Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni, "ke fa ba ki iya ganin mutum cikin wani hali ki masa sannu ba ko ki tambayi meke damunsa, a'a ke fatanki a biya miki buƙatarki, to sai ki jira sai na gama wartsakewa". "Eyyah Gwaggo tah wallah nai zaton ko kinyi training ne, ban kawo wani abu ke damunki ba". Wani wawan kallo ta wurgo min wanda yasani yin shiru da sauran maganata. "to idan kin aza sai ki sauke ba training nake ba, zawo nake fama da shi, shiga ta banɗaki na huɗu kenan a cikin rabin awa. Ban yarda da abincin jiya da muka ci ba, ina tunanin waɗannan ƴan iskan sun fara mana barbaɗe a abinci". Da sauri na ƙarasa wurinta cike da tausayawa, duba da yanda idonta ya faɗa lokaci ɗaya. "Subhanallahi, Gwaggo Zawo kuma? to taya akayi hakan? me kika ci da za ki kwanta?". ta ƙara kufula tana cewa,"da wanne yare nayi miki maganar da kika kasa fahimta, ko kuma ƙara maimaita miki kike so nayi, ba kiji nace ina zargin masu kama da tantabarun can ba. Mutum na fama da kansa dole sai kinsa yayi magana". taja guntun tsaki, "ke sam ba ki da saurin fahimta, dole idan za'ai miki bayani sai an faɗaɗa shi, kisa aita doguwar magana". nace, "Gwaggo to aini ban zargesu ba ne, tunda abincin nan dai nima na ci shi, wataƙila dai ko cikinki ne ya ɓaci kawai". ƴar maganar da nai kuma sai ta jawo masifa da sababi, faɗi ta ke,"auto ni za ki gayawa cikina ya ɓaci dake ban san takan cikin nawa ba. Da can da nake girkina naci lafiya na miƙe lafiya fa, da kika ganni sarai nasan takan lafiyar cikina, wannan girkin dai dole anyi wani barbaɗin a ciki domin nasan halin mugwayen matan Babanki, so suke su ƙarasa ni kuma ba yanzu ba, kema Allah ne ya kiyayeki, saboda haka bazan iya ci gaba da wannan haɗakar girkin namu da su ba, anyi an gama daga jiya, kowacce cikin su tayi nata taci da iyalanta, mu kuma yazo ya samo mana wadda zata dinga yi mana namu, wacce zuciyarta ta cika fal da tsoron Allah". Ni dai ina dafe da bayanta nayi murmushi, saboda ban isa na hanata wannan mitar da masifar ba sai kuma ta samu lafiya, cike da tausaya ma ta nace, "Sannu Gwaggo, bari a kira Baba sai ya turo likita". "ehh kirawo shi ɗin, dan cikina a ɗaure yake ni ɗaya nasan irin azabar da nake ci. Ba don ina gudun haɗa rigima ba ai da saina zayyane masa wannan muguntar da aka haɗa min, amma Allah dai...". sai kuma tayi shiru tare da yin ƙwafa. Cikin faɗa kuma taci gaba, "ni dai kaf cikin Yarana babu mai halin kirki irin Auwalu. haƙuri, mutunci, karamci komai ya haɗa, amma kuma duk cikin Ƴaƴana shi ɗaya ne bai yi sa'ar Mata ba, Mahaifiyarku kaɗaice ta ƙwarai, sauran auran nasa kam sai dai a kira shi da auran ƙaddara, jiya na gama yarda da duk wani mugunta nasu da kuke faɗa nake ƙaryataku, saboda kwana nayi ban runtsa ba ina kokawa da cikina. dama duk wani iya shege da suke ina ɗaga musu ƙafa ne saboda darajar Auwalu da suke ci amma na kusa yiwa tufkar hanci, kaf ɗin su za su gane shayi ruwa ne. Hmmm banda ma dai ina da tausayi ai da sai naja musu Allah ya isa, to idan