Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gida ba sai ga shi ta kwana kuma har karfe 9 shiru."


Baba anje ke nan






Jafar ya ce "Ai na yi zaton ma anan ta kwana domin jiya banganta ba ."


Darammm a zuciyar Kalisa da Baba anje


Kowa shiru ya yi yana sake-sake cikin ranshi , Jafar ya ciro wayarsa a aljihu ya ya nufi numbar Nabila domin kira,
wayar ko shiga ba tai ba balle ya sa ran jinta




Jin sallama duk ya sa hankalinsu ya koma kofar shigowa




"Assalamu alaikum".


Suka amsa sallamar tare da wani yanayi a cikin furkarsu


Baba garba ne ya shigo , shi ma yadda ya gansu ne ya sashi tambaya


" Ya haka , ko lafiya na ganku haka."? Ya karasa maganar ya na zuzzura musu idanu,


"Nabila ce ba a ganta ba."


Jafar ya ba shi amsa


"Subhanallahi kamar ya kuma Jafar."?


Tun kafin Baba Garba ya yi magana , Umar ya shigo yana tambaya


Duk shiru sukai kawai suna jin abin a ransu,




" Bata kwana a gidan ba ne ko ya". ?
Baba Garba ya yi maganar yayin da ya katse musu sake -saken su."




A wannan karon ma dai Jafar ne ya fara magana "Ni wallahi ban sani ba , jiya na gaji hakan ya sa ina shiga gida na kwanta."






"Kuma ba ta makota."? Baba anje ta jefawa Jafar tambaya




Jafar cikin takaicin yadda kowa shi yake tuhuma ya fara cewa " Ba mu tabbatar ba kawai mu fita mu duba." Ya karasa maganar tare da fita bai jira kowa ba .






A jiyar zuciya Kalisa tai , ba tare da ta ce komai ba
amma kana iya hangar tashin hankalinta a furkarta .




Bayan Uncle Yahaya ya sauka a legos, yabi wannan adireshi na Fa'iza ,wato inda gidanta yake , babu jan lokaci ya sami gidan


"Assalamu alaikum."


Uncle Yahaya ya yi sallamar a gidan Fa'iza tare da takatsan-tsan din kamar ba gidan ba ne , ba tare da ya kuma sallama ba ya ringa duban gidan yana lekawa




Jin muryarta ne ya tabbatar masa tabbas ya zo gidan masoyiya


"Haba baby, ni daya ce fa a gidan , daga ni sai kai , sannu da zuwa."


Ta karasa maganar yayin data aje buta tare da jan bandakin data fito .




Ajiyar zuciyar farin ciki ya yi yana gyarawa jakar kafadarsa zama yana cewa "Ga kyakykyawata farin cikina yau a gabana."




Wani irin kallo Fa'iza tai masa tare da kashe ido , lokaci guda kuma tana kai hannu tana karbar jakar tashi."




Suka nufi daki suna shiga dakin wayarta ta fara ruri , tabbas tasan Abdul ne , hakan ya sa bata bi ta kanta ba ,
shi ma Yahaya ko tayin daukar kiran bai mata ba , domin ga dukkan alamu bai ma jiba , saboda wani shegen kallo da yake binta dashi .




To ga dai Uncle Yahaya a lagos


Ko ta ina zai fara , kuma ya zai rayu
Ga kuma bangaren Kalisa, har yanzu babu labarin Nabila, da Sahid, ga ciwonta kullum abin tafiya yake , ko Kalisa zata sami lafiya?




Ga kuma bangaren Zainab da Mahmud, ga mutumin ku Harun .




Tofa duk ba za mu ji yadda abin zai kasance ba ,sai mun had'u a








A tare da ni Fatima Abdallaah kano
Wato Auta ga marubuta






Mu had'u a kashi na biyu karku mance fa ๐Ÿ‘‡




Share and comment..................................๐Ÿ“š






Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน
By
Fatima Abdallaah kano
. (Autar marubuta)


______________________________________






*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>






Page 27 & 28






Duk hankalinsu ya gama tashi matukar gaske, har magariba ta yi amma babu labarin Nabila , da tananan sun tabbatar yanzu Kalisa tana India, amma duk inda ya dace a duba kuma a tambaya an yi , sai dai babu wani cigaba.


