Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama lazimin da take yi ba, sai da ta gama sannan ta juyo da kallonta kanmu tace, “oh yau naga abinda ya ishe ni, yo bakwa iya zama sai dai ku tsaya min haka aka ƙi ƙam sai kace kunzo ɗaukar fansa”. Farhana tayi dariya ta zauna kan kujera, ni kuma na tsugunna a lokacin da nake jin kamar nai fiffike na isa ga Yaya. Farhana tace da ita, “Allah ya huci zuciyar Gwaggo, ina abin ɗaukar fansa anan, sauri muke yi shisa muka ga ba sai mun zauna ba”. Gwaggo ta ajiye carbin dake hannunta tace, “to naji sarakan iya tsari, meye ne dama?”. tana tambayar ga Farhana ne a lokacin da take kafeni da ido. na ɗan ɓata fuska gudun karta harbo jirgina nace,"bafa ni kika tambaya ba da kike jiran amsa daga bakina". ta watsa min Harara kana ta juya inda Farhana take tana faɗin, “ina jinki Farhana meye ne?". “Gwaggo dama tare da Sabina zamu je gida gobe insha'Allah sai mu dawo, ina so zata rakani taron get together da zamu yi ne a school”. Gwaggo ta gwame baki tana kauda kai, sannan ta samu damar furta,“ta jira ubanta ya shigo in yaso sai taji daga gare shi”. nasan sarai ta faɗa ne dan bata so naje, kuma ba zata iya cewa Farhana a'a ba, domin a rayuwarta in akwai abunda bata so shine na kwana ba kusa da ita ba. na yamutse fuska nace, “Gwaggo dan Allah”. na rufe ido ina ƙara faɗin,"Gwaggo, Gwaggo, Gwaggo wai ce nake kece ke da iko da ni, to kuma why zaki ce sai Baba ya amince". tayi ƙwafa bata ce min komai ba, ta ɗau carbi taci gaba da lazimi. duk na ƙosa ta bani attension ɗinta na fara yi mata magiyar dana saba, amma gaba ɗaya sai naga ta sauya fuska, har Farhana ta miƙe tace ita kam tafiya zata yi, nai saurin riƙo hannunta ina roƙonta sai ga Baba yayi sallama muka amsa mashi, ya samu wuri ya zauna, yadda ya ganmu ya sashi faɗin, “duk yadda aka yi akwai abin da kuke buƙata ko...ko kuma wata matsalar ce?". ni dai nayi ƙasa da kaina, Farhana kuma tace,“Baba dama..dama muna son zuwa..”. Baba yana murmushin manyance yace, “ina jinku meye ne dama?”. tana sosa gira tace,"Baba dama ina so mu tafi gidanmu ne tare da Sabina tunda kun kusa tafiya ku barni". ina kallon yanda Gwaggo tai saurin juyowa tana kallon Farhana da ɗumbin mamaki, tama kasa rufe baki, saboda jin furucin daya banbanta da wanda ta faɗa mata a ɗazu, fuskarta kuma na haskawa da rashin yarda damu, dan yanda maganar Farhana ta banbanta tasan dole kwai wani abu da muke ɓoyewa. laɓɓanta suna motsawa da son faɗin wani abu amma sai bata faɗa ba, ta ɗauke kai ta kama ƴan waƙoƙinta na ɗan ƙwairo. "mai zai hana ni ƙin amince miki Farhana, ba ke ɗaya da kuke aminan juna da Sabina ba, ko dan mutunci da karamci irin na mahaifinki babu