Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na zama sila...shi yasa ko dana ganshi naji ba zan iya yin yanda kike so ba...so please lets go, i beg you". ganinta nai kawai ta wuce ta gabanmu bakinta na faɗin,"tabɗijam, ko duniya za'a tasa tafiya da wannan ɗan wiwin ba'a motata ba, don babu abinda zai sanya ni yayibar mahaukaci na kama tafiya da shi, ai yasan da gidan nasu yazo ya zauna anan....mtswww ke da kin kalla ma fa kinga alamun rashin lafiya a tare da shi, saboda haka kinga tafiyata". "kece ki ke masa kallon mara lafiya amma ƙalau ya ke kamar yanda muke". "a'a ba dai kamar ni ba kam, me lafiya dai ba zai zo kusa da bola ya zauna ba har yana shan sigari. Ai da gani kin san waye, cikin biyun dole ɗaya, mahaukaci ko kuma riƙaƙƙen ɗan daba, ki sake kallonsa da nazari tukunna ki dube yanayinsa da idon fahimta". ta ƙarasa faɗa tana nuna shi da baki a yatsine. Kallon Farhana kawai yake yana ganin yanda ta ke banka masa wata uwar harara. na san yaji rashin daɗin abinda tace, amma gani nake kamar nafi shi rashin jin daɗin hakan.
"haba don Allah Farhana, ya za ki dinga aibata ɗan'uwanki musulmi da irin waɗannan kalmomi marasa daɗi, bayan ba ki da masaniyar komai a kansa. Ki tuna fa addininmu ya yi hani da tozarta musulmi". "hmmm! lallai har yanzu ba ki da wayo Sabina, kuma indai za ki ci gaba da biyewa wannan zuciyar taki zata kaiki ta baroki akan saurin taimako da kuma tausayi. kuma ina mai gaya miki tun wuri ki bar wannan ɗan shaye-shayen kizo mu tafi, don wallahi irinsu ne tantiran ƴan iskan nan masu lalata ƴaƴan mutane, waɗanda bakin uwa ya gama binsu". maganarta ta ƙarshe tai wani dukan ganga a zuciyar Alhussain, dan haka yay saurin rumtse ido da gaggawa ko ya sami sassaucin raɗadin da maganarta ta haifar masa. yau rana ɗaya kuma rana ta farko da aka taɓa faɗa masa kalma mafi muni da ɗaci a rayuwarsa. lalata! bakin uwa!, to shi da bai taɓa ma yin gaba da gaba da wata ƴa mace ba ta ina zai lalatata? wama ke raɓarsa daga maza har Mata? Babu! Shi ɗaya ne a rayuwarsa, kuma bashi da iyaye balle yace yana da uwar da bakinta yabi shi...amma sai gashi yau har ana kiransa da ɗan daba, zai iya rantsewa a iya tsayin rayuwarsa baya tunanin ya taɓa riƙe wuƙa ko makami, yaji yana shan wiwi amma baya taɓa ɗarawa daga kanta, itan ma dan ya kanji sauƙi ne idan yasha...sai gashi yau ƙanƙanuwar yarinya na gaya masa son ranta ba tare da ta san shi ɗin waye ba kamar yanda shima bai san kowaye ba. ƙwayar idonsa tai masa nauyi kamar an baɗa masa ƙasa a ciki, buɗe su yayi da matsananciyar damuwa gami da ɓacin rai, bai da ikon yi ma ta komai saboda ya cancanci a faɗa masa dukkan wasu kalmomi masu muni. idonsa yana bin Farhana da kallo da saƙa wasu abubuwa cikin ransa, yana jin tsakin da ta ke taja acikin kansa.
