Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanyar vedio calling, na cuno baki haɗe da yin ƙaramin tsaki na ajiye, na rasa me yasa kwana biyu yake takura min da kira, shima kiran dole sai yace vedio call, idan ban ɗaga ba kuma ya addabeni da message, har saina fusata na ɗaga zan masa tsiwa sai karsashin muryarsa ya hanani aiwatar da komai, ta hakan zargina akan Yayana ya ƙara yawaita, na kuma ɗora ayar tambaya akansa akan abinda zuciyata ke saƙa min a game da shi. inata mita a zuciyata kiran ya kuma shigowa a karo na kusan biyar, dai-dai da lokacin da nake ɗaure jelar gashina, garin kai hannu na katse kiran saina danna answer ba tare dana sa ni ba naci gaba da abinda nake. sai bayan dana kammala na ɗau wayan zan fita kawai naga mutum ya tallabi fuskarsa yana aikin kallona, kallonsa nayi ya sakar min murmushi yana faɗin,"gyaran gashin yayi kyau, sai ya ƙara fito da beauty nah, kin kalla kanki a madubi kuwa ko kuma kin bar min gari na faɗa?". na samu bakin gado na zauna ina zumɓura baki, nayi ƙasa da kaina ina cewa,"to wa yace ka kalle ni?". wani siririn murmushi ya saki yace,"yanzu ni har sai an bani izinin kallon Beauty? kallonki fa shine abincin idanuna". na ɗago ina kallonsa, nayi shiru bance komai ba saboda wata magana da ta haska acikin kaina, wannan furucin nasa yayi salo dana Yayana da ya taɓa cewa Kallon Cutie nah abincin idanuwana. kamar yanda Proff yay ƙuri yana kallona haka nima na ƙura masa ido, don so nake na ga aina yake a zaune, idan har naga wani abu mai kama da gidan nan to tabbas zargin Yaya da nake na shine Proff to ya tabbata, sai dai banga wani alamu na shaidan hakan ba. yace da ni, "Beauty please ki bani aron hankalinki yau muyi magana kinji". "ina jinka". nace ina daɗa haɗe fuska. "ki fito gani a ƙofar gidanku". nai saurin ɗagowa ina dubansa da mamaki,"gidanmu kuma?". yace,"kar ki ɗauka wasa, am serious". ina daɗa dubansa nace,"taya akai ka san gidanmu, ni fa ban yarda da kai ba". Yay murmushi mai sauti kamin yace,"Beauty me nayi kuma na rashin yarda, kin kalla nan". ya faɗa yana nuna min wata ƙatuwar waya dake ɗaya hannunsa. map naga yana aiki, lallaima mutumin nan wato wayo yay min kenan ya kirani ya biyo sahun kiran, kamar ya san tunanin da nake yace,"nayi miki wayo ko. kiyi haƙuri nazo ba tare da izininki ba, yanzu dai ki fito waje muyi maganan da ya kamata". nace,"ai bani nace kazo ba, don haka sai ka koma". "aikuwa to yanzu zan shigo da kaina, dama yau weekend nasan Baba na gida kinga saina sanar masa da abinda ke tafe dani". nayi zumbur na miƙe ina faɗin, "ni ban saka ba, gani nan". ƙaramin gyalena na ɗauka na yafa na fita, na ce da Gwaggo nayi baƙo ina zuwa, ta bina da kallo baki a sake wato abin ya bata mamaki, ina buɗe ƙofan parlo naji tana cewa,"wayyo ni Hannatu daɗi barni da raina, yau Sabina taga zaɓin ranta, yau zanyi kwanan farinciki, dama zuwan wannan rana nake ta jira, Allah yasa dai ku daidaita, fargabata Allah