Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara damƙar zuciyata, Allah kaɗai yasan wanne hali wannan bawa nasa ya shiga a rayuwa, a raina nayi adu'ar _Allah ka kawo mishi mafita._ Tunda ta fara magana ya kasa ɗauke idanunsa akanta, wani abu a ga me da ita na shiga zuciyarsa, tunaninsa ya katse sanda naci gaba da cewa,"Yaya nah zaka iya min alƙawarin daga yau ka daina shan sigari?". kamar wanda yake acikin tsoro da furgici sai yay saurin ɗaga min kai alamar ehhh. Murmushi na saki nace, "da gaske daga yau ba zaka kuma shan sigari ba?". amon muryarsa ya fito da faɗin, "Nayi miki alƙawari, Allah ya bani ikon cikawa". na lumshe ido na buɗe, har ga Allah sautin muryarsa na min daɗi shi yasa wani lokacin nake jan maganar da zai tilasta shi yay magana. ina dubansa da washewar murya nace,"Yaya idan har ka daina shan sigari zanji daɗi, amma fa ka sani duk ranar da na kuma ganin kana sha ina mai tabbatar maka da nima zanyi koyi da kai, dan sai na sha taba sigari naji wanne ɗanɗano kake ji a cikinta". abunda bai taɓa yi ba, yay Miskilin murmushi mai ɗan sauti wanda hakan yasa na buɗe ido ina dubansa, na ɗaga masa gira da faɗin,"murmushin na mene? kana tunanin ba zan iya ba?, ko kuma ce min da kai ba zaka ƙara ba yaudarata ne kayi?" "duk ba haka bane, ina so na koyi irin yanda fuskarki ta ke ne kullum cikin murmushi shiyasa na gwada, kuma sai naji ya haɗe da ciwon dake maƙale a zuciyata kenan yafi ƙarfina. yanzu dai Sabina tashi ki tafi gida". laɓɓana na motsawa na saka hannuna duka biyu a kumatunsa na talasu ina cewa,"indai ka saka a ranka cewar Allah zai maka magani to kullum wannan fuskar zata kasance a haka. ai ba abu ne mai wahala ba". yana ɗauke hannuna yace,"ni dai nace ki tashi ki wuce gida". "Kai Yaya daga zuwa na kuma sai ka kore ni, ni ai bamu gama hira da kai ba, kaga shi Yaya Abba baya bani lokacinsa kullum.yana wurin ball". yace, "aini ban iya hira ba, kuma kinga ke macece ya kamata ace kina cikin gida idan ba makaranta za kije ba. Gaki nan ma da alama makaranta za ki tafi". "a'a na dawo daga tahfeez ne yanzu sai dai ta ƙarfe huɗu". "to ki tashi ki tafi lokaci ya kusa". na miƙe ina gyara zaman jakata nace, "tom Yaya sai wataran?". Gani nayi shima ya miƙe yana zura hannu cikin aljihu, ya kalleni kaɗan yace, "ki ɗaura niƙab ɗinki mana". ina yamutsa fuska ina karayar da kai nace, "Yaya zafi akeyi ne yanzun, ɗazu ba zafi shi yasa na saka". "ki ɗaura don Allah, saboda kan hanya akwai mutane, idan kika je gida sai ki cire". ina marairace fuska nace,"Yaya Allah...". bai bari na ƙarasa maganata ba ya katseni da tashi,"ni dai don Allah". "tom shikenan na ɗaura". na faɗa a sanda na gama ɗaura niƙab ɗin, sannan nace da shi. "na tafi sai wataran". "muje na raka ki". ina kallonsa ta cikin niƙab ɗin zanyi magana ya tari numfashi da cewa,"bana son mutum me musu". Hakan yasa na fasa maganar da zanyi, nan muka jera tare muna tafiya. yau kam ya sake dani sosai, dan harda ce min wai na cika magana, nace masa ai kaima kana da surutun gashi nan tunda muka taho kana magana. sai ya tala laɓɓansa da cewa,"wannan ne karo na farko a rayuwata". "me yasa?". "saboda banda wanda zanke magana da shi". "har ƴan gidanku?". sai yay ɗan jim kamin ya gyaɗan kai, wani ciwo dake ƙasan zuciyarsa na nunawa a fuskarsa kamin yace,"na faɗa miki ban taso na ganni ina rayuwa a gidanmu ba. zuciyata ma faɗa min ta ke wataƙila daga sama na faɗo". ayau gam na gama gasgata shi da wannan furucin nasa, dan haka ɗaya naji zuciyata ta gamsu da shi ɗin. muka ci gaba tafiya ina bashi labarin zaɓata da akai acikin waɗanda zasu yi musabaqa a wannna shekarar.


