Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya wuce ya tafi, ya barta a gun , .


Zuciyar shi cikin kuna
da tunanin irin maganar data fadaa masa ya fara shirya kayanshi a jaka, babu bata lokaci ya shirya tsaf , sannan ya fita domin yin sallama da mutanen gida .




A lokacin Hajjiya tana shirya break fast , ya fito , mamaki ya cikata , haka data sanar da Alaji Kabiru, shi ma .
uzururruka ya basu sosai wanda ya kirkiro , sannan suka barshi ya tafi bayan ya karya , Ahmad ya hau mota ya rakashi zuwa.........










Abdul ne yake kwala sallama gidan Fa'iza ,
Ni ko na ce ashe yana da hankali irin haka har baya fada mata gida 😤




Suna kwance tare da Uncle Yahyah a cikin bargo , da jin sallamar Uncle yaja dogon tsaki tare da sakinta daga rungumar da ya yi mata ."Yi hakuri baby , kasan Abdul ba hankali gare shi ba bari naje. "




Ta sakko daga gadon tare da daukar kaya zata ,sa kawai ta fasa ta aje tasa wani dogon farin hijab ta fita




Yana tsaye rai a bace , yana ganin ta ya fara masifa "Ni fa tunda wannan dan uwannaki ya zo bana ganewa , me ya ke faruwa ."?






A jiyar zuciya ta yi cikin murya mai dadi tana cewa" Haba baby tun yaushe wai ya tafi ne. "


Wani dadi Abdul Salim yaji ya rufe shi tare da nuna yadda yaji dadin maganar ya fara magana , "A gaskiya Fa'iza na matsu mu yi aure , ko ba komai ki dena zama haka domin kinsan ina son ki."


Ya aje maganar yana kallon cikin idanunta.




A jiyar zuciya ta yi , kana ta fara cewa , "Na sani Abdul, amma fa banajin za a bari ka aure ni , sannan kuma...."






Yadda ya dakatar da ita da maganar ne ya sa ta yi shiru tana saurararsa
"Haba waye ya isa , ai duk fadin legos...." Shiru ya yi ,wanda a lokacin ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa ,sakamakon kiran da ya shigo masa .






Yana kara wayar a kunnen shi bai fi wasu sakanni ba , sannan ya aje cikin gaggawa yana cewa da Fa'iza "Bari na je , zan kira ki mu ci gaba da magana."




Ba tare da ya jira jin wani abu daga Fa'iza ba ya tafi


hakan ya sa Fa'iza ta koma ciki , tana shiga dakin ta cire hijab din dake jikinta, kana ta zauna bakin gado , ya yin da uncle yahaya yake zuba mata kallo , lokaci guda kuma yana kai hannu jikinta .


"Gaskiya akwai matsala." Fa'iza ta fada tana ture hannun Uncle a jikinta


"Mene kuma ."? Uncle ya yi maganar da takaicin yadda ta hana shi abin da yake yi . Ba tare da ta jira ba ta fara da cewa " Wannan gidan , gidan Abdul ne , sannan aure yake so mu yi , bansan mene zan yi ba ."




Had'e rai ya yi Uncle yana cewa "Aure kuma da wannan. To ni kuma fa."?


" Nima shi ne abin dake damuna ai , ya zan yi."?
Fa'iza ta fada tana kallon uncle




"Fa'iza sanin kan ki ne bani da kud'i , bani da gida ke ce kike ciyar dani. Amma wallahi ko kin auri wannan Abdul din , to har gida zan na biyo ki . Gara ma karki fara kisa Allah ya konamu."




Dariya Fa'iza ta kwashe da ita tana cewa, "Kana nufin yanzu kai Allah ba zai kona ka ba Yahaya , ka sabawa Allah ba mace daya ka nema ba fa."






"Ki bar Wannan maganar, ai Allah mai gafara ne, kawai ki fada masa ni zaki aura in sha Allah ba zan baki kunya ba ."




Fa'iza ta kalli Uncle yahaya tana cewa " Kar fa wallahi ka ci amanata Yahaya."


Ta'be baki ya yi Sannan ya ce "Ni da ke mutu karaba Fa'iza."


Ya jawota jikinshi lokacin da ya gama maganar.




Yadda Fa'iza taji dadin yanayin ya sa ta fara cewa "Amma kasan kana da HIV ko."




Rassss . Abin da Uncle ya ji ke nan a zuciyar shi , ya cireta a jikinsa yana cewa "Amma wasa ki ke koh."?