abinda zaki nema ki rasa daga gareni. dan haka kuje Allah yay muku albarka, gidan ku ai kaman gidansu ne itama...kya gaida Abban naki don na kwan biyu bamu haɗu ba". godiya muka yi masa sannan muka miƙe muna nufar hanyar fita. “au ko sallama don iya shege ba zaku min ba, shi ne kuka miƙa kai kamar ƴaƴan zabi”.dariya sosai Baba yayi, ita kuwa Gwaggo ko dariya bata yi ba, Farhana tace, “wallah Gwaggo kin iya yanka, salon muce wani abin kice mun ce”. “yo ai gaskiya na faɗa, ina kallo fa ko kaya bata ɗauka ba. Ko haka zata tafi babu kaya? ko da yake zumuɗi na gaba da suturta jiki ai”. na manta da Baba yana wajen nace da ita,"Allah Gwaggo kin fiya sa ido, haka zanje ɗin ni don Allah ki ƙyale ni...Baba mun tafi”. ina faɗa naja hannun Farhana zamu fita. Gwaggo ta kuma cewa, “yo ai sai kiyi kuma, da wuyanki kamar mariƙar lema, na san dai kayan Farhana ba zai maki ba ko ɗaya, dan haka ki dawo ki ɗauki dai-dai ke”. duk wannan maganar da take saboda dai a fasa tafiyar ne, dan haka ban tsaya tanka mata ba balle ta sami abinda take so, naja Farhana muka fice, muna jinta tana faɗin,"Allah dai na kallonku, ni bance sai kunji tsorona ba amma kuji tsoron Allah". A mota kuwa muna tafiya Farhana sai dariyar kalaman Gwaggo takeyi, yayin da ni ko kaɗan dariya bata zo min ba, tunanina kaf bai wuce neman mafita ba. idan muka bar garin nan sai yaushe zamu ƙara dawowa?, idan na tafi ba tare da nayi sallama da Yaya ba shin idan na dawo zan sake ganinsa?, ban ɗau tsawon lokaci tare da shi ba, amma ya fara sakewa na san da wannan, ba kullum nake kasancewa da shi ba, amma a jikina nake jin rayuwarsa ta fara sauyawa, haka zalika ajikina nake jin sauyin rayuwarsa na gab da zuwa, gab, kusa-kusa, kusan da bata da wuya wurin Allah, sai da a wurinmu ƴan adam...to amma abunda na kasa ganewa shine, tun a ranar farko zuciyata ke faɗa min kece wannan ƙaddarar, kece ƙaddarar da zaki sauya rayuwarsa, silarki komai nasa zai warware, wataƙila yanzu wataƙila sai an ɗau tsayin lokaci. kuma ayau da wannan abin farin cikin ya samemu, tun bayan dana gama murnata, haka zuciyar tawa ke faɗa min, ki tafi da shi, karki barshi anan, acan inda zaki je, acan inda zaki je zaren wata ƙaddarar zai warware, zuwa Abuja alkhairi ne...abinda zuciya faɗa tana ƙara faɗa kenan tun a ɗazu. kuma maganar Farhana data kutso cikin shirun da nai yasa ni rufe ido ina sauke numfashi, tukunna furucin nata daya fito ya tsaya a iska ya sami damar shiga kunnena.

   

_Masu Karatu what do you think will happen on this trip?_

_ta yaya zamu fassara kalaman zuciyar Sabina?_

_kuna ganin akwai yiwuwar ƙara haɗuwarsu da Al-hussain kamin tafiyarta?_

 
       
#Vote.
#Comment.
#Share.