#Vote.
#Comment.
#Share.
#mikiyawriters.*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(5)*
"Allah ya bada sa'a". abunda yace dani kenan, kuma har muka isko titi ba wanda ya ƙara magana cikinmu. ya faɗa min abunda bai taɓa yi ba iyakar tsayin rayuwarsa shine tsayar da mota ya hau, duk inda zaije ƙafarsa ke kai shi balle ma babu inda yake zuwa. ni kam na dage akan sai ya tsayar min, haka ya miƙa hannunsa na rawa ya tsaida me napep ɗin daya taro, daga hakan na yarda da maganarsa, dan kana kallon ma yanda yake tsayarwar da yanda yakewa mai napep ɗin magana zaka san frin shiga ne.
"ɗan dakata Malam". yace da me napep ɗin sanda na shiga ciki na zauna shi kuma yana ƙoƙarin ja, sia ya tsare ni da ido yana kallona kamar ba zai ɗauke idonsa akaina ba. Yanayin kallon nasa yasa ni sadda kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna ina murmushi, ji nake kamar kar na tafi na barshi ko kuma kawai mu tafi tare, domin ina jinsa ne tamkar wani ɗan'uwana na jini. "Sabina". Ya kira sunana a hankali cikin zazzaƙar muryarsa. Ɗagowa nayi na dube shi tare da faɗin, "na'am Yayana". "kiyi haƙuri bani da kuɗin biya miki". Ina murmushi na gyaɗa masa kai, "karka damu Yayana, na gode". Yana kallon mai motar yace, "don Allah ka tuƙata a hankali, ka kula da ita amana ce na baka". Ya faɗa yana ɗauke hannunsa daga ƙarfen motar zai juya. nai saurin riƙo hannunsa da sauri ba tare dana sa ni ba, ya juyo yana kallona, nima ɗin kallonsa nake kaman zanyi kuka nace,"Yaya don Allah kazo muje gidanmu, bana son tafiya na barka anan". sai ya tala leɓensa da murmushi, a cikin magana ta rarrashi yace min, "kin kalla yanzu ai makaranta zaki je, ki bari sai kin dawo wataran sai mu tafi tare". Cike da murna da kuma zumuɗi nace, "da gaske Yayana?". Shi kansa ya lura da yanayin farincikin dana shiga, kansa ya jijjiga min alaman ehh da gasken yake. Sai kuma na kwaɓe fuska ina marairaicewa a hankali na furta, "to ai Yaya kace kar na kuma dawowa inda kake, idan ba haka ba zaka yi fushi dani". Idonsa naga ya ɗan rumtse ya buɗe ya zuba su akan hannuna dana riƙe nashi gam. Na lura so yake ya zare hannun nasa amma naƙi bashi damar hakan saboda riƙo na masa kamar wanda za'a ƙwace shi. "ya kamata ki tafi karki makara". Ya faɗa muryarsa a sanyaye. "tom shikenan yaushe zan kuma dawowa?". "a'a karki dawo don Allah, kinga ke macece mutuncin ki zai zube idan kina zuwa wurina, alhalin kuma mutane ga kallon da suke min". Na tari numfashinsa, "to ni ina ruwana, ai na san Yayana ba yanda suke tunani bane...". Ban kai ga ƙarasa faɗin Abinda zan faɗa ba naji yana kiciniyar cire hannunsa daga nawa, riƙewa na sake yi har ina ɗan cije leɓena, ganin naƙi sakar masa yasanya shi sunkuyo da