yasa kar jami'an tsaron kanki su sauya miki ra'ayi, domin nima a yanzu banda burin da ya wuce naga na kaiki gida mafi girma da daraja a wurin ƴa mace". tana ta murna take faɗin haka don harda ƴar rawarta, ni dai ban kulata ba nayi ficewata. gaban gate ɗin gidanmu kaɗan yay parking motan nasa, na ƙarasa wurin da sallama, da jikin motar na jingina sai haɗe rai nake, ni har ga Allah banso wannan zuwan nasa ba, wayana yay ringing, ina kallo naga sunansa ne, na ɗaga ina cewa,"to mene kuma na kirana bayan gani nazo, ai nasan ka ganni ka fito mana". na faɗa cike da tsiwa a lokacin dana ɗaga, da murya mai ban tausayi yace,"Beauty da ace ina da ƙafafun da zan taka, da kamin fitowanki zan iso tarbanki, ki tayani da adu'a na samu lafiya naci gaba da takawa kamar yanda nake lokacin da ina ɗan shekara uku, na rantse miki Beauty daga wannan lokacin za ki zama sarauniya ta gaske, domin ni zan zame miki bafadanki a duk wani taku na tafiya naki". gaba ɗaya sai naji wani nauyi ya kamani tare da yin da nasanin furucina, dan sosai ya bani tausayi har naji dama ban faɗa masa hakan ba, driver ne ya zagayo ya buɗe min murfin motar, na leƙa kaina ciki nace da shi, "ba zan iya shigowa ba saboda Gwaggo ta hanani shiga motan kowa, ka faɗi ko mine daga nan ina jinka". yace da driver ya fito masa da wheel chair nasa, jin hakan nace. "a'a barshi kawai, bari na shigo ɗin amma sai dai ka hanzarta". kuma nima dama na faɗa masa ne don na gwada shi, saboda in har ya damu da maganar da ta kawo shi to zai fito da ƙafafunsa, ashe dai da gaske bayada ƙafan ba wasan kwaikwayo ne yake ba, tabbas shi ɗin ba Yayana bane. bayan na zauna na ɗan dube shi kaɗan naga mood na fuskansa ya sauya, raina naji babu dadi domin nasan magana ne silar hakan, nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace," kayi haƙuri don Allah, nasan baka ji daɗin furucina ba". kwantar da kansa yayi a jikin kujera, hakama idonsa a lumshe suke, da raunin murya ya fara magana yana cewa. "wannan shine rashin yarda da kika yi da ni? Beauty miye ribana idan na ɗorawa kaina cutar ƙarya, don kawai na samu shiga a wurin mutane? to me na rasa? ban rasa komai ba na jin daɗin rayuwar ba, ki yarda dani Beauty wallahi babu yaudara a tare dani, dukkan abinda kike gani tare dani gaskiya ne, wannan ƙafafun da ki ke gani shekaru 27 kenan rabon da su taka, anyi maganin amma shiru, kullu yaumin a zaune suke basa iya sarrafa kansu sai da taimakon wani". yay shiru tare sauke wani nauyayyan numfashi, na goge ƙwallar dake neman sauko min nace,"Allah ya baka lafiya". har lokacin idonsa a rufe ya amsa min da amin kamin ya ɗora da cewa,"tun da nake a rayuwata ban taɓa jin wata mace ta shiga raina ba sai dana fara ganinki Beauty, duk da nasan ke ɗin kinfi ƙarfina amma ina da yaƙinin za ki iya kasancewa tare dani a cikin kowanne irin hali, domin ke din kina da zuciya mai kyau, halinki mai kyau, ko mai naki me kyau... ko da nace miki kin min sata ba