Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan da yake kiran gidansu.


Wani gida ne babba suka shiga , Harun yana mata kalamai masu kwantar da zuciya har suka shiga cikin falo.




Maryam dakatawa tai cakk , sakamakon duhun da ta gani a cikin falon , saida Harun ya kunna haske sannan ta ji hankalinta ya kwanta .


"Duk kin wani furgita zauna mana baby bari shaf-shaf na shiga ciki na kira momy."
Harun ya yi maganar yana shige wa ciki.






Nabila kam tasha aiki sosai ta yi girke girke , duk saboda 'kannen Umar da zasu kawo musu ziyara .




Wajen minti biyar Harun ya yi bai fito daga dakin ba ,


Hakan ya sa Maryam ta yi shiru tana sa'ke-sa'ke cikin zuciyar ta


ba ta gama tunanin abin da ya rike su a ciki ba , sai ga Harun ya shigo jikinshi duk a mace ."Mene kuma ya faru."?


Maryam ta yi maganar tare da tashi tsaye


"Ina shiga ciki, na ga momy kwance wallahi hawan jininta ya tashi."
Inji Harun


"Subhanallahi." Maryam ta fad'a




"Amma karki damu , ki shiga ciki ki kula da ita dan Allah, ki kula min da mahaifiyata zan kira likita."


Da sauri Maryam ta fad'a dakin cikin tausayin Harun.






Duhu ta kuma gani cikin dakin , amma ba tare da ta nemi inda glove yake ba , ta nufi gadon wanda tana iya ganin mutum a kudundune a kai.
"Mama , Mama." Tana ta'ba mahaifiyar Harun tana kiran sunanta .




Wani tashin hankali ne ya bigi zuciyar Maryam tare da tsoro , sakamakon yadda taji tulin kayan Harun ne a kan gadon ba wai mahaifiyar shi ba ce .


Da firgici ta tashi tana shirin fitowa taji an rike ta.

"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Maryam ta fad'a sa'ilin da take da tabbacin Harun ne a gabanta



Dauuuuuu ya kunna glove din dakin yayin da yake rike da hannunta yana dariya.


A yadda mamaki ya kasheta ne ya sa ta kasa cewa komai, zuciyar ta tamkar ta fito musamman jin yadda ya fara magana.



"Kin ga yadda shiri na ya yi koh. Ga ki gare ni yau Maryam zaki ga irin san da nake muki , babu kowa a gidan nan daga ni sai ke yawan."
Ya karasa maganar yana fincike mayafin dake jikinta .






"Inna'ilaihir wa inna'ilaihir raji'un Harun , kaji tsoron Allah, na roke ka karka rabani da mutunci na , dan Allah." Cikin matukar kuka da firgici Maryam ta yi magana.






Dariya ya yi yana cewa ,"Haba Maryam, karki zama yarinya mana , wallahi tun lokacin da nake zuwa wajenki Wannan ranar nake jira , ban samu Zainab ba , domin na so mu shiga irin wannan yanayin da ita ,amma shegen yayan ta Mahmud ya hana."....




"Dan Allah Harun kar ka cutar dani, wallahi bazan jure ba."


Ya tunkud'eta ta fad'a kan gadon , haka har mai faruwa ta faru .
Sannan Harun yaji dadin rayuwar shi .










Bayansu su Umar sun shigo suka zauna a falo nan suka fara hira dasu Jafar da baba anje


Ya yin da Nabila ta fito daga wanka tana shiryawa.


Da siririyar murya kanwar Umar Salma , wacce take kusa da yayanta Nasir ta ce ,"Wai ina Nabilan ne to."?






Jafar ya ce ,"Ta na zuwa yanzu. "






Nabila ta karaso cikin falon sanye da wata doguwar riga abaya , wacce taji ado ga launi mai matukar kyau.




Tun daga 'bullowarta Nasir ya kasa jire idanunshi a kanta , har ta karaso ta zauna


"Ya ya Umar har kun zo."? Nabila ta yi maganar da Umar yayin da kuma ta ke kallon Nasir da Salma




" Kanwata mun iso, yau dai ga salma nan." Ya yi maganar yana nunawa Nabila kanwar shi .


Murmushi Nabila ta yi tana cewa, "Eh yayana ka cika alkawari kuma naji dadi."




