Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka gaya musu karsu ƙara dawowa". "shikenan kun dai ji abinda tace, ku fara bata haƙuri kamin ku tafi". "Gwaggo kiyi haƙuri".
Suka faɗa tare. tayi musu kallo mai harara, tana nuna Haidar da yatsa tace da Baba, "kai Auwalu wancan yaron idan aikinsa ba mai ƙarewa bane a kusa to ka nema masa wani gidan ya koma can da zama, bana son ganinsa a gidan saboda bashi da mutunci". Ƙaramin tsakin da Yaya Haidar yaja duk sai da muka jiyo, Baba ya juya zai masa magana yaga har ya fice, Gwaggo na jijjiga kai tace, "kagani ko, sam bashi da mutunci. Banda Allah yasa a gabanka ne da zagayowa zaiyi ya bangaje ni tukunna yasa ƙwalelen kansa ya fice. Ɗan banzan yaro mai kama da alkaki sam baiyi halin ƙwarai ba, shi Sulaimanun zai zo ya same ni, naji idan akan hanyar daya ɗora shi kenan". Baba ya nemi wuri ya zauna, nai masa sannu da zuwa, yana kallon yanayina yasan faɗan Gwaggo da su Yaya Abba akaina ne. Gaisheta yayi yay mata sannu da gida, "yauwa". ta ansa mishi. "ya aikin naka?". "Alhmdl". sai naji yana cewa, "Gwaggo tun ɗazu kika ɗaga hankalina, da kika kira kika ce akwai matsala nayi gaggawar tahowa, lafiya dai ko?". "tun a lokacin da na kiraka mai ya hanaka dawowa?". ta faɗa muryarta na nuna ɓacin rai. "kiyi haƙuri ko a lokacin mun riga mun shiga meeting ne, to naso tahowa sai kuma naji kince na kwantar da hankali na amma dai na dawo gida, jin haka nace ba babbar matsala bace har na kammala komai ma". "to dama akan Sabina ne". Na ɗago da sauri ina kallon Gwaggo, gabana na faɗuwa, to ni kuma ƴar gidan Gwaggo na mai nayi. Baba naji yace mata, "me Sabina ɗin tayi?". tace da shi, "kaji na taɓa kawo maka ƙararta ne da zaka tambaye ni me tayi, to ita bata laifi salahar baiwa ce, ka dai ce me ya faru da ita". Baba ya haɗiyi yawu yace, "to mai ya faru da ƴar lelen taki?". "aljanu ne da ita". "aljanu kuma Gwaggo".
Baba ya faɗa yana zare ido, don maganar sosai ta dake shi. "ƙwarai kuwa, amma basu yi nasarar shigarta ba, sun dai shafeta ne, wancan fitsararran baƙon yaron shi yay mata ruƙiyya kasan Malami ne, ƙwaƙwalwarsa taf da haddar qur'ani amma babu tsoron Allah a zuciyarsa, amma haka dai na haɗashi da ita yay mata karatu da adu'oi, sannan ya fita cikin gaggawa yaje islamic chemist ya haɗo magunguna da turare aka haɗa mata, nan da nan cikin ikon Allah komai ya lafa. amma farko fellawa tayi da gudu, da ace babu mai gadi ma ba'asan inda zata nausa ba, nan ta faɗi tana aikin shure-shure da buge-buge da ife-ife. Ashe ajiye shirgegiyar mace ma acikin gida yana da amfani, don wannan ƙatuwar matar taka ita ta ɗaukota duk uban nauyin da suka sa Sabina tayi, don ni dana ɗaga hannunta ma banyi zaton hannun mutum na ɗaga ba...yau ai Ƙatuwar can tayi min rana". jin abunda ta ke cewa yasa na fashe da Kuka, gaba ɗayan su hankalinsu ya tattaro ya dawo gare ni, musamman ita da ta ke bada bayani. "me kuma aka yi miki?". ta jefo min tambaya. ina shashsheƙar kuka