kansa saitin fuskata, idonsa na kallon gefe guda yace, "ke ɗin ba muharramata bace, ni dake gaba ɗaya mun kai munzalin daya zama haramun wani ya taɓa wani, duk da ba lallai kina sanin lokacin da kike aikata hakan ba, amma riƙen hannu da kike saɓon Allah ne". Sai naji kunya ta rufeni, jikina kuma yay sanyi, zuciyata ta motsa, na kasa raba hannu na dana shi sai shine ya cire nasa. Ɗago idon da zanyi naga har ya tsallaka kwata, ido na zubawa bayansa ina jin kamar na fita na bishi, Allah ya sani ina tausayinsa kuma ina sonsa, irin son da nake ma Yaya Abba. gashi shi ɗin dai ba wani ba, ba kuma ɗan wani ba, amma yana da matuƙar burgewa, domin komai nasa me kyau ne, yanayin rayuwar daya tsinci kansa ne kawai ya maida shi wani kala, amma tabbas da ace shi ɗin a gidan gata ya fito, to lallai da anyi namijin gaske, nayi murmushi mai sanyi. na shiga duniyar tunanin ta ina zan iya taimaka masa, zuciyata na faɗa min taimakon da zan masa shine sada shi da ahalinsa, aina zan gansu? ta ina zan fara?, wani abu daya shigo ta cikin kaina ya wuce shi yasa na kulle ido tare da kwantar da kaina jikin kujera, Dai-dai lokacin kuma wata mata tai mani sallama na matsa ciki itama ta shigo ta zauna sannan napep ɗinmu yaci gaba da tafiya. A gadon ƙaya muka sauketa, daga nan kuma mai napep ɗin bai kuma ɗaukan kowa ba, ina jinsa yana ta mani surutu ni dai bance masa komai ba, kasancewata ba ma'abociyar magana da kowa ba, har muka isko ƙofar makarantarmu ya sauke ni, na bashi kuɗinsa ya tafi ni kuma na juya na shiga makaranta, Allah ya taimake ni kuwa ban makara ba. Ina shiga aji sai ga Farhana ta shigo, ashe taga lokacin da nake shigowa ta tagar ajinsu, kallo ɗaya na mata na ɗauke kaina akanta, nifa alallai fushi nake da ita tunda har ta ke aibata mun Yayana. Ta dafa kafaɗana tana ƙaramar dariya tace, "ƙawata wai ina kika je ne? Na biya maki ɗazun Gwaggo ke cewa ai baki dawo ba, sai nace ma ta ƙilan kin zauna bada hadda ne don bamu haɗu ba". "ummm". Shine abunda nace ma ta kawai ina maida kaina a window. "to daga ina kike?". "daga inda kika aike ni".Na bata amsa a taƙaice. Bata damu da sha re ta ɗin da nake ba ta kuma matsowa kusa dani, hannuna dake kan littafin ta dafa, ta fara mani magana cikin damuwa da kuma nuna kulawa. "Sabina tun muna ƙananun yara muke tare, mun riga mun zama tamkar ƴan'uwa, muna bawa junanmu shawara kuma mun zama sirrin juna. Shin mene yasa lokaci ɗaya wani zai sanya ki sauya daga yanda kike a gareni, kawai akan ina faɗan gaskiya...". "karki yaudari kanki da cewan kina faɗan gaskiya akansa, ko za ki Kawon hadisin daya ce ka aibata musulmi? Ina sauraron ki". Na faɗa idona tarr akanta. "babu". "to Kin san da cewan babu kenan amma kike taƙarƙarewa