Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙanƙameta, a gaskiya ina bala'in son ganin Yayana, dan a yanzu jin zuciyata nake na wani matsewa sa zafi. Ta tureni da ƙarfi tana cewa, "je can ki ƙarata da halinki ke ɗaya, idan kika ƙarar da hawayen kya rasa na zuwa ɗakin miji ace ba ki da kunya, ke baza'a taɓa tambayanki mene ke damunki ba ki faɗawa mutane ba a lokacin, sai kin gama iskance-iskancenki tukunna. to Wallah ki ka kuskura kishiya ta gane ma ruwan hawayenki gasa ki zata dinƙa yi". Sai a sannan ne nayi shiru, nace mata, "Gwaggo tunda munyi hutu yau don Allah ina so naje naga Hajiya da Mami da su Uncle Nasir". Ina nufin dangin mahaifiyata. Taja tsaki tace, "amma ke kuwa kina da abin haushi, dama abinda kike wa kukan kenan?". "a'a bashi bane. Wani Malaminmu ne yace na masa sata, har da kirani ofishinsa ya ƙara min wulaƙanci, shine nasa kuka sai yace wai Kukana kamar kukan Shanuwa, ita kuma ɗayar Malamar tamu tace min daƙiƙiya". Gwaggo tai wani zabarin gyara zane tana furzar da goron bakinta tace,"shi Malamin naku? Yace kin masa sata kuma kukanki kamar na shanuwa?". na ɗaga mata kai alamar tabbatarwa. ta jijjiga kai da kyau sannan tace,"To sata ta ƙare a ahalinsu, kuka kuma nasa ne ke kama dana tumaki. Ita kuma Malamar itace babbar daƙiƙiya da ta kasa fahimtarki. Kuma suje da halinsa na rashin kyautawa Allah zai saka miki, yanzu kije ki wanke fuskarki kizo kici abinci, na san babu abinda kika ci ki ka fice karatun da ba lada ba zunubi". na goge hawayena ina tambayanta cewa,"to Gwaggo zanje ɗin?". "za kije mana, ba kunyi hutu ba?". "ehh munyi har na wata guda ma". "to kinga kuwa kina da lokacinma da za ki je ki zazzaga musu. Ki bari idan Karima tazo sai ku wuce tare idan zata koma". Na miƙe ina cije leɓe nai ɗakina, gado na faɗa ina jin farinciki da nishaɗi, zanje naga Yayana, kuma mu taho tare da shi don bazan kuma barinsa acan ba, dole ne ma ya biyoni. Na rugume pillow inata murmushi ni ɗaya, dana rufe idona babu hoton dake haska min sai nasa, zumuɗi duk ya hanani sukuni, na ɗauka waya na kira Inna Karima na tambayeta yaushe zasu tace sai nan da sati biyu, ina jin haka ban san lokacin dana gilla mata ƙaryar ai Gwaggo bata da lafiya ba, aiko hankalinta a tashe tace min suna kan hanyar zuwa gobe ko jibi. Na kashe wayar ina dariya sai kuma na fara Allah na tuba Allah ka ƙarawa Gwaggo tah lafiya, ina haka ta shigo, hannunta ɗauke da kwanon abinci, yanayin da ta riske ni yasa tace, "ke lafiya?". "lafiya lau Gwaggo". Ta dire min abincin saman table tana faɗin, "da dai sauƙi kam, Allah ya bada lafiya inda rabon samunta". Ta juya za ta fice na dakatar da ita da tambayata. "Gwaggo kin taɓa ganin Halitta ɗaya a mutum biyu?". ta wani juyo a sukwane tana ambaton sunana, jin na amsa yasa ta cewa,"ohh ke ɗince dai". sai na ɓata fuska na turo baki gaba nace,"wai Gwaggo ba zaki bar ce min mai aljanu ba". tana gyara ɗaurin zanen da a ko yaushe nake takaicinsa tace,"to ai tambayar taki ce Sabina ta a bincika ce". "to ni dai ki bani ansata". "ansar me zan baki Sabinan Gwaggo?". na ƙara jefa mata tambayar, a wannan karon daya kasance tana fuskantata ne sai kawai ta bini da ido tana kallona da kyau cike da nazari, sai kuma tasa kai tayi hanyar fita tana faɗin,"to Allah yasa ba gamo kika yi ba...ni dai Rakiya Allah kayi min maganin abubuwan da suke neman fin ƙarfina".