sai ya cire hannunsa daga nawa, na dube shi da rashin jin daɗin abinda Farhana tai, tausayinsa naji ya daɗa kamani, ko da wannan ɗaga ƙafar kaɗai da yayi mata zan iya shaida na rantse yana cikin wannan halinne kawai dan bashi da yanda iya, amma ba da son ransa ba. Muryarta a sanyaye nace da shi, "don Allah Yaya kayi haƙuri da abinda ƙawata tayi maka, rashin fahimta ne ya janyo hakan, amma a madadinta ina mai baka haƙuri, na san kowane aka yi masa ba zai ji daɗi ba, karda ka sanya ɓacin ran hakan a ranka ya kuma haddasa maka damuwa". sai kawai naji ya buɗi baki yana cewa, "kema kar da ki damu, dama na shirya fuskantar wannan ƙalubalen, irin wannan kalaman ba zasu dameni ba, ko da finsu ne ma ba zanji ciwo ba...da sannu kema za ki faɗa min su ne, wataƙila yanzu, wataƙila zuwa wani lokaci". "Allah ya kiyaye bana fatan hakan ko da ba akanka ba". sautin muryarsa ya washe da ce min, "ke kam wai ba kya da tsoro ne?". Ya faɗa murya da ɗan ƙarfi. sai nace, "Allah shine abin tsoro ai, kuma kai ɗin ai ba kayi kama da mugu ba da har zan tsorata da kai. Yanzu dai kazo mu tafi kaga magriba na gabatowa kuma Gwaggo nah zata mani faɗan ban dawo da wuri ba". "baki sanni ba, baki san wane ni ba amma kina nema na raɓe ki, nace miki bani da gida, anan wurin nake rayuwa ta. Shin wai baki gudun na cutar dake ne ke kam?". na marairaice idanuwa ina dubansa da rashin jin daɗi nace, "Annabi S.W.A yace *KAMATUDINI TUDAN* (duk abunda kayi sai anyi maka). kai ɗin kana da Mama, kana da Ƙanwa, ƙilan ma kana da Yaya mace, nan gaba zaka auri mace, kuma ta iya yiwuwa ka haifi ƴa mace. Kaga kuwa nayi amanna da cewar ba zaka cutar dani ba saboda ba zaka so wani ya cutar da naka ba". sai yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace min, "ki dinga kiyayewa. Yanzu kibi bayanta ku tafi gida, kar Gwaggo'n ki tayi miki faɗa". maganarsa ta haddasa jikina yin sanyi, naji raina fayau, nai ƙasa da idona ina kallon yatsun ƙafata nace,"to idan na tafi kai fa?". "so nake ki yarda dani, bana magana balle har ta kai ga nayi ƙarya. inda kika ganni anan nake rayuwata tsayin shekarun dana faɗa miki, idan har nabi ki bani da wani gida da zan nuna miki nace ina da alaƙa da shi. don haka ki tafi kawai ki ƙyaleni". "to amma kayi alƙawari idan na tafi na barka ba zaka kuma shan wannan abar me cutarwa ba?". sai ya rufe ido ya ɗan kauda kai gefe, ba zata taɓa fahimtarsa ba, ba zata taɓa ganewa ba. "akan mene zan ɗauki alƙawarin da bazan iya cika shi ba? Kawai ni dai ki tafi kuma karki kuma dawowa inda nake". "kana nufin ba zaka iya daina shanta ba kenan? Na faɗa maka fa shanta haramune, ko ka fi so ka aikata abunda Allah ya haramta?". idonsa a kulle ya shiga girgiza min kansa alaman A'a. "to in dai haka ne, don Allah kar ka kuma shanta daga yanzun nan. Kaga shi yasa ma mutane ke maka kallon ɗan iska, kuma alhalin kai ɗin ba shi bane. Wannan ba zata yi maka maganin damuwa ba sai dai ta cutar da kai, ka miƙa lamuranka ga ubangiji sai kaga ya yaye maka damuwar dake tare da kai. Ƙilan mu kuma haɗuwa ƙilan ba zamu kuma haɗuwa ba, amma ina roƙonka da Allah karka kuma shan taba, ka nisance ta nisa na har abada kaji Yaya". kawai sai na kalla ya runtse ido yana jijjiga min kansa alaman yaji kuma zaiyi yanda nace. har cikin raina sai naji daɗi, na saki Murmushi kana nace masa, "na gode Yaya nah. Kuma ka sani idan ni bana ganinka Allah yana kallonka, dan haka ka riƙe alƙawarin daka ɗauka...alƙawari yana da girma, kayana ne karka manta da wannan". na juya cikin rashin kuzarin jiki na barshi a tsaye, yayin da nake jin kallonsa da yake bina da shi ajikina, kuma har sanda na shiga mota na zauna idonsa na kaina, zuwa lokacin da Farhana ta yiwa motar key sannan naga ya juya ya koma inda muka fito.
