan samu zuwa a ranan ba sai washe gari don maigidana yafita aiki ko.
Bayan yadawo ne nake fada mai zan tafi gidan wanan matar don suna son sayen kaya na.
Bai so ya barni ba amma da Umma ta sa baki yace sai na dawo sai dai yake ce min nayi a hankali na dai san halin da nake ciki a yanzu nake cewa ai da yar sokoto zamu tafi bani kadai zan tafi ba gidan.
Washe gari bayan mun gama komai ne muka shirya sai gidan mun shiga da kayan da muka kwaso a cikin manyan ghana mostgo.
Nai sa, a masu son sayan kayan har sun riga mu zuwa gidan suna jiran isowar mu.
Kowace bata son yar uwarta ta zabi wanda yafi nata kyau yasa suka riga mu zuwa.
Mun gaisa na baje kayan suka fara dubawa sai gida ya rude da suratai kawai irin ta mata.
Matar gidan bata cikin falon nata tana daga ciki da yarta dake kuka cewa wai bata jin dadin jikin ta takewaya uwar tana mata tsarki .
Yarinyar tana kuka tana cewa uwar tai mata a hankali wai ta haihu ne.
Dariya yarinyan taba uwar ta tafito rike da hannun yariyar tana dariya.
Nan take fada muna abinda yarinyar take fada mata yanzu a bayi wai tana mata tsarki yarinyar ke cewa wai don Allah mama ki min a hankali na haihu ne fa.
Sai sauran matan suka saka dariya a lokaci daya suna tawa yarinyar dariya sosai wai ko a ina tasan haihuwa har take zancen sa haka.
Ido na kurawa yarinyar har na wani dan lokaci naja tsuki mai karfi nace aiba karya take maku ba haihuwa tayi.
Ido suka zaro suna kallo na take na fara wani irin hamma ina murza hannaye na .
Lokaci daya murya na ya koma wanda ba nawa ba ina fadin ku mahaukantan inane.
Yarinya ta haihu shine kuke mussa mata zancen ta da dariya haka babu tausayawa.
Wanan da kuke gani haihuwanta uku ke nan yanzu ba wasa take fada ba wanan haihuwan yazo mata da dan wahala ne yasa har ta fada maku.
Haihuwa fa maman Abba nace ba maman Abba bace mukkadarasiyatu ce ke magana da ku.
Sai duk hankalinsu ya tashi a lokaci daya nace bil, adam baku da kula akan jinjiranku ko kadan.
Yarinya tana a cikin wani hali amma kuna nufin baku fahinceta ba har kuna mata dariya haka.
Kema ai maman siyama yar ki tana da sabon ciki yanzu haka ajikin ta ki koma gida zaki samay ta tana amai yanzu haka.
Nashiga uku inji maman siyama din tafadi a cikin fargaba tare da dafe kirjinta cikin razana tamike tana fadin don Allah ku bari naje na leko wanan almaran da nake ji yau.
Da sauri ta mike tare da saka hijjab din ta tabar gidan acikin sauri tafice duk suka bita da kallo.
Shiru nayi kawai batare dana kara magana ba sai wata daga cikin su take cewa wanan magana akwai ban mamaki.
Wani kallo na watso mata daga inda nake a zaune ina cewa ki min shiru kina cewa haka baki san halinda mijin ki yake aciki ba kwanan zai kawo maki abokiyar zama a gidan ki.
Ta mike tana cewa kai ina yanzun kan ban yarda ba ni da mijina akwai alkawari bazai taba min kishiya ba don ni mijina dan kaki ne.
Tana nufin barin falon nace idan kin shiga gida ki daga takardan dake gefen gadon shi zaki samu sheda a guri amma aure babu fashi a gareshi.
Tsayawa tayi cak tana kallona nace jeki yanzu ki duba ki gani mana da sauri ta kwasa tabar gidan.
