Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

_ina farawa da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Ƙai._

*(1)*
*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....ka zalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai dake cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana yake tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shine; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine mecece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!..._*

*Kano, 3:00pm.*
sanye nake da maroon hijab wanda ya ɗauki kyawuna matuƙa, a yayinda Farhana ke yafe da ƙaramin gyalenta wanda itama yay ma ta kyau sosai. Cikin takun natsuwa da hankali muke fitowa daga cikin Sahad Store da ke nan anguwar zoo road. Ledar hannun Farhana kawai zaka kalla ka gane cewa ba ƙaramar siyayya ce muka yi ba. muna tafe muna ƴar magana a cikin nishaɗi, duka fuskokinmu kewaye da glasses, sai dai akwai banbanci a tsakanin glasses ɗina da nata, domin nawa na magani ne wanda ake kira da medical glass, ciwon idon dana gada a wurin Kakata mahaifiyar Abbana, ita kuma Farhana na gayu ne, wanda bata iya rabo da shi a kullu yaumin.
zuwanmu bakin jar motar da ta ke mallakin Farhana ce muka tsaya, sannan Farhana ta buɗe booth ta sanya ledar kayan hannunta, tukunna na buɗe gaban motar na shiga, bayan Farhana ta rufe booth sannan itama ta zagayo ɓangaren mazaunin driver ta shigo ta zauna tana yiwa motar key. "wash Sister wallahi na gaji da yawa yau, kai ni kam sai na kwan biyu ban kuma zuwa wani biki ba". na faɗa a sa'ilin dana ke kunna Ac'n motar. "yanzu ai zamu ƙarasa gida, nima da kika ganni duk a gajiya na ke, buƙatata kawai na jini cikin shower". cewar Farhana tana karya kan motar zuwa kan titin da zamu hau. na ƙara cewa,"ke kin san ma za ki samu ruwa a gida, ni yanzu na koma da wuya idan ba sai na fita neman mai ruwa ba, saboda anguwar mu muna cikin matsalar ruwa...Gwamnati gaba ɗaya bata tausayin rayuwar talaka, ba wuta ba ruwa a inda talaka bawan Allah ke rayuwa, kai Allah kayi mana magani". na numfasa kamin na ƙara cewa,"Allah sarki Gwaggo nah nasan yanzu tana can tana tsumayin dawowa ta, kuma kin san fa sai da ta ce ka da na jima". Farhana ta ce,"kinga ba wannan bama, ni damuwar ma Allah yasa mu tarar da telan nan yana shago, kar musha wuyar banza ga wannan uban go slow ɗin, kalla fa tun ɗazu danja ta ɗaga amma har yanzu motoci sun gagara wucewa". "to amin dai, Allah ya nufemu da ritsa shi a shagon ɓuyarsa". na faɗa ina yatsine fuska alamar gajiya sosai a tare dani. Direct sharaɗa muka wuce shagon da Momin Farhana ta aikemu amso ma ta ɗinki.
Ba ƙaramin takaici muka ƙunsa ba da muka je ba mu sami me ɗinkin ba, tsabar haushi ma ko jiran yaron shagonsa dake mana bayani bamu yi ba muka fice dukanmu rai a ɓace, danni har ji nai kaman na gwaɓe bakin saurayin dana san ƙarya ce kawai yake gilla mana. tun fitowarmu daga shagon nake ta duban jefi-jefin jama'ar da ke layin, kasancewar sa layi ne da bai tara mutane ba, sai ƴan tsirarru haka, unguwa ce bata masu kuɗi ba amma kamar wata babbar estate shiru kake ji. nace da Farhana, "ni kam kiyi sauri mu bar layin nan ina tsoronsa, kin san yanzu kidnappers sun yi yawa a gari, mutane ba tsoron Allah". itama tace,"hmmm sauri ai kece zance kiyi, kina tafiya kamar ba za ki taka ƙasa ba, kee ni ko dai kina da matsalar ƙafa ne?". na harareta sannan nai murmushina mai sanyi ba tare dana ce ma ta komai ba, muka ci gaba da tafiya hannunmu riƙe dana juna kace mu twins ne, sai dai muna gab da ƙarasawa inda mukai parking naji ƙafafuna sun tsaya cak daga tafiyar, yayinda hannuna ya zame daga cikin na Farhana, na bi gefen haguna da kallo kafin naji ƙafafuna na jana suna tafiya da ni zuwa wani wuri, wani wuri da ban san me zai iya faruwa ba idan na riske shi, na bar Farhana naci gaba da tafiya tana ta maganarta ita ɗaya duk tunaninta tare muke. sai da tayi gaba sosai sannan ta fahimci tafiyar tamu ba tare muke ba, ta waigo da kanta sai kawai taga babu ɓurɓushina ma a wajen, kuma a wannan lokacin ɗaga idon da zatai can gefe ta hangeni ina tafiya cikin sauri-sauri har ina harɗewa, saurin da a duniyarta zata rantsewa wani bata taɓa ganin nayi shi ba tun yarintarmu.