naja musu binsu zatayi su zo su ƙara lalacewa, ni kuma gyaruwa nake so suyi kar a tafi lahira da tarin zunubai, tunda dai Allah ya ƙaddara auren su da Ɗana". ta juyo ta kalle ni, wadda nayi shiru ina sauraronta, ince tace nace shi yasa ma nayi gumm. tana wurgan harara tace, "kinyi shiru ba ki ce komai ba". nace, "to Gwaggo ni me zance". "ki faɗi abinda yake zuciyarki karta kasheki, saboda ina faɗar gaskiya shine kike jin haushina, to sai dai ko me za kice kice ehe, sirikaina ne amma bana sonsu, saboda mutanan sun cutar min daku, yanda bana manta akhairi haka bana manta sharri. ai tsakanina da su Allah ya...". Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba, ni kuwa dariya ce ta taho min, duk masifar da Gwaggo zata yi akansu da zarar tazo kan Allah ya isa to fa ba zata ƙarasa ba sai tayi shiru. "ki sa ki dariyarki mana ki bar ƙunsheta kina cutar kanki, ina faɗa miki gaskiya tausayinsu nake ji ne saboda bakina kaifi ne da shi kamar wuƙar daba, inaja musu Allah ya isa binsu zatayi kuma tabbata lahu sai sun lalace, ai nayi na gani ne, tunda najawa kishiyata Hussaina har kwanan gobe gata nan halinta bai sauyawa ba, iskancinta sai ƙara gaba-gaba yake taƙi tayi dai-dai". na sauke numfashi ina cewa,"yanzu dai Gwaggo kiyi haƙuri ki rabu da su, kowa yayi na gari kansa, ki barsu da halinsu, kuma insha'Allahu kamin nan kamin anjima za ki sami sauƙi, na kira Baba yace Family doctor zai zo". tace, "ai shikenan nayi shiru tunda kinsa baki, amma batun haɗakar girki kam ya ƙare, ni lokacin hutuna ne yazo tunda Allah ya kawo mu cikin wannan ni'imar, kema kuma bana so ki wahala, wannan aikin gajiyar kin gama shi tun a tsohon gida sai kuma bautar gidan mijinki. Saboda haka zan kira Karima idan zata zo ta samo min ƴar budurwar yarinya mai hankali da tsoron Allah". Kamin na buɗi baki nayi magana Zainab ta shigo ɗakin ɗauke da sallama bakinta, Ta tsuguna har ƙasa ta gaida Gwaggo. "lafiya". Gwaggo ta amsa mata fuska a haɗe, murya a can ƙasa. Nima tace min, "Yaya ina kwana". "lafiya lau Zainab". Na amsa mata fuskata ɗauke da fara'a. Yaran dukansu sun hankalta tun jan kunnen da Gwaggo tayi musu, don sun san sarai zata iya aikata komai, ba kasafai ta ke faɗa bata aikata ba, abu ne mai sauƙi a wurinta tai musu auren ƙauye. "kin shigo min ɗaki kin wani tsareni da idanu lafiya aka mutu kai na motsi, ko wani kinibibin ne?, ko kuma an aiko ki gulma ne?. To idan ma itace aka aikoki sai a sami damar juyawa don babu abinda za ki ɗauka". baki Zainab ta turo gaba, bata tanka ma ta ba tace min, "Yaya". nace, "na'am". "Yaya Abba says if you did'nt come out he will leave, becouse you are westing his time". na dafe goshi nace, "Ya rab, tell him yayi haƙuri dan Allah, am comming out now". kuma bata kai ga fita ba Gwaggo ta Gwame baki tana cewa. "idan ka haɗu da abinda ya isheka sai ka zubawa sarautar Allah ido. wannan barbaɗin rashin mutunci har ina?, a shigo min har cikin ɗaki a dinga sauya harshe a gabana, to duk wanda ya zageni kansa ya zaga tunda