Yar sokoto dake a zaune kamar ruwa yaci ta mamaki da al,ajabi sun rufe ta a lokaci daya don bata taba sanin wanan labarin ba akaina.
Sauran matan da muke zaune kowace na gudun motsawa nata ya samay ta .
Maman siyama ce ta shigo gida a rude rike da hannun yarta tana kuka tana fadin wallahi amai na samu tanayi ita kadai a bayi.
Nace to ku tambaye su a ina suka samu hakan ai zasu fada maku nace Siyama fadawa uwar ki ko ke wacece yau don su sani.
Yarinyar tai shiru tana kallona cikin wani tsawa nace bazaki fada masu ba ne ?
Ta soma magana kamar muna fuka yarinya yar shekara bakwai tana cewa jecob ne yai min ciki.
Wanene jecob inji uwan tace wani ne shine mijina yau shekara biyu da mukai aure kullun dare kuma yana zuwa ya dauke ni a gidan mu dake Abuja muke kwana.
Nashiga uku inji uwar tace nice na aurawa baby deniel don yace min yana son ta.
Sai ga baby har tafi ni haihuwa don yanzu baby tana da yara uku niko ina da na biyu ke nan.
Waye jecob da Daniel yarinyar tace a school din mu daya dasu shine ya bani biscuit tun wanan lokaci muke tare dashi.
Nace yaya kuke yi ku fita dashi tace wani lokaci muna hawa bawan gyada shine motan mu wani lokaci kuma muna amfani da takalma wanda ake bari a kofan daki shine muke fita dashi ya zama jirgin mu
( Gareku masu barin takalman sawan ku a waje idan zaku shiga kwana wanan ba wai labari bane it happen always don ba kyau barin abin amfanin ku awaje wallahi )
Nace gida nawa jacob din yake dashi siyama ?
Tace mai kudine sosai yana da gidaje har a America mukan tafi wani lokaci.
Yana da motoci masu yawa a tare dashi sosai da bodyguard masu bin bayan shi don shi ogane.
Nace, matan shi nawa yanzu tace mu tara ne matan shi amma ya fada min yafi so na acikin su.
Uwar yarinyar tace na shiga uku na lalace Siyama a ina kika san irin wanan maganan haka ?
Nace ki barta tai bayani ki zaune da mugun abu a gidan ki tana halaka maki yan uwa baki sani ba.
Itace ta bayar da jinin mahaifiyar ki takuma da na kaunar ki da suka mutu a cikin wata daya a lokaci daya.
Nace ko karya nake maki siyama yarinyar ta dukar da kanta a kasa tare da girgiza kanta tace a hankali gaskiya ne.
Nace may yasa kikaba Daneil baby tace saboda inajin haushinta kada mijina watarana yace yana son ta.
Nace shi mijin baby din acikin cult din ku babbane ko karami a cikin ku ?
Tace shima mai kudi ne sosai yana da dukiya mai yawa sai dai ita baby bata son shi kullun fada sukeyi dashi.
Kuka sosai uwaye suka fara kamar ruwa yaci sauran matan dake falon lokacin.
Nace kuyi muna shiru duk sakacine iein naku na uwayen zamani yakai ku ga hakan.
Baku damu da damuwar yaran ku ba babu addua akan su idan zasu shiga barci idan kuma sun tashi haka kuke bari su fita agida.
Gurin ku kawai suyi ilimin boko su samu duniya sunan ku ya daga shine naku kawai.
Yaran ku da dama suna cikin matsalan rayuwa amma rashin kula irin naku yasa kunyi watsi da nauyin da Allah ya aza maku nasu.
Yaran ku idan sun fita baku san dasu wa suke hurda ba baku san tambayan su damuwar su ba baku saka ido ga dabiun su ko kadan.
Nace siyama yarinyar ta karba kamar muna fuka nace yau zan raba ki da Jecob din ki kina so?
Kai ta girgiza min nace saboda may bakya so na rabaki dashi ?