tsananin mamaki sai yasa ta riƙe haɓa, cikin zuciyarta na ayyanawa da me zanje yi a cikin bola?.
"Sabina! Sabina!! ke Sabina wai ina ki ke neman zuwa haka? bola fa naga kina neman shiga, wai kin yi hauka ne? Keee!!".
zan iya cewa a sama-sama naji abunda ta ke cewa, dan haka hannu na ɗaga ma ta ta baya kawai ba tare dana yi yunƙurin tsayawa ba, kuma zagin da ta ƙunduma ta wurgo min shi yasa ni ɗaga ƴar muryata ina cewa da ita,"Farhana ba fa bolar zan shiga ba, ki biyo ni ko ki jira ni yanzu zan dawo".
Farhana ta sauke numfashi tana zubawa sarautar Allah ido, tabbas banda tasan wace ƙawarta lallai zata iya cewa aljanu ne da ita ko kuma tana da ciwon hauka ne, amma a yanzun ma ba zata ƙi cewa Sabina ta sami matsala ba. Gani tai sam ba zata iya barinta ita ɗaya ta shiga cikin wannan bolar da shigarta babu abinda mutum zai kwasowa kansa fa ce musiba, hakan yasa ta bi bayanta itama cikin sauri, abunda ya ƙara bata mamaki kuma hangenta da tai ta tsaya gaban wani mutumi da ke zaune saman bulon wani kango a jikin bolar. Farhana tai turus ta tsaya domin ita kuwa al'amarin ya fara bata tsoro, gwara ta tsaya daga nan ɗin idan taga abin bana tsayuwa bane saita arta ana kare, domin ta fara tantama da lafiyar ƙwaƙwalwar Sabina.
Saurayi ne kyakykyawa na ajin ƙarshe zaune saman bulo a bakin wani kango, shekarunsa zasu kai 27-28, shi ba fari ba kuma shi ba baƙi ba, hasken sa dai-dai misali, jikinsa sanye da yadi me arha ruwan madara wanda ya amshi jikinsa, a kallo ɗaya zaka yiwa kayan jikinsa ko da ace daga nesa ne ka gane cewar yadin a koɗe yake, irin koɗewa da jemewar da suka gaji da duniya, Farin silifas ne wanda ya ɗanji jiki sanye a doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu, Kansa a ƙasa yake hannunsa riƙe da taba sigari, cikin ƙwarancewa yake zuƙa yana fesar da hayaƙin ta gefensa. zai kuma zuƙa kenan yaji an ƙarɓe ta daga hannunsa, ya ɗago jajayen idanunsa domin ganin mahaluƙin dake da ikon karɓe masa abokiyar rayuwarsa.
Idonsa ne yay tozali da ƴar kyakykyawar budurwa tsugune gabansa, tana sauke masa kyakykyawan murmushi, da wannan idanun nata masu zurfi, kallo ɗaya yay ma ta yay saurin ɗauke idonsa saboda faɗuwar gaban daya tsinci kansa a ciki, ba tare da sanin dalilin hakan ba, kuma haka kawai sai yaji ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri abinda bai taɓa riska ba tsawon shekarun rayuwarsa. ina lure da shi da yanda yake bina da kallo ta ƙasan ido, wucewar sakan ɗaya, biyu, uku, ya ɗago da kansa gaba ɗaya yana sauke kallonsa gaba ɗaya akaina, har yanzu ban bar yi masa murmushi ba, hakana ban ɗauke idona daga ƙwayar idonsa ba dake haskawa da ƙyallin mamakina ba, kuma zan iya rantsewa a wannan lokacin abinda yake rayawa acikin ransa shine _ko dai ni mahaukaciya ce?._
na gyara zaman glass ɗina sannan nace da shi, "Hy Mr Man". na faɗa ina ɗaga masa gira sama, sai dai shi idonsa na kan tabar dake hannuna da ban yar da ita ba, sai na kalli tabar tukunna na maida kallona kansa kamin na shiga ce masa. "wannan tana cutarwa, ba ta amfanar da mai shanta, Almubazzaranci ce, tana cutar da na kusa da kai. a bisa haka Malamai suka ce tunda duk abinda ta ke haddasawa haramun ne to itama ta zama haramun".