kuma tun bayan zaman Alhussain da kuma bayan tafiyar Sabina, tunaninsa guda ɗaya ne yake yi, _dama akwai ranar da zata zo wani ya kusance shi da nuna kulawa gami da tausayawa irin haka? Dama a cikin Mata akwai masu uzuri da kirki irin haka?_
tambayoyin da yay ma kansa kenan, a yayin da hoton Sabina ke haska mishi a ido da amsar tambayar tasa. ta kasance a tare da shi alhalin bata san shi ba, bata san waye shi ba, ba zagi, babu ƙyama, babu walaƙanci, babu tozarci, sai ƙoƙarin janyo shi a jikinta domin ta nuna masa illar halin daya jefa kansa ciki, halin daya na zaune acikinsa ne ta dole bisa ƙaddara. ayau kuma sanadinta yaji yana bala'in son kasancewa da ahalinsa, ya gansu ko da ace ba zasu kalle shi ba, ko da ba zasu karɓe shi ba, ko da zasu wulaƙanta shi. Wani abu mai zafin gaske yaji ya taɓa zuciyarsa, *SHIN WANENE SHI?*, *SU WAYE IYAYESA?*, *MENE SILAR KASANCEWARSA A WANNAN HALIN*, *YAUSHE ZAI FITA DAGA WANNAN ƘANGIN RAYUWAR?*, *HAR TSAWON WANNE LOKACI ZA'A ƊAUKA KAMIN ƘADDARARSA TA SAUYA FUSKA?*... sai yaji zuciyarsa ta matse sosai, ta yi rauni, ya dafe goshinsa ya kuma runtse idonsa da ƙarfin gaske, ya cije leɓensa na ƙasa hawaye masu zafin gaske suka shiga malala a fuskarsa, sai kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi tare da kifa kansa a saman cinyarsa yana riƙe da kansa dake mugun sara mishi tamkar zai bar jikinsa. wannan yanayin, wani yanayi ne da yake tsintar kansa a duk sanda ya rasa amsar waɗan can tambayoyin, ya ɗau tsawon lokaci a haka cikin rera wannan kukan mai ƙaramin sauti tamkar ba matashin saurayi ba, tukunna ya miƙe ya tafi masallaci dalilin kiran sallar daya ji ana yi, bai baro cikin masallaci ba har sai da akayi sallar isha'i kana, nan ma sai da za'a rufe masallacin sannan ya fito. A dawowarsa ya tsaya a dai-dai inda motar su Sabina tayi parking ɗazu, kallon wajen yake da haskawar hoton abunda ya faru a ɗazu, bai san dalili ba, amma haka kawai yaji yana so yarinyar ta ƙara kasancewa da shi. sai yasa hannu ya matse idanunsa dake rufe, ƙasan zuciyarsa na raya masa da cewar _ko zata sake dawowa?._


*Please don't forget to comment, vote and share.*
*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(3)*
da wannan tunanin ya samu wuri ya zauna, zuciyarsa tana cigaba da tunani iri-iri, tunanin duniya, tunanin rayuwarsa da tunanin yarinyar da ta fara raɓarsa tun bayan sanin kansa da yay. motar Farhana na tsayawa ban ce komai ba na buɗe murfin motar na fita cikin fushi ba tare da ko na dubi inda Farhana ta ke ba, can ƙasan murya na furta,"nagode ki gaida su  Hajiya". tace da ni,"zasu ji insha'Allah, amma ba ki ɗauka kayan da muka saya ba”. wani irin kallo na bita da shi ta ƙasan ido, ban ko yunƙurin amsa ma ta ba, dan abunda tayiwa wancan bawan Allah'n ji nake tamkar Yaya Abba da muke ciki guda ta yiwa, shi yasa tun tahowarmu nake fushi da ita, kuma ina ganin kaman ba zamu shirya ba har sai mun koma wajensa ta bashi haƙuri yace ya haƙura tukunna.
