Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari ba , hakan ya sa kawai yake jin gara ya yaudareta kamar yadda ya saba yiwa sauran 'yan mata.






Tom ni dai comment din na PC , share, like ...........๐Ÿ“š




Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน



By

Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta )







*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>






Page 11&12








Zainab ganin yadda kallon ya mata รฑauyi , ya sa ta ta fara tsarguwa , ta kasa zama daidai .
"Harun lafiya kuwa kake mini irin wannan kallon."
Murmushi ya yi mara kunyan yana cewa, "Haba Zainab akwai abin da nake son sanar dake ."


Zainab murmushi ta yi tare da gyara zaman mayafin dake jikinta tana cewa, "To ka fad'a mini mana baby."


"Tom fatan kin shirya ji domin kalmar tana da zafi."


"Zafi kuma."
Zainab ta fad'a cikin mamaki


"Ina san ki."
Zainab ta kau da kai tana dariya


yayin da Harun ya ce ,"Ba fa abin dariya ba ne , Ina jin san ki a raina kamar zai fasa zuciya ta ya fito , Ina kaunar ki da dukkan yakini da sadaukarwa, fatan zan same ki cikin girmama soyayya ta da bata kulawa."
Ya karasa maganar yana duban cikin idanunta


"Ni ma ina san ka Harun , soyayyar da uwa takewa yaronta , soyayyar da bata da karshe kuma bata da misali , domin kai din Rayuwata ne ."


Murmushin farin ciki ya yi da jin wannan batun na Zainab
hakan ya sa ya fara fadin , "Gaskiya naji dadi Zainab amma ina mai sanar dake cewa Gobe zan yi tafiya zuwa gida wato garin Tiga zan gaida iyayena, domin fa kinsan anan gidan kanin ummanmu nake."


Murmushi ta yi Zainab da ya matukar kara fito da kyanta tana ce masa , "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya , a kuma gashshemin da Umma ta."


"Karki damu my baby za su ji gaisuwarki Sarauniyar soja."
Ya yi maganar yana sara mata , ita kam ta yi masa dariya








Bayan malamin lissafi ya fita daga ajinsu Khadija
Ajin ya rufe da surutu yayin da wasu suke yin bitar lissafin


Laila ko rubutun ma batai ba ta yi tagumi idanunta sun kawo ruwa


Khadija ce ta dungureta tare da cewa ,"Haba Laila Adam mene yake damunki ne ."


Laila ta kalli Khadija tana cewa, "Wallahi ke ma kinsan Uncle ne , wallahi ina son shi , amma yanzu duk ba ya kulani , ko gani na ba ya yi , so yake ya juya mini baya , wallahi ina san uncle Khadija."


Khadija ta ce ,"Kuma babu abin da kika yi masa ."


Laila ta ce ,"Babu abin da nai masa Khadija, duk fa ya juyan baya."




Khadija ta ce ,"To ki bari anjuma ki same shi mana ."


Laila cikin fushi da bacin rai tace wallahi ko ganina fa ba ya san yi ."


Khadija ta ce ,"Tabbb ki ce dai akwai matsala. "






Yanzu dai Uncle Yahaya ko d'ar ba ya ji idan zai tafi hotel wajen Fa'iza
Domin kafin ya tafi makaranta ma ya sanar da kakarshi cewa ba zai kwana a gida ba yau , domin akwai aikin da zai , haka ta yi masa addu'a tare da fatan alheri....








Duk iyalan Alaji Idris zaune suke suna karyawa cikin farin ciki , domin Allah ya sauki Alaji Idris lafiya ya kammala azumi


wajen kwana uku ke nan


"Hajjiya kin san yau ne fa zami tafiyar nan zuwa kauye , da safiyar nan zamu tafi domin kinsan gari ne mai nisa kuma hanyar ba kyau ne da ita ba ."




Hajjiya Maryam ta ce ,"Alaji ke nan , ai na fika zumudi , domin tun dazu nasa Musa driver ya wanke mota , kuma ya zuba duk kayan abincin da za a kai musu."






