Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

๏ปฟGubar Rayuwata


By


Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)






_____________________________________
Wannan Labarin kagagge ne da babu duban yadda wani yake rayuwarshi aka tsara shi, amma wanda yaji kamar dashi ake to ba nayi dan tozartashiba, kuma ni bansan dashi ba.














Page 1 & 2










Cikin wata babbar makaranta ce ta kud'i da ke cike da kayan wasanni na yara kala-kala , wannan makarantar ba kowacce makaranta ba ce face . DR DD SECONDARY SCHOOL.


Uncle Yahaya ne zaune a cikin staff na malamai yana making d'in wasu littattafan d'alubai.


Wayarshi ce ta fara ringin , kawai yana kallon wayar ya ga Harun ne ke kira murmushi ya yi yana cewa, "Zaka dame ni Harun."
Har kiran ya yanke Uncle Yahaya bai d'auki kiran ba .


A karo na biyu dai Harun ya sake kiran wayar uncle Yahaya ya 'ki dauka , Harun bai sake kira ba.
Hakan yaba Uncle Yahaya damar cigaba da aikinsa.


Anan cikin wani babban gida kuwa , Zainab da Ahmad ne zaune cikin falo , Zainab ce ta kalli Yayannata Ahmad tana cewa, "Yaya Ahmad! Abokinka Harun ya zo nemanka."
Da sauri Ahmad ya kalleta yana cewa, "Da gaske , ai na yi zaton ya mance dani zasu zana jarabawar sojoji."


Zainab cikin zumud'i ta kalleshi tana cewa, "Da gaske , to dan Allah yayana ka gayyato mana shi cin abinci, wallahi yana da kirki sosai."


Wani zumm Ahmad yaji a ransa , ya kalleta ya yi murmushi yana cewa, "Zancen ki ya yi tsari kuma zan gayyatoshi."
Zainab tai godiya , a jiyar zuciya Ahmad ya sauke yana satar kallonta gumi ya had'u masa , ga dukkan alamu Ahmad ba ya san zuwan Harun cikin gidansu.


Iyalan Alaji Kabiru ke nan , babban mutum d'an kasuwa da ya san ya kamata .


Anan cikin gidan Alaji Idris kuma abin har yafi na can , domin gida ne babba da babu makosa a jikinsa , yaran Alaji Kabiru guda uku ne , Kalisa , Jafar sai Nabila , sai matarsa Hajjiya Maryam .
Alaji Idris yana kaunar yaransa matukar gaya , duk yadda zai don si farin ciki yana musu, hakan ya sa su ma yaran suke kaunar iyayensu.


Zaune take cikin doguwar riga mai launin d'awisu tana waya cikin farin ciki , da wanda take kauna wato Umar, kai da ka ganta zakasan matukar farin ciki yake sata , musamman taji labarin zai zana jarabawar sojoji , Alaji Idris ne ya shigo d'akin , tai saurin sauke wayar kasa tana kallon mahaifinnasu , Alaji Idris ya samu guri ya zauna kusa da ita yana kokarin fara magana, ganin haka yasa Kalisa saurin kara wayar a kunnenta tana cewa da Umar zasi magana .




Fuskantan mahaifinta ta yi sosai Kalisa cikin girmamawa


Alajin ya kalleta yana cewa, "Wato Kalisa a kullum wannan rayuwar gudu take mana , bani da burin da ya wuce naga walwala a tare daku , a dan haka naga lokaci ya yi da zan samar miki da abokin rayuwa , wanda ko bayan bama nan za ki alfahari da shi ."


Da sauri Kalisa ta d'aga kai tana kallon mahaifinta
hakan yasa Alji Idris cewa , "Karki damu ba shi da wani aibu."
Ya karasa maganar yana tashi , da hanzari Kalisa ta riko hannusa tana cewa, "waye shi dady."
Alaji Kabiru ya yi murmushi yana shafa kanta yana cewa, "Zai zo Kalisa."
Ya fita waje , ajiyar zuciya ta sauke tana binsa da kallo .