satar komai nake nufi ba fa ce zuciyata da kika sace, Beauty na rantse miki labarinki yasa mahaifiyata acikin farinciki, yasa ƴan'uwana a farinciki, Daddyna kaɗai ya rage ya sanki kuma shima ina jiran dawowansa ne, Beauty shin za ki iya yimin alfarma? ki aminta dani ki zama matar aurena?". na wani ɗago a zabure ina kallonsa, da gaske ne dama sona yake? me yasa na bashi fuskar da har ya iya furtamin wannan maganar? cikin tsiwata nace,"dama wannan maganar ce ta kawo ka wurina?, dana san ita ce da ban fito na ɓata lokacina ba anan, idan kai kana sona to ni bana sonka domin ina da mijin aure". mtswwww naja tsaki na fito daga motan na wuce gida raina a ɓace, ba tare dana tsaya sauraron me yake cewa ba. abinda na gani a parlo ne ya razani, har ban san lokacin dana jefar da wayana a ƙasa ba na ruƙunƙume Gwaggo, sosai ganin Yaya ya furgita ni, idan nace muku shine Proff karku musa min, abinda ya bani mamaki taya akai ya rigani shigowa cikin gidan nan? na rumtse ido sosai jikina ya hau mazari, idan Yayana ba aljani bane to shi wane? adu'oi na shiga karantowa cikin raina ina ƙara damƙe hannun Gwaggo wadda ta zubawa sarautar Allah ido, har ina neman tasar hankalinta. gaba ɗaya su ma kuma saina basu tsoro saboda yanda nake yi, ina buɗe idona naga yana kusanto inda nake wanda shima ya cika da mamaki gami da tsoron abinda ya sameni, na shiga nuna shi da hannu ina karkaɗawa nake cewa,"karka zo inda nake, karka kusanto ni tunda kai ɗin mayaudari ne". yanda nake kamar wata wadda ta tada iska, ni kuwa tsabar baƙin cikin yaudararmu da yay shi ya tsayan a rai, lallai yayi wasa da hankalina, naji Gwaggo ta doka wani uban tsaki ta yarfar da hannuna. domin itama ta fahimci abinda ke tsakanina da Yaya, sai dai tunda ta gane soyayya muke ta nuna min bata so domin ba abune da zai ɗore ba. ta wuce tana faɗin,"aikin wofi, to da yake sonki sai akace miki da ke kaɗai zai zauna? to ko ni da kike ganina duk wannan uban kyan nawa Sahibina bai zauna dani ɗaya ba, haka ya ringizani da ɗai ɗai har ɓiyu, atoh tun wuri ma ki bar damun kanki akan ɗa namiji". wani takaicinta ya kamani, ni ga abinda ke damuna ita kuma tana wani zance na daban. Yayana yana zuwa ya damƙi kafaɗuna yana girgiza ni da tambayar mene, nayi watsi da hannayensa, kallonsa nake da takaici ina zubda hawaye, sam bama zan iya kwatanta haushinsa da nake ji ba a raina. cikin muryar da ta jiƙu da ɓacin rai nace. "a tunaninka mu kayiwa,? to ka yi babban kuskuren tunani domin kuwa kanka ka cuta, Allah ma ba zai barka ba domin kaci amanarmu, musamman ma ni kaci amanata kuma bazan yafe maka ba, mayaudari munafuki kawai". ai ban kai ga rufe baki ba tass naji an ɗauke ni da mari, ina kallonsa yake nuna kansa yana cewa,"me nayi miki da har za ki dinga dangantani da waɗanan maganganun?". cikin ƙunar rai nake kallonsa, cikin baƙin ciki da takaici na ɗaga hannu nima na yarfa masa maruka har guda biyu, domin nima a hasale nake kamar yanda yake.
