Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisuwar kakarshi , yake ba shi labarin yadda yake fantamawa da karuwai , Allah ya sa mu dace










Yau Laila tana cikin farin ciki ta yi wa Uncle Yahaya kalamai wanda ba ta taba masa ba , ta tabbatar wa kanta Uncle zai sakko daga yajin da ya yi mata , hakan ya sa ta tafi makaranta cikin kwarin gwiwa.





Cikin zumudinta ta aikawa da uncle wannan wasika mai matukar dadi da kwantar da hankali
har Khadija na tsokanarta yau uncle zai susuce
dariya laila ta yi tana cewa, "Zuciyata tare data Uncle take bugawa da zarar ya barni to zata tarwatse."


Dariya Khadija tai mata tana cewa, "An fa kusa tashi ga shi Uncle bai kiraki ba."


A lokacin ta ji karar kararrawar makaranta, Laila ta 'bata rai tana cewa, "Aikin banza , wai ina Uncle ya shiga."


Khadija tashi tai ta dauki Jakarta tana cewa, "Wallahi ba zan jiraki ba, indai sai kin tsaya wajen shi ."


Laila ganin Khadija zata tafi ta barta ya sa ta fasa ganin Uncle ba dan taso ba ,






Cikin matukar bacin rai Uncle ya koma gida
"Wannan yarinyar ni zata wani rubuta wa kalamai , to ni yanzu har akwai yarinyar da zan tsaya ina soyayya da ita , Allah ya kaimu gobe , zata gane kuskurenta kuwa , ga mata nan wacce nake so ita zan samu , zan yi maganinki."


Kiran wayar Fa'iza ne ya sa ya sarara da maganar ya dauki kiran.




Har dare ya yi Laila da matukar shaukin Uncle ta kwanta
A washe gari da safe ta shirya cikin uniform din makaranta ta tafi


Sakamakon yau talata d'alubai suna ta mamaki da aka ce su fito assembly, shi kan shi shugabร n makaranta duk sun fito da sauran malamai


haka Laila ta ringa amfani da wannan damar tana hango Uncle Yahaya tana kallonshi tana jin dadi .Sai dai shi Ko ta tata ba ya yi , sai dai ma idan ka kula kana iya ganin tsantsar rashin mutunci a idanunsa .


A lokacin Uncle Yahaya ya fara magana cikin muryarsa mai dadi ga kunnen Laila.
"A yau cikin wannan makaranta."
Uncle ya fara magana yana kallon malamai da d'alubai .




Washhh Allah na kuna sa ina dena typing da rashin like d comments wallahi๐Ÿ™


Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน
By


Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)



*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>






Page 17&18









"Akwai wata sabuwar d'abi'a da d'alubai suka shigo da ita , wanda hakan yana jawo raini da lalacewar tarbiya, to gaskiya ba za mu yadda da wannan abin ba , kuma zamu fara hukunci a yau ga irin wannan d'alubai."








Wani fad'uwar gaba Khadija ta ji ya bugar mata zuciya, ta kalli Laila , amma ita Laila sam babu wannan yanayin a tare da ita




"Mene Uncle ya ke nufi."?
Khadija ta tambayi kanta cikin tashin hankali, Lokaci guda kuma tana tana maida hankali ga Uncle Yahaya da ya cigaba da magana.




" Laila Adam. Fito waje."
Uncle Yahaya ya yi maganar da turanci
Sai a lokacin Laila wani firgici ya sameta ,
tashin hankali ta sami kanta tare da tunani kala-kala, a kan Uncle ko dai ba lafiya yake ba .
Jin ya sake magana ne ya sa ta sake furgita ta fara takowa domin fitowa


Saman gurin ta hau tana raba idanu
"Kun san mene ta aikata." Uncle Yahaya ya tambayi d'alubai d turanci .
Suma cikin irin harshen suka ce masa "A'a."
"Yanzu zata fad'a muku abin data aikata , kuma duk wacce take shirin aikatawa, ita ma hukunci zai biyo baya ."




Shugaban makaranta dake zaune yana saurara ya ce ,"Gaskiya ne ."