Allah ya kawo sauki da mafita , haka rayuwar take, kowa da kalar tashi kaddarar.




Washe gari


Jibril ne zaune kusa da mahaifiyar shi yana rarrashinta , tun da garin Allah ya waye take kuka
Cikin tausayin mahaifiyar tashi Jibril ya ce "Babata dan Allah ki jure wannan jarabawar , wallahi komai mai wucewa ne ."






Cikin rashin gwarin gwiwa ya karasa maganar
Cikin kuka tana face majina tana gogewa da zaninta ta ce "Wallahi Jibril kaninka ya yi asara duniya d lahira , domin ba zan yafe masa, ya je indai duniya ce , wanda ba su zo ba ma jiransu take , sai ta sashi kukan da babu hankicin da zai share masa."๐Ÿ˜ญ


Ta kuma fashewa da kuka


Jibril duk ya kasa cewa komai domin zuciyar shi shi daya yasan zugin da take masa .






Kasar waje




Sahid ne ya fito daga asubitin kashi yana dingishi , guri ya samu ya zauna
iska mai dadin gaske ce ke kai wa tana dawowa , ga duk kan alamu yana jin dadinta fiye da su mazauna kasar


Lokaci guda kuma ya hade rai yana magana shi daya , yayin da ya hango wani gurgu bisa keke ana turashi


" Allah ka raba mu da wannan masifar kawai a yankewa mutum kafarsa ,
wannan asubitin za su min komai ba sai na koma Nigeria ba , Allah sarki babata da na ce ciwo zata daukon magani ,
ni da na koma Nigeria sai na yi aure na haihu da baturiya ,daga nan ma Pakistan zan wuce."
Ya aje maganar yana kallon ambulance din da suka shigo asubitin.






A d'azu jikin Kalisa ya rikice sosai da sosai , nan hankalinsu ya tashi
sun yi kokarin fitar da ita , amma Kalisa ta ce bazata bar kasar nan ba ba tare da tasan halin da kanwarta ke ciki ba .


Duk da an sanar da 'yan sanda amma har yanzu ba ta sauya zani ba




Fitar kannen Umar ke nan daga asubitin , su biyu mace dana miji
macen tana kuka da wannan yanayi data gansu a ciki. To ya za ai da lamarin ubangiji






Umar ya matukar ramewa sosai , su baba anje ma ba a cewa komai ga su Jafar da Garba , abin dai sai wanda ya gani.




Jingum suka yi duk din su a dakin


wayar Jafar da take ruri ne kawai ya sa ake jin wani sauti


da kasala ya cirota a aljihunsa tare d amsa kiran yana karawa a kunne .


Koda jin wata kakkausar murya ce ke magana hakan ya sa ya tashi tsaye , yayin da duk hankulansu suka dawo wajenshi


Da alamar magana da kai Umar yake tambaya ko lafiya, hakan ya sa Jafar ya sata a sautin da kowa kan iya jin abin da ake cewa


"Na ce kai ne Jafar."
Aka fad'a cikin muryar rashin girmamawa, cikin faduwar gaba Jafar ya amsa da shi ne



Aka ci gaba da magana kamar haka "To wallahi mu harkar mu babu karanta , da zarar mun baka lokaci ba kai amfani da shi ba komai na faruwa, mu ne muka dauke kanwarka , kud'in fansa muke so , idan kuma ka shigo da 'yan sanda cikin kasuwancin mu to ku shirya jana'izarta."


Yana gama maganar ya kashe wayar








Tare da dukkan tashin hankali da matukar hanzari duk suka tashi , su baba anje da Garba tare da salati suna kiran sunan Allah suka tashi .




Kalisa ma kana iya hangen mummunan tashin hankali a kan idanunta, cikin tsananin ciwo da fargaba tare da tashin hankali gami da juriya ta fara magana.


"Mun shiga uku Jafar , ka dubi rayuwar data riskemu a bayansu momy, Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un."


Ta karasa maganar cikin ciwo tana Ajiyar zuciya tare da hawaye .