Tace I love him mummy.
Kuka uwar ta ta kara nace amma kin san ba adinin ku daya ba ko dashi ?
Tace na sani amma yace kadda mummy ta dake ni nayi addini na ba zai hanani ba.
Idanuwana da sukayi jajajir na kafe yarinyar dashi nace zo nan take ta karaso inda nake zaune na kama hannunta a hankali ina murzawa kamar wasa nake mata.
Sai ga yarinyar tana kuka cikin wani irin murya sautin wani yaro mukaji yana fadin don't live me Siyama please i love you .
Iam dying becouse of you .
Nace a cikin wani murya mai kaushi live her alone go back to your people don't ever come back to her life.
Kuka sosai akeyi ana fadin mummy don live us please ?
Ruwa nace abani da sauri wata matar ta miko min ruwa a cup na gunda ruwan abakina tare da matse yarinyar na dura mata a bakinta na shafe mata fuskanta da sauran ruwan.
Nan ta kwanta tana wani irin birgima akasa cikin sauti kala kala na ban tsoro.
Uwar zata tabata na hanata yadda naiwa yarinyar farko haka naiwa baby din ita ma take yaran sukai ta birgima a kasa sai zuwa wani lokaci suka lafa nake cewa karbi nan tare da mika masu hannaye na.
Garin magani ne suka gani shi na basu nace asaka aman shafin yaran a dinga shafa masu daga yau ba abinda zai kara samun su da yardan Allah.
Matar da ta fita zuwa binciken gidan ta tashigo da kuka tana nuna muna resist din da tagani na kayan lefen da mijin ta ya hada kusan miliyan daya da wani abu.
Tana cewa ku cece ni wallahi ashe da gaske ne aure zai kara bai fada min ba.
Nace ki rufa muna baki bakece kika jawa kanki ba kullun ba mutunci gare ki sai bani bani ya gajine da halinki yasa zai kara aure.
Idan kuma kince zaki dauki wani mataki a haka zaki samu matsala sosai a rayuwan ki.
Wai ma kuwa kin san wanda mijin ki zai aura kuwa to bari na fada maki sunan ta hajara diyar wani babban mutum ne a Abuja.
Don haka kiba kanki lafiya shi ne zaman lafiyan ki don an wuce ki ga komai.
Nace nabarku lafiya sai na fara wani irin atishawa a lokaci daya take na duka gurin da nake a zaune na lamay masu a kasa.
Cikin karfin hali yar sokoto take kiran sunana maryam maryam maman Abba na amsa mata da kyat tare da nuna mata hand bag dina.
Tamiko minjikin ta yana rawa da kyat na lalabo hantirina na shiga shakawa kamar zan tura shi a hancina duka.
Sai lokacin na dan samu sa, ida a raina na mike ina fadin tashi muje gida please.
Duk matan sun shiga tashin hankali sosai nan muka barsu cikin tashin hankali muka fice gidan.
Koda muka iso gida a gajiye nake kaman an bani kashi jikina ba lakka tare dani.
Nan na zube a falo ina mayar da numfashi haka baban Abba ya shigo ya samay mu.
Cikin kidimay yake fadin may ya faru kuma please abin ya tashi ne kuma ko yaya ?
Dama maman Abba tana da jinnu ne haka masu karfi a tare da ita ashe ?
Nan dai ra kwashe labarin abinda ya faru take fada masu fada ya farayi bayan ya gama sauraren ta.
Yana fadin ni wallahi maryam ina gudun kada wanan matsalan naki ya jawo min magana a garin nan.
Wanan ai ba so bane basu taimaka maki sai dai su sakaki yiwa mutane tonon silla kawai.
Gaskiya gara ku bar garin nan zaifi min kada a fahince halin da kike ciki kija muna matsala.
Ni dai ina kwance ina sauraren shi ban iya cewa kallallahu ba don ko ni abinda akace inayi yanzu ya fara damun rayuwana sosai.
