Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nauyi bata iyawa.
Shi ya dauko ruwa da jan shi ya zuba min na sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi zubur namike ina mayar da numfashi a hankali tare da dan waige waige.
Ina ganina a kasa abinda ya faru na zuwa mari na da yayi ya fado min a rai.
Take na karasa mikewa zaune da kyau nakai tsaye kasa tafiya nayi na koma saman kujera na zauna.
Kaina jin shi nake kamar zai tsage min gida biyu don ciwon da yake min.
Wayana dake saman kujera ne yai kara shi ya dauki wayan a rikce yake a lokacin.
Muryan mace yaji kuma da bakuwar nomban da ba suna akakirani ya amsa da hello matar ta ce don Allah maryam nake nema please.
Maryam bata da lafiya mijin take magana matar tace idan ta falka ka fada mata matar tsohon shugaban kasa ce takirata tana son magana da ita please.
Layin ya mutu da mamaki ya furta a fili matar tsohon shugaban kasa maryam ?
A ina maryam ta san matan ko chairman balle matar shugaban kasa masu fada aji a kasan.
Mamakine sosai ya rufe shi a lokaci daya yana cewa a ran shi kai al,amarin maryam fa ya fara bani tsoro gaskiya.
Ga yadda ya kasance da ita a yanzu gaban shi yaga yadda ta juye takoma kamar namijin zaki.
Ga hannun shi da aka rike yana mai wani irin zugi kamar zai balle mai don zafi da ciyon da yake mai ga Umma dake kuka wiwi a gaban shi abin ya taru yai mai yawa a lokaci daya.

****** ********* ******
Hajiya Aisha dake zaune tana kallon yadda ake kwashe kujerun gidan ta tace tabbas yarinyar nan mutunce ke nan da gaskiya.
Tunda ga mijin ta har munyi magana dashi ya tabbatar min da tana kwance bata da lafiya.
Taso ta gaiyace ni zuwa dakin tane na duba mata idan ba sihiri a cikin sa sai ta bar kayan dakin nata dama duk ko ina na gidan.
Gashi yau har taji sauki ta fita zuwa gidan marayu kai ziyara kamar yadda takeyi acan baya.
Ta dade idan tana barci tana ganin fuskan wanan yarinyar ana fadin zata taimaka mata itace zata taimaka mata a dalilin tane kawai zata iya samun sauki.
Sai gashi Allah ya kawo mata maryam har gida da kan ta ta taimaka mata sai dai kuma yarinyar taki karban komai daga gareta ko abin gidan bata yarda ta taba komai ba.
Dole ne ta nemo gidan wanan yarinyar a duk inda take a cikin garin nan ko kasan nan yazama wajibi a gareta don tanemo yarinyar na don lafiyan ta dana yaran ta.
Mutunci da kamala da kuma tarbiyan da tagani ga yarinyar yasa taji son yarinyar ya shiga zuciyar ta farat daya a lokaci guda.
Wayan ta dauka takara kiran layin yarinyar har lokacin mmijin tane ya dauki wayan again.
Cikin kwantar da murya take cewa don Allah a wani unguwa kuke ne ina son na gantane please.
Bai tsaya tunanen komai ba ya fada mata uguwa da gida da yadda zata ce idan tazo gidan.
Ba bata lokaci ta shirya take cewa kanin ta da ta dauko yanzu ta aje shi a gidan ta don yanzu hajiya tsoron kowa take ji.
Bashir ka shirya mota zamu fita ni dakai ban son ka fadawa kowa fitan mu kasan yadda kayi ka kawar da kowa a get yanzu ganinan saukowa.
Asirtacen hanyan daba kowa yasan dashi a gidan ba tabi har tafice daga gidan su karimay basu sani ba.
Uguwar da zasu tafi ta fada mashi nan Allah yakawo su har gidan mu lafiya.
Baban Abba wanda yaki fita gidan don tsoro ga hannun shi dake ciwo yana son zuwa ya gaskanta zancen da yaji yanzu a bakina yanajin tsoro.