nace, "Gwaggo aljanu fa kike cewa ina da su, kinsan kuwa mene aljanu, na rantse ni lafiyata ƙalau". Wata harara ta jefa min kamin tace, "nufinki ƙatuwar mace da ni zan zauna ina gillawa ubanki ƙarya ne, to ribar mai zan samu idan nayi miki fatan wannan lalurar da ba'a so, mtswww shi yasa ɗazu nake gaya miki da ku masu aljanu da mahaukata ɗaya kuke, tunda duk bakwa sanin abinda kuka aikata a lokacin da kuke kan ciwo. To a faɗuwar da kika yi ɗazu sune suka zo, Allah shaidata, Haidar Shaidata, Matan gidan nan shaidata, a tou balle ace nayi ƙarya, ƙwamma na sanar miki gaskiyar komai kamin ki ƙullaceni a zuciya". Shiru nayi ina ci gaba da kukana, ƙasan zuciyata kuma ina tantamar anya Gwaggo bata fara daina ƙaunata ba. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Shine abunda Baba ke nanatawa cike da al'ajabi da kuma tsoro. "Sabina garin ya haka ta faru, me yasa kikayi sakaki da azkar?". "Allah ni Baba bana da wata iska, kawai dai faɗar gwaggo ce kuma ka kira shi Yaya Haidar ɗin ka tambaye shi, anyi haka ko ba'ayi ba, tare ma mukaje koyon mota, kuma har yanzu ma muna zaune da su shida Yaya Abba babu abinda ya sameni. Ina jin dai ko Gwaggo ta fara rikicin tsufa ne, shine ta fara rikicewa ta kaina". Ta kalleni ta jijjiga kai, "to ai kaji, itama ta hau sahun waɗancan fitsararrun yaran, amma ba laifinta bane ita zan mata uzuri, tunda yanzu ta zama ba ita ɗaya ba, adu'a kawai zan bita da ita, idan na fahimci kuma sune sai na hauta da duka". Ta kalle ni tace, "ki sami damar yimin shiru, Allah yasa a gaban ubanki ne bare kija ace zane miki jiki nayi, kin ɓare baki kina kuka mara daɗin saurare, Kefa dama haka halinki yake wani zubin, sam-sam ba ki da daɗin sha'ani". na kuma fashewa da sabon kuka na miƙe zan bar wajen. "dawo". Tace da ni. Na koma na zauna ina jin kamar nayi me saboda baƙin ciki. "to yanzu Gwaggo mene abunyi?". Baba ya tambayeta. tace, "abunyi shine ka tattaro min kawunan Matanka suzo nan. Don ina tantama da wannan Al'amarin, ni dai ba aljanu ba, kai ba su ba, uwarta har ta mutu babu wata alama data nuna tana ɗauke da aljanu, kai kafatanin dangina ban samu labarin wanda ke ɗauke da su ba, kaga kuwa bana gado bane. Bugu da ƙari shekarar mu nawa a wancan gida kamin mu dawo nan, babu wata alama da taɓa nunawa tana da mutanen ɓoye sai da muka zo nan. To da sake a wannan lamarin, su zo idan acikinsu akwai mai su sai ka kwashe su daga gidan nan, kuje can kai musu magani idan sun warke sa dawo. Idan kuma ma wani mugun ƙullin aka ɗaura to azo a warware shi anan, don wallahi aka kuskura na gano ture ne akayiwa Jikata ba za'aji da daɗi ba". Baba yace, "To amma Gwaggo ai a cikinsu kaf babu mai aljanu". a harzuƙe tace, "shine ai nace maka ka kirasu suzo koma wace acikinsu, to ta kunce baƙin ƙullin da tayi tun wuri, dan billahillazi bani da kyau, ni gaskiya ce nake faɗa babu ruwana. Kar na ɗau mataki kai tsaye ace nayi rashin kyautawa...dan kai kanka ba zaka ji da daɗi ba".