kullum kina aibata shi akan abunda baki da masaniya akai, ko kin san asalin rayuwarsa ne?". "ai ba wai ƙarya nayi ba. Zahiri fa na gani, don nace masa ɗan iska ko ɗan daba ai banyi ƙarya ba". "wallahi da ace kin san yanda nake jinsa a zuciyata ba za kike jifansa da waɗannan kalaman ba. Da kin san matsayinsa a wurina da tuni kin jima da rufe wannan dogon bakin na ki". Na faɗa ina kawadda da kaina bayan na jefeta da banzan kallo. Tayi wani munafikin murmushi sannan tace min, "wato Sabina idan banyi kuskuren hasashe ba son wannan ɗan wiwim kike ko?" .ta tambaye ni tana kafe ni da ido cike da rainin wayo. Tsaki naja ina faɗin, "Kinyi hauka ne hala? Taya za ki ce mani ina sonsa, To akan mene ma zan so shi? Kawai ban san shi ba ban san daga inda yake ba na wani kama sonsa, abunda na sani kawai shine ina tsananin tsausayinsa na kuma damu da shi". Murmushin rainin hankali ta ƙarayi tace, "to ai dama ke ba za ki gane ba, amma tuni kin faɗa a son wancan ɗan isakan, sai dai zan faɗa miki tun wuri ma idan haka ne karki bar abun ya girmama ki cire shi a zuciyanki domin ba zan taɓa yarda da hakan ba, tunda shi ɗin ba mutumin arziƙi bane". Sosai naji zafin maganarta a zuciyata, daurewa nayi na sha re ta ban saurare ta ba, sai ƙwafa da nake ƙasa-ƙasa. "kinsan Allah Sabina, idan har baki fita a harkan wannan ɗan shaye-shayen ba na rantse miki saina faɗawa Yaya Abba, wai akan mene zaki ke kai kanki inda baki dace da nan ba. Ke ni walla ma tsab zan iya ɗauko masa police su kamashi ai dama ɗan wiwi irinsa bai dace da zaman cikin anguwa ba". Nan ma shiru na mata ban tanka ta ba, haushin hakan yasa ta shiga zaginsa ta inda ta ke shiga bata nan ta ke fita ba. Babu zato babu tsammani taji na sauke mata zazzafan mari saman kuncinta. A zabure ta ɗago ido tana dubana da nake faman huci akanta. "tashi ki fita a ajin nan tunda bana ku bane". Na faɗa ina ma ta nuni da hanyar ƙofa. "ni kika mara Sabina? Akan wani banza ɗan iska wanda bakin uwa ya bishi kika mare ni?". Cakumar kwalar hijabinta na ƙarayi, raina a matuƙar ɓace nake dubanta, dukan mu huci muke tun ba ma yani. "Farhana kinyi kinyi karki kuma kiransa da ɗan iska, idan ba haka ba na rantse zan miki abunda bazaki taɓa mantawa ba. Kuma shi ɗin da kike kira ɗan iska bari kiji ya fiki matsayi a wuri na, wallahi ina mai gargaɗin ki karki ƙara kiransa da shege ko makamancin haka". Ta yarfar da hannuna dake ciwkwikwiye da Hijabinta. "ni kika mara ko? Za ki san kin mare ni, kuma kinyi da ƴar halak. Kuma indai ɗan iska ne yanzu na fara faɗa duk abunda zakiyi karki fasa". Cikin zafin nama na shaƙo wuyanta ina kaɗa mata kashedi. Kan kace mene wannan idon ƴan aji ya dawo kanmu, tuni akaje aka sanar da Malaman makaranta.