Alaji Idris ya yi dariya yana cewa, "Eh lallai ki ce abin na yi ne , amma baba anje ba za ki ba ne ."?


Hajjiya tayi dariya tana cewa" Tabb ka ji Alaji da zance , baba mai jikin tsufa ina zata wannan garin , ai kam tayi zazzabi."


Dariya baba anje ta yi tana cewa, "Gaskiya kam ku je Allah ya dawo daku lafiya , ina nan dasu Nabila."


Jafar ya ce ,"Ai ko dai baba ki yi zamanki wannan garin ba abin zuwa ba ne kuma kauye ne."


"Ka ci gidan ku. Ina ce dangin ku ne ." Hajjiya ta yi maganar


Kalisa ce ta zumburo baki tana cewa, "Ni dai ina san zuwa momy."


Hajjiya ta ce ,"Ai na sani Kalisa danta Jafar da Nabila baza ai zumunci ba .


Alaji Idris ya mike da cewa ,"Hajjiya ki tashi mu shirya ina san har na dawo naje office. "


Ya shige ciki .






Bayan duk sun shirya suka fito harabar gidan
Duk suna musu a dawo lafiya


"Baba dan Allah karki bari yarannan su fita yawo , a kula dasu."


Hajjiya tai maganar cikin girmamawa tare da shigewa cikin mota


Sukai sallama suka tafi


yayin dasu kuma suka koma gida






Bayan wajen minti goma da fitarsu , sai ga GARBA ya shigo


Suke tabbatar masa Alaji sun tafi kauye


Garba ya koma yana takaicin rashin ganinsu domin ya basu sako zuwa wajen Shehu .




Bayan sun fito break Laila ta nufi staff don ganin uncle Yahaya


aiko yana zaune suna hira da wasu tsurarun malaman wanda duk kusan sa'anninshi ne
yana ganin Laila ta shigo ya had'e rai , hakan ya sa Laila Adam tasha jinin jikinta da 'ker ta karasa wajen shi ta tsuguna
Tun kafin ta kawowa ranta ta yadda za ta masa magana taji yana cewa, "Tashi ki tafi baki ganni da malamai ba ne."




Sau dubu nawa yake kiranta a gaban malamai ,amma yau yake wannan maganar, abin da ya zo mata kai ke nan


Cikin nutsuwa ta kalli cikin idanunshi da fuskar maraici ta fara magana da turanci ."Uncle dan Allah, wallahi na matukar damuwa da kai , mene na yi maka ."




Uncle Yahaya ya tashi ya fita waje
wani abu taji ya turnuke mata zuciya ta kalli sauran malaman wanda duk hankalinsu ba ya kanta , sannan ta tashi ta fita
Uncle yana can gefe yana waya ga dukkan alamu koma wayar me yake da mace yake yi


Laila ta sawa zuciyar ta wannan maganar


zafafan hawaye ne suka zubo mata , hakan ya sa ta kasa daurewa ta nufi aji tana kuka , kafin ta karasa ta ci karo da Khadija


"Mene ya faru kuma".? Khadija tai tambayar tana jawota jikinta


cikin kuka Laila ta fara magana ," Khadija kin san ya nake son uncle kuwa , me ya sa yake min haka , ni ce fa Lailanshi , wallahi zuciya ta zata buga a kan shi , zan tarwatsa zuciya ta idan ya rabu dani. "


Duk d'alubai sai hankalinsu ya fara yowa kansu
"Mene yake damun Laila?
waye ya dake ta?
Me ya faru ?...."


Sunata tambaya da turanci yayin da wasu suke yin Hausa


Khadija ta kallesu tare da basu amsa guda cikin yaren Hausa "Bata ta lafiya ne."


Suka mata fatan lafiya wasu suka bar wajen , Khadija ta ja Laila suka koma aji
"Wata kila fa Uncle wannan kalaman naki ne basi masa ba."