na ɗaga muryar da ta karaɗe duka parlon nace,"an gaya maka ɗin, idan da kalaman da suka fi wannan you deserve them, me kake nema a rayuwarmu da ka biyo mana ta wannan siga? who are you?". wani irin kallo yake min na rashin fahimtar inda maganarki ta dosa, na cakumi kwalar rigarsa ina daɗa ɗaga siririyan muryana nake cewa,"Ka faɗa min waye kai? kuma mene dalilinka na shigowa rayuwata?". yay watsi da hannayena, shima ransa a ɓace kuma murya a ɗage yace,"na shigo rayuwarki ko kuma kika shigo da ni rayuwarki? idan ke zan miki ƙarya tunaninki zan zauna nayiwa manyan mutane ƙarya ne, wallahi inda na san nufinki wulaƙantani ne da cin zarafi ne da ban jinginu dake ba...me tasa za ki saka min da hakan a lokacin da na riga na gama sakankanewa?". na juya na kalla Gwaggo nace,"Gwaggo shi ɗin azzalumi ne kuma mayaudari, kice ya faɗa miki gaskiyar shi wane, ni ban yarda da shi ba, wallahi idan ba mugun mutum bane to aljani ne, ki tambaye shi Gwaggo kiji". kamar bada ita nayi magana ba tayi min shiru, Ya juya zai fice ransa a dagule. nac,"idan kana da gaskiya ka tsaya mana". tsayawa yay ba tare daya juyo ba, naje gaban Gwaggo ina daɗa ce mata,"Gwaggo ki tambayeshi shi ɗin wane? waya aiko shi? kuma me yazo yi mana?". tana sauya channel tace,"yo dama ki tsinci mutum a bola kiyi tunanin bil'adama ne, a wannan yafi kama da aljan". na turo baki ina mata wani duba saboda gaba ɗaya ita ɗaukan abin wasa take, na kuma ce mata,"Gwaggo ki bar batun wasa Alah shi ɗin dama na jima ina zarginsa, yau kuma na ƙara tabbatar da zargina akansa, yaudararmu kawai yake da sunan shi ɗin ba kowa bane, yana wasa da hankalinmu, Gwaggo ki kore shi kice ya bar mana gida kar ya cutar min daku". sai yanzu dai taga da gaske ne nake maganar, babu batun wasa, ta dube shi dake tsaye hannayensa zube cikin wandon aljihu kamar yanda ya saba, sai idonsa dake rumtse gam. a hankali yake magana. "Dama bada niyyar taimakona kika shigo rayuwata ba?, me kike zargi akaina da har kike min kallon macuci?". "na shiga uku". na faɗa ina ɗora hannu akaina. "Gwaggo ke faɗin ni dai daka zo gidan nan tsakani da Allah na ɗauke ka, ina jinka kuma tamkar jikina, bana taɓa banbantaka dasu Abba ba, shin Yaya maganganun da take gaskiya ne?". gabanta yazo ya durƙushe ƙafafunsa. "Gwaggo kamar yanda na faɗa miki a baya yanzu ma haka zan maimaita miki, na rantse da Allah bani da niyyar cutar da kowa a rayuwata, bare ku da kuka gama yimin gatan komai. ni kaina da Sabina tai yunƙurin taimakona nayi mamaki saboda babu wanda zai so haɗa alaƙa da mutumin da baya da asali, mutumin da baka san shi ba, ki yafe min Gwaggo, ban cuce ku ba kuma ban yaudareku ba, ina matuƙar godiya da kyautatawar da kuka yi min a rayuwa". ya faɗin hakan yana miƙewa, jikina yay sanyi nai saurin kamo hannunsa na miƙe tsaye, nauyinsa ya kamani sai dai wani gefe na zuciyata na rasa me nake ji, wani abune ya tokare wurin. shi kuma ya ɗauke kai daga kallona yay kauda fuska, yana kuma kiciniyar ƙwace hannunsa dana damƙe, murya a hankali nace,"to amma Yaya idan ba kai bane to shi ɗin daya zo wane?. kayi haƙuri na maka bahaguwar fahimta, Yaya ko kaina ka tsinci kanka a irin yanayin dana tsinci kaina za kayi mamaki." "waike