ina gama faɗa na jefar da sigarin a ƙasa, na ta ke da takalmina, sannan na maida glass ɗina dana cire nai cleaning ɗinsa. yaji sanda iska ta ɗebo abunda tace ta shigar cikin kunnensa, kuma yaji yanda kalaman nata suka sami zama acikin kansa, ya tantance maganartata cikin kowanne futar harafi, sai dai ya kasa tantance zaƙin sautin daya fita acikin amon muryartata. ni kuwa ƙura masa ido sosai nai ko tsoronsa ma banji, kuma shi ma sosai yake kallon ƙwayar idona, sai dai Allah masanin gaibu, dan ban san me zuciyarsa ke karanta masa ba.
sai kawai na ƙara murmusa kuncina a karo na babu adadi, tare da harɗe hannayena a ƙirji ina faɗa masa abunda bai tambayeni ba, haka kuma babu nuni na yana baƙatar sanin hakan. "Sunana Sabina Auwal, anan garin kano nake. And you?". a wannan lokacin abinda Sabina bata sa ni ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewar_anya ita mutum ce kuwa._
bai bani amsa ba, babu kuma yunƙurin hakan a tare da shi, abu ɗaya ne kawai ke ɗawainiya dani, aiwatar da wasu abubuwa da bana sanin lokacin da nake yinsu ba...matsowa kusa da fuskarsa nai, na ɗaga masa kai alamar ina jiran cewarsa akan tambayar sunansa da nai. sai naji shi da saɓanin abunda na tambaye shi ɗin. "me yasa ki ka faɗan sunanki bayan ban tambaye ki ba?". "ka fara bani amsar tambayata tunda ni na fara". na faɗa ina ɗan karayar da kai gefe.
a hankali naji muryarsa na fita, kuma a lokacin so nake na toshe hancina saboda warin sigarin dake fita a bakinsa, amma na kasa saboda bana so na nuna masa walaƙanci. "duk da bana jin yaren da kika yi min tambayar, amma zai iya yiwuwa na fahimta. indai yanda na fahimci tambayar taki ne to ni ba ni da suna, kuma bani da sunan Baba, ban san kuma garin da na ke ba". sai kawai na saki baki galala ina ƙare masa kallo da maɗaukakin mamaki, kuma ƙwayar idona na haska masa da cewar ban yarda da abunda ya faɗa ba.
"tun ina ƙarama kamin Mama nah ta rasu, ina tunawa kamin ta rasu ta gaya mun babu kyau ƙarya, don haka kar na yi kuma kar na koyi yinta, kuma kar nayi tarayya da me yinta. Sannan da na girma, Gwaggo nah wata rana ta yiwa Yaya nah faɗa cewar Babba baya ƙarya. So dan haka kaima karka yi ƙarya kaga babba ne kai, kuma ni yarinya ce, idan kayi zan koya a wurinka, kuma nasan ai ba zaka so hakan ba ko Yaya?". ina masa maganar ne da yanayi irin na yara. "me ya kawo ki nan wurin?". Ya tambayeni yana mai tsareni da ido da alamu na tuhuma.
na tsarota sosai, kuma tsoron bai sa ni yi masa ƙarya ba, na faɗa masa ainihin abunda ya kawo ni. "na zo ne domin na hanaka shan sigarin da ta ke haramtacciya".