#Mikiyawriters*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(9)*
"Sabina tun a washegarin ranar da idanuwanki suka sauka akan ɗsn wiwin kan bola na kalli wani abu acikin ƙwayar idonki akansa, sai gashi ayau abunda na gani a saman fuskanki ya ƙara tabbatar min da shi...Sabina a haƙiƙanin gaskiya ba tausayinsa kike yi ba, sonsa kike, irin son da kika kasa ganewa balle har ki gasgata shi". Nai mata wani kallo na rashin fahimtar maganar tata sannan nace,"ina kika dosa kenan? i din't get you well". tai wani guntun murmushi da ya tsaya iyaka leɓenta sannan tace,"wanda kike kira da Yayanki mana...Sabina Whether you agree or not; you love him. Kuma irin son da kinyi zurfi a ciki, since za ki iya shiga wannan yanayin na tashin hankali becouse you are going far away from him. Tun a ɗazu fa ina lure da yanda Mood naki ya sauya lokaci guda bayan kin gama murnarki, kuma dana gama karantar fuskanki, i saw nothing beyond love full of compassion". Naja wani uban dogon tsaki, wanda yasa har mai napep ɗin dake janmu sai daya juyo ya kalle ni. Cikin masifa nake ce mata,"kina raina min ajawali da yawa Farhana. Wai me kika ɗaukeni ne hala ma tukunna, kawai kin bi kin Haɗa da wani hasashenki mara kan gado kin dage akan cewan Sonsa nake. Well, I dont like him at all, I just know I feel very sorry for him. And I can do anything to see that I change his life to a world of happiness unlike the one he is in now". sai ta saki wata dariyar ƙeta tana kallona tace, "ta ya kenan?". ta kuma harzuƙa ni, na wulla mata harara na ɗauke kaina, ina kallon waje nace da ita, "I just told you karki kuma cewa ina sonsa, otherwise kuma zamu yi faɗa". "ke wallah bazan bar cewa kina sonsa ba, ai labarin zuciya a tambayi fuska, ba wai na ƙirƙiro na faɗa ba ne". Na kaɗa kaina ban kuma ce ma ta komi ba, the way I heard her hypocritically laughed, saina tsaida mai nepep ɗin na sauka, dan ba zan iya tafiya da ita tana ci gaba da faɗan wannan banzan zancen nata ba. Allah yaso na fito da sauran kuɗi a hannuna na bashi, ina jinta tana min magana nai mata banza, saboda ma karta takura ni nayi saurin tsallaka titi, har cikin ranta nasan ba taso hakan ba, to amma kuma ya ta iya, dama ni na nema mu tafi tare kuma nace na fasa. Wani mai napep ɗin na kuma tara na faɗa masa unguwarmu, yana sauke ni ƙofar gida mukai karo da Ya Abba, shi ya biya kuɗin motar saboda ni babu a hannuna. Fuskata a turɓune na shigo ina sallama a ciki, sai dai duk ɓacin ran da nake ɗauke da shi, show ɗin Gwaggo da Baba sai ya kawar da shi, take na fara ƙyalƙyala dariya. Sai a lokacin ne ma suka san da shigowata, Baba ya dube ni zai yi magana Gwaggo ta riga shi tana ce min, "mutan kan naki sun sauya miki ra'ayi kenan?". Ina zama kan kujera nace, "ɓata min rai tayi shi yasa na fasa binta, dama ba wata uwar zata tsinana min ba, bare ta sani gaba tana min dariya kamar taga mahaukaciya sabon kamu". tace, "oho miki dai, mai jure ma halinki sai ita ɗin. Ke nifa da ni ce ita da tuni mun jima da gama ɓaɓewa dake, yo ina dole a nan, zamaninmu idan naga ƙawa na min iya shege saboda taga ina sonta sai na nuna mata ba'a haifi wanda ya haife ta bama". "to su Hajiya Gwaggo Allah yasa ba ke ɗin bace, kuma Allah yasa bata nan bare ki zugata. Nima fa Gwaggo ko ni ɗin, da kece ƙawata yasin ba zan iya zama dake ba". Ai tun ban rufe baki na ba tace, "yo ga mai mugun hali ke kuwa ai dole kice