*Please Vote, Comment, and Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(14)*
*Monday Morning.*
kasancewar yau monday tushen aiki, kuma yau ɗin da izinin Allah zan fara ɗaukan lectures, dan haka tunda na kammala azkhar ɗina ban koma bacci ba shiri kawai na fara yi, kwalliya nayi sosai wanda ta ƙarɓe ni matuƙa musamman dana ɗora da medical glass ɗina, dama gani ƴar son kwalliya da ado, tabbas duk wanda ya kalle ni dole ya so kuma gani na. Tunda na fito parlo na kalla yanayinsa nasan Gwaggo bata tashi ba, saboda indai ta farka ta fito zata sa karatun ƙur'ani ta kuma saki turare. jakata da mayafina na aje kan kujera na wuce kitchen don samarwa kaina abinda zanci, dai-dai da zan shiga nayi karo da Yaya Haidar zai fito, da sauri naja baya nayi gefe a tsorace, Allah ya taimake ni ban tankwaɓar masa da tea cup ɗin dake hannunsa ba. Na murguɗa baki gefe don banda niyyar gaida shi, sai naji kamar na koma idan ya fita sai na dawo, sai wata zuciyar tace min kawai na tsaya na ƙara bashi hanyar wucewa, ina kallonsa ya wani haɗe rai yana jifana da harara, bai yi niyyar saurarena ba amma saboda neman magana yaja tsaki yana kallon kayan jikinsa kamar nayi masa ɓari a jiki. Ya ɗago ya kalle ni yana kuma hararata, ya ƙara jan tsaki yace, "ba kya gani ne da ba za ki iya lura da tahowar mutane ba". Na kalle shi kaɗan nace, "ai ban san da tahowan naka bane, kuma ina sauri ne". Tsaye yayi yana kallona ta ƙasan ido, "stupid girl". Ya faɗa yana ƙare min kallo ta ƙasan ido, ni dai zumɓuro baki nake ina alla-alla ya wuce, wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗauka yana waya, sai daya gama wayar kana ya bar wajen, nabi bayansa da murguɗa baki. Ni dana shiga kitchen ɗin ma rasa me zan dafa nayi, na duba agogon dake saƙale a wurin, lokaci ƙara tafiya yake kuma yau tara ne zamu shiga lectures, ga time har takwas tayi, na doki ƙafa a ƙasa, ko me fa zan dafa sai yaja min lokaci tunda ni bacin Indomie nake ba, ko da tea ɗin zan dafa it will take time too, tunawa nayi da Yaya Haidar zai fita da tea Kettle a hannunsa, da sauri na suri cup da spoon, na zuba madara da bounvita da nescape na fita, ina zuwa kuwa na sa me shi kan kujera yana kurɓan shayinsa, naje gabansa na tsaya ina sosa gefen kunnena. Ya saci kallona ya ɗauke kai kamar bai ganni ba, na turo baki gaba na duƙa gaban table zan zuba tea a tsawace yace da ni,"kee". Na ɗago ina marairaice fuska nace, "Please Yaya Haidar, Makaranta zan tafi and idan nace i will wait to cook something i will be late. tea ɗin da yawa, barinsa ma za'ayi tunda Gwaggo is not drinking". Na faɗa ina ɗaga kettle ɗin na jijjiga naji yawansa. "wallah idan ba ki aje min kayana ba sai na zabge ki da mari, ke kika dafa min da za ki zo kice na ba ki, mara kunya kawai ana magana kina turowa mutane baki, me zai hana ki jira Kakar taki tazo ta dafa miki, ko kuma ni sa'an kine da zan dafa abu kici". ya faɗa yana ƙara tamke fuska. Na aje ina ƙunƙuni ina cewa, "to amma ai dai a kitchen ɗin Gwaggo tah aka dafa". Ashe ya jiyo ni, hakan yasa yace, "an dafa a kitchen ɗin nata kuma baza'a bayar