dai ba iyawa nayi ba bare na rama, ni dama tunda na ganki a ɗakin nan nasan ba alkhairi ne ya kawoki ba...ke kuma da ba ki da wayo kiyita biye musu suna ɗoraki a hanyar lalacewa, kaf gidan nan dai kin san babu mai ƙaunarki sama dani, amma tunda ubanki yay arziƙi kike neman juyawa min baya, to indai waɗannan makiranne gaki gasu nan". Zainab tace,"kai Gwaggo bafa zagi ne akai ba". sai ta kauda kai tace,"sarai ai na sani, Abba ne yayo aike yana jiran ta fito, banji yaran ba amma na fahimci me akace tunda naji an faɗi sunansa...to hakan da kika ga nayi gargaɗi ne nayi saboda kar a ƙara kwatanta hakan wataran, dan baza'a ji daɗin martanin da zan mayar ba...bana son sauya yare a gabana wannan halin munafukai ne". Zainab dai tai murmushi ta juya ta fice. "to ni kam Gwaggo tunda kinji sauƙi zaɓar min kayan na fita, kin san halinsa yanzu zai ƙara yo aike ko kuma yay tafiyarsa". "wa yace miki sauƙi naji, ƙarfin hali ne fa kawai nake...ni matso da kayan na gani". na tura mata kayan gabanta, ta ɗaga wata red ɗin riga tawa ta aje a gefenta tana faɗin,"wannan kamar sawarki uku ko. bari na bawa ƴar aikin gidan can da aka aikota t gaishe dani". tukunna ta zaɓar min wata doguwar riga ta shadda wadda taji aikin stones a jiki, ɗinkin yay kyau sosai. na ɗauka na saka na zaɓi gyale na yafa, na duƙawa nayi zan kwashi kayan tace, "ki barsu idan na miƙe zan gyara miki na kai miki, ko ba ki kalla duk karin guguwar ya hargitse bane, kuma kika tsaya cewar sai kin kai ɗaki wancan ɗan masu kwazazzafan sabon aike zai kuma danno miki, ma za jeki sai kun dawo Allah ya kiyaye". nai mata wani hug irin wanda ta gani a tv sanda muna kallo, yanda Patriva ta rungume kakarsu shine tace to nima nake yi ma ta hakan tana so dan Allah. nace,"Gwaggona na gode, Allah ya bar min ke ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Na faɗa fuskana ɗauke da murmushin jin daɗi tare da bata sumba a kumatu. Sauri-sauri na isa dressing mirrow na ɗauka faran powder na shafa, na ɗora da man leɓe sannan na zira takalmina. Duk abinda nake idon Gwaggo akaina, ina ƙoƙarin fita tace. "ke wai dan manzon Allah wacce kalar macece, kina nufin a haka za ki fita da wannan buyagin gashin naki da ba kya so a taɓa shi, ke kin ganki kuwa kamar sabuwar kamu". na yatsine fuska nace, "Gwaggo wancan satin fa aka taje shi, kuma naga baiyi komai ba ne, kuma fa na sanya hula babu mai ganewa sai ɗan sa ido". tace, "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi. to Sabina da aka taje shi wancan satin ma ai tsami yake, Ina taje shi fa ina tara yawu a bakina, kuma yanzu har kina faɗin kin saka hula, ke dai kin shiga uku da ƙazantar kai wallahi, samu ki kai ma shi yasa. to kizo ki wuce ki ɗauko wannan abar mai kama da indararo kizo ki busar da shi ki taje don bazan gayara miki ba, kuma baki isa kin fita a haka ba bare kija min zagi ace Gwaggo bata gyara ki". kamar zanyi kuka na maƙale jikin ƙofa ina roƙonta akan ta ƙyaleni, don ni wallahi idan da abinda na tsana taɓa kaina, da ace