ban rufe ma ta ƙofa ba sai dana ja tsaki tukunna na fara tafiya na ɗauka hanyar gida, ganin hakan yasa Farhana fitowa daga motar ta buɗe boot ta ɗauko kayan da muka saya ta biyo bayana da shi. A ɗan ƙaramin tsakar gidanmu wanda yasha shara baka ganin ko da ɗigon datti, na tarar da Gwaggo tana goga kuɓewa, sallama kawai nayi na shige ciki, ban ma san ta amsa ba ko bata amsa ba, kuma ajikina nake jin yanda Gwaggo ke bin bayana da kallo, kuma shirunta ya bani tabbacin tana tunanin yanayin da ta ganni aciki ne. Farhana ta shigo, Gwaggo ko amsa sallamarta ba tai ba tace mata,“yauwa yanzu kuwa zance to ya akayi baki shigo ba, ashe kina bayanta, meye sa me ta ne? naga daga sallama ta shige ciki, Allah yasa lafiya ne". Farhana tace, “lafiyarta lau, ai kin san halinta da ɗan banzan saka damuwa a rai, wai fa wani mahaukaci ta gani a hanyarmu ta dawowa gida shi ne ta ɗaga hankalinta haka". ta duƙa a gaban Gwaggo ta aje ledar hannunta da cewa,"ni dai zan wuce Gwaggo sai wani lokacin, ga shi wannan nata ne”. Gwaggo ta maida hankalinta kan kuɓewar da ta ke gogawa tace, “to madalla, kyace ina gaida Hajiyarku”. Daga haka Farhana ta gyara zaman glass nata ta fice. Maganar Farhana ta tsayawa Gwaggo a rai, don kuwa sarai ta san halin Sabina, zata iya yin komi akan wannan mahaukaci kamar yadda Farhana ta faɗa mata, to amma meye nata na damuwa haka, koma meye dai zata ji. ina kishingiɗe jikin pillow naji Gwaggo na Ƙwala min kira, kaman ba zan amsa ba sai kuma na buɗe ba ki nace da ita ina zuwa, na miƙe jiki babu ƙwari kamar mara lafiya na fito. na rakuɓe gefe guda ina jiran abinda zai fito daga bakin Gwaggo, abunda naji tana faɗi ne yasa na ɗaga ido ina dubanta. “wanne Mahaukaci ne wannnan har da zai ɗaga maki hankali haka?, Sabina kin san halina fa sarai, ina da sauƙin kai amma bana son shashanci, waye shi?”. sai naji zuciyata tayi min nauyi saboda kalmar mahaukaci da Gwaggo tayi amfani da ita wurin kiran Yaya da shi, na turo baki gaba ina daɗa dubanta ta cikin glasses nawa nace. “don Allah ku daina kiran shi da mahaukaci, baku san yadda zuciyata ta ke duka ba, kalmar mahaukaci ai bata danganci mutum musulmi ba, mahaukaci ai sai dabba, shi kuma mutum ne mai kamala, don a maganar shi bata yi min kama da mai taɓin hankali ba, kawai halin rayuwa ne ya mayar da shi haka”. Zuru Gwaggo tayi tana dubana, maganganuna sun bata mamaki matuƙa gaya, cikin faɗa-faɗa ta kama cewa, “yo wai ke shin kin yi hauka ne, a ina ma kika gan shi ne tukun har kike faɗin haka, kin san dai Farhana ba zata maki ƙarya ba ko?”