Khadija wani yanayi ta shiga na matukar damuwa , haka Laila mamaki ya isheta


Takardar ya amsa wajen shugaban makaranta ya mikawa Laila Adam




Rassss taji zuciyar ta ta bada tare da wani saurin bugawa da take yi
Kallonshi tai cikin tashin hankali ba tare da ta amshi takardarba


"Karbi mana ki karanta musu abin da kika aikata." Yadda ya yi maganar cikin tsawa ya sa ta saurin amsa hannunta na rawa


a lokacin data amsa ya tabbatar mata wannan takardar data yi masa kalaman soyayya ce


"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. mafarkina nake yi ko zahirin Rayuwata ne." Laila ta fad'a cikin zuciyarta


Wani Uncle Sani ne ya daka mata tsawa da cewa ,"Yi sauri mana bamu da Lokacin batawa zamu shiga aji."




Hannunta rawa yake sosai jikinta na 'bari ta fara bud'e takardar
bayan ta bude ta zuba mata idanu tare da kallon Uncle




Khadija kuwa Allah ne yasan abin dake ranta na bacin rai
da kakkausar murya ya ce ,"Fara mana."




Da malamai da d'alubai duk ita suke saurara ,
ta fara karanta takardar wacce ta kasa riketa da hannu biyunta .




"Assalamu alaikum my Uncle,
fatan kana lafiya kamar yadda nake bukata,masoyin raina ."
Da sauri ta d'aga kai ta kalli Uncle Yahaya da matukar mamaki da wani mummunan yanayi,
wata Aunty ce ta ce ,"Baki ji kunyar rubuta masa ba , sai kunyar karantawa cigaba dallah izina ga masu son aikatawa. "






Laila ta maida kanta ga takardar wanda hawaye suka ciko mata fal har bata iya ganin rubutun da kyau .


"Masoyina kafi na kowa , ina san ka fiye da komai, kai ne dadin duniyata kuma muradina a duk Lokacin da nake cikin damuwa kai ne nake son gani domin yayewarta ,
Ina maka san da baka tunani, son da uwa take yi wa danta, soyayya mara gushewa , abu ne mai sauki zuciya ta ta buga a kanka".




Hawaye ta share yayin da wasu masu yawa suke zubo mata suna sauka a kan takardar
idanunta sun yi jajir , jijiyoyin kanta duk sun tashi ,
ita ma Khadija ta shiga wani yanayi




" Bani da burin barinka domin kai ne mahadin zuciyata,
Rayuwata taka ce , na yi tanadin kauna da soyayya saboda kai ,
bada kwakwalwa nake son ka ba , bada zuciya nake son ka ba , da raina nake kaunar ka , Ina tunanin ka da kwakwalwata , ina rikonka da zuciya."๐Ÿ˜ญ
Kuka ta sake fashewa da shi mai matukar ban tausayi kowa ya yi shiru yana sauraranta
Khadija kuka take kamar ba gobe








Laila kam wani jiri take ji yana dibarta , tana kallon takardar idanunta amma bata iya ganin komai






Sai ji suke timmmm Laila ta fadi kasa , ko shurawa ba tai ba






Da gudu Khadija ta nufo ta tana kuka
haka malamai duk hankali ya tashi




"Dama tana da aljanu ne." Shugaban makaranta ya fad'a




Cikin tsananin fusata Khadija ta nuna shi da yatsa tana cewa, "Zaka ga aljanu , ko numfashi bata yi , Allah ya sa ta mutu."
Ta fashe da kuka




"Ke shugaba kike fad'awa wannan maganar." wani a cikin malamai ya fada




Yayin da sauran malamai suka fara kora d'alubai aji


Lokacin da malamin lafiya ya zo aka duba Laila, amma ya tabbatar musu sai an tafi asubiti


a sannan shugaban makarantar ya tabbatar ya ya yi kuskuren barin wannan abin da ya faru


Kneel down aka sa Khadija a gefe guda yayin da suke shirin kai Laila asubiti


mikewa tai Khadija ta nufi hanyar fita daga makaranta da gudu tana kuka ta nufi gidansu Laila


yayin da duk malaman mamaki ya matukar kamasu da fitar ta
hakan ya sa aka tura malamai mata biyu suka bita, domin a zatonsu aljanu ne




Bayan sun isa asubiti aka kwantar da Laila dake asubitin gwamnati ne kuma babu wadatattun ma aikata
likita daya aka samu ya yo kanta .