Nasir ne ya 'ba ta rai yana kallon Umar da cewa ,"Haba Yaya Umar to ni ba za a gabatar dani ba."




Jin hakan ya sa kowa ya kalleshi suna masa Murmushi.


Umar tsaki ya yi yana cewa, "Nabila wannan matumburin kanina ne sunan shi Nasir."


"Haba Yaya Umar matumburi kuma." Nasir yayi maganar yana kallon shi .




Dariya suka kwashe da ita baki dayansu har da Umar yayin da ya ce ,"Ai Nasir din ne ya cika zance wallahi. "






Nasir ya kalli Nabila yana cewa ,"Baki gabatar mana da kanki ba sister. "




Cikin haushi Umar ya Had'e rai yana cewa, "Kun ji ba , baka ji an ce Nabila sunanta ba ,banan surutu bama kasan mene za ka na tambaya ba."


Dariya suka kuma yi wacce tafi ta d'azu , har ita Nabilan ya yin da Nasir yake kallon yadda dariya take mata kyau.




Sannan ta tashi ta nufi dakin girki domin kawo musu abinci , Nasir harda lekenta .






Lomar farko ta Nasir ya ce ,"Gaskiya Nabila kin iya girki sosai , sai ka ce a Australia. "




Wata harara Umar ya watsa masa tare da cewa ,"Su Australian girki suka iya? dan Allah ka yi hakuri ka yi shiru haba."


Dariya suka sake yi a karo na ba adadi
haka suka gama cin abincin cikin farin ciki da walwala .




Bayan su kammala suka tashi tafiya, nan ne Nasir ya karbi number Nabila sannan suka yi sallama. Sun matukar jin dadin wannan ziyara baki dayansu."














Fa'iza a gidan kawarta ta samu guri , inda ta tabbatar wa da kawarta zuwa gobe zata koma garinsu .




Tana tsakar gida a zaune ta yi tagumi , a lokacin ne wannan kawarta ta ta fito daga daki .




yadda ta ga Fa'iza ta yi tagumi tana kallon taurarin dake sama ya sa
kawarta cewa ,"Haba Fa'iza lafiya , kin zauna a farin wata kuma kina kallon sama ."




Fa'iza ta yi ajiyar zuciya tare da cire hannu daga tagumin da ta yi
"Ki dena damun kanki fa dan Allah." Cewar kawarta






Ajiyar zuciya Fa'iza ta kuma yi tana cewa, "A kwai abin da ban fad'a miki ba kawata, kuma nasan yanzu duk wannan ruwan saman da akai ga dare yana kwance a wajen nan."






"Topha waye ke nan." Cewar kawarta




Fa'iza ta fara bata labarin halin da Uncle yahaya yake ciki da kuma yadda ta baro shi .




"To yanzu ya kike so a yi masa Fa'iza, ki rabu dashi kawai , idan ya mutu Allah ya jikanshi , kema shawara nake baki tun kina da lokaci ki tuba wallahi, domin ya zama izina gare ki ga yadda Yahayan nan ya samu kanshi , ki manta da komai ki koma ga Allah domin shi mai gafara ne , kuma ba damuwarki ba ce idan Yahaya ya mutu , nan zasu sa wuta su kona shi , idan kuma yana raye to rayuwa ce zai gani ya more duk yadda Allah ya yi daidai ne ."


Yanayin zazzakar muryarta ya sa Fa'iza ta gamsu da zancen kawartata .






Fa'iza ta ce ,"Haka ne kawata , in sha Allah bana komawa karuwanci domin gobe ma yobe zan koma, Allah ya yafe mana. "




Kawarta ta ce ,"Yawwa Fa'iza ki je kawai ki kwanta saida safe. " Fa'iza ta shige dakinta ta rufo ta kwanta .


















Washe Gari


Hauwa ce zaune tana karyawa a lokacin mahaifin ta lu'utanal ya shigo


"Dady har yau baka samu time ba ni gaskiya yau zanje na ga Surayya."


Kai tsaye Hauwa ta yi maganar




Murmushi ya yi yana cewa, "Ehh gaskiya ne , ban samu lokacin ba kije abinki ki gaida mini da ambassador."




"Thanks dady."