haka. Yanzu ai idan baki zauna dani ba kya zauna da matan ubanki da basa ƙaunarki". Yaya Abba dake shigowa yace da ita, "don zamu koma can ai ba yana nufin zamu zauna gida ɗaya dasu bane". Gwaggo ta taɓe baki tace, "to dan masu iya magana ai bani na faɗa ba, ubanka shi ya faɗa gashi nan a zaune sai ka tambaye shi". tana maganar tana hararsa. Sai kuma taci gaba da wa Baba faɗa tana cewa, "nan inace lokacin da Allah ya jarabceka da karayar arziƙi, cikin ƴaƴan su babu wanda yayi yunƙurin taimaka maka har zuwa yanzu da muke ciki, ni kaina daga lokacin suka bar zuwa gaishe ni saboda baka da abinda zan sanya kayi musu. Amma kake ambaton zamu tafi da iyayensu, saboda gaka wanda yafi kowa zuciyar imani, to ni ban yarda ba". Ni dai ban gane akan mene suke magana ba, amma yanda naga Gwaggo ta rikeɗe nasan maganar kishiyoyinta akai, domin Allah'n daya halicci Gwaggo bata ƙaunar sunan kishiyoyinta, sai kace yanzu ne ta ke zaune da su suke bugawa, idan tayi wani abunma sai kai zaton ko ita ɗaya ne aka taɓawa kishiya. Baba ya numfasa, cikin magana ta sigar lallashi yace, "Gwaggo ai ita rayuwa idan zakama mutum abu karka dubi halinsa, duba Allah sai kayi masa, kuma idan Ubangiji ya azurtaka da shi, the more kana badawa the more kana ƙara samu. Hadisi ne fa guda karka rama sharri da sharri...". Ai tun bai kai ba Gwaggo ta dakatar shi, tana jefa goro a baki tace, "kai ba dama a fara magana sai ka nemi yanda zakayi ka kashewa mutum zuciya da faɗin Allah da ma'aiki. To naji na yarda amma fa da mutum guda zamu tafi, kaje goben kaiwa Addagana magana ita kawai nace bance da wannan mai zubin sauron ba. Domin ita a rayuwarta sam bata da mutunci, itama Addagana arziƙi ɗaya taci ta taɓa sammin gishirin miya amma wallah da bazan yarda ta ɗanɗani arziƙinka ba Auwalu, saboda matar nan lokacin zaman mu iya shaƙa na shaƙa a wurinta, to da yake ma ni ɗin ba kanwar lasa bace sai muka yi dai-dai da ita. Itako waccen mai yanayin dusar awarar ko bayan raina ban yarda da sisinka ka kashe mata ba, domin ta cutar dani iya cutarwa saboda tana gani na ƙwaila dani a lokacin, haka ta haƙa rami ta binne borkono da citta da sauran barbaɗenta ta ƙyallo mu ta mudubi ni da Sahibina amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai kaidinta ya koma kanta, hakan bai isheta ba sai da tayi nasarar haɗani faɗa da shi na tsawon mako guda, ya daina min magana ya daina saurarona. Kai Allah ya isa tsakani na da Hussaina, insha'Allahu sai ta wayi gari idonta ɗaya ya koma ƙeyarta na gaban kuma ya ma ce". ta faɗi hakan tana matsar ƙwalla, Baba kuma na bata haƙuri, ni da Yaya Abba muka tafa muna kwasar dariya muka ce, "Gwaggo; Gwaggo; Gwaggo; ikon Allah...Hajiya Gwaggo a daina ruƙo dan Allah, duk abunda ya wuce ya riga ya wuce, shekaru aru aru kinƙi cire abu a ranki". ta ɗago ta kalleni aka wurgan harara aka ce, "Sabina ina jiye miki ranar da zaki wayi gari ki kalla kishiya a cikin gidanki, ina mai faɗa miki karda ki sa ke kizo wurina na baki tofin Allah tsine don kifi ƙarfinta, saboda kina ɗaya daga cikin masu cutar da zuciyata, duk sanda nake bada labarin zamana da kishiyoyi maimakon ki tausaya min, a'a sai dai ki bushe da dariya kamar wadda aka bugawa guduma a tsakiyar ka jini da ƙwaƙwalwa suka gauraya suka haɗe. Ko da yake yau ai kin nuna min matsayi na a wurinki, tunda mutuwar Sahibina ma baki iya cewa Allah ya jiƙan rai ba sai dariya to ai