Gwaggo ta bani dama tuni na jima da aske shi, to sai tace wallah bazan aske ba haka kawai na rasa mijin aure, tunda ta lura mazan yanzu idan ba gashi ba ƙirji sai su raina mace. "wai kuwa ba za ki zo kiyi abinda ya kamata ba ki wuce kije ku tafi sai kunyi yamma. Kin wani tsaya kina turon baki gaba kamar wadda za'a bawa nono, to bari na kira Abban nace masa gaki anan ba uwar da kike kawai dai ba za ki fito bane". nai saurin cewa, "don Allah Gwaggo ki bari sai na dawo, ko a yanzu zafi yake min, kuma kin san ko ya na taɓa sai ciwon kai". "ai kuwa dai kika je gidan miji da wannan ƙazantar baƙar wuya za ki sha, a tou ni dai gaskiya nake faɗa miki. dan ba zai juri ganinki tsab-tsab ba yana jiyo tashin ƙamshi ta ko'ina a jikinki sai ya doshi kai yaji hammm, yasin sai to miki hanyar gidanku zai yi, idan za ki gyara tun wuri gwara ki gyara". na ƙara cewa, "to Gwaggo nace ki barni na aske ba shikenan sai na huta ba kema ki huta da mita". "yo dama aini ban isa na faɗa maki gaskiya ba, shikenan sai ki ce na cika mita. to kije Allah ya kiyaye, ina kuma faɗa miki karki yarda da tuƙin ganganci irin na Abba, da kinga yana neman wuce gona da iri ki sauka ki nemi mota ki dawo gida, ranki ɗaya ne ba biyu ba...sai kun dawo". Fita nayi ina jinta kuma tana ci gaba da faɗa akan rashin gyaran gashin, idan na dawo ya zama dole ta kaini wajen bayerabiyar nan ta gyara min kai, ba zan kasheta da tsamin kai ba lokacinta bai ba, kuma wallah kaina ba wani wari da yake sharri ne irin nata kawai. ni na lura sababin Gwaggo ma ƙaruwa yayi tunda muka dawo gidan nan. Ina isa ƙofan parlo kiran wayar Farhana ya shigo, ina murna na ɗaga domin mun kwan biyu ba muyi waya ba, hiran yaushe gamo muka hau har tana bani labarin exams ɗinsu ta fito ta sami second class, na tayata murna sosai, na tambayeta yaushe zata zo suga gidanmu tace sai anyi hutun islamiya, nace ma ta Allah ya kaimu, har na bata labarin nima an samo min addimission, tai min congratulations tare da bada shawarwari saboda karatun Uni ba ɗaya yake dana Secondry ba. tun fara wayarmu so nake na tambayeta Yayana amma gudun kar ran junanmu ya ɓaci na haƙura, mu kai sallama na kashe wayar raina ba daɗi. ina ƙarasawo parking lot gabana naji ya faɗi, ƴaƴan cikina naji sun kaɗa har jakar hannuna ta kusa faɗuwa ƙasa, na kuma yin ƙasa da kaina ina takawa kamar bana son tafiyar, don ina ƙwaƙwƙwarar tafiya zan kifa ƙasa, gaba ɗaya a tsorace nake da Yaya Haidar wanda tunda na taho idonsa ke kaina, fuskar nan tasa a haɗe kamar hadarin gabas ya taso, sai wurgan wani mugun kallo yake. Ni dai har na iso inda yake tsaye jingine a jikin mota ƙirjina bai bar duka ba, tsorona da fargabana kar dai ace da shi zamu fita yau. sam shi mutum ne mara daɗin sha'ani, miskilanci da masifa su kaɗai yasa a gaba, kuma tunda yazo gidan ya hanamu sakewa, Amina ce ma take iyawa da shi saboda mara kunya ce ta ƙarshen gaske. ni kam da magana ma bata isheni ba, sai dai yay min son ransa, shi yasa duk na ƙagu ya koma gidansu. kuma tsawar