Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaske kana sona kayi min buking jirgi yanzu, zuwa anjima zan dawo gida". "ki dawo kuma? Wani abu ya faru ne?". Nace da shi,"a'a Baba babu abinda ya faru, kawai zan dawo ne na gaji da zaman". "a'a ban yarda dake ba ki dai faɗa min gaskiya, ko Hajiya tayi miki wani abu ne?". "ko ɗaya Baba, mun gama gaisawa da Hajiya kuma dama ai ita nazo gani, don Allah Baba ni dai a biya min kuɗin jirgi yanzu kujeran mutum biyu, yau nake son dawowa". "tom shikenan, Allah ya dawo min dake lapia". Kai tsaye wani private hospital muka wuce, ƙwararren likita na nema, aka ƙara treating ciwukan Yayana sosai, dan sai da aka sauya masa bandage, aka kuma lodo mana magunguna kamar me, banda allurorin daya sha. Bayan fitowanmu muka nufi resturant, ordering lafiyayyan abinci na sa aka mani wanda nasan Yayana zai san ehh yaci abincin daya amsa sunansa abinci. Gaba ya saka abinci ya kasa ci sai ido daya ƙura min, dana kalla baida niyyan ci na ɗauka spoon na kai bakinsa ina cewa, "oya haaa". Bai buɗe bakin ba sai neman sauke hannuna da yayi. Na ɗan tsuke fuska nace, "Yayana zafa kasha magani naka ne, ko baka so ciwonka ya warke da wuri?, to idan kai baka so ni ina so, plsss kaci abinci idan ba so kake nasa maka kuka ba ka rasa yanda zaka yi da ni, yanzu mutane suzo su tafi da kai a kuma sanyaka a cell". Na faɗi hakan ina kuma kai abincin bakinsa, ya dafa hannuna yana tayani kai cokalin bakinsa, haka naita bashi abincin har sai dana tabbata ya ƙoshi kana na ƙyale shi, na sauke kaina ƙasa ina ɓallo magani cike da jin nauyin kallon da yake min, na bashi magungunan duk daya dace yasha yanzu, sannan muka bar wurin muka wuce wani boutique na kayan maza. Kayan maza nake ta ɗauka sama da kala nawa, duka ƴan kanti ne kowanne haɗe da takalminsa, duk wanda na ɗauka saina kara ajikinsa don tabbatar da cewan zai masa, kuma duk wanda zan gwada mashi sai ya dace da shi, hakan yasa na ƙara jin ƙananan kaya sun kuma shiga raina, domin ni ina son naga namiji nasa ƙanan kaya amma na mutumci. Shi dai bina da ido kawai yake har na kammala na kuma riƙo hannunsa muka fito, kansa na kalla wanda gashinsa ke buƙatar aski, amma saboda ciwon dake goshinsa babu damar yi. Ina kallon Hajiya nata kirana naƙi ɗagawa, na kuma taran mota muka wuce kasuwan kwari, nan ma manyan shaddojiji na saya, yadi da boyel da huluna. Muna fitowa daga kasuwan naga kiran Baba, ina ɗagawa yace da ni yasa abokinsa ya kammala komai, bakwai na dare jirgi zai tashi, ina murna nayi masa godiya, dama cikin tunanin inda zamu wuce yanzu nake. Ko rabin awa bamu yi ba a airpot jirginmu ya tashi, cikin ƙanƙanen lokaci sai gamu mun sauka a abuja, minti biyu da isowanmu Yaya Abba yazo ɗaukana. Sai yanzu ƙirjina ya hau bugu, to waima mene zance idan na kai masu shi? ta ina zan fara bayani? lallai fa nayi wawta da yawa, ko Gwaggo da nake sa ran zata fahimce ni to zan sha gwagwarmaya kamin ta aminta da buƙatar da zani da ita. Tsaye nayi na kasa ƙarasawa gaban motar, na ɗago na kalla Yayana, hannunsa