Khadija ta fad'a


Laila da idanun kuka tace ,"To ai sai ya fad'a mini ko , zan yi wa Uncle kalaman da ban taba yi masa ba na ba shi , matukar bai dawo yadda yake ba to ya dena sona, kuma Khadija ciwo ne zai kashe ni."


Khadija tai ajiyar zuciya tana takaici .










Kalisa da Nabila ne suke girki yayin da baba anje take daki shi kuma Jafar yana falo
"Aunty tin d'ร zu gabana yake fad'uwa wallahi."
Nabila ta yi maganar
Kalisa ba tare da tace mata komai ba ta nufi wayarta sakamakon kiran Umar da ya shigo .








Saukarsu Alaji Idris cikin kauyen driver ya fito da kayan abincin yana shiga dasu cikin babban gidan .




Sai ga yaran gari riiiiiiii sun nufo Alaji domin basu dari bibbiyun da ya saba basu duk zuwa , aiko sai da ya sallami kowanne yaro , sannan ya samu nutsuwa




Malam Shehu ya yi musu jagora cikin mutunci da tarbar arziki zuwa cikin gidan , kowa kuma sai murna , kafin ka ce komai a kawo musu nau'ikan abinci daga kowanne sashi na gidan , dambu fate , dashishi, dahuwa, da dai sauran su da dama sun ci sunsha sosai kafin matan gidan Alaji ya sallamesu


sun yi matukar farin ciki .






Uncle Yahaya ana tashi daga makaranta ya wuce wajen Fa'iza




Zaune take cikin wata mara kunyar doguwar riga fara shara-shara , bayan wannan rigar jikinta babu komai data sanya domin kana hango dukkan surar jikinta , bayan ma dai Fa'iza karuwa ce to 'yar iska ce ta gaske๐Ÿ˜‚




waya take yi da wata kawarta ," Aisha ya kike so na yi da Abdul ne dan Allah, ni fa wallahi bazan aure shi ba ai na fado."


Fa'iza tai maganar cikin fada


hakan ya hassala Aisha ta fara cewa ,"Sannu sara ,idan banda Abdul Salim wane yake sonki da gaske, to kuwa wallahi sai ki dena ci masa kudi , ki fada masa gaskiya, ai wallahi ma shi ne zai rufa muki asiri , to wallahi kiji tsoron Allah kiyi aure , ni yanzu tunda na samu masoyin gaskiya nayi aurena ba abin dana rasa."


Fa'iza ta ce "Ke ni zan kashe waya ai gobe zan dawo." Ta kashe wayar tana tsaki




A lokacin Uncle Yahaya ya turo kofa ya shigo
Fa'iza ta mike domin taro shi ."








Share, like and comment..............๐Ÿ“š




Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน


By

Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)






*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>








EditingโŒ








page 13&14








Hannayena biyu ta rike tana cewa "Tun dazu nake jiranka fa baby sai yanzu."


Uncle bata rai ya yi yana cewa, "Me ya sa zaki sa wannan kayan yanzu, kin san dai bana san haka sai da daddare ko."


Sakin hannayensa tai ta hardo wuyanshi , yayin da Uncle Yahaya ya ke sake kallon cikin jikinta yana ajiyar zuciya. "


"Nasan kana jin yunwa muje mi wanka sannan muci abinci."


Duk uncle ya kasa cewa komai kawai kallonta yake ......


kakartashi ma a halin yanzu bata da lafiya ga gidan ba kowa .










Anan gidan Alaji Kabiru
Zainab na falo a zaune , a lokacin Mahmud ya shigo yana kallonta


kujerar da take zaune shi ma ya zauna yana cewa, "kawo mini ruwa Zainab."
Ta tashi ta kawo kamar yadda ya ce


tana mika masa tai hanyar d'akinta


"Ina zaki zo mana."
Ta juyo tana cewa, "Uhum."