maganar me kike ne?". Gwaggo tace dani, ina riƙe da hannunsa na juyo gareta ina cewa,"na rantse da Allah Gwaggo su biyu ne. surarsu iri guda ce, maganar iri guda ce, yanzu haka dana fita wajensa irin kalar kayan nan dake jikin Yaya shima sune a jikinsa, kuma shima ɗin baƙin glass ya saka saɓanin fari daya saba sanyawa, kamar yanda na dawo na tarar da Yaya zaune shima haka na tarar da shi a mota. Gwaggo dole na tsorata nayi tunanin shi ɗin ba mutum bane". na kama hannunsa ina ja nace," idan baku gasgata ni ba kazo muje na nuna maka shi nasan har yanzu yana nan domin na barshi da abinda ba zai iya tafiya lokaci ɗaya ba". ko da muka je gate babu motarsa bare ƙyallinsa, kaina ya kuma ɗaurewa, abin ya kuma ɗaure min kai da kuma tsoro, anya kuwa?. dariyar Yaya tasa ni juyowa ina dubansa, sosai yake dariya wadda har haƙonsa suka bayyana gaba ɗaya,"yarinya ta gama sa ni a ranta tazo wurin saurayinta tana masa kallon ni ne". shine abinda yake faɗa yana kuma dariya har da tafawa. "Yaya kana ɗaukan maganata wasa ko". naji haushi na bar masa wurin. abinda ya ƙunsa min shi na dawo Gwaggo ma ta kuma ƙunsa min, takaici ya isheni na shige ɗaki. cikin kwana biyu gaba ɗaya sai suka koma cewa wai aljanun kaina ne ke buɗe min ido, haka ina ji ina gani da lafiyata amma kullum a cikin yimin hayaƙi ake. na rasa ta yanda zanyi su gasgata ni amma ni dai yanzu ina da yaƙinin Yaya na da alaƙa mai ƙarfi da Proff idan har da gaske ba mutum ɗaya bane kamar yanda na fi zargi, a yanzu jira kawai nake a koma makaranta kamar yanda Farhana ta bani shawara.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(25)*
"oak see u letter". na faɗa cikin wayar dake maƙale a kunnena, kuma daidai lokacin da nayi perking motana a parking lot. Hidaya tace,"yauwa karki manta in zaki shigo ki taho min da Arable crop handout ɗin nan". na amsa mata,"ba zan mata ba insha'Allah, bye". na kashe wayan ina jefawa cikin jaka, yayin da Aisha wacce muka fita tare ta buɗe murfin motar ta fita. tana tsaye daga bakin ƙofar tana cewa,"na tafi zaki shigo da kayan ko na ɗauka?". nace da ita a sanda nake fitowa,"ɗauki ki tafi da su, ba zan shiga part ɗinku ba zanyi karatu ne". "oak". ta faɗa tana buɗe bayan motar ta ɗauki kayan da muka amso a office ɗin Baba.
ko sanda na shiga ma Gwaggo bata san na dawo ba, ɗakina kawai na shiga nai wanka na sanyo english wears na fito, naci alelen da na tabbatar Gwaggo ce tayi shi saboda yanda yay daɗi. ina gamawa kuma na suri maltina a fridge nayo waje.
cikin rumfar bunun dake garden ɗin gidanmu na nufa, na zauna kan deck chair ɗin dake wurin. hannuna riƙe da waya wanda na gaza ɗauke ƙwayar idona akanta tun ɗazu, abar ta batun littafin dana ɗauko zan karanta, dan tuni nayi watsi da shi gefe. kallon screen ɗin wayar nake fuskata sai fitar da yalwataccen murmushi take me cike da annashuwar jin daɗi, hoton Yayana ne na shagala a kallonsa wanda yayi matuƙar kyau, gaskiya shi ɗin kyakykyawa ne, a duk wani kallo biyu da zanma hoton sai na lumshe ido. kuma ban sani ba kawai ta bayana naji an rufe min ido, ban tsorota ba saboda ƙamshin turaren daya daki hancina kaɗai ya riga ya bayyanar min da kowa ne. na ɗora hannuna saman nasa ina