Yadda Umar ya kalli masoyiyarshi Kalisa duk wani tausayin ta ya kama shi , duk da bata da lafiya sannan ga baba anje ga Garba, amma tana daukar lamarin 'yan uwanta a kanta .Matsawa ya yi kusa da ita a sa'ilin da yake jin kamar ya sa hannu ya goge hawayen dake gangaro mata kana ya rungumeta ya rarrasheta .




Amma ina duk ya kasa ma cewa da ita komai ya juya ya fita.








Tun da lamarin ya faru babu wanda ya yi wani yunkuri , domin yadda Kalisa ta damu da lamarin Nabila duk abin sai ya sake d'aga musu hankali.






Babu inda kowa ya motsa har dare ya yi , idan ka ga wani a cikinsu ya fita ,to bai wuce ya nuna damuwar shi a waje ba , sannan ya dawo , domin duk dakon kiran kidnappers din suke .




Ai kuwa wajen karfe goman dare , sai ga wata sabuwar number ana kiran Jafar, hakan ya sa duk suka mayar da hankali ga kiran, sannan Garba ya ce ya saka a speaker.




"Kana jina." Ha kan da aka fad'a ya tabbatar musu muryar wannan azzalumin ce ta d'azu


Cikin rawar murya Jafar ya ce "Ina jin ka."


"Zuwa gobe na baku, da karfe 4 na yamma, idan baku amsheta ba , zamu hada ta cikin masu bakuntar lahira gobe , Million 3 za ku aiko."


Ya kashe wayar daga can bangaren .




"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un, yanzu ya zami , kud'in aikin Kalisa ne kawai damu bayan fafutukar da akai aka had'a su , ina zamu sa kanmu ๐Ÿ˜ญ
Yanzu da Sahid ya bamu kud'i ko million dari ce ai ba wahala za tai fa."


Baba anje ta yi maganar tana rushewa da kuka .




"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Garba ya fad'a yana samun guri ya zauna


Cikin rawar murya tare da fargabar abubuwan da suke faruwa Jafar ya ce "Dole a fitar da Kalisa baba Garba, tun da wannan kudin...."




Kalisa ce ta dakatar da Jafar cikin ciwo tana cewa "Babu inda zani sai Nabila ta dawo , dukkan abin da aka tara dan zuwa neman lafiya ta ,a halin yanzu Nabila ce mabukaci , ita jini na ce ,dan haka kawai ku karbota Jafar." Ta aje maganar tana wani irin nishi .




Baba anje kuka ta sake fashewa dashi tana neman taimakon Allah.
Baba Garba ma ya kasa cewa komai ,










KANO






Mahmud ne a zaune a falo kamar kullum, cikin zuciyar shi ya fara tunanin ya kamata ya koma gida, domin wani abokin sa ya tabbatar masa aikin da suka nema koyaushe za a iya kiransu .


Zainab ce dake kwas kwas kwas da takalmi ta dawo dashi cikin hayyacinsa .ko kallon inda yake bata yi ba ta wuce ta gabanshi .


Ganin suturar dake jikinta ya tabbatar masa fita za tai
zama ya gyara yayin da ta kai bakin kofa tana kokarin budewa ya ce "Ina zuwa."?




Wani zafin takaici ta ji a ranta " Zan je gidansu wata ne , kuma momy ta sani , ba sai ka tuhume ni ba."


Duk jikin Mahmud wani iri ya masa domin ya tabbatar Zainab ba gaskiya ta fad'a masa ba , wajen Harun zata ,haka zuciyar shi ta ba shi.




"A dawo lafiya". Abin da ya fada ke nan ya koma ya yi lakaf kamar ya saduda .






Hakan ya sa Zainab ta fita








Zumbur ya yi ya tashi kamar wanda aka tsikara ya zura wayarshi a aljihu ya fita ya bi bayanta.








Yana binta a baya- a baya har tasha kwana ta nufi bayan gidansu , wanda hakan ya tabbatar wa da Mahmud abin da yake tunani, tana tsallaka titi ya ga ta doshi wani babban gidan abinci da hutawa mai suna Shuwa Love , mamaki ne ya sake rufe shi ya ci gaba da binta , wanda harta shiga ciki bata san yana bibiyarta ba .














Sahun kujera number ta goma sha bakwai ta hangi Harun yana zaune yana jiranta, hakan ya sa ta nufi wajen shi cikin farin ciki.