_Short Update☹️. Anyway lets just say i don't feel motivated anymore🥴, like i just stop the typing mu huta gaba ɗaya ko? becx i dey see you people you dont like the story at all...ina gani daga comment & voting naku wanda yanda kuke yi baya encouraging nawa gaskiya...so please and please you guys should changed or you just tell me to stop westing my precious time._*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(6)*
kamin a kawo mana rahoton Malam na kiranmu, masu jin haushin alaƙarmu da Farhana sai zugata sukeyi, mu kuwa lokacin shaiɗan ƙara buga mana ganga yake a kunnuwa, faɗa kamar ƙananun yara, abunda zamu iya rantsewa wani bamu taɓa yi ba tun wayonmu. gashi dai haushin hakan nake ji a ƙasan raina, amma kuma na rasa dalilin daya sa ko na nemi na huce sai zuciyata ta kuma ingizoni da zigar kar na raga mata, wataƙila shi Yayan da take zagi wani abu ne mai muhimmanci da Allah ya turo shi cikin rayuwata. kuma a hakan bakin Farhana bai mutu ba, dagewa take tana ƙara zaginsa, ni kuwa ina ƙara ƙuluwa har na rarumo wata kujera zan buga ma ta Allah ya kawo Malam Isma'il.
Office ya kaimu, raina idan yayi dubu to kuwa tabbas ya ɓaci, sai cika nake ina faman batsewa. Malam Hamza principal ya shigo office ɗin ya gyara zaman shi akan kujera da hularshi irin ka fiya nacin nan, ya dube ni tsaf, sannan ya juya ya duba Farhana, a iyaka saninsa da mu yasan duk ɗinmu bamu da hayaniya, daga ni har Farhana, wani lokacin idan har ana faɗa da ɗaya, ɗaya yakan shigar wa wani, gashi a wannan karon abinda ya bashi mamaki mu da kanmu muke faɗan. wanda ada saboda irin kyawun alaƙar dake tsakaninmu da yawan Malamai da ɗalibai zatonsu gida guda muke. Malam Hamza yayi gyaran murya ya dubi inda nake tsugunne yace,  “Sabina lafiya yau kam, kuda ba’a jin kanku sai kuma gashi yau anji?”. Bance da shi komi ba, saboda ina da saurin ƙwalla duk da nakan mayar da martani, amma a wannan karon muddin nace zan buɗe baki nayi magana to fa zan iya yin kuka, saboda irin kalaman cin mutumcin da aka dinƙa faɗa min, ana cewa Farhana wai dama tsiyar abota da ɗan talaka kenan, shi yasa tuntuni suke nusar da ita munafukarta ce ni, ba dan Allah nake zaune da ita ba sai dan kuɗin gidansu, ita kuma lokacin ban san meke shiga zuciyarta ba har ta ɗauki huɗubarsu ta yaɓo min maganar data tsayan a rai, wadda ba dan da kunne naji daga bakinta ba, wallah ba zan taɓa yarda ba.
Malam  Hamza ya dube ni ya kuma faɗin, “Ko ba zaku iya magana ba ne sai nasa muku bulala, sanin kanku ne baku fi ƙarfin hukuncin makaranta ba". Farhana zata yi magana kenan nai caraf na tari numfashinta, saboda nasan idan na barta tsab zata iya faɗin abin da ya haɗamu. “Malam yau dama ban koma gida ba, na zauna bada hadda wurin Malam Ibrahim, tana ta tambayata, ni kuma yau banjin magana, ita kuma ta takura min da magana shine muka fara faɗa, kuma kaja mata kunne idan ta kuma gani na a irin wannan yanayin ta daina kula ni”. Malam Hamza yace, “to shikenan ke Farhana kinji abinda tace saboda haka ki kiyaye karku ƙara bari shaiɗan ya shiga tsakaninku, ku tashi ku bani wuri”. Farhana zata yi magana Malam Hamza ya dakatar da ita, na faki idon shi nayi mata gwalo wanda nasan ya sosa ranta, ta girgiza kai tare da yin ƙwafa muka