kuwa babu abun alkhairin da za ki iya min". ta dubi Baba shima ta jefe shi da harara tace, "kai kuma saboda ƴarka ce shi yasa ba zaka iya tsawatar mata ba akan tsiyar da take shuka min. Wannan yarinya ai da miji ɗaya muke aure baƙin cikinta ne zaisa na bar mata gidan". Baba yace, "Gwaggo ke da jikarki ai bana shiga zancen ku ba. Kefa kika ce duk wani mai ƙaunarki to ya zuba muku ido a sha'aninku ke da ita, saboda tsakaninku ko aure ba zai raba ba, ƙaunace ta har abada". tace, "wannan magan kuwa na soke ta a yau ɗin nan. Saboda itama halin Hussaina gareta, a fuska su nuna suna yinka amma a zuciyar su kamar su kasheka, ta bayan gida su dinga maka mugun ƙullin da zasu daina ganinka a raye". Ina dafe ƙirji nace, "kai Gwaggo yanzu duk wannan mugun halin ni ɗaya, Ki sassauta min mana kona sami rangwamen zafin zuciya". "karki samu sauƙin zuciya ki shekara ki shekare a cikin zafinta ba damuwata bane, mara kirki kawai". Yaya Abba yace, "Gwaggo mita; to wai ita Inna Hussaina me tayi miki haka ne da kika sanyo ta a gaba, kika kasa mancewa da abunda tai miki tun kina amarya". sai ya riƙe haɓa yace,"kai Allah ya raba mu da riƙon abu a rai irin naki". ai yana rufe baki ta furzar da goron bakinta ta hau sababi,"au wato ni ce ma na sanyota a gaba kenan. To dan yayar ubanka bari kaji abinda tayi min, matar nan saboda baƙar azzaluma ce, na wayi gari wani dare na aza sanwar tuwo, nazo kaɗa kuka bani da ita, gashi ana ta ruwan sama bare na aika yara a sayo min, haka na dinƙa safa da marwa a tsakar gida ina gudun Sahibina ya dawo ban kammala girki ba, Ashe idonta na kaina, taje ta ɗauko kuka a ɗakinta kamar ta Allah ta bani, ina godiya ina jin daɗi nazo na kaɗa miya, tun ina kaɗawa naji jiki na yay sanyi saboda duk babu yauƙi amma sai na barta a ko tsohuwar ajiya ce, sai da Sahibina yazo cin lafiyayyan tuwon dana tuƙa, miyar kuka tace shani kaji daɗi, ashe ƴar tahalikar nan lalle ta bani na kaɗa, tana jin Sahibina ya fara faɗa ta fito tana ce min kayya amma Hannatu wannan abu baiyi daɗi ba, dama sai dana ce miki karki saya wannan kukar bata da kyau ashe ma ƙarshe lalle ne, da tun farko kin karɓi guntuwar dana baki da ba haka ba. kai kuji min baƙar makira, ai ranar naga ƙarshen makirci da iya kissa ganin idanuwana biyu, ranar dai ban ƙwaci kaina ba a wurin Sahibina ba, amma nima dana tashi nayi ƙundun bala sai dana juye mata Maɗaci rabin kwano a cikin damun kokon safe, akan hakan sai data karɓi farar takarda a wurin Sahibina, tsabagen farinciki sai dana yi sadakar ƙuli... Saboda haka wallahi ba za'aje Babaja da ita ba, sai dai ta dawwama a ƙauyen ɗan kande". ta dubi Yaya Abba dake dariya cikin ƙufala tace, "ɗan banza mai kama da ƙosai". Wani abun mamakin sai gani muka yi Gwaggo ta fashe da kuka, duk sai kuma hankalinmu ya tashi, na matso kusa da ita muna ta jera mata tambaya. sai cewa Baba tai, "wallah Auwalu ina tunanin tafiyar nan ne na bar bazawari na, Ya'u mai kayan miya mutumin nan na ƙaunata har ransa, sai dai bazan iya cin amanar Sahibina, domin kuwa har Aljanna shi ɗaya ne zaɓina. Yanzu dai shi Ya'u ka bashi haƙuri kace ya nemi wata amma ban yaudare shi ba, babu yanda na iya ne da ƙaunar Sahibina, duk wanda na aura bayansa tabbas naci amanar ƙauna". Kunyar maganarta a gaban Baba yasa na miƙe na wuce ɗaki ina dariya, banma san lokacin da Baba ya tafi ba, sai can na fara bacci naji shigowarta itama zata kwanta.