Tintsirewa ta yi tana muguwar dariya lokaci guda kuma cikin dariyar ta fara magana


" Sannu san banza , ka yi irin Wannan shanawar sannan ka tsira ko. To wallahi cutar HIV ta wajen shekara biyu , kuma ko matan kano din ma da kaje gunsu ai suna da ita . Kawai ka shirya muje asubiti asan matsayin taka , shi ne kawai ."


Cikin dariya ta karasa maganar.




Tashi tsaye ya yi cikin tashin hankali yana kallon Fa'iza "Fa'iza bana san irin wannan wasan wallahi, ki dena har duniya ta tashi babu ni ba wannan cutar."




Ganin yadda Fa'iza ta lura dashi dari bisa dari bai yadda yana da Hiv ba ta tashi tsaye.




"Haba dan Allah sai ka ce wani yaro , HIV ai ruwan dare ce , to wallahi kana da ita sannu dan san banza."




Cikin tsaki da harara ta aje maganar, tare da juya masa baya tana zama bakin gadon .




Timmmmm, abin da taji ke nan wanda hankalinta ya bata fad'uwa ce .




Cikin sauri ta juyo , ai kuwa sai ga Uncle Yahaya a kasa kamar matacce .






Da firgici ta yi kanshi tana jijjigashi tana kiran sunan shi .




Yadda ta ga alamun kamar ya mutu ne ya sa ta tashi , ta sanya kaya riga da wando , sannan tasa hijab ta fita neman taimako.








Koda ta fita babu kowa a wajen , domin anguwa ce bata mutane ba , sa 'a ta ci Allah ya kawo wani mai napep sannan ta kira shi , suka dauki uncle suka tafi asubiti.



Tare da dukkan tashin hankali, Fa'iza domin tunaninta Uncle Yahaya ya mutu kawai , to idan Uncle ya mutu Allah ya jikanshi , dama kowa na haka ne.






A halin yanzu Likitoci suna kan Kalisa domin tunda garin Allah ya waye suma basu samu damar ganinta ba , abin dai ba a cewa komai .
Baba Garba ya musu waya cewa ya taho da million biyu , yana hanya, haka suma akwai wasu kudaden da suka samu daga al'uma .




Bayan likitocin sun fito tare da dukkan tashin hankali su Umar suka tambayi jikinta nata. Yadda doctor ta tabbatar musu ba mutuwa tai ba wani sashi daga zuciyar su ya yi fari .




"To zamu iya shiga gurinta."?


Nabila ta tambayi Aisha likita " Me zai hana. "


Ta bata amsa , hakan ya sa suka shige baki dayansu .




Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa dactor Aisha, tana sharewa amma sun ki dena kwararowa


"Da kun san matakin jiwonta , duk wannan kwarin gwiwar ba za ku same shi ba , ta ya zan fara fada muku wannan bayan kun kasa fitar da ita."


Aisha ta karasa maganar tana dena kallon kofar dakin Kalisa tare da tafiya tana share hawaye.




Cuta ba mutuwa ba ce .








Share and comment..........................📚














Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)








No editing




_________________________________________


Page 33 & 34




Ba yadda Fa'iza ta iya da Uncle, gida suka dawo bayan likita ya tabbatar mata da ciwon barin jiki ne ya kamashi wato paralysis.


Ta shiga rudani tun a asubitin, bata da kudin jinyarshi ya sa ta dawo gida , wani abin takaicin da yake damunta tun a asubiti ya fara bata aiki , domin wata gudawa da yake yi abin ba a magana , haka bayan ta dawo gida bai fasa ba , amma likita ya bata magunguna duk da haka abin bai lafa ba , yau ta sha bacin rai .










Ido ta zuba musu tana kowanne su, yadda abin ya basu mamaki rabon da manyan idanunta su bude irin haka tun tana da lafiya


"Kalisa ki daure ki ci abinci yaufa kwana biyu baki ci komai ba." Baba anje ta yi maganar tana rike hannun Kalisa.






"Ku yi hakuri, na wahalar daku." Kalisa ta fada da kyer


"Sahid ya ci amanar dady ."
Kalisa ta kuma fada


"Yi hakuri Kalisa da Wannan maganar, baba garba ya taho da kud'i yana hanya."
Kalisa ta yi murmushi


Umar ne ya ce "Dan ma yau juma'a ne da tuni ya karaso."