Maryam babu wanda ta sanarwa da abin da ya faru , gashi tana cikin halin rashin lafiya , tun da Harun ya samu abin da yake so bai kuma waiwayarta ba , Allah sarki.
Tuni ya barta har ya samu wata , wacce yake da irin wannan nufi a gunta , amma abun da yake ba shi tsoro yadda babanta yake babban mutum ambassador,


Amma sai ya samu salama da ya yi tunanin ya ta'ba'yar malami ma ya zauna lafiya, bare yaran manya da suke chilling suke shoshalewa tabbas cikin sauki zai samu abin da yake so .














Umar ne bayan ya amsa wata waya da akai kiranshi ya tashi da sauri ya fita , a karshe gudu yasa kamar mai shirin tashi sama , yana sake nanata sakon da aka isar masa cikin wayar .


Jafar da Nabila ne zaune , sai baba anje , bayan sun gama karyawa
"Gaba na fad'uwa yake Yaya Jafar." Nabila ta yi maganar cikin damuwa.












Share and comment...................📚














Gubar Rayuwata⚡🌹
By

Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)




Editing❌




_________________________________________


Page 39 & 40












Jafar ya kalli kanwar tashi yana cewa," nima haka Nabila, tun jiya da daddare ma kuwa."

Baba anje ta ce ,"Tofa! Ikon Allah, Allah ya sa alheri ne yake tunkaro mu."


Kafin su kai ga cewa Amin suka Umar kamar an wantsiloshi ya shigo yana haki idanunsa sun yi jajir , ga dukkan alamu akwai damuwa.




Duk tashi tsaye su kai kafin kowa ya ce komai yana ta sake saken abin da ya shigar da Umar wannan hali .




"Tantancewar sojin da akai babu shi ne ? Amma hakan ba zai tada hankalin Umar ba ." Jafar yake fada cikin zuciyar shi .






"Bai zo ba."??? Umar ya yi musu tambayar cikin tsananin jiran amsa .




Kallon juna suka yi alamun samm basu gane mene yake nufi ba .






Jafar ya karasa kusa dashi da cewa ," Kwantar da hankalin ka Umar, mene yake faruwa ne ."






Daga can wajen gidan kuwa wani saurayi ne mai jiki wanda ya ginu ya wadatu da farar fata, ya nufo gidan yana d'ingisawa , yayin da yake tafiya cikin isa yana tattare farar jallabiyar dake jikinshi .






"Sahid nake magana akai domin ya dawo Nigeria a daren jiya , kuma duk inda yake zanje na nemo shi." Umar ya fada tare da matukar nuna kiyayyar Sahid a zahiri








Duk wani tashin hankali suka ji ya sake bugar musu zuciya da kiran sunan maci amanarsu


"Assalamu alaikum."




Sautin sallamar da suka ji ke nan wacce ta daskarar dasu a tsaye


Tabbas yau idanunsu sun ga abin mamaki domin kuwa Sahid ne tsaye a gabansu , yayi wani kyau dashi yayi kiba .






Wasu zafafan hawaye suka zubo wa Nabila masu matukar ciwo






Umar ya kasa cewa komai domin zuciyar shi tana ayyana masa mummunan abu a kan Sahid, hakan ya sa yake 'kokarin sarrafa kanshi






"SAHID".


Jafar ya kira sunan shi




," Na'am Jafar, na sani cewa bani da bakin magana a gabanku , amma ba a son raina komai ya faru ba , na yi tafiya Britannia, jiya da na dawo nake jin labarin mutuwar Kalisa. "




'Kuummmm
Wani wawan duka da Umar ya kai masa , ya fadi ya bige da bango, Umar ya taso shi cikin tsananin takaici ya cigaba da dukanshi .




"Me nai maka ne , haka , mutuwar Kalisa ai haka Allah ya tsaro me ya sa za ka doran laifi."


Cewar Sahid ke nan yayin da Umar yake bibbige shi .




"Jafar ka yi masa magana mana ya dena dukana , ina ciwon kafa."




Jafar ya nufi bayan Umar ya ture Umar ya amshi Sahid.


Yadda Sahid ya ganshi a tsaye ya fara ajiyar zuciya da samun 'yancin da ya yi .




Ba tare da ya ankara Jafar ya kwarfe shi ya fadi ya bugu da bango, ya taso shi ya ma'kure shi kana ya fara magana.