Harun ne a kan hanyarsa ta zuwa gidansu Ahmad , yana tafe cikin ransa yana tunani a zuciyarsa , "Kai yau kuma koda wacce macen zan kwana oho, ni wallahi matan ne ma duk ba tsafta garesu ba , kai gaskiya mata sun yi arayuwa , dubi dai ta ranar juma'ar nan yarinyar nan ta susuta ni ta sumar dani,
Haba malam yanzu nasan ina rayuwa, amma dah na fashe a Tiga Dam ba inda nake zuwa."
Sauri ya yi ya matsa sakamakon wani mai keke zai cusa masa taya , hakan yasa ya yi tsaki yana ," idan da wannan banzan ya gyaran mota ta ai bazan taho a kafa ba ."
Yaja tsaki yana kokarin tsai da abin hawa .


Anan kuma Zainab ta matsu da isowar Harun , sakamakon ta yi masa girki kala-kala
aiko tana zaune a falo sai ga Harun ya shigo da sallama yayin da Ahmad a lokacin ya fito daga d'akinsa .


Mutuwar tsaye Harun ya yi yana kallon Zainab cikin mamaki, a cikin ransa yace , "Wow kyakykyawar yarinya kuma karshe."


Ahmad ne ya katse sa yana cewa, "Karaso mana Harun."
Harun ya yi murmushi yana kallonsu tare da karasowa cikin falon
"To Zainab ga Harun yazo."
Ahmad ya fad'a yana kallon Harun da murmushi
Zainab cikin wata siririyar ta kalli Harun tana cewa, "Sannu da zuwa yayana, ya hanyar fatan kazo lafiya."


Murmushi ya sake yi yana jin dad'in maganarta yace ,"Nazo lafiya Zainab, fatan kin mini girki mai dad'i domin ni indai akwai abinci to ba matsala."


Dariya tasa tana nuna teburin cin abinci tana cewa, "Na yi ma girki mai dad'i sosai."


Ta mai jagora zuwa teburin yayin dashi Ahmad har ya ruga da ya zauna a wajen yana danna ayarsa .
Harun yana isa wajen ya saki murya yana cewa, "Gaskiya wannan abinci ya yi kyau sosai, amma bai kai wacce ta had'a shi ba ko kad'an."


Ahmad ne ya yi sauri ya kallesa yana cewa, "Hmmm."
Ya ci gaba da danna wayarsa
yayin da Zainab ta kuma murmushi bayan ya zauna ta fara zuba musu abincin ,
tana zubawa Harun ya satar kallonta yana kallon duk kan jikinta yana girgiza kai , shi Ahmad sam baisan abin dake faruwa ba,
bayan ta gama tace dasu bismillah , aiko duk suka maida hankali kan abincin , wanda lokacin ne Alji Kabiru da Hajjiya suka shigo falon.








Anan cikin DR DD kuwa uncle Yahaya ne cikin staff room shi da wata d'aluba mai suna Laila , Uncle Yahaya ya kalli Laila cikin soyayya yana cewa, "Me yasa jiya ina kiranki ki tsaya mu tafi gida ba ki tsaya ba."?


Laila ta d'ago fararan idanunta tana kallon Uncle d'insu tana cewa, " ba komai."
Ya yi murmushi yana cewa, "Tom ni dai gaskiya kalaman soyayya nake so ki mini."


Zaro idanunta ta yi tana kallonsa ,"Uncle ni ban iya kalaman soyayya ba gaskiya. "
Ta fad'a cikin shagwa'ba
Murmushi ya yi tare da jin dad'in yanayin yana cewa, "To gaskiya kije koya ina so , ki ringa rubuto mini a takarda ina karantawa ina jin dad'i."
Laila tace ,"To."
Yace" za ki iya tafiya lailata".
Laila ta mike ta fita tana tunanin ta ina ma zata farayiwa Uncle Yahaya kalaman soyayya
saiga wata d'aluba 'kawar Laila tazo tasha gabanta tana cewa, "Ta Uncle har an gama love d'in ."
Murmushi Laila ta yi tana cewa, "Wai kalaman soyayya yake so, kuma ni ban iya ba Khadija ki taimakan ."