Haka ya daure don tabbatar da zargin shi ya nufi gidan hanna din bai tsaya sallama ba ya sakai dakin.
Suna kwance tsakiyan aikata masha,a da wanda take kira wai dan uwanta ne yasan mutumin farin sani don wani lokaci har tana sa sai ya taimakawa mutumin.
Ganin su a haka yasa shi rimtse idanuwan shi suka dago a firgice suna kallon shi juyawa yayi yabar dakin da sauri yafada motar shi yabar unguwar.
Ina kwance naji sallama a kofan falo da kyat na iya daga kaina ina kallon mai shigowa gidan.
Tana saye da bakin abaya ta yafa dan kwalin shi a kanta rataye da jakarta a hannun ta.
Umma dake zaune take gaiyawa jin yadda Umma ta amsa mata magana bai fita cikin daga hannu yasa ta fahinci umna din ba lafiya gareta ba.
Namike zaune da kyat ina gaida ita da mata sannu da zuwa lokacin ne kuma yarana suka taso daga makaranta suka shigo gidan.
Nace mama kece tafe shine baki kirani ba nazo kika taso tace na bugo waya ance baki da lafiya diyata shine na taso.
Nace ni lafiyata kalau ina dan murmushi a fuskana mamakine baiyyane a fuskan ta karara tace to yaya kuke nace lafiya kalau mama.
Mama kin dai ki koran mutanen gidan ki ko idan baki koresu ba sun kusa ganin bayan ki dake da dan ki Ahmed da zai dawo satin nan suyi shiri sosai akan shi don shine matsalan su dake, sauran diyan naki matane basu damu dasu ba sosai.
Ikon Allah inji hajiyan ke ko diyata duk a ina kika samu wanan labarin haka dan Allah nace nima ban sani ba na dai gani ne a tare dake kawai.
Ta gyara zama da mazaunin glass din idon ta da kyau tare da kura min ido sai wani hamma nakeyi kamar mai jin barci a lokacin.
Kafin tai magana nace mama Alhaji Ibrahim ya sha alwashin rabaki da komai naki a duniyan nan har rayuwanki dana diyan ki sai dai kuma da yardan Allah bazai taba cin nasara akanki ba don halin ki na alheri garesu .
Matsalan ki daya dasuke samun galaba akan ki shine sakaci da Ibadan ki da kuma saurin yarda da bokaye da malamai don dasu ake hada baki ana kara cutata maki.
Duk wanda kika gani a gidanki an riga da an saye shi da makuddan kudi masu yawa.
Aikin wasu sukeyi a gidan ki banaki ba kawai don sunfi ba da aminci ga wancan din dake biyan su fiye dake.
Kinga hajiya halira da itace ake kulla maki komai gashi kuma itace ta kusa dake sosai kin watsar da yan uwan haihuwan ki kin kama yan bariki ajikin ki.
Mama ki jawo yan uwanki ki saka ajikin ki zauna da abinki lafiya don sune naki naji.
Yan adam suna sakaci da zumunci a wanan zamani zumunci kuma ba abin wasa bane.
Idan kin bar gidan nan zaki shiga gida ki tabbatar da abinda hajiya harira ta kawo maki wata biyu da ya wuce antone wanan mugun abin a gidan ki don babu ke ba lafiya muddin wanan abin yana a tare dake a gidan ki.
Yanzun nan kisa Bashir ya shiga bayan ban dakin ki dai gurin da ruwa ke zuba zaiga katon dutse sai ya daga dutse duk abinda yagani ya dauke shi a kona akan ki da yaranki akai wanan sihiri wanda haka kawai zaki dinga jin haushin su kina hattaran su kiji baki son hulda dasu ko kadan.
Duk wanda yai maki aanan aiki nan da kwana biyu da kan shi zaizo neman gafaranki da bakin sa.
Abuna karshe yar uwarki halima dake lagos itace kawai nake son ki dan ja dabaya gareta ki rike sirinki a cikin ki don tana maki zagon kasa sosai a rayuwan ku.