da nake riƙe da shi na saki, maganganun bakina na neman rasasu nake. "Karfa naja maki matsala a gida". Nace, "babu wani matsala ka jirani anan bari na dawo". ko dana isa wurin Yaya Abba da ƙyar nasha kansa ya fahimceni, shima don yana da tausayi ne kuma mutum ne mai son yin taimako, ba komai na faɗa masa ba, hasalima ce masa nayi a yaune na fara ganinsa. Baya Yayana ya shiga ni kuma na shiga gaba, su kaima juna musabaha, naji daɗin hakan, muna shiga gida muka tarar da Yaya Haidar shima ya dawo, kallo kawai ya bimu da shi ya amsa key ɗin part nasu wurin Yaya Abba ya wuce. Na kalla Yaya Abba nace masa, "ga wannan kayan na saya masa, ka ajiye a wurinka kamin Allah yasa muji amincewan su Baba". Ya amsa ya wuce ciki bayan yacewa Yayana yaji tsoron Allah ya faɗi asalin tarihin rayuwarsa karya ɓoye komai. A parlo nayi masa masauki, na wuce ɗakin Gwaggo domin kiranta, sai na tarar bata nan, na fito zan duba kitchen saina kalleta tsaye tayi turus tana kallon Yayana dake zaune kan kujera kansa na ƙasa baima san da zuwan nata ba. Zuwa nayi na rungumeta tare da fashewa da kuka, nan ta ke hankalinta ya tashi maganar dake bakinta ta mutu. A ruɗe ta hau tambayana mene ya faru, ni dai shiru na mata ina ci gaba da kukana, sai da ta tsawatar min kana na ɗago ina kama hannayenta na shiga roƙonta. "Gwaggo nah kene kika ce min duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi, kika ce mana mu taimakin mutumin da yake cikin tsaka mai wuya domin Allah yana son masu taimako...". "ke ni naji duk, ban son kuma wani bayanin, idan har ba za ki mani shiru da wannan kukan naki ba, kukan zan saurara ko kuma bayanin". Nai shiru ina goge fuskana. Tace, "to mene dama?". Na kama hannunta zuwa kujera ta zauna ni kuma na durƙusa a gabanta nace. "Gwaggo baya da gatan kowa sai na Allah, ko iyayensa bai taɓa sa ni ba, shine wanda na ba ki labari kika ce na fita sha'aninsa ko ki saɓa min, wallahi wallahi Gwaggo ki yarda dani shi ɗin mutumin kirki ne, jarrabar rayuwa ce ta jefa shi cikin wannan mummunar rayuwar ta shaye-shaye, Sai dai nasan ba za ki taɓa yarda dani ba sai idan kinji daga bakinsa, don Allah Gwaggo kiji tausayinsa ki taimaka masa kamar yanda muma Allah ya taimakemu ya daɗa rufa mana asiri, ina so naga ya fita daga wannan halin kuma kema nasan za ki so hakan". ta sauke ajiyar zuciya, ta kalle shi wanda tuni ya sauko daga kan kujera ya durƙusa a ƙasa. "tashi ka koma ka zauna". tace da shi tana dubansa da tausayawa, don jikinta yay sanyi da kallon yanayinsa da tayi. ta kalle ni tace, "Sabina ba wai ina ƙin ta taki bane, a'a ina tsoron yanda halin wannan rayuwar ta koma. za ki kalla mutum abin tausayi har kiyi masa kuka ki taimaka masa amma ƙarshe yazo ya cuceka, yaci amanarka, kuma kinga ke macece ina tsoron abinda zaije ya biyo baya, ba kowa ne kake yarda da shi ba yanzu. Kar muzo mu taimake shi yaci amanarmu daga baya". Sannan ta kalle shi tace, "bawan Allah tsakanin ka da Allah har zuciyarka baka da wata mummunar manufa, baka da wani ƙuduri na cutar da wannan