nufi hanyar fita. Bayan fitar mu shi kuwa Malam Hamza murmushi yayi gami da girgiza kai. Kafin mu ƙarasa aji kuwa, muna tafe ina banka mata harara itama tana aikomin da martani a haka har kowa ya isa ajinsu. Ƙarfe shida saura kwata aka tashi, kamar kullum tana inda ta saba jirana, ni kuma na gama cin alwashin ko ita ne mai mota ɗaya a duniya wadda dole sai na hau zanje gida sai dai na shekara ban isa gida ba. Ina kallonta ta gefen ido, tana bina da kallo, ni kuwa har wani sauri na ƙara tamkar zan kifa, ƙafafuwana har sarƙewa suke yi, amma hakan baisa na daina sauri ba. Ina tarar mai napep nayi sauri na shige don ko bayanin inda zai kaini ban samu damar yi ba sai da nashiga muka fara tafiya. A ƙofar gida ya sauke ni inda ina sauka su Adda Karima suna fitowa ita da Mardiyya daga gidan mu, ko kallo Addan bata ishe ni ba bare nasan Allah yayi ruwan halittarta a wurin, da hanzari na ƙarasa da fara’a fal shimfiɗe kan kuncina na shiga gaida. Itama anata ɓangaren Murmushin baƙin cikin tayi asanda ta kafe ni da ido tana neman inda zata samu makusa, saboda macece wanda Allah ya dasa mata zuciyar kushe, akwai fara’a amma fa irin mai ɗauke da taɓe bakin nan. ta dube ni sannan ta dubi Gwaggo tace, “Wai ni Yaya me kike bama yarinyar nan ne gaba ɗaya sai ƙiba take kamar ana hura ta, billahillazi idan baka santa ba sai kace ba ita bace, ke duba min yadda take kumatu ta ke cika tana ɓatsewa kamar wadda take shan sha ka fashe”. Yadda ta ke sababinta ni kuma yana saka ni nishaɗi, ita kuma idan duniya akwai abinda ta tsana tana faɗa ina dariya, duk da kasancewar ta itama Kaka ce a gare ni, Gwaggo tayi murmushi ta dube ni tace, “Karima wannan kuma ai gaki gata, yo me zan bata ni kuwa, abin ma da ba wani ci take yi ba, gaba ɗaya makaranta ta saka ta gaba, ko baki kula ba yanzu ma daga can ta ke”. Adda Karima ta gwame baki tace, “kuma fa haka, ita wai huda-huda, gara dai ayi aure duk sa’anni sunyi sun dire ku kuma kunce karatu to ayi dai mugani, lafiya ƙalau”. Saboda tsabar gulma nacin ta bata samu damar amsa gaisuwar da nai mata ba sai da ta gama habaicinta. ni kuwa ina dariya nace, "7Adda Karima kenan, ke dai ba’a raba ki da abin faɗa, to abinda kema kina da iko akaina, miji ai sai kimin wannan abu ɗan sauƙi..”. Kafin na ƙarasa tuni Adda Karima tace,"abu ɗan sauƙi fidda wando ta ka, Sabina ai shikenan tunda haka kika ce”. ina jinta na shiga ciki, duk bakin Gwaggo idan Adda Karima tana wuri tofa nata mutuwa yake yi muɗus. Napep ɗin dana sauka shi ya ɗauke su, ita kuma Gwaggo ta dawo ciki daga rakiyarsu. ina ɗaki ina canja kaya Gwaggo tayi sallama ta shigo ɗakin, gefen gado ta zauna tana faɗin, “ina raba ki da mayarwa Karima martani idan tana maki magana, kinsan dai kaf dangi babu wanda ya kaita shiga abinda babu ruwanta, saboda haka ki kiyaye ta wallah”. Ina gyaran zaman rigata, na miƙa hannu na ɗakko hula na sanya akaina sannan na dubi Gwaggo nayi mata kallon tsaf nace, “to karki damu Gwaggo zan kiyaye, wai da naga itama matsayin Kaka take a wuri na shisa ma nake yi da ita, baki ga ita wancan ko kallo bata ishe ni ba”. Gwaggo tace, “au yo to ni ai nazaci baki ganta ba, kinga fa bana son iya shege, sai kace baku san juna ba, kai ku dai ko miji kuka haɗa iya ka