ƙoƙarin cirewa, sai ya zuro kansa ta gefen wuyana yana leƙen abinda nake kallo, ina jin hakan nayi saurin kifa fuskar wayan saman cinyata don karya gani. "ni bazan gani ba?". Ya tambayeni cikin zazzaƙar muryarsa me sanyaya ilahirin jiki. ban buɗe baki na ba shi amsa ba, sai ɗaga masa kai da nayi alamar ehh, kuma har zuwa yanzu idona a rufe yake da hannunsa, ni kuwa sai aikin murmushi nake ina jin wani abu me sanyi na tsarga min. "ƙanwar Yaya ki barni na kalla abinda ya ɗauke miki hankali har na jima tsaye anan ba ki san da zuwana ba". gabana ya faɗi, wato ma ya daɗe da zuwa ban sa ni ba. _wayyo Allah yasa bai san abinda nake kallo ba._ na faɗi hakan a zuciyata ina rumtse idona dake cikin hannunsa. ajikina naji ya ƙura min ido yana kallona, duk na jin wani iri a tare dani saboda rigar jikina mara hannu ce, ga saman ƙirjina duk a waje kasancewarsa dukiyar fulanina acike take kuma a sama, abinda ma yasa na fito a haka saboda babu mai zuwa wajen idan ba ni ba, saima Aisha dana gani ranar nan tazo tana karatu zasu fara exams. na yunƙura zan miƙe ya maidani na zauna yana me zagayowa ya zauna kusa dani, yana jana da wasa Alallai saina bashi ya kalla. ina samun damar ƙwace hannuna daga nasa na miƙe da sauri ina ja da baya ina dariyar dake daɗa ƙawata kyawun halittar fuskata, haɓa ya riƙe yana kallona, ni kam sai dariya nake masa. na ɗan tsaya ina cewa,"ka gama ƙiyasce ƙiyascenka amma ni kam bazan baka ka gani ba". nace da shi ina yi masa gwalo. tasowa yay ya biyoni muka fara guje-guje, gaba ɗayanmu ƙyalƙyala dariya muke, banyi aune ba caraf naji ya damƙo hannuna ta baya, muka tsaya muna aikin sauke numfarfashi, ina ƙara ƙanƙame wayata saboda bana so yaga hotonsa da nake kallo. dab dani ya matso kamar zai mannu da jikina, yana zuro kansa ta kafaɗata yace,"wa na kama?". ina maida numfashi na lumshe ido, jikina yay sanyi ina jin wani iri a tare dani saboda yanda tsigar jikina ta tashi sakamakon ɗumin iskar bakinsa dake sauka ajikina adalilin numfashin daya ke saukewa shima. na turo ɗan ƙaramin bakina gaba ina cewa,"to wai miye ruwanka da abinda nake kallo, ni Allah ba zan baka wayana ba". na ƙarasa faɗa cike da shagwaɓata mai narkar da zuciya. juyo dani yay muna facing juna, fuskarsa lulluɓe da murmushi mai kyau, ya kafeni da ido ko ƙiftawa babu, nima hakan take agareni domin tunda na fara kallonsa na gaza ɗauke idona ko da na second. sautin murmushinsa ya fito har haƙoransa farare na bayyana, ya ɗan zoro min ido kaɗan yana ɗaga gira duka biyun. da sauri na sauke idona ƙasa cike da wata muguwar kunya, na fizge hannuna zan gudu ya kuma kamoni yana faɗin,"zo nan sai kin faɗa min mene kike yi da hotona?". gabana ya faɗi na ɗago na kallesa, ya sake ɗaga min gira yana cewa,"uhmm tell me, ai ina ganinki tun ɗazu, me yasa kike kalle min hotona? idan ba haka ba yanzu na shigar da ƙararki kotun Gwaggo". na hankaɗo baki gaba ina ɗan tirtirjewa nace,"wane yace maka hotonka nake kalla, to ni mene zanyi da hotonka da zan zauna ina aikin kallonsa bayan gaka a gida. na ma gane wayo ne kake son yi mani kuma naƙi wayon bazan dai nuna maka abinda nake kallo ba". na ƙarasa faɗa ina siririyar dariya me bayyanar da haƙora. shima