Ni zan tafi lokacin kararu yayi idan kin tsare wanan abin dana fada maki da yardan ubangin ba abinda zai kara samun ki ki karbi wanan dake da yaranki kuyi wanka da hayaki kusha na barku lafiya.
Suuu natafi na koma saman kujera sai atishawa na fara sakewa mai karfi har sau uku na mike zubur ina dan waige waige Umma nagani zaune tana barci a saman kujera sai hajiya da ke zaune cikin damuwa ta kura min ido kawai tana faman yi min sannu.
Nace mama ni lafiyata kalau ba abinda ya samay ni fa kina min sannu haka.
Tace ai na sani amma sannu da kokari maryam nagode nagode kinji.
Kallon Mamaki nake mata don ban san may takewa wanan godiyan ba haka a gareni.
Wani atishawa na sakeyi again nace hajiya Aisha barka da zuwa tace yawa dawa nake magana kuma tace mukkadarasiya ce diyar Alhaji malam kike magana da ita.
Tace sannu dazuwa ko muryana sak ya koma kamar wata balarabiya dani nace yauwa hajiya.
Kin dai yi arziki mahaifina yasa hannu ga aikin ki amma ke ma baki da dama hajiya duk abinda ya faru dake kece sillar sa.
Zaki iya tuna baya lokacin da kika tafi wani kauyen kasan Ibo gurin wani hatsabibin boka keda kawarki Ajoke.
Wacce yau shekaran ta goma ke nan da mutuwa to tun wanan lokacin matsalarki ta fara.
A matsayinki na musulma da kika san Allah da Annabinsa kikaje gurin kafirai inda ake tsafi don kawai son duniya.
Ku bil,adam kuna da taurin kai sai ku sani ku take sani kamar yadda namu jinnu suke da taurin kai sosai idan an hadu da miyagun mu.
Wanan bokan ba kowa yasa akaiki furin shi ba sai makiyin ki dan uwan mijinki kuma abokin shi Ibrahim.
Sun hada baki da wanan matar data kaiki inda ya bata makudsan kudi masu yawa.
Da ace kin dogara ga Allah kin mika kukan ki gareshi da zakifi samun nasara da haske ga bukatun ki.
Da adam Allah zai mai falala yatsaya ga taimakon dan uwan shi musulmi, kina ziyaran asibitocin ku kina taimakawa marasa lafiya kina taimakon maraya ko dabbobi da zaki samu haske ga duk wani bukatan dakike dashi a gurin ubangiji.
Wanan godiyar tamu maryama boyar Allah ce da tana dashi zata taimakawa marasa galihu sosai a rayuwan ta sai dai kukukuku ta kada kai arziki bai zuwa gurin da bayi ke bukatan shi .
Hajiya tace don Allah wama kikace sunan ki tace sunana yana da wuya a gareku.
Hajiya tace yanzu idan ina tin wanan abubuwan dakika lissafo min kina ganin zan gyara tace dayafi maki alheri.
Waccan kawar ki Ajoke tuni aka gama da ita akan wani aiki da akaso tayi akan ku amma takiya.
Ku dinga sa tsoron Allah ga al, amarinku matan bani adam sun shaga da son duniya suna mantawa da komawan su ga mahaliccin su.
Macen bani adam zata bushe zuciyarta ta aikata ko maynene akan abokiyar zaman ta ko wani dan uwanta mutum wanda hakan ba daidai bane a garemu bisa ga koyarwa da manzo yai muna.
Akwai hanyoyi da dama da zaka kai ga nasarorin ka amma duk an watsar dasu ankoma ga hanyan shedan wanda dama shi gurin shine yaga ya halaka duk wani mumuni na Allah su kone a tare.
Nakima yana da sauki sosai gana wasu don ke neman zaman lafiya da maigidan ki da farin jini kikatafiyi bakice ai mashi wani mugun abin ba can.
Kuji tsoron Allah ga rayuwan ku akwai jinsin mi jinnu da aikin su halakar dakune kawai zuwa ga halaka duniya da lahiran ku ni zan barki don godiyar mu ta huta sai mun sake hadu wani lokaci.