*Please Vote, Comment and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(18)*
bayan fitar Gwaggo kuwa raina fes nake jin shi, murmushi kuwa idan ka kalla fuskana kai kace gonar auduga ce saboda yadda haƙorana suka gagara rufewa. Har sai da Gwaggo ta dawo ɗakin ta iske ni kwance kan gado still dai murmushin nake, ina kuma ta faman juyi akan gado, sai da ta ƙare min kallon tsaf kafin ta samu gefen gadon ta zauna kana tace. “Allah mai girma da ɗaukaka, yau naga Mace. Anya Sabina lafiyarki kuwa, na fita kina dariya haka zalika na shigo kina dariya, to ki daiyi a hankali don wallah dariya illah ce, kuma kin san bana son dariya”. matsowa nayi kusa da ita, na kuma sakin murmushi. Sai naga ta miƙe tsaye zata nufi hanyar fita nayi caraf na riƙe hannunta, ina ƙunshe dariyar da ta ciyo ni, don nasan sarai abinda ke ranta nace,“wai Gwaggo me kika gani, ina zaki je dana ga kin miƙe?”. tace, “yo Sabina na sani ko aljanun ki ne suka dawo, wannan dariyar haka sai kace an maki bushara da shiga aljannah”. “yo Gwaggo kika sani ko busharar aka min, kinga ai sai mu tafi tare”. sai kuma na kwaɓe fuska nace,“amma fa gaskiya Gwaggo kibar cewa ina da aljanu, waye ke son su, amma ke duk magana ɗaya sai kice aljanu, mutum ba zaiyi dariya ba sai ya zama jinnu”. na faɗa ina yin ƙasa da kaina tamkar zanyi kuka. Ganin haka yasa Gwaggo kamo hannuna tace, “haba ƴar lalen Gwaggo, kinga kece naga sai murmushi kike ke ɗaya kuma kin san Allah da yayi ni ina da tsarguwa shisa kika ga nace haka, ko kuwa akan maganar ɗazu shi ne duk kike faman wannan murmushin, ko dai a makaranta kin samu ɗan..”. bata ƙarasa maganar ba muka haɗa iɗo, sarai na gane inda ta nufa sai na waske nace. “Gwaggota kenan mai abin mamaki, ki bama mutum daɗi ki bashi haushi, nasan fa abinda kike nufi, to ni bashi yake sakani nishaɗi ba, kawai dai ina son zuwa Kano saboda naga Farhana, kuma naga dangin Mama shi ke sani nishaɗi wallah. Kuma duk lokacin dana tuna yadda Kike tattalina kamar ƙwai sai hakan ya kuma tsundumani cikin nishaɗi da jin daɗi, ke dai Gwaggo Allah kaɗai zai biyaki ya kuma ƙara maki nisan kwana mai amfani ya ɗora ki kan maƙiyanki. Ina son ki Gwaggota”. na ƙarasa faɗa ina bata sumba a goshi. Gwaggo ita ma ta shafa bayana tana saka min albarka tana faɗin, “ai kema kin san indai akan kine sai inda ƙarfina ya ƙare, Allah dai ya haɗaki da miji nagari. Oh Allah ka nuna min wannan rana, gaskiya ranar akwai shagali, ke ranar sai na kwaso shoki, don ma wai babu Sahibina a kusa da nake faɗi maki abin sai yafi armashi”. Dariya nayi na janyo kwanon abincin da ta kawo min ɗazun na fara ci kafin nace, “ɗakko wata hirar don yanzu idan kika fara labarin Sahibin kin nan sai mu kwana mu yini baki gama ba, sai kace Sahibin kin nan yafi kowa”. ta ɗan dungure min kai, “munasira!, yo har kya faɗi min wani zancen Sahibina, baki ji akace kowa da bazarsa yake taka rawa, to ni tawa rawar da ta Sahibina ce, yo Allah na tuba ke har kya yimin zancen zan ɗakko maganar Sahibi, kema fa idan kika samu wuri tsaf nasan sai kin zarce ni, yarinya baki san loɓe ba(love)”. wata dariya ce ta suɓuce min wadda yayi sanadiyar zubar da abincin da nake ci waje, Gwaggo tamin duban sheƙeƙe kafin tace,“kinga ba nayi magana kice ke baki san zance ba, yo meye abin dariya anan?”