. “Gwaggo Allah ba mahaukaci bane, kawai dan ta gan shi a cikin kango kan bola shikenan sai ta kira shi da mahaukaci, idan ita aka faɗawa ɗan uwanta haka ai ba zata ji daɗi ba, ni idan bata yi wasa ba ma sai na daina kulata akansa wallah”. Gwaggo ta wurgo min daƙuwa tana faɗin,"ungo wannan, nace ungo, yau naji Mace, ke anya ma kuwa da kike je wurin shi bai shafa maki haukan ba, wannan wace irin macece ke, wai ke baki san duniya ta lalace haka ba, waye ke yadda da irin su musamman ma masu zama cikin kango, wannan waya san adadin yaran daya lalata daya fake a cikin nan, kar na sa ke jin wannan maganar a bakinki, kar in kuma jin kin amabace shi da sunan Yaya’n ki balle damuwa akansa...ince ko kin jini da kunnen fahimta?”. na muskuta gefe guda, ji nake kamar nayi kuka da kalaman Gwaggo, ƙasan zuciyata tuni yayi baƙi tana bugawa da sauri da sauri kamar zata fito waje. Bance da Gwaggo komai ba na Miƙe haɗe da buga ƙafa a ƙasa na bar wurin, ta biyo ni da faɗin, “ai ba ki buga ƙafar da kyau ba, da kinyi yanda zan shaida kin zama mara kunya, sai na san ta inda zan karɓeta". da faɗin hakan ta miƙe ta nufi inda wutar gawayi take ta zuba kuɓewar, kana ta shiga toilet dake tsakar gidan don ɗora alwalar magriba. ni kam shigewa ɗaki nayi na faɗa kan gado ina kukan irin cin zarafin da Gwaggo tayiwa Yaya, yau da ace ba Gwaggo bace ta faɗa haka da ko waye mun rabu da shi kenan.
Washe gari da Safe kuwa ina gama ayyukan gida nace da Gwaggo zanje gidan su Farhana, bata yi yunƙurin hanani ba, sai ma ɗumamen tuwo data zuba a plask tace na kaiwa Hajiyar Farhana saboda ta san tana son ɗumamen tuwo. fitowana na tari mai napep, tunda na hau ko passenger bai ɗauka ba har muka isa ƙofar gidansu Farhana, na fito na ba shi kuɗin shi na shiga gidan. A parlon gidan na iske su duk, suna ta hira gwanin burgewa, gaishe da su nayi har yayunta Maza suka amsa suna min tsiya. na miƙa plask ɗin hannuna gaban Mamansu ina cewa,“Hajiya gashi inji Gwaggo tace na kawo maki”. Hajiya ta amsa tana murmushi ta buɗe, ƙamshin ɗumamen ya daki hancin Hajiya har da lumshe ido tana faɗin, “kaii Masha Allah, kuma kamar kin san yanzu nake cema Farhana ta kiraki ko Gwaggo tuwo tayi yau ashe kuwa shi ɗinne, kaii madalla nagode ƙwarai Allah yayi albarka”. na amsa da Amin sannan muka haura sama nida Farhana inda ɗakinta yake. kamar bani nai fushi da ita ba jiya, itanma kaman ba itane ta shareni ba, tunda muka zauna hira kawai muke zubawa ba ƙaƙƙautawa, sai ma can da ta lura ne kaman hankalina ya rabu gida biyu ta ke faɗin, "wai wani abunne kuma?”. na girgiza mata kai, ta ƙara cewa,"to sai ki bani complete attention ɗinki dan ban iya ta magana alhalin ba sanin me nake cewa kike ba". sai na ɗan yamutsa fuska nace,"ke ni yanzu ma zan wuce, amma tukunnama me kuka dafa yanzu?”