daya doka min ita tai sanadiyar gurɗewar ƙafata. "kin bar mutane tsaye kamar aikinki suke kina biyansu, za ki ɗago ƙafa ko kuwa nima sai nayi tafiyata". A ruɗe nace, "Yaya Haidar to ina Yaya Abban?". bai bani amsa ba ya wurgan harara ya zaga ya buɗe gaban mota ya shige, dana tashi nima na buɗe baya na shiga. ta cikin madubi ya jefo min harara yace, "who is your driver?". Na haɗe fuska ina shirin fashewa da kuka, muryata a sanyaye nace, "Ohh Yaya Haidar then where should i stay? ". "dilla Malama fito ki dawo gaba, sai anyi magana ki nemi ki ɓarewa mutane baki, ki jawa mutane masifa a wurin waccan tsohuwar da bakinta bai gajiya da magana. a'a ke gaki ƴar gwal ba'a isa an taɓa ki ba. Kamar akan ki ne aka fara yin mutuwar uwa". matsalar ɗaya ni ban iya rashin kunya ba, furucinsa na ƙarshe shi yay sanadin taruwar ruwa a idona, na fito na dawo gaba na zauna, ko ƙarasa rufe kofan banyi ba ya figi motar kamar wanda zai tashi sama. kuma tsoratar da nayi ya haɗe da sakkowar hawayena, shi ko a jikinsa ma dan ba lallai ne ma idan ace na faɗa waje ya lura ba. har muka hau titi ban bar kuka ba don sosai maganarsa ta bani haushi, idan shi bai damu da tashi mutuwar uwar ba aini na damu da tawa, sam Yaya Haidar baiyi halin Uncle Sulaiman ba don ba haka Babansa yake ba. Shi ko tausayi ban bashi ba, saima tsaki daya dinƙa ja yana shafo sumar kai har muka isa wurin koyan motar, hakan ya ƙara bani haushi, saboda ni fa ina takaicin naga ina kuka aƙi lallashina, nafi so ko ya na fashe to a karkato da hankali kaina, ta irin haka ne ma muke faɗa da Gwaggo wataran, idan na bata haushi sai tayi biris da ni. Ni dai yau nayi dana sanin fitowa koyar motar nan, gaba ɗaya ma naji koyon ya fice min a rai, kullum da murna nake fitowa nake komawa indai da Yaya Abba ne, kuma muna wasa da dariya yake koya min, amma yau tsabar tsoron Yaya Haidar koyan kwanar da na kasa yi sama da sati biyu sai gashi cikin rabin awa na iya, mu kanyi awa biyu zuwa uku idan muka zo amma yau ko ɗaya bamu cika ba naji yace tafiya zamuyi shi ya gaji. muna ɗaukan hanya na ɗago na dube shi, murya a ɗarɗace nace, "Yaya Haidar ai bada wuri fa muke komawa ba, Baba yace Yaya Abba yake tsawa ya tabbatar da na iya sosai kamin mu koma". Farko banza yayi min, sai can naga yayi wani miskilin murmushi yayi revers, a bakin filin wurin yay parking, kansa na gaba kamar bada ni yake ba yace, "buɗe ki fita". nai sororo ina kallonsa. ya ƙara ɗaga murya wanda na tabbata har na waje sunji. "nace ki buɗe ki fita. in yaso ki sami wani ya koya miki sai ki biya shi, ko kuma ki kira shi Abba'n ya koya miki shi daya ga zai iya aikin wahala amma ni ba kalata bace sanya daƙiƙiya a gaba ina koya mata abu tana kasawa". "Amma tsakani da Allah Yaya Hydar ai kasan koyon driving ɗin nan da wahala, kuma ma yau ai nayi ƙoƙari dai, gashi kai baka encouraging ɗin mutum, sai dai kai ta faɗa. kuma fa ni ba daƙiƙiya bace Allah, saboda ina da ƙoƙari akan komai, kaje makarantarmu ma ka tambaya, har na gama first