Yadda Kalisa take wani mike mike ya sa duk hankalinsu ya tashi


Da sauri Nabila ta kira Aisha, koda aka kirata kawai a jikinta ta ji Kalisa mutuwa za tai


tana karasowa tare da wasu nurse aka fara buga mata iska


tana haki Kalisa tana wahala tana jan wani numfashi tana mikewa


wata doguwar ajiyar zuciya taja , sannan tai shiru , hakan ya sa suka dena buga mata iskar


Doctor Aisha ta cire dukkan masu machine da aka sanyawa Kalisa.




Yana yin yadda suka ga tashin hankali a fuskar dactor ya sa duk suka tsure .


babu wanda ya iya tambaya wanne hali ne Kalisa ke ciki , duk da taja malullubi ta rufe fuskarta ,sai da doctor Aisha ta juyo ta kallesu tare da girgiza musu kai , wanda hakan yake tabbatar musu babu ranta .




"Me ki ke nufi ne."? Umar ya sha gabanta yana tambaya a bisa yanayin rashin ganewa


" Ku yi hakuri, ta rugamu gidan gaskiya. "🙊




Aisha ta fada cikin matukar tausayi tare da fita , waje , fitar ta ke nan Garba ya shigo cikin daki ya ci karo da gawar Kalisa.






Kacokan din su suka rufe ta , abin yana dukansu ,


Nabila ta bude fuskar Kalisa, " Haba dan Allah aunty Kalisa, ke ma kin san a'a ne , mutuwarki tashi kawai."


Cikin matukar zautuwa Nabila take jawo Kalisa domin ta tashi .






Ganin haka ya sa Jafar ya fara janyeta ta karfi yana kuka .


A wannan lokacin Umar Allah ne kawai yasan zuciyar shi , domin kawai wasu hawaye ne suke zubo masa yayin da ya kafa mata idanu.




Baba anje kawai sunan Allah take kira jikinta na rawa kamar mai shirin zaucewa .


Allah sarki Garba tun da ya yi burki , ya yi mutuwar tsaye ya rungume jakar kud'in da ya zo da ita .


"Haka Allah ya kadarto , amma Sahid tabbas ka cutar damu."


Umar yake yin maganar lokacin da hawaye suke zuba jikin malullubin da aka rufe Kalisa


"Shi ke nan . Kin barni Kalisa, kin tafi inda ba a dawowa."


Ya sake fashewa da kuka yana zube gwiwowinsa a kasa cikin karyayyar zuciya.




A Wannan lokacin Nabila ta fad'a jikin Kalisa
"Haba dan Allah, Haba dan Allah."


Tana ta kuka mai gwanin ban tausayin gaske.




"Baba ya kamata mu tafi kawai." Jafar tare da dukkan rauni ya kalli Garba ya yi maganar.


innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un


Kowa na haka ne daman sannan mutuwa dole ce ga kowa , kawai kowa da hanyar ajalinsa .
Mu dai muna addu'a ya Allah👐 ka kashe mu bisa hanya ta addini, ka jikanmu taji tausanmu ya Allah.








Haka suka koma gida ,wanda duk kafin su isa an sanarwa da kowa , domin da zarar wani yaji labarin zai kira ya sanar da wani .Haka suma mutanen kauye , abin ya girgiza su sosai .




"'Yar uwata ce fa ita , da farko momy da dady yanzu kuma ita , ban yi tunanin shiga irin wannan yanayi ba , wannan shi ne Guba mafi girma da bazan mance ba a Rayuwata har ranar da Allah zai dauki raina . Allah ya jikanku aunty ku yafe mini."


Maganar Nabila ke nan yayin da aka aka fito da gawar Kalisa za a tafi




"Nabila ki yi hakuri kina yin salatin annabi, addu'a kawai Kalisa ke so yanzu." Cewar wata baba Ramma da ta zo daga kauye .




Nabila dai ba a magana, saima lokacin da aka isa makabarta ,


Jafar da Umar 😭
Abin dai sai mazan wajen da suka gani😭




Allah ya sa mu dace






A bangaren Fa'iza kuwa a halin yanzu rayuwata kawai wahala take sha kullum cikin bacin rai da masifa take wa Uncle , fitowar ta daga toilet ke nan ta nufo daki




tana shigo wa ta toshe hanci cikin bacin rai tana kallon uncle tana cewa "Haba dan Allah, wannan, wanne irin wulakanci ne , na ce maka duk sanda kaji kashi kana mini magana, amma sai kana yi a kwance kamar wani yaro , to wallahi na gaji , na gaji da wannan masifar gaskiya mwtss."