" Ohh Zainab! Wajen wannan wawan kika sake zuwa ya Allah. " Ya yi maganar cikin tsananin haushi da bacin rai .




Daga inda yake labe yake hangosu ya kalli hagu da damar sa , sannan ya nufi inda suke




Zainab wani yarrrr take ji duba da yadda Harun yake kallonta kamar mai shirin fada mata kah yana daga zaune






"Masoyi wannan wanne irin kallo ne."?


Zainab ta tambayi Harun cikin ya'ke tare da murmushi wanda lokaci guda zaka gane duk hankalinta bai kwanta da kallon ba .








Ajiyar zuciya ya yi yana kokarin fara magana , sai dai kafin ya kai ga cewa komai




Mahmud ya tsaya 'kyem a kansu rike da kugunsa








Duk mikewa tsaye sukai suna kallonshi , ba tare da ya bari wani a cikinsu ya ce komai ba , ya fara magana "Sannu ku, ashe nan kika taho."




Tare da duk bacin rai Zainab ta fara magana"Wato bibiya ta kake , amma wallahi ka bani kunya , wannan wacce irin. "..




" Shiru mara kunya." Mahmud ya fada cikin zafi da hassala, ni yayanki ne , amma ni kike fadawa wannan maganganun , saboda duk kin ga na zama wani zato .








Rashin hankalinki ya wuce tunanina , kwakwalwarki ta dena aiki , kin zabi mutumin da yake da burin kashe ni ."






Sauri Harun ya yi ya tari numfashin Mahmud, wanda a wannan lokaci duk mutanen dake zaune a wajen hankalinsu yana wajensu suna ji da kallon hayaniyar tasu .


"Ta ya zan kashe ka Mahmud, ai ko ba komai kai abokina ne kuma yayan Zainab, ka dena min kazafi dan baka so na ." Ya yi maganar cikin muryar tausayi da marairaicewa .










Hakan ne ya matukar hassala Mahmud, cikin fusata ya yi sauri ya daki kirjin Harun da hannu biyunsa , wanda sai da ya kai kasa


har kasan rigarshi ya yage , sakamakon kujerar da ya bige ta rike shi .








"Nasan duk abin da kike dan bamu sanar da dady ba ne , kuma wallahi yau sai ya san komai." Mahmud ya fada yana nuna Zainab da yatsa


"ka fada mana, ko tsoron hakan nake ka dameni ka ishi Rayuwata, kai azzalumi ne mara tausayi."






Wani saukar mari da taji a fuskarta ya sa tai shiru ta rike gurin , tana kallon Mahmud da mamakin ya mare ta .




Kafin ta ce komai taji muryar Harun yana cewa "Security ga shi nan."
Yana nunawa security na kula da gidan Mahmud.




Suka sashi gaba domin ya fita a gurin , kawai kallon Harun ya yi , ya wuce ya fita .












Share and comment...............................๐Ÿ“š












Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)








No editing
_______________________________________


*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>










Page 29 & 30










Cikin mummunan 'bacin rai Mahmud ya fito , duk ya rasa mene yake masa dadi , kawai ya nufi gida kanshi tsaye , har ya isa gida yanayin shi bai canza ba , yana shiga falo ya ci karo da Alaji Kabiru shi da Ahmad suna zaune.




Yanayin yadda ya musu sallama a ciki ya sa suka tambayi mene yake faruwa .






Bai boyewa Alaji komai ba , haka shi ma Ahmad ya sake bada tabbacin abin da Mahmud ya fada .




Cikin bacin rai Alaji Kabiru ya kallesu yana cewa "Mutanen banza ku tashi Ku bani guri , duk kunsan da wannan baku fada mini ba saida abin ya kai haka ."


Ya karasa maganar lokacin da Hajjiya ta shigo ,
"A yi hakuri dady , mun yi zaton zata gyara ne ." Mahmud ya bada hakuri.


"Zaku bani guri ko sai na ci mutuncinku ."
Suka tashi ya yin da kafin su fita suna iya jin karashen maganar tasa
"Ta zo ta same ni , ina nan ina zaman jiranta ."...