Khadija tana shiga gidansu Laila ta sanar da mahaifiyar ta , ita ma da sauri tayiwa Barrister waya
kafin ka ce komai sai ga shi ya dawo cikin tashin hankali
sauran malaman da suke tafe da Khadija suka nufi asubitin
sakamakon barrister Adam yana zuwa matarshi da Khadija ya dauka suka tafi .


Yana zuwa ya ga da gaske Laila ce cikin mummunan yanayi, bai ce da kowa uffan ba ya dauketa ya sata a mota .A Lokacin malaman suka ringa kokarin yi masa magana , amma babu wanda ya kula a cikinsu ya shiga mota ya nufi babban asubitin yayanshi . Suma suka bi bayan shi.














Tom ni Fatima Abdallaah kano


Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna


wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share.


zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba
dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba


A kiyaye


















Kalisa ce cikin d'akin mahaifiyarsu cikin tsananin kadaici da kewa , bayan tasha kuka ta more , sannan ta zauna kan gado , wata loka dake kusa da gadon ta jawo , haka idanunta suka kai kan wasu takardu
d'ebosu tai kallo guda tai musu ta ji jikinta ya mutu , a sa'ilin data fahimci takardun gidan Hajjiya ne wanda Alaji ya bata , ta mayar ta aje


Wayarta ce ta fara ringin ta dauki wayar ba tare da yanayin ta ya canza ba ta ce ,"My Umar har ka zo."


Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Haba My Kalisa ta ya zan yi wasa da lafiyarki , bayan an ce yau ne dactor zai zo , kawai maza ki fito mu tafi ."
Kalisa ta ce ,"Tom shi ke nan." Ta aje wayar ta fita
tana fita falo ta yi sallama dasu baba anje , suka mata fatan samun lafiya sannan ta fita , tana fita
Umar suka nufi asubitin,sakamakon ba nisa ne dashi ba , a kafa suka isa suna hira .


Doctor jamil ne zaune cikin office dinsa tare da laptop a gabanshi , a lokacin sukai sallama suka shiga . Cikin girmamawa doctor ya tashi ya taro su , sa'ilin da ya basu wajen zama
"Sannunku fa , wato Umar duk an mance damu."
Doctor Jamil ya yi maganar cikin kyakykyawan yanayi


Umar ya mai da masa da cewa ,"Kai fa ka fiye surutu dan Allah haba naga kusan kullum muna gaisawa a online. "


Jamil ya ja tsaki yana kallon Kalisa da cewa ,"Kalisa ya karin hakuri. "?


" Mun gode Allah dactor. " Kalisa ta ba shi amsa
a lokacin wata nurse ta shigo , yayin da Doctor ya kalleta tare da mika mata wata takarda yana cewa,"Ku je tare da Kalisa ai mata wannan gwaje-gwajen , yanzu fa ."


Nurse din ta amsa yayin da Kalisa ta bi bayanta .


Umar suna zaune suna hira ba jimawa Kalisa ta shigo da takardar binciken lafiyar da aka mata.
Ta mikawa dactor sannan ta zauna tana kallon Umar yana mata murmushi.


Bayan dactor ya bude sakamakon ya yi ajiyar zuciya yana kallon Kalisa .Wanda duk hankalinasu ya koma ga dactor Jamil .




A zube min comment a private mu had'u next page.




Share, like and comment.........,๐Ÿ“š








Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)




*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>





Page 19&20





Ba editing







"Wato Kalisa zahirin gaskiya wannan ciwon naki , sai an miki aiki , domin a halin yanzu ma hunhunta ya samu matsala." Ya karasa maganar yana kallon Umar
wani faduwar gaba Umar ya ji ya bigi zuciyarsa ,

"Kuma gaskiya wannan aikin na gaggawa ne , don haka zan yi magana da dactor Aisha dake babban asubiti, zan tura ku can ." Doctor ya kuma fade


Kalisa cikin mutuwar jiki ta kalli Umar tana cewa, "Ka ga ni ko Umar , na kusan mutuwa."