yarinya dake tausayinka?". "Gwaggo zuciyata tsarkakkiya ce, bani da fatan cutar da wani a rayuwata". "to shikenan Allah yasa da gaske kake, ina son dukkan abinda Sabina ke so, dan haka zamu taimaka maka da iya abinda ta buƙata, sai dai bazan fasa ce maka kaji tsoron Allah ba. Bari mahaifinta yazo". "na gode Gwaggo Allah ya saka da alkhairi". Wayyo Allah nah wani sanyin daɗi naji ya baibaye ni. tace da ni, "kinje kin gudo ko. Bamu jima da gama waya da Hajiya ba tace za ki sani karki kuma zuwar mata gida. Kuma kayanki bayar da su zata yi, karta soma ganin koɗaɗɗiyar ƙafarki da sunan ɗaukan kaya". Dariya kawai nayi bance komai ba, tace naje na zubowa Yayana abinci, na miƙe naje na kawo masa abin sanyawa a baki, ina duƙawa zan aje masa yace,"na gode amma ki koma da shi, a ƙoshe nake da wanda kika ciyar dani ɗazu". Zuwan Baba Gwaggo ta zayyane masa komai. Baba ya numfasa yace da shi, "bawan Allah ka duba girman Allah ka faɗa mana wane kai". Ina kallon Yayana yay saurin rufe ido, kuma da alama tambayar ta Baba ta jefasa a wani yanayi na baƙinciki, ya buɗi baki muryar na fita da ainihin damuwar dake ransa yace,"wanene ni? Da ace nasan wanene ni da ban kasance a cikin wannan rayuwar ba, wallahi Baba ban san asalina ba. Abinda kawai na sa ni shine na taso a hannun wasu bayin Allah har na tsawon shekara biyu, suma kuma sun tsince ni ne a bola lokacin ba zan wuce shekaru huɗu ba a duniya a cewarsu. Amma mene asalina? daga ina nake? wanne gari? mene asalin sunana dana iyayena? ina zan bi in neme su? ina zan dosa? duk ban sa ni ba. Wallah summa tallahi bani da masaniyar komai a ga me da tarihin rayuwata". Ya faɗi hakan yana kuka. Baba Yace, "to su ina waɗanda suka tsinceka ɗin?". "sun gaji da riƙona shi yasa suka koreni daga garesu saboda mutane na zargin cewar ƴarsu ce tayi cikin shege. tun ban gama wayo ba nake yawo kwararo², idan na samu abinci naci idan ban samu ba hakan zan kwana da yunwa, banda matsuguni da makwanci sai kanguna, sai dai ina zuwa makarantar almajirai a duk garin dana tsinci kaina a haka har nayi sauka, sai dai duk inda na shiga jama'a ƙyamata suke suna hantarata. sigari na fara shanta ne saboda samun sauƙin abunda ke damuna, amma ni ɗin ba mutumin banza ba ne". Yanzu na ƙara jin tausayinsa ya kamani, su Gwaggo ma hakan take a gare su, Baba yace,"haƙiƙa duk wanda yaji labarinka dole ya taimaka maka in har yana da damar hakan. To ka kwantar da hankalinka, munyi maka alƙawarin zamu taimake ka mu share maka hawaye ka fita daga rayuwar ƙuncin da kake ciki, zan kuma maidaka tamkar ɗan dana haifa da cikina. Ina fatan ba zaka taɓa cin amanarmu ba". Furucin Baba ya sa ni shauƙi a ruhina ba kaɗan ba, ta yanda fuskata ta gaza ɓoye farincikin da nake ciki. "Allah yay miki albarka Sabina, lallai ke ɗin kina zuciya mai kyau tunda har kika yi tunanin taimako irin haka, tabbas nayi dacen ƴa ta gari. Kina da halin kirki da mutunci kamar mahaifiyarki". nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsun ƙafata ina jin daɗin adu'ar Baba da kuma yabona. Yayana