. ta tambaya babu wasa a fuskar ta, da alamu ta ƙulu, don haka nayi gaggawar tsayar da dariyar da nake yi kafin nace,“yo Gwaggo kece da fama, sai kice sai kinyi turanci kuma baki iya ba, ai sai ki haƙura haka, idan kuma ba haka nace maki zan fara koya maki haruffan hausa shima kinƙi da duk kin san yadda ake faɗan words a hankali”. “ke kika san wani was(words), hakan ma tunda zan faɗa a gane ai shikenan tunda ba wurin wani naje na faɗa ba, bare naji kunya ato”. “yo ai kuwa wataran zaki faɗa a wurin wani wallah idan baki daina ba”. Gwaggo tace, “yau naga iya shege, ke Sabina fice min da gani”. Daga haka na miƙe ina dariya har na fice a ɗakin, dama yau na gama shiri na ba zan kwana wuri guda da Gwaggo ba duk tabi ta dameni da hayaƙi. Kai na tsaye nake tafiya dariya nacin cikina, har na isa corner da zata sadaka da kitchen kaina a ƙasa naji nayi tuntuɓe da abu da sauri na ɗago kaina ina duban meye ne, karaf muka haɗa ido da Yaya Haidar, da sauri na zaro ido shima ni yake kallo da irin kallon wanne abu zan maki na huce. ni kam ganin kallon da yake watso min tuni na sauya hanya, nayi gefe da niyyar wucewa yace,“dutsen da kika taka hala bai ji maki ciwo ba?”. Na ɗan ɓata fuska nace, “eh bai jimin ba”. ina faɗar haka na kuma niyyar wucewa. aiko a zafafe ya damƙo hannuna, tuni ido na ya raina fata, duk lokacin da muka haɗu sai naga kamar zai kuma tsotsen baki ne, fuskata ta cika da tsoro, baki na fal in-ina nace, "ka..kaj..kaji tsoron Allah kaga dai ba abinda nayi maka karka tsotson baki don Allah”. ina gama faɗar haka hawayen da suka cika ido na suka samu nasarar sauka kan ƙafar Yaya Haidar ya kuma ƙulawa fuskarsa tamkar ta bijimin sa yace,“an faɗa maki kowa ɗan iska ne kamar ke, da za’ayi tayin abu guda, ko an faɗi maki kowa maye ne kamar ke sha uku kawai, goge min ƙafa na ko na zane maki ƙaramin mazaunanki nan”. takaici ne ya ishen, a zuciyana nace, _wallah kamar na zabga maka mari nake ji._ zaro idon da Yaya Haidar yayi yasa ni tsorata ba ƙarama ba, don wata iriyar damƙa ya kuma yima hannuna ya matsa min ya kuma galla min mintsini, take na buga tsalle idona ya cigaba da zubar da hawaye da ƙarfi ya buga min tsawa yace,“ni sa’an kine, Sabina ina wasa da ke ne, ni zaki kalli tsabar idona kice za ki mara?”. ya ƙarasa maganar yana nuna kansa. “wallah zancen zuci ne ya fito fili ban san na faɗa ba, don Allah kayi haƙuri please Yaya Haidar Allah ban san ya fito ba”. ɗan cif-cif gemunsa ya kama yaja kana ya kawar da kanshi gefe guda, ban ankara ba yaja hannuna fuuuuu sai ɓangaren shi. ina ta bashi haƙuri amma sam bai kulani ba, saboda maganar tayi mashi ciwo, yana shiga yasa key a ƙofar ya saki hannuna, nan na shiga bashi haƙuri akan ya barni na tafi kar ya kuma tsotson baki, sai kawai na tsinkayo muryar shi yana