"Burinka ya cika ba , Kalisa ta rasu , kuma ka zaune dukiyarmu."


Gummmm


Ya bugashi jikin wani karfe , sai jini .






"Jafar ku bari karku kashe shi mana , ya jigata sosai." Baba anje ta yi maganar tana kokarin kwace Sahid a hannun Jafar.




Jafar bai san lokacin da ya ture baba anje ba , Allah ya sa bafa fadi ba , ya kalleta cikin takaici da tarin hawayen dake idanunshi , yana cewa.






"Shin baki tuna lokacin da Kalisa take kwance ba ? ko kin manta sanda muka tashi aka yi garkuwa da Nabila, kin mance ranar da Kalisa tai Allah wadai dashi , mu bamu jigata ba ne baba ? ko kuwa bamu ga tashin hankali ba ."




Ya aje maganar cikin wasu zafafan hawaye da suka zubo masa , sannan ya maida kallon shi ga Sahid yana cewa, "Kai azzalumi ne mayaudari ka kashe Kalisa ka kashe mahaifin ka ."






Ya tun kude shi gefe


Sahid yana jiri ya ya tashi ya nemi hanyar fita ya hau mota ya tafi .Kai tsaye masaukinshi ya nufa wato hotel ya gyara jikinsa ya sauya kaya, kana yasha magani.






Kwanciya ya yi da nufin hutawa sai maganar Jafar take fado masa tana masa amsa kuwa .
"Kai azzalumi ne mayaudari ka kashe Kalisa ka kashe mahaifin ka."








Ya yi ajiyar zuciya ya tashi zaune, ya dauki mukullin motar shi da kafar shi mara lafiya da taji duka ya nufi gidan nasu .






Zuciyoyin su jafar tafasa suke yi matukar gaske, hakan ya sa suka fita domin daukar matakin da ya dace a kan Sahid.








Hauwa ce cikin wani babban falo suna hira da kawarta surayya




Hauwa ta zubawa Surayya idanu tana cewa, "Allah koh , ki ce sabon saurayi kika yi , shi kuma Faruk din fa."




Surayya ta kalli Hauwa tare da jefa mata wata harara tana cewa, "Shi fa soja ne, kuma wallahi ya kwanta mini a rai domin gaye ne Hauwa."






Hauwa ta ta'be baki tare da tashi tsaye tana cewa, "Kin ga ni tafiya zan yi , har akwai wani gaye da zai kuma shiga zuciyar ki bayan Faruk, wallahi kin bani kunya."




Surayya cikin dariya da zolaya ita ma ta ta shi tsaye tana cewa, "Wallahi duk sanda ya zo san had'aku ku gaisa besty ta."




"Mtwss." Hauwa ta ja tsaki tare ta bud'e kofar falon .




Lokacin ne wani farin mutum lukuti mai sanye da farar shadda ya turo kai , ba kowa ba ne kuwa fa ce ambassador.




Nan Hauwa ta gaidashi har yake tambayar mahaifin ta , nan take sanar masa yana gaida shi,
shima ambassador ya sake aika masa da sakon gaisuwa.


Haka Hauwa ta dawo gida.........














Anan bangaren su Zainab kuwa


Suna zaune a falo ita da yayan nata Ahmad, laptop ce a gabanshi yana dannawa




Zainab ta ce ,"Yaya Ahmad dan Allah ka yi hakuri ka bawa daddy hakuri, ka amson wayata, wallahi na tuba na canza."






Ahmad ya kalleta ya ta'be baki ya ci gaba da aikinsa






"Haba yayana Ahmad, wallahi na tuba ka kula ni mana , har abada babu ni ba HARUN."






Tsaki Ahmad yaja yana wurga mata harara "Dan Allah ki barni na yi aikina , ki bari ki kuma hankali da kanshi Dady zai baki."




Wayar Ahmad ce ta fara ruri , yana ganin mai kira ya dauka cikin farin ciki.






A yadda Zainab ta ga yayan nata yana waya tasan cewa Mahmud ne .


hakan ya sa yana gama wayar ta titsiye shi da tambaya, "Wa ne Yaya."?






Ahmad cikin farin ciki da washe baki ya ce ," Wallahi Mahmud ne , yana sanar min ya samu aiki a matatar mai ta kasa, abin ya farantan rai ."






Zainab ta yi murmushi tana cewa, "To yaushe zai zo."?