Ta fita cikin bacin rai ta barshi a dakin






A jiyar zuciya ya yi yana daga kwance ya fara cewa "Rayuwata ke nan , kasan farkon ka baka san karshe ba , wallahi alhakin Laila Adam ne wannan, alhakin ta ne , in banda haka saurayi kamar ni Yahaya da wannan cutar , Allah ka bani ikon cinye ta ."
Kun ji fa uncle, sai yanzu yasan haka .
Ita Laila ma a halin yanzu tana makaranta, domin Allah ya bata lafiya .








Fa'iza na daga tsakar gida tana tunanin yadda za tai da Uncle ta fara jin sallama.


Ranta sake baci ya yi da jin hakan , ba tare da ta yafa komai ba ta fita rai turbine .








Koda Abdul ya ganta haka , sai ya tambaya ko lafiya


"Ka ga dan Allah mene ya kawo ka Abdul kana bani matsala fa."




Ta yi maganar da dukkan d'aga murya tare da fushi
mamaki ya rufe Abdul da jin haka


"Mene kuma haka ni ne fa Abdul Salim naki , mai shirin zama angonki fa."




Fa'iza ta kalleshi da takaici tana cewa "Allah ya sauwake wallahi, ni ba auren ka zan yi ba , ai ba hauka nake ba mwtss."




Matukar mamaki ne ya rufe Abdul , yasan Fa'iza ba za ta masa haka ba , hakan ya sa ya maida abin wasa yana cewa "Haba Fa'iza na , a dena wasa mana ."




Wata muguwar harara ta buga masa tana cewa "Wasa kuma , aikin banza , ai wallahi banga abin aura a gun ka ba gara ma ka sani."




"Okay haka kika ce."?
Abdul ya fad'a






Fa'iza ta ce " Haka kaji , kuma haka na fad'a."




Ya ce "Okay shi ke nan ."


Ya kama hanya ya tafi , yayin data samu damar shiga gida








Tana shiga gida taci karo da wayarta ta gama ruri sakamakon kiran wata kawarta , wacce take son ta da Abdul wato Zuby wacce tun tuni ta yi aure ta tuba .




"Gayyar hauka." Fa'iza ta fad'a yayin da taga ita ce ta kira.






















Harun ne tsaye kofar gidan malam na lado , wato anguwarsu Zainab ke nan


yana tsaye yana jiran fitowar Maryam, a yadda yake yatsine fuska zaka gane cewa almajiran dake kofar gidan suke karatu sun dame shi , lokaci guda kuma yana iya saurara duba ga malam na lado yana cikin gida .








Lokacin da Maryam ta sako kai zata fito ya zuba mata idanu kamar kullum , Allah ne yasan karatun kurma , amma zuciyar Harun cike take da sha'awar Maryam

tana karasowa kusa da motar shi ya fara tsarata kamar kullum yana shiryata , Allah ma ya sani Maryam ta kamu da son shi , domin tun da aka masa iya ka da Zainab ya dawo wajenta ka'in dana 'in




"Gaskiya nifa ina shan kalamai shi ya sa kullum kake sake shiga zuciya ta ." Cikin murya mai dadi Maryam ta yi maganar.




"To baby naji , amma yaushe zamu je ki gaida momy , domin kullum maganar ki take fa, Gaskiya ya kamata ki shirya na kaiki ."




Ya karasa maganar yana mata wani shegen kallo, lokaci guda kuma yana sauraran jin amsarta."
























Share and comment.....................................📚













Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta)








No editing




_____________________________________




Page 35 & 36




Kafin Maryam ta kai ga bude baki ta yi magana malam na lado ya fito da babbar riga da hula tare da allo da carbi .


Ganin Maryam da Harun tsaye ya nufi wajensu ,
Harun ya yi saurin kai wa kasa yana gash she shi , bayan sun gaisa yana daga kasa


Malam ya fara cewa "Kai ka sanar da iyayenka a zo anema maka aurenta , bana san wasa ."




Harun ya ce "To baba in sha Allah zan sanar dasu yau ma kuwa."


Malam na lado ya nufi wajen almajiransa ya zauna .




Sannan Harun ya tashi yana ajiyar zuciya yana cewa "To kin ji ba , sai ki shirya kin kusa zama amarya."