faɗin,“abinda yau yafi tsotsar maki baki shi zan maki, za ki gane shayi ruwa ne zalla, za ki san kince ni za ki mara marar kunya kawai”. Nan ta ke ya shiga cire rigar shi ya zama daga shi sai gajeran wando, na saka hannuwa na rufe idona, gabana sai dukan dubu-dubu yake yadda kasan ana surfe akan ƙirjina, zuciyata kamar zata faɗo ƙasa tayi dancing haka nake jin yanayin yadda ta ke duka. Ta cikin hannuna nake ganin shi yana takowa, sai daya iso har inda nake naji ya cafki hannuna, sai ji na kawai nayi ya wulla ni kan gado, yana ƙoƙarin hawa gadon nace,“na rantse da Allah idan ka hawo gadon nan kamar a bakin Baba, tunda na kalla sam baka tsoron Gwaggo ka mayar da ita sakarya Kuma wallah Allah indai...”. Ban kai aya ba na jiyo muryar Gwaggo tana ƙwalo min kira. Da sauri ya mayar da rigar shi da wandon shi ya samu wuri ya zauna ni kuma yace min, “tashi ki shiga toilet ki tabbatar kin wanke fuskarki ta wanku, zance ma Gwaggo kina wanke min toilet kuma wallah idan naji kin faɗa mata magana ɗaya akan abinda na maki”. ya nuna ni da yatsa alamun kin san sauran. Cikin hanzari kuwa na diro daga gadon na faɗa toilet ina shiga Gwaggo ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin, “a’a Zainab tace min Sabina’n tana nan, ko kuwa tayi wani ɓangaren?”. “Eh tana nan, tana wanke min toilet ne”. ya bata amsa ataƙaice, kansa na ƙasa kamar me yankan farce. “Tolet kuma?, yau kuma ƴar wankin tolet ka mayar da ita bayan wulaƙancin duk da kake mata a baya bai ishe ka sai ka haɗa da folishwan?”. ina toilet amma yadda ta faɗi kalmar Punishment ba ƙaramin dariya ya bani ba. Yaya Haidar yace,“Gwaggo wai yaran nan idan ba’a basu aiki dame zasu horu idan sunje gidan miji, ki riƙa kawar dakai akan Sabina mana bafa ita ɗaya ne ƴa ba”. “au tou, haba sai ka ce min kai kayi ƴaƴan ai har daka san horo, tunda har ka iya tsayawa tsegege ina faɗa kana faɗa, Aliyu ka shiga hankalinka dani, wai bance ma ka daina zuwa gefe na ba har ka ganta ka saka min ita aiki ba, Aliyu ka fita idona na rufe billahillazi tun kafin nayi maka abinda har ka koma ga ubangiji bazaka manta ba wallah”. tana ida zancenta, ta ƙwala min kira, ni kuwa dama ƙiris nake jira na fito muna haɗa ido tace,“jakar uban can, kar kace min kuka ka bata, don wallah mai barinka ka ƙara kwana gidan nan sai ikon Allah”. da sauri na girgiza kai ina tuna sharaɗin daya gindaya min nace,"a’a fa Gwaggo, ina wanki ne ƙwaro ya faɗa min a ido, shine kika kalla yayi ja haka, amma na fitar sai dai bai daina min zafi ba, muje”. naja hannun ta muka wuce don nasan zata iya fahimtar abinda ya faru.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(20)*
*Kano.*
"idan ka gama ka kulle masallacin". limamin masallacin da ke tsaye akan Alhussain yace da shi. Alhussain da kansa ke ƙasa kan ƙur'anin dake hannunsa yana karantawa bai ɗago ba sai daya kai aya tukunna. sannan ya ɗago da kansa dake masa nauyi ya kalli Liman ya amsa mishi da,"tom Malam". har Liman ya kai bakin ƙofa sai ya dawo ya duƙa ya ajiyewa Alhussain naira 200 a kusa da shi.