na zubar hawaye yake yiwa Baba godiya, nima kuma yake ƙara gode min. Da wannan ya samu kyakykyawan matsuguni a cikin gidanmu, kamar yanda aka bawa Yaya Abba part nasa haka shima aka mallaka masa nasa part ɗin wanda dama shi ɗaya ne ya rage a gidan, da har su Umma na zargin Baba da munafurtarsu yake aure ne zai ƙara, to yanzu da aka bashi sai hankalinsu ya kwanta. Kowa na gidanmu Yaya yake ce masa har Baba da Gwaggo, kuma naci sa'ar ƙannena akansa. Sun zama kamar tagwaye shi da Yaya Abba, kuma duk sanda Baba zai fita office da shi yake fita, haka duk saturday and sunday yana zuwa makaranta mai suna Comprehensive collage, har mota Baba ya bashi, haka ma duk dare su kanyi zaman karatu shi da Yaya Abba don babu girman kai a tare da shi. Bayan kwana biyu na fito ɗauke da flask ɗin abinci zan kaima Yayana ɗakinsa, Ina shiga parlonsa na lumshe idanuwana ina shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake tashi aciki, na lura Yayana dai ma'abocin son ƙamshi ne. Kamin na kai ga gama shaƙar ƙamshin tuni wani mugun warin taba ya dakar min hanci, nayi saurin buɗe idona nasa hannu ina toshe hancina dan ƙiris na kwara amai. Raina a ɓace na wuce cikin ɗakinsa, zaune na hangeshi daga can ƙuryan gado yana zuƙar abarsa hankali kwance. idan da abinda ke sa zuciyata ɗaci na tsince shi a irin wannan yanayi, nafi minti biyu tsaye ina masa wani duba, baima san da zuwan nawa ba, zuciyata naji tayi zafi. plastic chair na ɗauka naje gabansa na ajiye, sannan na ɗauko kwalin sigarin daya ajiye saman table na ɗauka guda biyu, tukunna na dawo kan kujeran na zauna, ƙafa na ɗora ɗaya kan ɗaya ina girgizawa, ashana na kunnawa sigarin, duk wannan abin da nake ina kallonsa ta gefen ido yana kallona, irin kallon kissima abubuwa da dama a rai. Zuciyata na lugude na rufe idona na kai sigarin bakina ina ƙoƙarin zuƙa, da mugun hanzari ya miƙe daga zaunen da yake ya warceta a hannuna. tsawa ya doka min wadda tasa ni firgita, yana huci yake cewa, "ke ba ki da hankali ne, kinsan me kike ƙoƙarin aikatawa kuwa?". Ya faɗi hakan ransa a ɓace yana kafe ni da jajayen idanunsa da suka yi jawur. tuni idona ya ciko da ruwan hawaye har yay nasarar gangarowa saman fuskata, na zube gwiwoyina gabansa hawayena na ƙara tsananta gudu. "don Allah Yayana ka bani nasha ko nima na samu sauƙin abinda nake ji a zuciyata. Please ka bani abata nasha damuwata ta yaye, wallahi ina jin zuciyata na min zafi ne". "tashi ki bar ɗakin nan bana son rigima". Ba tare dana miƙe ba nace,"ba zan fita har sai ka bani maganin damuwata nasha, please ka bani a bata, ko kai dana zo na sameka kana sha na hanaka ne? to kuma sai kaine zaka min baƙincikin maganin matsalata".Na faɗi hakan ina ɗaga sanyayyiyar muryata. Shima gwiwoyinsa ya zube a gabana, ya runtse ido yana ajiyar zuciya, sannan ya miƙo min sigarin still idonsa a rufe kansa kuma a ƙasa a sunkuye. nasa hannu na amsa, ina karɓa ne ya buɗe idonsa, ganin da gaske shan zanyi yay saurin miƙo hannu zai kuma ƙwacewa, da sauri na ɓoyeta a bayana ina turo baki gaba.