Ahmad ya jefa mata wani kallo yana cewa," To sannu , ke da ganin Mahmud sai Allah, sai dai ke ki shirya kije."


Ya cigaba da aikinshi




Duk atake Zainab ta shiga damuwa .










Bayan ya yi burkin motar shi a kofar gidansu, ya fito da kyer ya shiga cikin gidan .






"Assalamu alaikum."


Sahid ya yi sallamar a cikin gidan , wanda bai ga komai ba sai tabar ma a tsakar gidan , sallama ya sake yi a karo na biyu babu amsa .




Yanayin yadda yaji karshi shi na masa zugi da zafi ya sa ya nufi tabarmar da shirin zama




"Kar ka sake ka zauna mini a gida mugu azzalumi."


Cewar mahaifiyar shi data fito daga daki ,
a lokacin ne shima Jibril ya fito daga wanka .






Tsololo Sahid ya yi da baki yana kallan mahaifiyar shi dajin wannan furuci da ta yi masa




"Ka gaggauta fita a cikin gidan nan Sahid."
Ta kuma fada cikin kunci




Sahid ya daure ya ce ,"Mama da gaske ne baba ya rasu."?




Jibril dai bai ce komai kawai yana sauraransu




"Sahid ni mahaifiyar ka Binta , babu abin da zance maka tsakanina da kai , abu guda dana sani ka ci amana, kuma tana tafe domin cinka , ka je za ka gani."




Tana gama magana ta shige daki , Jibril ma ya shige dakinshi ya sanya kaya ya fita , yana fita ya ci karo da 'yan sanda tare da Umar da Jafar .






Kafin su yi masa tambayar ina Sahid, Sahid ya fito suka sashi a mota suka tafi .














Share and comment...............................📚












Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)





Editing❌




_________________________________________




Page 41 & 42


Hankalin Harun duk yabi ya tashi
ganin yadda wasu abokanshi da dama an turo musu sakon ni da yake tabbatar zasu tafi training amma shi Harun bai ga wannan sako ba ko tuntuba, hakan ya sa yake bibiyar inda matsalar take .






Anan ma Umar Allah ya ba shi sa'a sai dai ba ya so ya tafi training ba tare da yaga yadda kotu za tai ga Sahid ba ,


sai dai jafar ya tabbatar masa babu abin da zai gagare shi , tun da suna da kwararran lauya , ga kuma baba GARBA shi ma ya zo.




Haka dai Umar ya hakura ya tafi kaduna ba tare da ya so ba.


Maryam ce ta fito da gudu daga daki tana sheka amai , tana gama amai ta malale a wajen tana shure-shure .




Haka cikin gaggawa mahaifiyar ta , ta kira malam na lado suka tafi asubiti.






Yadda alakar Harun da surayya take , lokacin da yake sanar da ita matsalar da ya samu , har an tafi training babu shi , ya roki surayya alfarma data mika takardunshi ga mahaifin ta ambassador, domin ya yi magana da lu'utanal a kan shi.




Haka kuwa aka yi surayya ta karba , domin a halin yanzu ma takardun suna hannun mahaifin ta , amma har yau bai samu damar magana da lu utanal ba .




Allah sarki Maryam, lamarin dai har yanzu babu dadi , malam na lado da babarta sun shiga damuwa , haka dai dactor ya sa akai mata gwaje-gwaje , daga bisani ta samu bacci




Lokacin dasu Hajjiya, matar Alaji Kabiru da zainab suka zo dubata , har suka dawo bata farka ba, Zainab dai ta ji tausayin kawartata tana kuma mata fatan samun lafiya..






Fitowar ambassador ke nan daga gidansu Surayya,
ya hau mota rike da wasu takardu a hannunshi, sannan driver ya ja mota suka tafi .


Ambassador sake kallon wannan takardun na hannunshi ya ke yi , lokaci guda kuma yana sake mamakin yadda saurayin 'yar tashi Harun ya zama mai irin wannan mummunan hali da lu'utanal ya sanar masa.




Wanda lokaci guda yana sake tuna maganar da tafi tsaya masa a rai , da lu'utanal ya fada kamar haka .