ba, bar min nan wuri ko kuma nayi ball da ke". Na miƙe na bar masa wurin, cikin raina ina faɗin mutum ba abinda ya iya sai shegen ci, tunda yazo gidan nan kamin kowa ya tashi zaka kalla ya tashi ya dafa abincinsa, kuma aikinsa kenan shan tea ko da rana ko da dare, sai kace wani balarabe. Kitchen na wuce na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na sauke na dama curstad, na fito na wuce dining nayi zamana ina shan kayana, Gwaggo ta fito ta sameni, tana kallona ta fahimci akwai abunda akai min. dan haka ta dakata daga gyaran ɗaurin zane tace min, "ke kuma me aka maki kike faman ɓata rai da sanyin safiyar nan? duk daƙe dama uwar miskilanci ce, ko ba'a taɓa ki ba iskokanki zuwa ɗaukar fansa suke". Na aje cup ɗin na ture shi daga gabana, daga tashinta zata hauni da faɗan da baya ma ta wahala. Taja ƙaramin tsaki tai juyawarta zata bar wurin tana cewa, "ke dai kika sa ni da halin nurƙufancinki da baida kyau, tashi na kenan ban bawa cikina ba, ba za ki sa ni magana ba". Na fara shashsheƙar kukan ƙarya nace, "to ba Yaya Haidar ba ne". Cak ta tsaya ta juyo tana kallona, "aina kuka haɗu da Haidar ɗin har kika masa rashin kunya, ban hana ki shiga sabgarsa ba, ina ce na miki faɗan babu ruwanki da shi ko". "ni fa ba sabgarsa na shiga ba, shine don nace ya sammani tea yaƙi, kuma nace masa na makara a school amma duk da haka ya hanani yace zai zabga min mari, yace naje na taso Kakartawa tazo ta dafa min". a wani sukwane ta dawo da dubanta kaina gaba ɗaya. "to shi aina ya sami tea ɗin bayan su ba kitchen garesu ba, kuma dai matan gidan nan basu isa tashi ba bare ace sun dafa sun bashi". "anan fa yazo ya dafa, na fito zan wuce na gansa ya fito daga kitchen". ta jijjiga kai kamin tace,"shi Haidar ɗin wai? Kai wannan yaro akwai baƙin hali, ruwan shayin da zai sammaki ba wata tsiya ba, ɗan ƙwal uba ina ce ma arziƙin ubanki yazo yake ci. tukunna ma ban ce masa kar ya kuma zuwar min sashena bane". "to dai ai gashi can yana kallo". Ta juya ta nufa inda yake, tana zuwa ta ƙarasa gaban socket ta kashe tv ɗin da yake kallon news ɗin da bai gajiya, ni nama rasa uwar me yake ji da news ko da yaushe, yana ganinta baice mata komai ba haka itama bata kula shi ba. Sannan ta kirani, ina zuwa tace, "kashe min wannan na'urar sanyin". Na jawo ƙaramin table na ƙara tsayi na kashe. Ita kuma ta ƙarasa taje ta janye table ɗin da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ƙafafunsa suka zube a ƙasa, ina kallon yanda ya cika yay fam ƙiris yake jira ya fashe, nasa hannu na toshe dariyar dake ƙoƙarin fitowa, tasa hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro handkerchf nasa sai tashin ƙamshi yake, ta shiga goge table ɗin daya ɗora ƙafafun nasa tana ta magana kamar bada shi take ba. "Haka kawai a dinga shigo maka wuri da sanyin safiya ko tashi baka yi ba ana takura maka. kuma ba taya aikin fari bare na baƙi, sai dai a hakimce a ware maka na'urar sanyi a kunna maka tv ana sauraren yaren da kai ba jinsa kake ba. Kuma Duk abi a zuba maka dattin ƙafa akan glass, ka yiwa mutum magana ya daina zuwar maka wuri amma saboda ba