*Gwarimpa, Abuja.*
ƙarfe tara da rabi na safe, kamar yanda tsarin gidan yake gaba ɗayansu ake haɗuwa a parlo idan za'aci abinci, amma idan Daddy na gari kenan. yanzu ma hakan ta ke, ba ki ɗayansu a dining, Mami da iyalanta, haka ma Mom da nata iyalin sai Anie dake zaune itama, Muhsin ne kawai babu. Daddy yay gyaran murya kamin yace, "lafiya Muhsin bai fito ba har yanzu? ko bai tashi bane?". "ya tashi, na barshi yana wanka ne, ban sa ni ba ko ya fito yanzu". cewar Muhsina. Daddy ya tashi ya wuce zuwa ɗakinsa, yana shiga ya gansa yana kokawan ciro riga a wadrobe, ya ƙarasa da sauri ya riƙe shi dan yana gab da faɗowa daga kekensa, rigar ya ciro masa ya saka masa, yana shafa fuskarsa yace,"me yasa baka kira wani ba?". da damuwa fal tare da shi yace,"Daddy ina so na fara sabarwa kaina da irin wannan ɗawainiyar, Muhsina zata yi aure soon idan Allah ya bata miji...". sai kuma yay shiru bai kuma cewa komai ba. Daddy ya sauke ajiyar zuciya cike da tausayin ɗan nasa, shima bai ce komai ba ya tura shi suka fita a ɗakin. kowa abincinsa yake ci baka jin ƙaran komi saina spoons, ana cikin ci ne Mami taja tsaki ta miƙe ta bar wurin, Abid ya mara ma ta baya, babu wanda yay magana bayan bin bayansu da kallo sai kuma girgirza kai. Khaleesat gaba ɗaya ta fara rikicewa domin wannan tashin da Mami tayi idan har bata bisu ba tasan sauran, ga shi jazaman ta miƙe sai Daddy yay ma ta magana, kuma zaice itama ta fara ɗaukan mugun halinsu ne. abincin ta dakata da ci, sai juya spoon ɗin ta ke, duk abinda ta ke Mom na lura da ita, bayan ta sauke numfashi tace, "Khaleesat". _innalillahi wa'inna ilaihi waji'un._ shine abinda Khaleesat ta ambata a ranta tare da jin faɗuwar gaba. tun ɗazu ta ke adu'ar Allah yasa kar Mom tayi ma ta magana, Mom ta kuma kiran sunanta amma bata amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi, ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa ce da mahaifiyarsu ta ɗaukar ma kanta, ita kam wannan dokar da ta kafa ma ta tayi mata tsauri, Mom ta wuce gban komai, saboda macece mai mutunci. doka tsawar Daddy yay dai-dai da kiran sunanta da Mom ta kuma yi a karo na uku. cikin faɗa Daddy ke cewa, "ke dan ubaki ba ki ji Mom ɗinku na maki magana bane kika ma ta banza, ko kema kin fara bin sahun uwar ta ki ne. to ni ba zan ɗauki wannan shirmen acikin gidana ba kinjini ko. idan kina so mu shirya kiyi abunda nake so idan kuma ba haka ba babu ruwana dake". muryarta a sarƙe tace, "kayi haƙuri Daddy". shine abinda tace da shi hawaye na sakko ma ta. "ba ni za ki bawa haƙuri ba". jin abinda yace sai ta juya saitin Mom sai dai ta kasa yi ma ta magana haka kuma ta kasa kallonta sai hawaye da take saukarwa. hakan yasa Mom ta fara fahimtar wani abu, dan haka ta dafata tana faɗin, "Maminki ta hanaki yimin magana ko?". ta ƙara yin ƙasa da kanta, duk tabi ta