"to ki tashi ki tafi, ni ɗin bana son kowa a kusa da ni, ki tafi kar naji miki rauni".
yanayin da yay maganar kuma ya ke dubana ba ƙaramin kaɗa ƴaƴan cikina yay ba, ina kallo ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kwalin sigari ya buɗe ya ɗauki ɗaya, sannan ya ƙyasta lighter ya kunna, zai kai baki kenan na miƙe da zafin nama na ƙwace ina yin jifa da ita. kamar zan fashe da kuka nace, "don Allah kar kasha, ba zan iya ganinka kana shan abunda zai cutar da kai ba. Kazo mu bar nan wurin don Allah". na faɗa ina kamo hannunsa don mu tafi. a tsawace yace da ni,"kar ki ƙara cemin Yaya, ni ba Yayanki ba ne".
"shikenan ba zan kuma ba. Amma sai ka faɗa min sunanka idan ba haka ba ni kuma bazan daina ce maka Yaya ba, tunda kai ɗin ka girme ni ka yi sa'a da Yaya Abba, tarbiyar gidanmu bata koyar damu faɗan sunan na gaba damu ba gatsal". Ƙwace hannunsa yay anawa yana doka min tsawar da tasa naja baya babu shiri, yana faɗin, "ki tafi ki barni ko. Nace miki bana da suna bana kuma da sunan Baba, banda kowa, na tsinci kaina ina rayuwa ne ni ɗaya kawai...dan haka bana son kuma jin maganarki anan wurin ki wuce ki bar nan". na kawar da tsoronsa ina kuma kamo hannunsa, roƙonsa nake kamar tsohuwar mayya ina cewa, "Yaya kar kayi fushi ka duke ni, na maka alƙawarin ba zan kuma tambayan sunanka ba tunda baka so. Amma yanzu ka zo mu tafi gida, zamanka anan zai cutar da kai, ga warin bola ga sigarin da kake sha, abun yayi yawa". cikin wata razananniyar muryar ya ƙara ce min. "shekaruna goma sha tawas ina rayuwa anan Wurin, anan nake yini nake kwana, sigari itace abincina kuma itace abokiyar rayuwata, Allah shi ke tallafe da rayuwata, maƙociyata da nake jin daɗin mu'amala da ita wannan bolar, warinta shi nake shaƙa naji daɗi. Duk tsawon wannan shekarun ban cutu ba sai a yau da kika zo?, to wace ke? me kika isa ki sauya a rayuwar da Allah ya tsarata a haka tuntuni?...kinga ki shige ki tafi ki bani wuri tun ban maki rauni ba".
Tsantsar tausayinsa naji ya kamani, da wani firgici da kalamansa suka haifar min, saboda ganin yanda damuwa ta kuma bijirowa a saman fuskarsa, har yana maganar tana rawa kamar zai fashe da kuka saboda ɗacin rai. saina sauke kaina ƙasa ina goge ƙwallar da ta tarar min, wucewar sakanni uku na ƙara kamo hannunsa naja shi da ƙarfin da Ƙafafunsa basu iya yin gardama ba. yayinda a lokaci ɗaya naji ihun kukan jariri na ƙwala ƙara acikin kunnena, ƙarar kukan da yasani saurin gimtse ido, tare da damƙe hannunsa da ƙarfi babu shiri, inda hasken hoton wani jariri ke giftawa acikin duhun idona, sai naji kaina na wani mugun sarawa da wannan tsala kukan da jaririn yakeyi...wani abu da ban fahimta ba a lokacin shine, wataƙila anyi amfani da gatari ne wajen sara shi a tsakiyar kaina ya rabe gida biyu, ta yanda yin gaba da komawa baya zasu gagara a tare da ni.

****
_Hey Guyz how are you doing, hope you are all doing fine. how was the first charpter? loving the story already bah? encourage me by comments and voting, thats the only way i will know my effort is beaing appreciated...it's not a new story buh an old story am updating, i just changed the story name, kuma no disappointment insha'Allahu☺....ina fatan zan sami haɗin kanku daga farko har zuwa ƙarshe. Allah ya bani ikon gamawa lafiya, amin Ya Rahman...mai karantawa kuma Allah ya cire shi daga sahun mugwayen da zasu karanta littafi suƙi appreciating, dan mugunta ne da munafurci ai karatu aƙi appreciating, mutum sai ya nuna kaman bai karanta littafin, honestly speaking babu daɗi irin hakan...promise you ba zanyi delaying maku posting ba, so you people ma karku ji ƙyashin yin vote da comment.👏👏_


#love you my readers😘
#mikiyawriter's
#2022.