shida zuciya zuwa yaƙi ya daina, dole dai sai an saka magana, to na kashe kayayyakina kar na soma naji an ƙara kunna min kayan kallo". Maganar ta ke kamar bada shi ta ke ba, tana gamawa ta wurga masa hanky nasa. Ina dariya ƙasa-ƙasa naje kusa da shi na ɗauka mayafina da jaka ina cewa. "Gwaggo zan tafi, ai mana adu'a Allah yasa mu shiga a sa'a". "to kin ƙoshi ne? ko za ki sha shayi ga saura naji a cikin butar nan, ƙila wannan yaron ne ya dafa". Na kalla Yaya Haidar naga ya ɗago yay mata wani kallo, ran nan nasa a haɗe, kawai dan na makara ne amma ko dan na ƙara ƙular da shi da sai na sha, na cije Leɓena ina dariya nace. "a'a Gwaggo bana sha, na ƙoshi ai". "to shikenan yana da kyau na tambayeki ne. Saboda ni ba sha zanyi ba ƙarshe zubar da shi zanyi. ban san ma wane shishshigi ne yasa aka zo aka wani yimin girki a kitchen ba tun gari bai washe ba, kamar ka saka mutum, a dai dinga jin tsoron Allah almubazzaranci babu kyau. kuma wani abin dariya da takaicin kai ɗin dai da aka raina duk tsiya wurinka ake zuwa". ni dai kamar kar na tafi haka nake ji, idan kuga yanda Gwaggo ke magana zaku rantse da kanta ita ɗaya takeyi, saboda yanda ta nuna tamkar babu inuwar Yaya Haidar a wurin, shi kam ina da tabbacin a zuciyarsa ji yake inda ace yana da iko baiga me hana shi saka mata hannu ajiki ba. maganarta ta dawo dani daga tunanin sakanni biyun dana lula. "ki shige ki tafi Allah ya bada sa'a". na ansa da,"amin". Zan fita kenan Yaya Abba na shigowa, na gaida shi ya ansa min, ni kuma fice. Part ɗin Baba na wuce, Anty na samu a parlo tana jera masa kayan breakfast, ina zama kan kujera nake gaisheta, amma ƴar matar nan ko iskar da ta kwaso ni bata kalla ba bare nasa ran zata amsa min. nima na bawa banza ajiyarta, sai can dai dana ga zaman ba zai kai min ba nace da ita,"Anty ina Baba?". tace, "ba dai kinzo ɗakinsa ba, sai ki jira ki gani idan zai fito ko ba zai fito ba. Ni bana son kinibibi". ta faɗa tana wucewa ɗaki ta barni zaune anan, nafi minti goma zaune banga alaman Baba zai fito ba, hakan ya tabbatar min bata sanar masa da zuwana ba. Raina duk yay ba daɗi, na ɗauka wayana na kira Baba, ringing biyu kam ya ɗaga, yanayin da yaji muryana ya shiga tambayana ko lafiya. na kauda ɗacin dake ƙasan maƙoshina nace,"lafiya lau Baba, nazo wurinka ne kuma ban sameka a parlo ba". sai muryarsa ta far fita da sautin faɗa-faɗa. "a'a to wannan wane irin shirme ne, ba sai ki hauro saman ba. Tun yaushe kike nan a zaune?". Dan dai ban iya haɗa rigima ba da nace masa Anty tasan da zuwana, to amma saboda bana son ɓacin ran Baba kuma ni bana so naga ana fitina acikin gidan sai kawai nace masa,"tun ɗazu ne, kuma zan tafi school ne gashi harma na makara". "sorry my daughter gani nan bara na sakko". Ko minti biyu ba'a ƙara ba sai gashi ya sakko, ya zauna kan kujeran da nake, kaina na ƙasa yasa hannu ya ɗago da fuskana, ganin idona ya ciko ya ɗaga hankalinsa. "whats wrong?". Ya tambaye ni. na girgiza masa kai alaman ba komai. "no no ba kya min ƙarya fa". Ina goge guntun hawayen daya sakko min nace, "ban ganka bane". nai mas aƙaryar hakan, wanda