Khadija taja da ba ya tana cewa ,"To nima wallahi ban iya ba Laila yanzu ya zami to."


Laila idanunta sun ciko da ruwa ta kalli Khadija tana cewa, "Wallahi ina son Uncle zan iya mutuwa zuciyata ta buga a kan shi ."
Kawai Khadija ta jefa mata wata harara .


Wayar Uncle Yahaya ce ta fara ringin , Harun ne dai ya d'auki kiran
"Kai shegen duniya har yau zuwa legos d'in bai zo ba ne ."


Harun ya tambayi Uncle Yahaya,
Uncle Yahaya yaja doguwar a jiyar zuciya yana cewa, "To ina ruwanka ko ance ma ni neman mata zani , biki ne fa ."


Harun ya kwashe da dariya yana cewa, "Wallahi mutumina ba da ban ina aiki ba , nima binka zan kawai naje na shanawata da manyan mata. To ya Tiga ya mutanen garin."




Uncle Yahaya dai mazaunin garin Tiga dam ne , ba shi da kowa sai kakarshi tsuhuwa ce da yake kira da kaka , yana koyarwa cikin private school ta DR DD
haka kuma yana soyayya da wata yarinya Laila mai kimanin aji 5 na babbar secondary, Laila Adam mahaifinta lauya ne babba , ita kawai Allah ya ba shi a matsayin 'yarsa hakan yasa yake matukar sonta.


A bangaren Harun kuma iyayensa suna a Tiga , shi kuma ya shiga cikin kano yana rayuwarshi a can yana d'an guba gubarsa ta neman kudi , kuma yana cin mutuncin mata da su .


Duk sun hallara a teburin cin abinci amma banda Kalisa.


Alaji Idris ne ya kalli a gogon hannunsa yana cewa , "Har 8:05 ina Kalisa ne."


cike da shagwaba ta fito tana jan jiki ta zauna kan kujera tana cewa, "Ni wallahi dady na gaji da abincin gida."
Alaji Idris cikin rarrashi yace ,"To me kike so ayi yanzu."
"Kawai mu tafi restaurant dady."
Jafar ya fad'a
Alaji ya kalli autarsa Nabila yana cewa, "Wai haka my baby."
Nabila tace, "Eh."


Hajjiya ta had'e rai tana cewa, "Haba Alaji ya ku ke son nayi da wannan abincin kuma , wallahi ka dena yiwa yarannan haka , sanda babu kai ya kake so su yi."


Alaji Idris ya kalli Hajjiya yana cewa, "Dakata Hajjiya! Kema in kina so kawai ki taso mu tafi , kuma da kike maganar idan ba nanan to ba mutuwa zan ba ni na barsu."
Alaji ya kallesu yana cewa, "Kai kona mutu ku d'ebi kud'i ku yi duk abin da kuke so, idan ban yi muku ba wa ku ke dashi."
Ba tare da Hajjiya taso ba suka tafi
suka ci duk abin da suke so , domin saida Alaji ya kashe kud'i ki manin dubu talatin sannan suka dawo gida.


A halin yanzu Harun ya rasa ta yadda zai gabatarwa da Zainab cewa yana sonta ,Harun ba karamin d'an iska bane , aiko duk yadda zai ya samu Zainab nasan zai aikata.




Wajejen yammaci yana kofar gidansu budurwarsa Rufaida suna cikin mota suna hira , wani langwa'be mata ya yi yana cewa, "Please Rufaida kizo muje gidana mu huta ."
Wani fad'uwar gaba taji a ranta , ta kalleshi tana cewa, "Ni fa babu inda zani , yanzu zaka ga an aiko ma na koma gida ".


" To har kafin a aiko ma munje mun dawo rakani za ki fa."
Ya karasa maganar kamar zai had'e jikinsa da nata,
Murmushin ya'ke ta yi tana cewa, "A'a gaskiya baby."