Na sake wani atishawa mai karfin gaske har uku sai sannu Hajiyan take ta faman yi min duk umma tana ta sharan barcin ta ba aikomai akan idon ta ba.
Wanda nasan haka aikin sune kada taji sirin wasu ko taga halin dana tsinci kaina aciki a garin mutane.
Maryam na gode ni zan tafi sai kuma kin karajina ki min godiya gurin Alhaji malam.
Ban fahince taba na dai amsa mata da to mama insha Allahu zaiji take ce min zaki kara jina da yardan Allah amma don Allah ina son nai maki wani tambaya idan bazaki damu ba.
Ba matsala mama kiyi tambayan ki don Allah nace koke mutumiyar wani gari ?
Nai murmushi nace ni mutumiyar Niger state ne mama tace ikon Allah zamane yakawoku garin nan ko aiki.
Nace aikine yakawo maigidana garin nan shi ma,aikacin custum ne na kasa, shine muka zonan din tare dashi.
Tace yanzun na gamsu dake maryama kin san duniya abin tsoro ne sosai yanzu dole nayi bincike sosai akan ki don gudun kada wani ya turo ki gareni cikin rashin sani a yaudare ni.
Don hakan yasha faruwa dani sai ka yarda da mutum yazo ya yaudare ka daga baya kuma haka yasa nake jin tsoron hurda da mutane yanzu.
Amma kinga yanzu na gamsu na dai fahinci ke alheri ce a rayuwana maryam
Don kafin kizo na dade ina mafalki dake duk dare idan na kwanta zan dinga jin sunan ki a mafalki na ana fada min cewa kece zaki kawo min maganin warakana.
Da farko har ina daukan zancen zancd ne na mafalki kawai, amma daga baya danaga abin yai yawa sai na fara tunane akai.
Kwasan ranan da zaki zone nai mafalki da nai bakuwa maryam sunan ta zato zo min da warakana.
Ba karamin jin jiki nayi a gidan nan ba watarana ma sai naji dama na mutu na huta da wahalan duniyan nan kawai.
Nace mama mutuwa dace ne ga rahamar ubangiji don haka bawa ya roki Allah sauki akan al, amuranshi shine mafita kawai.
Tace hakane wallahi ina yawan kai kokena ga ubangiji kin ga Allah ya karba min.
Ta saka hannun ta a cikin hand bag din ta tana cewa Aisha da tashigo dakin baby zonan ki karba a saya maki alawa kinji.
Aisha tazo gareta tana cewa yaya sunan ki yan mata ?
Sai Aishan take ce mata Aisha Aliyu Auna.
Kai kice ke takwaratace ashe ?
Ikon Allah to karbi mummy ta saya maku alawa keda yan uwanki kinji ki yi kokari a school kinji kada kiyi ragganci ba, asan Aisha da tsoro ba.
Aisha tace na gode mummy abin yaba hajiya sha,awa yarinya karama ta san anbata abu tayi godiya haka.
Murmushi nayi daga inda nake zaune ina jin yadda hajiya take yaba mai sunan su.
Kudi ne sabbi rapper yan dubu daya mike dasu har guda biyu.
Nace kai mama kudin nan sunyi yawa wallahi da dai ki rage su please.
Tace haba maryam don baki san ko nawa na kashe akan jikin nan nawa ba ko .?
Na kashe kudi masu yawa ga banza banyi nasara ba don dan wanan dana baki aiba komai bane don ban iya biyan ki abinda kikai min arayuwana.
Sana dinki nake gani insha Allahu sauki ya samu a gareni da yardan ubangiji.
Nace dama haka rayuwa yake ciwo daban magani daban sai an wahala kafin asamu nasara akai.
Tana mikewa tana gyara tsayuwan glass din ta Aliyu ya shigo gidan ranshi abace.
Tun daya shawo kwanan mu ya hango wani katuwar motar jeep tsaye a kofan gidan shi yake mamaki kowake da wanan motan haka ?