class nake ɗauka". Na faɗi hakan ina turo baki gaba, na san wannan ƴar maganar da nayi ba zai barni ba, ile kuwa ina rufe baki ya ɗalle min laɓɓana da yatsansa wanda sai daya sani yin ƙara ina sosa wurin. "karki yi min rashin kunya saboda ni ba Abba bane, tun kamin a haifeki nazo duniya, sai da nayi shekara ɗaya-ɗaya har 13 kana aka haifeki a tsumma, kashinki da tunbuɗinki babu kalar ƙazantar da ban gani ba, saboda haka ki iya bakinki wajen yimin magana, ni ba sa'anki bane". Haushi ya tuƙeni hakan yasa na shiga ƙunƙuni. ina jinsa yana faɗin, "banda kinci darajan Baba daya ce na kawoki, kuma motar ba ta gidan mu bace, ai da sai kin fita in yaso ki daɓa a ƙafa ki koma gida...mara kunya fitsararriya ana magana kina tura baki gaba kamar shantu, ke ai gaki goyon Kaka goyon gata, to ba gata wannan tsohuwar ke nuna miki ba, dan a nan gaba wuya za ki sha da wannan halin naki". Ni dai bance masa komai ba har muka iso gida, bare ya kuma gaya min no sugar, na cika nayi fam saboda haushi, Allah ko da kuɗi, kai ko shi ɗaya ne mai koyar da mota a duniya ba zan ƙara binsa mu fita ba sai dai har na mutu kuwa ban iya motar ba. Yana yin parking na buɗe na fice, Ina ji yana min magana nayi masa banza kome ma yake cewa oho, ɗakina na wuce kai tsaye na kifa kan gado ina kuka, to fa dama da biyu kukan nan nawa, tun jiya kewan Yayana ya isheni, ga shi yau kuma wannan matsolon raken ya ɓatan rai. Ina kwance ina faman shashsheƙar kuka Gwaggo tayo sallama, ina jinta ta buɗe wadrobe ta zuba kaya ta mayar ta rufe, kana ta karkato kaina tana faɗin. "ke kuma yaushe kika dawo? Me akayi miki kike kuka? Me Abban yayi miki? Ko kuma shigowarki wata a cikin gidan nan tai miki hali na rashin kyautawa?". Duk a jere ta jefa min tambayoyin, na miƙe zaune ina goge hawayena ban dai ce ma ta komai ba, ƙaramar wayata dake gefena kawai nake kallo naga ko kira mai sabuwar numba zai shigo, don a kullum bana yanke tsammani da kiran Yayana. ta kama ƙugu tana faɗin,"yau naga sarautar Allah". "keee to ko kin gamu da ciwon baki ne da kika gagara bani amsa? Ina daɗa tambayarki me Abba yayi miki? Za ki bani amsa ko sai na ƙwala miki wannan murfin tasar". Sanin zata aikata yasa da sauri na buɗe baki nace, "ba Yaya Abba bane, Yaya Haidar ne". "Haidar dai! shi Haidar ɗin da yake baƙo ya ɓata miki rai? To me ya haɗa ku? Ki faɗan gaskiya ke dai ban sanki da rashin kunya ba". ina goge ƙwalla nace, "ni fa ba abinda nayi masa, tunda na fita yake tayi min masifa har muka je muka dawo, har cemin yake wai kinyi min goyon lalacewa, banda taɓara babu abinda na iya, da anyi min abu dana fashe da kuka sai kace a kaina aka fara mutuwar uwa". sai ta shaki ƙugu ta kama haɓa. "shi Haidar ɗin ne ya faɗa miki haka?". na ɗaga kaina, "ehh mana. Ni dai daga yau bazan ƙara binsa ba in dai shine zai koya min mota, acan ma harda ce min daƙiƙiya, ya bige min baki saboda na faɗa mishi gaskiya ni ba daƙiƙiya bace, Gwaggo har muka je muka dawo fa ba abinda na iya wai shi ai ba bawa bane, hakan ma daya