Had'e rai ya yi sosai yana cewa, "To Gaskiya na yi fishi."
Rufaida tace, "Yi hakuri to ka fad'i wani abin da zanma sai ka hakura."


Cikin fushin Harun ya kalleta yana cewa, "Abu daya za ki mini ."
Ta sake fuskantarsa tana cewa, "ina ji."
Yace ,"To rufe idanunki."
Rufaida ta rufe idanunta tana murmushi, ba zato ba tsammani kawai taji Harun ya cafki bakinta yana tsotsa
Furgita tayi tana ture shi tare da saurin fita daga motar
shima sauri ya yi ya fito yana cewa, "Haba mene hakan kuma."
Ta kaici ya hana Rufaida cewa komai kawai yawu take tofarwa tana share bakinta


"Ai ni dama na dad'e da sanin ba sona kake ba kawai kanason lalata dani ne Harun." Ta sake tofar da yawu tana cewa, "To wallahi indai ni ce daga sama na har kasana haramun ne a gare ka, kwarton banza mahaukaci , malalaci kawai ."
Ta tofa masa sauran yawun dake bakinta tai shigewarta gida .


Share yawun ya yi yana cewa ,"Na kwafsa na yi gaggawa ,amma shi ke nan."
Ya shige motarsa ya tafi .




Ma daidaici ne mai fad'in jiki wasu sa iya kiransa da kyakykyawa, yana zaune cikin falon Alaji Idris, yana kallon yadda wannan gidan ya burgesa , bayan su gaisa da dukkan mutanen gidan ne , sai suka tashi suka bashi guri shi da Kalisa.


kallon Kalisa ya yi ya kuma yana kwarai da gaske kyakykyawa ce , "Kamar yadda dai kika sani suna na Sahid , sannan ina aiki ko ince ni ne manager company na Alaji Tasi'u mai turare."
Kalisa da zancen Sahid ya isheta ta bukaci komawa cikin gida , aiko hakan yasa Sahid komawa gidansu.


SAHID


Sahid dai d'an abokin Alji Idris, kuma Amininsa wato malam Aminu , a kwai matukar Amana a tsakaninsu ,
kuma Alaji Idris ya yi wa Sahid sanin mutumci da tarbiya, ga tsoron Allah da sanin ya kamata , hakan yasa dukkan wasu kadarori daga abin da ya shafi ,gonaki , filaye gidaje da sauransu na Alaji Idris suna karkashin kulawar Sahid , domin Alaji kallon d'an cikinsa yake masa, hakan yasa yake son ya ba shi auren Kalisa domin yana da ya'kinin zata samu farin ciki, saidai Kalisa babu wanda ta mallakawa zuciyarta sai Umar.




Anan gidan Alaji Kabiru , Zainab ce kwance a kan gadonta tana karanta littafin Hausa wato novel, hangen wayarta tai ta kawo haske , hakan ya tabbatar mata da message ne ya shigo , ta mike ta ciro wayar a caji tana kokarin ganin message d'in da ya shigo mata .






Share and comment...๐Ÿ“š








Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน

By


Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta).


_________________________________________












*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>


EditingโŒ




Page 3 & 4




Number ta gani babu suna an rubuta ,"masoyiya ya kike ? ya gida Allah yasa kina lafiya."
A zuciyarta tace to waye wannan ni dai nasan ba yaya Mahmud ba ne .
Typing ta fara tana mayar masa da cewa ,"lafiya kalau nake amma waye ."?


Harun da ganin sakonta ya zabura yana murna ya sake maida mata da cewa, "Bani da suna amma mafi yawanci ana kirana da mai kaunar Zainab."


Murmushi tasa da ganin ganin sakon nashi , kafin ta sake turawa ya turo mata cewa,"Mai kaunar Zainab da fatan rayuwa da ita har abada ".
Kawai Zainab tai a jiyar zuciya.
" Yanzu Uncle tafiya zakai."
Laila ta fad'a cikin damuwa




Uncle Yahaya ya kalleta yana cewa, "Haba Laila kwana biyu ne fa , ni dai kawai idan na dawo ina san kalamaina masu dad'i."