Don iya sanin shi bai san wani ba aduk fadin garin nan da zai mallaki motar miliyoyin kudi har yazo gurin shi.
Har ya fito idon shi yana akan motar yana kiyasta yawan kudin wanan lafiyayyen motan daya gani fake kofan gidan.
Sun dai gaisa da bashir a waje amma bai mashi magana ba yashigo gidan.
Lokacin ya samu hajiya tana shirin ficewa daga gidan ganin shi yasa hajiya dakatawa daga tafiyan da zatayi.
Tace ko wanan ne surikin nawa ko ?
Tace mai barka dai yaya aiki yaya iyali ya amsa adan darare don rashin sanin ko ita din wacce.
Tace to ni zan tafi sai anjima ke nan nagode ko Aisha Allah yabamu Alheri.
Tana fita daga gidan yakai idon shi kan kudin da Aisha take mika min a hannun ta.
Cikin wani murya yake cewa maryam wacece wanan matar dana gani yanzu tafita.
Nace nima ban san ta ba kawai dai Allah ne ya hadani da ita har tazo gidan nan amma nima ban sani ba wallahi.
Sai dai naji ance kamar matar tsohon shugaban kasan nan ce ita.
May yakawota gurinki yanzu kuma ina kika santa ma wai ?
Nace sako tazo na bata kuma na bata abinta ta tafi sakon may naji ya jefo min tambayan abazata.
Nace magani ne irin na maganan mata kawai tazo na bata kuma nabata ta tafi.
Kallon sunkin kudin dake aje a gabana yakeyi yana kada kafan shi har lokacin
Kudin nan fa nace yara taba kyauta tace,
Yace mu gani nawane kudin kamar fa duk yan dubu dubu ne nace ban duba kalan su ba don basu gabana yanzu.
Mikewa yayi yatako har gabana ya dauki kudin ya bude wrappers din dubu dubu guda biyu a ciki.
Yace what kyautan dubu dari biyu kai tsaye haka ikon Allah.
Nace wanan bakomai bane a gurin su don Allah ya hore masu shi basu hasaran bawa nabaya dasu.
Kallona yake a cikin mamaki Ummace da tai magana yasa zancen ya katse bai samu furta komai ba again.
Nake cewa Umma may kike so ne na karasa da kyat zuwa inda take don duk jikina yai nauyi sosai a lokacin kamar nai wani aiki mai nauyi.
Ruwa take so na debo mata ruwa na kafa mata tasha tace Allah yai maki albarka.
Amin umma nace har na zauna take cewa kuma tana son ta kewaya bandaki.
Namike nakaita ta kewaya tafito duk yana zaune yana kallon mu duk abinda mukeyi da ita.
Haka yasa ya dan nisa kadan tare da dan bubuga kafan shi a kasa don yaga irin faman da nake da mahaifiyar shi abin yai yawa sosai cikin ma wai ta samu sauki ke nan.
Yace cikin dan sauke ajiyan zuciya amma yanzu naga kaman jikin na umma akwai sauki sosai don gashi har naji kaman tana magana ko ?
Gashi kuma tana dan takawa da kafan ta a hankali dai sauki na shigowa ke nan.
Har yanzu maganin hawan jinin ne kukeyi ko may ?
Nace ba hauwan jini bane ke damun ta ciwo dai ne don maganin hawan jinin ai halakata ya so yayi.
Sai dana canza mata da na gargajiya gurin dana taba karbawa Nusaiba ta samu lafiya can na karbo mata shine mukaga wanan saukin haka.
Maganin hausa kukeyi aka samu wanan saukin haka ke nan ?
Nace shi mukeyi da yardan Allah kuma zata samu lafiya takoma daidai da ita.
Allah yasa yace tare da mikewa tsaye yana fadin shi zai fita ke nan ko akwai abinci yunwa yake ji.
Kai Umma ta girgiza don takaici ni dai na mike na kawo mai abincin shi ya fara ci ga nama zuku zuku a ciki ya zauna yaci sosai can yace wai naman may ye haka kuka samu mai dadi ?