#Share.*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(2)*
kusan daƙiƙa huɗu kaina na juyawa kafin na iya sakin hannunsa na ɗan matsa gefe da shi na dafa jikin gini. sama-sama nake jiyo muryan Furhana na faɗin,"wai Sabina kin san shi ne?". ta faɗa tana ƙarasowa inda nake. na buɗe idona da ƙyar na dubeta ina cewa,"a'a ban san shi ba, ban ma san waye ba". cikin ƙarfin hali nai magana ina dafe da kaina, ta matso kusa gareni da tashin hankali tana dafa kan nawa da shiga jera min tambayoyin,"lafiya?". a wannan lokacin babu abinda nake so irin a cire min kaina a dire shi a gefe, in yaso a barni naci gaba da rayuwa a haka idan da yiwuwa kenan, idan kuma har cire kan zai zama silar rasa raina to tabbas zaifi min sauƙi a cire shi dan na rabu da wannan tsananin sarawar da yake min, da kuma amsa kuwar kukan jaririn da har yanzu ban bar jinsa ba. "na shiga uku menene naga kina dafe kai? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...kinga abinda kike neman jawa kanki ko Sabina, ni uban me ma kika gani da kika yo cikin bola sai kace mahaukaciya". muryar Farhana na fita ne cikin faɗa sosai da kuma tsananin nuna kulawa gami da matuƙar nuna damuwa. magana nake so nayi amma na kasa, sai laɓɓana dake aukin yin rawa, ko idona dake buɗe kaɗan dishi-dishi nake gani da su, jiri ya ɗebeni na nemi na zube a wajen tai saurin riƙeni ta zaunar akan bulo ɗin da Yaya ya tashi. hawayen azaba ya shiga min sintiri a saman fuskata, Farhana ma ko da bana kallonta amma a yanda muryarta ke fita da rawa nasan kuka ta ke, ta kama kaina tayi min adu'a, sannan ina jinta ta miƙe tana surfa zagi da bala'i ga bawan Allah'n dana san bashi da hannu a wannan halin dana shiga. ta dage akan sai ya faɗa ma ta abunda yayi min ko kuma ta kira masa ƴan sanda yanzun nan, shi dai bai saurareta ba dan banji yayi ma ta magana ba...kuma haka ta ƙyale shi ta dawo kaina duk a ruɗe tana ƙara faɗa masa wallahi komai ya sameni sai inda ƙarfin shari'arsu ya ƙare ita da shi, dan ba zata ƙyale shi ba.
da ace tasan irin azabar da nake ji acikin kaina, da kuma hoton dake haskawa cikin duhun idona, da bata tsaya tana wannan jarabar ba, kamani kawai zata yi mu tafi gida a sama min lafiyar ciwon da nake ji. "na banu ni Farhana, ban san me kika shigo yi wajen nan ba, yanzu duba matsalar da kika jawa kanki...yanzu me zan faɗawa Gwaggo". kuka ta ke yi sosai a sa'ilin, kuma har ga Allah maganartata na ƙara ƙarfin iskar guguwar dake wucewa ta kacikin ƙoƙon kaina ne. sai dai cikin lokacin da ba zai haura sakanni takwas ba na manta da halin da nake ciki da duk wani abu da naji yana damuna, hatta hanzarin miƙewar da nayi ban san nayi ba dalilin jin Farhana tana cewa da shi. "ina zaka je? ina zaka tafi? kasan Allah ka ƙara ɗaga ƙafarka daga nan saina yi maka ihu, kazo ka sakar min ƴar'uwa dan nasan koma menene kaine sila". duk da cewar ba sosai nake gani ba, amma a taku biyu na cimma inda yake tsaye, kuma ban manta da wannan kama hannun nasa da nayi ba gudun kar ya tafi ya kai kansa wajen da zaici gaba da cutuwa, hakan zuciyata ke ce min, "barinsa nan wurin zai kai kansa ne inda yafi nan muni". shi yasa komai zai ƙara faruwa dani ba zan sakesa ba, ko da ace zan dawwama anan babu tafiya. amma ga wani maɗaukakin mamakin da al'ajabi, damƙar hannunsa