Laila tai murmushi, saida ya sake komawa gidansu ya sake sallama da kakarshi sannan ya tafi.


Ita kuwa Laila sai 'ku'kewa take tana had'o masa kalamai. tana cikin yin ne Khadija tazo ta warta, aiko ta bita .




Yau ma Sahid yaje gidan Alaji Idris, saidai ita Kalisa har yanzu bata jinshi a zuciyarta, kullum saidai Umar kuma ta'ki fito mana da Umar mu ganshi.




Alaji Idris yana cikin a zaune, sai ga Garba nan ya shigo Alaji ya kalleshi yana cewa, "Ahh, haba Garba sai kace ba ka garin , nan da nan baza a ringa zuumunci ba ko na yi laifine."


Garba da sauri da Girmamawa ya fara cewa, "Haba Alaji, wallahi babu abin da kai mini , kasan zaman birni , motar tawa ce ta lalace shi yasa ba a ganina har saida aka gyarata."


Alaji Idris ya had'e rai yana cewa, "Haba Garba yanzu motar taka ta lalace amma ba za ka sanar dani ba , to mene amfanin ...."


Dakatar dashi Garba ya yi yana cewa, "Haba Alaji , Yanzu ni saboda abin kunya da raashin tausayi , motar tawa ta lalace shi ne sai na jira ka gyara mini .


To mene amfanin kud'in da nake hayar da ita ."
Garba ya sake gyara zama cikin tausayi da girmama Alaji yana cewa, "Haba ! Ai wallahi bazan mance da abin da kai mini ba , ka kawoni birni ka bani sana'a ka ko ya mini zama da mutane, ka se mini..."


Alaji Idris ya dakatar dashi yana cewa, "Karna sake jin kana fad'e , to mene 'yan uwanta kar GARBA."
Garba yace ,"Gaskiya ne ."
Nan dai suka gaggaisa Garba ya koma , domin gidansa yana cikin gidan Alajin daga wajen gefen gate , ya dauko shi daga 'kauye ya ba shi mota ya ara masa gida , domin Garba da Alji Idris 'yan uwa ne , mahaifinsu d'ya wanda yanzu basu da kowa.






Ahmad ne zaune kan kujera , Zainab kuma na kwance kan 'kafar yayannata suna hira, hirarsu suke cikin kwanciyar hankali da farin ciki , ga shi kuma anata 'kwad'o sallama amma babu wanda yaji a cikinsu , saida Hajjiya Salima ta fito daga d'akin girki ta tsaya kansu cikin b'acin rai sannan suka san halin da ake ciki ,


Kafin su ce komai Hajjiya Salima ta je ta b'ud'e kofar


Yaya Aminu da Yaya Mahmud ne
Hajjiya ta dawo gabansu Ahmad tana cewa, "Kuna ji ana sallama amma kun yi shiru ."
Zainab ta tashi kan 'kafar Ahmad yayin da Ahmad yake cewa, "Wallahi momy bamu jisu ba ko kad'an."


Mahmud da ke tsaye ya kalli Zainab yana cewa, "Taya za ai kuji , kullum ba ka da aiki sai shagwa'ba wannan yarinyar."


Da sauri Ahmad ya cafe yana cewa, "Haba Mahmud kasan bani da kowa , sai ita kawai , ai dole na sota na nuna mata soyayya kafin ta barni , kuma momy ta'ki haifo wasu."
Dariya yaya Aminu yasa ya kallon Zainab


Hajjiya ce ta kalli Ahmad tana cewa, "To aku , sai kai musu shiru ai su zauna su huta ko ."




Duk dariya suka saka yayin dasu Aminu suka zauna .


Aminu da Mahmud kamar 'ya'ya suke wajen Alaji Kabiru, domin dukkansu 'ya 'yan kannensa ne da suke zaune a Kaduna, wanda Yanzu sun kawo musu ziyara ne .