dariyar waskewar da nake neman yi yayi, ban aune ba kawai naji ya fizgi wayar hannu, nan da nan kuwa na hau dukan ƙafafu kamar zanyi kuka ina cewa ya bani wayata kar ya buɗe min. na murguda baki ina cewa,"to ai dai ma baka san password ɗin ba, ni ka bani kayata bincike babu kyau". na faɗi hakan ina miƙa hannu zan amshe shi kuma yana kaucewa. kallona yay kawai yayi dariya kaɗan kana yace,"ki ƙaddara ban san password ɗin ba, amma idan na buɗe kyautar me za ki bani?". na ɗaga kaina sama ina nazari, tsawon daƙiƙa ɗaya nace,"shikenan naji in har ka buɗe ni kuma duk abinda kake so ka faɗa zan baka ko menene shi". na faɗi hakan saboda ina da tabbacin ba zai iya buɗewa ba, kusa da shi na tsaya ina kallon yanda zai buɗe ina masa dariya ƙasa-ƙasa. gani nayi yana rubuta Yayana, abinda ya matuƙar bani mamaki, taya akayi yasan password ɗina? bayan wayata bata taɓa zuwa hannunsa ba, kuma ban taɓa buɗewa agabansa ba tunda fingerprint nake amfani. muka haɗa ido ina masa kallo mai alamar tambaya da kuma tuhuma. na tsuke fuska na kama ƙugu ina cewa,"taya akayi kasan passowrd ena? wato ka jima kana ɗaukar mani phone kayi min bincike ban sa ni ba ko?". yanayin irin yanda yara ke rantsuwa yayi yace,"ni wallahi Allah ban taɓa ɗaukar maki waya na buɗe ba, kawai fa nayi guessing ne....to ni dai bama wannan ba tunda na buɗe saiki ba ni kyautar da kika ɗau alƙawari". ya faɗa yana sarƙe hannayensa ta baya. zanyi magana ya tari numfashina da cewa,"tsaya tsaya! tukunna ma kika ce mene za kiyi da hotona?, to yanzu mene wannan, gashi nan a wallpeper kuma gashi a screensaver. shikenan ma gano ki yarinya, wato kina kallona kowanne lokaci don ki cinye min kyawuna ya dawo kanki, saboda na fiki kyau, shine ma idan mun fita kike jin haushi idan ƴan mata na bina, to kuwa wannan kyan ƙwalelenki, ba za ki taɓa ƙwace min shi ba ki kashe min kasuwa". na kalleshi ina hararansa, na ɓata fuska na juyar da kai gefe ina cewa,"su ƴan matansu sune basu san kyau ba da har suke maka kallon me kyau, ni kam dana ke wise ai ban taɓa ganin kyan ba bare har ya burgeni...yanzuma Malaminmu ne yace mu zana mutumin da yafi kowa muni a duniya za'a buga shi a kafa hoton a gidan zoo, ni kuma ina shawara da zuciyata tace nayi drowing ɗinka, kaga ma na taimaka maka tunda kana jin daɗi ƴan mata na kallonka, kaga idan ka fita yanzu sai ake biyan naira biyar naira goma ƴan wahala suyita zuwa can suna ganinka". dariyar da ya bushe da itane yasa na juyo ina kallonsa cike da jin wani abu a raina da na kasa tantance menene, ya dage sai sheƙa dariyar yake babu ƙaƙƙautawa harda su tafa hannu yana kifawa, sai ya ɗago ya nuna ni da yatsa ya kuma kifawa ya tuntsire da wata dariyar. kamar na fashe da kuka don haushi, na juya zan tafiyata ya biyoni yana dakatar dani da cewar,"Malama dakata mana. kin manta da kyautata fa. ki tsaya ki bani sai kiyi tafiyar kije kici gaba da aikin zane na tunda na zama celebriry". "sai ka faɗi abinda kake so ai". ina faɗa ina murguda masa baki don duk haushinsa nake ji, na rufe ido ina ƙara tamke fuska ina hura hanci, kawai kuma sai kuka ya taho min lokaci ɗaya hawaye ya shiga sauko min. jinsa nayi ya

Please Login or Register in order to submit comment