"Lokacin da Hauwa ta zo min da zancen, sai da muka bibiyi rayuwar shi , muka tabbatar da zargin da ake masa sannan muka hana shi wannan dama , irin Harun mummunan tashin hankali ne zamansu cikin al'uma, kuma bugu da kari mu kara ba su gwarin gwiwa tare da basu aiki irin na soja , ambassador hakan ba mai faruwa ba ne."






Ambassador ya yi ajiyar zuciya bayan tunanin da ya gama .




Har suka isa cikin gida, ambassador jefi jefi abin yana damunshi , daga karshe yana shiga cikin gidan ya zauna a falo




Yadda matarshi ta ganshi haka , ya sa ta fara tambayar ko lafiya, nan take ya sa ta kira masa surayya.






Bayan surayya ta zo ya mika mata takardun Harun yana cewa




"Ki maza ki kira wannan yaron ki ba shi , kar na sake jin komai daga gare shi , hatta mu'amalar ku na wargaza ta."






Dauuu ta ji gabanta ya fadi
"Rabuwa da Harun kuma yanzu." Surayya ta fad'a a cikin ranta


ta kalli ambassador tana cewa cikin harshen turanci , "Dady me ya sa kuma ? Me yake faruwa."?





Nan take ambassador ya sanar wa da Surayya komai , da irin binciken da lu'utanal sukai a kan shi , har suka haram ta masa aikin soja."





Surayya ta yi matukar mamaki da jin hakan , abin ya matukar d'aure mata kai.


Tashi ta yi ta shiga daki da nufin kiran Harun ,

Amma sai ta fasa , ta kira Hauwa ta ce ta zo tana ji ranta.


Bayan Hauwa ta Harun Surayya ta sanar mata halin da take ciki , nan Hauwa ta sake tabbatar mata da waye Harun, ta tabbatar mata yaudara ce ta kawo shi, babu yadda Surayya ta iya ,



Ta kalli Hauwa tana cewa, "To yanzu mene abin yi Hauwa."


Hauwa ta ce , "Ki kira shi ya zo."





Ko awa daya Harun bai 'ba ta ba ya karaso


Ya shigo yayi parking da motar shi , sannan ya dauki waya ya kira Surayya.








"Ya zo."


Surayya ta yi maganar sa'ilin da ta kashe wayar tana kallon Hauwa.


Hauwa ta ce , "Ta shi mu je."




Surayya ta kwashi takardun suka fita .




Tun da ya hango su ya fara washe baki domin a lissafinsa
Surayya zata gabatar masa da kawarta ne , ya sa suka taho tare .






Suna karasowa Surayya ta sake had'e ranta , ammo sam Harun bai lura da hakan ba, domin yadda ya ga kawartata Hauwa zazzafa ya sa hankalin shi ya koma kanta yana kallonta sama da kasa.




Yadda Surayya ta lura da hakan ya sa ta sake jin tsanarshi ta kuma yadda da abin da aka fada mata.






Lokaci guda ya maida kallon shi ga Surayya yana cewa
"Annurin Rayuwata, barka da fitowa."






Tasssssss Ya ji saukar mari a fuskarshi
Da gigicewa da tsananin jin zafin marin da mamaki ya kalli Surayya , hannun shi dafe a kuncinsa .






Cikin turanci Surayya ta fara magana, "Kalle ni da kyau mayaudari, azzalumi ,na tsaneka Harun ."




Ta d'ago hannunta na hagu da ta rike takardun ta watsa masa


Sannan da yaren Hausa ta cigaba da cewa , "Sai ka kwashe su , kuma kai da aikin soja har abada. Allah ya mana tsari da kai yi waje ."






"Haba Surayya waya shiga tsakaninmu haka , ban yi muki komai ba , amma...."


Kafin ya karasa maganar ta sake shara masa mari tana cewa, "Matukar baka fita a gidan nan ba ka sake magana sai na sa an kulle ka."




Harun matukar mamaki ya rufe shi ya kasa gane dalili, idan ma shi mayaudari ne ta ya ta sani. Abin ya d'aure masa kai sosai.




Ya durkusa ya d'ebi takardunsa ya shiga mota ya tafi .




Surayya ta yi ajiyar zuciya tana kallon Hauwa.










Malam na lado yana Cikin tashin hankali , jikin Maryam babu kyau , gida suka koma sakamakon tabbatarwar likita cewa Maryam

Please Login or Register in order to submit comment