. tana hararata tace,"ban sa ni ba. wannan wanne irin kuturun wulaƙanci ne, muna hirarmu me daɗi kawai kice za ki tafi. hala fushin da kike da ni ne har yanzu bai baki daina ba?". "dilla ni ba haka bane, kawai dai ina so zan tafi ne. idan ban bar fushi dake ba ai ba za ki kalla ma nazo ba". "to amma daga zuwa sai tafiya abinda ba ki taɓa ba, to ina ma zaki je wai wanda ban sani ba?, dan dai ba za ki zo ki wuce gida da wuri haka sanin cewar za kisha tambaya gun Gwaggo". naja tsaki cikin ƙosawa nace,"ke dilla Malama ni ina tambayanki me kuka dafa kina wani tsareni da tambayoyinki kamar kin kama me laifi, na faɗa maki bana son irin haka, idan kuma abincinne ba za ki banba ki faɗa min na sa ni, daɗin abun gidanmu ma akwai". duba da yanda raina ya ɓaci kuma nake magana a hasale yasa tace,"ahh ba rami me ya kawo zancen rami?, kinga ni ba baƙuwar zafi bace Allah ba ki haƙuri. indai abinci ne irish potato ne da ƙwai, kawo maki zanyi ko da kanki zaki zubo tunda Allah yasa kin san inda yake?". na kuma jifanta da harara, ban saki fuskata ba sai ƙara ɗaureta da nai, na miƙe ina cewa,"muje kitchen ɗin". itama kuma sai ta ɓata tata fuskar, tai kicin-kicin da ita har muka sauko muka shiga kitchen, kuma da yake zuciyar kowa a wuya take ko Hajiya dake mana magana ma bamu saurara ba muka shige Kitchen, na ƙarasa drowern dana hangi ƙaton cooler ɗinsu da anan ake zuba abinci, ita kuma ta tsaya gefe tana kallona, ƙaramin plask na ɗakko na zuba dankalin da ƙwan a ciki, na samu wani plask na tea ƙarami bayan na haɗa tea ɗin na zuba a ciki sannan na dubi Farhana nace,"muje ki raka ni". tana dubana da mamaki tace,"gida ko ina? ban fahimce ki ba, cin abincin ne ba zakiyi anan ba ko me?”. na ƙara jan ɗogon tsaki saboda tana neman ta ɓata min lokaci da wannan shegiyar tambayar tata. "kinga Gwaggo Farhana, wannan abincin ban zuba dan cikina yaci ba...so rakiya zaki yi min, idan baza ki raka ni ba sai na tafi ni ɗaya ba komai bane ai tunda ni ba makauniya bace balle tafiyata ta zama dole saida ɗan jagora". na faɗa ina bin gefenta zan fice, sai tayi saurin kamo hannuna tana faɗin,"daɗina da ke kenan, babu baya ni sai saurin fushi. kin shigo da damuwa tare dake, ke biki yi min bayani ba sai neman sauke fushinki kike akaina...ina zamuje dama?”. "anguwa”. na bata amsa a taƙaice.
tai ɗan jim tana min kallon tsanaki, sai da ta gama nazartata tsaf tukunna tace,"wurin mahaukacin jiya zamu koma?". tayi tambayar da rainin hankali. a ƙufule kuwa nace da ita,"kin faɗa sau biyu kenan, karki gigin ƙara jingina shi da wannan mummunar kalmar a karo na uku, ina faɗa miki ne dan kinji da kyau. Farhana mamaita kalmar can daidai ta ke da yankewar alaƙar dake tsakaninmu, i dont fucking care dan mun rabu". ina faman huci nasa kai zan fita taƙi matsawa,"ki ban hanya zan wuce. ina ce kince ba ki rakani ko. kinga ki daina ganin kamar idan babu ke ba zan iya tafiyar nan ba, nasan hanya sarai, so da ace jagora za ki min sai na tsaya ki gama faɗa min baƙaƙen maganganunki...kinga tafiyana". ina kaiwa nan na tureta na fita, ta ƙofar baya nabi yadda Hajiyarsu ba zata ganni ba.