Yar sokoto tai muna sallama ta tafi tana fadin zata dawo da yamma ta duba ni insha Allahu.
Tana fita gulma bai bari ta shiga gidan ta ba tun a kofa take kwadawa anty hauwa kira.
Anty hauwa dake kitchen tafito da sauri take cewa yau anty naga abin mamaki sosai ashe maman Abba tana fama da jinnu ne haka masu karfi ban sani ba?
Jinnu kuma yaushe ta samay su haka nan dai ta shiga bata labarin abinda ya faru a gidan mutane damu.
Sai da anty hauwa ta kewaya don tsoro da fargaban da ya kamata a lokaci daya.
Nan dai suka shiga magana akai har yamma yai masu bayan magariba suka shigo gidan namu.
Ina ganin su tare nasan takai gulma ko sun zo su tabbatar da zancen ta.
Zaune nake a kasan ties gurin kafan umma muna kallo suka shigo gidan.
Mun gaisa muyi komai take tambayana yaya jikin nawa nace masu da sauki.
Ban yarda munyi zancen komai dasu ba akan zancen don nasan shine ya kawo su gidan.
Har suka gaji suna cewa su zasu tafi don dare ya somayi a lokacin nai masu sai da safe suka fice.
Ashe suns fita sukaga wata katuwar mage bakakirin da its ta kura masu ido.
Da sauri suka wuce ta a razane sai suka ga kamar magen tana bin su a bayan su aiko binsu take cikin tashin hankali suka ruga aguje kowa ta shige gidan ta hankali a tashe.
A cikin wanan daren ne shima baban Abba yai mafalkin ana mashi kashedin idan ya fara ya mayar damu gida zai hadu da tashin hankali a rayuwan shi da dama .
Yana falkawa ne kawai yaji yana ta wani irin sufa wanda kamar ba sanyi akeyi ba a lokacin.
Hankalin shi yai matukar tashi a lokaci daya yake sharan zufa tare da sauke ajiyan zuciya.
Falkawa nayi nagan shi a zaune yayi tagumi kawai yana faman tunane nima hankali a tashe na mike zaune ina tambayan shi ko may ke faruwa kuma ?
Nake cewa akan wanan zancen ne ko nima baban Abba abin ya fara damuna inaji wa kaina tsoron kada na jawo maka matsala a garin mutane .
Komawa na gida naga kamar shine abinda ya dace dani da yaran nan don gudun abinda kaje yadawo muna nan gaba.
Baiyi magana ba har lokacin da nai shiru yake ce min debo min ruwa nasha.
Namike zuwa falon don na dauko mai ruwan yasha kamar yadda ya bukata, abinda idona yaganan min a falon namu ne ya tayar min da hankalina.
Yara ne a zaune suna cin abinci wasu kuma suna kallon Tv wasu na karatu kai su nan dai birjit dasu kowa da abinda yakeyi.
Hakana na ratsa a tsakiyan su ba wanda ya kulani a cikin su har na bude fridge na dauko ruwa da nufin nakai mashi.
Sai naji wata murya na fadin kai maman su Abba din nan yanzun ma dan ruwan da zan sha idan nagama cin abinci shine kuma zata dauka ta tafi dashi.
Wata kyakyawan mace ce tafito daga kitchen hannunta dauke da wani plate mai kyau dashi taci kwalliya sosai tana cewa.
Kai Afir idan na sake jin kana wa babba rashin kunya sai na nayi
maganin ka a gidan nan.
Mayar da ruwan nayi na aje ina cewa yi hakkuri ban san ai naka bane .
Ina fadin haka na juya zuwa gurin fanfo na debi ruwa nakai mai yadan kurba yadago kai ya kalle ni yana cewa babu mai sanyi ne zafi nake ji sosai.