To haka muka fara shirye-shiyen tafiyarmu, ni dai duk bana cikin hayyacina, idan ka ganni kamar wadda tayi sati tana rashin lafiya, duk na faɗa, ramin idona ya ƙara zurfi. Tafiya ce ta farinciki amma ni babu wannan farincikin sai tarin damuwa daya farma ni, walwalata duk ta tafi, nayi wani suku-suku dani, Gwaggo na lure dani amma bata ce min komai sai dai ta bini da ido tana faɗin, "hmmm". Farhana itace mai kwantar min da hankali idan ina damuwa, itama yanzu bata tani saboda tana cikin damuwar zanyi mata nisa, ni kuma ina fushi da ita. Ko gidanmu bata zuwa yanzu, idan ta kirani a waya ma ƙarƙari tace, "Ina fatan kina lafiya". Da zaran nace ma ta, "ehh Lafiya, hope kema lapia?". shikenan zata kashe wayanta ba tare da ta bani amsar tambayana ba. Yauma naje wurin Yayana na dawo, cikin ɗakinmu na shigo na sami Gwaggo na haɗa sauran kayayyakinmu, kasancewar gobe ne tafiyan mu, na nemi wuri na zauna na haɗe kai da gwiwa ina rera kuka, kun san mene ya sani kuka? Yayana! Karo na huɗu kenan yau ina zuwa wurinsa bana samunsa, babu shi babu dalilinsa, babu kuma wanda zan tambaya yace min ga inda yake, wannan dalilin yasa hankalina tashi, na nemi natsuwar zuciyata na rasa, sai aikin bugawa da sauri da sauri da take, tambayar da nake wa kaina wai anya zan iya ci gaba da numfashi ba tare dana san halin da yake ciki ba? ina ya tafi tsawon wannan kwanakin? Na rasa amsar hakan, sai na kuma fashewa da kuka, ina rayawa a raina in har Baba ya dawo zance masa mu fasa tafiyar nan har sai zuwan ranar da Allah ya dawo da Yayana, idan yaso sai na fa ke masa da wata ƙaryar dana san zai ɗoru akanta, tunda duk abinda nace yanayi.
Ina wannan kukan ne naji Gwaggo na cewa dani, "ke ɗago ki kalle min nan ki bani amsa sai ki koma ki ɗora daga inda kika tsaya". Tana faɗa da nuna halin ko'in kula akan kukan nawa, wanda ni kuma hakan ke ƙara bani haushi, dan atleast ina so a kula dani a wannan lokacin. "yo baiwar Allah ina miki magana ne fa, kuma nasan kin jini amma kinyi uwar kunnen shegu dani". ta kuma cewa dani, sai a sannan ne na ɗago, a tunani lna wani abun arziƙin zan gani, sai ta wani nuna min gajeran wandon Yaya Abba tana faɗin, "kema naga ƴar ƙwallo ce, za ki san takan amfanin kayan, wannan naga ya tsufa da yawa zai yiwa Abba amfani ko nasawa almajirai saboda naga mazaunansa duk sun ɓuɓɓule, kuma wannan rigar ma naga hammatar ta ɓeke, kuma duk bashi-bashi suke, na bayar ko na bar masa kayansa?". Haushi baisa na bata amsa ba, na maida kaina naci gaba da kukana, sai dai a wannan karan kukan zuci ne nake bana hawaye ba. ina jin Gwaggo na doka tsaki tana faɗin, "karki bani amsa ɗin. Idan kinji haushi kin amsa ke ɗin ba rainona bace, miskila kawai uwar nurƙufanci, kici damuwarki ke kaɗai tunda babu wanda ya isa ya tambayeki abunda ke damunki ki faɗa masa. Ni kuma idan na ƙara tambayanki tagwagwa ta gwagutse min". Har dare Gwaggo bata