Aka kawo musu kayan motsa baki masu da kyau suka ci suka sha, yayin da wata iska ke shigarsu suka fara hira.




Mahmud ne ya kalli Zainab yana cewa, "Su Zainab'yan mata."


Wani kallo ta jefa masa tana cewa, "Uhum."


Wayarta ce ta nuna mata alamar sa'ko hakan yasa ta 'bud'e wayar tana karantawa,"Dan Allah my life ki amshi soyayyar da nake miki dan Allah. "
Zainab ta mayar masa da , "Bana san zancen banza koma waye kai ka fito fili mana ."


Su kam su Aminu hirarsu kawai suke , amma Mahmud rabin hankalinshi yana wajen Zainab da ba ta sauraransu.


Harun ya dawo mata da amsa, "Idan kin shirya ina son mu had'u gobe ."
"Ina zamu had'u."
Ta tura masa .


"Gidan abincin dake bayan gidanku da karfe 11na safe."
Kawai ajiyar zuciya ta yi ta mi'ke zata shiga d'akin ta, Mahmud ne ya dakatar da ita da kiran sunanta ,"Zainab. "
Ta juyo tana kallonsa


sannan yace , "Ina son gobe da safe za ki rakani asubiti zan je wani aiki."


Tsayawa tai tana cewa, "Gobe kuma da safe."
Mahmud yace ,"Eh."
Saida ta d'anyi jimmm sannan tace ,"To Allah ya kaimu."
Ta shige cikin d'akinta .




Yau Alaji Idris shi da Hajjiya Maryam ziyara ya kai wa wani tsohon abokinsa . a hanyar dawowa ne ya kad'e wani yaro wanda yake tafe da kakarshi ,
aiko hankalin Alaji ya matukar tashi sosai , hakan yasa ya garzaya asubiti da yaron , sai dai ina rai ya yi halinsa domin yaron ya rugamu gidan Gaskiya,


Hankalin kowa ya matukar tashi sosai , aiko Alaji Idris ganin cewa wannan tsohuwa bata da gata yasa ya taho da ita gidansa , ta tabbatar musu yaron jikanta ne da iyayensa duk suka rasu , su kad'ai suke zama .


Tare da gawar yaron ya taho gidansa , anan akai masa komai aka kaisa makwancinsa.




Bayan Uncle Yahaya ya isa legos , sun yi biki , aiko suka ringa yawon bud'e ido da abokansa ,
a garin yawon ne Allah ya had'ashi da wata karuwa wacce ta manne masa .


Yanzu haka yana zaune da wani abokinshi ranshi a matukar 'bace yace , "Ni wallahi Shu'aibu zuwa na legos bai amfane ni da komai ba sai masifa."


Shu'aibu ya kalli Uncle Yahaya yana cewa, "Haba !Karka bada maza mana , kawai don yarinya ta mannema shi ne masifa , to wallahi kafin ka tafi ka amince mata kawai inba haka ba Wallahi za kai asara."


Cikin haushi Uncle Yahaya ya kalli Shu'aibu yana cewa, "Wai wannan banzar yarinyar , sanin kanka ne karuwa ce , me zan samu a gunta."


Dariya Shu'aibu ya kwashe da ita yana cewa, "Wallahi ina ma ni ne , ai ko ita ce zaka samu wani abu agunta kana ganin yarinya cikakkiya , ai wallahi dani take so tuni an wuce gun , kuma wallahi babbar karuwa ce , domin ko kud'in yaharta bani da shi."


Dogon tsaki Uncle Yahaya yaja yana cewa, "Dama dai sona take da gaske shi ne , amma kana ji fa , wai gayyatata take na kwana a d'akinta fa."