"Haba Kalisa ai cuta ba mutuwa ba ce , an yi wa mutane da yawa aikin kuma sun sami lafiya dan haka kema insha Allah zaki warke , saidai aikin gaskiya akwai kud'i sosai ,duk da nasan baku da matsalar sa ."
Umar ya ce "Yanzu dai yaushe ne za mu je asubitin.".....






Ahmad ne yake wa Zainab fad'a sosai a kan Harun, amma sai kare shi take tana nuna Mahmud ne yake son bata masa suna , Ahmad saida ya matukar yi mata gargadi tare da mata barazanar sanar da Alaji abin dake faruwa duk da hakan dai har zuciyarta bata shirin barin Harun .



Kalisa har sun je wajen doctor Aisha a yau , nan ta tabbatar musu da dinbin kud'in da aikin zai ci .


Bayan sun dawo gida suka sanar da baba anje komai . Nan akai waya suka sanar da Sahid halin da Kalisa ke ciki ga kuma irin kudaden da ake bukata
Nan ya tabbatar musu ba wata matsala zai turo da kud'in
har yake sanar musu ma zai basu dukiyarsu ta dawo wajensu.
Amma har washe gari shiru , Sahid bai ce komai ba , wayarshi ma a kashe
Jafar ya je companin da Sahid yake aiki amma bai samu ganin shi ba .


A halin yanzu Laila ta sami lafiya, amma har yanzu Barrister Adam bai ce da makarantar DR.DD komai ba
Ansha matukar jinya kuma ana kansha a kan ciwon Laila , barrister yana kashe kud'i sosai
babban abin da ya ke ci masa rai wai Laila 'yarshi za a wa wannan tozarci har hakan ya jawo mata ciwon zuciya.


Rashin sanin irin matakin da zai dauka a kan makarantar ya sa har yanzu bai ce komai a kan lamarin ba .
Su ma malaman makaranta sun shiga rudani , musamman ma shugaban , yarinya ta kamu da ciwon zuciya lokaci guda , to da zuciyar bugawa tai ta mutu fa .
wannan kaddara ce ta shigo masa makaranta, kuma yadda ya biyewa Uncle Yahaya har hakan ta faru .








"Wai Khadija yaushe zaki dawo makaranta". Wata Zainab kawarta ta fad'a


Khadija ta kalleta tana ta'be baki ta ce ," Ni na bar wannan makarantar wallahi, domin dady ma ba zai takurani ba."


Zainab ta ce "To Allah ya kyauta ya bawa Laila lafiya, ni Wallahi ma abin da yake bani mamaki ashe da gaske Laila haka take son Uncle, ki dubi yadda zuciyarta ta so bugawa. ai wallahi Allah zai saka mata."


Khadija da duk kan 'bacin rai ta kalli Zainab ta fara magana, "Ai wallahi Uncle ya yi asara , kuma jira nake kawai dadyn Laila ya yi magana."


Zainab ta ce ,"Allah dai ya kyauta."








Cikin tsananin fad'a baba anje take magana
"Wannan ai wulakanci ne , haka ake yaron nan ya bamu kud'i amma har yau shiru , tun yaushe ake masa magana kuma kullum ciwon Kalisa girma yake."


Umar dake zaune a gefe guda cikin falon ya girgiza kai alamun goyon bayan abin da baba anje take fad'e




Jafar ne ya ce ,"Gaskiya kam dai Sahid bai kyauta ba kaka , to mene abin yi."


Kalisa ta ce ,"Me zai hana muje gidansu yanzu Umar, kasan babanshi abokin dady ne, kuma da zarar mun je zai masa magana. "




Baba anje ta ce "Eh gaskiya ne Umar ku tashi ku je yanzu domin wannan lamarin bana zama ba ne ."


Kalisa cike da kwalla ta kalli baba anje tana cewa ," Muna matukar godiya Baba anje , kina tsayawa da nuna damuwa a kan lamuranmu Allah ya baki.......".


Dakatar da ita tai tana cewa, "Haba Kalisa ai zan tsayawa lamarin ku bakin rai bakin fama ku amana ne gare ni . Tashi ku je kawai a dawo lafiya ."




Umar ya tashi yayin da Kalisa tabi bayanshi , sannan ta juyo ta kalli Jafar tana cewa, "Bari na tafi da mota jafar."