LEGOS


Abokan Abdul Salim ne a d'akinshi suna ta shaye shayensu da bushe bushe .
Wani daga cikin su da ba ya iya magana sai ya karkata baki ya ce " Kai Abdul yarinyar nan taka fa , naji an ce ta aje kato a gidanta ."


Abdul na kokarin jan shisha ya ce "Ai na sani dan uwanta ne , ta fada mini komai."


"Kai dama baka da kishi ai koda yake ita karuwa ina ruwanta koma waye." Mari ya ji an d'auke shi dashi , yayin da duk abokan suka razana .


"Kar ka kuma kiran matar da zan aura karuwa, da yau a ce Fa'iza ba za ta aure ni ba , sai na wulakantata , amma tana sona, kar na sake ji ."


Kowa yasha jinin jikinshi, su abokanshi sun sani sarai ba sanshi take ba , amma sun bari duniya ta fada masa domin ba zai yadda dasu ba .




Uncle Yahaya dai asara ta tabbata , ba shi da abin yi , hatta kudin kashewa Fa'iza ke ba shi amma a haka suna shirin yin aure , ba tare da Abdul ya sani ba ,
Mu je zuwa Fa'iza zancen duniya ba ya buya.




ABUJA




Har yanzu sai dai saukin Allah, jikinta babu dadi Nabila ce rike da ita tana tsala kukan bakin ciki "Aunty Kalisa wallahi lafiyarki tafi komai a kan mene zaki bari a karbo ni , bayan bama da wasu kudaden , ke ce damuwarmu , amma yanzu bamu da wata dama." Rurutaccen kuka suke yi baki da yansu, sai dai abin da basu sani sani ba a halin yanzu Kalisa bata iya magana.




Tsanani ya kai ya wuce tunaninsu , ita kanta dactor Aisha tana mamakin yadda Kalisa ta kai har yanzu a raye, bayan tsananin da matakin da ciwonta ya haura.


"Likita , Likita likita ." Jafar da Nabila suka fita da gudu suna kiran dactor, wasu nurse ne su biyu suka shigo sukayi kan ita Kalisa data sassan kare , Umar ganin bai gamsu da nurse dinta ba fita neman doctor Aisha


da gaggawa Aisha ta taho gurin Kalisa, ya yin da taci karo da wannan nurse din su biyu , nan take suka ja baya suka bata guri .






"Baba Yaya Kalisa mutuwa za tai." Nabila ta yi maganar tana rushewa da kuka , baba anje bata iya cewa komai ba , domin a yadda take kallon Kalisa yanzu ita ma ta cire rai , domin a halin yanzu numfashi ya gagara ,


cikin kokari da sanin aiki na dactor Aisha aka sawa Kalisa oxygen machine
, wanda daga nan ne aka samu sauki ta koma kamar matacciya .




"A gaskiya ku dauketa ku koma gida , tunda har yau fitar da ita ya gagara , nasan halin da kuke ciki , amma hakan ba yana nufin ku zuba idanu ba , domin taya Allah kiyo yafi Allah na nan , ciwonta ya wuce duk yadda kuke tunani , musamman ma cancer dake kafarta wacce take cigaba da yawo."
Doctor Aisha ta yi maganar tana kallon kowanne a cikin su .






Ba tare data jira wani ya ce komai ba ta fita yayin da wannan nurses din suma suka fita da fatan samun lafiya .








Baba Garba ya kalli , baba anje yana cewa "Gaskiya ne wannan, duk abin da yake faruwa daga Allah ne , ya kamata mu tashi zuwa jibi a fitar da Kalisa a samo mata lafiya."


Baba anje dai ta kasa cewa komai, sai wani ajiyar zuciya da ta yi mai cike da fargaba tana kallon Kalisa.


"Zan je na sayar da gadon gidanmu , amma ba wani kud'i ba ne mai yawa." Umar ya yi maganar yana kallon Baba Garba




Baba Garba ya mayar masa da cewa "Ni ma yau zan tafi kauye, zan tattaro duk abin kadara ta da kiyo , a siyar dasu in sha Allah." Ya mike yana cewa


"Bari na tafi ba a bori da sanyin jiki , zan kuma tun-tu'bi duk mutanen kirki cikin 'yan uwa zasi wani abun."