Kafin ya rufe baki ya hangota tana tahowa inda suke kawai Uncle Yahaya ya juyar da kanshi yana tsaki ,


hakan yasa Shu'aibu kallon inda take yana sakin baki , riga da wando tasa wanda suka kama jikinta sosai , tun daga nesa Shu'aibu yake jin kamar ya rungumota , bari ma lokacin data 'karaso bada ban ya daure ba da Fa'iza taji wani abu๐Ÿ˜‚.




,"Haba Yahaya, sai ne manka nake a cikin garin nan ."


Uncle Yahaya ya yi mata shiru ko kallonta bai ba , ta sake cewa, "Na yi maka girki jazo muje ."
Kallon wayarta tai dake hannunta sakamakon kiran da ya shigo, Abdul Salim , kawai ta kashe wayar tana cewa, "Da kai fa nake magana Yahaya."


Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Ke ni fa babu inda zani , baza ki ta'ba samun abin da ki ke so ba , kawai dan kinga kirjinki dam -dam shi ne za ki tunanin za ki rud'eni."
Ya sake jan dogon tsaki ya bar waje , shi kuwa Shu'aibu ya tsaya yana kallonta dama shi ne .


Fa'iza cikin ranta tace, "To wallahi matukar na cika karuwai gaske sai na jawo Yahaya jikina, mu zuba mu gani ." A'a ni ko na ce Allah ya ba mai rabo sa'a .


Uncle Yahaya a yau ya shirya ya baro legos, lokacin da dare ya yi tazo ta sami Shu'aibu, yake tabbatar mata da Uncle Yahaya ya koma Kano , aiko ta yi takaici , kawai ta amshi numbarsa ta koma.






Zainab da Mahmud ne a kan hanyarsu ta zuwa asubiti, Mah.mud ya kalli Zainab wanda duk hankalinta yake kan had'uwarsu da Harun yana cewa, "Kin san wazan dubu ."


Zainab tace, "A'a Yaya Mahmud."


Mahmud ya jawo hannunta ya ri'ke , hakan yasa Zainab tsayawa tana kallonshi , shi ma ya kalleta yana cewa, "A haka zamu taafi."


Tai ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya badan taso ba .














Sisters kar a manta comment dina a private za a ajen.










Share , like and comment.........๐Ÿ“š







Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน


By


Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta )


_________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><










Page 5&6




Shigarsu asubitin ke nan Mahmud ya saki hannun Zainab yana nuna mata guri yace ta zauna ta jirashi .


Tsayawa tai tana kallon shi , yayin dashi kuma ya shige d'akin gwajin cuta mai karya garkuwa jiki ,


Zainab hankalinta ya sake tashi ta kasa zama tanata sake-sake a ranta har Mahmud ya fito tasha gabansa da sauri tana cewa, "Wai me yake faruwa? mene ne ka yo a ciki , nifa ka fara bani tsoro ."


Mahmud ya yi murmushi yana cewa, "Babu komai kawai ki taho."
yasa kai ya fita waje yana cewa, "Harun zan kasheka."


Zainab sauri tai tasha gabansa tana cewa, "Ni gaskiya yaya ka fad'a mini abin dake faruwa."


Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Budurwata ce Maryam, ake jita-jitar tana da HIV, kuma an tabbatar mini da anan take ansar magani, a halin yanzu ina cikin mummunan yanayi, na ro'ki alfarma a bincika mini , sun ce kuma zasu kirani ."
Ya kauda kanshi yana cewa, "Harun idan tana da wannan cutar zan kasheka ." Cikin tsananin fusata ya yi maganar har saida idanunsa ya yi jah , Zainab ta kalleshi tana cewa, "Yaya kamar kana magana ko gaskiya kana cikin damuwa."


Mahmud yace ,"A'a ba komai mu tafi kawai ." Suka d'auko hanya


Bayan sun zo gida 1:25 hakan yasa Zainab ta kaici rashin samun da mar fita , kafin ta Zauna Harun ya turo mata sa'ko cewa zai zo har gidansu wani lokacin.
Bayan Mahmud ya koma bai sanar da Ahmad komai ba, a kan zan cen Harun , amma abin yana

Please Login or Register in order to submit comment