Jafar ya ce "To a dawo lafiya daman akwai mai a ciki ai."


Suka nufi harabar gidan ita da Umar.




Anan kuwa cikin makaranta duk kan malamai sun had'u suna tattaunawa a kan matsalolin makaranta, ana cikin haka wani mutum ya shigo a mashin
guri ya samu ya yi burki sannan ya sauka ya nufi ofishin shugaban makaranta,
ai kuwa duk malamai suna cikin office din
mutumin karasawa ya yi yana gaida shugaba, sannan ya mika masa sako ya fito , bai jira cewar komai ba ya fito ya hau mashin din sa ya tafi .


"Ikon Allah".
wani a cikin malamai ya fad'a, Uncle Yahaya ma yana zaune shugaban makarantar ya bud'e takardar


jin abin da Dr Dauda ya fad'a yasa duk hankalin malaman tashi


Cikin yaren turanci wata malama yare ta ce ," Me ke faruwa sir."


Sauran malaman kunne suka kasa domin jin amsar da zata fito daga gareshi , domin a halin yanzu suma ita ce damuwarsu


Ido ya kafa wa uncle Yahaya cikin tashin hankali, hakan ya sa Uncle tsarguwa yana cewa ,"Shugaba lafiya kuwa."


Cikin zafi shugaban makarantar ya tashi tsaye yana cewa, "Barrister Adam ya shigar damu kotu , wannan takardar tuhuma ce ." Ya karasa maganar yana cillawa Uncle Yahaya takardar


Wani tsoro da mamaki ne ya ziyarci malaman


Dr. Dauda ya zauna yana kifa kansa kasa yana cewa, "Innalillahi, yanzu sunan wannan makarantar zai baci a idon duniya , na tabbatar har mane ma labarai za su yad'a wannan case a labaransu , innalillahi wa Inna.....".


Uncle Sani ya kalli sauran malamai yana cewa," To yanzu mene abin yi , ya kamata a nemi mafita wallahi. "


Dacter ya dago kai yana magana cikin tsafi ,"To yanzu mene mafitar."
Yanayin yadda ya yi maganar suka sha jinin jikinsu , musamman ma Uncle Yahaya.



Tafiya suke cikin mota , Umar yana tu'ka su
kallon Kalisa ya yi yana cewa, "Ki ce dai gidan nasu da nisa. ga shi kauye, to ina zai aje min ke saboda rashin kunya."


Dariya Kalisa tai tana cewa, "Wallahi kuwa da nisa."
Umar ya yi tsaki yana cewa "Ai wallahi ya bani mamaki, dama fa shi dan kauye bai san arziki ba , sai ka yi masa rana ya tashi ya yi maka dare , yanzu ina amfanin wannan, garin nasu duk daji."




Wani gau suka ji wata babbar mota ta bige su , a sa'ilin da sam ba su ganta ba
hakan ya sa motar ta su ta kwace ta nufi daji
"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un, abin da suke fad'a ke nan


Umar ya bude murfin kofa
da nufin su fi ce a irin wannan gudun da motar take " Kalisa fita , fita kar kiji tsoron komai. "


Amma ina Kalisa duk ta rude rigarta ta makale
" Kai ka fita Umar ka fitaaaaaaa". Kalisa ta karasa maganar a yanayin firgici da ta ga sun kusa dukan wani dutse .




Kauuuu motar ta bigi dutse ta tashi sama , a lokacin suka fado kasa dukkansu , yayin da motar ta kama da wuta tun daga saman sannan ta fad'o kasa .




Kalisa ko shurawa ba tai ba


matukin waccen motar yana ganin haka ta faru kawai ya gudu abin sa ya bar su .Duk da shima yaji rauni .




Cikin mummunan yanayi Umar ya tashi kanshi duk jini , yana tashi ya fad'i kasa yaja jikinshi da kyer ya nufi Kalisa.


Yanayin tashin da ya yi mata ya tabbatar masa fa ta mutu bugu da kari wani karfe da ya gani a cikin gwiwarta ya tsagata .


Wani tashin hankali ne ya ziyarce sa ya kwalla ihu yana kiran sunanta da dukkan muryar da Allah ya hore masa.