fito dani darajar Baba naci". ta shiga tafa hannaye tana faɗin,"iko sai lillahi, duk shi Haidar ɗin yayi miki wannan rashin kyautawar yaci zarafinki da yawa haka?". "Allah Gwaggo ba zan ƙara binsa ba, ki faɗawa Baba indai Yaya Abba bayanan na haƙura". ta dire farantin dake hannunta, tana gyara ɗaurin zane tace, "yo dama ai ba za'a kuma na biyu ba, anyi na farko anyi na ƙarshe. yo ni kuwa ina dole irin wannan cin mutunci har haka, idan kuka ci gaba da fita tare waya san irin cin kashin da zai yi miki agaba, daga ke sai shi sai Allah'n daya ke kallonku. gashi ke ba ki iya halin rashin kirki ba bare ki rama. Saboda haka kwantar da hankalinki, ki sha re hawayenki haka kar ya rainaki, ni nasan yanda zanyi da shi, kuma idan shi gyatumin naki ya dawo ki sa me shi ki faɗa masa...ina dalili wannan ɗibar albarka har ina". Na kuma turɓune fuska ina fizgar numfashi, ta matso kusa ta cire ɗan kwanlinta ta gogen hawaye tana lallashina. "ki kwanta ki rama baccin safiyar da Abba ya azalzale ki, kamin anjima muje wurin bayerabiyar nan ta wanke miki kai, domin ba zan iya da wannan ƙazantar gashin naki ba, haka kawai muna zaune ƙalau ki jajuɓo mana abinda yafi ƙarfinmu, kwarkwarta ta shafeki. na rasa inda zan saka kaina, nan dai ba tsohon gida bane bare nasa miki omo, yafi nai ta kaiki inji suna dirje shi yanda ya kamata, tunda ba ƙaunar kitso kike ba". ni dai duk ba wannan zancen nake son ji ba, so nake ta fusata ta tafi wurin Yaya Haidar kai tsaye, ita da shi hali ɗaya ne, ya kaishi bango ya fusata ya kwashi kayansa ya tafi shine kawai abinda nake so. sai na shiga rera kuka a hankali, hakan kuma yasa ta hauni da banbami tana faɗin tunda dai na faɗa ma ta ba shikenan ba, na zuba ido kawai naga abunda zata yi, ai nasan bata barin ta kwana akaina.
na goge hawaye na Kwanta, Gwaggo ta gyara min abinda zata gyaran a ɗakin...har ta gama idona na kanta, godiya nake ga Allah daya bani Kaka kamar Gwaggo tunda ta fita nai luff jikin pillow na tafi duniyar tunanin Yayana da nake matuƙar kewarsa. Gwaggo na fitowa ta sami Haidar zaune kan kujera a parlo, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya akan centre table, hannunsa riƙe da cup yana kurɓan lemu yana kallon tv yana ssuraron labarai. bata ko bi ta kansa ba saboda tana jin haushinsa ta wuce ɗakinta. ta ɗau tsawon mintuna a ɗakinta yana nan, kuma har ta shiga kitchen ta gama abinda zata yi ta fito still yana nan zaune, amma yanzu waya yake latsawa saboda an gama news ɗin. tsayawa tayi tana tunanin abinda zata yi masa ta huce takaicinta, Amina ta shigo parlon ɗauke da sallama bakinta, hannunta kuma riƙe da basket na kayan abinci. Gwaggo ta ansa gaisuwartata a ciki, ta nufi Dining zata aje abincin Gwaggo tace, "ke tsaya, mene wannan?". "Gwaggo abincinku ne". "to koma da shi, jiya kwana nayi ban runtsa ba har safiyar yau lafiya bata ishi cikina ba, kuma duk sanadiyar abincinku da naci ne. don haka tsautsayi ba zai kuma sawa naci ba,

Please Login or Register in order to submit comment