Ya aje maganar lokacin da yakai kofar fita nan sukai masa sallama da fatan alheri






ajiyar zuciya Jafar ya yi tare da kallon can gefe guda idanunsa kamar zai yi kuka, sallamar da aka shigo ana yi ne ya sa ya dawo da kallon sa bakin kofa




"Ahh Jibril kai ne." Cewar Umar


Jibril ya gaida baba anje ,Wanda nan suma suka sami damar yi masa ta'aziyya








ya kalli Kalisa dake kwance da oxygen idanu a rufe yana cewa "Allah ya bata lafiya dan annabi."






Duk tare suka amsa da amin , wanda ya kalli Nabila yana sake cewa "Sannu ke ma Nabila, haka Allah yake kudurarsa , amma da wannan azzalumin Sahid ya bada kud'i n nan ai na tabbatar komai zai zo da sauki."


"Haka ne ." Jafar ya fada a takaice yana kallon Kalisa yayarshi wacce bata san inda kanta yake ba kwana guda babu abinci.






A lokacin Jibril ya kalli Jafar lokaci guda yana had'a kallo da baba anje yana cewa "Sahid jinin mu ne babu yadda muka iya , kuma bamu da bakin ba ku hakuri ku dauki duk matakin da ya dace dashi."




Ya ciro wasu
makudan kudade daga jikinshi yana ajiyewa gaban baba anje yana cewa "Wannan ku had'a ayi amfani dashi wajen lafiyarta amma babu yawa."


"Allah sarki, Allah ya saka muku da alheri." Baba anje ke nan




Jafar ya kai ido kan kudaden wanda kallo guda ya musu ya gane dubu dari biyu ne, Sannan shi ma ya mika godiya, shi ma Umar haka .........






Haka har wajen dare Kalisa jiki babu dadi , su ma Umar da Jafar a wannan dare suna ta kokarin samo wannan kud'i, haka bangaren baba garba kowa yana ta kokarin sa .










๐ŸŒนRayawa da kashewa duk na Allah ne, kuma duk yadda ya yi babu mai tuhuma , amma muna yiwa Kalisa fatan samun lafiya ta dawo kamar yadda take dah.๐ŸŒน














Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)




No editing

__ _____________________________________



*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>





Page 31 & 32







A wannan daren Zainab ta ci matukar kuka , duk ranta babu dadi , domin Alaji Kabiru ya matukar taka mata burki ya mata abin da yake mata ciwo , babban abin da yake mata ciwo take yawan tunawa wai ita dady yau , ya mara ya kuma kirata da sha sha sha,









bugu da kari ya amshi wayarta duk saboda Mahmud, sannan aka yabi Mahmud , abin yana mata ciwo ta ci kuka har gari ya waye .






Da safiya ta yi , ta fito cikin lambun gidan nasu ko taji wani saukin ,
yadda ta ga Mahmud yana motsa jiki cikin lambun tare da kwanciyar hankali ya sa ta ji duk ta kuma tsanar shi.







"Hankalin ka ya kwanta ." Ta yi maganar lokacin data sha gabanshi




Mahmud dakatawa ya yi yana fuskantarta, wanda wannan lokacin ne da ya dubi idanunta ya san taci matukar kuka, amma ba tare da ya bayyana mata ya gane ba ya fara cewa "Eh kam na ji dadi , tun da yanzu bakya cikin hadari irin na Harun." Ya karasa maganar yana korawa da ruwan jarkar dake hannunshi .








Wata sabuwar 'kufula Zainab ttaa sake yi da jin hakan "Ka rabani da farin cikina , kasa dady ya mareni , kasa yayana Ahmad ya dena kulani , wallahi kai masifa ne , dan Allah ka koma garin ku kai ma ka yi rayuwarka haba ." Cikin bacin rai Zainab ta karasa maganar






Mutuwar tsaye ya yi shi kuwa Mahmud, mamaki ya cikashi da jin wannan zance na Zainab,


komai yaji ya sire masa , wai shi ne masifa


"Zainab na yi miki gata .Amma sam ba za ki gane hakan ba yanzu, ni yayanki ne , ko ba komai ban can can ci wannan kalaman naki ba ." Bai jira komai daga gareta ba , domin shi ma ba iya abin dake bakinsa ba ke nan , amma

Please Login or Register in order to submit comment