sake kulani ba kuma nima ban kulata ba, ni haushina ɗaya akanta da taƙi zuwa ta lallasheni naji sauƙin abinda ke damuna, sai dai ina jinta tana ta kai komon haɗa kaya, tana yi tana waƙarta cikin nishaɗi, tai waƙar Mamman shata da ɗan ƙwairo, ta kuma juya tayi ta yarensu na buzanci. Idan tayi ta gaji ta hau mitar ni da Yaya Abba bamu da tausayi sam, tana tsohuwa da ita amma mun barta da hidimar haɗa kaya, to walle ba don ta gaji da wannan gidan mai rufin kwano da yoyon ruwa ba, sai dai a fasa tafiyar. haka Ina jinta da Yaya Abba ya dawo yana tambayarta abincin dare, tace yaje ya duba kitchen akwai daddawa ya daka yay kwaɗo idan zai iya ci kenan, idan kuma ba zai iya ba ya bar mata abinta idan aljanun kaina sun sake ni ƙila ni naci, idan kuma duk ba zamu ci ba sai a barshi ya zama rabon almajiri, domin itama baci zata yi ba, ita da abinci sai na sabon gida. Baba daya zo yaji ni shiru ban fito ba, suna tsaka da hira shi da Gwaggo da Yaya Abba yake tambayana ina ina, tace da shi, "tana can ƙuryar ɗaka tana fama da aljanun miskilancinta, yau ban san uwar da akayi mata ba har suka zo ɗaukan fansa. Ƙilan kai idan ka kira ta tazo tunda suna jin maganarka sa tafi, amma ni da basa gani na da gashin ido ko ta kaina ma basa bi". Tana maganar ne tana shan raken da Yaya Abba ke ɓare mata. Baba ya ƙwala min kira, na ansa ina miƙewa, ban fita ba sai dana saita natsuwa ta, na sami guntun ruwan ledan pure water na wanke fuskana, saboda a rayuwata bana so naga Baba ya fuskanci ina ɗauke da damuwa, yanzu sai hankalinsa ya tashi. Duk yanda naso ɓoye damuwan abun yaci tura, domin kuwa ina zuwa Baba ya shiga tambayana abunda aka mani, kamar nace masa bana son tafiyarmu sai kuma naga rashin dacewan hakan, na ɗago na dube shi nace, "Baba babu komi". "ba kya min ƙarya karki farata a yau, mene aka yi miki?". sai na tsinci bakina da faɗar abun kwata-kwata babu lissafinsa cikin kaina. "Baba ina fargaban zaman mu da su Aunty ne". Yace na taso na dawo kusa da shi, cike da kulawa da kuma lallashi yake ta bani baki har naji zuciyana ta fara sanyi.
Washe gari tunda ƙarfe takwas Baba ya kira waya yace to mu shirya ƙarfe sha ɗaya ne zamu tafi. zai aiko mana driver ya tafi damu, shi kuma zai tafi da matansa. Ina jin hakan nayi maza na faɗa wanka, cikin sauri na shirya na fito na gillawa Gwaggo ƙaryar data hau ta zauna akai, domin kuwa ce nayi ma ta Malam Albani ne ya kira yace yanzu naje makaranta suna son ganina, da yake zancen na makaranta ne bata musa ba tace,"Sai kin dawo Allah ya kiyaye, amma kiyi sauri kin dai ji abinda gyatuminki yace".
"insha'Allahu yanzu zan dawo Gwaggo. Amma fa sai kin bani kuɗin mota saboda nafi sauri, kinga bada Farhana zamu tafi ba, koma da ita ne ɗin motanta ya lalace". Nan da nan ta kunce gefen zanenta ta ɗauko dalleliyar ɗari biyar ta bani, yanzu tana ji da

Please Login or Register in order to submit comment