Murmushi ya yi mata yana cewa, "Gobe ina san zamu fita."
Tasa kai tana cewa, "Allah ya kaimu ."




"Kaii! Lallai ma yarinyar nan ba komai."
Ya girgiza kai


wayarshi ya ciro a aljihu ya nufi numbar Hauwa
"Bari na kira yarinyar nan mu gaisa." Mahmud ya yi maganar yana danna kiran
har ta tsinke ba a da ga ba , ya sake kira amma shiru


wayar ya aje a gefenshi tare da cewa "Ai shi ke nan ."


Ya kashe kujerar ya kwanta , wajen wucewar minutes 3 sai ka kira ya shigo masa , ba wata-wata ya daukin kiran
"Hello 'yan mata ya kike ya gida."?
Cikin muryar rashin sanin waye Hauwa ta ba shi amsa
jin hakan ya sa Mahmud cewa ," Kamar baki gane waye ba KO."?


Murmushi tai tana cewa, "Eh gaskiya ban gane waye ba."


"To Mahmud ne."
Ya fad'a kai tsaye


dariya ta saki tana cewa, "Gaskiya ne wallahi ban dauki murya ba , ya kake ya gidan ya su momy."?


Mahmud ya bata amsa cikin girmamawa
nan su ka yi hirar da bata kai minutes 6 ba sukai sallama da juna .


Yayin da Mahmud ya fara bacci bisa kujerar da ya kwanta.




Tun tuni su Alaji Idris sun baro kauye sun nufo hanyar gida.......




Wayar Kalisa ce ta fara ruri , hakan ya sa baba anje dake kusa da wayar tana caji ta fara kiran sunan Kalisa


kafin ta iso kiran ya yanke,
" Kaiii ai dady ne ya kira." Ta yi maganar tana kokarin bin kiran , sai dai kafin ta kira ya sake kira
"Gaskiya aunty Kalisa girkin nan ya yi dadi."
Nabila ta shigo falon tana fad'a
Jafar ya harareta yana cewa, "Wannan wanne irin abinci ne tun d'azu ba a gama ba."


Kalisa ta kara wayar a kunnenta tana cewa, "Hello dady har kun dawo."?


Wata kakkausar murya taji tana cewa,"ke ce Kalisa."?
Jin hakan ya sa duk hankalinta ya tashi
" Eh ni ce ina dadyna fa."


Daga can bangaren aka sake fadin ,"Sun sami accident, yanzu haka suna asubitin dake Kuje Abuja."


Wani mummunan faduwar gaba taji tare da mugun jiri ya ziyarceta
ta sullubar da wayar cikin mugun yanayi


Duk su baba anje suka yo kanta tare da matukar damuwa da tambayoyi
Daurewa tai ta basu amsa da cewa "Su momy ne sukai accident, suna Kuje hospital."


Idanunta matukar ruwa suka kawo , yayin da ita Nabila ma ta bud'e bakin kuka . Jafar bai ce komai ba kawai tsaye ya yi ya kasa motsi


Baba anje cikin tashin hankali ta ce da Jafar , "Jeka sanarwa Garba , ya zo yanzu mu je musan halin da suke ciki."
Jafar ya fita da ker ya shiga gidan Garba , aiko yana sanar masa ya fito cikin tashin hankali, duk suka rankaya suka nufi asubitin




Bayan sun je asubiti, suka sami doctor suke sanar dashi akwai wanda aka kawo sun yi accident


likitan cikin far a ya kalli nurse din dake gefenshi sannan ya kallesu yana cewa, "Ai karku damu mun yi musu aiki nan da anjuma zaku gansu."


"Alhamdulillah."
Garba ya fad'afad'a


Nurse din ce ta kalli doctor tana cewa, "Dactor ina tunanin fa , wanda aka yiwa aiki , ba su ne 'yan uwansu ba , kuma accident biyu ne ya faru yau wanda muka ansa a nan."


Wani firgici suka sake shiga dajin batun nurse


Likitan ya cire tabarau din sa yana cewa cikin turanci ,"Haka ne ."