Ya yi maganar yana yatsine fuska , kunya ce ta rufe Maryam da jin hakan




"To kinga gaskiya naji dadin jin wanna maganar ta baba , don haka gobe ki shirya zan zo mu tafi shop domin ina son faranta miki baby ."








Maryam ta ce "A gaskiya zan fi kowa farin ciki Allah ya kai mu."......






Yau ne aka gudanar da addu'ar bakwai ta Kalisa


Duk sun matukar jin jiki wallahi, sun rame kowannensu rashin ne yana matukar taba su , ba a gama nasu Alaji Idris ba , Kalisa ma ta zo ta tafi .


To babu yadda aka iya dama kowa na haka ne .


Har aka gabatar da addu'ar 40 babu abin da ya canza domin mutuwa mummunan tabo ce , wannan lamarin ya zame musu Gubar Rayuwa babu yadda suka iya.








Wani mahaukacin bugun kofa Fa'iza taji ana mata , lokaci guda kuma ana cewa " Kina ina mara mutunci."


A yadda taji tabbas ba mutum daya ba ne , ba kuma ta shaida murya ba


duk tabi ta rude tana tunanin ita dai batai fad'a da kowa ba , bare a zo kamata , tana yin wannan tunanin ta saka hijab ta fita .




Koda ta fita ajiyar zuciya ta yi ganin Abdul ne da abokanshi


"Haba dan Allah mene haka." Ta yi maganar tana kallon Abdul da fuskarshi babu wani annuri .




Ragowar cigari din dake hannunsa ya jefar tare da take ta , kana yana wasa da makulli da kwadon gida , wanda da gani sabo ne da ke hannunshi yana cewa "Ki tattara kayanki , zamanki ya kare , ki shiga na baki minti biyu ."




Wani rass Fa'iza taji a ranta "Haba Abdul lafiya kuma."?






Abdul ya kalli abokanshi yana cewa " Ku shiga jiki , domin idan ita ta shiga zata bata mana lokaci, duk ku yo wurgi da kayanta ."






Cikin masifa Fa'iza ta fara cewa "Haba Abdul wannan ai cin mutunci ne ."


Ba tare da ya saurareta ba ya fara cewa "Duk abin dake cikin gidannan ni na siya , dan haka abin da nasan bani na siya ba , daga akwatinta sai bahon wanka , da tukunya , ku shiga ku fito mata dasu."






Babu wata-wata suka shige gidan domin aikatawa


Zuciyar Fa'iza kamar ta fashe ta kasa motsi ta kasa cewa komai, tana tsaye taji an wurgo mata takalmi,wanda sai da ya sameta a goshi taji zafi


wani takalmi ne mai tsini ruwan zuma ta kalli takalmin ta kau da kai , yayin da tana kau da kai idanunta suka kai inda aka wurgo mata tukunya da soson wanka da baho.




Bayan su gama fito mata da kayan suka tsaya carko carko kamar masu shirin dukanta




"Ya ka ce mi mata shegen duka mana." Wani a cikinsu ya fada yana kallon Abdul.




Abdul ya ce "A'a ku barta kawai , domin duk abin dana ba ta na karba , dama taimakonta zan na aura , tana karuwa waya san cutukan dake jikinta .Ai yanzu na gane Allah ya yaye mini wahala."




Fa'iza duk ta rasa inda yake mata dadi ta kasa cewa komai




Abdul ya mika musu wannan kwadon gidan yana cewa "Rufe min gidana mu tafi."




"Kai Abdul akwai wani gardi fa a gidan kamar bacci yake ma." Wani a gefenshi ya yi maganar yana nuna gidan






Abdul da ranshi ya yi matukar baci ya kallesu yana cewa "To uban me ya sa bai fito ba ku koroshi tunda ba gidanshi ba ne ."




Kamar suna rige -rige suka fada Cikin gidan kai tsaye sukai dakin




Uncle duk yabi ya tsure ganinsu a kanshi "Ba yin Allah lafiya ."


Uncle ya yi maganar yana kallonsu daga kwance


"Tashi ka fita dan uwarka , kwarto kawai . Ita ma kwartuwar taka mun am she gidan mu."




Haka Uncle taji an fada , ba tare da ya gane wane ya yi maganar ba .




"Dan Allah ku yi hakuri, wallahi cutar barin jiki gare ni bana iya tashi."