tsawon wucewar mintuna talatin sannan ya kammala karatun ƙur'anin, ya shafa adu'ar da yay sannan ya mayar da ƙur'anin ya kai cikin drower ya aje. ya dawo ya tsuguna ya ɗauki kuɗin da Liman ya aje masa yana tayi masa adu'a cikin ransa. sannan ya fita ya rufe duka ƙofofin masallacin ya ɗora mukullin a inda ake ajiyewa. bayan sallar isha'i ne lokacin, dan haka unguwar ta daɗa yin shiru sai haushin karnuka da kake shi, haka kowanne layi duhu saboda rashin wutar nepa. tafiya yake yana takawa a hankali saboda yanda ƙafafunsa ke yi masa tsananin ciwo, haka har ya fito bakin titi, anan ya hangi wata ƴar tsohuwa mai siyar da tuwa ya ƙarasa wurinta ya siyi tuwo da miya na hamsin, a wurin ya zauna yaci sannan ya tashi ya koma bakin masallaci inda yake kwana anan yanzu tun bayan fitowarsa daga cell. kuma a wannan zaman da yay ne gyangyaɗi ya fara ɗaukarsa, cikin baccin dake neman ɗibarsa yaji kamar hayaniya, dan haka ya buɗe idonsa da sauri, dai-dai lokacin da motar ƴan sanda ta tsaya a wurin, a gabansa, dan haka ƙwayar idonsa akansu ta sauka. bakinsa da zuciyarsa suka shiga furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a sanda yaga Ƴan Sanda na tunkaro shi, wasu matasa kuma a tare dasu na faɗa musu cewar,"ehh shine, wallahi shine". kalmar shine ta bada tartsatsin tsawa acikin kansa, yaja numfashi ya sauke tare da lumshe ido. a cikin duhun idonsa abunda ya faru da shi kwanakin baya da suka shuɗe ya shiga haska masa, ko kaɗan baya fatan hakan ta ƙara maimaituwa masa, ko da a mafarki baya fatan ƙaddara ta ƙara kaishi hannun ƴan sanda. zuciyarsa a yanzu faɗa masa ta ke akan ya tashi ya gudu, ya tashi gudu tun kamin su cimmasa su kama shi, bai san dame suka zo ba wannan karan, idan har ya ƙara shiga hannun hukuna taya za'ai ya fito?. ya buɗe idanuwansa ya suke kan ƙafafunsa biyu, ɗaya ta kumbura suntum ɗayar kuma ta ɗan sace ba kamar da ba. ya ƙara maimaita kalmar innalillahi a cikin ransa, ko daya miƙe tsaye, ko da yace zai gudu, la shakka babu inda zai kai ga ɗora ƙafarsa zasu cimma masa, da ƙyar ya takawa, irin takun da ko kusa ko kaɗan ba zai iya yin gudu ba. maimaituwar kalmar innalillahi a bakinsa ta haɗe da damƙwar kwalarsa da ɗan sanda yayi, ya fizgo shi ya miƙe tsaye, sannan ɗayan ɗan sandan daya ƙaraso shi da wasu mutane ukun da bai sansu ba ya kama hannunsa ya saka masa ankwa. sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin mota suka tafi. _"gani nan Yaya. Yaya gani nan, karka bari ƙwallar ta zubo dan Allah"._ maganar daya ji na shiga kunnensa kenan, muryar Sabina ce, daga ina?, tana ina?, ya rumtse ido da ƙarfi ya kuma buɗesu, acikin motar dai yake, cikin motar dai daya ji ana faɗar direct gidan gyara hali za'a kai shi. bai san lokacin daya daki kansa da jikin motar ba, inda tasan abunda ta ke haifar masa, da ta hana ganinta da jinta suna yi masa gizo, da ta hana sunanta ambatuwa acikin zuciyarsa. kuma buguwar da yay a wannan lokacin shi yay sanadiyar ɓallewar jini daga kansa, saukar jinin da yay sanadiyar tsayar komai acikin kansa, ya daina ji da ganin komai.