Nace kasha wanan kawai falon baida dadin zuwa yanzu yace kamar yaya ya mike zai fita daga dakin nai saurin rike shi ina cewa kada kafita baban Abba bamu kadai bane a gidan nan.
Masu gidan suna falo suna hutawa a yanzu da sauri yadawo ya zauna yana kallo na acikin mamaki.
Bamu kadai bane agidan kamar yaya na bude baki da zuman nai magana amma kuma na kasa yin hakan.
Sai wani irin zazzabi mai radadi yazo ya rufe ni a lokaci daya haka na shige a cikin bargo ina rawan sanyi dani.
A haka na kwana har gari yawaye gashi yana son fita amma kuma yana tsoron kalamina danai mashi na bamu kadai bane a gidan.
Kalamin yai matukar firgita shi sosai hankalin shi yai matukar tashi dole da safe yakaini asibiti aka dubani.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[11/15, 11:15 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


BAMU KADAI BA NE A, , , ,


๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
2โƒฃ5โƒฃ


Sosai naji jiki ranan don na saka abin da nagani araina don ba wai a mafalkine naga wanan abin ba.
Bayan mun dawo daga asibiti ne barci ya dauke ni misalin daya na rana nai mafalki da matar da nagani a mafalki tare da yaran nan a falo.
Ta shigo dakina inda nake kwance mu ka gaisa da ita take ce min yaya jiki na dan yunkura na amsa mata da sauki.
Tace kiyi hakkuri yar uwa ban san zaki fito ba a wanan lokacin dana boye mu daga ganin ki.
Kin san halin yaran yanzu bajin magana sukeyi ba gashi kuma dare ku shine rana a gurin mu.
Likacin da kuka kwanta kuke hutawa muma a lokacin muke samu muna rayuwan mu yadda ya dace.
Fitan dare idan ba dole ba bai da amfani ga dan adam don gudun yin gamo da ire, iren mu jinnu.
Yanzu ki karbi wanan ruwan kisha insha Allahu idanbkin tashi zaki daina jin komai akan mu.
Daga yau kuma daga ke har duk wani wanda ke gidan nan bazaku kara ganin mu ba har sai idan kece kikaso ganin mu da kanki.
Godiya nai mata na karbi ruwan nasha nashafa a fuskana kamar yadda tabukata nayi.
Ta mike tabar dakin tana min Allah ya sauwaka tafice daga dakin a lokacin na falka daga barci nima.
Fuskana da na shafe da ruwa naji alaman shi a fuskana na shafa naga kamar ba zufa bane nayi nan dai na dade a kwance sannu a hankali naji jikina yana sake min.
Idanuwa na na lumshe a hankali ina tuna mafalkin da nayi nace a raina nikan maryam nawa kaddaran ke nan kuma hurda da mutanen boye a muraran haka.
Nai adduan neman tsari ga Ubangijina na mike zaune falo nafito na samu su Umma zaune da Nusaiba suna kallo
Na samu guri na zauna Umma tana min sannu yaya jikin nace da sauki tace min abinci fa nace na koshi Umma.
Maryam tun safe fa bakici komai ba ki daure ki dan ci wani abu mana ko ?
Nace umma tea zan sha maimakon namike na hada tea din sai ma nakai kwance kawai a gurin.
Ina bin komai na falon da kallo yadda nagan su a daren jiya ne ya fado min araina komai ma yanzu na gidan tsoro yake bani.
Tunda nasan bamu kadai bane mallakin komai da muke dashi agidan ashe muna sharing ne tare da wayanda bamu gani.
Nace kuka ganin mu bamu ganin ku don Allah kuyi muna adalci akan zaman mu yan uwa musulmai.
Umma take tambayana dawa kike magana nace ba kowa Umma ido ta tsura min tana zargina.
Gani take kamar mutanen nawane zasu taso min sai cewa tayi dauko hantitin ki kusa maryam.
Nace babu komai Umma magana kawai nakeyi amma lafiyata kalau.