a haƙiƙanin gaskiya a lokacin ina kewar mahaifiyata ne, sai Yay murmushin manyance yace, "rainon Gwaggo sarkin shagwaɓa, to yanzu gani me kike so?". Dai-dai lokacin da Anty ta ƙaraso da tea flask hannunta, ta aje kan dining sannan tazo ta zauna itama, tana murmushi ta ke ce min. "Ƴar gidan Babanta har an fito, yau za'a fara shiga makaranta ko, to Allah ya taimaka a maida hankali sosai kinji, banda wasa don Allah, abinda aka je yi shi kawai za'ayi". Tsabar mamaki kasa ce ma ta komai nayi, nai kamar ban jita ba don kar ma Baba yace wani abun. Nace da Baba, "dama zan wuce makaranta ne nace bari nazo na gaisheka". "oh yaune fa za ku fara taking lectures ko, eyyah sorry dear na ɓata maki lokaci". Ya zaro 2k a aljihu ya bani, na amsa ina sambaɗa masa adu'a da kuma godiya. Nace masa ko zaisa Yaya Abba ya kaini, idan naje yau naga yanda yanayin school ɗin namu sai na fara zuwa da nawa motan. Ya kira Yaya Abba a waya yace masa ai yanzu ya tashi ko wanka bai ba. "ina Haidar fa?". Ban san me Yaya Abba yace masa ba naji yace, "to kace masa ya fito ya kai Sabina makaranta, yay sauri tayi late". Mu kai Sallama da Baba na tashi zan tafi, Anty tace, "Sabina tsaya kisha tea mana nasan ba lallai kinyi break ba". "na ƙoshi". nace da ita ataƙaice. cike da ƙwaracewa na kissa tace, "a'a ni dai nasan ba ki ƙoshi ba, saboda ba ki ci komai ba tunda ban kai muku ba, ki daure kizo ki zauna ga plantain nan kici ko kaɗan ne, ba kya tafi makaranta a haka ba". Shi dai Baba wayarsa yake dannawa, ni kuwa mamakin kisisinarta nake. ta kuma cewa, "to ko na zuba miki a flask ne sai ki wuce da shi?". Ƙaramin tsoki naja, na ɗaga kai na jefa mata harara nai tafiyata. sai ga su Aisha sun shigo, suma jikinsu sanye da uniform, Zainab da Khadija ne kawai suka gaida ni, amma Aisha da Amina da suke ganinmu kai ɗaya kallo ɗaya suka mani suka ɗauke kai suka wuce inda Baba ke zaune. Kuɗin makaranta ya basu, ina ji kuma yana musu faɗan latti da suke kullum. Suka bashi haƙurin kan zasu daina. Aisha tace, "Baba yau Umma bata da lafiya tace ba zata iya kaimu ba, sai dai ko Anty ta taimaka mata ko kuma kasa Yaya Abba". Anty tayi karaf tace, "a'a ga Haidar nan zai kai Yayarku, sai ku tafi tare ya saukeku". Baba yace, "ehh hakan ma yayi, kuje Allah ya bada sa'a". A bakin mota muka tsaya muna jiran fitowarsa, ni dai kamar na haƙura da binsa na hau motana kawai na wuce, tun fa ɗazu Baba ya kirashi ko shirin me yakeyi ai yaci ace mun fito mun same shi ma yana jiranmu, kuma duk dan ni zai kai ne shi yasa yake wannan delay ɗin. "Yaya anya kuwa Yaya Haidar yana nan. Kalla fa morethan 5minutes muna tsaye nan muna jiransa bai zo ba. Ni kam yanzu ma nasan an rufe gate". Khadija ta faɗa kamar zata yi kuka, da yake itane autarmu. Har na taka ƙafana zan bar wurin sai gashi ya fito yana gyara zaman hularsa, fuskar nan a ɗaure babu alaman kawo wargi, sai wani takun ƙasaita yake kamar jinin sarauta, na taɓe baki na harari inda yake, ya ƙaraso ya buɗe motan, na buɗe da sauri na shiga. Ya duba su Aisha dake ƙoƙarin shiga yace, "ku kuma fa?". "Baba yace ka aje mu a hanya".