*Abuja.*
"haka za ki fita ba ki ci komai ba?".
"ina tsoron layi ne shiyasa, idan naje can ɗin na sami resturant a kusa saina saya na ci". "hakan yayi, a dawo lafiya. Idan kinga mutane ba sauƙi a wurin ki dawo ya ba ki kuɗi a hannu kawai saiki amfani da shi". "ameen..tom Gwaggo". Na amsa ina gyara yafa mayafina. Da sauri na fito compound, ina zuwa na tarar motana babu mai, na daki kai ina jan tsaki, ni yanzu ya zanyi? Shine tambayar da nayi ma kaina, ga Yaya Abba baya nan, ni kuma bana son kula Yaya Haidar bare nace ya ara min tasa, to ya zanyi dole haka zan haƙura neje wurin nasa tunda dai babu wata motar a ajiye sai ta matan gidan, su kuwa ba shiri muke ba bare nace zan ari tasu, shi yasa nacewa Baba a ɗaukar mana driver a aje, yace a'a baida amfani tunda dai kowa ya iya motar nan kuma ga Yaya Abba da Yaya Haidar ma. Har na nufi part ɗin su Yaya Haidar na hango Anty na shirin fita, na dawo da sauri na ƙarasa wurinta lokacin harma ta shiga mota tana ƙoƙarin fita, na tsayar da ita, ta zage glass tana jiran cewata sai faman haɗe rai ta ke tana min gani-gani. cikin ƴar murya nace,"Anty please bari na biki ki ajeni a bank, motana babu mai aciki, jiya su Yaya sunyi tafiya ina tunanin basu san ya ƙare ba basu tsaya sunsha ba, idan nace zan bari aje a sayo zan ƙara yin late". Nace da ita ina maganar da sigar roƙo na lallami. "tunda ubanki ya saya min motar ai dole ne na zame miki driver, to ko na rasa abar ɗauka a motana bana yayibi mai aljanu ba na kwasarwa kaina matsala". Ta faɗi hakan tana ɗauke kanta akaina taja motar ta fice a gidan. Oh ni Sabina, yanzu har ta kai ake min gorin mai aljanu, na goge guntun hawayen daya sakkomin, _Allah ka yaye min da ni da sauran ƴan'uwana ba ki ɗaya._ nayi adu'an a zuciyana ina nufar hanyar gate, saboda na san idan na koma Gwaggo cewa zata yi na fasa zuwa, ni kuma nafi so nayi abuna yau na huta, don akwai terming ɗin da nayi. Har na kai gate zan buɗe ƙofa na jiyo Gwaggo na ƙwala min kira, na juyo na ganta tsaye tana jan kwandon shara, ko ina zata da shi oho, rigima dai irin tata kawai, Baba yace su Zainab suna zuwa suna mata aiki tace bata son marasa mutunci suke zuwar mata inda take, Inna Karima zata kawo mata mai aiki. daga inda ta ke tsayen tace, "idan kin gama ƙare min kallon, nace har yanzu ba ki tafi ba dama?". "ummm motan nawa ne babu mai, zanje na hau ta haya sai na tafi". "to zuwan yau dama dole ne ko ƙaƙa?". ina ɗan marairaice fuska nace, "nafi so ne nayi yau ɗin, please Gwaggo ki barni na tafi". Ina kallo ta taɓe baki, "wai please, dole dai idan za'a maka magana sai an haɗa da ɗan iskan yaran da ba jinsa kake ba, yare bana uwa ba bana uba ba, shegen bature duk ya lalatawa ƴaƴan musulmi harshe, banda kece ma da sai nace zagi na akai". Ina nesa da ita banji mai tace ba, na juya zan tafiyata tace, "riga Malam masallaci ai ban gama maganar da ke ba, ina Abba ko wannan yaron Haidar?". Tana rufe baki Yaya Haidar na fitowa daga