Share ,like and comment...........๐Ÿ“š
Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน

By
Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta)






*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>





Page 21&22

Cikin tsantsar mazantaaka Umar ya yi jarumta ya nemi mutane
Allah ya taimaa ka wasu mutane suka kawo dauki .Wanda har motar asubiti da 'yan sanda suka karaso
Yadda Umar ya ga an dauki Kalisa ya sake tabbatar masa Kalisa ta tafi ta barshi

Timm ya fadi kasa kamar matacce , asubitin cikin gari aka karasa dasu , tare da turasu emergency
Sai ga su Nabila sha'be -sha'be cikin kuka da matukar tashin hankali
suna isa wajen doctor ya fito daga d'akin Umar
da sauri suka tare shi , Jafar ne ya ce "Ya jikin na su likita."?


Baba Anje cikin damuwa ta kallo likita tana sauran amsa


" Ita macen tana ICU room, gaskiya akwai bukatar a yi mata aiki, shi na mijin yana sume , amma nan da anjuma..... "




Likita maganar da yaji a bayansa ne ya sa su duk baba anje saurin juyawa
"Likita ya jikin Kalisa ta." Umar ya fad'a cikin wasu ruwan hawaye dake shirin zubo masa
"Haba malam ka koma ka kwanta , komai zai iya faruwa da kai a wannan yanayi kana bukatar hutu da kulawa."
Dactor ya yi maganar yana kallon Umar
Umar ya karaso gabansu , kawai Nabila ta fashe da kuka ta rungume Jafar


ita ma baba anje duk tausayin Umar ya rufe ta da ganin ciwon dake tare dashi
"Dan Allah yaya Umar ka je ka huta a halin yanzu kaji abin da doctor ya ce ."
Jafar ya yi maganar Nabila kwance a kirjinsa yana rike da hannun Umar.




Umar ya janye hannunshi tare da fara cewa ," Ni bana jin komai Jafar , yanzu kawai Kalisa ce damuwar , domin karku mance akwai bukatar yi mata aiki tun kafin wannan accident din."


Wasu zafafan hawaye suka zubo masa sannan ya ci gaba da cewa ,"Na ga karfe ya huda gwiwar Kalisa, na ji zafi a zuciyata kuma na bayar ta rasu , yanzu kawai lafiya zamu nema mata. "


Baba anje cikin tashin hankali ta ce "Gaskiya ne , innalillahi wa inna'ilaihir raji'un."






Dactor ya ce "Tom gaskiya ciwonta ni bazan iya dubata ba , ku jira kwana biyu likita yana zuwa." Yana gama maganar ya wuce


Ba zato sukaji Umar ya shako sa ,"Kai wanne mara hankali ne , har gobe zamu jira tana cikin wannan yanayin, ina imaninka da tausayinka ka je fa su."?




Likita da ya ji shakar sa ta yi yawa cikin wahala ya fisge ya hankade Umar "Kai mahaukacin ina ne , bari na kira security su fitar da kai." Dactor din ya karasa maganar ya nufi wajen masu gadi




Umar ya ce , "Mu dauki Kalisa mu koma babban asubitin dactor Aisha hakan zai fi."


Nabila ta yi ajiyar zuciya tana kiran sunan Allah .










Mahmud ne ya fito waje yana duban yanayin anguwar yadda tsarinta kullum yake sake burgeshi , duba ga manyan gidaje da sanyin anguwar
hakan ya sa har yau ya kasa komawa gida, har Aminu ya koma , amma shi ba shi da niyya , amma babban dalilin 'kin komawarsa a kan Zainab ne .


Sake bude idanunshi ya yi yana sake kallon abin da ya hango daga gefe ,
kofar gidan wani mutum malam na lado , wanda har almajirai yana dasu


Mahmud ido ya sake zubawa yana kallon ikon Allah






"Mene Harun yake yi anan".
Mahmud ya tambayi kanshi .


Daga bisani lokacin da Harun ya kula da Mahmud ya yi murmushi ya nufo wajensa.


" Malam Mahmud me ake kuma anan." Harun ya tambaya lokacin da ya karaso gaban shi




Mahmud zuciyarshi

Please Login or Register in order to submit comment