Ya kalli Garba ya ce ,"ku ne masu mata biyu.? wanda aka yiwa aiki. "?


Cikin gagarumin matsanaicin kuka Kalisa ta ce ," No dactor mu fa kiranmu akai d'azu."


Likitan ya maida gilashinsa yana cewa "Okay sorry, police ne suka kira ku , ina mai baku hakuri, ku je mutuware."
Yana gama magana ya wuce


Tashin hankali๐Ÿ˜ฟ


Mutuwaren suka ne ma cikin mummunan yanayi , suna isa suka tarar da police men .


"Wai da gaske sun mutu." GARBA ya tambayi daya daga cikin police din cikin tashin hankali
nan aka tabbatar musu duk sun ruga mu gidan gaskiya har driver.


Nan ne fa wani kuka da zaucewa ya same su ,
"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'u, la'ila ha illallah...."




Nabila tana fad'e cikin tashin hankali


Jafar ya kalli yayarshi Kalisa dake tsaye tana kallon gawarsu
kawai yaji wani kuka ya kuf ce masa ya fadi kasa yana kiran sunan Allah
a sannan Kalisa ita ma ta sake fashewa da kuka ta nufi gawawwakin tana cewa ,"Kun gani momy , ku dubi Nabila da Jafar irin halin da suka shiga , ko dan haka karku mutu , ba dan ni ba , momy dan Allah wannan wacce irin mutuwa ce."
Ta kwanta jikin Alaji Idris tana kuka


baba anje gefe taja tana salati,tana kuka har da majina


Garba kuwa Allah ya kawo masa dakewa a halin yanzu amma yana matukar tashin hankali
kallon su ya yi yana cewa, "Ku yi kuka wallahi, ku yi kuka , Allah ya kawo mana jaraba." Idanunshi sun yi jajir


mota suka hau tare da su domin zuwa ai musu suttura


ana cikin motar ana tafiya, Garba ya ciro wayarshi ya fara sanar da mutane


lokacin da ya zo kan numbar malam Shehu ya fashe da kuka yana cewa, "Yanzu su Alaji sun baro kauye lafiya, Yanzu kuma na sanar musu da mutuwarsa, innalillahi wa Inna ilaihir raji'un."๐Ÿ˜ญ


Wayar ta zame a hannunshi tai kasa ya cigaba da kuka , hakan ya sanar da malam Shehu
nan shi ma ya rikice ya kid'ime da jin zancen, shi ma ya sanarwa da sauran mutane
ai kuwa kafin ka ce komai su ka yo zuga suka taho cikin jimami .




Bayan an isa gida babu abin da ya canza na tashin hankali


haka akai musu wanka , tare da dukkan abin da addini ya tanadarwa mamaci sannan aka kaisu ,wajejen magariba.
Allah ya sa mu dace .






Bayan idar da sallar magariba, Mahmud yana zaune yana jiran dawowar Ahmad
mota yaji daga can harabar gidan, hakan ya sa ya yi sauri ya fito






" Me zan gani"? Mahmud ya tambayi kanshi cikin tsananin fusata


Harun ne ya fito daga motarshi yana murmushi ga Mahmud, hakan ya sake hassala Mahmud ya nufi wajen shi


"Gurin wa ka zo a nan gidan? , na ce gurin waye."?
Ya yi maganar cikin huci yana niyyar naushinsa
cikin gadara da isa da samun guri Harun ya ce ," A'a gurin budurwata na zo mana Zainab. "


Hannu Mahmud ya kai jikinsa ya sha'ke wuyansa ,"Harun zan kashe ka , ka fita daga rayuwar Zainab, ba irinka ba ce , ka lalata mini Asma'u , Zainab kuma kanwata ce ka rabu da ita Harun, wallahi ba zan barka haka kawai ba."




"Kamar ya , Yaya Mahmud mene haka , ka sake shi."