Amina ta bashi amsa, ya wurga musu harara ya shigo cikin fushi ya figi motar, Allah yasa na rufe ƙofar da ba abinda zai hanani faɗawa waje. su muka fara saukewa tukunna muka wuce tamu makarantar, sai daya raba tafiyar biyu naga yaja yay parking, ya kashe motar yana danna wayarsa, naga bashi da alamar ci gaba da tafiyar na kalle shi nace, "Yaya Haidar ya dai, ko wata matsalar ce ta sami motar?". Shiru yay min kamar bada shi nake ba, sai dana ƙara magana a karo na uku tukunna ya juyo a fusace yace, "Get out". Na tsaya ina kallonsa, zan kuma magana ya doka min tsawa, "ba za ki fita ba". Na buɗe motar na fice, dama jira yake ina fita ya figi motarsa ya buɗe ni da ƙura. Na samu na tari mai napep ya ƙarasa da ni. Yau na kuma yarda da cewan karatun university bana wasan yara bane, sai na tuna Farhana tah da idan ta dawo tana min complain nayita ce mata raguwa, ita dai bata son karatun ne kawai. Ashe abin ba haka yake ba, lectures uku muka yi ayau kuma duk masu zafi, Har sai dana ji dama ba Accounting na zaɓa ba. Ƙawar da nayi Asma'u tai dariya tana cemin, "to ce miki akayi sauran courses ɗin sauƙi gare su, kowanne da irin nasa wahalar, ke dai Allah ya bamu sa'a kawai". "kuma fa haka ne". Na faɗa ina zura sauran littafaina a jaka. Nace ma ta, "muje ko". Har titi muka zo ni da Asma'u, Anan ne muka rabu, ta hau mota ta wuce ni kuma na tsaya jiran wani, saboda hanyanmu ba ɗaya ba. Sai dana jima tsaye rana duk ta gama zane ni sannan na sami taxi na hau. A matuƙar gajiye na dawo gida, ina shiga parlo nai wurgi da jakata na haye kan kujera dan ko ɗaki bazan iya ƙarasawa ba, takalman ƙafata ma ban cire ba. "Lazy lazy".
Yaya Abba yace da ni cikin sigar tsokana. "Yaya Abba wallah ba wani zancen Lazyness, kaga wuyan da muka sha kuwa, Allah ya haɗamu da wani lecturer mara mutunci mugu harda mana test". "to yace ko kinyi abin arziƙi?". "ahh na rubuta masa abinda na iya, na bar masa wanda ban iya ba. Allah tun ƙwaƙwalwata na ɗaukar komai har nazo na daina kwashewa". "dagewa za kiyi yarinya. Karatun bana yara masu lalaci bane". Nai murmushi kawai na juya na gyara kwanciyata, kamar an tsikare ni na zabura na miƙe, na duba Yaya Haidar wanda ke kwance shima kan kujera, na sauko na buɗe jakata na ɗauko littafina na nufi wurinsa. "Yauwa Yaya Haidar kaine kayi Statistic, Please help me to solve this". Kamar bada shi nai maganar ba, "Yaya Haidar please mana". Ya kuma share ni. Na miƙe da sagaggiyar gwiwana zan tafi sai kuma yace, "lem me see". na dawo da ƴar murnata na miƙa masa yace, "i dey hear you; readout". ya faɗa ba tare daya dubi ko inda littafin yake ba balle ni. ina waro ido waje nace, "tabɗi ai bazan iya karantowa ba, wasu numbers ne fa a watsaltsale". sai ya

Please Login or Register in order to submit comment