abin da zakuyi kenan, Allah ya shirye ku to”. Miƙewa tayi tana faɗin bari nayi alwala, har ta kai bakin ƙofa ta ɗaga labule ta dawo tana faɗin, “au ke la ɗazu kuwa Farhana tazo zaku tafi, nace mata baki dawo ba, ƙila ko kin tsaya bada hadda ne”. saboda kar taja zancen da sauri nace, “eh, hadda na bayar saboda jiya ban bayar ba, kuma bana son tayi min yawa shisa”. “au to madalla, ai na zaci ko wurin ɗan iskan yaron can kika koma, dan ta kawon ƙorafin hakan”. Sai da zuciyata ta buga, bugun da ban taɓa jin tayi ba, zuciyata bata son ana zagin bawan Allah'n nan ko kaɗan. Rumtse ido nayi ta dubi Gwaggo da wani irin kallo, da ƙyar leɓena na ƙasa ya samu nasarar motsawa kana na sama ya motsa suka haɗu suka samu nasarar furtar kalmar a’a ga Gwaggo. Bata kuma yinƙurin cewa komi ba ta saki labulen ta fita. ni kuwa na dafe kaina saboda yanda naji yana sara min na furta,“Ya Salam!”.*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(7)*
"kinga farar singlet ɗina?". muryar Yaya Abba ta amsa a cikin kunnena. "ban ganta ba, bani na kwashe kayan ba sai dai ka tambayi Gwaggo". na ƙaraso wajensa ina ƙara faɗin,"Yaya Abba dan Allah zuge min". ya kama zip ɗin rigata ya zuge min sannan yasa kai ya fice ya zabga mitar da baya rabo da ita. ban dai ji Gwaggo ta tanka masa ba kuma nasan saboda karta yi magana suyi da shine shiyasa ta share shi, ni kuwa da ina gyara naga singlet ɗin amma na manta inda na ajeta shi yasa nace masa ban gani ba, dan ina cewa ban san inda na aje ba na shigesu da jaraba yau.
bayan na gama shirina na fita parlonmu da yake madaidaici, na zauna naci sauran ɗumamen tuwon da Gwaggo tace ta rage min, ina gamawa kuma na dawo ɗaki na ɗauki littafin da nayi renting shekaranjiya na shiga karatu, tun a daren jiya na gama karanta book 1 ɗin, Sumayya Abdulƙadir ce ta rubuta shi ina masifar son littafanfa.
sai wajen sha biyo na miƙe, na fito falon ina gyaran ɗaurin ture kaga tsiyana sai ga Farhana ta shigo bakinta ɗauke da sallama. fuskarta na washewa da siririyar dariya ta ƙaraso inda nake, wanda ni kuma ganinta yasa na cukule fuska, na dakata da waƙar da nakeyi, ina faman cika ina batsewa, saita hannu tasa da nufin ture ɗaurin nawa tana faɗin, "bari na ture sai naga tsiyar". Na wani bankama mata uwar harara sannan nace, "da kuwa kinga tsiya ganin idonki". Tayi dariya tana kama hannuna da nufin mu zauna kan kujera, na turje ina daɗa nuna mata nifa ban bar fushi da ita ba. cikin daɗin baki ta kama cewa, "haba mana Sabina wai mene kike hakan...wai so kike sai duniya ta jimu ts mana dariya". ta faɗa tana duba na tare da manno min kiss a goshi. ganin dai kamar ba zan sauko daga kan dokin fushin dana hau ba sai fuskarta ta sauya zuwa damuwa, nan fara'arta ta ɗauke gaba ɗaya, ni kaina na sa ni Farhana na tsananin so na, haka nima, bama iya faɗan minti biyar bamu shirya ba, kai hasalima bama yin faɗan, mukan yi ƙoƙarin kiyaye duk wani abu na ɓacin ranmu, duk da cewar wani lokacin ni na kan kasa haƙuri amma ita ko menene haƙuri takeyi. sai dai a wannan karon ina mamaki da silar abunda yasa nake faɗa da ita har nake irin wannan fushin haka, fushi da ita akan mutumin da ban sa ni ba, na tsince shi ne kawai a

Please Login or Register in order to submit comment