Zainab ta karaso tana fad'a


cikin bakin ciki Mahmud ya kalli Zainab yana cewa, " Me ya sa haka Zainab, karki fad'a tarkon sa , Harun mayaudari ne , azzalumi mara tausayi , shi ne wanda ya lalata mini Asma'u."


Ya aje maganar yana huci


"Harun mutumin kirki ne , ba shi da wani aibu , kawai kana kishi dashi ne."
Zainab ta aje maganar cikin 'bacin rai da jin haushin Mahmud.






Ina jiran comment a private mara adadi fa ๐Ÿ˜Ž


saina jiku


Share and comment and like..........๐Ÿ“š
Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน

By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)






*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>








page 15& 16




Wani abu Mahmud yaji ya tokare masa zuciya
hakan ya sa duk ya rasa kalaman bakinsa
Cikin nutsuwa da sanyin murya ya fara cewa ,"Kishi kuma , Harun Guba ne mai girma , yana da illa , Zainab karshen magana manemin maza ne ."


Da sauri Zainab ta kalli Harun cikin tashin fahimtar abin da Mahmud yake fad'a
hakan ya sa Harun saurin faraiwa Zainab magana ,"Wannan ba gaskiya ba ne Zainab, Mahmud ka ji tsoron Allah mene na tare maka."


Wani bacin rai ne ya tokare Mahmud
"Minutes biyu na baka , ka fita daga gidan nan , karka sake kula Zainab ka fita daga rayuwar Zainab."
"Dakata yaya Mahmud, ba ruwanka dani , ni shi nake so , ai ba haka ya kamata ka nuna kishinka ba , kuma dan kana yayana baka da wannan damar a Rayuwata." Zainab ta fad'a cikin bacin rai


Cikin mamaki da takaicin kalamanta ya fara magana "Matsayina ya wuce haka a rayuwarki, kuma ban damu da gun uban wa ya zo ba , dole ya fita yanzu, kuma ko ba komai ni na isa nayi hukunci a gidan nan ."
Ya koma ya kalli Harun yana cewa, "Minutes daya na baka , wallahi idan baka fita ba sai na fasa motarka."


Harun yanayin Mahmud ya razana shi , hakan ya sa ya hau mota ya fita , Zainab na kiranshi .


Bayan Ahmad ya dawo Mahmud ya sanar dashi komai , tun daga Asma'u har ranar yau .
Ahmad ya ce ,"Ni wallahi na yi zaton ya canja halinsa , shi ya sa na yadda har yake rabata , tabbas dole ya bar Zainab kuma zan sameta .
Abin mamaki yana nan da halinsa."
Ahmad dai abin ya taba shi sosai ya ba shi mamaki




Anan kuwa cikin hotel Fa'iza da Uncle Yahaya sai wanda ya gani
tana kwance jikinsa yana shafa kanta tare da cewa ,"Ni dai na shiga uku , idan kin tafi gobe ya zan yi."


Dariya Fa'iza tai tana fad'in ,"Wallahi ka shirya mu tafi tare , domin ni wallahi bana iya zaman kano ta ishe ni ,
dama soyayyarka na zo nema kuma na samu."
Uncle Yahaya ya ce ,"Kin samu kuwa , domin ni duk bana ganin wasu mata sai ke Ina matukar son ki baby." Fa'iza ta tashi zaune tana masa wani irin kallo . Yanayin kallon ya sa yaji......






Laila tana matukar cikin damuwa da rashin kulawar uncle Yahaya, ga shi ita ba waya gareta ba , zaune ta ke ta yi tagumi cikin falon gidansu
hawaye fal cikin idanunta tana tambayar kanta ,"Wai shin Uncle me ya sa haka , wallahi zuciya ta , ta damu da kai sosai , me ya sa nake kaunar ka haka , ya Allah ka dawo da Uncle gare ni."


Daga wajen gida taji karar motar shigowar barrister Adam , wato mahaifinta hakan ya sa ta sami nutsuwa.