nayi sa'a yanda nake saurin nan ina fita na sami napep, Allah ya taimaka bai tsawwala min kuɗi ba, dama ba isashshen kuɗi ke garen ba, shi yasa ma nace Farhana tazo muje tunda ita a motarta ne. ina sauka daga napep ɗin na nufi cikin bolar, kai tsaye kuma cikin kangon na faɗa, a tunanina zan ganshi amma sai ban ganshi ba, na fito ina ƙara dudduba bakin bolar da gefe da duk inda dai idona idan ya wurga zaiga mutum, amma sam babu shi, sai naji wani abu mara daɗi na bin jikina, na koma cikin kangon na aje basket ɗin abincin na fito ina ƙara dube-dube. ta hannun haguna na gange shi can ƙarshen bolar kwance shame-shame, da sauri na nufi wajen, ina zuwa ban kula da komai ba na durƙushe a wurin na rarumo shi jikina ina faɗin, "subhanallah! Yaya meye sa kazo nan ka kwanta, baka da lafiya?". na tambaya duk a ruɗe ina taɓa kansa, amma babu zafi. "Yaya tashi mu bar nan dan Allah". Kallona kawai yake yi, yayinda ko leɓan shi bai samu damar furta kalma ɗaya ba, yayi min nauyi amma a hakan nake ƙoƙarin ganin na janyo shi da iya ƙarfina, sai dai sam na kasa, kuma ganin hakanne yasa shi miƙewa zaune kafin ya dubeni da kyau yace,"tashi”. muryarsa na fitowa da kaifi kamar na reza. na miƙe lokacin da idona ya cika tapp da ruwan hawaye, sannan shima ya miƙe, nai saurin kama shi ganin kamar zai faɗi, kayan jikinsa duk wari suke amma wannan sam bai dameni ba, haka nake kamashi ajikina bana ko lura da ɓacin da kayana zasu yi da najasar wurin. ya ƙwace a jikina yana cewa,"bar nan wurin". ƙwayar idonsa ce ta shaida min baya so ya ƙara maimaita min, hakan yasa naja da baya har na sauka daga saman bolar, tukunna naga ya fara takowa a hankali har ya sauko daga kan bolar shima, bai ko kalleni ba ya wuce ya shige cikin kangon, ganin haka yasa nima nabi shi na shiga ciki. A ƙasa na same shi zaune, nima na samu wuri na zauna ina duban shi kafin na furta, “Yaya baka da lafiya?...au ina kwana". bai amsa ba, sai ido daya kafe ni da shi yana nazarin rashin hankali irin nawa, tsawon wasu daƙiƙu kaina yana ƙasa na jiyo muryar shi na fita da faɗin, “Sabina ko?”. nai saurin ɗago kaina, “eh” .na bashi amsa. sai kuma muryarsa tayi ƙasa, "me yasa kika dawo inda nake?, wai meye sa baki da tsoro ne?, ke bari kiji na faɗa maki, nifa ɗan iska ne, ɗan yan kan kai ne, ina yanke kan mutane na kai ayi tsafi dasu, ki daina zuwa wuri na idan ba ki son na yanke kanki, ko nayi maki fyaɗe, dan duk na saba yinsu”. abunda zance a wannan lokacin maganarsa ta bani nishaɗi, furuci ne da ko kusa baiyi kama da shi ba, ya faɗa ne kawai dan ya tsoratani, dan da ƙyar ma ya dinga haɗo kalmomin. na saki ƴar ƙaramar dariya ina faɗin. “Yaya ai babu mai yiwa bawa wani abu fa ce abinda Allah ya rubuta zai sa me shi, kuma idan kai ɗan yankan kai ne, ai da baka zauna a haka ba, da baka zauna anan ba, da tuni kana da dukiya mai yawa kamar yadda masu yi suke da ita, ni bana jin tsoronka, hasali ma sai ƙaunarka da nake yi. tun jiya dana ganka zuciyata ke faɗa min ko me zaka yi min kar na rabu da kai, tana faɗa min akwai wani abu da zai kasance a tsakaninmu, tana faɗa min kai mutumin kirki ne, tana faɗa min an halicceni ne domin na tambayeka...so ka bar tsorata ni, ni bana tsoron kowa da komai saboda ina tare da Allah. yanzu dai ga abinci nan kaci mu tafi gida”. Kanshi ya kai duba ga plask ɗin da

Please Login or Register in order to submit comment