dabarbarce ta rasa abin cewa. "kar ki damu Khaleesat kinji, ki taiwa mahaifiyarki adu'a domin abunda ta ke buƙata kenan". kai kawai ta iya jijjigawa ba tare da tace komai ba. Anie na gefe tace, "Allah dai ya kyauta halin wannan Mata, ni na rasa randa zata yi hankali wallahi". ran Daddy a ɓace ya miƙe ya bar wurin yana cewa Khaleesat ta biyo shi. Khaleesat na gaba yana biye da ita a bayansa, tana kuwa yin sallama parlo Mami ta damƙo wuyanta ta fara sauke ma ta ruwan bala'i. "saketa". Daddy daya shigo ya ce da ita a tsawace. sakinta tayi ta kama ƙugu tana faman cika tana batsewa sai hure huren hanci ta ke. shi kuma yaci gaba da magana a zafafe,"wai ke Na'ima me yasa a rayuwarki sam ba ki son zaman lafiya ne. yanzu abu da kika aikata a tunaninki dacewa ne?...". ai bat bari ya ƙarasa ba cikin hargowa yace,"to me nayi kuma ni ƴar gidan laifi, ni da aka tsana ake ɗora min laifi ko da yaushe". yay ƙaramin tsaki yace, "kinji matsalar taki ai, babu wanda ya tsaneki a gidan nan sai dai kowa ya tsani halinki, wannan ban zan halin naki shine ba'a so...yanzu kawai ki kama sakin tsaki a gaban babbar mace, fisabillahi wannan ɗabi'a ce mai kyau?". ta taɓe baki ta juya masa baya tana harare harare. "to ita ɗin uwa tace da ba zanyi tsaki a gabanta ba. kaga ni fa Alhaji na gaji da wannan takurawarka akan waccan baƙar matar taka, akan abinda bai kai ya kawo ba bini-bini sai kazo ka kama sauke min buhun masifa, to ni na gaji, na gaji gaskiya". ido kawai ya bita da shi yana kallonta kamin yace, "to ita kuma Khaleesat da kika hanata kula Mom ɗin nasu mene dalili?". "saboda ba ita ta haifeta ba, ba kuma ta tayani naƙudarta ba". "amma aini ubanta ne ko, kuma na isa da ƴata ko". ya kalla Khaleesat yace, "ke kije ki tattaro duk kayanki ki koma wurin Fa'iƙa da zama har sai randa na ba ki umarnin barin wajenta kinji ko". Ta ke kuwa Mami ta lailayo wata ashar ta yarfa sannan tace, "wallahi ba zai yiwu ba. ba'a isa an maida ni ɓora ba acikin wannan gida. a rasa inda za'a kai min ƴa sai wurin kishiya saboda ba'a sona ba'a ƙaunata. tun wuri Alhaji ka sauya shawara ko kuma wallahi na ɗaga hankalin kowa a cikin gidan nan". yay guntun murmushi da takaici sannan yace,"kije gidanku sai ki ɗaga hankalin kowa acan...ai tunda har yanzu kika gagara hankali to tabbas baki da ranar da hankali, kin girma amma sam baki san abunda ya dace ba. to ki bar min gida na ba ki hutu". "mtswww". taja tsaki da ƙarfin daya doki kunnuwansu. "to sai me da hutunka dama. ko baka faɗa ba dama zan tafi, abunda kawai nake so ka sa ni shine baka isa ka kaimin ƴata wurin kishiya ba, ehh wallahi kayi kaɗan". Daddy yay mata wani kallon banza kamin yace,"ba ina nufin na ba ki hutu bane. kije na sake ki saki guda". ya kalla Khaleesat yace, "wuce muje". ya bar Mami anan da ife-ife tana zage-zage kamar mahaukaciya sabuwar kamu.