Washe gari da safe
Fa'iza ta koma legos, Uncle Yahaya dai ko kadan bai ji dadi ba , yana komawa gida ya sami kakarshi cikin mugun yanayi na zazzabi, wanda dole sai da suka tafi asubiti.




Yau kwana guda ke nan da rashinsu Alaji Idris, duk rayuwar su babu dadi, babu farin ciki , mutane suna girgiza idan suka ji wannan zancen mutuwa, haka Umar abin ya taba shi sosai , musamman ganin Kalisa cikin yanayi mara kyau. Haka Sahid da mahaifinsa malam Aminu abin ya bige su .






โšก๐ŸŒนโšก








Tom ni Fatima Abdallaah kano


Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna


wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share.


zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba
dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba


A kiyaye






โšก๐ŸŒนโšก












A ranar yau kakar Uncle Yahaya ta rasu , tabbas ya ci kuka sosai , haka aka shirya daluban makarantar DR .D.D suka je gaisuwa.
Allah ya jikan musulmi




Harun yana matukar takaici da abin da Mahmud ya yi masa
amma babban farin cikin da yake samu Zainab sam bata yadda ba , hakan ya ke faranta masa rai .
Sun zana jarabawarsu , wanda hadda Umar




Ahmad ya sami Zainab ya mata fad'a sosai a kan Harun, ta ga bacin ran sa , wanda sai da ya yi niyyar sanar da Alaji Kabiru mahaifinsu , amma Mahmud ya ce kar ya sanar dashi tukun zata gyara .


Yadda Zainab take ganin Mahmud ya shiga tsakaninta da Ahmad ya sa ta dena kulashi , tana matukar jin haushinsa, kuma ta sanar masa ba za ta rabu da Harun ba.




Yau an gabatar da addu'ar bakwai ta su Alaji, mutanen kauye sun zo da matukar yawansu, wajen yamma kuwa kowa ya watse in ka cire mutanen anguwa dake shigowa jefi-jjefi su yi gaisuwa




Iyalan Garba ne shirye tsaf sun fito harabar gidan,
Kalisa ce ta kalli Garba tana cewa ,"Dan Allah Baba Garba kai ma tafiyar za kai , ka bar mu , ai muna jin dadin zama dakai."


Nabila ce ta ce ,"Haka ne wallahi mun jin sauki idan kana nan."


Baba anje da Jafar basu ce komai ba dai , face tsayawa suna sauraron abin da kowa yake fad'a


cikin kasalalliyar murya da rashin kwarin gwiwa Garba ya fara magana


"To ya zami da mutuwa, ta tozarta mu babu yadda muka iya , kuma ni ba kud'i ne gare ni ba , zamana daku wahala zai ja , gatana Alaji ne , kuma yanzu babu shi , mota ta an sace Allah bai nufi ya canza mini ba , ya rasu , bani da komai , gara na koma kauyen zan fi nutsuwa."
Ya aje maganar cikin rauni


d'aga kai ya yi yana sake cewa ,"Duk abin da ya taso da kuke da bukatata , ku kirani."


Baba anje ya kalla yana cewa, "Dan Allah Baba, kiyi hakurin zama da ...."


Baba anje dakatar dashi tai tana cewa, "Haba Garba , yaran nan sun zama amana a gare ni , babu yadda na iya , Alaji da Hajjiya sun wuce haka , kuma ta su ta yi kyau , sai dai mu ce Allah ya jikansu da rahma ya kuma sa mu dace mu ma ."




Matar Garba ce ta ce ,"Ameen ya Allah. "
Haka su kai sallama da juna Garba ya tafi .




A yanzu dai Uncle Yahaya sai Allah, domin tun tafiyar Fa'iza ya haukace da neman mata , lokacin da ba ya goyawa Harun ba ya a kan hakan fad'a suke , amma yanzu Uncle Yahaya sanda Harun ya kirashi ya masa

Please Login or Register in order to submit comment