Nace naman baunane aka bani nai miya dashi da sauri naga ya mike tsaye yace what naman bauna a ina kika samu naman bauna haka?
Nace kaidai ba kaci ba may ye na tambaya kuma haka kaman wanda yaci naman mugun dabba.
Look ina kika samu nama nace maki please ?
Nace anbani ne a wani tsibiri danaje karbowa Umma magani.
Yace what ?
Sai naga ya fara kakaro amai kamar mai son amaye hanjin cikin shi lokaci daya.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[11/11, 12:10 AM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง

BA MU KADAI BANE A, , , ,

๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง

2โƒฃ2โƒฃ


Ya shiga damuwa don yasan tabbas akwai bakon al,mari ga zancen na a yanzu.
Fita yayi daga gidan bayan ya gama kare karen aman shi a back yard yafito zuwa waje.
Wayan shi dake a aljihu shi yaciro ya kira layin mahaifina wanda yake gani shi ya dace ya fara fadawa wanan zancen.
Sun gaisa da babana tare da tambayan jikin shi shima baba tambayan jikin Umma yayi da aikin shi.
Ya amsa alhamdullahi ba duk muna lafiya Umma ta samu sauki sosai don yanzu har tana tafiya tana magana.
Alhamdullahi inji baba din yace,
Aliyu yace baba dama nakiraka ne na fada ma wani magana akan maryam.
Subbahanallahi inji baba din yace maryam kuma may samay ta kuma ?
Aliyu yace baba a gaskiya maryam yanzu gaba daya ta canza wani bakon al, amari ne nake gani a gareta.
Ga mamakin Aliyu din sai yaji baba yace na jinnu ko ?
Yace a sanyaye haka ne baba.
Yace gaskiya maryam tana tare da jinnu kuma masu karfi ne a tare da ita sai dai bama su cutawa bane.
Dama kasan matsalan mahaifiyar ta ke nan shine yanzu suka koma kan yar ta.
Kada ka damu da wanan don nayi iya yina akan hakan amma babu abin da zan iya akai dole mu barta da abinta don musulmai suma kamar mu.
Al,amarin maryam da jinnun nan yai nisa Aliyu matsala daya ne ka kaucewa shiga harkan ta ta baya don kada su dauki fansa akan ka.
Saboda duk wanda ya shiga harkan maryam a shirye suke da su dau fansa akan mayshi.
Saboda son da sukewa mahaifiyan tane ya shafe ta har suke mata wanan irin son haka.
Amma gaskiya al, amarin maryam nima yafi karfi na don maryam tasan abinda ni dakai da ma wani bai sani ba a yanzu.
Kallo daya zataiwa mutum ta gane matsalan da mutum yake ciki kaga ashe al, amarin nata yayi nisa ke nan.
Nisawa Aliyu yayi yace to yanzu baba yaya za, ayi ke nan ko haka zamu sa mata ido muna kallon ta.
Murmushi baba na yayi yace Aliyu ka kwantar da hankalin ka akan al, amarin nan don abin yai mata nisa sosai.
Kuma zuwan ku gidan nan na kaduna ne abin ya karu a kan ta don a gidan kuna tare dasu duk inda ma kake tunanen zaku yanzu a tare dasu kuke.
Duk gidan da kake gani akwai su sai dai mu bamu sani ne sunfi mu yawa a duniya don su basu mutuwa.
Muko kaga muna ragewa don muna mutuwa kuma bamu da shekaru kamar su.
Maryam tare take da babban malamin jinnu wanda kowa ya sani da Alhaji malam
Sunan shi sulaimana malami kamar shehi ko waliyi a cikin su yai taimako ne shi a duk inda yaga musulmi yana a cikin halin bukatan taimako.
A sana diyar yar shi maryam ta hadu dashi wanda har yakai sun bude mata ido tana ganin su ko yaushe har tana zuwa biranen su ziyaran su.
Ziyaran su baba ita maryam din ?
Babana yace ita din kuwa duk sanda taso zuwa

Please Login or Register in order to submit comment