da nai sai kawai naji komai na washewa, ciwon yana tafiya, komai na janyewa, kuma a hankali komai ya tsaya cak, kamin ya tafi gaba ɗaya. sai naji ni nayi sanyi ƙalau, haka kuma wani abu da ban san menene ba na tsargawa a jikina. na buɗe ido ina dubansa, yana nan dai tsaye a wurin, kenan tun a ɗazun bai motsa ba, sai dai wannan karan hannayensa duka biyun na zuɓe ne cikin aljihun wandonsa. sai kawai na ƙara kamo hannun nasa a haka naci gaba da jansa,kuma a yanzu bai min gardama ba, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, kawai bina yake kaman yaron dake bin uwarsa. ni kuwa ƙara saurin tafiyarmu nake dan mu bar cikin bolar da wuri, saboda zuciyata faɗa min kawai ta ke karki tafi ki barshi nan, sai dai komai zai faru ya faru dake. gaba ɗaya na manta ma da wata Farhana sai dana jiyota tana faɗin, "Allah kayi min maganin abunda ke neman yafi ƙarfina...yanzu da kike janshi ina za ki da shi?". ba tare dana tsaya daga tafiyar ba ko kuma na juyo nace da ita. "tare zamu tafi. bana son zamansa anan". "Allah uwar da ta haife shi". sai kuma ta ƙara da cewa,"amma dai kinyi hauka ko Sabina? ba ki san mutum ba, ba ki san shi ɗin ko aljani ne ba, ko kuma macuci kawai dan ɗebarwa kai masifa da nemarwa kai jaraba shine kika wani kama zuwa inda yake harda ƙarfin halin riƙo hannunsa za ki tafi da shi, to ki kai shi gidan uban wa uwar masu son taimako ta duniya...yanzu wannan ɗan wiwin har ina dalilin da za'a taimake shi". "kenan Farhana kawai idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan halin sai aƙi danganta hakan da jarabawar rayuwa? saboda hakan kuma sai aƙi taimakon mutum?". na faɗa ina tsareta da ido a sanda na tsaya da tafiyar. "oho ni bance haka ba amma wannan dai ai baiyi kama da wanda za'ace ƙaddara ce tasa shi shiga wannan yanayin ba...dan haka kawai ki sake shi mu tafi, karki so ki tona zuciyata kiga takaicin da ke ciki". "ohhh Farhana ki fahimce ni mana, duk abinda zaka yi kayi shi don Allah kuma zuciya a tsarkake, wataran baka san ta inda za'a taimake ka ba kaima. Nifa kawai na tausaya masa ne, naga kuma bai dace muna ganin halin da yake ciki ba mu tafi mu barshi a haka. Yanzu tafiya zamu yi da shi sai mu sauke shi a gidansu". ta galla min harara tana faɗin,"mtswww ƴan wiwi nawa ki kai arba da su ba ki taɓa yunƙurin taimaka musu ba sai akan wannan mahaukacin". kuma furucinta na ƙarshe ya tsaida ƙafafuna, na rufe ido kaɗan sannan na buɗe, magana nake so na yaɓa ma ta, amma ba zan iya ba, bata cancanci hakan daga gareni ba, kuma hakan ba halina ba ne sam. sai kawai na kaɗa kai da cewar,"su sauran basu yi kama da waɗanda suke biɗar a taimaki rayuwarsu ba ne shiyasa kika kalla banyi hakan ba. shi kuwa sai dai idan idon mara imani ne ya sauka akansa, amma a hoton fuskarsa na farko daka kalla zaka shaida ɗan adam ne da yake cikin wata jarabawar rayuwa, ki kalla ƙwayar idonsa da kyau ki gani, ita kaɗai me shaida miki halin ƙuncin da yake ciki ne, balle shi yanda ba ki ɗaya abunda ke zuciyarsa ya bayyana a saman fuskarsa...Farhana ko kaffara ba zanyi miki ba mutumin nan yana da ciwo a tare da shi, wannan ciwon na damuwa da yake roƙon Allah dare da rana ya magance mishi, kuma wataƙila Allah ya sakoni cikin rayuwarsa dan

Please Login or Register in order to submit comment