ɓangarenta, yana gyara maɓallin hannun rigarsa fuska a haɗe yace, "ni fa ba yaro bane karki kuma ce min yaro". "to ubana". Tace da shi tana hararsa. Sai kuma tayi masa kallon tsab kamin tace, "fita zaka yi ne?". "umm". Yace da ita yana tafiya. "yauwa to ga Sabina nan zata je banki, sai ka ajeta a can motarta ce babu mai". "ni ba driver bane, taje ta nemi nepep ta hau mana". Tace da shi, "yanzu Haidar ni zance kayi abu kai tsaye kace min ba zaka yi ba saboda banda girma a idanunka. Wannan yarinyar fa ƙanwarka ce, me yasa kake nuna mata tsana da yawa har haka ne, idan baka ɗauketa ba ai kaje ka ɗauki wata ƙatuwar banza. Kuma motar nan dai naga ai Babanta ne ya saya maka ita, amma saboda kai mutunci bai gama ratsa jininka ba shine zaka ce ba zaka kaita inda take so ba". cikin jin haushi yace da ita,"da nayi magana sai kice bana ganin girmanki, shi yasa idan kina magana nake miki shiru. Kuma shi Baban daya saya min motar ai ba cewa yayi gata nan ka zama driver'n Sabina ba. And again motana bata ɗaukan marar kunya ne". "idan bata ɗauka mara kunya ba ai ta ɗauka fitsararru". Gwaggo ta sa ki wani guntun murmushi kamin tayi ƙwafa tace, "hmmm ina jiye maka ranar ƙin dillanci. Ina roƙon Allah kar ya jarabce ka da son wannan yarinyar kayi tunanin zan baka ita Aliyu, ko da zanga ledar jini gefe, ledar ruwa gefe babu zancen mallaka maka Sabina, atoh ka jini da kyau". "nima kar Allah ya nuna min wannan ranar, dan babu abinda zanyi da wannan mummunar jikar taki. Da za ki ce mata ma ta daina kwalliya idan zata fita may be ta ke yin samari, wannan kwalliyar babu abinda ke ƙara mata sai girman ƙwailancinta, ƙwaila kamarta ace babu mai so, ki miƙe tsaye ki samu ki haɗata ta farfaɗo don tayi tsala da yawa". "akwai babban tsala ma irinka, kai wacce asararriyar macen ma zata iya aurenka, cikakkiyar mace dai cewa zata yi baka girma ba, tunda gaba ɗayanka yaushe ne ma aka cire maka shayi". Wani shu'umin murmushi naga yanayi yana cizon leɓe, yayi ƙwafa murya can ƙasa yace, "to Gwaggo koma wace a bamu ɗaki ɗaya da ita a jira wata tara a gani. Anan za'a tantance darajar kaciyar tawa". ni kaina kalmarsa ta ƙarshe ba kaɗan ɗin kunya ta bani ba. Gwaggo kam sheƙeƙe tayi tana kallonsa kafin tace,"kai dama ai ba kunya gareka ba, Allah dai ya shiryeka idan na shiryuwa ne, idan kuma bana shiryuwa bane yay mana maganinka". Murmushi kawai yay mata baice komai ba, yasa key ya buɗe motar, tana dubana tace, "to ki taso ku tafi". Yay saurin waigowa ya kalleni ya kalleta, "ni fa babu yarinyar da zata shigar min mota, tunma wannan jikar taki mara kunya. Yarinyar da gaba ɗaya kayan jikinta suka girma a gabanka amma ji take kamar ita ta baka nono". kawai saina Durƙushe a wajan na fashe da kuka, idan da kalmar dana tsana naji yana cewa na girma gabansa, ranar nan haka yace min tun twins ɗina na ƙifil-ƙifil ya sansu amma saboda yanzu sun cika min ƙirji shine nake

Please Login or Register in order to submit comment