_😅Masu cewa maganar Gwaggo yayi yawa hakana zakuyi haƙuri, dan Kakata nake tunawa in akazo babin Gwaggo, mu ma tamu Kakar idan ta fara sababi sai mun matseta Babban Yaya ya juye mata coflin a maƙoshi tukunna muke samun salama😅, so ku barni nake tunawa da Marigayiyata._
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(23)*
cikin ɗagin murya yace da ni. "ba za ki bani ba?". nima na cukule ina kauda fuska nace, "ehh ai kaima ga taka can kaje ka ɗauka ka ƙarasa sha, idan kuma ka ƙoshi da itane sai ka ɗauka wani sabo a kwali ai akwai da yawa". Na faɗi hakan ina fito da ita zan kuma kaiwa bakina, cikin amon muryarsa nan mai dadi ya dakatar dani. "don girman Allah karda kiyi gangancin sha, wallahi Allah bata dace dake ba, babu abinda takeyi fa ce ƙara damuwa amma bata maganin komai...". na saki wani yalwataccen murmushi da sautinsa ya amsa acikin ɗakin. sai ya ɗago yana kallona da kallo irin na mamaki. na ɗaga masa gira nace,"Yayana wai ni zaka ma wayo ko, saboda karna sha zaka ce min haka, to naƙi wayon sai nasha nima naji irin daɗin da kake ji acikinta har yasa kake min rowa". Kasaƙe yay yana dubana yayinda yake jin wani abu ga me dani na ƙara ɗarsuwa a zuciyarsa. sai ya kulle idonsa ya wani fizgi numfashi. "na rantse ba wayo ne nake miki ba. Da gaske nake miki bata maganin komai kuma wallahi bata dace...". Bai ƙarasa ba nayi saurin sanya yatsana a leɓensa alaman yay shiru. "Yayana". Na kira sunansa kiran daya ji har ƙwaƙwalwarsa, ya zuba min ido kamar yanda na zuba masa idanuna da suka taru da ruwa. "Yayana idan har wannan abar bata dace da ni ba to na rantse da Allah kaima bata dace da kai ba, saboda mutumin kirki baya shanta, mutumin da yake jin tsoron Allah baya shanta. idan har kana son lafiyarka ba zaka shata ba, idan har kana so damuwarka ta yaye ba zaka sha ba sai dai ka ɗauka maganin damuwa kankat Al-qur'ani me girma ka karanta, wannan shine hanyar da ma'aiki ya koyar damu, ba wai mu ɗauka abinda mun san zai cutar damu ba don magance damuwarmu, ita ɗin fa haramun ce na faɗa maka haramunce mene yasa ba zaka haƙura da ita ba?". Bayan na numfasa naci gaba da cewa,"haƙiƙa ba zan hanaka damuwa ba amma ba zan bar damuwa ta dameka ba Yayana, amma ina so ka fahimci cewar ƙaddararka ce a haka domin tuni Allah ya rubuta hakan zai faru da kai, dole ne kayi imani da ƙaddararka muddin kana son cika mumini na ƙwarai. A baya na faɗa maka bayan imani da ƙaddara akwai haƙuri, Yayana kayi haƙuri da yanda ka sami rayuwa, Allah da kansa yake cewa ana cikawa masu haƙuri ladansu ba tare da ƙididdiga ba. Yayana shaye-shaye babban zunubi ne mai girma ya kamata ka nisance shi, musamman abinda zai kawar da hankali ko kuma yasa maye, Allah ya mana umarnin mu guji kayan maye zamu rabauta, da kansa acikin littafinsa mai girma ya ambaci kayan maye da aikin shaiɗan. Ka sani lallai fa aikata saɓo yana hana arziƙi ya kuma gusar da ni'ima da albarkar dukiya. Don girman Allah Yayana kayi haƙuri da ƙaddarar da ta sameka, ka bar shan abinda yake haramun". Na faɗa hawaye na sakko min. Ganin yanda nake hawaye gaba ɗaya sai yaji ya ƙara shiga damuwa, ya rumtse idonsa ya buɗe sau uku a lokaci guda. "don Allah ki bar kuka bana son zubar hawayenki". Muryana na rawa nace,"wallahi Yayana wannan hawayen ba zasu taɓa daina zuba ba har sai randa ka rabu da wannan haramtacciyar abar. Na rantse maka idan har zaka dinga shanta to ko da yaushe hawayena zai dinƙa zuba a ƙasa ne. ka faɗa min a yanzu mene ka nema ka rasa da har ba zaka iya rabuwa da ita ba? Ka faɗa min ko mene shi na maka alƙawarin samar maka shi ko don ka bar cutar da kanka in har baifi ƙarfina ba. ko kuma Baba ya gaza yi maka ne?, Adu'a fa itace maganin damuwarka ba wannan muguwar abar ba".

Please Login or Register in order to submit comment