Gaba dayan mu yanzu munyi farin ciki da samun natsuwan baban su Abba yanzu a gida.
Don idan bai gurin aiki yana gida tare da mu cikin kulawan da ya dace duk magidanci yaba ma iyalinshi.
Haka yasa hankalin Hanna ya kara tashi gashi yanzu sai ta kira wayan shi fiye da sau goma bai daga wayan ta.
Ni dai zan iyacewa tun lokacin da na fara amfani da abinda matar baba na tsibiri tabani yake min wanan irin likewan idan nabi ta nashi koda rana ma zamu kasance a tare dashi.
Ya soma mantawa da zancen wata hanna can idan ba itace takira wayan shi ba.
Koda takira din bai dagawa sai dai yaja tsuki kawai yabar wayan har ya katse.
Idan ma ya dauka ba wani magana mai dadi da zataji daga gare shi karshe ce mata yayi please hanna live me alone for god sake is over now between me and you.
Wanan kalamin ne yai matukar tayar mata da hankalinta sosai take gani idan ta rabu dashi wazata samu da zai kashe mata kudi kamar shi haka.
Ta samu mahaifiyar ta da zancen uwar taita mata fada tana cewa duk yadda zatayi ta gyara tsakanin shi da ita tayi kokarin gyarawa gashi har sun fara shiga wani halin dan rasa shi sa da suka yi kwana biyu a tare da su.
Hanna a cikin damuwa take sosai ta tafi gidan wata yar garin su dake zaune a kaduna ta fada mata halin da take ciki yanzu.
Matar ta girmay ma hanna sosai ga shekaru take cewa ke dama baki shiryawa shiga bariki ba kika shigo ta hanna ?
Kina da kaman wanan guy din zaki bari har ya kufce a hannun ki yaushe zaki kara samun kamarsa kuma.
Nan dai take fada mata akwai gurin wa ni boka da zata kaita aikin shi kamar yanka yake da sun tafi komai zai koma daidai gareta.
Hanna taji dadi sosai sai dai kuma can take cewa gaskiya anty akwai dan matsala sosai wallahi.
Namau kuma hana ?
Matar ta tambaya cikin son jin ina matsalar take kuma ?
Hanna tace wallahi anty matar Aliyu muguwace matsafiyace ta gaske don yanzu haka ma idan nace maki tasan wanan maganan da mukeyi baza, ayi mussu ba.
Dariya sosai mata mai suna Rabeca tayi tace amma har kin bani kunya hanna yaushe zaki tsaya wani tsoron matar shi kuma ?
Ai kawai fito nafito zamuyi da ita komai tsafin ta bata kai wanan gurin da nake shirin kaiki ba ke dai kawai kisa ido ki gani yadda za, ayi da ga ita har mijin nata.
Nan dai suka aje magana washe gari zasu tafi gurin bokan nasu a can wani kauye a yankin jos.
Tunda safe suka shirya don su samu suje su dawo a ranan suka kama hanya.
A gaban boka bai bari sun fadi abinda ya kawo su ba shi da kan shi ya labarta masu komai dake gudana tace mai hakane.
Yan abubuwan su na bokaye yayi suna kallon shi daga shi sai dan bante a jikin shi.
Yadago kai da sauri bayan ya watsa wasu farin kudi a kasa ya fara dan girgiza kan shi kadan kadan.
Can ya dago da idanuwan shi da sukayi ja yana kallon su.
Yace da zakubi shawarana sai nace ku rabu da mijin matan nan gaba daya duk son da kukemai.
Don wanan matar banga kurwanta ba a nan shi dai mijin gashi nan amma kinga matar ba, a ganin ta.
Akwai wasu abu da suka tare ta wanda basu bari ma aganta balle ai mata wani aiki.
Matar tace boka a daiyi kokari a duba muna don idan ba, a kawar da ita ba

Please Login or Register in order to submit comment