Ba tare da sun ce komai ba suka dauko shi su su hudu , biyu sun rike hannaye , biyu sun rike kafafu .




Haka suka fito suka wurgo Uncle waje


"Kan uban can dama har yau wannan yana nan , to Allah ya kuma tonaki ."


Abdul ya karasa maganar yana kallon Uncle da yaji wurgi yana kwance a kasa




Suka rufe gidan suka hau mota sukai tafiyarsu .




Cikin mummunan takaici Fa'iza ta fara tattara kayan da aka watso mata , waje guda ta had'a su tana kallon tare da tunanin sauran kayan dake ciki, a cikin ranta ta lissafa yadda zata dauki kayan a hannunta ba tare dasun mata yawa ba .




A lokacin kuma hankalinta ya kai ga uncle yahaya da yake zararar da hawaye .
Wanda sa'ilin ta kuma kula da yadda gari ke rugugi sakamakon had'owar hadari .


Had'e rai ta yi tana kallon Uncle tare da matsawa kusa dashi tana cewa "Ni zan tafi , domin babu inda nake dashi bare na je dakai ."


Cikin tashin hankali Uncle yahaya ya zaro idanunsa ya fara magana a yanayin wahala.
"Ya za ai ki barni a nan Fa'iza, ga hadari , ina zan sa kaina , ban zata zaki mini haka ba."




Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce ,"Ka so gaskiya mana Yahaya ina ne zan kai ka , dama kowa yana da kaddarar shi , to ka dauki wannan matsayin abin da ba za ka ta'ba mancewa ba , shi ne Gubar Rayuwarka."




Tana gama magana ta juya da sauri tana kwashe kayanta , sakamakon tsawa da iska da aka fara.




Ba tare da ta ko kalli Yahaya ba tasa kai cikin sauri ta fara tafiya, sakin baki ya yi yana kallonta cikin mamaki ganin cewa da gaske fa tafiya ta yi ta barshi .


Wasu hawaye ne suka zubo masa yayin da ya fara ba za idanu da nufin neman wani ya taimake shi , amma babu wanda ya gani sai wani yaro dake gudu a keke sakamakon yayyafin da aka fara .




"Yanzu ya zan yi , wallahi da nasan abin da zai faru ke nan bazan zo legos ba , basu da mutunci yanzu sai su kone ni a gun nan ." Uncle cikin kuka ya sauke maganar yayin da aka tsuge da ruwan sama .Domin ko ita Fa'iza kafin taje inda zata wannan ruwan ya dake ta , bare Uncle naku dake guri daya.








Yau tun da gari ya waye Maryam take murna da fitar da zasi da Harun , mahaifiyar ta kawai ta sanar wa da wannan labarin , domin ta san malam na lado mahaifinta idan ya ji bazai yadda da wannan shirme ba ,




A tsakanin uwa da 'yah haka sukai maganar su , nan ta ba ta goyon baya tare da umarnin karta jima har Mlm ya tambaye ta.






Doya da kwai take soyawa , daga gefe kuma kana iya hangar wani kunu na gero wanda yasha kayan kamshi.


"Wai Nabila har yanzu ba a gama girki ba yunwa fa nake ji nasan ita ma Baba haka ."


Jafar ya shigo madafa yana wa Nabila maganar cikin mita ,




"Hmmm ." Kawai abin da Nabila ta iya fad'a ke nan


Jafar ba tare da hakan ya dameshi ba ya sake cewa "Kin san dai yau ne Yaya Umar ya ce zai kawo 'kannenshi ko , to ki musu girki dan Allah."




Ta kalleshi tana cewa, "Ban fa mance ba Yaya Jafar."


Ya karaso yana daukar doyar da zummar d'and'anawa.








Bayan Harun ya iso
ba 'ba ta lokaci Maryam ta fita suka tafi


"Ya kamata mu biya ki gaida momy na fa." Harun ya yi maganar yana kallon Maryam


Cikin shagwa'ba Maryam ta kalleshi tana cewa.










Share , like and comment......................📚










Gubar Rayuwata⚡🌹

By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)





Editing❌


________________________________________




Page 37 & 38






"Amma gaskiya ba za mu dad'e ba."


Harun wani dad'i yaji ya rufe shi dajin amincewarta , hakan ya sa ya ce ,"Haba sarauniyata yadda ki ke so ai haka za ai besty na." Cikin 'kwarewa da farin ciki ya cigaba da tuki ya nufi

Please Login or Register in order to submit comment