Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi har na dawo an ce wai ya tafi legos. ". Ya karasa maganar cikin tsananin son jin Sa'id ya yi magna a kai








Sa'id ya ce ," Allah sarki Yahaya , ai wallahi bamu da labarin shi tunda ya tafi legos, bamu san halin da yake ciki ba ."






Cikin damuwa Harun ya ce ,"Gaskiya ya kamata mu san halin da yake ciki doctor. "






Sa'id ya ce ,"Insha Allah zan sa a bincika mana legos din , domin akwai wani abokinshi Shu'ai bu."








A lokacin Ummi ta shigo ta mikawa dactor result din Harun




Yayin da ta zo fita ya sake 'kura mata idanu ta jefeshi da wata harara ta fita




Bayan ya bude sakamakon ya tabbatar wa Harun yana d'auke da ciwon hanta


Amma Harun bai damu ba , sai da doctor ya tabbatar masa ciwon hantarshi mai tsanani da muni ne , domin a kan mutuwa lokaci guda ko kuma hantar mutum ta dan'kare waje daya.






Sannan ne hankalin Harun ya yi matukar tashin gaske , nan ya nemi matakan kula d kanshi da magunguna ,bayan ya koma gida ma dai jikin nashi ya sake matsawa sosai musamman ciwon kunnenshi da yake fitar da ruwa mai warin gaske , iyayenshi suna matukar iya yinsu domin samun lafiyarshi amma har yau Allah bai yadda ba .








Haka anan cikin gidan yari Sahid rayuwa ta juya masa baya , ya matukar yin nadama yadda ya kula ba shi da wani gata , mahaifinshi babu , mahaifiyar shi bata tare dashi ga kuma wannan ciwon kafar da a halin yanzu zuwa anjuma za a yanketa , innalillahi wa innailaihir raji'un


Baya jin dadin rayuwarshi ko kadan a halin yanzu. Allah ka yi mana da kyau






A yanzu zainab da Mahmud ranar biki kawai ake jira , domin tuni an yi shiri tsaf dukkan family suna ta murna da wannan had'i .








Haka farin ciki a gurin su baba anje , komai ya komai daidai ba su da wata damuwa , Umar yana tare dasu ga dukkan abin da ya taso musu , domin ya sadaukar da rayuwarshi ga Kalisa , sai dai muce Allah ya jikan wanda suka rasu , muma kuma Allah ya....






Matukar ciwo Harun yake ciki, yana tabbatar wa kanshi wannan yanayi da ya tsinta kanshi sa'bon Allah ne da ya ringa aikatawa, sai dai a halin yanzu Harun ya matukar shan jiki




Wannan ciwon kunne , matukar wari, ruwa kuwa ba dare ba rana , sai ya tafi ya fara jin sauki sai komai ya sake lalacewa, ya ringa sunbatu ke nan har yake sanar da iyayensa irin abin da ya aikata a kano , ya ce musu alhaki ne ke bibiyarshi, su dena nemar masa magani .




Sun matukar koka sosai dajin halin yaron nasu , sai dai dukkan inda aka ji mai magani ana nemawa Harun , amma har yau ba a dace ba , ko da ya tafi sai ciwon ya dawo , har da kanshi ya gane mutane gudunshi suke saboda wannan wari da yake cutar dasu.






Babban abin da ya sake girgiza shi yadda doctor Sa'id ya tabbatar masa da mutuwar wulakancin da Uncle Yahaya ya yi abin ya sake d'aga masa hankali da jin tsoron duniya.










Wata mata ce dumur mur da ita zaune a falo tana wasa da 'yarta wacce bata wuce shekara biyu ba


Matar tana jin an kwankwaso kofar falon ta tashi ta bude




Mijinta ne ya dawo daga wajen aiki , nan ta tarbeshi ya karaso ciki yana d'aukar 'yar tashi yana mata wasa






Matar tashi ya kallah yana cewa, "Faiza wannan babyn tamu fa ta yi wayo , a gaskiya ya kamata a yi maka 'kani."








Ohhhh ni ko na ce ashe faiza ce da mijinta , iko sai Allah








Cikin wata kissa ta kalleshi tana amsar babyn ta aje ta gefe , kana ta rungumo mijin nata tana cewa, "Ai ni kai nake jira , duk sanda ka shirya."


Yadda yaji yanayin ya masa dadi ya sa ya fara sunbatar Fa'iza , ita ko ta sake kankameshi tana.......








Ooooooohh nan mata da miji ne , kowa ya basu guri , daman Fa'iza yaya a baya , bare yanzu me dalili .








Ni ko na ce Alhamdulillah ala kulli halin , anan na kawo karshen wannan kaggagen labari mai suna GUBAR RAYUWATA⚡🎈










Abin da mukai daidai Allah ya amfana
Abin da ya faru sakamakon karancin ilmi ina fatan Allah ya haskakan anan gaba






Ni Fatima Abdallah kano
(Autar marubuta)


Ina mika godiya ga masoyana masu comments, like da kuma sharing Allah ya saka muku ya cika muradan ku.




A kan haka nake muku albishir da sabon labari mai suna


FATIMA
DA
ZARAH. Wanda ya samu tsarawa da shiryawa daga gareni .








Anan zan barku tare da dukkan wani fatan alheri 🙏🙏🙏




07040805269
Autar marubuta Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment